Abdoul-Nasser Alfah Hausa Novel
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*
WRITING BY.
MRS BB
MOM MUHSEEN.
WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.
*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*
🅿️…..2
Taxi ya shiga yana cikin tsananin tunani,har tsoran farkawar Alfah yake,don shikadai yasan rigimar dasuke don dai Allah yabashi juriya da kuma hakuri,da zaman shi da Alfah bazaije ko inaba.
Yadda kowa ya gujeshi shima da tuni yadade da kama gabansa,saidai alkairin da yayi mashi bazai iya saka k’afa ya shure shiba,bacin haka yayi alkawarin da bazai iya karya shiba,hkr dai shine zai cigaba dayi watan watarana komi zai zo ya wuce.
Wani k’ayataccen pharmacy yaje kamar ba a nigeria ba yasiyo maganin,ya taho yana adduar Allah ya taimakeshi yasha maganin,duk da abun zai wuya Alfah ko ciwo me zai kasheshi idan ba yaga yana mashi kuka ba tofa bazai shaba,karshe har yagane inayin hakanne don yasha d’in.to dana fara kuka zaibar mun wajen.dafe kai yayi yana ajiyar zuciya kurun…….
***********
“Mamana Zan wuce isalamiya,duk da dai na makara,idan yasmen ta dawo don Allah ga hijabina nan ka igiya mama don Allah ta wanke mun.”
Mahaifiyar tasu data fito daga d’akin sanwa tace”baki tausayinta Fiyah,tun safe fa bata gidanan. tana can tana wahala da gidan jamila,nasan in ta dawo ta gaji kiyi hkr kisaka wata mana.”
Tsaye take bakin k’ofar d’akinsu tana saka safah,tace”shikenan mama idan nadawo na wanke,daman abunda yasa nace haka jinai nafara atishawa ina tsoran tab’a ruwa,gashi kinga yau akwai sanyi sosai.”
Maman tace”subhanallahi,aikuwa in hakane kibari na wanke maki,inma dole sai ita zakisa,injin tsoran wannan lamoniyar taki Fiyah.”
Jikkarta tad’auka tana murmushi mai tsananin kyau tace”kibarshi mamana,zan saka wata bari natai saina dawo in babana ya dawo ki sumbatar mun shi amadadin.”
Duka ta kawo mata ta ruga waje tana dariya,ita ma uwar dariyar tayi tana cewa Allah ya shirya ki sofiyyah.”
Tafiya take cikin estate d’in wanda babu kowa cikin unguwar tasu,hakan yazama dabiar yan unguwar badai kasameta da mutane sosai ba,sauri take ta isa bakin titi tasamu taxi batason ta rasa qarin ahalarin da za,ai masu yau…………get d’in estate din taga an wangale,bayanta ta waiga ta hango wata dan k’areriyar G wagon fara tas zatafita. ta saba ganin irin wad’anan motocin cikin unguwar tasu *maitama estate* domin kaf unguwar babu karamin mutun duk manya manyan y’an siyasane da masu manyan mauk’ami,gaba ki d’aya unguwar sune suka fita daban,sune kaskantattun talakawa ababen kyama,don babu mai hudda dasu cikin unguwar inbanda gida guda…….don ana kallonsu wulakantattu wad’anda talauci yayiwa katutu,bacin su sunsan suna cikin rufin asirin Allah basu rasa ciba,basu rasah shaba,mahaifinsu yananiyakar kokarinsa don gani ya kawar da idonu aka kallon nawasu,taaye kan iyalinsa………
wani uban burki aka taka gabanta,duk saurinta bata samu ta riga motar fita ba,ajiyar zuciya ta sauke tana kallon wadda ke cikin motar tana murmushi.
“Kin bani tsoro rafeea,ashe kin dawo shiyasa ma ban shigaba.”
Dariya tayi tace “matoraciya kawai,shigo mu wuce baki ga time ba,nadawo wlh ko minty ashirin banba wanka nai nai salah naci abinci kurun nafito.”
Bud’e motar tayi tashiga tace”kinfi kowa sanin Fiya bata da waya aiko.rabona da time tunkan nafito gida ”
Dariya rafeea tayi tace”to uwar gasa magana namance,amman fah gaskiya ya dace ace yah jalal ya barki kirik’e waya hakanan.”
Murmushi tayi tace”kinmance waye yah ko,to ni ai ban mance ba,amman nasan soon zai siya man tunda daman jira yake saina fara jamia.”
Haka suka ringa fira har suka isa makarantar,kasancewar sometimes tare suke tafiya saidai idan daya bata dawo makaranta da wuri ba.
************
Kamar karya shiga d’akin don yana gudun ace ya farka,saidai kuma inhar Yafarka tokuwa bazai zaunaba ficewa zai………..ahankali yashiga d’akin ya ajiye ledar magungunan yana kare mashi kallo,yanajin tsananin tausayinsa yana ratsashi……kwallah suka cika idonsa ya kalli hannunsa da aka nad’e da bandeji ya girgiza kai yana tunano abunda yayi dalilin faruwar hakan.
_Waiwaye_
Exercise yake d’akin motsa jikinsa,don shikadai yake yi malik baida ra,ayin sa yakai one awa yana gudu kan injin gudun,kafin ya sauka ya dauki wani gingimemen karfe yana d’agawa shima yajima yana d’agashi kamar ba karfe yake d’agawa ba saboda yadda yake d’ashi kamar wani tsinke…….malik ne yashigo wajen dauke da tiren breakfast,ya ajiye gefensa yana cewa”tun bakwai nasafe kake nan wajen gashi har sha biyu saura ka ajiye kasaka wani abu cikinka.”
Kamar yana magana da dutsi haka yayi mashi,kasancewar malik baya fushi da Alfah duk abunda zai mashi,saboda Nauyin da yadaukar wa mahaifiyarsa da kuma wanda ya daukar wa kanshi………….maganar yasake nanata mai yasake banza dashi tashi yayi ya isa inda yake,ya dafa shi yace “Alfah duk wannan abun da kake baya canza komi,kuma bazai canza ba kayarda da kaddara mana,akwai fa wad’anda suka fika shiga kunci kuma suka fawwalama Allah,saikai kace bazaka yi biyayya ga hukuncin Allah ba.sannan Nariga nayiwa momi alkawarin kulawa da…………… *malikk!!!* ya kwatsa mai tsawar da saida tasaka malik firgita,jefar da karfen da yake d’agawa yayi yana zazzaro idanu,dandanan fuskarsa ta idasa rikicewa da tsananin masifa…….tunkaro shi yake yana ja baya har suka dangane da bango.hannunsa yana kerma ya daga shi ya kaiwa bango naushi,dan danan hannun ya fashe,saboda bangon ba kamar irin na bulo bane,wani sumfarine nadaban.
donsa yayi masifar jaa cikin voice d’insa mai firgitarwa yafara magana cikin dakiya,
“Wlh wlh wlh kajidai rantsuwa uku ko in kasake gigin anbata mun sunan wani cikinsu saina kashe kaina,har sau nawa zan jamaka kunne ne wai ehy.”
Furzar da iska yayi yana huci ya matsa daga kusada malik yana jan numfashi,duk da tsananin tsoran temper dinsa da yake,hakan bai hana shi sake magana ba,don yana ganin inyace zai ringa kyale shi bazai ta6a sauraren sa ba,balle har ya samu zuciyarsa tayi sanyi.
“Wallahi Alfah kome zakai saina fad’a maka gaskiya,ayanzu bakada wani wanda zaigaya maka gaskiya saini,dole nafada maka kokayi aiki da ita ko karkayi nidai saina sauke nauyin alkawarin mahaifiyar………….wani uban naushi ya kawo wa malik,yayi aurin kaucewa azafafe,yanzu ma bangon ya kaiwa bugu amman saboda zafin rai bai damu da halin da hannun nashi yake ciki ba.
Cikin wani irin yanayi ya ya kalli tiren daya malik shigo dashi,wata yar wuk’a ya gani baiyi wani tunani ba ya daukota,babu wani jinkiri ya saita hannunsa ga6ar hannunsa na dama ya yanke jijiyar dake wajen.dananan jini ya 6alle kamar an kunna famfo.
