A SANADIN A BAYAR SALLAH
Gajeren Labari
Na
*Rabi’atu.B.Abdullahi*
(Ummu Maher)Miss green
*Alk’alami yafi takobi
︎ARUMAI ︎ WRITERS ︎SSOCIATION
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa*_
*Shafi na 16&17*
*Gidan Malam Tahir*
Ba ga Habiba ba hatta Salma sai da lamarin mahaifin na ta ya gir_giza ta matuk’a,wani tsohon son Bashir ya d’arsu a zuciyarta ka fun kace me har ta ji kamar ta ma k’ure Habiba ta kashe ta kowa ma ya huta don ba za ta jure cin mutunci ba, don ta ce ba ta son Bashir shi ne za’ah d’auki wannan mummunan matakin a kan ta?to wallahi ba za ta sab’u ba bin diga a ruwa.
oh ka ji fa mai sauraro Salma fa da kanta ta ce ba ta son Bashir yanzu kuma ganin an baiwa k’anwarta Bashir d’in shi ne ta ke ba k’inci.
Malam Ya ce”to ku ta shi ku fita na gama magana ta don haka ku fita zan sha iska, ke kuma Salma ki tsaya za muyi magana.”
Har lokacin ban i’ya ce wa komai ba kuma ban d’ago kaina ba, saboda tsananin da muwar da na ke ciki, har ga Allah har yanzu i’nason Bashir don ba don son da na ke mishi ba da bazan yi kishinsa ba.
“Salma i’nason ki yi wa wannan yaron magana ya turo a yi zancen Aurenku Saboda ba na son abun ya yi ni sa don tare na ke son had’a ku keda y’ar uwarki.”
Sai alokacin ne na yi saurin d’ago idanu na na kalli Malam, shi kuwa bai ma san i’na yi ba saboda shi sha’aninsa kawai ya ke a lokacin ya d’auko qur’ani yana du bawa kuma da alama karatun zai fara, don haka dole in ta shi in ba shi waje.
Da k’er naja k’afa funa da suka fara yi mun tsami tsaba gen zama a kan k’afa ta,don ji na ke yi kamar k’afa funa ba za su i’ya d’au ka ta ba, ga damuwar da ta cika cikin zuciyata, na fi kowa sanin halin Sooraj da mugayen halayensa amman a haka na keson Auransa don kud’insa, wa su hawaye ne masu sanyi da zafi suka sauka a kan fuskata na go ge na shiga d’akin mu na yi rub da ciki i’na kuka.
sai a sannan ne na kula da Habiba da take Zaune tana kuka, don har cikin zuciyar Habiba bata ji da d’in abinda ya faru ba, ba bu yadda za’ayi ta ce ba ta son Bashir don duk wata nagarta da A ke so Namiji ya kasance da i’ta to fa Bashir yana dasu kuma yana da rufin asiri dai_dai ba kin k’ok’a ri, Amman sai dai tana da wanda ta ke so wato Sa’ad k’anin Bashir Amman ba bu yadda za tayi ta karb’i k’addarar ta ba bu wanda ta ke ji Sai Sa’ad sai dai tana yi mai fatan samun mace ta gari da fatan hak’uri da dan gana tare da juriya.
Wani haushin yarinyar ne ya d’arsu a zuciyata don haka na tashi na yi tsaki tare da ce wa”Hmm muna fuka kina so kina kaiwa kasuwa wai kema kin girma kina son Aure to bismillah, Auren talaka har wani Aure ne ballan tana a ce wani abu, don haka ba gilin gilin ba ta yi mai, Salma ta wuce fuu tare da jin haushin kanta da haushin k’anwarta Habiba.
Habiba ta kalli ya yar ta ta tare da mamakin yadsa a ka yi ta canza halayenta, don ta san a da ba haka ya yar ta ta take ba ko da ya ke ance a bokin b’arawo b’arawo ne saboda kaf duniya yanzu Ba bu mutumin da Salma ta fi jin maganar i’rin Zulaiha wato Zuly, Kuma kaf unguwarsu ba bu wanda bai san Halin Zuly ba na Yawan tara samari ga saka ma tsatstsun kaya tare da shegen son kud’i.
*Gidan Hamisu*
Mahaifiyar Hamisu ce ta gyara zamanta ta re da Ce wa “Wallahi tallahi Hamisu ba ka da kirki ko ka d’an yanzu da man Rabi’atu ka keso shi ne ka k’i fad’amun saboda ta ce maka anyi mata miji.”
“Bazan ce maka ba’ayi mata miji ba tabbas anyi mata miji sai dai ba kowa ne mijin ba wanda ya wuce kai, saboda ni na yi maka ka mu sannan na nu na kada a fad’a maka hat sai yarinya ta amin ta tana son ka sannan komai ya tabbata.”
“Kuma a da cen ba ya suna soyayya da wani yaro sai dai Mahaifiyarsa ta hana Auren wai ta fi son ya Auri y’ar k’anwarta to kaji yadda a ka yi.”
“To Alhamdu lillahi tunda yanzu kai da kanka ka furta kana son ta don zan cen da na ke yi maka har an saka ranar Aurenku kai da Rabi’atu nan da wata uku masu zuwa.”
Murna tare da wani ni shad’i tare da jin son Rabi’atu ya yi matuk’ar sha k’uwa a cikin zuciyarsa, ya ce”kai Inna ta kin gama yi mun komai wallahi tunda ki ka ba ni Rabi’atu Allah ya k’ara arzik’i.”
*********
To kwana biyu da yin haka Hamisu ya fara zuwa zance suna soyewarsu da Rabi’atu don yanzu ga ba ki d’aya ya fita hanyar Zeenatu i’ya karsa ya ajje mata kud’in ce fanen ta kan windo ya yi tafiyarsa don gudun fitanar Zeenatu.
*Ummu Maher miss green*
*Vote*
*Share*
And
*Comments*
[…] Karanta a sanadin abayar Sallah […]