Abin cikin kwai Hausa Novel Complete
ABIN CIKIN ƘWAI…!
📃Littafi na 1
By🪶
*Ummu maher(Miss green)🍏*
_✨TEAM GAWURTATTU BIYAR 5✨_
———————–
Noticed⚠️Labari ne akan zazzafar Ƙiyayya,ban tausayi ban dariya,ban al’jabi,wa’zantarwa,nishaƊantarwa.
*Godiya:*
ina miƙa godiya ta ga dukkanin masoya na marubuta da kuma makaranta,ina ƙara muku godiya wajen nunamin kulawa da kuma soyayya Allah ya barmu tare amin.
*Sadaukarwa*
na sadaukar da wannan littafin ga mahaifiyata hajiya maryam moh da mahaifina engineer Bashir Abdullahi,Allah ya Ƙara musu lfy da nisan Ƙwana mai albarka.
*Doka⚠️⚠️⚠️:*
ban yadda a canzamin labarina ta kowacce irin siga ba,ba tare da an tuntuɓeni ba.
Ku kasance da gawurtattu 5 don jin yadda za ta kaya.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
———————————–
HAJIYA KAKA POV
1 2
… . . .Kana shigowa tunda kan layinmu zaka san cewa ana wani mashahurin biki a layin,gidane kato sosai daga gani ko da ba’a gaya maka ba kasan cewa gida ne na family house farin fenti ne dashi me tsari,a ɓangare kusan sha uku ne agidan.
A babban hall ɗin na gidan ake sha’anin kamu,amaryar na hango taci adonta sosai cikin kayan fulani mai ƙyau da kuma tsari,ƴan matan amarya suna gefe suna selfie ana tsokanar amaryar.
“Khairat ki yi sauri ki fito,don Kin san ke kaɗai suke ta jira”.wacce aka kira da khairat ta jiyo,wow na faɗa don yarinyar irin yarannan ce black beauty,ta juya eyes balls ɗinta da ɗan ƙaramin bakinta cikin shagwaɓa ta ce”to Mama ganinan fitowa”.
Su Rashida ne suka shigo suna ce wa”don Allah Khairat ki fito kina ƙanwar ango amman kina yi wa mutane delay,ga ƙawayenmu nan duk sun zo mu kaɗai suke jira”.
tsaki Iman taja sannan ta ce”Allah Rashida kina nema mana raini wajen wannan kucakar yarinyar shiyasa ni bana son haɗa harka da ita ko kaɗan,yanzu muna zuwa wajen wasu ma sai sun tambayemu anya kuwa wannan ba ƴar aiku ba ce?”.
Wani irin baƙin ciki ne na ji ya tokaremin zuciyata amman babu yadda zanyi don Iman ba sa’a ta bace baya ga haka ma ni ba ma’abociyar yin faɗa bace.
Jikina ne duk ya yi sanyi don ganin irin kallon dasu Iman suke min da ƙannenta su Baby,na rasa me yasa suka tsaneni agidan tunda duj ba haka suke yi wa sauran ƙannen na su ba amman ni daga zagi sai hantara,kaf cikinsu mutum biyu ne suke sona daga Rashida sai Amira.Iman babanmu ɗaya dasu amman kuma sunfi kowa ƙyama ta.
A haka na zauna a tsararrun kujerun da aka ajje acikin gidan,ina juyawa na hango Hajiya Kaka wato kakarmu tasha gwaggwaronta harda jan baki,dariya na fara yi mata har ta yi gaba kuma sai ta dawo baya ta ce”ke kinji ja irar banza malik ne da Maryam su ki ke yiwa dariya don ni dai na fi ƙarfin uwarki da zaki sakani agaba kina yimin dariya yo me ye laifin wannan ƙwalliyar dana yi da zaki ringa yimin wannan dariya kamar kinga mahaukaciya?yo ko uwarki inyamura da take a uwar ango yau bata isa ta nuna min ƙyau ba,don haka ki shiga idona in rufe,shegiya ƴat baƙa kawai”.
tana faɗar hakan ta tafi tana taunar goronta tana cigaba da mitarta don Kaka ta tsani ta yi ƙwalliya kace bata yi ƙyau ba.
Babu abinda yaban haushi a maganar kaka don daman idan da sabo mahaifiyata ta saba da wannan zagin da kuma toxarcin awajen kaka don ita arayuwarta ta Ƙi jinin mahaifiyata duk don a kasancewarta ba yaransu Ɗaya ba,uwa uba kuma gashi mahaifina ne Ya musuluntar da ita shiyasa gaba ki Ɗaya kaka ta tsani mama na,kullum cikin gori kuma abinda ke Ƙara bani haushi da kaka ko a gaban waye sai ta yi in dai Ƴan faƊan suka zo,yaya Aliyu shine Ɗan farin mama sai yaya Salim sai ni khairat sai auta afrah.
“ke kuma Khadija ranar auren na ki kika saka wannan ɗamammun kayan duk jikinki a waje?Ina shi sokon angon na ki ya ke ne?da ya barki kika saka wannan kayan?.Wannan tozarcin da Kaka ke yiwa Khadija a lasifiƙa ta taƙarƙare ta ke faɗa son ranta babu abinda ya shafeta.
Gaba ki ɗaya wajen shiru kowa ya yi don jin ƙatoɓarar da kaka ke yi,don yanzu kana magana masifar zata dawo kanka shiyasa ma kowa ya shafawa kansa lafiya don abin na ta sai ita ɗin.