Wata k’ara malik ya fasa yana tunkaro inda yake,shikuma yana ja baya yana cewa”karka nufoni,indan ka iso nan wlh saina sake yanke wata jijiyar,kafita anan inb fita ba nizan fita malik karka matsoni,kabarni na mutu kabarni natai inda zan fi samun jindadi,kuka malik keyi yana cewa”Alfah waya gaya maka mutiwa hutuce,mekayi wa Allah daza katai dashi matsayin guziri,inhar kamutu ahalin yanzu wlh wuta ce makomar ka……karka fita Alfah katsaya katsaya nace……….amman bai saurari malik ba ficewabyai daga cikin d’akin,waje ya nufa yannunsa jini kurun yake fitarwa b kadaba……..kfi Malik yafoto tuni alfah yafice daga gidan,tafiya yake baisan inda yake jefa k’afarsa ba………ko minute biyar bai da fitowa ba zai tsallaka titi,mota tayi sama dashi ya zube wajen babu numfashi.
_back to story_
Likitanne yashigo yace”bai tashiba kenan,”malik yayi ajiyar zuciya yace”eh dr gashinan naga ma kun cire jinin,gashi ruwan shima ya kusan karewa…….akwai sauran ruwan da za asake saka maine.”
Dr have”sauran leda biyu hudu ce ansaka biyu,saura biyu da wani abune?”
Shafa kai malik yayi yace”bani son ya farka ba agama saka ruwan ba,don ba lallai ya zauna ba daya farka zai iya fixge carnula ya fice.”
Jinjina kai yayi yace”wane irin mutunne shi haka,na lura yana da wata irin zuciya amma da gani akwai abunda ya faru dashi baya,don nidai nasan wannan fuskar sai yanzu na tuna inda nasanta.watarana na bar wajen aiki nan ina sauri zanje gida saboda maidakina tamun waya gidan babu lafiya,saurin danake yasa har nabanki wani mai anoconder kuma nai mashi babbar 6anna………dandanan titin ya cika yafito yana ta bala,i saina biyashi gashi ko sisi ban dashi ga aljihuna,ga shi yaci kwalata duk hkrin da ake bashi ya rufe ido cewa saina biyashi,saiga wannan bawan Allah cikin mota shida driver sa,fitowa yayi yana tambayar lafiya? don titin ya cinkushe babu hanyar wucewa.
Bayani nai mashi da halin da nake ciki na sauri inje ga iyalina.wlh malik check ya rubuta ma mutumen,na five hundred thousand bacin kuma kudin duka dubu dari uku ne……….naita mashi godiya ba karamin dadi najiba kullum ina adduar allah ya had’ani dashi inyana neman taimako nima nataimaka mashi.”
Malik ya yi ajiyar zuciya yace”Dr labarin mai tsayine kuma bazan iya baka shi ahalin yanzu ba,saidai ko nan gaba,amman tabbas Alfah yana cikin halin taimako,wlh nikad’ai bazan iya shawo kanshi ba.”
Gyara tsayuwa dr yayi yace”na fahimceka malik,karka damu ga ID card dina nan duk sanda kake bukatar taimakona,ga address dina nan ajiki da contact dina,insha Allah nima zan bada tawa gunmawar karka sare kacigaba dayin iyakar kokarinka har mukai ga ci……………shiru sukai ganin yana jujjuya kai yana ya mutse fuska,kafin ya bud’e idinsa yana kallon rufin d’akin……….idonsa ya sauka kan Malik da dr suna kallonsa suma.
Da alama yana nazarin abunda yafaru dashi ne.duk sunyi zuru suna kallonsa gaban malik na fad’uwa saboda gudun abunda yake tunani…….ai baigama nazariba yaji wata irin shak’a da ya kawo mashi ya gama shi da bango,idonsa saboda tsabar masifa da zuciya kamar anzuba mashi garwashin wuta.
“Meyasa kakawoni nan ehy,banace karka sake ka tab’ani ba,meyasa bazaka barni nabar masu duniyarba!”cikin tsananin tsawa yake maganar ya cigaba da cewa”malik!ka cuceni kacuce ni nace,yafada yana jijjigashi kafin ya tunkud’a shi ya fad’i. Kallon carnula dake jikin hannunsa yayi yayi mata wani irin fizga,dandanan ini yace yaga hanya k’ofa ya nufa atsananin fusace ya bude yafice tare da bankota da mugun karfi……..Dr da malik binsa sukai agune don ahalin da yake ciki komi zai iya faruwa dashi yadda yake tafiyar zaka gane cewar gentle guy ne kuma k’ak’k’arfane………gudu suke yana sauri shikuma amman sun kasa kamoshi,har sun bar titin asibitin sun yanki wata hanyar daban,duk yadda suka zo iskeshi abun yacitura……..titin nasarawa suka hangoshi zai tsallaka kenan wata mota ta rugo da mugun gudu jikake……….kuuuuuuuuu karar burki da cin taya.
Command share pls.
[03/10, 7:52 pm] +234 916 116 0547: 💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*
WRITING BY.
MRS BB
MOM MUHSEEN.
WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.
*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*
🅿️………1
Wani irin traffic ne aka had’a kan titin central park,wanda ya jawo tsaikon motoci.ko kad’an ma motocin basa tafiya tsaye suke,wasuna fitowa daga cikin motarsu suna hangen abunda ke faruwa,dan dazon mutane ne kan titin yayinda wasu keta fitowa kallon abunda ya faru.nima dai matsawa nai sosai don kashe kwarkwatar idona,mutane nake ta turewa ina kutsawa don isa inda wannan dan dazon mutanen yake…………..wow oh may god masha Allah,wani tsalelen guy ne na gani kwance k’asa cikin jini,duk da yadda jini ya wanke fuskarsa da kirjinsa hakan bai hana tsananin kyawunsa fitowa ba,ko makaho ya shafa yasan wajennan akwai kyau na fitar sharia…………..araina nace kai mutanen mu sai abarsu yanzu duk nan babu wanda zai iya kawo mashi d’auki……ban idasa tunani naba naga wani guy yashigo wajen a dari da hamsin yana shashsheka,,,,,bai tsaya ko inaba sai gaban wannan guy d’in dake kwance cikin jini………kuka yake yana jijjigashi yana cewa mutanen dake zagaye dasu. “Don Allah ku tai makeni na kaishi asibiti,bana iya daukarshi….don Allah kuduba halin da yake ciki,ko numfashi fa bayayi.”amman saboda rashin mutunci babu wanda ya kulashi saima tsogumi suke akan ya kauda masu shi suna da abunyi,wani babban mutun yakalleshi yace”wai ba d’an gidan ALH MAINAH bane,wannan tsinennen yaron zamu taimaka,ai baida wani anfani,tunda har iyayen dasu haifai ma sun yardashi basu so wa kuwa zai jefa kanshi cikin matsala,gara kabarshi ya mutu domin itace tafi dacewa da mai irin layyarsa la,anennen yaro kawai.”
Nanfa kowa yaita fad’an albarkacin bakinsa akan wannan guy dake wance har lokaci baisan wake kanshi ba,kuka guy din dake rike dashi yake yana neman taimako amman babu mai kulashi,daker yajashi gefen hanya yana kuka yana cewa.
“Allah yana tare dakai *Alfah* insha Allah ba yanzu zaka mutuba,kowane mai rai da tashi jarabtar kai kuma haka taka tazo,Allah ya baka ikon cinyewa………..kwantar dashi yayi ya koma bakin titin yana tsayar damai taxi cikin ikon Allah yasamo,da gudu suka zo suka daukeshi shida mai taxin suka sashi cikin motar,basu tsaya ko ina ba sai asibiti.
Cikin gaggawa suka ansheshi suna ta fad’an meyasa ba,a kawoshi cikin gaggawa ba shidai wannan bawan Allah baida bakin magana,domin shidai burinsa yaga aminin nashi yadawo hayyacinsa,card ya siya yaje aka rubuta mashi duk abunda ake bukata.ansa yai ya wuce pharmacy ATM yabada aka zara sannan aka bashi abunda ake bukatar,yaje yakai yadawo ya zauna yadafe kai.hawaye share share ga fuskarsa yake magana kamar mahaukaci shikadai.
