A Jininsa Yake Hausa Novel Complete

Ajininsa yake 1-01
Posted by ANaM Dorayi on 07:24 AM, 03-Nov-15
Under: Ajininsa yake
__________________ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
________
Rabe jikin daya daga cikin bishiyon da suka yi wa
filin sukuwar kawanya. Jikinsa kayan mkrntar
firamare ne. Farar riga da koren wando. Gaba-
daya hankalinsa tattare ya dora bisa dawakan da
ke zuba tsere kamar za su tashi sama. Babu
abinda yake tunani, illa ina ma shine bisan dokin
da yayi wa saura fintankau?”
Jama’a suka hau ihu, don taya mai dokin daya zo
na farko murna. Shi ma ya kwasa a guje.
Yana isowa bai ma san ya jefar da jakar
littattafan sa ba. Ana ture shi, yana turawa, sai
da ya kutsa ya ta6a jikin saurayin daya zo na
farko.
Kamar an sanya shi al-janna, haka yake ji cikin
ran sa.
Wasu rukunin dawakan ne za su taso yanzu, shi
yasa duk jama’a suka koma inda suke.
Haka shima ya nemi wata bishiyar ya kuma
ra6ewa jikin sa na tsuma, tamkar na ‘yan dambe.
Caraf!
Ya ji an cafke kunnunwan sa 2, a firgice ya juyo,
su kai ido 4 da mahaifinsa. Ido warwaje ya daga
hannayen sa sama, amma ya kasa cewa komai.
“Ba za ka daina bata min rai ba Naseer?
Makarantar kenan?
Ya 6ata rai kwarai, manyan idanuwan sa suka
kada jajir!
Haka ya tsurawa Baban sa ido.
“Zo mu je mkrntr, jikinka ne zai gaya maka,
tunda kai kunnan kashi gare ka, ni ma ba zan
fasa ba!
Ina jakar ka?
Ya shiga dube-dube,”Au jakar ma ba kasan inda
take ba?”
Ya maka masa duka a keya,”Wuce mu je ka nemo
jakar, dan banzan yaro marasa jin magana!”
Yaja kunna sa suna tafiya har suka yi karo da
jakar,”Duka ka dauko ta!”
Ya sa hannu ya dauko, a haka suka shiga. Cikin
mota, kunci kamar Naseer zai yi bindiga sabo da
kunburi.”(L.E.A Primary School) da ke kusa da
ofishin “Yan-sanda na Tudun Wada Zaria nan
suka shiga shugaban makaranta.
Ya tsura masa ido ya-ce,”Ba za ka bar Babanka
ya huta bane Naseer! Kai wane irin yaro ne?” Ya
juya gefe ya tura hannunwan san a aljihu.
Hedimasta ya dankwafar kan sa ya ce,”Rage
tsawonka, ka kuma cire hannayen ka daga
aljihu!”
Ya durqusa yana huci, saboda tsabar zuciya,
kirjinsa na bugawa muraran kowa na gani.”
Malam Balarabe ya ce,”Zane min shi za ka yi a
gaba na in gani.
Idan kuma ba za ka iya ba, ni zan dauki bulalar
in hukunta shi bar ni da shi.
Ya ce,”nan da nan ban zuwa Hedimasta, sai na
ga jikin Naseer yayi rudu-rudu.
Ina bulalar take? Miko min ita nan!”
Hedimasta ya jawo dorina, Baban sa ya cire masa
riga da karfin tsiya yana kallo aka rinka tsala
masa dorina dai-dai har goma sha biyu.
Amma Naseer ko gezau bai yi ba, balle ya fidda
hawaye.Takaici kamar ya kashe Malam Balarabe,
ya ja kujera ya zauna, ya ce,”Ban san yadda zan
yi da wannan yaron ba, shi kadai gare ni, amma
gaba d’aya ya buwayeni.”
Hedimasta ya ce,”Sai addu’a, yaran yanzu addu’a
ce ke ladabtar da su, don haka ka yi tayi masa
ita.
Babu komai, ka na iya komawa ka bar ni da shi
kawai.
Ya karkada kai cike da damuwa, yasa aljihu ya
labubo Naira 2 ya dora bisa tebur ya ce,”Ga
kudin tarar sa nan don na san da wadancan ya
shiga mota ya je filin sukuwar.”
Ya ce,”To shi ke nan.
Allah ya shirya mana.”
Ya mike yana fadin,”Amin.
Ya mika masa hannu suka yi Musabaha.
Ko ta kan Naseer bai sake bi ba, ya sa kai ya
bar ofis din.
Hedimasta ya duba shi ya ce,”
“Naseer!”
Ya sunkuyar da kai kasa, ban tanka ba.”
Haba Naseer, ka na da kokarinka, kaf ajinku
babu mai kwakwalwar ka, amma ka zauna cikin
aji, sai ya gagare ka?
Kai kullum hankalinka na filin Sukuwa.
Idan ba kayi karatu yanzu ba, sai yaushe za ka
yi?”
Ko alama kai ba ka koyi da abokanka, ba ka
tausayin mahaifinka.
Kodayaushe shine zarya filin sukuwa yana kamo
ka.
Ka yi wa kanka fada Naseer, ka ga yanzu aji 6
ka ke, a gantale, a gantala dai ka kusa zana
jarabawar shiga sakandire, idan ba ka maida
hankali ba, ka na ji ka na gani abokanka za su
wuce su bar ka anan.Yanzu abinda na ke son ka
da shi, shine ka maida rigan ka, ka wuce aji, ka
ga sauran minti 10 a fito (Break), sai ka zo ka
amshi kud’in ka.
Ga su nan aje su waje na. Idan ba ka zo ba,
wannan zai tabbatar min cewa ka gudu ne.
Tashi ka wuce.”
Ya mike ya maida rigarsa, bayan sa rudu-rudu
da zanan bulala.
Kai tsaye ya wuce ajinsu.
Malamin da ke cikin ajin yace , “Sai yanzu ka ke
zuwa?” Yayi shiru yana hura hanci.
Ya ba shi rankwashi 2 masu kyau, sannan ya-ce
ya je ya zauna.
Ya taho a kunbure ya tsaya gaban bencin baya,
inda ya saba zama.
Kallon sauran yaran kawai yayi, suka hau
matsawa ya sami wuri ya zauna. Ya ci gaba da
kunci, bai ko sauranon Malamin turancin da ke
ajin har aka kada Break tara. Malam ya fita,
kowa yayi waje, sai Naseer kadai ke zaune yana
tunanin yaya za’a kare wasan da ya baro ana
yi? Wani yaro dai-dai tsawon sa wankan tarwada
ya shigo, ya zauna kusa da shi.
“Naseer, ashe ka zo?
Ya dube shi ido jazur!”
“Eh,
Ya kura masa ido ya-ce,”Yau ma dukan ka aka
yi?”
“Ban sani ba!”
Ya fada cikin fushi.
Ya-ce,”Ai na gaya maka, kar ka je, amma ka ki
ki, don na san dole ne Babanka zai zo nan ya
bincika.”
Ya nuna shi,” Kar fa ka dame ni Sageer, meye
ruwan ka!
To!”
Ya mikie ya-ce,”Allah ya ba ka hkr. Ni zan je
wajen masu abinci, in sayo maka gyada ne?”
Ban ci!”
Ya amsa, bai kalle shi ba.
Sageer ya wuce abin sa.
Tsaki yayi, ya jawo jakarsa ya fidda littafin sa da
biro yayi ta zana dawaki suna tsere, ko alama
bai yi tunanin ya je ya amso kudin sa ba. Duk
da cewar Hedmasta ya-ce idan bai zo ba, to ya
san ya gudu ne.
Kuka yake ta ji, ta bayan tagar ajin da yake
zaune. Kwarai kukan ya dauki hankalinsa, don
haka ya mike ya leka.
Wata ‘yar yarinya-ce rabe take ta gurshashan
kuka ba ji, ba gani.
Akalla za ta kai shekaru 8 ko fin haka.
Ya sanya mata ido, duk tayi zufa, majina sharaf-
sharaf, nan take tausayin yarinya ya lullube shi.
Ta tagar yayi tsalle, ya diro gaban ta, don haka
ta dube shi a firgice.
“Ke da wanene?
Ta kasa magana, saboda kuka da ya ci karfinta.
Ya kamo kafadun ta, ya-ce,”An ce wa ya duke
ki?”
Cikin muryar kuka ta amsa,”Kudi na ne suka
fad.”
Kudinki?”
Ta amsa da ka.
“To ina yan-uwanki?
Ko ba ki da su?”
Da ka tasa ke amsawa.
Yayi dan shiru, ka-fin ya-ce,”Ki yi shiru, zo nan
ki zauna ki jira ni.
Ya jawo hannun ta, suka zagayo barandar ajinsu
ya zaunar da ita,” Zauna nan ki jira ni.”
Ta zauna tana share hawaye.
Wasu na sake zubowa.
Kai tsaye ofishin Hedimasta ya nufa.
A kofa suka yi kicibi6.
Hedimasta ya-ce,”Ai na dauka ka yi halin naka
ne.
A jinku da za ni yanzu, shigo ka amsa.”
Suka shige tare, ya jawo dirowa ya dauko, ya
mika masa.” Ana tashi kuma, ka zo nan kafin ka
wuce gida.”Can kasan makoshinsa ya amsa da
“To.”
