A DAREN FArko
kotun ta yi tsit, kowa ya yi jigum, ana sauraran abinda xai fito
daga bakin alkalin wanda yasunkuyar da kansa yana rubuce-
rubuce.
Lauyoyi dasauran ma,’aikata wadanda suke da alhakin zama a
kotun sbda sauraron shari’ah, kowanne yana xaune a
mazauninsa daya dace dashi,haka yan kallo da iyayen yarinyar
da ake gudanar da shari’ar a kanta al’amarin yan ba kowa
tausayi shiyasa indai mutum yakalli fuskokin kaso tara cikin
goma na mahalarta kotun sai kaga kowa cikin matsananciyar
damuwa musamman wadanda abin yashafa, iyayenta da yan
uwanta knan.
Mai shari’ah usman muhammad yadaga kansa a hankali
yadubi wacce ake ka ra tana tsaye inda ake tsaida wadanda
ake tuhuma hannayenta biyu sanye da ankwa.
Bakar rigace a jikinta da bakin hijjabi sanye akanta, ba
dankwali idanuwanta sunyi wani irin ja saboda tsabar kuka, ba
ta son dago kai tadubi kowa saboda tsanar kanta datayi don
haka ma da alkalin yakira sunanta bata dago kanta ba ta dai
amsa cikin dashashiyar murya wadda da kyar ake iya jin
abinda ake fada.
Alkalin yakuma cewa “Fatima Musa”
Ta amsa “Na’am”
“Ke kika kashe doctr Abubakar saddik wanda akafi sani da
doctr khalifa???
Fatima tayi shiru alkali yana maimaita tambayar har sau uku
batayi magan ba, yadda kasan kotun ba kowa saboda tsabar
shiru, koda fatima da mai shari’a yake kallo ana sauraron
abinda fatin xa tace amma taja bakinta tayi shiru kamar dam
chan yadda Llah yahalicce ta ba ta da bakin magana.
Mai shari,’a Muhammad Bamaina yana magana cikin yanayi na
tausasa harshe yace “Fatima kotu tana tuhumarki da laifin
kashe mijinki Dr. Khalifa kamar yadda ka kamaki da gawarsa
shiyasa muke son ki bayyanawa kotu gasjiyar al’amari da
bakinki tunda ke ba bebiya bace kuma ba kurma bace kina jin
abinda muka fada kuma kina iya magana.
idan ke kika kashe shi kifadawa kotun sannan kifadi dalilin
dayasa kika kashe shi, idan ba ke bce ba to kidanyi magana
kiyi bayani.
Fatima tadago kanta a karo nafarko tadubi duk jama’ar kotun
suka hada ido da mahaifiyarta wadda tazuba tagumi dukda
nisan dake tsakaninsu da Fati, Fati ta san kuka take wiwi tana
girgiza kai, Fati tadubi mai shari’a sai kawai taj kanta yana
juyawa kafafunta suka shiga rawa, hakan yasa suka gaza
cigaba da daukar gangar jikinta tazube a gun, nan take mai
shari’a Usman M Baina yadaga shari’a zuwa uku ga watan
gobe idan Allah ya kaimu.
Kotu tarude da hayaniya, koke koken iyayan fati da yan uwanta
ya cika kotun ga uar uwarsu a matsananciyar hali amma ba
yadda xa ayi su taimaketa, sunaji suna gani wasu yan sanda
mata suka daga fati aka fice da ita da gaggawa sbda
numfashinta ne yake sama saa kamar zai dauke.
*******×*×***********×***×******×**
Yammaci ne akalla za mu iya kiran lokacin karfe biyar na
yamma dawasu mintuna, ummi na zaune gefen tabarma ta
hada kai da guiwa tana kuka kamar ranta xai fita, goggo Abu
ne gefenta itama tana goge hawaye cikin yanayi na tsananin
damuwa kobaka sansu ba kaga halin dasuke ciki sai ka tayasu
wnnan kuka dasuke, ko ba a maka bayani ba ka san damuwar
daxata sa a yi irin wannan kuka ya isa a tayashi kuka.
Malam musa yashigo da carbi a hannunsa yayi sallama
yatsaya chan daga bakin kofa yana kallonsu tsawon mituna
biyar sanan ykaraso inda suke ,Allah sarki bawan Allah mai
saukin kai wanda bai dauki duniya a bakin komi ba, fuskarsa
cike da tausayi da karaya yake kallonsu ya ka sa magana, xuwa
chan goggo Abu tagoge hawayenta cikin karfin hali tace
“Malam ka dawo?? sannu daxuwa.
Ya daga mata hannu yace ba na son gaisuwar ta kui tunda
idanuwanku baxasu daina xubda hawaye ba akan abinda ba xai
yi mana amfani ba. kokuwa wannan kukan xaiyi mana magani
akan damuwar damuka samu kanmu aciki??
Goggo Abu tace “Mala to yaya xanyi tunda abinnan yfaru ummi
bata daina kuka ba. na yi lallashin duniyar nan yarinyar nan ta
ki daina kuka har na rasa wacce kalma xan gaya mata wanda
xa yasa tayi hakuri.
Malam yace “Ummi kiyi hakuri ko mu damuka haifi fatima babu
abinda xa mu iya akan wannan lamarin sai dai addu’a.
Cikin matsananciyar damuwa Ummi tace “Shin baba shikenan
daga hakuri babu abinda xa ku iya gaya min wanda xan samu
sassauci a xuciyata game da halin da fatima take ciki???
Wyyo Allah kaicon rayuwata ni ummi in har xan xauna ina
rayuwa a cikin tunannin fatima na kulle a kurkuku ana
tuhumarta da laifin dani daku daduk duniya sun san baxata
taba iya aikata shi ba.