” babu abunda zai sameka *ALFAH* zaka tashi,insha Allah babu abunda xai faru,duk yadda kake kaunar mutuwa idan kwananka na gaba bazaka tab’a mutuwa ba,saidai kasha wuya kurun ban san har sai yaushe zaka gane abunda nake nusar dakai ba,ko mutuwar kayi Alfah bakada tabbacin acan din zaka dace da jin dadin daka rasa anan duniya,kayi hkr komi mai wucewa ne no condition is permanent.inaji araina watarana komi zai daidaita………kuka yake yana tsananin tausayawa abokin nashi,baida kamar Alfah duk duniya shine gatanshi shine kominsa, duk abunda yasamai na dadi dana bakinciki tare suke raba wa,………dafashi akai ya d’ago fuskarsa ta b’aci da hawaye wani likitane tsaye kanshi,saurin tashi yayi yana goge face d’insa cikin kermar murya yace”Dr ya farka yadawo hankalinsa ko,babu abunda yasamai.”
Murmushi Dr yayi yace”don’t worry ur brother is a life,amman muje office i need to talk 2 u serious issure.”
Binsa yayi harma yaso wuce dr saboda sauri duk ya susuce,rik’oshi Dr yayi yana mashi dariya dafa kafad’arsa yayi suka k’arasa har office d’insa.
💞💞💞💞💞💞💞
“Assalamu alaikum.”
Wata tsaleliyar budurwa tayi sallama acikin wani gida wanda baza akirashi da gidan mai arzik’iba,haka baza ka kirashi da gidan talaka ba,gidane daidai wa daida ginin bulone na sumunti,saidai kallo d’aya zakayi mar kasan cewar ginin yasha jiki,kuma bana yanzu bane don wani wajen ma yad’an gugure,d’akuna ukune biyu ciki da falo saidaya single,sai kitchen acan daidai hanyar fita,public toilet daga can ciki yake.sai filin tsakargida mai d’auke da dalbejiyar umbrella tsakar gidan shafe da smuntu,dagani ba ajima da yin saba.duk dadai babu fenti tsakar gidan, saidai cikin d’akunan ya keda shi,shima yasha jiki dagani andauki shekaru dayawa dayinsa daga gefe idan kashigo zaka hango rijiya.gaba kadan kuma wajen kiwon dabbobine da kaji………atakaice dai wannan gida mamamallakinsa yana da rufin asirinsa,daidai gwargwado daga waje kuma inzaka shigo akwai shaguna biyu jikin gidan,d’aya d’aki aka maidashi dayan kuma kayan masa rufine aciki ake siyarwa.
“Assalamu akaikum”
Wannan tsaleliyar budurwar tasake maimaita sallamarta tana yamutsa fuska,sai hakan yayi matukar sake k’awata fuskarta,farace fess don kadan zai hana ba kace mata zabaya ba,haskenta hade yake da jajaja amman saika lura zaka gane hakan……..”wai gidan ba kowane sai sallama nake idan kuma nashigo ace ba ajiba saina sake,wlh nidai shigo zan nagaji da wage bakina har yafara ciwo.”
Wata matace ta fito daga wani lungu rik’e da buta da alamar ma daga ban d’aki take.
“Wlh ina band’aki najiyoki nasan wasu kaya sai amale inba *SOFIYYAH* ba babu mai shigowa gida yayita kwala ihu yana hayagga.”
Turb’une fuska tayi tana sake yamutseta tace”wayyo Allahna mamana kefa kikace indaina shigowa gida banyi sallama anjiba,yanzu kuma nayi kince ina hayagaga ke kullum yasmeen ce keyin daidai,nadawo ma ko sannu bakiyi man ba,ga yunwa ga kishirwa ga gajiya,koma kice *FIYAH* yau kin dade meya tsaidaki aa sai kika hau yiman fad’a…….tafiya take zuwa d’akinsu tana wannan tsogumin.
Murmushin matar tayi tana biye da ita tace”Allah yashiryaki bazaki tab’a canza waba fiyah.”
Binta tayi cikin d’akin tana cewa”to yi hkr uwar masu gida,yau lafiya kika jima haka ko lectures d’inne suka yi yawa.”
Kaya take tub’ewa tana turo d’an bakinta kamar na tsuntsu,tace “mama yau dawuri muka tashi wlh,inata murna zandawo intai islamiya,mama muna zuwa titin wajen central park wanda ya mik’e har zuwa *ALFAH STORE SHOPPING MALL* wlh mama traffic ya tsaidamu munkai one hour wajen,ashe wanine yayi had’ari amman akarasa mai taimakonsa,mafarin muka kai har kamar yanzu.”
Daga itasai undey da bra,sai surutu take ma maman.matsa kusa da ita tayi tace “mama ballemun donAllah.”
Girgiza kai uwar tayi tana balle mata bra d’in tace”baki tab’a canzawa fiyah ace katuwar budurwa dake fiyah kullum ni ko yasmeen mune y’an 6alle maki breziya,kinji kunya wlh aibanganin laifinta intayi maki dariya.”turo baki take tana sun6ure sun6ure.
“Bari naje in sauke miya kin d’auke man hankali karta babbake,ta fice ita kuma ta d’aura karamin towel d’inta daya bayyana santala santalan k’afafunta,farare tas idona yakai ga bombom d’inta zaro ido nai nace masha Allah madaidaita masu ban sha,awa,komi dai jikin fiyah masha Allah,komi yaji gashinta kwance yake kan tsakiyar bayanta,toilet dake cikin d’akin nasu tashige *fiyah* kenan matashiyar budurwa yar shekara ashirin cif.
***********
“Dr kakirani kuma kanata y’an rubuce rubuce,na matsu naji wane hali d’an uwana yake ciki.”
Ajiye biron hannunsa yayi yana cewa”sorry abokina,ya sunanka ma dai.”
” *malik*” yafa d’a atakaice
Dr yace”nice name,yi hkr malik ina rubuta wasu magungunan nanne,i think wad’ancan bazasuyi mashi aiki sosai ba.”
Shafa kanshi yayi yana fesar da iska yace”nifa ba wannan natambayeka ba cewa nai wane hali yake ciki yanzu,shine abunda nafi bukatar ji daga gareka.”
Ajiyar zuciya Dr ya sauke yace”ka kwantar da hankalika ya dawo ciki hayyacinsa,munyi masa d’inkin raunikan da yaji,sannan munyi kokari munga muntsayar dajinin dake fita ta jijiyar da aka yakesa.yanzu haka jini meke karamai……..shiru yayi na wani lokaci kafin ya sake kallon guy d’in yace”amman ya akai kabari brother naka yakeshan giya,giyarma the most high one.”
Sadda kai yayi yana jin wani irin bakin ciki cikin ransa,mezaicewa dr shin cemai zai eh yasani yanasha.koko aa bai isa hana Alfah yin duk abunda yaga damaba,adacan ma bai dakatar dashiba balle yanzu daya sake rikicewa,babu maigane gabansa balle bayan sa.don yayi imanin muddin ya farka yasan cewa asibiti yake ba karamin rigima zasuyi ba………”kayi shiru abokina.”
Gyara zama yayi yace”nasani dr saidai banda yadda zanyi dashine yafi karfina wlh.nayi iyakar duk kokarin dazan wajen ganin yabarta abun yaci tura,”
Kallonsa dr yake fuskar sa ta nuna 6acin rai”mekake son gaya man,wannan ba reason bane ina iyayensa ina mahaifiyarsa duk yake wannan,sannan kaikuma bakaje ka sanar dasu ba kasan mekayi kenan?to kaci amanar su kai Allah zai kama da laifi tunda kasan hakin da d’ansu yake ciki bakaje kasanar dasu ba sud’auki mataki.to gashinan tafara mashi illah donma yayi sa,a ni ban ta6a ganin wanda yake ta ammalli da irin wannan win dinba bata kasheshi har lahira ba,yaci sa,a bawani dayawa ta ta6ashiba amman ka sanar da iyayensa su sai sudauki matakin dakatar dashi,tunda kace baijin maganarka.”
Maganin ya bashi yace yaje waje yasiyo don nan basu dashi gaskiya.
Fita malik yayi yana cikin tsananin tunani da maganar dr.