Ya fice.
Malama Abu da ke zaune ta ce ,”Ina son yaron
nan, amma bai son karatu, ga shi da kokori.
Hedimasta ya ce,”Ke ko ni wallahi akan dole na
ke dukan sa, saboda baban sa tausayi yake ba
ni, koma yana son yayi karatun.”
Ta ce,”Yara ai sai hkr, Allah dai ya shirya mana.”
Ya ce,”Amin.”
Shi kuwa wajen yarinyar nan ya koma, har
yanzu tsiyayar hawaye take yi.
Ya kamo hannu ta yana fad’i,”Har yanzu kukan
ki ke yi?
Ta so mu je ki zabi abinda ki ke so ki ci.”
Ya ja ta zuwa wajen masu abinci.
Can ya hadu da Sageer.”
Ina ka samo wannan?”
Ya ce,”Kudin ta ne ya suka fadi, shine take
kuka, kuma bata da kowa anan.
Zo ki zaba, me ki ke so?”
Kankara kawai ta nuna.
Ya siya mata, sannan ya kara mata da aya mai
siga da gyada mai gishiri.
Ta ce,”Na gode.
Ya kamo ta suka dawo da Sageer.
Nan bisa baranda suka zauna su 3 tana ta shan
kankara ta.”
Ya sunan ki?”
Ya tambaya ta.
Ta-ce,
“Zahra Umar.Ya ce,”Wane aji ki ke? Ta amsa,
“Aji uku.” Ya ce,”To maza ki cinye, ki koma aji.
Ya juya suka ci gaba da hira da abokan sa.
Labarin wasan da ya baro ana yi, shi yake ba
Sageer.
“Abinda ke hana ka karatu kenan Naseer, kai
kullum hankalinka ka akan polo yake.
Ya gyara fuska, don shi Naseer akwai iya tsare
gida tamkar wani babba, ya ce,”Kowa ya dame
ni akan Polo, ni kuma ina so, burina in ganni ina
sukuwa, kamar Yakubu Jah-Jah. Yau ba karamin
burgeni yayi ba, sai da na kukkutsa na ta6o
shi.”
Ya ce,”To ai komai dan lkc ne Naseer. Ina
amfanin kullum sai an yi maka bulala? Dubi jikin
ka, ko’ina ta6on bulala ne, sam ba ka jin
magana Naseer.” Ya ce,”Ban ji din idan ka yi
min iskanci yanzun nan, zan kwashe ma hakori
wallahi, ka kuma sake magana, ka gani.”bai ce
kala ba, ya juya ya ci gaba da murza gyad’ar sa,
yana afawa baki. Naseer ya juyo kan Zarah, sai
ya ga wayam!
Tuni ta kama gaban ta. Yayi dan shiru, kome
yake tunani? Oho.
Ya dubi Sageer, ya ce,”Yaushe Zarah ta gudu?”
Yayi banza da shi, yana ta jan gyadarsa.
Tsaki yayi shi ma, ya mike ya haura aji ta taga.
Yara cike da ajin ga littattafin sa da biro, amma
babu wanda yayi gigin ta6awa, don sun san
kayan Naseer ne.Yana zama ana kada
kararrawa. Muryar Sageer ya ji ta taga yana
cewa,”Dama ana tashi ka yi tafiyar ka, kar ka
sake ka neme ni!”
Ya ce,”Kai din banza, wa zai neme ka?
Mts!
Ya dauke kan sa daga kallon sa.
Shi ma tuni ya bar wajen ya nufi ajin su.”
Karfe sha biyu da rabi aka tashi.
Naserr ya fito rataye da jakarsa, babu abinda ya
tsinana da littafin sai dai dan banzan zanen
dawakai.
Yana tsaye bisa barandar yana kallon yara na ta
wucewa.
Can sai ga Zarah a gujeni ta za ta wuce.” Da
sauri ya kwala mata kira,”Zarah!”
Ta dawo gunsa da fara’a ta,”Sai ku gudu, babu
sallama?”
Ita dai dariya ta sani. Sai gobe kenan?” Ta ce,”
Eh.”
Ya ce, shi kenan, amma ki dina gudu, kar ki fadi
kin ji?”
Ta ce,”To.” Bata saurari komai ba, ta juya ta tafi
a hankali, kamar yadda ya ce. Ya kasa dauke
idonsa a kanta, har ta sha kwana.
Kawai ya ji kaunar sukuwa. Ya sakko daga
barandar, ya nufi ofis din Hedimasta, yana fadi
a ran sa,”Shi kuma wancan dan rainin wayau,
wai sai na je gun sa, kafin in tafi gida.
Mts!
Ya ja tsaki.
Fuska murtuke ya shiga ofis din.
Kaf Malaman da ke ofishin, sai da suka tanka
masa.
Ba su ishe shi kallo ba ma, balle ya tanka ma
su.
Gaban tebur ya tsaya, yana kallon
Hedimasta.Shine ya yi masa magana,”Manya!”
To akama hanya, kar ayi kwana ko’ina sai gida.
Ka ji ni da kyau?”
Ya juya manyan idanuwan sa ya ce,”Uhm

Gobe kuma 7 da rabi ka same ni anan.
Kama hanya ka wuce.”
Ya juya ya ce a ransa,”D’an rainin wayau!”
Malama Abu tayi kiran sa.
Ya matsa wajen ta ya tsaya.
Ta kare masa kallo sannan ta ce,”Ayi kokari, a
zo, makarantar gobe don Allah.”
Ya murza ido ya amsa,”Ai zan zo.”
Ya wuce tana kallon sa.
Yana fita ya saki tsaki,”Wannan matar, wata
rana sai na tara ma duwatsu wallahi!”
Bai nemi Sageer ba, ya kama gaban sa.
Dai-dai wata kwana yahango Malamin
turancinsu, wanda ya rankwashe shi da safe, ya
rabe jikin kwanar, ya waiwaga bai ga kowa ba.
Yasa hannu ya dauki katon dutse, ya wulwula
masa.
Kau!
Malami ya ji saukan dutse bida ga keyar sa.
Ya dafe keya yayi ta neme-neme, amma bai ga
kowa ba. Cikin hanzarinsa ya dawo kan kwanar,
ba kowa a wajen.
Makale yake jikin wani gida, yana hango Malam
na ta murza keya yana kwafa.
Sai daya bar wajen, sannan ya fito ya dafe a
guje.
Ya kusan isowa gida, ya ci karo da wasu yaran
‘yan makarantarsu suna tafe su hudu sun gara
kwallon nan sama,Babu bata lkcn kwallo ta
haura katangar mutane, ta fada cikin gidan.
Yara suka tsaya suna kallon Naserr.
Ya gyara fuska ya ce,,”Ku shiga ku dauko mana.”
Guda ciki ya ce,”Malam kar ka raina mana
hankali ma na, ba kai ka jefa ta ba?”Yana rufe
baki. Mai-gidan na fitowa da kwallon a
hannunsa. Suna kallon yasa wuka ya yanka ta 2,
ya jeho musu, ya juya cikn gida abin sa.
Me Naseer zai yi?
Ba dariya ba.
Yaro mai kwallo ya ci kwalar Naseer,”Wallai sai
ka biya ni kwallo na!” Haka sauran yaran suke
ta fadi, duk suka yayyame shi.
Wani dan murmushi yayi yace,”Malam ka sake
ni girma da arziki.
Idan ka yaga min riga, kaf hakorinka kaf, sai na
kwashe ma su.” Ya ce,”In ka isa.
Allah ya tsine min!” Koda Naseer ya dunkule
hannu, sai kwaf!
Bisa hancin mai kwallo.
Nan take jini ya tsinke. Dambe ya kwaure da
abokan mai kwallo. Su 3, amma ba su ishi
Naseer komai ba, haka ya ringa wuji-wuji da su,
ya na jefarwa. Mutane suke fara taruwa, aka
raba, binicike ya tabbatar da Naseer ne bai da
gaskiya.
Amma bakin sa yaki mutuwa, saboda haka
samari 2 suka cukuikuyo shi, har gida da yaron
nan jini na ta fita ta hanci. Hayaniya Malam
Balarave ya ji zauren gidan sa, don haka ya fito
yana tambaya ko lafiya?
Ganin Naseer da gayyar yara. Shi ya tabbatar
masa Naseer ya sake dauko masa wata
maganar. Akai masa bayani, dole Malam
Balarabe ya biya kudin kwallo.
Sannan ya kai wanda aka fasawa hanci kemis
aka wanke masa da magani, kuma ya kai shi har
gidan su, saboda gudun tashin hankali.Naseer
na zaune, ya kunbura suntum, da gani ya sha
fada wajen mahaifin sa. Malam Balarabe ya
shiga tsakar gida ya zauna bisa tabarma ya sa
wa Naseer ido.
Ya kada kai, ran sa bace ya ce,”Kai
jama’a,”Naseer ko kauye zan maida ka ne?
Wannan fitina, ta ishe ni! Jin muryan sa yasa ta
fito da daki.
“Ka dawo Malam?”
Ya ce,”Na dawo Mairo.
Zo ki zauna ki ji.” Ita ma ta zauna a
tabarma.”Naseer ya ishe ni, zan maida shi
kauye, ya je can yayi noma, tunda karatun ma
ba son shi yake ba, sai dan bazan daukan
magana.” Ta ce,”Malam ka ce ya kara lalacewa
kenan……….”Ya katse ta,”To ya ki ke son in yi?