Ya ya xa ayi ace fatima xa takashe rai, kisan ma ace tarasa
wanda xa takashe si mijinta? kadubi wannnan al’amari ayi wani
abu akai har yaushe muna zaune fatima na cikin mummunan
zargi irin wannan”.
Malam. musa yai xaman dirshan a wurin yace “Ummi toh yaya
xamuyi? Saboda girman Allah me kike ganin xa mu iya yi
kinsan indai ace muna da bakin yi din da yanxu ba wannan
xancen akeyi ba.
kinsan mudai ba kudi garemu ba, kuma ko idan mutum na da
kudi idan akace case din me xafi ne da tsanani irin wannan ba
ka da tacewa, kudinka ba xa suyi amfani ba dan ba xa su sayi
ran da aka kashe ba balletana kasiya domin ko da ke biyan
diyya idan wani yakshe wani ba a irin wnnan yanayin ake biyan
diyya ba kinsan ita shari’a sabanin hankali ce, duk yadda kaje
tunaninta ta wuce nan.
Kuma idan ma muna da abin yin a yanxu ba xa mu iya ba idan
Fatima ba ita takashe docta Khalifa ba tai magana man a kotu,
kinaji kina gani daxu a kotu ka sa magana tayi ,tayi shiru
tabude bakinta tace ba ita takashe shi ba tafdi yadda abu
yafaru akalla idan ma akwai abinda za a yi ai a yi tunda tayi
shiru me za ace??
Yagirgiza kai cikin dan zuciya yace “Allah kadai yasan yadda
wannan abu yakasance sai kuma fatima.
Ummi taciji yatsa har yanxu kuka take mai ciwo a rai tace “Shi
kenan baba shikenan goggo tunda kuma kun yarda fatee ita
takashe doctor sai kusa ido itama a kasheta ba tare da
hakkinta ba, amma dai inaso kusani ko ku kuka haifi mutum to
ba kune kuka halicceshi ba yadda kake da hakkin yayi ma
biyayya haka shima yanada hakinsa akanka idan kadanne Alah
subhanahu wata’ala xai tuhumeka baba.
Nikam ba xan bar maganar fatee tawuce haka ba ,ba xan bari
acigaba da xalintarta akan abinda bata aikata ba, zan shiga
infita ko xan rasa zanin daurawa sai na taimaki Fati Insha
Allahu.
Malam yace ummi ba na shakku akan abinda kika fada mun
tabbatar xa ki aikata fiye da abinda kik fada akan fatima
kaunar dake tsakananin ku ya wuce a fadadeta da baki, Allah
kadai yasan iyakacinta, sai dai inason kisani ba wai mun yarda
cewa fati itace ta aikata kisan ba, kifahimci wani abu day
ummi ba mu da kudin daxamu iya daukan lauya daxai kare fati,
ba ki da bukatar mugaya miki halin damuke ciki na kaka ni ka
yin rayuwa a gidannan kinsan kome da ina mukaga halin
daukar lauya sannan idan ma mun dauka dawacce hujja xa
mufidda fati daga wannan zargi tunda ta ki magana? wannan
shi ne a dalilin dayasa muka mikawa Allah lamuranmu, idan
fati ba ita takashe likita ba insha Allahu Llah xai bayyanar da
gaskiyar alamari Allah xi kawo mana mafita.
Ummi duk wanda na sa yashiga matsanancin hali irin wannan
ya gama kwanciyar hankali kada kidauka bamu dmu da ita ba
illa iyaka shi lamari irin wannan idan kaga kanka acikinsa ba ka
tsananta damuwa wadda ita dama rayuwa jarravawa ce
acikinta, idan Allah yajareba ka dawani alamari kagode masa
kawai karokeshi yabaka juriyar cin wannan jarbawa dayayi
maka domin ba wanda ya isa yakaucewa jarabawar Ubangiji .
kiyi hakuri ummi.
Ta jinjina kai yace “Na hakura baba, na hakura dakuka na
hawaye, tunda ba ka son ganin hawayen saidai ba xan iya
hakuri da fati ba ko da nima xan shiga halin datake ciki, ko
nima xan rasa raina, idan ba halin daukar lauya ai muna da
halin daukar akwai guraren da ake taimako a samu agaji su
taimako ne a gabansu kawai a gabansu ba kudi ba, su ake kira
gatan mara gata”
Goggo tace”Allah shi ne gatan mara gata shi xai xama
gatanmu, Ummi kiyi hakuri”
Tayi murmushin karfin hali tace goggo nakanyi mamakin masu
cewa inyi hakuri akan maganar fati, wa yace banyi hakuri ba?
Tabbas na yi hakuri domin na hakura daduk wani farin ciki
Insha Allahu akan nemawa fatee hKkinta sai inda karfina
yakare ko da hakan shi xai kasance abinda xan aikata
nakarshe a rayuwata”.
***********************************
Suna a wani dan daki mara girma Ummi da Barrister Nuruddin
,aka bude kofar dakin wani kakkauran dan sanda ne a gaba
fuskarsa ba fara’a, fati na biye dashi a baya kamar kamar
koyaushe bakar rigar nan ce ajikinta da bakar hijabi kai ba
dankwali ta rame sossai ta yi duhu idanuwan nan kamar gauta
saboda jan dasukayi, hannayenta biyu cikin ankwa, wani dan
sanda a bayanta saidai shi fuskarsa akwai sassaucin ra’ayi.
Fati tadubi ummi tayi murmushi cikin dasasshiyar muryarta
tace “Ummi ku ne?
Dan sandan yace “mintunanku ba su dayawa ku gaggauta yin
abinda yakawoku dan kar kuyi asarar lokacinku”.
