Hausa Novels

A Sanadin Furucina Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*A SANADIN FURUCINA!*

_(YA SANI ZUBAR HAZUBAR

 

*(True life story)*

 

 

Written and story

By

SUMAYYA MUHAMMAD MRD

 

 

 

ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION

{R.S.W.A}

 

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Faɗakarwa, ilimantarwa da kuma nishaɗantarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alƙalaminmu ƴancinmu*

 

 

 

*GODIYA*

 

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah mahaliccin kowa da komai, Allah ya kara dada tsira da annabinmu annabin rahama Muhammad saw ina kara godiyawa Allah daya bani ikon dawowa a cikin wnn littafin mai dinbin darasi, Ya ubangiji kabani ikon rubuta abu mai kyau Wanda zai amfanar da al,ummah ka kare hannuna da alkalamina ga rubuta shashan abunda bashi da kyau ameeen

 

 

*GAREKU MATA*

Wannan littafin kalubale ne garemu mata, domin kuwa ina son jan hankali gareku akan wannan takaitaccen labari da ya faru a zahiri, harshe ne ya ja mata musiba, harshen nan da kuke gani babbar musiba ne, domin kuwa yana iya kai mutum ga halaka, idan kayi furucin wani Abu kai ba zaka taba tunanin zai kaika ga halaka ba, amma kuma zai ja maka wata irin musibar da ba zaka iya kare kanka daga gareta ba. Wannan dai littafin yana dauke da darussa masu d’inbin yawa. Ku dai ku kasance a cikin wannan littafin domin jin yadda zai kaya.

 

 

 

 

Da sunan Allah mai rahama mai jink’ai………

 

Episode 1&2

 

 

 

*A GIDAN YARI*

 

*A B’ANGAREN MATA*

 

Ko wacce mace ta na sanye da uniform din gidan yari, tare da lamba a bayan rigar, ya yin da ko wacce mace ta na aikin gabanta, wata ce matashiyar mace zata kai shekara ashirin da shidda 26, hannunta rike da kwasar da ake noma da ita, ta na tsaye cikin wani wuri wanda duk ciyayune a cikin babban wurin, wasu da suke a wurin sai faman aikin cire shi su ke yi, ya yin da ita kam take tsaye sai kwalla ce ke sintiri a fuskarta wata na biyo wata.

 

Shugaba Zahrah ce wacce take rike da wata irin zabgegiyar dorina wadda tasha man shanu, da ita ce take dukan duk wadda taki yin aikin, ita kuma sanye take da uniform din kaki, fuskarta babu digon fara’a. Cirr idonta ya fada kan wannan baiwar Allah da taketa faman zubar da hawaye, cikin rashin imani na Shugaba Zahrah ta ce cikin daga murya wadda take tare da masifa.

 

”AMINA!! Wanne irin iskanci ne, ke ba za ki duka kiyi aikin ba ko sai nazo na zabga maki bulala sannan”. Cikin wani irin firgici da ya yi kama da tsoro Amina ta yi saurin dukawa ta fara aikin amma kuma ta rasa yadda za ta yi da kwasar har ta iya cire ciyawar. Sai dakata take yi inda ma ba nan zata yi aikin ba.

 

Wasu mata su biyu daga can gefe suka bushe da dariya tare da kallon juna, da alama kansu hade yake, kuma suma manyan tantirai ne a gurin, ya yin da wasu kuma suka girgiza kai alamar tausayawa Amina dan duka2 yau kwanan ta uku anan, bata iya aikin nan ba, wasu kuwa ko kallonta ma basu yi ba dan basu da lokacinta..

 

Shugaba Zahra cikin harzuka da jin haushin Amina bata san lokacin da tayo kan Amina tare da daga dorina sama ta zabgawa Amina a baya, Amina cikin gigita da tashin hankali wurin ta gudu tayi rashin sa’a ta yi tullubu tsaye ta fadi kasa tare da taushe dayan hannunta. Wani irin uban ihu ta rafka sai da kowa ta tsaya da aikinta tana kallonta. Ita kuma Shugaba Zahra ko tausayi babu ta fara zuba mata bulalar nan mai mugun ciwo a baya, tare da fadin ”dan uwarki ki tashi ki ci gaba da aikin nan tunda ba ke ki ka fi kowa ba anan”. Amina kam ta kasa tashi dan duk ta rikice sai ihun ceto take, wadan nan tantiran guda biyu, su ka yi saurin isowa wurin dayar ta na fadin ”amma dai kam anyi muguwa irinki Aunty Zahra ji yadda kike dukan wannan matar kamar kin samu jaka” ta karashe maganar ta na rikewa Shugaba Zahra hannu, ita kuma dayan ta ja Shugaba baya.

