Hausa Novels

A Gidan Mu take Hausa Novel Complete

A Gidan Mu take Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: A gidan mu take

Page 1&2

A Gidan Mu take

“Haba Ahmad meyasa bazaka dauki kaddara ba, kasani fa kowani dan Adam da irin tasa kaddarar, na wani yafi na wani amma Sam kai baka dauki kaddaraba.

 

Nan naga Wanda aka kirada suna Ahmad ya dago kanshi, yana hawaye fuskarshi tayi ja, buɗe baki yayi yanason yin magana amma ya kas, sai kuka yake kamar wata mace, hadda shesheka dakyar ya iya cewa “Haba Habeeb ya bazanyi kuka ba, bacin kai kasan abinda yake damuna, idan Banyi kukaba me zanyi?” Yaƙare maganar cikin sanyin murya.

 

Gyara zama Habeeb yayi haɗe da cewa.

“Addu’a ya kamata kayi Ahmad, domin itace abinda yakamata kowani musulmi yayi, a lokacin daya samu kanshi cikin yanayi na kunci.”

 

“Ya isa haka Habeeb, ka ƙyaleni naji da abinda yake damuna, bawai ka cikani da surutunka ba, sanin kanka ne nayi babban rashi a rayuwata, rashin daba zan taɓa mantawa ba, tunda narasa FATEEMAH narasa komai,

na wulaƙantata, na ƙuntata mata, nayi mata abinda bazata taɓa mantawa daniba, Ina zanga Fateemah? Ina zanji labarinta? tana raye ko Tana mace?” Ɗan jinkirtawa da maganan yayi, kana ya cigaba da cewa.

“Idan Tana raye Ya Allah Ka bayyana min ita, idan kuma tamutu Allah Ka kai haske kabarinta!!” Ya ƙarashe maganan yana wani irin gunjin kuka.

 

Awannan lokacin har Habeeb ba’a barshi abaya ba, duk dauriyanshi shima seda yayi hawaye, yana me tausayawa abokinnashi.

*** ***

 

“Wai Ina kike ne BINTU? kiyi sauri dan Allah kinsanfa mommy Tana jiranmu a mota.”

 

“Ina zuwa Sis HABEEBA, gyalena nake dubawa ban gani ba.” Naji wata siririyar murya Tana fada.

 

“Kiɗauki nawa a wardrobe mana bintu.” Habeeba tafaɗi haka cikin yanayi na ƙosawa.

 

“Okay nama dauka ae ganinan.” Beentu tafaɗi haka tana mai ƙoƙarin yafa gyalen ajikinta.

 

“Okay dama koban ce kidauka ba zaki dauka kenan?” Habeeba tafaɗa tana ɗan kallon gefen da Beentun take.

 

Nan naga Beentu na sauƙowa daga kan step, cikin takunta mai ɗauke da nutsuwa. Farace sol doguwa siririya, tana da manya manyan idanu, bakinta dan karami, ƙoƙarin gyara gyallen take, tayadda zai zauna akanta.

 

Cewa tayi “Haba My Hussaina, Kinsan fa bama haka dake, kuma naga kema ay kinasa abuna ko my sis?”

 

“Da ma ay haka zakice, kullum se kinwa mutum laifi kizo kina mishi sanyin murya, to yanzu de muje kinga Mom nata kirana, kusan 6 missed calls tayi min” Habeeba tafaɗi haka tana mai duban wayarta dake riƙe a hanunta.

 

“Okay to muje” Cewar Beentu.

 

A tare suka fito daga falon suna sauri.

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

_see me next page_

 

*Jidderh S Mapi*

[6/23, 12:43 PM] Ummi Tandama:

*A GIDANMU TAKE!!!*

 

 

_story written by_

Jiddah S mapi

 

_dedicated to fateemahsardauna_

 

_wattpad jiddahpretty_

 

Page 3&4

 

Suna fita daga falon habeeba ta kwalawa driver Kira yace gani hajiya

 

tace Ina mommy yace ay hajiya ta dade da tafiya tace bazata iya jiranku ba idan kun gama ku sameta agidan abinci

ok to kaimu driver yace to nan suka shiga motar suka tafi

bayan driver yayi parking naga sun shiga wani waje me kyau Wanda naga ma’aikata da uniform suna rabawa mutane abinci wasu kuma suna dafawa

 

Wasu na wanke plates daga gani de wannan gidan abinci ne Wanda yayi suna agarin

 

ADAMAWA Ina daga kaina naga an rubuta HASSY and HUSSY’S KITCHEN

 

suna fita a motar idanun mutane suka dawo kansu Ana tacewa kaga ‘yan biyun hajiya bada kunku asare

 

Kuje gida kuce yafadi habeeba ce kadai me cewa sannunku

 

Samarai barka da war haka ita kuma bintu sai murmushi take nan naga sun nufo wata kykkyawar mata wacce zatakai shekara 40 habeeba tafada kan cinyar matar

 

Tace mommy shine kikayi tafiyarki kika barmu

 

matar da aka Kira da mommy naga tayi murmushi nan naga tsananin kamanta da habeeba tace ba dole natafi ba

 

Kun tsaya kunata shirme kuma kunsan yau ranar biyan ma’aikata ne

 

Mommy ai bintu ce ta tsayar damu kinsan yanayinta dayin Abu kamar karkashi

 

Aa karki sake kizagammin ya zo maya my bintu kizauna anan

 

Bintu tayi murmushi tace mom inason yau zanyi stew da kaima

Mom tace Haba bintu yazaki gajiyar da kanki kizauna kihuta kinji my bintu

 

Aa mom kibari zanyi

Toshikenan bazan hanakiba jekiyi

 

 