Karatu fa Naseer ba yin zai yi ba, ai gara ya
koma can yayi Noma.”
Ta ce,”Wannan mai kunnen kashi ne zai yi
noma?
Bai yi karatu ba, sai aikin wahala? Malam, barin
Naseer a gaban mu, shine mafi alkhairi a gare
mu, don ko banza ba mu gan shi ba a
makaranta ba, in ka je filin Sukuwa za ka gan
shi.
Duk rigimar da zai kwaso, zai fi kyau ya kwaso ta
a gaban mu.
Da ka dauke shi ka kai wurin da bai sa ba, ba
kuma shakkar su yake yi.
Mu yi ta yi masa addu’a.
Allah zai duba mana.”
Malam Balarabe yayi shiru, jin ka fin ya sauke
numfashi ya ce,”Ya ci abinci?”
Ta ce,” Ina fa.
Ai ka san yadda ya kumbura, ya dankare anan,
haka zai yi ta zama, idan ba Sageer ya shigo
gidan nan ya daga shi ba.
Ya ce,”Allah ya shirya.
Ta ce,”Amin.
**********
Satin nan tsaf! Naseer na zuwa mkrnt kamar
abin ya dore a haka. Kuma kodayaushe aka fito
tara. Zarah na tare da shi, ya siya mata
wannan, ya siya mata wancan.
A ‘yan kwanakin nan sosai ta saba da shi, don
har gida tana ba Innar ta labarin Naseer.
Ba karamin mamaki Naseer ya ba kowa ba,
ganin bai ta6a jera kwana biyar cur, yana zuwa
mkrnt ba.
Yau litinin yayi shirin mkrnta, sai dai zuciyar sa
bata raya masa ya je makarantar ba.
Kai tsaye bakin titi ya nufa, ya shiga motar
sabon gari. PZ. Daga can ya karasa filin sukuwa
a kasa. Baban sa bai neme shi ba, don ya ga
abin yayi sauki wancan satin, saboda haka
shima yayi zamansa a runfar sa da ke kasuwar
Tudun Wada, inda yake siyar da kayan miyan sa.
Naseer kuwa can ya wuni, domin wasan da yake
son gani ba a fara ba ma, sai 10 na safe. Gab
da sallar azahar ya dawo gida cike da farin ciki,
don yau sosai ya sha hannu da mutuminsa
Yakubu Jah-Jah.
Umman sa ba tayi masa magana ba, duk da
cewar ta fahimce ba makaranta ya je ba.
Bayan ya ci abinci, yayi Sallah. Nan ya gungura
bisa tabarma yayi ta barci har karfe uku da
rabi.
Umman ta shi, ta tashe shi ta ce yayi sallah, ya
tafi Islamiyyar sa.
“Sai ka ki zuwa mkrnta yau?” Inji Sageer. Ya
ce,”Ban je din ba, sai me?”
Ya ce,”Sai me kuwa? Hedimasta na nan yana
jiranka.” Ya ce,”Kar ya rage min rai. Sageer yayi
dan murmushi ya ce,”Ba ka ma san wani abu
ba, na je ajin ku neman ka, sai na ga yarinyar
nan Zarah ta sha kuka, ta gaji, wai bata gan ka
ba.
Ni ne ma na rarrashe ta, na je na siyo mata
kankara da gyada.
Tun da yake magana, ya sanya masa ido har ya
kare.
Hankalinsa tashe ya ce,”Inna lillahi. Wallahi
mantawa na yi.” Ai kuwa ta sha kuka, har da
‘yan mangwaron guda 2 a hannu, na yi na yi ta
sha mangwaron ma, ta ki wallahi.
Nan da nan ran sa ya 6aci ya fada tunanin
Zarah.
Can ya nisa ya ce,”Gobe zan je mkrntr. Ya
ce,”Da dai ya fi.
Suka isa Islamiyya suka shiga aji.
Fadan sa biyu da yara ka fin Malam ya shigo
cikin aji.
Washe gari Naseer ya je makaranta, kuma Zarah
ya fara nema a jin na su, ka fin a shiga asanbili.
Tana tsaye bisa barandar ta hango shi tafe.
Da gudu ta sauko ta kama shi, tana murna.
“Zarah!”
Ta dube shi,”Jiya ban zo ba ko?”
An ce ki na ta kuka.”
Ta ce,”Inna ce ta ba ni mangwaro ta ce,”In sha
daya, in kawo maka daya.
Ina ta neman ka, ban gan kaba.”
Yayi dan murmushi, ya ce,”Kuma sai aka ce ki yi
kuka?
Kar ki sake kin ji?”
Ta ce,”To.
Tana lalubar Jakar ta.
Mangwaron ta dauko ta mika masa,”
Ga shi nan, na boye maka shi a jaka ta.’a
Ya amsa yana fara’a sosai,To na gaode, idan kin
koma gida, ki cewa Inna na gode.”Ta amsa da
,”To.”
Tana fadi ana kadawa, don haka ya ja hannun
ta zuwa layin su, ya sanyata a layi har yana ba
na kusa da ita gargadinka kar su sake su ture
ta.
Da (Break) tare suka yi kamar yadda suka saba.
Koda aka tashi, sai da ya tsallakar da ita titi,
sannan ya dawo suka wuce tare da Sageer. Har
cikin ran Naseer, yayi alkawarin ba zai sake
fashin mkrnt ba, sbd Zarah, kar ta neme shi, ta
rasa, hankalin ta ya tashi ta yi kuka.
Ranar laraba ya je mkrnt, ya nufi ajin su Zarah,
aka ce masa bata iso ba tukuna. A asambili bai
gan ta ba, har aka fito break. Ya shiga damuwa
kwarai, dn haka ana tashi, ya binciki wadanda
suka san gidan su.
Ya samu, suka dunguma tare da Sageer da
sauran yaran.
A gangare gidan su yake, suka tsaya a zaure.
Baban ta ya ritsa su, sai ya wucr cikin gidan. Ya
ce,”Lafiya yaya aka yi?”
Naseer ya ce,”Ba mu ga Zarah a mkrnt bane,
shine mu ka zo mu duba ta.
Cike da fara’a ya ce,”Ayya!
Zarah yau babu lafiya, zazza6i take yi.
To ku shigo mana, shine za ku tsaya a zaure ku
na leke?
Ka yaro ho!”
Suka bi bayan sa har dakin Innar Zarah.
Tana kwance, anyi mata shimfida a bakin kofa,
an daga labule don ta sha iska.
Malam Umar ya ce,”Ku shigo, ta nan a kwance.
Ina A’in take ne?”
Zarah ce ta gaya masa tana bayi.
Su Naseer suka shigo suka zauna gefe suka,
gaishe ta, bata iya amsawa ba, wai kunya sai
6oye fuska take yi.
Innar ta ta shigo tana fadin Baki mu kayi?” Ya
ce,”Yan makaranta ne, suka zo duba autar
ki.”Ta ce,”Ah! Sannun ku da zuwa.” Suka gaishe
ta, ta amsa tana zama kusa da Zarah, hakan ya
ba Zarah damar hayewa jikin ta, tana mata
rada.
Cike da fara’a Innar ta ta dube su,”Wanene
Naseer din? Ya sunkuyar da kai, yayin da Sageer
ke nuna shi. Ta ce,”Kullum sai an ba mu lbrn
Naseer. Ya tare fada, ya siya min wannan, ya ba
ni wancan.
Ashe babba ne.
Ajinka nawa?”
Ya ce,”Shidda 6,.”
Ta ce ,”Ashe ma ka ku san gamawa.
Lallai Zarah za ta yi kewa, don shekaran jiya ne,
ba ka zo ba ko?
Nan ta ishe ni da magana, Inna yau Naseer bai
zo mkrnt ba.
To mun gode Naseer.
Allah yayi ma ku albarka.”
Duk kunya ta rufe shi da kyar ya ce,”Amin.
Malam Umar ya ce,”To an gode, sai ku tashi
kowa ya tafi gida ko?” Kar aga kun dade ba ku
koma gida ba. Mun gode.” Suka mike suna
fadin,”Allah ya kara sauki.” Iyayen ta suka ce
“Amin.”
Sun fice, jim kadan wani yaro ya dawo cikin ‘yan
rakiyar Naseer.
Wani kulli leda ne ya shigo da shi,.” Wai ga shi
in ji Naseer.
Ya aje gefen Zarah ya ruga a guje.
Inna na ta dariya. Ta kwance bakar ledar, kullin
gugguru da gyada ne a ciki da aya soyayya. Ta
kada kai ta ce,”Allah sarki yaro, shi kuma jininsa
da na Zarah ya hadu.
Malam Umar ya ce,”Shiririta ke nan.
Ko ina ne gidan su?
,”Oho.”
Ita kuwa Zarah tuni ta fara diban abin ta tana
ci.
Kwana 2 Zarah na kwance a gida.
Kullum sai Naseer ya je gidan da safe da
yamma. Hakan yasa iyayenta suka san Naseer
sosai.
Innar ta ke cewa”Lallai Zarah Allah ya ba ki
yaya daga sama.”
