A wani gari hausa novel complete
Tag: A wani gari hausa novel complete
*ZAFAFA WRITERS FRUM*
*A WANI GARI*
*Story and writing*
*BY*
*Leemart Yar pilloh*🌲
*Page* 1_2*
*Bismillahir’rahamanir’rahim*
“`Duk kan yabo da godiya sun tab’bata ga Allah ubangijin talikai Wanda shi yabani ikon Fara wannan littafin lafiya kuma Ina rokon Allah yanda yabani ikon Fara shi lafiya yabani ikon gamasa lafiya Kuma Ina fatar wannan littafin zai karbu agareku FANS dan akwai abun Al ajabi acikinsa“`
“Zaune suke itada iyayen’ta suna’cin rogon da suka dafa,ba kajin motsin komai saina taunar’da mahaifiyar’ta takeyi kasan’cewar’ta me raunin hankali.
Cikeda tausayin’ta baban marcy yad’ago yazuba mata idanu idanunshi ne sukaciko da hawaye tsayin shekara ashirin kenan take famada wannan lalurar tun basu haifi Mersy ba ko yaushe zata warke oho
‘Daga robar burkutunshi yayi ya tuttulawa cikinsa yasaki wata uwar gyatsa me cikeda d’oyi.
Da sauri Mersy tarufe hancinta zuciyarta na tashi.
Wani wawan dundu ya zuba mata abayanta
“Ni kike toshewa hanci??
Saurin mi’kewa tayi Dan tasan yanzu yana iya kaimata duka.
Bayan bukkarsu taje ta d’ebo ruwa a raminda sukayi Dan zuba ruwan cikin ‘bawon kwakwa mai d’an zurfi ta zubashi tadawo wajen uwar tata .
Ahankali take bata ruwan tagama tawanke mata hannu sannan ta matsar da ita gefe takwanta
Itakuma tawuce wajen tanufi gidansu ‘kawarta yemmi a bakin ‘kofar suka had’u da ita tafawa sukayi had’eda Jan hannun juna suka nufi jeji
Gani nayi kawai suna ta ratsa tsakanin kwakwa batareda wani yayiwa d’an uwansa magana ba
Abakin wata ‘korama Naga sunyada zango sunzauna alokacinne suka sake ajiyar zuciya atare
Yemmi ce tad’ago ta kalleta
Kinsanme ‘kawata??
” a’a saikin fad’a.
“Cikine dani”
Wani kyakykyawan murmushi Mersy tasaki Daga baya kuma idanunta yaciko da hawaye
Natayaki murna sosai da sosai kice wannan shekarar za’ayi aurenki zaki huta zaki tafi kibarni shikenan iyayenki zasu zama ‘yantattu acikin garinnan.
Ta’karashe maganar idanunta cikeda hawaye
Dafa kafad’arta Yemmi tayi sannan tace.
“Ki kwantar da hankalinki Mersy kema zakiyi aure zaku zama ‘yan tattu kuma mahaifiyarki zata samu lafiya”
Murmushin takaici mersy tayi tad’an ‘batarda zancen ta hanyar cewa.
“Cikin waye ne kuma watanshi nawa??
“Wata biyu kenan kuma Daniel ne yaron sarki”
“Ah kice ke jinkirinki yabaki Abu me kyau kunzama manya,amma yakamata ace kinfad’a asan da zaman cikin, tunda kinga yanzu matanshi biyarne bansan mata nawa zai aura wannan shekararba,Ni wallahi banason wannan halaiya tamutanen garinnan shiyasa kikaga na’ki amincewa da kowa bare ayimin cikin nayi aure su suna ganin ba’kin jinine dani hmm.
Tagumi Yemmi tayi sannan tace.
“Nifa ajikina inajin ayanayin rayuwarmu ba rayuwa me kyau mukeba kiduba kigani yadda ake Abu kamar dabbobi agarinnan kwata kwata shekararmu shabiyarne amma anbar iyayenmu abayan gari anharamta mana cin komai sai rogo anhanamu shiga gari sailokacin bikin shekara,hmm abinnan yana bani haushi sosai”
Hmm.
Cikin bacin Rai Mersy tace “ni yadda suke Tara matane yake bani takaici kiga namiji da mata samada goma kuma basajin kunyar kusantar matansu ako ina ko agaban yaransune saikiga yara ‘kanana suna neman junansu amma saima ace kaga yara masu kwazo”
Ta ‘karasa fad’a hawaye nabin fuskarta na tausayin ahalinta Dan tasan akwai duhu sosai cikin rayuwarsu.
Ihunda sukajine yasasu mi’kewa da sauri suka nufi bakin gari tunda anhanasu shiga cikin
Megarin suka gani yana ri’keda jariri sabon haihuwa yanausa daji tsirara yaron yake sai tsala uban kuka yake jikinsa duk jini ko cibiya ba’a yanke masaba yayinda mutanen garin suka biyosa abaya sunata ihu wasuna kuka suna jifan jaririn yayinda sarkin kuma yaketa sauri kuma afusace.
Fashewa da kuka sukayi suka ru’kun’kume juna cikin tausayawa wannan jaririn Domin sunsan zuwa z’ayi a yaddashi a rami yagama kukansa ya mutu ya ru’be domin haka sukeyiwa duk jaririrn da uwarsa ta mutu wajen haihuwarsa acewarsu ‘kashin tsiyace dashi sun chanfa wannan abin sosai.
Sunanan tsaye suka ga dawowarsu tabbas dasunada halin taimakawa dasun taimaki wannan jaririn amma babu yadda zasuyi.
Bukkarsu Yemmi suka nufa suka zauna saidai kukanda Yemmi takeyi yawuce hankali.
Bakomai take tunawaba sai yadda takeda ciki yanzu kenan idanta mutu shikenan haka za’ayiwa jininta tabbas tana cikin tsaka mai wuya
Tunaninsu yakusan zuwa d’aya da Mersy haka sukacigaba da kukansu har sukagaji sukayi shiru
Saidare Mersy takoma gida sanin cewa ba inda mahaifinta yakezuwa kodayaushe yana zaune agidane
Tana zuwa takwanta a bukkarta Dan tasan sunyi bacci itamma bata dade da kwanciyaba baccin yadauketa cikeda mugayen mafarkai irin Wanda tasabayi
Comments and share please more comments more typing inbahakaba shima zansaidashi ne
Love you all
Dan ALLAH A cigaba da rubuta littafin a wani gari