Ahmad dama nayi niyan tafiya yau amma bazan iya tafiya nabarka awannan yanayin ba

 

Nagode habeeb Allah yabarmin kai dan Allah habeeb ko bayan na mutu idan kasamu my teemah dan Allah ka aureta sabida kai Kadai nayadda dakai Kai Kadai nasan zaka riketa da amana tinda kasan bakar wuyar datasha kasan na zalinceta naci amana dan Allah kayimin wannan alkawarin

 

_see me next page_

[6/23, 12:44 PM] Ummi Tandama:

*A GIDANMU TAKE*

 

 

_story/written by

 

Jiddah s mapi

 

 

_dedicated To fateemahsardauna_

 

 

_wattpad_

Jiddahpretty

 

Page 5&6

 

Ahmad kadaina irin wadannan maganganun

 

Banajin dadinsu Sam meyasa kake maganar mutuwa bayan bakaga fateemahn kaba

 

Ahmad insha Allah Bazaka mutu ba seka ga fateema

 

Ka nemi yafiyanta Sannan ku Gina rayuwa me kyau

 

Kuma inada tabbacin fateemah zata yafe maka

 

Habeeb bana tinanin my teemah Zata yafemin koda bayan raina ne

 

Habeeb babu abinda yake damina kamar yanda mommy tadau

 

Zancennan da zafi ka duba kagani

 

Yau kusan shekara daya ban sa mommy a idona ba

 

Yazanyi da rayuwa ta ya karashe maganan yana me hawaye

 

Abin tausayi

 

Habeeb kam ba bakin magana

 

Shi mamaki ma abun yake bashi wai ace yau

 

Ahmad ne yake kuka yana fada mishi damuwanshi

 

Shida magana ma be dameshi ba

 

Gsky dayana da yanda ze taimaka mishi daya yayi

 

Amma shi besan ma ta ina ze fara ba

 

Allah ka gaggauta kawo mana karshen

 

Matsalarnan Ameen

 

 

*BINTU*

 

Mommy wai meyasa bintu take zubar mana da class ne

 

Kiduba fa yanzu wajen masu aiki zataje suyi tare

 

Gsky mom abinda takeyi bata kyautawa wannan aji down ne

 

Habeeba kibi rayuwa a hankali

 

Ita duniya a hankali ake binta

 

Wanda batazo bama Tana jiranshi bale muda muke cikinta

 

Ni gsky mom kina daurewa bintu gindi dama nasan

 

Niba sona kike ba

 

Bawai bana sonki bane beebah babu Wanda ze haifi da

 

Yakishi sede idan kaddara ne

 

mom tafada idonta yana cika da hawaye

 

A hankali tajuya kanta yanda bintu bazata ganta ba ta goge idonta

 

Bintu kuwa iyayen son aiki tanata girki suna dan hira da ma aikatan

 

Dan ita ba ma’abociyar son magana bace

 

Cikin hiranne wata Wanda suka dan saba da bintu

 

Take tambayan bintu

 

Friend dama inason inyi miki wata tambaya

 

Ok nabeela inajinki

 

Amma Allah yasa ranki baze baci ba

 

Aa ba komai yi maganarki ok

 

Dama inason tambayanki tum bayau ba

 

Hajiyace ta haifeki!!!?

 

Haba nabeela wannan wace irin magana ce yazakimin wannan tambayar?

 

Bacin kinsan mu ‘yan biyune nice babba

 

Gsky bintu ba kowane ze yadda ba

 

Duba da irin yanayinki Kiga beebah mana

 

Tana Kama da hajiya

 

Amma ke Sam babu abinda yahadaki da hajiya ta kamanni ko hali gsky akwai abun dubawa anan

 

What are you saying nabeela!!!?

 

Cewar mom Wanda tin farkon maganarsu takejinsu

 

Ta taso tambayar bintu kota gama hadin?

 

 

See me next page

 

 

_Wattpad_

Jiddahpretty

[6/23, 12:44 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*A GIDANMU TAKE!!!*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

 

_story/written_by

Jiddah S mapi

 

_dedicated to fateemahsardauna_

 

Page 7&8

 

A take suka juyo ganin yadda mommy tayi maganan da karfi

 

Nan take jikin nabeelah yayi sanyi ganin yadda yananayin mommy yacanza a lokaci kankani

 

Haba nabeelah wannan wace irin magana ce meyasa kike son sa shakku a zuciyar

 

‘Yar da Nina haifeta a cikina? shin bakida labarin Akwai ‘yan biyun da Sam basa Kama da juna?”

 

“meyasa ku mutane

Bakwa gane abune yanzu da ace bani na haifi bintu ba dazaki hada abinda Baza’a taba cewa ke kika hada ba” saikuma tsaya

 

“Gsky bana son irin wannan tambayar”

 

Kai daga yau ma kada nakara ganinki da bintu Dan nan gaba bansan mezaki ce mata ba

 

“Kiyi hakuri hajiya in Allah ya yadda hakan bazata Kara faruwa ba….” inji Nabeela

 

“Banason dogon magana nabeela nariga nagama magana” hajiya ta mayar mata

 

“Bintu wuce mutafi”

Tafada cikin bacin rai

 

“To mommy” cewar bintu wacce tinda mommy tafara fada ta Sunkuyar da kai saida zasu tafi ne takuma ɗaga kai tadubi Nabila wacce duk kunyar momy ya isheta

 

 

*AHMAD*

 

Dakyar habeeb yasamu ya lallabashi yai shiru

 

“Ahmad gobe idan Allah yakaimu kafin in tafi dan Allah inason muje asibiti Aduba lfyrka dubi yadda karame” inji Habeeb

 

“Aa base naje asibiti ba maganin cutana bana asibi bane Maganin cutana my teemah ne idan nasameta zan warke insha Allah” inji Ahmad