Shi yasa da ya zo, sai ta ce, “Zarah ga yayanki
ya zo.” Ko barci take kuwa za ta tashi. Sai dai
Zarah ta warke ta koma Mkrnta, sannan
hankalin Naseer ya kwanta.
A dalilin Zarah. Naseer ya nutsu a mkrnta, ko
sau daya baya fashi, duk da cewar bai bar Polo
ba, domin duk asabar da lahadi in dai akwai
wasa, toh yana can. Ba karamin mmk ya ba
kowa ba. Iyayensa na ta murna, suna yiwa Allah
godiya, duk da dai rigimar sa ta neman magana,
tana nan babu abin da ya sauya.
Naseer kam bai iya zama na cikakkiyar awa 3,
sai ya nemi abokin dambe.
Duk sa’o’insa tsoronsa suke yi, sbd karfinsa,
balle kananan yara.
Ganin ya nutsu a mkrnt, yasa Hedimasta ya
nada shi (Labour prepet). Sosai yake gudanar da
aikinsa, don ba sauki, ga yara.
Zarah ko ajin su kuskuran kallon banza, babu
mai yi mata shi, sbd kanwar Naseer ce.
Kokarinsa da komai, sai ya nuna shi babba ne,
ke sawa yana kara kwarjini a idon kowa.
Allah yayi masa kyau, surar jikinsa kaf bai da
makusa.
Shi ba fari bane, kuma ba baki bane,.”
Sannan ya zarce wankan tarwada.
Wasu manyan idanuwa da Allah yayi masa
farare sol!
Su ke sawa duk wanda ta kallai, sai tayi
sha’awar sa.
Ubangiji yayi wa Naseer wannan baiwa.
Wanda adalilin haka ne kawai yake shiga ran
jama’a su kamu da kaunar sa.
Yau suke zana jarabawar share fagen shiga
karamar sakandire (Common Entrance). A
kwalejin Alhuda-huda. Sun yi, sun gama cikin
sa’a kowa ya koma gida.
Ranar litinin suka taru a mkrnt, kamar yadda
aka bukace su.
Hedimasta ya raba masu satifiket da
Testimoniya, sannan ya sallame su, sai ranar da
jarrabawa ta fito, za’a neme su.Suna fitowa,
ana tashi tara. Naseer ya kama hannun Zarah
ya kai ta siyen kayan kwalama. Daga nan aji ya
zagaya da ita, yana ba yara kashedi da gargadin
NI duk wanda ya kuskura ya ta6a masa Zarah,
musamman zai zo mkrntr kuma kashin mutum
ya bushe, idan ya kama shi.
Shi dai Sageer bin sa kawai yake yi, yana dariya.
To wa zai ta6a ta? Bayan Naseer sunan ya gama
firamaren ne kawai, amma kodayaushe yana
can, sai ya tabbatar da Zarah ta yi break, an
koma aji, sannan ya kama gaban sa.
Idan ya ga dama ya zauna rumfar Baban sa,
idan bai yi ra’ayi ba kuma ya buga yawon sa,
musamman idan akwai wasa a filin sukuwa.
Kwalejin jeka, ka dawo ta gwamnati da ke
kufena, ita Naseer ya samu, yayin da Sageer ya
sami kwalejin Alhuda-huda.
Karatu ya kankama, hakan bai hana Naseer kula
da ‘yar kanwar sa ba.
Kullum safiya a bakin kofar mkrntr su take
samun sa yana zaman jiranta, sai ya danka
mata kudin tara da dukkan abinda ya ci ya rage
mata, sannan ya wuce.” Bai hada wata 3 ba,
gaba daya a mkrntr sunan sa yayi tambari, ko
dama shi ne shugaban ajin su watau (Monitor)
Tun daga Malamai har manyan da ke gaba da
shi, sun san Naseer da kokari da rashin ji.
Babu damar manyar sa su ta6a shi, ana fita
wajen mkrnt, zai tara masa duwatsu.
Suna ji suna gani Naseer ya gagare su, ba’a
dade ba, ya zama abokin kowa, suna kiran sa
HUKUMA.
Ba wanda bai san Naseer Hukuma ba, har
shugaban mkrnt (Principal). A yau da aka kawo
masa Naseer gaban sa da laifin rufewa Malamin
su kofa.Principal ya dube shi da kyau ya
ce,”Mece ce hujjar kullewa Malaminka kofa?”
Yana daga durkushe kyar! Ba alamar tsoro ya
ce,”Duk ranar da babu asanbili, karfe 7 da rabi
yake rufe mana kofa, duk wanda ya zo bayan
wannan lkc, sai dai ya zauna a waje.
Darasin English ya wuce shi kenan. Shi yasa na
gaya kowa yayi kokari yau ya zo da wuri, sai
kuma ga shi yau Malam bai zo ba, sai takwas
saura kwata, dalilin da yasa kenan na rufe kofa,
don shi ma ya makara.
Principal ya tsura masa ido, yana mamaki,”A ina
ka ta6a jin an rufe wa Malami kofa?”
Ya sosa keya ya ce,”A kufena.” Nan da nan
Principal ya shaka,”Iskancin ka ya zo kaina ne?
To na lura ba ka da tarbiyya, sbd haka bayan
sajen ya hukunta ka, za ka koma gida ka huta
sati 2, idan za ka dawo kuma da Babanka.”
Naseer yayi shiru, ko ajikin sa, shi nan take ma
yake tunanin zai sami isasheshen lkcn zuwa filin
Sukuwa. Yana tsaye garau!
Sajen yayi masa bulala goma masu kyau.
Aka mika masa takardar hutun cewa aji.”
Ga wata sanarwa!. Zan tafi Saudiyya, sati 2 zan
yi idan Malama ya sake rufe ma ku, kofa ku aika
min da sako daga can zan sa masa (Road
block’ .
Duk suka dau ihu……..

See also  Amatulmaleek Hausa Novel Complete

 

Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100

 

Ajininsa yake 1-02
Posted by ANaM Dorayi on 09:40 PM, 03-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_____________Ya
daga hannanyensa sama, ya ce,”Sai na dawo!”
Suka ce,”Hukuma!” Hukuma!!”
Ya ce,”Ko ba’a rarrashe ta ba, hakuri take don
U……..in karasa?” Ihu kawai suka yi.
Shi ya jawo hankalin Malamai.
Nan take aka firfito da su waje, duk aka ce su
zube sajen yayi masu biyar-biyar.
Shi kuwa Naseer aka tasa keyar sa ana dukan su
suna ihu.”
Abar mana Naseer! A bar mana Naseer!!
Karfe tara da kwata ya dawo gida, lkcn Baban sa
ya riga ya fita.
Umman sa ta ji motsin bude dakin sa da ke
zaure.
Ta leko, don ganin wa ke taba kofar, Sai ta gan
shi.
Fuska yamutse ya ce,”Koro ni aka yi.”
Ta ce,”Ka biya kudin mkrnt Naseer, me zai sa a
kore ka?”
Yayi dan shiru, ka fin ya ce,”Laifi na yi Umma.
Ta tsura masa ido, ta ce,”Haka dai, kullum kai ba
ka girma Naseer, balle ka yi wa kanka fada.
Laifin me ka yi kuma?Kai tsaye ya gaya mata
abinda ya faru.
Ta kame ha6a ta ce,”Tirk’ashi! Allah ya shirye ka.
Zaman gida ka fi so ko? To ai shi ke-nan, sai ka
yi ta zama ranka na maka dad’i.” Ta juya ta shiga
cikin gida abin ta. Ya tura kofa ya shige d’aki, ya
watsar da littattafansa gefe, ya kwanta ringigine
bisa ‘yar katifarsa yayi shiru, can ya ja d’an tsaki
ya ce,”Komai dai ni ne mai laifi, mutum ya raina
mana wayau, sai a k’yale shi?
Mts………”
Ya ci gaba da kuncin rai, wai kullum shine mai
laifi. Da yamma Baban sa ya dawo. Mairo ta
mayar masa da abinda ya faru. Yayi shiru bai iya
cewa komai ba. Suna zaune k’ofar gidan su
Sageer, shi din ke masa fad’a.
Naseer 6ata lokacin ka ka ke yi. Wallahi ina gaya
ma wannan maganar ka na ganin ihun banza
nake, ba za ka gane kuskuren ka ba, sai nan
gaba. Shi karatu ko na k’wana d’aya ya wuce ka,
ai an cuce ka, balle na sati 2. Amma fa sai ka
yarda.”
Ya ce,”Me zai faru, idan ban yarda ba? Ya
amsa,”Me kuwa?” Kawai ina gaya ma gaskiya ne.”
Ya nuna shi ya ce,”To ashe kai ne babban mai
6ata lokacin sa. Ni nan da ka ke gani, ba’a raina
min wayau. Gidan su Zarah za ni, za ka?”
Ya hahare shi ya ce,”Ban zuwa..” Kar ka je, sai
me?”Yayi banza da shi.
Ya mike ya wuce abin sa.
Sageer ya bi shi da kallo, ya kad’a kai ya ce,”Ina
tausaya ma Naseer.
Allah ya shirye ka.” Shi kuwa gidan Zarah ya je
suka sha hira cikin gidansu da Innar ta gab da
kira magariba, sannan ya koma gida.