Ummi tagirgiza kai hawaye wasu na bin wasu ta ta so tadafa
kafadar fatima tace “sannu Fati da izinin Allah zai kawo mana
mafita a cikin alamarin nan, mun shiga tashin hankli da dmuwa
akan halin dkike cki fati inajin ciwon damuwarki kamar
xuciyata xa ta buga sbda tashin hnkali.
WNnan shine barrister Nuraddin Mustapha,na daukeshi ne dan
yazamo lauyan dazai kare ki a kotu. Fati inaso kibamu hadin
kai duk tambayoyin daxai miki ki bashi amsa sannan idan anje
kotu a zama nagaba kibude baki kiyi magana.
Fatima tayi murmushi hade da hawaye tace “Ummi bansan
dawani kalamai zanyi amfani gun gode miki ba ,komi nafada
ba zai wdatar dxuciyata ba hai inji cewa na nuna miki godiyata
kan soyayyar da kikemin dakuma kokarinda kike don ganin kin
ceci ryuwata daga wahala.
Saidai inaso kifahimci wani abu duk yadda kaso yankewa
mutum wahala idan Allai bai kaddara lokacin yankewar
wannan wahala ta sa ta yi ba ba za ka iya yanke masa ba. na
godewa Allah daya kaddara min shiga wannan hali ina fatan
wannan jarabawar da Allah yayimin tazamo kaffara agareni,
ummi inaso kisani ban tsananta bakin ciki akan halin danake
ciki ba ni a karan kaina wannan kukan dako dayaushe za aga
idanuwana na yi inayinsu ne sbda tausayin iyayena daku yan
uwana a Bisa halin dxaku shiga ba bakin cikin halin dana tsinci
kaina a cikinsa, dkuma uwa uba rashin mijina wanda xuciyata
ba ta da juriya akan wadannan abubuwa biyu, wannan
damuwar ba zanyi kuka ba inhar akan halin danake cikibne.
Zaman danake ummi ina jiran ranar da za ayanke min
hukuncin kisa ne inbi mijina. idan har akwai taimakon danake
da bukata daga gareku ayanxu shi ne ku taimaka ayanke min
hukunci inhuta wannan damuwar kuma kuhuta domin idan an
kasheni kun daina ganina dole watarana kuhaura idan ko ina
raye haka xa kuyi taxama cikin damuwa.
Wannan shi ne dalilin dayasa naki magana a kotu kuma ina
nan akan bakana na ba xance komai a kotu ba don ba ni da
abin cewa duk abinda xan furta bai wuce ince ba ni nakashe
doctor ba, idan nace ba ni nakashe shi ba in neman kariya
knan wadda e nufin inci gaba da rayuwa alhali ni kaina banga
amfanin rayuwata a duniya ba.
Umi kiyi hakuri kiba iyayena daduk yan uwana hakan kirokar
min su gafara kowa yayi hkuri yamanta dani ba na bukatar
taimakon kowa agareku sai addu’a, na gode kwarai dagaske
kada kisake wahalär dakanki gun dauko min lauya…….
Ummi takatseta cikin huci tace “Fatima kin amince kidauki
laifin daba na ki ba, kin amince kikashe kanki,? wayake kin
taimako kin amince kijawa dukkan zuri’arki abin fadi?
kina zaton wannan ba zai zama mugun aibi ga zuriarki ba?
wanda xaija adinga aibata muku zuri’a mata surasa mazajen
aure?
Kina zaton idan ankashe ki wani zai sake zama lafiya acikin
iyayenki da yan uwanki?
To kisauya tunani lauya tunda kince ba kya so na janye shi,
amma ko shakka babu kuskure ne babba wanda xa kitafka idan
har kikayi ikirarin kece kika kashe docto khalifa alhalin ba ke
kika kashe shi ba.
Fatima tace toh idn ni nakashe shi fa ummi?
Ummi tayi murmushin takaici tace ba ke ce kika kashe docta
ba, dankuwa ba ki da dalilin kasheshi, kina fadin hakanne
kawai dan kin gaji da duniya ba kyason rayuwa a halin da
kinason ki gaggauta barinta, shiyasa kike furta abinda xai raba
ranki da gangar jikinki”.
Dan sanda yace “Lokaci ya yi”
Ummi tace kayi hkuri ina fada mata abinda xai amfaneta ne.
Yace ba shi da amfani gareta da saita karba kidaina wahalar
da kanki.
Ya tisa keyar fatee, kallon data waiwayo tayiwa ummin tawuce
shiya sa tsigar jikin ummi tashiga tashi tazube a kasa tarika
kanta da hannu bibbiyu.
Shi kansa barrister nura jikinsa ya yi sanyi, ya jima xaune agun
yana kallon ummi daga can yadan ja numfashi yace “Tashi
mutafi ummi tun anan na tabbatar yarinyar nan fati ba ita
takashe docta ba dukda Cewa ta ki amincewa daduk wani
taimako daxa abata ta rufe duk wata kofa takariya daxa a ba
ta, bawani abune kuma yasatayi hakan ba ta yi ne kawai sbda
bakin ckin dake damun xuciyarta wanda yake tafarfasa
xuciyarta yasa rayuwa tafita a zuciyarta.
Hakan yasa taki mgana a kotu sannan taki yarda da taimakon
da za a ba ta, ba komi Llah yana tare damasu gaskiya, sannan
ba ya goyon bayan zalinchi, indai ba ta da hakki dasannu xa
kiga hukuncin da Allah xaiyi. ”
Ummi bata kuma cewa komi ba har suka fice daga gun.
[5:07PM, 7/13/2017] ‪+234 706 196 7803‬: A DAREN FARKO
2
dasauri yagoge hawayen dake zuba a idonsa jin sallamar
matarsa, goggo Abuwa tazauna sharaf a gabansa jikinta na
rawa ta ajiye flask d’in abincin datazo kawo masa, yadda
jikinta ke rawa haka muryarta take rawa, tace “Innalillahi wa
inna ilaihir raji’un malam kuka kake?