 

“Toshikenan yanzu de ka kwanta kahuta sannan karage damuwa saboda zata haddasa maka cuta” inji Habeeb

 

“Nima Bari nakira agida nafada musu na shaida bazan samu dawowa ba sai gobe”

 

Mommy na isowa wajen Beebah tasamu sit nata ta zauna rai ɓace

 

Beebah bataga fuskar tambaya ba

 

Sai takarasa wajen Bintu tace “Bintu yanaga ran mommy a bace”

 

“babu komai sis” inji Bintu saboda tasan idan Beebah taji maganarnan bazata ɗauka da sauki

 

“Yazakice min ba komi bayan gashi ranta a matukar ɓace”

 

 

 

“Nace miki ba komai ke meyasa kin fiye naci ne? Inji Bintu

 

“Ko zaki dake nine to?” cewar Beebah

 

“Nibance zan dake kiba dan haka kimatsa min anan” Bintu ta mayar mata

 

“Zaki fara ko beebah meyasa bakya girmama tane tagirmeki fa” inji mommy

 

Beebah ta zumburo baki tana kunkuni wai datayi magana sai ace ta girmeta abinda baifi ƴan mintuna ba

 

“Yanzu de kutashi mutafi gida sabida yau yayanku ze dawo” cewar mommy

 

“Yee mommy dagaske kik?”cewar beebah

 

“Dama nataba miki karyane?”

 

Nan wayan mommy yafara ringing

 

“Yawwa ga shima yana Kira”

 

amsawa tayi takara a kunnenta

 

“Hello my son yakake? ok se gobe? Amma meyasa yau bazaka dawo ba? Ok to Allah yakaimu goben” saikuma ta kashe wayar

 

“Kunga yayan nakuma yace se gobe ze dawo” mommy tafaɗa musu

 

“Kai amma naji haushi mommy” cewar beebah

 

Mommy tace “Yau da gobe duk dayane beebah kawai muyi addu’a Allah yakawo shi lafiya”

 

“Ameen” cewar bintu

 

_See me next page_

 

_wattpad_

Jiddahpretty

[6/23, 12:44 PM] Ummi Tandama:

*A GIDANMU TAKE!!!*

 

 

_story by_

jiddah S mapi

 

_dedicated to fateemah sardauna_

 

Page 9&10

 

 

Washe gari bayan sun gama breakfast ne,

 

Habeeb yake cewa Ahmad

 

“To kaga ni yau zan tafi kuma bazan dawo nan dawuri ba”

 

Saboda wannan zuwanma dakyar mommy tabarni.

 

Acewarta bataso nayi nesa da ita

 

Dan Allah Ahmad kada kasa tinani a ranka

 

Sannan kuma karka gaji da Zuwa gidanku neman tuba a wajen

 

Mommynka

 

“Aa Habeeb bazan iya zuwa inda mom take ba gsky”

 

Sabida mom idan taganni bacin ranta karuwa yake

 

Har Tana barazanar Zata tsinemin idan harna sake zuwa inda take

 

Ba tareda Fateemah ba

 

Kai innalillahi wa’inna ilaihiraji’un abun haryana kai da hakane Ahmad

 

Wlh Habeeb shiyasa kaga damuwan sunyi min yawa narasa yanda zanyi

 

Yanzu ma tafiyar da zakayi banso ba

 

Koba komai kana debemin kewa.

 

Amma yana iya, idan kaje ka gaida mommy

 

Da kannan ka duka

Nagode Allah yabar zumunci

 

Habeeb yace Ameen

 

Ahmad yace “Kashirya nakaika airport karkayi missing flight”

 

Ok

 

 

 

Bintu kinga yau broh ze dawo

 

“Kizo mushiga kitchen dakanmu muhada mishi delicious”

 

Bintu tace “Ok sis karki sami damuwa muje”

 

Suka tashi suka shiga kitchen suna ta hira

 

Mommy Tana kallonsu Tana Mejin farin ciki a zuciyarta

 

tace “Allah yasake hada kanku my twins”

 

*AHMAD*

 

Tafiya suke a mota suna hira shida Habeeb.

 

Nan Habeeb yake kara jaddada masa akan yakula da kanshi yadaina yawan tinani.

 

Ahmad yace “kaga karka dameni tin jiya kana ta maimaitamin kalma daya kamar karatu”

 

Ohh “dama nasan bazaka taba canza haliba Ahmad”

 

Eh naji bazan canza ba

 

Dahaka har suka isa airport

 

*BINTU*

 

Bintu kuwa anata aiki a kitchen bebba se surutu take zubawa.

 

Banda eh, aa, to,

Ba abinda Bintu take cewa har suka gama hada frid rice da kaji

 

Bintu tahada sobo me cucumber

 

Mommy tace “yanzu natura driver yaje dauko shi a airport

Wai ya karaso”

 

Yeeeee mommy “Aida kin fadamin da tare zamu tafi dashi”

 

Kai Beebah kin fiye gaggawa

 

Haba mommy “yabazanyi gaggawa ba yaufa kusan 2weeks ban ganshi ba sede waya”

 

Bintu kuma murmushi kawai tayi

 

Horn sukaji abakin gate

 

Nan Beebah tafita da gudu Tana oyoyo yaya oyoyo

 

Kafin driver yagama parking harta fara

 

Bubbuga motan

 

Seda yafito da sauri yana oyoyo my sis

 

Nan ta rungumeshi kamkam Tana murna

 

Yace ina dayarki? Tana falo itada mommy

 

Ok mushiga daga ciki

 

Suna tafiya Tana rike da waist nashi har suka shiga falon.