 

 

Shugaba sai huci ta ke yi tamkar zakin dawa da ya yi farauta bai samu ba, Karima boss ce ta tada Amina tare da ce mata ki yi haƙuri, tare da goge mata kasa a jiki.

 

Shahuda ce ta ce ”gaskiya Aunty Zahra ke muguwa ce ace ki rinka dukan mace kamar kin samu jaka, kowa fa nan da kika ganshi bawai bai da gata ba kawai dai kaddara ce da jarabawa yasa muka shigo wannan gidan kaso, wallahi ke muna raga miki ne dan kina da uniform din hukuma da tuni mun taru munyi maki dukan tsiya sai kin gaza tashi dan ubanki……” Cikin wani irin jin haushin Shahuda Shugaba Zahra ta yi wani irin kukan kura dan damko Shahuda, KARIMA BOSS ce ta yi saurin cin gaban Shugaba tare da cewa ”kull! Karki sake ki taba min aminiyata dan wallahi idan kika fara sai yanzun nan mu likida maki na jaki wallahi duk abinda zai faru sai dai ya faru.

 

 

Matan wurin sai ihun jin dadi su ke yi dan kowa tana mugun jin haushin Shugaba Zahra, ita kuma Amina ba abinda take sai kuka tare da rike hannunta wanda ta fada akansa dan kuwa ciwo yake mata sosai da alama ta yi targade a hannun..

 

 

Shugaba Zahra in ranta yafi dubu ya bace cikin masifa ta nuna Karima boss da hannu tare da ce wa “ke baki isa ba ki dakeni, ke nan yau ma rashin mutuncin ne naki ya tashi to wallahi kwalelenki nafi karfinki…” Kafin ta ida maganar ne Karima boss ta ce ”karya ki ke ni fa kai tsaye zan iya rabaki da ranki!!! Ni babbar annoba ce ke ma kin sani” hehehehehe ta bushe da wata irin muguwar dariya.

 

Shugaba Zahra jikinta ne ya yi sanyi dan ta san wallahi Karima boss bata da imani sam, kuma koda dambe aka hadata da ita ta san ba zata iya da ita ba, dan ko kwarin jiki ta fita… Maganar Karima ce ta dawo da ita a gutun tunanin da ta tafi.

 

 

Zahra!!! Kin ji tsoron kalamaina ko nasan yanzu zuciyarki ta na maki tunani kala2? Karima boss ta dan yi kasa da muryarta yadda ba mai jin maganar daga Shahuda sai Zahra. Ta daga wa Zahra gira kafin ta ci gaba da ce wa.

 

”Ki nutsu ni ba zan kashe ki ba domin na tuba da kisan kai, amma fa kashedin daya zan maki wannan maganar duk kika bari Oga Sa’id yaji wallahi! wallahi!! wallahi!!! kinji nayi mk rantsuwa uku sai na rabaki da ranki guda daya takkk!!!!”.

 

 

Wata irin zabura Zahra ta yi kafin ta nutsu dan kar sauran su gane ta saita nutsuwarta sannan ta ce ita ma cikin kasa da murya ”insha Allah ba wanda zai ji ki gafarceni Boss”.

 

 

Karima boss ta dan cije leben kasan alamar ta yi nasara kafin ta ce ”oya ki kama kanki, mun tafi mu yi aikin gabanmu”.

 

 

Karima boss ta ja hannun aminiyarta Shahuda ta ce muje mu ci gaba da aikin nan kar lokaci ya yi bamu gama ba, ta fada suna juyawa tare da tafiya.

 

Da saurin gaske ko wacce jiki na bari ta duka dan ci gaba da aikin su, dan suna mugun jin tsoron Kareema, dan ita babbar tantiriya ce kowa ya shigo ya sameta a ciki dan ita har ta tsofa shekara da shekaru ta na nan gidan kaso, kasancewar daurin rai da rai aka yi mata.