Yayi d’an murmushi yace “haba dai kuka ba kuka nake ba
Zainabu. ”
Tace “Dom Allah karkace haka malam bayan na gani da idona
kana kukan kuma na ji shasshe’kar kuka, malam idan kayi kuka
akan wannan al’amari mu kuma yaya za muyi da ranmu?
Kai kake nuna mana muyi ha’kuri bisa fushi dayin Allah me zai
sa kai kayi. ”
Malam musa yace “Zainabu al’amarin nan yana matu’kar bani
mamaki da d’aure min kai, ya ya za ayi fati ta iya kashe
mutum? idan munce ba ita takashe shi ba wa ne yakashe shi?
alhalin da Ita sai shi a gidan d’akin a rufe da sakata taciki.
Meyasa fati takashe Dr. khalifa me yayi mata?
Meye iyayen khalifa basu yimana ba? shi kansa khalifan meye
bai yi mana ba? Ace fati tarasa tukuicin dazata saawa wad’an
nan bayin Allah saida wannan mummunan aikin? ”
Goggo Abu tace “malam ka yarda fati ita takashe Dr. khalifa?
Yace “to zainabu idn a ita bace waye? daga ita sai shi a d’aki
yashiga yarufe ‘kofa shi zai kashe kansa ne zainabu? ”
Tayi shiru na lokaci mai tsawo, daga bisani tajinjina kai tace
“ko shakka bbu acikin wannan al’amari akwai rikitar da
‘kwa’kwalwa sannan duk wanda yayi wannan aikin wanda
yasan sirrin gidan ne, tabbas fati ba ita takashe dr. khalifa ba
don ba ta da dalilin kashe shi ko tanada dalilin kashe shi ba ta
da ‘karfin halin dazata aikata wannan mummunan aikin, saboda
zuciyarta tanada sau’ki akan al’amura, Allah kad’ai yasan
yadda al’amarin nan yakasance. ”
Cikin sanyin murya malam yace “Zainabu nima abinda yake
damuna knan kowa ma haka yake fad’a su kansu iyayan khalifa
haka suke cewa basu yarda fati takashe shi ba, to amma
meyasa ba za tayi magana akotu ba idan akaci gaba da tafiya
a wannan hali za asamu mafita ? Tunda ba ita bace tayi
magana mana ”
Goggo tace “wannan shi ne abinda yadamu kowa ma ba kai
kad’ai ba malam. ”
************************************
Kasancewar mahaifin marigayi Dr. khalifa babban mutum,d’aya
daga cikin masu fad’a aji a cikin gwamnatin garin yabasu
damar ganin fatima cikin isashen lokaci batare da tsayawar
‘yan sanda ba, ko kuma ankwa. Alhaji Muhammadu Nazif
mahaifin marigayi Dr. khalifa da hajiya maijidda mahaifiyarsa
suna zaune a wani babban d’aki da aka ‘kawata da kujeru,
Malam musa da goggi suna zaune gefensu sai babban wansu
fatima dakuma ummi da Barrister Nuraddeen, fatima na
tsakiyarsu kanta a ‘kasa ba kuka takeba su d’in ne baki
d’ayansu ke sharar ‘kwalla sakamakon matsanancin tausayi da
bayanin datake furtawa yabasu Alhaji muhammad yace
“Fatima abinda nakeso kigane shi ne dukkanmu nan mun san
ba ke kika kashe Dr. khalifa ba sbda kamar wanda zaiyi kisan
kai ya fita daban, ko da auren dole akai maki dashi ba za ki iya
kashe shi ba balletana anyi auran nan ne da amincewarki, ke
yarinya ce mai biyayya ga iyayenki, wadda kike zaune dakowa
lfya kowa na yabon kyawawan halayenki tayaya za ayi Muyarda
kin kashe Dr. khalifa.
Ki bud’e bakinki fatima nan ba kotu bane mu ba lauyoyi bane
mu iyayenki né duk duniya ba wanda kike dashi wadanda suka
fimu idan rufin asiri ne ba rufin asirin dayafi na Allah, ba wanda
zai rufa miki asiri bayan mu, kigaya mana saurin lamari waya
kashe Dr khalifa ??
Falon yayi tsit kamar ba kowa sai ‘karar A. C ko motsi fati
batayi ba ballantana tabasu amsa, malam yace “fati dame
muke magana kigaya mana yadda akayi idanma ke kika kashe
khalifa ya ya za muyi dake ? khalifa dai ya mutu kuma ba zai
dawo ba, fad’a mana gaskiya shi yafi dacewa, kullum
hankalinmu a tashe yake fati ba mu da sukuni idan mun
kwanta don muyi bacci bacci ba ya yiwuwa, abinci ba ya
ciyuwa, muna cikin matsananciyar damuwa ,bansan dawani
ido zan kalli iyayan khalifa ba, bansan da wanne ido zan
cigaba da kallon ‘yan uwansa ba damutanan unguwa, ba wani
abu ne ma ba fatima shirun dakikayi har yau baka fad’i Wata
magana wadda za a kama ba akan maganar nan kin mana
adalci, dukkan ‘yan uwansa da masoyanki kowa yana cikin
damuwa. ”
“Ni na kashe shi baba. ”
Akayi tsit kowa yazuba mata ido, maijidda kallonta kawai take
ta yi tagumi d’ansu da suke mutuwar so khalifa ta sake
rushewa da kuka,
Goggo Abu tace “shikenan tunda kince ke kika kashe shi to
lallai ne kidaina wahalar da mutane idan anje kotu kifad’i dalilin
dayasa kika kashe shi, kin san ba wai kice ke kika kashe shi
kiyi shiru ba dole ne kifad’i abinda yasa kika kashe shi.