 

Tana cewa “yaya kadauko tsaraban toh”

 

Mushiga de tukun kinsan tsarabarki ta daban ce.

 

Mommy tace “oyoyo my son sannu da zuwa nan itama ta rungumeshi tana murna”

 

Bintu ta tsaya Tana tayi mishi murmushi

 

Yace “kekam meyasa bazaki Waye ba Bintu”

 

kullum kina cikin rashin sabo da mutum.

 

Cheww Allah yakyauta halinnan naki.

 

Kina gani fa ‘yar uwarki tazo tayi min oyoyo

 

Amma ke kina tsaye

 

Daga nanne Bintu taje ta rungumeshi

 

Yahada su duka uku ya rungume sunata murna

 

 

 

“Ahmad yana komawa gida ya kwanta agado yana tinanin mommynshi

da kanwarshi”

 

Wai yau shine Kanwarshi wanda yafi so aduniya take gudunshi?

 

“Yau shine mommynshi take ikirarin tsine mishi”

 

“Idan yatuna rayuwarshi na da se yayi kuka”

 

*WANENE AHMAD*?

 

AHMAD KABEER yarone awajen alhaji kabeer.

 

Alh kabeer shahararren dan kasuwane

 

“Wanda yayi suna a duniya”

 

Alhaji kabeer de dan asalin garin adamawa ne

 

Shi asalin fulani ne

 

Wanda yafara harkar kasuwanci tin yana saurayi

 

Allah kuma ya buda “mishi sabida yanda yake da kyauta da taimakon talakawa”

 

Alh kabeer yabude gidan marayu tin yana saurayi,

 

sabida yadda Allah yasa mishi tausayin marayu a zuciyarshi.

 

Dan hakane har yaki yin aure

 

” dan yana gudun kar ya auri matar dazata hanashi taimakon marayu”

 

Iyayenshi ne suka nema mishi aure Agidan marayu Wanda shiya bude da kanshi

 

Acewarsu zatafi jin tausayin marayu ‘yan uwanta

 

“Inda suka nema mishi wata kyakkyawar yarinya me Suna mariya”

 

“Ba matsala a auren mariya da alhaji kabeer sabida mariya Yarinyar kirkice”

 

Bayan shekara hudu Allah be kawo musu haihuwa ba

 

Har abun yafara damin mariya

 

Inda alhaji kabeer yake cemata

 

“karki damu mariya haihuwa na Allah ne”

 

“Idan ma Allah be bamu b! Baga gidan marayu ba, semu dau daya murike kaman mu muka haifa

 

Mariya tace “haba Alhaji kasan fa akwai banbanci tsakanin ɗa da kuma ɗan riko”

 

Aa mariya ɗa na kowa Ne!

 

Ganin yahau matsifane mariya tayi shiru

 

 

“To dahakane har Allah yakawo ranar haihuwanta inda aka sha shagali akayi murna”

 

Akasawa yaro sunan baban alhaji kabeer wato AHMAD.

 

Ahmad de yasamu gata dan kota ina anaji dashi

 

“Ahmad kyakkyawa ne”

 

Fari Ne shi, dogo, da dogon hanci, ga karamin baki, Atakaicede shi yayi kama da larabawa.

 

Sede kuma matsalar shi nada yawa

 

Yanada girman kai sosai

 

Ga kallon banza

 

“Ga zama da abokan banza”

 

Wasu abubuwan dayake yi abokai ne suke zigashi

 

“Sai yayi ta tsula rashin kunya son ranshi”

 

Dafarko yasamu daurin gindi awajen iyayenshi

 

Se daga baya abun yafara damunsu

 

 

*bayan wasu shekaru*

 

“Dahakane har allah yasake basu haihuwa”

 

“Yarinya taci sunan wacce take kula da gidan marayu na mahaifinsu wato FAREEDAH”

 

Fareeda de kykkyawa ce tana Kama da Ahmad sosai.

 

 

“Sannan kuma tinda aka haifi fareeda Ahmad yakara bude sabon rashin kunya”

 

Shi adole yana da kanwa

 

 

Bayan haihuwar fareeda fareeda ne Alhaji kabeer yafara diban yaranshi suna zuwa gidan marayu kai tallafi.

 

Acewarshi idan sun girma suma zasu taimaki marayu.

 

“Ranar farko dasukaje gidan marayun”

 

Ahmad yasa fararen kaya masu kyau yanata Hada rai danshi beso zuwa ba.

 

 

“Bayan an tara yara ana raba musu kudi ne”

 

Alhaji kabeer yahango wata kyakkyawar yarinya.

 

“Tana zaune a gefe tana kallonsu tana murmushi”

 

Alhaji Kabeer yaɗan tsaya da rabiyar yana kallonta.

 

Se ya yafito ta da hannu yace zo!

 

Yarinyan ta tashi a hankali tana tafiya

 

Harta iso su, seta durkusa tace gani.

 

“Alhaji Kabeer yayi mamakin wannan yarinya batafi shekara goma ba”

 

Amma take da natsuwa haka gata dakyau.

 

Shi kuma Ahmad se harara yake tayi wai ana bata mishi lokaci

 

Alhaji yace “ya sunanki?”

 

Ahankali tace “sunana Fateemah”

 

 

*JIDDAH S MAPI*

[6/23, 12:45 PM] Ummi Tandama:

*A GIDANMU TAKE!!!*

 

 

Story/written by

Jiddah S mapi

 

_dedicated to walidation S mapi_

 

Wattpad

Jiddahpretty

 

Page 11&12

 

Wow nice name inji Fareedah,

 

Gsky Daddy yarinyannan kyakkyawa ce, gata fara ga ido wow.

 

Daddy yace meyasa ana raba kudi amma baki zo kin karɓa ba?