**************
Washe gari da safe 7:30, kamar yadda ya saba
fitowa yana tsaye gefen titin Kongo, wanda ta
mik’a har (W.T.C). Jar T.Shirt ce a jikin sa da
wandon Jeans. Nan ya saba jiran Zarah, don bata
kud’in tara.Zuwa can ta doso, kayan makaranar
nan sun sha guga, sai d’aukan ido suke yi tamkar
yadda ita kanta Zarah ke d’aukan hankalin
jama’a, sbd tsabar kyau da kullum take kara yi.
Kayataccen murmushi suke wa juna, sai da ta zo
gab da shi, ta ce,”Yayana, ban gane ba, ina
uniform?” Ya tura hannayen sa aljihu ya ce,”Ga
su nan a jiki na.”
“Wai ba za ka makarantar bane ko yaya ne?”Ya
zura mata ido yadda take motsa bakin ta, yake
burge shi,”Huta na ke yau.” Ta ce,”Wasa da
karatu Yaya na?” Gaskiya ni ma zuwa na bai da
amfani, mu je gida kawai ni ma in cire.” Yayi
d’an murmushi ya ce,”Ki na so in yi miki bulala
kenan? Ita ma murmushi tayi,”Ka san Allah, sai
na had’a ka da Inna. Ya sanya mata ido, ya
kasa cewa komai.” Ka na ta kallo na, magana na
ke.”
Ya ce,”Yau fuskar ki tayi min kama da hasken
zara, sai na tuna ashe zarar ce.”
Ta dan shagwa6e fuska,”Kai yayana, maganar
makarantar na ke. Ka koma gida ka sayo
uniform, ka wuce makaranta, idan ba ha ka ba
Inna za ta ji
” Ya ce,”Don Allah ki share.”
“To me ya hana ka zuwa?”
Ya ce,”Hmm……laifi na yi.”
“Wane irin?”
“Ke dai zo mu je in raka ki, na gaya miki a
hanya.
Suka wuce ya na labarta mata.
Ta dube shi,”Kai yayana, saboda Allah me yasa
haka?”
Ban kyauta ba ko?”
Ya tambaya. Ta ce,”Gaskiya ba ka kyauta ba,
don wanna 6ata Record ne. Don Allah kar ka
sake.
Ya numfasa ya ce,”An gama.Kuma sai da ki ka
fad’a na gane ban kyauta d’in ba.
“Tayi ‘yar dariya, yana kallonta,”Yayana, kai
kullum ba ka sanin ka yi laifi, sai na fad’i?
Amma in na ce ka gyara, sai ya gagara.”
Ya dan ja ya tsaya,”Me ki ka ce in gyara, ban
gyara ba?” Ita ma ta tsaya,”Da kana gyarawa,
yaushe za’a ba ka hutun dole? Yadda yayana ke
so na, ya kamata ace komai na ce, ta zauna.
Yanzu ni ka ga babu yadda za’ayi in tsallake
maganar ka.”
Yayi murmushi, suka ci gaba da tafita, yana
tad’in,”Komai ki ka ce, ba na tsallakewa, ke ce
ba kya ganewa.” Ta dube shi kamar yadda yake
kallon ta, ta ce,”Na sakar ma yayana.” Suka yi ta
tafiya har kusa da mkrnt, sannan ya ja birki ya
ce,”To bari in bar ki anan, amma Zarah hak’uri
za tayi, yaya bai da kud’in (Break).”
Ta shagwa6e a gaban sa,”Ni a’a.
Allah ni na saba kashe kud’in yayana.”
Ya d’aga lallausan gashin girar sa, bak’i wulik!
Yana kallon ta.
‘Yar dariya yake yi mata.
Ita kuwa shagwa6ar ta take,”Allah ni ma zan
koma gida!”
Ya laluba aljihu, ya ciro Naira 20 ya mik’a mata.
Ta amshe tana fad’in,”Dama tsoka na ce?
Shi kenan ni ma ba zan rage maka abinda na ci
ba.”
Ya ce,”Har kin isa. Ki na son bulala kena.” Ta yi
murmushi ta ce,”To na gode, sai na dawo. “Ya
ce,” A dawo lafiya.” Ta juya ta shiga cikin ‘yan
mkrnt, tana tafe tana waigen sa, shi kuwa yana
tsaye, ya kama tafiyar ta k’ule masa.Ya sauke
numfashi, ya juya ya dawo gida. Sati 2 suka
cika. Naseer zai koma makaranta. Malam
Balarabe ya ce bai san zancan bin sa
makarantar ba. Ran Naseer ya 6aci, ga shi yana
son komawa makarantar, don kar Zarah ta ce
shine bai son zuwa. Sageer ya samu a karo na
farko ya rok’e shi, su je ya rarrashi Baban sa
yayi hak’uri, su tafi makarnta gobe tare. Abin ya
ba Sageer mamaki k’warai, kuma yayi farin cikin
jin hakan.
Saboda haka babu 6ata lokaci, suka same shi da
daddare. Sageer yayi ta rok’o a madadin
Naseer. Malam Balarabe ya ce,”Sageer ni na
haifi Naseer, amma ko alama Naseer bai san
mutuncina ba, bai san mahimanci na a gare shi
ba.
Tun da abin nan ya faru, ban iya cewa da shi
k’ala ba, sbd takaici da 6acin rai, amma Naseer
bai san ya durk’usa gaba na ya ce Baba ka yi
hak’uri akan abin da na aikata ba. Sai yanzu ne
zai ce in zo muje makaranta? Me zan ma sa?
Bayan ba ni da amfani a gun sa? Sageer ya kara
duk’awa ya ce,”Baba ka yi hakuri, ka yafe
masa.” Ya ce,”Naseer yaro ne?” Shekarunsa
goma sha takwas, yayi hankalin da zai san 6acin
ran iyayensa.
Babban kuskur ne a gare shi.
Amma shi komai yayi, sai ya d’auka dai-dai ne.
In banda tsageranci, menene na rufewa Malimin
ka k’ofa, don shi yana rufe ma ku? Ashe za ka
iya rufe min gida, duk ranar da na yi dare a
waje. Ka kiyayi duniya Naseer, ranar da za ta
koya ma hankali sai ka gwammace ba ka zo
cikinta ba.”
Ya k’ara sunkuyar da kai ya ce,”Ka yi hak’uri
Baba, in Allah ya yarda ba za’a sake ba.”Sageer
ya ce,”Baba, ka amince goben za ka d’in?” Ya
ce,”Ya zama dole, tunda ka sa baki Sageer, don
ka fi shi hankali, da ace yana koyi da kai, ai da
ba haka ba.
Ni dai bn ma sa mugun baki ba, iyakata da shi
add’ur Allah ya shirye shi. Amma daga yau in ya
sake d’ebo rigimarsa, ko alama ba ni a ciki. Kar
ma ku dunfaro ni. Ina fatan kun ji abinda na
ce,”Sageer ya ce,”Insha Allah.”
Ya ce,”Allah ya kai mu goben.
Allah yayi maku albarka.” Suka amsa da “Amin-
Amin.”
**************
Washe gari Malam Balarabe ya maida Naseer
makaranta. A gaban (Principal) da sauran
Malami Naseer ya d’auki alk’awarin ba zai sake
sa6awa dokar makaranta ba.
Shugaban makaranta ya ce idan ya sake korarsa
za su yi, don fitinar sa ta ishe su.
Malam Balarabe yayi ta ban hak’uri, sannan aka
sallame su. Malam Balarabe yayi gida. Naseer
yayi aji. Akwai Malami a cikin ajin, don haka a
salihin sa ya shige. Sauran d’alibai na ta
bayyanar da farin cikin su bisa fuskokin su. Bai
kula kowa ba, ya wuce mazaunin sa, ya zauna a
d’aure.
Malam na bada baya, duk suka yanyame
shi”HUKUMA! HUKUMA!!” Ya dube su ya
ce,”Yawa ku ke, kowa ya zauna, in ba ku wani
labari.” Suka zauna sauraron sa.
Ya mike ya zo gaban allo ya tsaya.
“Gata nan, gata nan ku!” Suka ce,”Ta zo mu ji
ta!” Ya ce,”Da Naseer ne da Englishi Master,
wata rana sun fita farauta, sai Naseer ya kafa
Malam, ya na da A B C D.
Englishi Master zai k’wace, dambe ya kaure.
Naseer ya kada Malam, ya na da A B C D a
gwafa, ya auna masa koda ya mike, sai ya rubta
wa Naseer SUSPENSION.”Gaba d’aya suka d’au
dariya da tafi har da masu fito, ya ce,”A
saurara!
Sati 2 Naseer ya dawo, amma da sabon
alk’awari.” Ya kame kamar soja, hannun sa ma
dama saitin kunne sa, ya ci gaba,”Na d’auki
alkawari ga makarantar kufena. Zan zama mai
ladabi da biyayya. Zan maida hankali ga
karatuna, zan tabbatar da ci gaban ta, idan ba
haka ba, kora ce!”
Ta yadda ya aje salon kalmar k’arshe KORA ce!
Shi yasa duk suka d’auki tafi,”Yayi! Yayi!! Allah
ya bar mana HUKUMA!” Ya ce,”Hukama na
ofishin principal, sbd haka kowa ya d’auki
wannan alkawarin, kar fushinta ya kama shi.” Ya
d’auki alli ya rubuta bisa allo.,”Ya ce,”Wannan
shine Nationar Anthem d’inmu.