 

Shahuda ita ma ta jima a gidan ita ce ta biyu a cikin tantirai, itama sai da ta buga game da Karima ta ga tafi karfinta sannan suka dawo dai2 suna abota amma duk da haka idan wata rana ta bace tsakaninsu har dambe sukeyi sai dai kowa ta wahala daga karshe kuma su shirya haka suke yi..

 

 

Amina kuwa wani karamin dutse ta samu ta zauna sai kallon masu aikin take yi ga zojin da hannunta yake yi mata, abin duniya duk ya isheta..

 

 

Bayan wasu lokuta ne Shugaba Zahra ta ce cikin babbar murya yadda kowa zai ji.

 

”Kowa ta daka da aikin lokacinta cin abincin rana ya yi”..

 

Cak kowa ta dakata da aikin yayinda kowa ta kama hanyar zuwa karbo abinci, Amina ita tsaye ta mike dan kuwa tun dazu hanjin cikinta ke yi mata kuka dan dazu ma da safe kasa karin kwamallo ta yi, dan bata shan kunun koko ga yunwa tana ji ko yanzu ma haka zata karbo shinkafar da bata da wani tasted amma ya ta iya dole haka zata ci Kodan maganin yunwa. Maganar Karima boss ce ta ji kamar daga sama tana cewa.

 

”Amina kike ko wa? Kizo mutafi mu karbo abinci, kuma ki daina zubar da hawayenki haka dan ba wani taimako da zaki samu tunda kin aikata kisan kai ai dole ki kare rayuwarki cikin *GIDAN YARI* ko mu nan haka muka yi hakuri har muka kawo wannan lokacin babu yadda muka iya” ta gama maganar tana yin gaba dan tafiya.

 

Amina ta share hawayen da suka gangaro a kumatunta kafin ta ce cikin muryar kuka ”wallahi ni ban yi kisan kai ba, bani na kashe ta ba, kazafi aka yi mani”. Juyowa Karima boss ta yi fuskarta dauke da murmushin kin raina mu, kafin ta ce ”Hmmm!! Uhmm!! Ai kowa ma haka take cewa idan ta shigo wannan gidan domin tasamu ta kufuta kuma ba haka bane zahiri ita ce ta yi kisan! Wannan maganar bazata sa a sake ki ki koma ga danginki ba, hasalima kara kallonki muguwa akeyi, dan haka kima daina wannan batun”. Ki wuce kawai muje kar abincin farko ya kare. Ta fada tana riko hannun Amina.

 

 

Wata kara Amina ta yi yayinda Karima boss ta rike mata hannu, Karima cike da mamaki ta ce ”ke lafiyarki kuwa? ” Amina ta ce hannu zafi yake min..

 

Karima boss ta ce ”kashhh kin sani matsala inaga dazun nan da kika fadi” muje na kaiki wurin Oga Sa’id ya sa agyara maki” Amina to kawai ta ce mata tare da bin bayan Karima………..

 

 

 

 

 

*Ku da kace ni a nan.!*

 

 

Inason inga comment nagode masoyana

 

 

*A SANADIN FURUCINA!*

_(YA SANI ZUBAR HAWAYE)_

 

 

 

*(True life story)👈🏻*

 

 

Written story

By

SUMAYYA MUHAMMAD MRD

 

 

 

*ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION*

{R.S.W.A}

 

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Faɗakarwa, ilimantarwa da kuma nishaɗantarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alƙalaminmu ƴancinmu*

 

 

 

 

episode 3&4

 

 

 

_________________________________

 

Sai da suka yi tafiya mai dan nisa kafin su isa wani babban ofishi na oga Sa’id. Karima kai tsaye ta tura kofar office din sannan ta kurna kai ta shiga, Amina ita dai na binta a baya jikinta duk babu kwari, Oga Sa’id wani attajirin mutum ne ya kai kimanin shekaru 43 yana zaune kan kurejarsa wanda tebur yana gaban kujerar, sanya yake da uniform din shi na kaki, wanda akwai tambarin star har uku a kafadar hannun rigarsa, da sallama suka shigo. Oga Sa’id ya amsa sallamar ba tare da ya dago ya ga mai shigowa ba kasancewar yana rubutu akan wani doguwar takarda.

 

Karima boss bata damu da rashin dago kai na Oga Sa’id ba kai tsaye wurin wata kujera ta zauna dake gaban teburin tana fesin din shi, ba tare da ya bata izinin zama ba.