“Oh ni malik,yazanyi da Alfah taya zan tursasa sa yabar shan win,ban isa ma nayi mashi wanan maganar ba,ni na isa addua ce kurin maganinsa don ko hauka nafara sabon kamu ban ma tunkarar *maitama estate* ni yanzu ubanwa ya haifeni balle har nakai ga isa gidan *ALH MAINAH* ince d’ansa yana cikin matsala wlh kaf rayuwata gidan kurkuku zan k’areta.zandai yiwa Alfah Addua ubangiji ya kawo wani cikin rayuwarsa da zai tallafeshi,yafitar dashi daga cikin wannan *bakar rayuwa*
Uhmm masu karatu yanzu muka fara,ko yatsa bamu tsoma ba,fatan za ku cigaba da kasancewa dani ahankali zan warware maku zare da kuma abawar.kudai kugyara zama *ABDOUL-NASSER (ALFAH) YANA TAFE SA ABUBUWA KALA KALA*
MRS BB CE
[03/10, 7:52 pm] +234 916 116 0547: 💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*
WRITING BY.
MRS BB
MOM MUHSEEN.
WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.
*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*
🅿️………4
Tun asuba da ta yi salla bata koma ba,kasancewar itakeyin duk ayyukan safe kafin tatafi makaranta,sharar tsakar gida ta farayi sannan ta gyara wajen dabbobi,ta samasu abinci da kajin suma.sannan ta wanke bayinsu ta fiddo wanke-wanke ta share kitchen din,sanwar kalaci ta dora sannan ta fara wanke-wanken,sai lokacin yesmin ta fito daga cikin d’aki tana hamma.
Kallonta tayi tana murmushi tace”kasa uwar bacci sai yanxu aka samu damar tashi,to azo ayimun d’auraya.”
Dariya tayi tana kallon gidan tace”sannu Adda nah,kina kokari fah ni ban sanma baccin ya sace ni ba bayan sallar asuba.”
Tana d’auraye plet cikin ruwa tace”hada gajiya ke damunki bakya samun hutu sosai,don ma kun samu interval aida abun ya maki yawa.”
Zama tayi tana yi mata d’aurayar suna hira.
Tsakaninsu Babu nisa don ashekaru,duka shekara biyuce ta shiga tsakaninsu,suna matukar son junan su duk abunda ya samu guda kamar suduka yasama,mahaifiyarsu tayi tsaye wajen tarbiyyarsu,don suna girmama yayunsu jamila da jalal,watau babban wansu yana aiki ne a kaduna,bai cika zama ba wata secondary school yake koyarwa.
Malam kabir El-ladan shima malamin makaranta ne,amman ya jima dayin retire tun tuni yanzu yana zuwa wani karamin company na hada kujerun amare da gadaje,yana aiki wajen babu laifi yana d’an samun na rufin asirin sa,don kullum ake biyanshi.
Ita kuma maman su kiwo take na dabbobi da kaji,tana daukar d’aid’ai tana siyarwa idan bukatar hakan tatashi,kuma ta kafa shagon sayar da kayan masarufi ak’ofar gidan,babu laifi suna ciniki don duk unguwar babu shago sai nasu,don dole masu kudin unguwar suke siyayya wajen,don inkana son abu dole saika je bakin titi.,ganin wiyar fitar yasa suka hkr suna siye awajensu,don bayarda suka iya,don basu son duk abunda zai hadasu da wannan kaskantaccen talakan,cewarsu kenan.
Kafin mamansu ta fito har fiyah ta dama koko,ta dora juluf din taliyar hausa da zasu had’a da ita…….kafin karfe takwas har tagama komi tayi wanka ta shirya,sai albarka maman take saka masu baban daman tun shidda yake fita,sai goma yadawo ya karya sanan ya koma sai kuma dare don can yake cin narana.
Yesmin ta fiddo wankinsu nata dana Addar ta dana maman,tana yi don yau bazata ko ina ba kasancewar weac da suke amman sun samu hutun kwana biyu.
Fiyah ce ta fito sanye da doguwar rigar atamfa purple and pink sai lemon green,tayi masifar daukarta duk da babu kwalliya fuskar sosai,hakan bai hana tsananin kyanta bayyana ba,purple din hijab tasa iyakar guiwa mai hannu,sai jikarta itama purple din da takalmata,fiyah badai daukar wankaba ta iya had’a matching color,bata yarda tayi hadin gambiza,kuma antyn ta jamila ta koyar da ita salon daukar wanka………ruwa tasha tana tambayar maman su karfe nawa tace mata ,
“Kina da sauran lokaci ki natsu kigama.”
Tana goge takalminta tace”mama jiya ban samu morning lecture ba yadda ya kamata,yau bazan so haka ba.”
Takalmin ta sa mamar tana mik’o mata dari biyar tace,
“Gashinan Dari uku yabaki naga bazata isheki ba yasa nace yesmin ta anso maki dari biyu wajen dalha kikara.”
Rungume maman tayi tana murmushi”nagode mamana Allah ya barmana ke.”
Ta sun baceta ta fice tana ma yesmin by by.
Sauri sauri haka ta fita cikin estate din zuwa bakin titi ta tari taxi.
💞💞💞💞💞💞
Tun safe malik ya fita zuwa company don yana aiki da company Alfah,mai suna *FATION&DESIGNER’S BANGLES COMPANY* nasa ne na kansa,suna siyarda sumfarin yan kunne yan hannu,sark’a da links na maza,agoguna new moden design ba karamin kudi suke samu ba,daga kasashe ake zuwa wajensu siyen d’ai d’ai ko sari,babu kasar da Alfah baya zuwa shida malik akan wannan kasuwancin,gefe guda kuma ga shopping mall d’insa duk malik ke kulawa dasu,bakamar yanzu da abubuwa suka rikice komi yake neman tsayawa ya lalace,dole malik ya tashi tsaye don ganin basuyi asara ba kuma basu rasa customers ba,dafarko cewa yayi yabar aikin bazai sake zuwa ba,saida malik yatusasa gaba yana kuka da ban baki sannan ya amunce yake yin aikin kan computer,duk abunda zaiyi acan office yana yinsa ga computer,saidai guiding din ma,akaitan da ya saka shakikansa dake cikin company suke mashi CID,kuma yana lura da komi ta computer shima,don kwanakin baya saida yakori wasu ma,aikata dasuka so sujawo masu matsala.
haka zalika malik tsaye yake akan dukiyar abokinsa safe rana dare ,kuma duk wata yana fidda albashin ma,aikatan su aba kowa hakkinsa.
don ma kayan yanzu sunyi ramai ramai,suna bukatar sabbin kaya amman yayi-yayi da Alfah su shirya sutai paris da sauran kasashen dasuke zuwa saro kaya masu inganci,yace bazaije ba inkuma ya matsa mashi wlh saida company zai ya kyautar kudin,mafarin ya kyakesa kenan.
Kwance yake wajen swimming yana shan iska,ga table dinsa nan kwalaben win d’insa wajen uku,ya shanye biyu saura guda itama ya sha rabi.
Ko ka dan giya bata bugar dashi,irin yadda take bugar da wasu sukoma kamar mahaukata,zaiji shi yana layi amman daya kwanta yayi bacci zai wartsake,amman idan akai kuskuren tunkarar sa cikin wannan condition din tofa akwai damuwa,don shikanshi baisan 6annar da zai aikata wa kowaye ba,hakan da malik ya lura yasa idan yana cikin mayensa baya kulasa.fita yake yabar mashi gidan har sai ya tabbatar ya lafah sai yadawo.
Malik ne ya iso wajen yana rik’e da computer akwai wasu bayanai da yake son nuna mashi,na email,don sakonnine na abokan kasuwancinsu suka turo suna bukatar zuwa cikin satinan idan ya anshi gaiyyatar, zasuyi wani ciniki idan yana da lokaci.
Idonsa arufe yake yad’ora d’aya kan d’aya,girgiza kai malik yayi zai juya don yasan bazai bashi hadin kai suyi magana ba inhar yanancikin wannan halin.
Jiyai yace mashi”kafasa abunda kazo yine”
Ajiyar zuciya yasauke yana dawowa ya zauna,laptop d’in ya tura mashi gabanshi yana cewa”bak’i garemu suna neman iznin zuwa don suna son siyen kaya,gashi kayan babu masu kyau sosai duk an zab’e shiyasa nace maka yadace kaban dama ni naje idan kai bazaka ba.”