Ummi tari’ke hannun goggo tazaunar da ita tace “goggo me
mye amfaninki yi hushi da fati alhalin kowa anan ya san takura
matan da akayi da maganar nan yasa tace Ita takashe shin to
haka idan ma akaje kotun aka takura Mata abin da za tace
knan ‘karshe idan tace ita takashe shin dole tayi shiru tunda ba
ta da dalilin dazata fad’a wanda yasa takashe shi. ”
Goggo tace “shikenan ummi haka za muyi tazama cikin
damuwa tunda ba ita takashe shi ba idan anje kotu ta fad’i Iya
abinda tasani mana. ”
Fatima tana kuka tace “kiyi ha’kuri goggi ba’kin cikin damuwar
danasa ku ya fi damuna fiye dakowa sai dai ba yadda zanyi,
goggo ba zan iya cewa ba ni nakashe Dr. khalifa ba sbda gaba
d’aya bayanan sun tabbatar dacewa ni nakashe shi.”
Kuyi ha’kuri shirun danayi a kotu wannan shi ne abin da yafi
damuwa na, idan nace zanyi magana bansan abinda zan fad’a
ba ‘karshe dai na san duk abinda shirun na wa zai haifar bai
wuce a yanke min hukuncin wanda yayi kisan kai bane a kashe
ni.
To dama abinda nake jira knan, ni kam rayuwa ta ‘kare a guna
sai dai sai dai jiran lokaci ko ba’a kasheni ba ba’kin cikin
halinda iyayena kuka shiga a sanadiya ta da ba’kin cikin rashin
mijina shi zaisa zuciyata tabuga in mutu ba zan iya cigaba da
rayuwa ba shi yasa ba na bu’katar taimako tako wani fuskar
lauya don ku’butarwa idan akwai abinda nafi bu’kata bai wuce
addu’a ba, wannan ba sai na ro’keku ba na san kuna yi min.
Dan Allah kuyi ha’kuri kuyafe min babu abinda zan iya cewa a
kotu.
Aliyu yayan fati yayi mgana a karon farko tun zamansu a
d”akin yace “fatima bamu amince kici gaba dayin shiru a kotu
ba dole kiyi magana. ”
Tace “shi knan yaya zanyi magana.
Alhaji muhammadu dakowa yafi sani da, abba yace “kar kice ke
kika kashe shi fati”.
Tace “Abba idan nace ba ni nakashe shi ba waye? idan kuma
akayi bincike aka gane ni d’in ce abinda ake gudu shi zai faru,
kuna fad’in hakane don fa kusamar min mafita wadda za ta ba
ni damar ci gaba da rayuwa a duniya, yayin da ni kuma ba na
son rayuwar ta fita daga raina so nake na mutu na bar duniya
yadda mijina yabarta. ”
Aliyu yace “Anya fati baki samu ta’bin hankali ba? ”
Tace “lafiya ‘kalau nake yaya “.kowa yarasa abin fad’i a kayi
shiru.
*********************************************
*********
Da sassafiyar ranar daxa a koma kotu hajiya maijiddah da
akafi sani da mama tana kwance kan faffad’an gadonta na
alfarma tunani da ba’kin cikin duniya ya isheta tarasa abin dake
mata dad’i, tana mutuwar son D’anta an kashe mata shi wata
‘kanwarta dake tayata zama wato anty sadiya tashigo d’auke
da abincin karin kumallo tazauna kusa da ita suka gaisa tace
“kidaure ki sha ko da ruwan sanyi ne zama da yunwa ya fi
komi illa duk abinda yafaru rubuttaccen alamari ne babu
wanda ya isa yago ge shi. ”
Tami’ke zaune tazubawa anty sadiya ido tace “anty sadiya kina
ganin haka yadace mu zubawa lamarn nan ido kullum Alhaji
yana cewa fatima ba za ta kashe khalifa ba toh ni so nake
agaya min wa yakashe min d’ana?
Anty sadkya tace “tabbas kam fatima ba za ta iya aikata
wannan mugun aiki ba abinda yake da sar’ka’kiya shi ne daga
shi sai ita a d’akin to waye yashiga yakashe shi?
Mama tace “ke sadiya idan ma ba ita takashe shi da hannunta
ba to da had’in bakinta aka kashe shi sbda ana ganin ubansa
yana da dukiya d’ansa d’aya ne ko don a mallake dukiyar
ubansa za ta iya yimasa haka.
Anti sadiya tace “kigafarce ni amma ban tari numfashinki ba to
amma idan haka ne da had’in bakin fatima ya ya za ayi ita data
kasheshi ko ta had’a baki aka kasheshi bata gudu ba har akazo
aka kamata? Allah (SWT) dasu kuma mahukuntan tunda Allah
yabasu basiran gano gaskiyar wannan alamari cikin hikima da
izinin Allah za su gano mana wanda yakashe mana d’a jininsa
ba zai tafi a banza ba.
A bisa hanyarsu tazuwa kotunne cikin mota mitar da mama ke
tayi wa abba kenan yayi tsit yana jinta ko tari vaiyi ba ya yi
tagumi yana jan charbi.
Suna shiga su malam da goggo suka shigo suka gaisa, Abba
yace”malam bana jin dad’i Yadda kake kaucewa had’uwa dani
tunda wannan abu yafaru. ”
malam yarufe fuskarsa da babbar riga dan kar abba yaga
fuskarsa yace “haba alhaji me, zan ce dakai? menake dashi
wanda zan gaya maka dahar zaisa intsaya in kalleka, kaico.
Ina ba’kin ckin faruwar wannan alamari har ina cewa ina ma
ace banzo duniya ba da dai ace ‘yar cikina ta kashe d’an
mutumin kirki kamar kai d’in nan Alhaji muhammadu.