Suna ta hayaniya. Malamin Geography na tsaye
yana kallon su, sai dai suka gan shi tsulum! Ya
karasa shigowa.Da turanci yake magana,”Meke?”
Naseer ya ce,”Ba komai.” Ya aje alli, ya wuce
wajen zaman sa.
Malam ya dubi allo ya karanta abinda Naseer ya
rubuta, ya dube su da kyau ya ce,”Wa ya
rubuta wannan?”
Baba wani 6oye-6oye Naseer ya d’aga hannu.
Ya ce,”Ya mik’e tsaye.
Tsaf!
Ya tashi fuska d’aure. “Menene wannan?” Ya
k’ara kirnewa, ya ce,”Sabon alk’awari ne, New
testament ba.” Dariya ta kubce masa, yayi d’an
murmushi, ya ce,”Naseer ba ka ji ko?” Ya dan
duk’a ya ce,”Allah ya shi taimaki Malam!”
Suka d’auki dariya. Malam ya ce,”K’wana 2 ba
na ganin ka, ina ka je?” Ya amsa”Saudiyya.”
Ya tsira masa ido, yana kad’a kai,”Hajji ko
umrah?”Ya ce,”Umrah.” An dawo lafiya? Ina
tsaraba?” Ya nuna allo ya ce,”Ga ta nan kuwa.”
Malam d’aurewa yayi ya ce,”To ka share.” Ya
k’ara duk’awa ya ce,”Allah shi taimaki malamin
binciken yanayi.”
Ya fito yana na tafawa, ya d’auki abin share allo
ya share.”Malam an share.” Ya ce,”Ka ci gaba da
tsayuwa anan.” Ya dubi d’alibai ya d’aga gira ya
ce,”Soja kenan a fakaice.” Nan ya ci gaba da
tsayuwa har darasi ya k’are , kuma hakan bai
hana shi abinda yake so ba, duk da cewa ya san
tsayuwar ma horo ce aka ba shi.
Naseer kam sai addu’a.
**************
Sannu a hankali. Malamai da iyayen Naseer
suna hak’uri da shi. Har ga shi gobe ake sa ran
za su fara rubuta jarabawar su ta karshe watau,
(WAEC). D’in su. Da yammacin wannan lahadin
ce. Naseer ya d’auki wankan sa yayi tsaf!
Cikin gogaggen yad’in sa ruwan madara yayi
kyau sosai, dan shi Naseer akwai son gayu, ga
kuma tsafta.
Zai yi wuya ka gan shi a yamutse. Kayan sa
kuwa duk inda zai nemo guga, sai ya nemo, sbd
babu yadda za’ayi ya sanya kaya ba guga. Ya
dan goge sandal d’insa bak’i, kai tsaye ya wuce
gangare gidan su Zarah. Bai nemi Sageer ba,
saboda ya san zai yi wuya ya fita yawo, saboda
karatun jarabawa.
Yana cusa kai cikin zaure, idanuwan sa suka
nuna masa wani abinda bai ta6a jin fad’uwar
gaba ba, sai akansa. Zarah ke tad’i da wani
saurayi, wanda ita ma a yau d’in nan suka
had’u da shi.
Sarai Naseer ya san saurayin a nan layin sarki
yake, sai dai ko gaisuwa bata ta 6a had’a su
ba.Nan take kishi ya lullube shi, mahaukacin
kishi kuwa, don sai da ya ji zuciyar sa ta kulle,
ta tattaro ta dawo iya wuya. Duk da cewar bai
ta6a furtawa Zarah kalmat so ba, illa iya ka
komai take so, shima shi yake so.
Tana ganin sa,tayi sauri ta rufe fuska da
hijabinta, har ya wuce cikin gida, bata bude ba,
haka kuma babu wanda ya tanka ma wani.
kujera ya ja tsakar gida, suka gaisa da Inna,
tana tsakar alayyahu. Ya jawo faranti yana
tayata.”Amma gaba d’aya hankalin sa bai jikin
sa.” Lafiya Naseer?” Ya ce,”Lafiya lau Inna, me
ki ka gani?” Ta ce,”Na ji ka yi shiru ne, ko anyi
fad’an da su Umma ne?” Ya kada kai,”Babu
komai wallahi.” To duk tunanin jarabawar ce?”
Ya ce,”Jarabawa ai mun gama da ita. Insha
Allahu babu abinda zai gagara.”
Ta ce,”Allah shi yarda Naseer, ai ba na haufi
akan dan nawa.” Ya mika mata alaiyahun da ya
tara a hannunsa, ta karfa tana yankawa.
Zarah ta yi sallama ta shigo, suna hada ido, ta
rufe fuska da hannayen ta, ta fad’a daki. Ya
ce,”Ki fito kawai, yau bulala za ki sha.” Inna ta
ce,”Yakamata, haka kawai ana zaune k’alau, za
ta fara jawo mana samari, wai shi nan auran ta
zai yi, ba yaudara ya zo yi ba.”
Shi d’in ya fad’i haka?”
Inna ta ce,
“Eh,
ai sai da Babanku ya fita, ya tsare shi a zauren.
Zuciya ta k’ara shak’e shi, da kyar ya
amsa,”Inna Zarah ai yarinya ce, kuma karatu za
ta yi.”
Ta ce,”Ni ma shi na gani, amma Malam ya ce
tunda da gaske yake, sai ta tsaida shi, tana
gama karatun, ayu da shi, idan Allah ya
nufa.’Kyar yake kallon Inna. Zarah ce ta d’auke
masa hankali da ta fito, tana fad’in,”Yaya na ina
wuni?” Ya maka mata harara. Tayi murmushi, ta
zauna kusa da shi,”Me na yi yayana?
Wannan harara ta bata min fuskar ka, dan yi
murmushi mana, haba Big Bros.” Ya dubi Inna
fuska daure, “Kin ji yadda yarinyar nan ta raina
ni ko?” Ta ce,”Kai ka kyale ta.” Ta d’auke
alayyahunta ta shige kicin. Shi
kuwa hararar Zara ya ci gaba da yi.
Ta sanyaya murya, ta ce,”Ba ka ga yadda ka yi
ba, me yasa?” Ya ce,”Karatu za ki yi, ko tara
samari?” Ta ce,”Salis ne kawai yayana, don Allah
ka yi hak’uri.” Ya ce,
“Zarah! Zarah!! Zarah!!!
Ta amsa.”
“Na’am.”
Sau nawa na kira ki?” Ta ce,”Ina jin sau 3 ne.”
Ya k’ara dubanta,” Ki na ma ji ne?”
To shi ke nan.” Ki saurare ni.”
Ya mik’e yana fad’in.”Inna na wuce!”
Ta lek’o ta ce,”To Naseer, agaida su Ummah.”
Yayi waje. Zarah na bin sa.”Yayana, me zan
saurara na ce?” Ya juyo cikin zaure, ya ce,”Ai ba
ki tabbatar da ko sau nawa na kira ki ba, it
means hankalinki ba a waje na yake ba. Saboda
haka ni zan yi wa tufka hanci, don hankalinki ya
tsaya waje 1.”
Ya sa kai ya fice ya bar ta cikin duhu. Yana ji
tana kiran sa, amma kishin daya mak’ure masa
wuya, ya hana shi amsawa.
Bayan sallar isha’i, gidan su Sageer ya nufa. Ya
yaye labulen dakin ya shiga. Kwanon abinci
Sageer d’in, ya bude zai fara ci.” Me ka ke yi?”
Ya ce,”Abinci zan ci, zo mu ci mana.” Ya ce,”Don
Allah ka rufe abincin nan, ka taso ka raka ni nan
layin sarki.” To ka za mu ci abinci mana!”
Kar in rasa wanda zan je nema ne.
Don Allah ta so mu je.” Sageer ya rufe abinci, ya
sanyo takalaman sa, ya rufe dakin sa, suka
wuce layin sarki, ba tare da ya san me za su je
yi ba.Kawai Naseer ya ce,”Wani zan je gani.”
Suna zauna da abokan sa 2, labarin yarinya
Zarah yake ba su, lokacin da Naseer suka iso
tare da sallamar har da Musabaha, kamar abin
arziki. Naseer ya dube shi ya ce,”Ah! Kai ne
Salees ko?”
Ya ce,”Eh ni ne, lafiya?” Ya ce,”Ita ta kawo
hakan. Na san ba sanni ba, amma watak’ila da,
da rana na zo, da ka gane ni. Well kar mu je da
nisa, kawai gargadin ka na zo yi akan yarinyar
nan Zarah. Ban som in k’ara ganin ‘yar k’afan
ka a gidan su. In kunne ya ji……..”
Ya juya zai wuce. Salis ya dafo k’afarsa ya
ce,”Dakata mana. Kalle ni, idan ka na takama
kai dan Tudun wada ne, ni ma kazalika haifaffen
Tudun Wada ne, saboda haka karan daji bai isa
ya budewa karan gida ido ba.”
Naseer yayi dan murmushi ya ce,”Allah ko?” To
lulaba da kyau ka ji, wannan ba kare ba ne,
kura ce, don uban kare karyar sa.”
Sageer ya rik’o shi yana fad’in.” Naseer! Dama
rakiyar da ka ce in zo yi kenan, Meye haka?”
Abokan Salis ma suka taso.” Me ye haka ku ke
yi? Don Allah ku bari, yawa ne. Zaarah sai
wanda ta za6a, sbd ha………..”