Tura mashi system din yayi yana cewa”katura masu acceptance latter,zuwa opper week sai suzo kafinan har kaje kadawo.”
Dadi yaji koba komi yau ya sauraresa duk da yana cikin halin maye,mikewa yayi zaibar wajen wayarsa tayi kara,ya duba yaga ba suna dauka yayi yana sallama.
“Wa’alaiku mussalam,da malik nake magana.”
Malik yace”yes i’m malik muazzam.”
“OK Dr ne don Allah katuro mun address din inda zan sameka.”
Kallon Alfah yayi daya kai cup din win dinsa bakinsa yana sha cikin kwanciyar hankali,amman fa kokadan hakan bai nuna kan fuskarsa ba,malik yace”ok dr bari na turo maka ina gida ban kaiga fita ba.”
Text ya tura mai sunan unguwar da kuma stress dinsu da no. Gidan nasu.
Wucewa yayi cikin gidan don cigaba da aikinsa.
********
“Yallabai gashi yaturo,amman don Girman Allah yallabai karka saka adaure wannan bawan Allahn,wallahi nagaya maka baicikin natsuwarsa hakan tafaru,kuma naba Rafeea hkr cewar baiyyi don yana sane bah.”
Cikin fushi Alhaji kwangila yace”karka raina man wayau Dr fahad,ya d’aga kantamemen hanunsa k’azamin hanunsa ya wanke y’ata da mari,sannan ya zageta har ya hada dani sannan kace inkyalesa wlh ko waye ubansa yau sai ya gane kurensa,saidai shi yaji tsoron sake aikata haka akan wata badai Rafeea ba.”
Shiru Dr yayi yana daya sanin sanar dashi cewar yasan sa.
Waya Alhajin yake cikin fushi cewar”yanzu yanzu nakeson kuje ku kama shi,karku ragar mashi har sai nazo zan biya na dauko feea makaranta zamozo tare,ga address din gidan nan zan turo maka.”
Kashe wayar yayi yana kallon dr daya sha jinin jikinsa”kodai dan gidankune sai haka dr jibeka yadda duk kawani lafke,garama katashi katai don wlh bazan ragar masa ba,da dai wani yata6o mani ba Yarlelena ba to da saina sassauta mashi,amman wlh bazan lamunci abunda zai ta6a man feea ba.”
Ta shi Dr yayi yana jin babu dadi kuma yasan malik zaiga yayi anfani dashi don ya cutar da Alfah bacin ba haka yaso ba,abun yafi karfinsa Alhji kwangila baida tausayi ko alama.
Malik na cikin gida yaji an danna bell d’insu tashi yayi yasan ko za,a shekara dubu ana danna wa Alfah bazai tashi ba balle ya bude.
Ajiye aikin dayake yayi yasaka rigarsa akan singlet din dake jikin sa.
Wuce Alfah yayi yana exercise dinsa,awajen swimming d’in.
Bude k’ofar yayi yana cewa”Dr u Are welcome…….wad’an da yagani ne yasa gaban sa faduwa sosai,bankesa sukai suka shigo cikin gidan,biyosu yayi yana magana cikin tsananin rudewa”yallabai lafiya,ya zaku shigo mana gida kai tsaye,”
Wani daga cikinsu ya shak’osa yana tambayarsa ina guy din daya mari diyar Alhaji kwangila.
Duk abunda kefaruwa Alfah yana hange,ganin yada suka shak’e malik ne abun ya tunzurashi ya jefar da karfen dayake d’agawa ya doso wajen cikin wani irin fushi da zuciya.
Basu san da tahowar shiba kawai ya finciko dan sandan da yashake malik ya wurgar dashi gefe har yana fad’uwa kasa.
Malik ya sha gaban Alfah yana mazurai duk ya gigice don yasan tabbas aikosu akai su kama Alfah…….”Aa Kadaina karka jawo mana wani tashin hankali”,ogansu da sukazo tare yace”ku fiddo mana wanda ya mari y’ar Alhaji,kokuma mutai daku kuduka.”
Cikin muryarsa dakakka yace”nine nan sai akai yaya.”
Kallon mamaki suke mai ogan yace”u are under arrest.”
KO akwalar rigarsa ya mik’a masu hannunsa suka sa mashi unka,malik duk ya gigice yace”wlh saidai mutai tare bazaku daukesa ba wlh. kunko san kowaye shi kushiga taitayinku kafin ………cikin tsawa yace mashi ” *malik!!! Karka sake wata magana anan”*
Ya kalli ogan yace “muje.”
Aguje malik ya fito ya bisu abaya taxi ya tara yarufa masu baya,sai station.
Fiyah da Rafeea school din su guda,amman kowa da couse dinsa sun fito hutun minty talatin Abbanta yakirata yace ta taho da qawarta da abun yafaru jiya zasuje police station………jikin fiyah yayi wani irin bala,in sanyi tace”yanzu fisabilillah feea kin kyauta,saida kika sanar da Abbanku wlh baki kyauta ba to ni innaje mezance sokike nabada shedar dazata saka akullesa,nidai banji dadi bah wlh.”
Rafeea itama duk taji jikinta yayi sanyi tace”wlh fiyah shine ya gane bani na sanar dashiba ,ganin shatin marin yayi ga kuncina yace inban fada mashi abunda yafaru ba saiya b’ata man rai,kuma koda nasar dashi cewa nai yabarshi na yafe mashi basai ya dauki mataki ba amman wlh su yah hashim suka tirashi cewar karma araga ma kowaye.”
Jinjina kai fiyah tayi tace amman inkinje ai kina iya sake rokon sa asake shi kin yafe kilan ya hakura.”
Tace”to zan jaraba muje yace yana bakin get yana jiranmu.”
Mrs bb ce
[03/10, 7:52 pm] +234 916 116 0547: 🅿️…….3💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*
WRITING BY.
MRS BB
MOM MUHSEEN.
WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.
*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*
🅿️…….3
Iya kar karfinta ta taka burkin,hankalinsu inyayi duba ya tashi.don sunyi tunanin sun banke shin,amman sadda ta bud’e idonta taganshi tsaye yana jiran motar tabi ta kanshi……..daidai sadda su malik suka karaso wajen sai shashshekar gudun dasuka yi suke,da sauri suka fito daga cikin motar duk sun rud’e.don *FIYAH* tuni ta fara kwallah don gwanace wajen tsoro ……..cikin sa,a Dr ya rik’esa gam yana kallonsa,idon nan nashi ya canza launi ya tausasa murya yace”plsss Alfah miye haka ya kakeyin abu irin na marasa hankali,meyayi zafi har haka ka tausayawa kanka kakuma ji tausayin wannan bawan Allahn abokin naka.”
Rafeea duk ta tsure saboda tunaninta ta bankesa saboda yadda ta taka burkin daf da shi sosai.
“Assalamu alaikum,bawan Allah bakaji ciwo ba dai ko,kuyi hkr wlh ina saurine shikuma ya hau titi bai duba gabansa ba.”
Wani kallon wulakanci yajefa mata ya fixge hannun sa daga na Dr yana dogon tsaki,fiyah na gefe tana goge kwallah ganin babu abunda ya same sa……..ran rafeea ya b’aci ainun,da abunda Alfah yayi mata kallon shi tayi,cikin fushi tace”dallah malam miye nayi man tsaki,daga d’an kuskure kadan zaka wani yiman kallon wulakanci,kana jaman tsaki ni nace kahau kan titi babu kulawa, ko angaya maka titin dakin gyatumarka ne ehy,”taja dogon tsaki ta juyawa zata bar wajen.
Jitai kurun anfizgota kamar kwali omo cikin zafin nama,wani irin jan rik’o yayi mata baiyi wata wata ba ya saka tafinsa tare da iyakacin karfinsa ya kwalhe ta da kyakkywan mari. Ga baki d’aya wajen sun shiga shock,Rafeea jitayi ganinta ya d’auke da jinta…….idonta sun kada sunyi jajawur kamar gauta wata k’ara ta fasa tana dafe da wajen………..aguje fiyah ta karaso wajenta tana rikeda ita,jikinta rawa yake saboda yadda karar marin tafita. tabbas kasan wanda akai mashi ba karamar d’imuwa zai shigaba.cikin tsananin tashin hankali Rafeea ke kuka tana dafe da fuskarta,cikin kaushin murya yace”daga yau zakiyi gigin zagin wani bama niba,don ubanki yar iska da iyayenta basu bata tarbiyya ba.”