 

Tace “banada bukatar kudinne shiyasa, duk abunda nake so mama tana bani.

 

“To ay zaki iya ajiye kudin sabida watarana cewar Fareedah”

 

Shi kuma Ahmad se duba agogo yake yanata tsaki, ba abun yacewa Daddy ze tafi ba, se harara yake ta bankawa yarinyan. Gani yake kamar ita take kara delaying nasu.

 

Daddy ya ciro kudi masu yawa ya bawa yarinyan, ta girgiza kai tace “aa nagode abawa sauran”

 

Kikarɓa ni na baki ay, a hankali tasa hanu ta karba tace”nagode Allah yasaka da alheri” Ameen

*************

 

Tin daga wannan rana idan daddy yaje gidan marayu sai yace a kira mishi Fateemah yadau kudi yabata.

 

To fa dahaka suka saba da Fareedah sosai watarana ma Fareedah takan zuwa gidab Marayun suyi ta hira da Fateemah, har yazama idan Fareedah bataje taga Fateemah! ba batajin dadi a ranta, sunyi muguwar shakuwa da Fateemah..

 

 

Ta ɓangaren Ahmad kuma yana dada lalacewa sabida abokai dayake tare dasu, mutane suna yawan kawowa Alh Kabeer karan Ahmad amma baya taɓa yadda se yace suyi hakuri yaranta ne daya girma ze daina.

 

Abun yana taɓa zuciyar Mariya taya za’ace yarinta bacin yaro yakai shekara 29 ina maganan yarinta anan?

 

yauma kamar kullum Alh Kabeer ne da yaranshi zasuje gidan marayu, yayinda Fareedah take ta rokon mom tashirya suje taga kawarta kuma Bestyn ta.

 

To Fareedah naji tashi muje yawwa Mom ko kefah

 

A hanyarsu tazuwa gidan marayu ne Alh kabeer yake tambayan Ahmad

 

“Wai kai son yaushe ne zakayi Aure? Ahmad yahada fuska yana hararan Fareedah wai ana tambayanshi Aure a idon yarinya karama.

 

Ba tambayanka nake ba?. Am daddy insha Allah very soon zan kawo muku matar dazan Aura.

 

 

Mommy tace “udan ma be kawo ba mu sai mu nema mishi”Fareedah tace “yess mommy nizan nema mishi ma dakaina.

 

Daya juya ya banka mata harara tayi tsitt

 

Bayan sun shiga gidan marayu ne Fareedah tafara neman Fateemah a inda tasaba ganinta amma bata ganta ba!

 

 

Ta tambayi wasu yara su biyu suna wasa tace”ina Fateema? ”

 

Sukace Fateemah batada lafiya tanata kuka tin ɗazu taki amata allura.

 

A wana ɗaki take? cewar Fareedah cikin tashin hankali tayi tambayar? muje nakaiki cewar wata yarinya

 

Suna shiga dakin taga Fateemah tana ta kuka tana rawan sanyi

 

Da gudu tafita tana kiran mommy!

 

Mommy naganin Fareedah ta fito da gudu, tafara tambaya lafiya?

 

Fareedah batayi magana ba se nuna daki take!

 

Mommy tace kiyi magana, dakyar tace Fateemah, wace Fateeman? Cewar Daddy…..

 

Nan suka shiga dakin da gudu. Suna zuwa sukaga Fateemah bata motsi nan Fareedah ta tsala ihu

 

Mommy tace kira yayanki awaje Fareedah ta taso da gudu tana kiran yaya yaya

 

Ya dago kanshi yace ke me haka? Kinata kiran sunana kamar wani sa’anki

 

“Yaya wai kaje inji mommy”

Yaja wata doguwar tsaki yace muje

 

Suna zuwa Daddy yace oya Ahmad dauke ta dawuri mutafi asibiti

 

Haba Daddy kaduba fa farin kayane ajikina ta yaya zan fara daukanta? Dubi jikinta fa duk datti……. Zaka dauketa ne ko sai ranka ya ɓaci cewar daddy.

 

A hankali yaɗauketa yana yatsina fuska

 

Yariketa kamar kashi ya ɗauka sai yayi sauri sauri ya wurgata a motar da iya karfinshi.

 

Har saida kanta ya bugu

 

Daddy yace shiga mutafi, dakyar yadaure yashiga yanata kunkuni.

 

Ita kuma Fareedah sai kuka take tana kiran sunan Fateema tana cewa ta tashi karta mutu

 

A haka har suka iso specialist hospital. Suna zuwa ba ɓata lokaci aka karbesu

 

Likitoci suka shiga ciki da ita, Ahmad yace dama daddy inason naje wani waje na karɓi sako, babu inda zaka kana gani mun kawo yarinya ba lafiya rai a hanun Allah kace zaka tafi, baka da imani ne?

 

Ahmad ya haɗa rai yasamu waje ya zauna yanata kunkuni me haɗi na da ita da za’a hanani yin uzirina akanta? Yarinya kucaka ma da ita

 

Suna cikin zama wata nurse ta fito tace doctor yana magana dakai.

 

Alh kabeer yace to, nan yashiga ciki, doctor yace kaine baban yarinyan daka kawo? Alhkabeer yace eh nine

 

Ok amma kasan da ciwon dayake daminta? Yace Aa

 

Doctor yagyara zama yace Alh rayuwar ‘yarka tana cikin matsala

 

“Ka taɓa zama da ita ka tambayi matsalarta? Daddy yace Aa

 

Tofa akwai babbar matsala! Am sorry to say, ‘yarka tana dauke da ciwon zuciya wanda idan har aka barta cikin tunani tayi nisa zata iya rasa ranta a ko wani lokaci.