 

 

Sai a lokacin Oga Sa’id ya dago kai dan ganin waye, da mamaki karara a fuskarsa yake kallon Karima domin kuwa yadda yaga ta ja kujera ta zauna ba tare da an bata izini ba, cikin mamaki yake ce wa ”Karima Hassan meye ya kawoki ofishina ko kuma kararki aka kawo min ne?”.

 

 

 

Dariya Karima boss ta bushe da ita kafin daga bisani ta ce ”haba dai Oga Sa’id ko dai ka fara rashin gani ne?, kasan dai inda karata aka kawo da tare da shugaba Zahrah zaka ganni, ni dai ba wannan ba wata ce na kawo sabuwar nan ina ga ta samu targade a hannu, wallahi Shugaba Zahra muguwar mata ce, sam-sam bata da imani, na tabbatar da cewa ita ma kai tsaye zata iya kisan kai dan……”.

 

 

“A’uzubillahi!!! Wacce irin magana ce ki ke yi Karima cewar Oga da sauri ya tareta cikin mamakin maganganu irin na wannan matar babu ko alamar tsayawa, Karima bata damu ba ta ci gaba da cewa ”yo ai muganci ne wannan ace ita bata kula da mutane, shin wani irin hali suke ciki, dan Allah ka duba wannan baiwar Allah duka2 kwananta nawa a gidan nan kasan kuwa tana cikin damuwa kuma bata iya wannan aikin ba sai ta yi mata a hankali ta nuna mata yadda zata yi kafin ta iya, tun da dai har kaddara ta kawota nan gidan dole ta yi hakuri kuma dole ta iya wannan bakar wahalar, hmm ni wlh in ma banda jarabawa me zai kawo ni wannan gidan kaico da irin wannan muguwar kaddara tamu” ta karashen maganar tare da juyowa ta janyo ma Amina dayan hannunta mai lafiyar, alamar ta matso kusa.

 

 

Amina wani irin mugun tausayin kanta ne ya kamata kafin ta matso kusa dai2 inda Karima boss take zaune, ba tare da Amina ta iya furta komai ba, tana dai saurarensu.

 

 

Karima boss ta kalli Oga tare da nuna masa hannun Amina da har ya fara haushin ya kumbura dai2 wurin yantsunta, ta ce ”fisabillillahi wannan adalci ne ko zalunci da cin amana? Kawai dai dan mutum ya shigo gidan kaso sai a dinga zibgar shi tamkar jaki, wallahi kai ko jaki ana sassauta masa, Oga Sa’id yadan zaro ido waje tare dan tausayawa Amina kafin ya ce ”innalillahi! Sannu Amina, yi hakuri bari in kira mai gyara yazo ya gyara maki,” Amina kai kawai ta gyada, Karima kuma ta sake mata hannu tare da cewa ”ki zauna kan kujera kafin mai gyaran yazo” Amina to tace tare da ita ma janyo kujera ta zauna kusa da Karima, kasancewar kujerun zagaye suke da wani babban tebur wanda yasha jibgin takardu da littafai can gefe guda, Oga Sa’id ya dauki wayarsa da take kan teburin ya fara duba lambar mai gyaran targade, dan dama yasaba yi ma wadanda sukaji ciwo irin wannan, bayan ya kirashi ya sanar mashi da yazo ofishinsa ya gyara ma wata targade, ya amsa da to gashinan zuwa da yake a cikin gidan yake aiki shima.

 

 

 

Su dai suna saurarensa bayan ya kare wayar ne, kuma sai wani kira ya shigo shi nan ya daga yana wayarsa, bayan minti 50 da kiran mai gyara sai gashi ya shigo, Amina har wata irin zuba take tsiyayo mata domin randa take a duniya bata taba samun targadeba sai yau, Allah sarki rayuwa kenan.

 

Wasu hawayene suka gangaro mata masu mugun zafi, tasa hannu ta goge, mai gyaran yace ta kawo hannunta nan ya fara latsa hannun har yakai dai2 asalin inda ciwon yake, wata irin gigitattar kara Amina ta kurna mai tare da tsananin tashin hankali da firgita, shi kuwa mai gyran ya ce Karima ta zo ta riketa, aka Karima boss ta riketa gam mai gyaran yayita luddar wajen itako sai ihu take, shidai Oga Sa’id inbanda murmushi ba abinda yake musamman yadda yaga Amina na ihu babu tsayawa, duk da dai yasan akwai zafi amma dai akwai ta da raki.