Ya fizge daga hannun dr da malik,yajuya tari taxi zai shiga yajiyota tana cewa”shege d’an iska,azzalumi ban yafeba wlh saina yi silar zuwanka gidan yari mugu……..azafafe yadawo wajen malik na rik’eshi yana cewa”haba Alfah karka biyeta macece zaka iya rauna ta tafa,wani irin juyowa yayi yana kallon malik yace”nasan da cewar macence ai shiyasa zan koya mata hankali yadda zata ji tsoron tunkarar namiji ko bani ba,don ubanki ba gidan yari ba kisaka akaini lahira inkikai hakan zan dawwama ina saka maki albarka jakar banza,”
Kuka take tana cewa”wlh sai babana yayi sanadin ajalinka,inhar yasan kaine ka mareni zaka gane kurenka mugu……..k’afa yasa zai halbeta yaji anrik’e k’afar caraf cikin mamakin wanda yarik’e kafar sa yake kallon wajen…….. *fiyah* ce tayi han zarin rik’e kafar tana hawaye duk sun wanke mata fuska,wani irin wurgi tayi da k’afar tana share kwallarta ta mik’e daga durk’ushen da take gaban Rafeea,cikin d’aurewar fuska kamar ba fiyah ba,cikin masifa da y’ar muryar ta kamar ta yan yara tace,
“Kar ka sake gangancin dukanta,kai baka da imanine ehy,bakasan kima da darajar mace ba,ana gaya maka cewa macece karka biye mata kaji mata ciwo,shine kake son sake kaimata duka,to kasani wlh muddin mahaifinta yaji bakaiba kaf danginka sai akulle tsinann……….cikin fita hayyaci Alfah ya yunk’uro zai kwasa mata nata marin,tai saurin ja baya Malik da dr suka rik’eshi……cikin zafin xuciya yace”kubarni na lahanta yan isaka…..janshi sukai har cikin taxi d’in daya tsayar d’azun suka shigar dashi daker, sadda xai shiga saida ya juyo idonsa cikin na Fiyah ya nunata da yatsa,yana girgizashi alamun worning.
Harara tabanka mashi tana mashi alama da hannu wuce kaidai.
Dr yace wa malik”abokina kaban no dinka pls don koda kai baka nemo niba nizan zo har gida induba jikin nashi,don zamanshi babu kulawar likita hadarine ga rayuwarsa.”
Babu damuwa ya ansa wayar yasa mai sannan yayi mashi asauka lfy.
Lallashin Rafeea take tana cewa”kiyi hkr muje gida kinga dare yayi nasan sai nasha fad’a wajen baba da mama,tashi kiyi hkr inkinje gida kisanar da Abbanku nasan dole zai daukar maki mataki,dole ne ma wannan.”
Tashi tayi tana share kwallarta don har ga Allah mari ya shigeta ba kadanba.
Dr ne ya iso wajen yana cewa”kiyi hkr Rafee,atu karki sanar da Alhaji kiyafe mashi bai cikin hayyacinsa hakan tafaru.”
Cikin masifa tace “shine zai juye haukanta sa akaina wlh saina fad’a ai gabanka yayi man wannan zalincin ko kuma baka dauki mataki ba”,ta nufi motarta tana masifa.
Tafiya suke zuwa gida fiyah tace”kinsan dr ne Rafeea.”
Tsaki taja tace”likitan kakane shike zuwa har gida yana dubata duk karshen wata.”
Jinjina kai tayi tace”amman baza kiyi hkr ba Rafeea kiyafe mai tun da kinji cewar baya cikin hayyacinsa hakan tafaru,don inkin lura hannunsa jini yake fitarwa,kuma sai yanzu na ganeshi shine wanda d’azun na taso makaranta aka bankeshi kan titin central park,na yarda da dr da yace bai cikin hayyacinsa ki yafe mai.”
Tsaki taja tana kara gudun motar don tuni angama sallar mangaruba,
“Ki kyaleni fiyah,wlh saiya gane cewa ya tab’o yar gidan Alh muazzam Canji.”
Shiru fiyah tayi don daman tasan za,ai hakan Rafeea na da fada aji wajen mahaifinta,don kuwa ita dayace mace wajensa,jida ita yake sosai duk abunda takeso yi mata yake,kuma duk wanda ya tab’ata yashiga uku don bazai kyaleshi ba.
Saboda haka mahaifin fiyah baison alakarsu,don dai kurun mahaifiyarta macece mai tsananin kirki da mutunci,shiyasa yake d’an barinta tana shiga gidan kuma take hudda da Rafeea,badan ransa yasoba.don yadda duk estate din suka kafa mashi k’ahon zuk’a akan zamanshi cikinsu,shiyasa yake iyakar yinsa don ganin ya kiyaye abunda zai saka suci mashi mutunci.
Har suka isa gida fiyah bata sake cewa komi ba godiya tayi mata da kuma saida safe kowace ta shige gidansu.
“Assalamu alaikum………..ina kika tsaya sofiyya badai kijin maganata ko,bance inkinga wannan yarinyar zata shiriritar dakeba ki kamo hanya kidawo gida,banson wannan alakar taki da ita ko kad’an kinsani,amman ina hakuri ne saboda mutuncin uwarta,amman inbacin haka bazan bari kina shigewa wadannan mutanen a da basu san mutuncin mu ba.”
Duk Malam kabir El-ladan ne yake wannan fadan watau mahaifi ga sofiyya.
Sadda kai tayi tana idasa shigowa cikin gidan,durk’usawa tayi gabanshi cikin ladabi da biyayya tace”baba kayi hkr wlh akullum ina kokarin kiyaye duk abunda kake gaya man,matsala aka samu shiyasa amman dawuri muka taho.”
Ta zayyane mashi duk abunda yafaru tacigaba da cewa”wlh baba dagaske Rafeea take zata iya fa da ma Abban su kuma har prison yana iya kaishi.”
Baban yace “Allah ya kyauta,ni shiyasa banson kina shiga motarta yanzu dada tsotsai wani abu yafaru fa,ki kiyaye ba koda yaushe zaki ringa shiga motar ta ba kinjiko mamana.”
D’aga kai tayi tace”insha Allah baba zan kiyaye kayi hkr.”
“Shikenan,nayi tashi kije kiyi sallah Allah yayi maki albarka.”
Tashi tayi tana ansawa da Ameen maman tace intayi sallar tazo ga abincinta nan ta d’auka,shigewa tayi d’akinsu tana magana da yesmin dake ta faman gugar uniform.
“Yaushe kika dawo yesmin.”
Tace”Adda nah nima ban jima ba uncle yahya ya ka woni bajima wa,anty tace gobe inkin taso kibiya tana da magana dake.”
Kayan ta ke cirewa tare da cewa”uhm ni wlh Anty zata matsaman kan wani kanen mijinta,ki kyaleta kawai yesmin ni 6allemun wannan abar.”
Tana juya mata baya ta 6alle mata bra d’inta.
*************
Tunda suka dawo gidan malik baiyyi gigin sake mashi magana ba,don yasan yanzu zai sake burkicewa babu mai taimakonsa kuma,don unguwarsu ba sosai mutane ke shiga sabgar da batasu ba.
Malik ya dawo daga masallaci sallar isha,i ya samai falo shima ya gama tashi sallar agida yana d’auke praymate d’in.
Girgiza kai yayi kawai don baisan yadda zai yasa Alfah cigaba da yin sallah cikin jam,i ba,ko masallacin bai zuwa duk sallar dazai tofa cikin daki zaiyyita.fuskarnan kamar kullum tur6une babu walwala babu rahma kanta.
Zama yayi yana kallonsa kafin yace mashi.
“Me zakaci abokina”
Kallon banza ya wurga mai kurun yana cigaba da opreting system d’insa,xuwa can ya ajiye ya tashi yaje gaban frig ya bude win d’insa ya dauko ya cire hancin,ya bulbula ga cup ya koma mazauninsa yana kurb’a yana aikinsa,….kallon bakin ciki da takaici kawai malik kemashi,don baima san yazaiyyi da Alfah ba,idan akwai abunda yatsana cikin halayyarsa sabbi to bai wuce wannan shan win d’in da yake ba.