 

 

*JIDDAH S MAPI*

Ummi Tandama:

*A GIDANMU TAKE!!!*

 

 

_story written by_

Jiddah S mapi

 

_dedicated to my lovly sister @walidation_

 

_Note me on_ _wattpad Jiddahpretty_

 

Page 15&16

 

Da kyar Fareedah ta janye Fateemah zuwa gefen hanya ta kwantar da ita tace “ki zauna anan bara naje na kama mana Napep”

 

A haka ta kama musu Napep ta rike Fateemah suka shiga se gida.

 

Shi kuma Ahmad yana jan motarsa ya wuce carwash yace a wanke mishi ita,

 

Alh Kabeer kuwa da mariya suna zuwa gidan marayu yacewa mama yanason magana da ita,

Tace “ok ba komai ina jinka Alh”

 

Yace dama so nake na ɗauke Fateemah na ɗan wani lokaci idan ba matsala,

Mama tace ba komai Alh. Ay duk an zama ɗaya,

Da haka suka tafi gida.

***************

Shakuwa me tsanani ta shiga tsakanin Fareedah da Fateemah,

Dan Fareedah sosai takeson Fateemah har cikin Ranta komai za’a siya mata zatace sai an siyawa Fateemah.

 

Shi kuma Ahmad a duniya babu abinda yatsani gani kamar Fateemah, kwata kwata Allah be haɗa jininsu da ita ba,

Ko abinci Fateemah ta dafa baya ci idan har ya san ita tadafa.

 

Yauma kamar kullum Fateemah ce take goge goge a falo,

tana kan goge TV ne taji ance mata “ke baki da hankali ne ko kin taɓa ganin inda ake goge TV da tsumma? Koda shike ba laifinki bane laifin iyayenki ne dasuka haifeki a titi, daga baya suka yadda ki”

Nasan da agaban iyayen ki kike, dakin iya goge TV. Wawiyar banza.

 

Tunda Fateemah take a rayuwarta ba’a taɓa faɗa mata maganan daya ɓata mata rai irin ta yau ba,

Ahmad ne farko yafara kiranta da shegiya.

 

A hankali ta ɗago kanta tace “kayi hakuri zan gyara insha Allah ”

Ai kuwa yaja tsaki ya fita a ɗakin yanaji kamar ya shaketa ta mutu kawai.

 

Wato yarinyannan duk abunda za’ayi mata bazatayi kuka ba, saide tayi tabada hakuri kamar marokiya, sai nayi maganinta ay.

 

Ita kuma Fateemah yana fita tasa kuka me cin rai,

Tana cikin kuka ne taji muryan Fareedah tana, Besty ina kike?

 

Ta share hawayenta tace “gani nan”

 

Fareedah ta rungumeta tace “meya sameki naga kamar kinyi kuka? tace “Aa babu komai kaina ke ciwo”

Ayya sorry kinsha magani?

Eh nasha,

Ok muje ɗaki to ki kwanta.

 

 

Da daren ranan Fateemah takasa bacci, data rufe ido sai tana tuna maganganun Ahmad na ɗazu.

_ba laifinki bane_

_Laifin iyayenki ne_

_Dasuka haifeki a titi_

 

Wato ni shegiyace? A titi aka haifeni? To ina iyayena suke!? Meyasa suka yadda ni?

Shine tambayoyin data kasa amsawa kanta,

Data kara tunawa seta fashe da kuka,

Jikinta yafara zafi, tana kokarin ta tsaida kukan amma ta kasa. Da haka har tafara tari, jikinta yafara rawa taja bargo ta lulluɓa jikinta amma har yanzu tana jin sanyi. Tana cikin wannan halinne Fareedah ta tashi zatayi fitsari,

 

Taga Fateemah acikin bargo jikinta yana rawa gashi fuskanta yayi ja,

A razane ta iso wajenta tana tambayanta meya faru

 

Fateemah ba bakin magana se ido kawai,

Ta fita da gudu taje ɗakin mommy ta kirata,

A tare sukazo da mommy,

Mommy tana ganin halin da Fateemah take ciki tace akira mata Alhaji,

Ai kuwa Alh Kabeer yana zuwa yace aje akira Ahmad yazo su tafi Asibiti.

 

Fareedah ce taje kiranshi tana zuwa tayi knocking yace “yes waye? ”

Tace Yaya Fareedah ce,

Yace me kikeso?

Tace “Daddy ne yace nakiraka”

Daddy kuma? Meya faru?

Nima ban sani ba!

 

Ok ina zuwa,

Ahmad yana zuwa Daddy yace “oya ɗauke ta da wuri mu tafi Asibiti kar dare yayi sosai.

 

Daddy wani Asibiti?

Dama wani Asibiti muke zuwa? Inji Daddy

 

Daddy Ai yanzu dare yayi abari sai gobe mana da safe….

Kai Ahmad baka da hankali ne? Ko baka ganin halin da take ciki? Ko da Fareedah ce zakace abari sai gobe?

 

Yayi shiru dan besan me zecewa Daddy ba ganin yahau 90,

 

A haka badan yaso ba ya ɗauketa yakaita mota,

Ji yake kamar ya shaketa tamutu ko ze huta

 

 

*jiddah S mapi*

[6/23, 12:45 PM] Ummi Tandama:

*A GIDANMU TAKE*

 

 

_story/written by_

Jiddah S mapi

 

 

_dedicated to my lovly sister_

@walidation

 

 

Page 13&14

 

“Alh ‘yarka tana cikin matsala” zai fi maka sauki ka kirata ka lallaɓata, ta faɗa maka meke damunta, sabida hakki ne a kanka.

 

To fa nan Daddy yafara share zufa, yanason yace ba ‘yarshi bace, amma yana tsoron kar likitan yace mishi makaryaci.