 

 

 

Sun kai minti 20 ana gyaran daga bisani ya shafa mata wani mai, tare da saka farin kyale ya daure wurin, sannan aka saketa, mai gyaran yace sannu kin sha wuya dan kashin wurin har ya goce amma na gyara wurin, in sha Allah a hankali zai saitu, kuma karki dauki Abu mai nauyi a hannu duk da dai hannun hagune amma ki kula karki dauki Abu mai nauyi kuma karki cika saka mashi ruwa wajen sosai, Allah ya sawaka.

 

 

Amin suka ce su duka, mai gyaran ya ce ”officer kuma asamu maganin zazzabi abata dan zai sauko mata da zazzabi, Allah ya bata lafiya nan da kwana 7 in sha Allah zai warke.

 

 

Oga Sa’id ya ce to shikenan, mai gyaran ya wuce, Karima boss ta ce ”to tashi mutafi, kuma kibar zubar da hawayenan dan basuyi maki maganin komai,” Amina ta mike tsaye, domin tafiya, Oga Sa’id ya ce ”Karima ki biya da ita dakin magani abata magani tasha” Karima to kawai ta ce masa.

 

 

Bayan sun fita office din Oga suka wuce dakin magani, nan aka bata maganin sauke zazzabi tasha sannan suka wuce, Karima boss ta ce ”to bari muje wurin karbar abinci dan nasan kilama na farko ya kare sai dai na biyu idan ma an gama dafawa”. Amina cikin muryar mai cike da damuwa ta ce ”Aunty Karima nagode sosai da kika taimakeni, naji dadi sosai amma ni dakin mu zan tafi bana iya zuwa layin abinci” Karima boss ta ce ”karki damu yiwa kaine ai, amma kije mu karbi abincinan dan ni yunwa nakeji” Amina ta ce bazan iya cin komai ba dan bana jin yunwa” da mamaki Karima ta kalleta tare da cewa ”hmm mikikaci ne da kikace ba kijin yunwa? ” AMINA ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa ”kamar zazzabi nake ji, bana sha’awar cin komai” Karima boss ta ce ”to shikenan yanzu tafi ki samu guri ki kwanta zan je in karbo muna abinda zamu a bakin salati dan yunwa babu dadi” ta fada tana yin gaba.

 

 

 

Amina kuwa ita ma hanyar da zata sadata da dakin da aka basu dan kwanciya, haka ta isa dakin ta sami wasu a cikin suna cin abinci wasu kuma suna fira, da kallo kowa yake binta har ta isa wani gado dake can kurya, dan can ta fara kwanciya tun da tazo, gadaje ne masu yawa a dakin akalla zai dauki adadin mutane 30 a cikin dakin gadajen irin wadanan masu sama da kasa masu hawa biyu, Amina ita dai jiki sanyaye ta kwanta kan gadon na kasa tare da jan wani bargo ta lullube dan tana dan jin sanyi.

 

 

 

Matan dakin wadanda basu gani su kyale suka fara gulmar cewa ”ashe dai taji ciwo” da wasu daga cikin suna cewa Shugaba Zahra muguwar mata wallahi da Boss ma dazu taci ubanta, dan haushinta sukeji, da masu cewa Allah yasa wata rana ta hadu da fushin boss’ wasu kuma suna cewa inama ace sun taru sun hada kai sun likidama Shugaba dukan siya, ko wacce dai taba fadin albarkacin bakinta.

 

 

Amina kam tana jiyo hirar wasu sama2 ita dai abin duniya ya dameta, sai abun da suka wuce suke dawo mata, yaranta guda biyu suka fado mata arai tare da tilon uwarta data rage mata kadai a duniya ko wanne irin hali suke ciki yanzu, tasankan ko ba’a fada mata ba, suna cikin tashin hankali da matukar damuwa, musamman mahaifiyarta, ga yarta da take mutuwar so Zainab………

 

 

 

 

 

 

*KU DAKACE NI ANAN!!*

 

 

#VOTE COMMENT

#SHARE

Leave a Comment

error: Content is protected !!