Wani wawan mari Naseer ya tsinkawa, mai
maganar. Shi yasa yayi gum da bak’in sa. Salis
na ganin haka, shi ma ya ware. Sageer ya kamo
Naseer ya ce,”Naseer, kada ka kuskara ka dauko
wannan fitinar! Ka ga k’ofar gidansu ka zo, duk
inda aka je, kai ne mai laifi!
Ya ce,”Da shi na ke magana, daya sanya min
baki?” Yana rufe da baki, ya ji saukan naushi.
Cikin zafin nama Naseer yayi kukan kura, ji ka
ke yi dim! Ya sakarwa Salis naushi a mukamuki.
Nan take kamar almara. Salis ya fad’i a sume.
Abokan Salis suka rude. Sageer ma ya firgice, ya
rinka jan Naseer, yana fad’in,”Ka gani ko?” Ka
ga irin ta ko?”
Su kuwa abokan Salis cikin gida suka shige,
neman taimakon jama’a.”Ka zo mu tafi Naseer!”
Yana jan sa, yana tirjewa,,”Babu inda za ni!” Ka
kyale ni. Duk abinda suka ga dama su yi!”
Ya ce,”Haba Naseer! Me yasa kai zuciyarka bata
kulla maka alkhairi ne? Dubi fa abinda ka aikta?
Ka na zaton iyayensa za su kyale ka ne? Wallahi
da na san abinda za ka zo ka yi aikata kenan.
Sam da ban biyo ka ba, ba za ka ja min masifa
ba wallahi! Ya dube shi da kyau, ya ce,”Sageer!
Bi tannan, in bi ta can, idan ka kuskura muka
had’u, sai na fasa maka baki!
Yana sa aya ya wuce, ya bi ta inda ya nuna,
suna jin abokan Salis na fad’in Ga shi can zai
gudu!
Sageer ya shafa a guje, ya tsere. Shi kuwa
Naseer ja ya yi, ya tsaya har gayyar jama’ar
suka zo gunsa.Me yayi maka, za ka kashe shi?”
Ya ce,”Ku zuba masa ruwa, ya farfad’o, sai yaga
maku.”
Samari suka yi caa! Za su rufe shi da duka,
mahaifin Salis ya hana, don tuni ya tura daya
daga cikin abokan Salis din ofishin ‘Yan sanda.
Ana ta kwaranniya, ga Salis a kwance shame-
shame. “Yan sanda 2 suka iso, nan take suka
wuce da Naseer da laifin yunk’urin kisan Kai,
kamar yadda aka shaida ma su. Salis dai sai da
ya hau gadon asibiti a daren nan, sannan ya
farfado.
Wuyan sa a kage, bai iya juyawa ta gefen da
Naseer ya naushe shi.
Kai tsaye gidan su Naseer, Sageer ya nufa. Yana
ta hak’i, kamar ran sa zai fita.
Malam Balarabe da Mairo, suka firgice.
“Menene Sageer?” Ya ce,”Ba lafiya Baba, ina
zaune Naseer ya ce in zo in raka shi layin sarki.
Ashe fad’a za shi yi. Wallahi Baba ban sani ba, a
takaice dai ya naushe masu yaro ya fad’i, suma
yayi mutuwa yayi? Allah kad’ai ya sani, ya zo
ma mu gudu, ya ki. Can na baro shi, ban san
halin da ake ciki ba!”
Mairo salati da d’auka, shi kuwa Malam
Balarabe cewa yayi,”To ba shi kenan ba, ka
koma gida abinka, ka yi kwanciyar ka.
Tsuntsun daya ja ruwa, shi ruwa zai yi wa
banzan duka.
Idan sun so ma, kar su bar shi da rai, babu
abinda zai dame ni.”
“Baba….” Ya katse shi,”Babu ruwanka na ce! Ka
wuce gida abin ka, idan kuma kai ma can d’in
za ka sake komawa, to Bismillah!
Amma ni Balarabe ba ni a cikin wannan
maganar.” Tuni Umma ke tsiyayar
hawaye,”Sageer mu je, ina ne, suke fad’an?” Ya
ce,” A layin sarki ne.” Malam ya ce,”K’ofar zaure
ban ba ki izinin takawa ba.
Yauwa.” Ya sa kai, ya koma d’aki. Umma ta
koma bisa tabarma, ta tallabe kai ta
ce,”Wannan yaro, wannan yaro. Allah ka shirye
shi.Sageer ya tsuganna ya ce,”Umma ki yi
hak’uri, ki daina zubda masa hawaye.” Ta dube
shi cike da damuwa ta ce,”Bari fad’i Sageer, ya
zama dole in yi hawaye, don bansan masifar da
Naseer ya jaji6o mana ba wannan karon. Me ya
had’a su da yaro?” Ya ce,”Ni ban san
takamaiman zancen ba, amma na ji wai yana
masa gargad’i akan Zarah.”
Ta ce,”Zarah? To shi me ya dame shi da
saurayin Zarah? Auranta zai yi?”
Ya amsa,”Bai ta6a yi min magana a kanta ba,
sai dai bn san abinda ke cikin ran sa ba a game
da ita.” Ta sauke numfashi ta ce,”Dubi wannan
abin kunya, akan budurwa, ya je yana haukan
banza, idan ya kashe d’an mutane, ya yake son
mu yi da ran mu? Yanzu kai Sageer ka yi
hak’uri, ka koma ka bincika mana halin da ake
ciki ka ji?”
Ya ce,”Ya zama dole Umma, bari in tafi. Allah
shi kyauta.”
Ta ce,”Aamin.”
Ya mike ya fice.
Nan ta ci gaba da zama a kunci, tana mai
tsananin al’ajabin halayen Naseer, kamar ba su
suka haife shi ba, don ko 1 bauko halayyar su
ba. Ta nisa face,”Kuda, ya haifi zuma.
Allah ka shirya mana!
Tsaye Sageer yake a cikin jama’ar da suka taru,
suna ta maida labarin fad’an da aka yi karya da
gaskiya.
A nan yake jin Naseer na hannun “Yan sanda a
anan caji ofis da ke kusa da su.
Jikinsa na rawa, ya bazama ofishin. Cike yake
daga waje, daga ciki kuwa abokan Salis suke ta
bada bayanan yadda abin da ya faru
(Statement).
Shi kuwa Naseer yana tu6e, a bayan kanta. Yana
isowa, mai magana lkcn ya ce,”Yauwa ga shi
nan, tare suka zo, amma shi raba su yake yi,
yana ta jan sa, ya k’i tafiya.Sai da ya sumar da
shi.” Dan sanda ya ce, wa Sageer shi ma ya
fad’in abinda ya sani.
Tiryan-tiryan ya maida wancan, dan sanda ya
ce, ya dubi mahaifin Salis ya ce,”Duk mun ji
bayanin kowa, kuma hakan ya tabbatar mana
Naseer na da laifi dumu-dumu, saboda haka za
mu tsare shi a
a nan a bisa laifin tada husuma, har zuwa lkcn
da Salis zai sami sauki.
Sajent!”ya amsa,”Sir!” A wuce da Naseer cikin
Cell.”Sageer ya d’ora hannu a ka yana
fad’in,”Inna-lillahi-“Wa-Inna-ilaihir raji’un!”
Insfesta ka yi hkr, ka ba ni shi beli. Gobe za mu
fara (Exams), ka ga za ta wuce shi.”
Dan sanda ya gyara fuska, ya ce,”Ya san da
jarabawar, ya je neman fad’a? Bata dame shi
bane, da ta dame shi, karatu yakamata ya
zauna yayi, ba fad’a akan budurwa ba. Saboda
haka babu, har sai Salis ya bar asibiti. Kuma
gaba d’aya abinda aka kashe a asibitin, za’a
kawo (Bill) nan, shine zai biya. Na gama da ku.”
Sageer ya na ji, yana gani, aka wuce da Naseer
ko gezau bai nuna a fuskar sa ba.
Har goma da rabi na dare. Sageer na aikin
rok’on a ba shi Naseer akan beli, amma dan
sandan nan ya k’i, anan iyayen Salis suka bar
shi, kuma da gani akwai wata ‘yar muna-muna
tsakanin insfesta da iyayen Salis.Sha d’ayan
dare, ya bar wajen ya koma gidan su Naseer,
har sun kulle k’ofar gida, ya buga. Malam
Balarabe ya bud’e, ya shigo ya kwashe kaf!
Halin da ake ciki ya fad’i. Malam ya balbale shi
da fad’a,”Me yasa ka ke wahalar da kanka akan
wanda bai san ciwon kan sa ba? Shin ba cewa
nayi ka tafi gida abinka ba? Yanzu k’arfe nawa
ne?” 11 ta wuce, kai ma so ka ke ka 6ata wa
naka iyayen rai ko?
Ya karkad’a kai.”To maza ka wuce gida, da safe
kuma ka shirya ka tafi jarabawar ka, kar ka
saurare shi!
Maza sai da safe.”
Ya juya ya tafi, ran sa in yayi dubu toh ya 6aci.
Abu 1 yake wa Naseer bak’in ciki, gobe ba zai
samu zana jarabawa ba.
Washe gari karfe 7:30 Zarah ke k’arasowa bakin
titi, sai dai yau babu yayanta a wajen, kamar
yadda kullum safiya shine mutum na 3 da ke
faranta mata rai, daga iyayenta, sai shi.