Kasa hakuri yayi yace mashi”Wai Alfah mai yasa kakeson kashe kanka,meyasa kai rayuwa baka daukar komi da sauki,duk abunda Allah ya kaddara maka baka hkr karok’esa sassauci,ina anfanin wannan halayyar daka k’irk’iro ma kanka………..cikin masifa dazafin zuciya ya jefar da cup din glass din dake hannunsa ya fashe kasa,yana huci.
Yanuna malik da hannu yace”kafita harkata malik,kadaina takurani da kalamanka,komi nake komi zanyi is not ur business.”
Hawaye suka cika idon malik yace”komi zakace kuma kome zakayi man Alfah wlh saina gaya maka gaskiya,koda kuwa kasheni zakai wlh saina fad’a,don kuwa ina kaunarka inason rayuwarka idan kai bakason ta,ka taimakeni ka kulaman da ita,idan narasaka Alfah yakake son inyi,banfa da kowa saikai.Allahne gatana kaine gatana.plsss karage shan win d’inan koda baka bari dukaba dr ya sanar dani yadda tayi maka illah.”
Kwallarsa suka silalo kan fuskara yaciga ba da cewa”Allah yasan da abunda yafaru baka da laifi,amman ya6oye gaskiyarsa saboda yana son jarabtarka yaga iyakar imanin ka,duk wannan ba daidai bane,kuma kaima kasani kake take sanin…..cikin sanyin murya ya katse malik da cewa”enough!and i’m sorry to hut u.”
Tashi yayi yashige bedroom d’insa da system d’in sa ga hannu.
Murmushi malik yayi yace “thank god,yaushe rabon da naji irin wannan sweet voice d’in naka Alfah,ina maka fatan Allah ya sanyaya zuciyarka ya kuma kawo mani matai makin da zamu taru mudawo dakai cikin rayuwa mai kyau.
*sorry jiya banyi update ba in busy ne kuyi hkr.*
Mrs bbce
Mom muhseen😘
[03/10, 7:52 pm] +234 916 116 0547: 💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*
WRITING BY.
MRS BB
MOM MUHSEEN.
WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.
*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*
🅿️…….5
Tunda take ba ta tab’a shiga mota irin tasu Abban feea ba motar kamar ba tafiya take ba ga wani irin sanyi mai dadin bala,i mai tsananin shiga jiki.
Kan kace me har sun isa station din mamaki ya cika fiyah idan da akan taxi ne sai sunyi tafiyar one hour basu je ba saboda dan banza nisan dake akwai.
Kamar karta fito taji amman dolenta ta fito dandanan kuma taji gabanta yayi wata irin fad’uwa,”nashiga ukuna fiyah, idan mama ko baba yaji labarin zuwa na police station ya zanyi wlh wannan karon baba dukana zai.saida Rafeea ta jawota sannan suka fara dosar cikin station din,gabanta yana faduwa dan danan tausayin wannan bawan Allah ya kamata,tana adduar Allah yasa Aban feea yayi hkr asakesa.
Malik suka fara cin karo dashi yabuga uban tagumi idonsa duk yayi ja saboda yasha kuka.
ba karamar kauna ce tsakaninsa da Alfah ba,duk abunda ya samu guda to dayan yana shiga tashin hankali,wanda zaka ce shine abun ya faru dashi,haka inhar na farin cikine tofa bazaka gane wanda abun yasama ba,ko yanzu babu irin roko da magiyar da bai masuba,akan su sakeshi zaibasu ko nawa sukeso.
Amman sai DPO din yace wanda yasasu aikin yafi karfin su anshi cin hanci da dai wanine bashiba,dasai su ansa su sakeshi.”
Alfah dake kulle cikin cell yace”malik idan har kasake magana wlh kaji narantse zanyi abunda bakaso,donme zaka ringa masu kuka iyayenka ne su don ubura ubansu wlh karka sake kask’antar da kanka kana masu magiya,idan sunga dama su barni nan har mahdi ya bayyana.”
Wannan maganar ta janyo tashin hankali,don kuwa ran DPO yakai mak’ura wajen b’aci yace sushiga su mashi dukan mutuwa.
Malik yace”yallabai,karka yi haka wlh zaiyyi b’anna fah karsu tab’ashi za,a samu matsala.”
Amman bai sauraresa ba ya tura wasu constable guda biyu suyiwa Alfah mugun duka,yana jinsu baice komi ba ko motsawa baiyi ba zuciyarsa takai mak’ura rabon ma dayaji irin wannan temper d’in shikanshi bai saniba………….jiyai kurun an kai mashi duka ga baya da wata k’atuwar k’ota, cikin tsananin zuciya ya d’ago ya kalli wanda ya buge sa,ganin zai sake kawo mashi bugun.baisan ma sadda ya kai mashi duka ga fuska ba,dan danan hakorinsa guda yafita. dukanshi yake kamar Allah ya aikoshi saida yaga baya motsi sosai ya juya kan gudan wanda yafara jin fitsari don ganin irin dukan da akaiwa dan uwansa.ko kadan Alfahbai ragar masuba k’wanjinsa ya saki ya dunga naushinsu iyakar karfinsa.
banda kiran sir babu abunda suke,sun kasa kwatar kansu saida Alfah yayi masu dukan da suka kasa tashi,ya bud’e kofar ya watsosu waje…..daidai shigowar su Fiyah da feea da Abban su kallon su yake yana mamaki,baki bude yake kallonsu kafin yace”mezan gani haka meye haka”
Duk sunyi tsuru tsuru suna kallon kallo,koshi DPO din ya kasa cewa komi saida ya daka masu tsawa sannan yace”yallabai wlh wannan guy din dan dabane,zaginmu yayi nasa adakeshi shine yayi masu haka.”
Kallon Alfah Alhaji kwangila yake cikin tsananin mamaki,takowa yake yazo har gabansa yana kallonsa ya dora hannunsa kan kafadar Alfah.
Cikin fusata Alfah ya ture hannun daga jikinsa yana ma Alhaji kwagila wani irin k’ask’antaccen kallo.ya jefar da hannun na Alhaji kwangila cikin wata irin murya yace masa tare da nuna sa da hannu
“Kar ka sake hannunka k’azami ya sake tab’ani.”
Dariya Alhaji kwangila yayi yana kallon sa k’asa zuwa sama yace”ban yi mamaki ba,ai indai kaine zaka aikata abunda yafi haka,domin iyayenka ma basu iya dakai ba balle………cikin wata irin anger yace”stop telling nonsense about my parent,if……”
Shima Alhajin cikin fushi yace”if me ehy,kai har mutunne,nace kai mutunne har da zaka daga kazamin hanunka ka mari y’ata,idan iyayenka da kayiwa sun kyaleka to kuwa banga ubanda ya isa ya hanani kulleka ba wlh,muddin ba hkr kabayar ba.”
Feea dake bayansa idonta yaraina fata don ganin yadda fuskar Alfah tayi babu rahma ko kadan,kiris yake jira yajuye tirar dake cinsa.
“Abba kabari wlh nidai dayayi wa na yafe,na hakura kazo mutai.”
Zare mata ido yayi yace wa DPO “ku kullesa har sai nina bada damar fiddoshi”aguje malik ya iso wajen yana tare Alfah agigice yace”baza su sake kullesan ba wlh,sannan kushiga taitayinku zaku yi dana sani akan hakan.”
Alhaji kwangila shima cikin bala,i yace”ubansa kadai zaizo nan na hakura kuma bazai tab’a zuwaba domin kuwa wannan dan iskan yaron ya riga yafita daga cikin zuriar su,kunsan kuwa abunda yayi kunsan irin bala,in dayayi har iyayensa suka korai to bari kuji wannan dakuke gani,matar………….jikake tas tatas Alfah ne tsaye gaban Alhaji kwangila ya wankesa da kyawawan maruka har uku.
idonsa yayi wani irin fitinennen jaa,dai-dai sadda wani babban mutun yashigo station din wada tacika da mutane,cikin shakewar murya da ta dishe saboda tsananin bacin rai “wlh kasake furta magana marar dadi akaina saina kasheka,saina fiddo yan hanjinka don ubanka katon banza katon wofi,b’arawon gwamnati baka iya komi ba sai yad’a karya da sharri………kai *Abdoul-nasser* kul akul nace in ka sake magana saina sasab’a maka awajen nan.”