Abba yaja hannunsa suka wuce cikin kotu ba tare dayace komi
ba, wuri d’aya suka zauna mutane suna mamaki sosai yadda
suke ganin iyayan wanda aka kashe da iyayan wacce ake
zargin ta yi kisan. wannan abu yana matu’kar baiwa mutane
mamaki haka zakaga jama’a na kallonsu, yai d’in ne ma dai
hajiya maijidda tasauya fuska sama sama suka gaisa ba wani
magana dasukayi fuska tamau ko da aka shigo da fatima ma
ko kallon inda take batayi ba.
ummi kamar ta fi su kansu fati shiga tashin hankali ta rame ta
lalace
.
Fati na shigowa kotu da ummi suka fara ido sannan tadubi
iyayanta dasauri tad’auke idonta xuwa ‘kasa tashin hnkali
datake ganin iyayanta a ciki ko wannan ma ya ishi mutum
tashin hnkli da ba’kin ciki ina amfanin rayuwarta.
Yau kam duk abinda zai faru sai dai yafaru lallai sai ta kawo
‘karshen wannan zaman kotu.
Bayan da akayi abubuwan daya dace ayi aka zauna mai
karanta ‘kara yakaranto, tuhumar da akewa fati na ta kashe
mijinta a ranar da aka d’aura musu aure a daren farko.
Mai shari’a Usman Muhammad Bamaina yace “fatima musa
kinji tuhumar da ake miki a karo na biyu? ”
Ta gyad’a kai tace na ji ya mai shari’a, yau kowa na jin
muryarta sosai, kuma kowa ya ji dad’in yadda tayi mgana har
alamun natsuwa a fuskar iyayanta da ‘yan uwanta musamman
ummi wadda har tsima jikinta yake a ranta tana fad’in yawea
fati gara ki yiwa kanki adalci da iyayanki damu masoyanki.Mai
shari’a yace “fatima musa me za ki iya Fad’awa kotu akan
haka? ma’ana kin amince ke kika kashe mijinki Dr. khalifa.?
Kai tsaye fati taware muryarta tace “Eh ni na kashe shi ya mai
shari’a.
[5:07PM, 7/13/2017] ‪+234 706 196 7803‬: A DAREN FARKO
3
Gabad’aya kotu tarud’e da sallalami kowa na fad’in albarkacin
bakinsa ,iyayan fati dasu kansu surukan suka rud’e, ummi kuwa
hannu tad’ora aka tana fad’in “wayyo Allah na wayyo fati
meyasa kikace ke kika kashe Dr. khalifa bayan ba ke kika kashe
shi ba.
Mai shari’a yayi tsawa akayi tsit sai dai kukan ‘yan uwan fati da
ba ya ‘karewa, ita kuwa fatin yau tana tsaye ‘kyam ko gezau
gadukkan alamu zuciyarta ta fara soyewa, idanuwan amma ba
kuka take ba zafin zuciya ne, ba ta son takalli iyayanta taga
mummunan tashin hnkalin dasu ke ciki, dama chan ita mutum
ce mai tsananin tausayin mutane balletana iyayenta.
Mai shari’a yace “fatima kotu tanason kiyi mata bayanin dalilin
dayasa kika kashe mijinki a daren tarewarku.
Fati tace “ban san dalilindayasa kika kashe mijinki a daran
tarewarku”.
Fati tace “bansa n dalilin dayasa nakashe shi ba, ba abinda
nao na zai iya furtawa a kan haka ya mai shari’a ina ro’kon
wannan kotu mai alfarma Data taimaka min tayanke min
hukuncin kisa a yau in bar duniyar nan inhuta, ba na son
bugawar da zuciyata keyi yazamo sanadin mutuwata na fi son
a yanke min hukunci dai dai da laifi na.
Tanumfasa tana kallon al’kalin daga bisani tad’auke idanunta
daga kansa zuwa kan jama’ar dake kotun, gaba d’ayansu su
ma ita suke kallo kowanne da abinda zuciyarsa ke sa’kamasa
game da ita.
Tayi shashe’kar ajiyar zuciya tace “iyayena da ‘yan uwana da
dukkan masoya na ina ro’konku don girman Allah kuyafe min
wannan yanayi dana sa ku nadamuwa sannan kuyi min addu’a
rayuwa ta fita daga raina minti d’aya ba na son in ‘ka ra yi a
duniya na fi son inbi mijina. ”
Tayi shiru kamar yadda kotun ma tayi tsit kai ka ce ba kowa a
kotun, al’kali yana ‘yan rubuce rubucensa, haka a ‘bangaran
lauyoyi wasu suna rubutu wasu shiru kawai sukayi suna kallon
fatima.
Taci gaba da fad’in “ya mai shari’a a karo na biyu ina ro’on a
taimaka a yanke min hukunci daidai da laifina na amsa laifina
ni ce nakashe mijina”.
Wani daga cikin lauyoyi yami’ke yanemi izinin magana daga
gun mai shari’a yace kanada daman magana.
Yayi godiya yadubi fatima yace “sunana barrister Abbas
Mukhtar inason kare wadda ake ‘kara sbda na fahimci ba ita tai
kisan ba ina nufin fatima musa ba ita takashe mijinta Dr.
khalifa ba ina ro’on wannan kotu
mai adalci data ba ni damar yin cikakken bincike a kan
wannan al’amari, kuma inason a ba ni damar dazan yiwa
fatima tambayoyi akan abinda ake tuhumarta dashi. ”
Mai shari’a yace “kanada damar yin haka.
Yayi dariya yana d’an murmushi ya’kara maida fuskarsa ga
fatima wadda itama shi take kallo fuskarta a tsuke, yace
“malama fatima musa ‘karfe nawa aka kaiki gidan mijin kuma
a wace rana ce. ”
Fatima tayi shiru kamar ba da ita ake magana ba, Barrister
Abbas ya’kara maimaita tambayar tare da ro’kon kotu data
tursasa fati tayi magana”.