 

“Yace toh doctor nagode” yanzu ya ake ciki? Doctor yace “a halin yanzu de an ɗaura mata ruwa, saura na rubuta muku magungunan da zaku saya”

 

Ahmad kuwa abokanshi sunata kiranshi awaya, yana ta tsaki wannan wani irin abune? Bamu santa ba! Ba dangi ba! Ba ‘yan uwa ba! Amma ahanani yin komai chewww….

 

Yasake jan wani dogon tsaki ganin ana sake kiranshi.

 

“Dan Allah karka dame ni Bash, ka kyaleni na huta wannan wana irin Bala’i ne?” naji da matsalar Da Daddy yasani yau ne ko da naka? Ɗittt ya kashe wayar.

 

Zo nan my son! “To”

Yawwa dama zuwa zakayi ka siyo magunguna acikin asibitin, to Daddy ya karɓi papern yana tafiya yana tsaki.

 

Fareedah kuwa takasa zama, da zarar taga likita yana wucewa sai tace doctor ya jikinnata? tin suna amsawa har sukayi shiru

*****************

 

Da ahmad yakawo maganin suka ɗunguma gaba ɗaya suka shiga ɗakin, suna shiga suka tarar da Fateemah ta farfaɗo, Fareedah tayi gudu ta rungumeta.

 

“Ita kuma Fateemah ta lumshe ido”

 

Ahmad kuwa yau kamar ido ya faɗo tsabar harara *nace oho de*

 

Ya jikin naki inji Daddy a hankali tace “da sauki” tom Allah yakara sauki tace “Ameen”

 

Daddy Yace idan kika ɗan samu sauki bazaki je gidan marayu ba gida zamu wuce, tnx Daddy gaskiya nima nafison taje gidanmu zamufi kula da ita.

 

A take Ahmad ya ɗago kanshi yana kallon Daddy, yace “Daddy wani gida zata wuce? ”

 

Wani gida kake ciki? Cewar Daddy, nan yai shiru yana kallonsu.

*************

 

Washe gari bayan an sallamesu ne daddy yace “Ahmad ka kaisu gida ni zan wuce gidan marayu nafaɗawa mamansu nacan bazata koma ba sai ta samu sauki”, to Daddy.

 

Mommy tace “Alhj tunda ga Fareedah me ze hana su tafi tare mu kuma muje gidan marayun tare”, ok ba matsala ay Ahmad kaisu gida, to Daddy

 

 

Da kyar Fateemah take tafiya, sabida tanajin jiki. Fareedah ce ta riketa har suka shiga motan a hankali.

 

Bayan sun ɗau hanya suna tafiya ne “Fateemah tafarajin Amai,

A hankali tace inajin Amai!

 

Fareedah tace yaya kayi hakuri ka tsaya tanajin Amai, yai shiru kamar bai jita ba, ta sake cewa “yaya Amai takeji”, nanma shiru ba amsa sema kara gudu dayake.

 

Nan Fateemah tafara sheka Amai kamar ba gobe, tofah nan yaja birki ya tsaya.

 

Yace “fitah” sukayi shiru dan Fateemah ta galabaita, ya sake cewa “nace kufita”

 

Fareedah tace “haba yaya baka ganin Amai take ne kabari mana tagama”.

 

 

Zaku fitane ko sai na Ɓata muku rai, ya daka musu tsawa!!.

 

Fateemah tafara yunkurin tashi Amma ina ba dama, da kyar Fareedah ta riketa suka fita, suna fita a motar Fateemah ta faɗi dan bata da karfi ko kaɗan.

 

Haka yana gani yaja motarsa yabar wajen

 

 

_wattpad_

Jiddahpretty

 

*jiddah S mapi*

Ummi Tandama:

*A GIDANMU TAKE*

 

 

Story/written by

*jiddah S mapi*

 

_Dedicated to my lovely sister walidation_

 

Note me on wattpad

*Jiddahpretty*

 

Page 17&18

 

“Suna shiga cikin Asibiti Likitocin sukayi kansu da gudu suka karɓe ta sai Emergency Room”,

Daddy kuwa hankalinshi duk a tashe yanata zagaye Asibitin.

 

Azuciyarshi yana tunanin to me ya tadawa Fateemah ciwon tane haka,

Dahaka har likita yafito daga ɗakin yacewa Daddy yana buƙatar magana dashi,

Daddy yace to.

“Bayan yashiga ɗakinne likita yace mishi Alh idan har kanada daman dazaka Aurar da ‘yarka to kayi mata Aure, kaga idan har agidan miji take bazata rinƙa yin wasu tinani barkatai dahar ciwonta zai tashi ba.

 

Daddy yayi shiru yana tinani, se daga baya yace to nagode Doctor.

Doctor yace “yau zamu sallameku sabida anyi mata Allura ansa mata drip idan ya kare zaku iya tafiya”

 

Bayan an sallamesu ne suka koma gida,

Daddy ya kira Hajiya Mariya yayi mata bayanin abinda Doctor yace,

Yace “Mariya bakya ganin kawai mu haɗa Auren Fateemah da Ahmad?

Tunda mun yadda da tarbiyanta,

To Alhaji ne dai banƙi ta taka ba Amma baka tinanin karmu shiga haƙƙin yarinya marainiya,

Kaga Ahmad shi bawani isashen hankali ne dashi ba kar muzo muyi abinda zai damemu,

Haba Mariya shi Ahmad ɗin ba haifanshi akayi ba?

Tunda haifanshi akayi ai munada iko dashi.

To Alh Allah yasanya Alkhairi cewar Hajiya Mariya.