Wannan babban mutumen daya shigo yanzu yake fad’ar haka.
Ajiye hannunsa yayi da yake nunnuna Alhaji kwangila dashi kamar zai kaimashi naushi,huci yake fiddawa yanajin kamar yadunga dukan bango kozai huce haushinsa……yace”Daddykabarni na koya mai hankali,kabarni na keta mashi rashin mutunci.ni….ni..zai….wulak’anta…….sai wasu zafafan hawaye suka shiga zarya kan kuncinsa.
Malik kanshi hawayen yake na tausayin amininsa kuma dan uwansa.
Mutumen yace”nadai ce karka sake magana idan ba haka ba zaka ga b’acin raina.
tunda ya shigo duk aka k’ame ana sara mai,saboda shine comissioner of police. kallon su yake shima fuskarsa babu walwala ya kalli Alhaji kwangila yace” kagani ko,u see i tall u last time ka guji tun karar shi kar watarana ya baka kunya,Abdoul ba kunya ce ta isheshiba tun wancen karon balle yanzu da yasake firgicewa baijin kunyar yaga maka rigar mutunci,gashi kuma hakan akai bacin malik yaje ya kirani da banson iyakar abunda zai maka ba wlh awajen nan.”
Zufa yake share wa yana jinjina kai duk ya gigice,feea na gefe na kuka ganin yadda aka wanke ubanta da mafi,wanda yafi nata. fiyah kuwa kamar kazar da aka tsamota daga cikin ruwan zafi,duk ta firgice.
Cikin taushin murya Alhaji kwangila yace ma mutumen daya ke magana “nagane hakan Alh maude,zan kiyaye.”
Alh ya kalli Alfah dake huci kamar tukunyar da aka gama sanwa da ita yace mashi.
“Abdoul.”
Kallonsa yayi ido jawur batare da yace komi ba,yace”wuce kutai gida zanzo in sameku,malik idan yayi wani misbehave tell me.”
Jinjina kai malik yayi yana cewa”thank u Daddy.”
Jinjina kai yayi kurin yana cewa Alhaji kwangila “kana iya koma wa ga aikin ka,amman ka kiyaye don wataran abunda yafi haka zai maka,kekuma kiyi hkr kiyiwa Abdoul uziri ba halinsa bane.”
Feea dake hawaye tace”wlh ni daman nace mashi nayi hkr shine yace sai ya kullesa.”
Girgiza kai Alh maude yayi yace “uhm shikenan kawai kuna iya tafiya zanje namasa nasiha anjima.”
Kamar kububuwa Haka Alfah yafito daga station d’in,malik binsan yake cikin sauri don yasan wannan fushin sai yayi kwana uku yana yinsa,inbai samu wanda yajuye haushin sa akai ba.
Tuni fiyah ta yanki hanyarta,don tace ma feea bazata bisu ba akwai inda zata bata d burin daya wuce tasan waye wannan guy d’in,ita sai take ganin kamar yana mata kama da yaran gidan *ALH MU’AZZAM CANJI* amman zuciyarta ta kasa yardar mata da haka,saboda in d’an gidanne mezai fiddoshi daga gidan yazo yana irin wannan rayuwar,girgiza kai tayi tanajin matukar tsananin tausayinsa na cika zuciyarta.
Hango malik tayi ya tare masu taxi gudu-gudu sauri-sauri haka take had’awa har ta samu ta tari itama taxi d’in tace mai yabisu baya,binsu yake har k’ofar gidansu tace yayi parking daga nesa,
Azafafe ya bude kofar motar yafito, sai soka hannunsa yake cikin kansa yana ya mutsa kyakkyawar sumarsa kamar ta larabawa,isa yayi bakin get din gidan nasu yana jiran malik dazai sallami mai taxi,dora hannunsa yayi ga bango sannan ya aza kanshi sama,daka kallai kasan yana cikin wani irin hali.
Hawaye taji sun sulalo mata bata ma sani ba.
malik ya iso inda yake yana bude masu karamar kofar shiga,yana mashi magana amman bazata iya juyo abunda yake cemai ba.saida taga shigarsu sannan tace ma mai taxin ya kaita maitama estate.
Don lectures din da zata koma tayi anriga angama,kuma daman ita kadai ta rage mata.
Har taje gida tana hawaye,ganin sun kusa isa yasa ta goge kwallarta tana daidaita natsuwarta,sallamarsa tayi ta wuto zata shiga gidan, ganin buta tayi bakin shagonsu ta dauka ta wanke fuskarta,yadda baza,ai mata tambayar kukan me tayi ba.
“Sofiyya yau ba magana.”
Maitsaron shagonne yayi mata maganar,watau dalha cousin dinsu ne ta wajen mahaifiyarsu,sadda aka gama had’a shagon ta je har rimi ta daukoshi don daman zaman banza yake acan.
Rimi garine cikin katsina
Cikin rashi kuzari ta juyo tana yak’e tace”ayya d’alha wlh nagaji ina sauri inshiga gida,sannu da aiki ya kasuwar.”
Murmushi yayi yace”da godiya,maza hanzarta kar acinye babu ke.”
Murmushi mai kyau tayi ta shige tabarsa.
Sallama tayi yesmin dake kwashe shanya ta ansa mata.
“Sannu Adda kin shawo rana.”
Jinjina kai tayi ba ta bata ansa ba,bin bayanta tayi da kallo cike da nazarinta,da alama Adda na cikin damuwa.
Mamace tafito daga cikin daki tace”kamar sallamar fiyah naji ko.”
Yesmin dake linke zane tace cikin rashin jin dadin ganin yayar tata haka “itace mama,amman kamar bata da lfiya tashige d’aki.”
“Subhanallahi,bari inje inji.”
D’akin nasu ta shiga tana kiranta,bata cikin dakin amman jiyo karar ruwa cikin bayinsu yasa tajuya,
tabarta ta fito.
Haka Allah ya yi sofiyya da daukar damuwar wani ta zama tata,mace ce mai tsananin tausayi abu kadan zai karya mata zuciya,duk da halayenta sunda yawa amman abu mafi bayyana tare da ita shine,san yinta kafin kaga zafin ta zaka jima sannan akwai zurfin ciki sosai,tana da shanye damuwa abu zai jima yana damunta bata bayyana shi ba.
Wankan ta fito tana shafa amman yanayin fuskarsa take hangowa,da zafafan kalaman da abban feea yake gaya mai,runtse ido tayi hango yadda idonsa yayi jajawur gwananin ban tsoro……..haka ta gama murza man ta saka kaya marasa nauyi tayi sallar azahar da la,asar sannan ta fito tsakar gidan.
Mama da yesmin nata hira tazo ta zauna,ta dora kanta bisa cinyar maman tana shagwabe fuska.
“Mama yunwa nakeji.”
Shafa kanta take tace”yesmin dauko wa Addarki d’anwakenta yau mutumen ki akai zakici ko.”
Daga kai tayi tana sake narkewa daman fiyah badai shagwaba ba,ajiye mata yesmin tayi tana cewa”Adda d’azun ina magana baki tanka niba.”
Murmushi tayi mata mai sanyi tace”sorry my little,ban cikin natsuwa ne kiyi hkr kinjiko.”
Tana murmushi tace “bakomi Adda nayafe maki,kinje gidan Antyn.”
D’an waken take ci cikin rashin kuzari,har yanxu amon muryarsa takeji sadda yake mayar wa da Abban feea magama cikin,kunci da bayyana bakin cikin da yake ciki.kamar bazata tan ka ba tace”banje ba yesmin,ban samu time ba kilan sai gobe.”
Ko kwatar dan waken bata ciba ta ajiye tace “na k’oshi mamana.”
Cikin kulawa tace”haba yar sofyna mekikaci anan kefa kikace yunwa kikeji,anya kuwa bakina b’oye man wani abuba.”
*wlh saboda ku yau banci abincin rana ba sai la,asar kuyi manage pls,sannan inhar banga comment 70% ba gaskiya zan dakata da typing,don haka na nuna bakwa jin dadinsa.*
Mrs Bb
Mom muhseen. Lov u all masoyana😘😉