A Likitance Meye Hukuncin Mai Tsotsan Farji Yayin Saduwa?

A LIKITANCE MEYE HUKUNCIN MAI TSOTSAN FARJI YAYIN SADUWA?

Sannan shafa maniyyin da mata kanyi a fuskar su shin da gaske ne yana maganin kuraje da sa kyawun fuska?

Bismillahir rahamanir rahimeen Ko kusa bamu nufaci wasa da wannan post din ba hasali ma wannan abune da yake faruwa ko yaushe yanzu. Don haka ku biyoni.

Tsotsan farji wannan dabi’a ce da mafi yawan ma’aurata dama wanda ba ma’auratan ba keyi, suna jin sunfi samun gamsuwa in suka hada da hakan ayayin ibadar aure koma ga maneman mata, Saide mu a likitance ba komi muke gudu da irin hakan ba illah gudun kar mutum yaje yasa ma matar kwayoyin bacteria da akan samu tattare cikin bakin mu ta sanadiyyar ragowar abincin da mukanci ya mammakale muna a hakora inda suke biyo miyau su taho ko kuma shi din yasha datti yazo yana fama da ciwon ciki domin wasu matan suna da karancin tsafta.

Idan har ya kasance mijin ba mai kula da tsaftar hakora bane ko yaushe to lallai zai iya sa mata wadannan kwayoyin infections din na bacteria daga cikin bakin sa, Kuma kar jin haka yasa mutum yace yanxu toh duk sanda zasui mu’amullar aure sannan zaike brush domin samun damar yin abunda suka saba, A’a ko abinci a ka’ida bawai daga kammala brush ya kamata aci ba, A’a an so sai kamar bayan minti 45 da yin brush sannan zakaci komi ko yin abunda aka saba saboda haka ga masu wannan lallai suke tabbatar da tsaftar bakunan su koda yaushe Sannan su kiyaye hakan.

See also  Wata Amarya Hausa Novel Complete

Sannan Kuma ga kaima namijin idan mace bamai tsaftace gabanta yarda ya kamata bane kaima zaka iya dibar kwayoyin cutukan musamman yadda wasu kan hadiye miyau din yayin wannan artabu, zasu iya fuskantar ciwon ciki da sauran yan matsaloli amma de tabbatar da cikakkiyar tsaftace itace maganin komi ake shaving akan lokaci. Ga masu ganin kuraje bayan sunyi shaving to abunda zasukeyi kafin sui shaving din da kamar minti 10—zuwa—5 su sami ruwan dumi suke zama aciki wajan ya jika su Kuma ke canza rezor duk sanda zasui akuma daina sa karfi ana kartar fatar gun, in ana haka baza a samu kuraje bayan shaving.

MUSANI

Tsotsan farji still a tsari na cikakkiyar tsafta wannan baya ciki saboda indai mutum Nada cikakken ilimin yarda mu’amular auren ya kamata ta kasance to basai ma ankai ga irin wannan ba saide dake kowa da yanayin yarda Allah ya haliccesa da tsarin sa, Amma azzakarin namiji yafi zamowa abun tsotsa mara matsala 90% fiye da farji, Saboda nan depot ce.

GA BATUN SHAFA MANIYYI A FUSKA

Har yau de ba binkicen masanan da ya tabbatar da hakan na maganin kuraje toh amma inma yayin ba abun mamaki bane duba da irin sinadaren da ya kunsa, Kuma anji da yawa matan da sukai hakan na nuna gamsuwar su 99% kan hakan cewar akwai biyan bukata.

SHAWARA DAGA LIKITA

1) A tabbatar da tsaftar al’aura akoda yaushe basai in ana shirin saduwa ba.

2) maza ake canza boxer akalla sau 4 a sati, mata ake canza pant akalla sau 10 ko 14 asati. Sau biyu kullum.

See also  Tubali Hausa Novel Download

3) a matsayinki na mace ki guji matsi tare da cushecushen abubuwa a farji, domin bafa bola bace.

4) Aski duka mazan da matan akalla duk kwana 30 zuwa 40.

Allah yasa mudace.

Ibrahim Y. Yusuf

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top