Mai shari’a yayi hakan amma Fatima cewa tayi “nagode da
kake burin taimakona a bisa halin danake ciki, sai dai inason
kayi ha’kuri gaskiyar magana ba zan iya ba ka amsa ko d’aya
ba a bisa tambayar dakake min sbda ba so nake in ku’buta
daga halin danake ciki ba, wanda yake bu’katar lauya shi
yakeson yatsira nagaya muku ba na bu’katar rayuwa dan Allah
kuyafe ni.
Mai shari’a Usman muhammad Bamaina yadubi wani dogon
d’an sanda dake tsaye gefe yace “Za a gwada ‘kwa’kwalwar
fatima don mu tabbatar da mai hankali muke shari’a, idan
munyi zama na gaba za mu ji sakamakon sannan mud’ora a
inda muka tsaya.
Daganan aka d’aga ‘karar zuwa mako biyu idan Allah yanuna
mana,amma kotun ta ba wa ‘bangaran lauyoyi guda biyu damar
suyi duk binciken su akan yadda al’amarin yakasance don ba
da kariya dawadda ake zargi.
Yau ma kamar wancan karon kotun ta tashi da hayaniya kowa
na fad’in albarkacin bakinsa akan kafiyar da fati tayi a shari’ar
mamakin da take bawa yawancin mutane shi ne tayaya za ayi
mutum yace shi ya fidda rai kwata kwata da rayuwa mutuwa
yake muradi, wasu suna ganin wannan ya isa kowa ma ya
amince ba ita tayi kisan ba, yayin dawasu ke ganin dan ace ba
ita bace shi yasa tasallama tami’ka wuya, idan ba ita bace
waye? Gida su biyu kachal ba kowa d’aki a kulle su biyu in har
ance ba fati takashe Dr. khalifa ba to sai dai ace shi yakashe
kansa, hatta hajiya Maijidda mahaifiyar marigayin dayawa
daga ‘yan uwansu abinda suke gani knan wannan kukan da
take abinda suka d’auke shi kukan munafinci ne kawai.
A harabar kotun kafin sutafi gaida malam musa ya tsaida
barrister Abbas yana masa godiya a bisa ‘ko’karinsa nakare
‘yarsa, barrister yayi murmushi yace, “Ba komai kada kadamu
baba na yi wannan ne domin Allah da tsananin tausayin da
fatima ke ba ni tun randa aka fara tsaida ita a gaban shari’a na
tabbatar ba Ita tayi wannan kisan ba, duk wanda yakashe Dr.
khalifa na gida ne wanda yasan sirrin gidan insha Allahu da
izinin Allah zamu gano ko waye,sai dai inason kataimaka min
fatima tadinga ba da amsa a kotu sannan xanje inganta
kutaima ka min tayimin cikakken bayani duka tambayoyin da
zan mata dan insan yadda zan ‘bullowa al’amarin.
Malam yace “To ni na rasa me yasa fati take tsuke bakinta
komi sai tace ba za ta iya fad’a ba sbda rayuwar ta fita Daga
ranta.
Barrister yayi murmushi yace “bako mi tsananin damuwa ne
yasa take fad’in haka, matsayinku na iyayenta ku yadace
kulalla’bata tafad’i yadda akayi.
Malam yayi masa godiya mai yawa bayan tafiyarsu malam d’in
barrister na xaune a motarsa shi kad’ai yana nazarin alamuran
fatima tausayin ta har ya yi masa yawa a zuci.,daurewa kawai
yau yayi ya zo kotun tun a wancan zaman da akayi hankalinsa
yatashi sosai gameda al’amarin yarinyar, tun lkcn abinda yake
d’aga masa hnkali matsalar d’aya matsalar kowama ita ce
shirun da fati tayi tana neman mutuwa ido rufe ta ‘ki ba da
had’in kai ballantana a samu mafita.
*********************************************
A hankali ummi tafito daga motar tabi bayan mama zuwa cikin
gida, kowanne zuciya ba dad’i , a falo suka zauna gaba d’aya
yayin da ita ta dawo dabaya zuwa ainihin d’akin Dr. khalifa na
gidan har yanzu mukullan d’akin yana hannunta ita kad’ai take
bud’ewa tashiga tunda ga lokacin daya mutu zuwa yanzu,
komi na nan yadda yake wani irin ‘kamshi mai dad’in gaske
yana tashi a d’akin, gaba d’aya kayansa nasawa suna jere a
cikin wardrobe gwanin ban sha’awa manyan hotunansa da
akayi enlargement d’insu guda biyu na gefe da gefe na gadon
ya yi kyau ba na wasa ba.
Tazauna a gefen gadon tanasa hannu tad’auki hoton
tarungume kam kam idanunta a rufe hawaye wasu na bin wasu
zuwa chan ta ajiye tashiga bud’e durowowin jikin madubin
hotunan bikinsa da fatima ne birjik musamman ma gun
lunching da dinner dayawa yarungume fatin ne ‘kam ‘kam a
‘kirjinsa wasu kuma tare da abokanansa maza da mata.
Kan cinyar ummi yaji’ke dahawaye kamar ruwa aka zuba mta a
cinya tun ranar da aka kashe Dr. khalifa take kuka amma bata
ta’ba kuka irin na wannan rana ba, har sai dataji numfashinta
kamar zai d’auke.
Ba za ta ta’ba mantawa da abinda yagya mata ba a yammacin
lahadin daza akai fatima gdansa wanda kuma a wannan rana
ce aka kashe shi bai sake kwana a gidan duniya ba.
Yana tsaye a harabar gdansu tare da manyan abokansa biyu
wad’ana baida aminai kamar su.