 

Dahaka Daddy yasanya ranan Auren Fateemah da Ahmad, suma kansu basu sani ba! ********************

 

Akwana atashi ba wuya a wajen Allah yau ne Ranan juma’a wanda yayi daidai da yanda Alhaji Kabeer yasa ranan Auren Fateemah da Ahmad,

Fareedah da Fateemah sai ganin mutane suke suna shiga gidan suna ta guɗa. Fareedah ta tambayi Mommy meyake faruwa mommy tace ba komai,

Shi kuma Ahmad yana wajen Abokansa sunata shashancinsu, inda suketa shaye shayensu,

Bayan juma’a aka ɗaura Auren Fateemah da Ahmad, akan sadaki dubu Hamsin wanda Alh Kabeer ne yabiya,

Se dare Ahmad yadawo gida,

Daddy ya kira wayanshi yace “kasameni a falo”

 

Daddy yacewa Hajiya mariya takira mishi Fateemah da Fareedah,

Bayan sun hallara a falonne,

Alh Kabeer yayi gyaran murya yace

“Da farko dai nasan yau zakuyi mamakin yanda mutane suketa zirga zirga agidannan, to yau Aure aka ɗaura,

Auren Fateemah da Ahmad”.

 

A razane Ahmad yaɗago kanshi yana kallon Daddy,

Ya buɗa baki zaiyi magana Daddy ya ɗaga hannu yace “Banason jin komai daga bakinka kuma babbar kuskuren da zaka aikatamin shine sakin Fateemah ko wulaƙanta ta”

Sannan kuma daga gobe zata tare zuwa side naka,

Idan naga yanayin zamanku ba matsala kuma idan kun fahimci junanku saiku koma gidanka na jambutu,

Yace zaku iya tafiya.

 

“Tofah dahaka suka wuce ɗaki kowa jikinshi a mace,

Ita kuma Fareedah murna take kamar me, suna shiga ɗakin ta rungume Fateemah tana ta tsalle, ita kuma Fateemah shiru kawai tayi ta rasa me zatayi,

Dahaka Fareedah tafara haɗa mata kayanta tana cewa gobe a ɗakin yaya zaki kwana kai ammafa i will miss you,

Fateemah shiru tayi batayi magana ba tana ganin anya bazataje wajen Daddy tace a raba Aurennan ba? ,

Kai idan tayi haka kuma batayi daidai ba domin sunyi mata halacci”

 

Azuciyar Ahmad kuwa yanata kulla salon muguntar daze yiwa yarinyan,

Lalle zakici ubanki Ai nagodewa Allah ma dayasa babu Wanda yasani acikin abokai na dako nasha kunya,

Ina yaro dani ace nayi Aure ay Akwai raini.

 

“Haka Fateemah da Ahmad suka fara rayuwa,

Inda Ahmad yake mugun takura Fateemah,

idan dare yayi sai yayi ta sata tsallen kwaɗo kuma yace idan ta faɗa saiya kasheta,

Haka Fateemah tayi ta hakuri dashi idan Fareedah tashigo saita saki fuska tayi ta dariya idan suna hira,

Amma da zarar taji muryar Ahmad tofa zuciyarta tafara tsinkewa kenan”

 

“Dahaka Fateemah tayi ta hakuri da Ahmad wulakancin yau daban na gobe daban haka zatayi ta hakuri dashi, babban abinda yafi daminta dashi shine shaye shaye dayakeyi, tanason tafaɗa ma Fareedah amma tana mugun tsoronshi dan yace mata idan ta kuskura tafaɗa wa iyayenshi yana shan abu saiya kasheta!”

 

Me karatu Fateemah tasha wahala a wajen Ahmad fiye da misali.

 

Yauma kamar kullum Ahmad ne yashigo gidan A buge yana tafiya yana tangaɗi,

Fateemah kuwa tana kitchen tana itada Fareedah suna girki,

 

 

Kawai se sukaji karan buga kofa Fareedah tayi sauri zata je taduba ko menene, Fateemah tayi saurin katseta.

Tace ki bari zanje naduba dan ita tasan halin Ahmad may be yaje yasha abune yadawo,

Tana leƙa ɗakinshi taga ya kwanta rub da ciki.

 

Ai kuwa tarufeshi a,

Dataje kitche tacewa Fareedah ay ba kowa.

 

“Tofah har dare Fateemah kwata kwata ta manta da ta rufe Ahmad a ɗaki, haka Har tayi abincin dare ta ci tayi wanka ta kwanta har bacci yafara ɗaukanta, amma taji zuciyanta yanata tsinkewa tarinka cewa astaghfurullah!

 

Shi kuma Ahmad lokacin da ya dawo hankalinshi yayi wanka yanason yaje club amma me yana buɗe kofan yaji gumm!

 

Ya rasa yanda zeyi gashi yanajin yunwa kuma ana ta kiranshi awaya club yacika saura shi kawai ake jira,

Yadinga buga kofan yana kiran sunanta amma shiru.

 

Haka ya zauna yana tuna abinda zeyi mata yau idan ta buɗe kofan,

Wato raini yafara shiga takaninsu kenan!

 

tana zaune kawai ta tuna yau Ahmad be zageta ba anya lafiya kawai seta tashi tafita tace bara na lekashi nagani,

Tana zuwa taga kofanshi a rufe, taɗan buga ƙofan kaɗan.

 

Kamar jira yake yace waye tayi shiru, yace oya open the door

 

Sai alokacin ta tuna abundance yafaru da rana ta zaro manya manyan idanunta tace kayi hakuri zan buɗe na mantaka ne wallahi,

Cabɗi ni ta manta?

 

A Gidan Mu take

 

 

Name: [A Gidan Mu Take HAUSA NOVEL ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: November, 2021

 


6 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!