Don haka ta tsaya shiru cike da mamakin me ya
hana yayanta zuwa yau? Ta kusan minti 5r a
tsaye, sannan ta wuce jikinta duk ya mutu.
Kuma ko alama zuciyarta bata cikin sukuni har
na rashin ganin Salis jiya da daddare, kamar
yadda yayi mata alk’awari.
Ta fe take tana zancan zucci fad’i take,”Ina ka
ke yayana?” Zarah.” Ta ji an k’wala mata kira.
Ta waiga gefen da aka kirata, firgici. Bak’in get
din ofishin “Yan sanda ta hango Sageer tsaye da
kayan makaranta.
Da sauri ta tsallako. Hankali tashe, ta
tambaya,”Ina yayana ne?” Ban gan shi ba yau.”
Cike da damuwa ya amsa,”Ai yayan nan naki,
sai a hankali.
Yana nan ciki.”
Ta k’ara ware ido ta-ce,”Ban gane yana nan
ba?”
(Police Station)Na ga ka nuna!
Ya ce,”Eh mana..” Hankalinta ya k’ara tashi,”Wa
ya kawomin shi?” Bata jira ya bata amsa ba, ta
wuce, ya biyo ta, yana fad’in,”Wallahi tsautsayi
kawai, jiya ya je wajen wani wai shi Salis, suka
fara gardama akan ki, sai fad’a. Kin san halin
yayan naki, k’ashi daya ke gare shi, yana dukan
sa, ya fad’i a sume.”
Tun da yake magana, ta rage sauri. Yana sa
aya, ta juyo ido cike da kwalla ta ce,”Shi da Salis
suka yi dambe? To saboda me?”
“Oho!
Amma a kan ki ne Zarah. Naseer bai son Salis
na zuwa gun ki, gargad’in da na ji yana masa
kenan.
Abin ya kai su ga dambe.”
Ta tsura masa idanuwanta da suka cika tam!
Da hawaye, ta ce,” Za’a bar ni in gan shi?”
Ya amsa,”Ban sani ba. Ni ma yanzu na kawo
masa abinci, mu je mu gani.
Suka shige cike, da k’yar aka sake yarda su gan
shi,don bai jima da komawa ba. Ana fito da shi,
suka yi ido 4 da Zarah, sai ya juya, ya koma ciki
da saurinsa. Kamar za ta burma ciki, ta bi shi,
kira take,”Yayana! Yayana ka zo mana, in gan
ka!” Dan sanda ya ce,”Yan mata, ihunki fa yayi
yawa wajen nan. Hala saboda ke aka yi fad’an?”
Bata iya cewa da shi komai ba. Sageer ke jawo
ta waje. Zarah, ki yi hak’uri ki tafi makaranta, ni
ma yanzu zan wuce.”Insha Allahu na san zuwa
anjima, za’a bada belinsa.
Yi hak’uri.”
Tayi tsaye tana share k’walla.” Zo mu je.” Suka
fito bakin titi. Sageer ya tare mai mashin, ya
yana fad’in,”Ki wuce Zarah, kin ga lokaci yana
kurewa.” Ta ce,”Zan ta fi.” Mai mashin ya ja,
suka tafi. Yana waigen ta, yana nuna mata
alama da hannu ta wuce, har suka yi nisa.
Tsaye kawai take kikam! Ta rasa na yi.
Tunanin ta, me ya kai Naseer fad’a da Salis?Nan
take ta samo amsar. Wani ni’imamman farin ciki
ya lallube ta.
In banda abin yayana, ai sai ya gaya min kai
tsaye, menene na fad’a da Salis? K’walla suka
cika idanuwanta, tana kallon ofinshin “Yan
sanda,”Ba zan iya zama cikin aji ba, kai kuma ka
na tsare a nan yayana. Ta goge kwalla ta
kwashe sauri sauri sai gida.
Babu ko sallama, ta fito dakin. “Ke! Lafiya?”
Innar ta, ta tambaya, kuka ta fasa,”Inna ‘Yan
sanda sun kama yayana! Ta dafe kirji a firgice ta
ce,”Me yayi?” Bakinta na rawa, ta mayar da
abinda ya faru. Inna ta d’auki salati, kan ta ya
d’aure”To ki yi shiru, bari Baban ki ya fito
wanka. Kai yara babu hankali, koma dai menene
cikin zuciyarsa, ai sai yayi hakuri, menene abin
fad’a?.”
Shigowar Malam Umar yasa tayi shiru,.”Me ya
faru? Inna ta amsa,”Naseer ke hannu ‘Yan
sanda. Wai jiya sun yi fad’a da yaron nan daya
zo gun Zarah jiya, har sumar da shi.” Ya ce,”To
saboda me?”
“Oho!”
Yayi dan tsaki ya ce,”Yara ba sa jin magana,
menene abin fada anan? Ko shi ma sonki yake
yi?”
Ta sunkuyar da kai ta ce,”Nima ban sani ba.”ya
ja tsaki. Inna ta ce,”Idan ma sonta yake, me zai
kai shi, fada in banda abin Naseer. Shi ma ya
san babu yadda za’ayi mu hana shi, mu ba Salis
in har ya furta.
Allah shi kyauta.
Yanzu yaya za’ayi Malam?” Ya ce,”Bari in shirya,
in je in ga Baban na sa, sai a san abin yi.
Ke kuma ga shi kin makara.
Ki bata sauran 20 din nan, maza ta je ta hau
mashin ya kai ta.
Ya fice daga dakin. Inna ta dauko 20 din ta
bata,”Tana bayan mashin hankalin ta na ofishin
‘Yan sanda.
Haka suka wuce tana kallon wajen har suka
k’ule.
Malam Umar ke wa su Malam Balarabe sallama
a k’ofar gida. Tare da Mallam Lawal mahaifin
Sageer.
Bayan sun yi Musabaha, sun gaisa sai ya
ce,”Magana na ji babu dadi, shine bari in zo in ji
yadda aka yi?”
Malam Lawal ya ce,”Zaman nan da ka ganmu
nan, rarrashi kawai na ke yi.
Malam Balarabe ya ce babu ruwan sa a ciki.
Sannan baban tashin hankali, na je ofishin, don
in yi belin sa.” Yan sandan, suke gaya min
iyayen wancan yaron, sun ce kara za su kai
kotu, wai da wuk’a ya zo, yana neman kashe
shi.”
Da wuk’a?
Ya ce,”Sharri ne kawai, don Sageer ya gaya min
tare suka je, kuma babu komai a hannu Naseer.
Dukan sa kawai yayi, ya suma. Shi kuwa Naseer
tun yana yaro haka Allah yayi shi da karfin
tsiya.
Malam Umar ya kada kai cike da damuwa,
“Wannan al’amarin bai yi dadi ba. Su kuma bai
kamata su yi haka ba. Menene amfanin yin
sharrin?” Malam Balarabe ya amshe,”Laifin su
ku ka gani? Karan banin da ya kai shi,ya ta6a
masu yaro. Shi zai fidda shi. Saboda haka kar ku
wahalar da kan ku, ku kyale shi, su koya masa
hankali.”
Malam Umar ya ce,”Ba kuwa za’a kyale shi ba.”
To wallahi babu hannuna acikin, kun ji kuma na
rantse..” Ya ce,”Shi kenan Malam Balabare,
amma ina tabbatar maka, bai kamata ka yi
saurin rantsuwa ba. Tunda abin ya zama haka,
mu sai mu je ko?
Ya fad’i yana kallon Malam Lawal, duk dacewar
ba su taba sanin juna ba, sai yau.
Ya ce,”Taso kawai mu tafi.” Rai 6ace suka bar
wajen, tamkar yadda ran Malam Balarabe ke
bace.
Ya jima a zaune, yana tunani da tambayar kan
san “Yaushe Naseer zai daina bata min rai?”Ya
ce,”Taso kawai mu tafi.” Rai bace suka bar
wajen tamkar yadda ran Malam Balarabe ke
bace. Ya jima a zaune, yana tunani da tambayar
kan san.”Yaushe Naseer zai daina bata min rai?”
Ya kada kai ya ce,”Allah ka shirya min.” Ya
mike, ya shiga gida, ya mayar wa Umma zancan
kai Naseer kotu inji iyayen Salis.
Idanuwanta suka kada, cike da tashin hankali ta
ce,”Wannan sharri ne, na san Naseer bai jin
magana, amma bai ta6a daukan makami ya hari
wani da shi ba.
Gaskiya Malam bai kamata ka tsame hannunka
daga maganar ba.”
A fusace ya ce,”To ai sai ki dauka ki maida min.
Ya ja tsaki, ya bar gidan, ya wuce kasuwa. Ya
bar Mairon, kamar ta aza hannu bisa kai tayi
kuka.
Duk iya kokarin da su Malam Umar suka yi, don
ganin su kwantar wa iyayen Salis hankali, don
su janye kudirin su, sam sun ki sauraron su, shi
mahaifin sa ma ya ki yarda su gan shi ido da
ido.
Abokan Salis din ke gaya masu, an ma riga an
shigar da kara.
Takarda kawai suke jira a aiko ofishin ‘Yan
sanda………..

See also  Gyaran Nono a sati daya ga budurwa

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top