Manyan likitoci Dr. Hafiz Bala Muhammad da Dr. Mustapha
Abubakar kura, yana tsakiyarsu suna hira, sai ita ummi tafito
daga cikin gida tana ganinsu tahau yimusu hoto a wayarta, Dr
khalifa yaharareta yace “wai meyasa kike daraina mutane ne
ummi ni kikewa hoto?
Sai Dr. Mustapha yace “kaima kanada saurin hushi khalifa ko
wacce rana idan an maka abu za ka ‘bata rai banda wannan
rana wadda tazamo ta auranka da matar dataza mo allura
cikin ruwa kaine kaxamo mai rabon daka zu’kota. ”
Dr. khalifa yarausayar dakai yana murmushi tare da lumshe ido
yace “ka fad’i gskiya Dr. Mustapha tabbas ni ne na cafko
wannan allurar data zamo tamai rabo ce, a daidai lokacin dana
fidda rai da ita sai najita kawai a hannuna ,tabbas wannan rana
ta dace tazamo ta farin cikina, ranar dazan sadaukar da komi
na wa sbda Fatima. ”
Ummi tay murmushi tace “shiyasa nima nake maka hoto
domin ka yi min kyawun daban ta’ba ganin ka yi shi ba a
duniya dukda cewa kai d’in me kyau ne kullum kyau kake da
ado. ”
Dr. Hafiz Bala yace “har bayan hoto yanada kyau ma yayi miki
kyauta ta musamman ummi.”
Dr. khalifa yayi murmushi yace “ko shakka babu a wannan rana
ina cikin farin cikin daban ta’ba samun kaina a cikin shi ba, sai
dai kasan tun safiya gabana ke fad’uwa bansan dalili ba
wannan yayi sanadin dayasa tun ruwan shayi danasha rabin
cup d’azun bayan d’aurin aure ban iyacin komi a bakina ba.
Ummi tayi wal da ido tace “fad’uwar gaba kuma Dr. a irin
wannan rana? ni dai na san ko kusa bakayi kama da wanda
mace za ta ba wa tsoro ba ballantana ince firgita kayi sbda
fatima.
Dr. Mustapha ya bugi kafad’arsa yace “wa wannan? ni tunda
ake ma gwargwadon bud’ewar idanuna ban ta’ba ganin
namijinda yayiwaa mata farin sani irinsa ba, farin ciki ne yayi
masa yawa sbda soyayyarshi yasa ma gabansa yake
fad’uwa……. ”
Tunanin ummi yakatse a nan lokacin da mama taturo ‘kofar
d’akin tatsaya tana kallon ummi kukan datake yabata tsoro
ta’karaso dasauri ta kamata takwashe hotunan dasuka ji’ke da
hawaye ta mayar, takamo hannunta tafito da ita tarufo d’akin
takar’be makullin tace “daga yau ko ‘kofar d’akin nan ba na so
kisake zuwa, haka kada ki ‘kara zuwa kotu ba xa muyi biyu
babu ba, mun rasa Dr.khalifa muna cikin ba’kin ciki mai tsanani
kema damuwa na neman xama ajalinki to B xai yiwu ba.
Cikin kuka ummi tace “Don Allah mama kada kiharamta mini
shiga d’akin likita, yin hakan ne kad’ai zaisa zuciyata ta
sassauta daga damuwar danake ciki, na rasa d’an uwana ga
aminiyata na cikin matsancin zargi na bi duk hanyoyin daya
kamata inbi don ganin fatima ta ba lauyoyi had’in kai ta ‘ki
burinta akasheta meyasa ba zanyi kuka ba mama?
mama tayi tsaki tace “ina mamakin yadda ke Da Alhaji kuka
d’auki damuwar duniya kuka d’orawa kanku akan fatima shin
dakuke cewa batace komi ba me za tace, fatima ba ta da abin
cewal shiyasa tai shiru, ko a hankalce kun san ‘karyane ace
akwai. mutumin da ake tuhuma irin hka ya’ki amsar taimako
daga lauyoyi don kawai yana burin mutuwa.
kinta’ba ganin wanda yazauna yana jiran mutuwarsa kuma yana
maraba da ita, saidai fa in ta zo a kar’beta don ba yadda za ayi
da ita.
Ummi tasaki hannun mama tazubla mlatla ido muryarta a
dashe tace “mama shin kina nufin kin amince fati za ta iya
kashe likita?
Mama tayi murmushi tace “ummi ummi kiji tsoron duk wanda
kika taimakawa.
Akoda yaushe idan za ki taimakawa mutum to kitaimake shi
kai tsaye don Allah ba wai don zai saka maki da alherin dakika
yimasa ba, shi dama mutum bbu abinda yake cika cikinsa sai
‘kasa shi. mai butulcewa mahaliccinsa ne ma ballantana ace
wani gama garin mutumin don hka ba abin mamaki bane ga
mutumin daka d’auko shi daga rana kadawo dashi inuwa shi
kuma yaturaka ranar,a cikin mutane mutumin dayake salihi ko
mai shiru shiru irin fatima mutane ba sa zarginsa da mugun
abu sbda yanayinsa amma Allha (SWT)daya halicci zuciya shi
yasan abinda ke cikinsa.
Ummi tayi shiru na lokaci mai tsawo daga bisani tace “Mama
kina nufin kin amince akashe fatima akan kisan likita? ”
Tace “ummi ba ni da masaniyar abinda shari’ar za tahaifar,
sbda ita shari’a macece da ciki ba wanda yasan abinda za
tahaifa sai Allah mudai mun mi’ka kukanmu ga Allah
yabayyanar da gaskiya. ”
Tayi gaba tabar ummi tana binta da ido jikinta yayi sanyi
‘kalau, da’kyar tad’aga ‘kafa tabita cikin gida.