Rafi’atu ce ta kalli kaka cikin fushi ta ce”Ke kaka shigar da kika yi a matsayinki na tsohuwa babu wanda ya ce miki komai sai ke ce zaki saka yaya ta a gaba da masifarki”.
“inye a lallai Farouku ya baku daman cimin mutunci tunda gashi kina zagina a gaban uwarki bata iya magana ba saboda tana tsoronki to ko farouku ubanki bai isa ba,shegiya ƴar tsigi tsila”.
ƙwashewa akayi sosai da dariyar dramar kaka don idan ka biye mata sai a ƙwana a tsaye.
Ana cikin hakan mukaji jiniya ta motoci ƙyawawa sun shigo cikin ƙaton gidanmu,ai kuwa sai Kaka ta fashe da kuka tana ce wa”To yau wai agidannan ni kuma kewa dariya tsabar rashin ta ido,ni dai wannan abin ya isheni ace ranar bikin jikata amman a nemi a kwashemin albarkar auren jikoki na to wallahi bazan yarda bari Soja Bilal ya dawo kowa sai ya ƙwashi kashinsa hannu”.
Gaba na ne ya yi wani mummunan faɗuwa ganin fitowar Yaya Bilal daga cikin mota ya yi ƙyau sosai cikin suite ɗinsa,ƙyaunsa ya ƙara fitowa sosai kamar ka ɗaukesa ka gudu,ƙyaunsa da nutsuwarsa sun ƙara fitowa sosai.na yi wani tagumi azuciyata ina tuna ranar da zan iya barin tunanin Yaya Bilal a cikin zuciya,Yaya Bilal namiji acikin maza yana da wani ƙwarjini da cikar zati,duk wannan abinda na ke yi Yaya Bilal bai san ina yi ba don tsakani na dashi hantara da kuma kallon banza,donshi aƙwaishi da miskilanci sosai.
Cikin takunsa mai ƙyau da haiba ya ƙaraso inda Kaka take ya rungumeta yana cewa”my grand fa dafatan na sameki lafiya”.da yake shiba mutum ne mai magana da yawa ba yafi yin magana kaɗan,ai kuwa nan kaka ta zage tana ta basa labarin cin kashin da aka yi mata,ina cikin satar kallonsa sai kuwa naji ta ce”kaga waccen ƴar baƙar ita ce ta fara wulaƙantani a wajen nan har kowa ya samu bakin yimin wulaƙanci,waiwayowa ya yi ya kalleni kallo ɗaya shima by mistake ya juya kansa,yaja hannun kaka suka tafi sashenta,kallonsu na yi cikin tsoro na ce”Rashida na shiga ukuna kinga wanna fitinanniyar tsohuwar zata jazamin ƙazamin duka,kinga wani banxan kallon da ya yi min kuwa?”.
Dariya Rashida ta yi sannan ta ce”ai ni dai na godewa Allah da ban ma haɗa ido da wannan mugun sojan ba amman wallahi da na yarda na haɗa ido dashi da tabbas naga wulaƙanci don wallahi haɗuwarmu baza ta yi mana ƙyau ba”.
Ɓata rai na yi na ce”ke kinga Rashida idan bazaki faɗi alkhairi ba to ki yi shiru don Allah don manzon Allah(S.A.W) ya ce ka faɗi alkhairi ko ka yi shiru”.
dariya sosai Rashida ta yi sannan ta ce”hmm so hana ganin laifi gaskiya Khairat ki rage son da ki kewa Yaya Bilal kada ya haifar miki da wata matsalar,don ni har tausayinki na ke ji kina ganin mutum kullum fuska a ɗaure ki rasa wanda zakice kina so sai shi,kuma ke kinfi kowa sanin baƘwa wani Ɗasawa dashi don shi kaf gidannan in banda wannan rigimammiyar tsohuwar babu wanda ya ke gani da gashi.”tsabar haushin Rashida da na keji don ni a rayuwata babu abinda na tsana irin zagin Yaya Bilal.
Anyi sha’ani sosai ranar anyi hotuna kala2 ana cikin hotunan na ce”Rashida don Allah muje wajen Kaka itama tazo muyi hoton babu daɗi wallahi tunda babu Kaka”.na faɗi hakan cikin shagwaɓar da ta zamemin jik.
“caɓɓijan wallahi idan ke zakije Khairat ga hanya nan amman ni la.la.la.don bazan kwasowa kaina masifa ba”.
Kinga tunda wannan masifaffan yazo gidannan yau to wallahi mu ta ka asannu idan kuma ba haka ba mu ɓallowa kanmu ruwa”.
Ɗaure fuska na yi sannan na ce to ni dai na tafi kada Allah yasa ki taho,uwa ɗaya uba ɗaya amman kina yiwa yayanki shedar zur.
Dariya sosai Rashida ta yi sannan ta ce”inna ta gaida aisha don wallahi bazanje in janyowa kaina masifar da zata saka in kasa bacci ba”.
a hankali na ke takawa har na ƙaraso sashen Kaka,na jiyo dariyarsu gwanin sha’awa,ina sakawa araina Allah yasa Yaya Bilal wataran inga yana yimin dariya haka don ni sai inga kamar kaf gidan ma yafi kowa tsanata har da ƙyanƙyami na ya ke yi,Don da kansa ya taɓa cewa Kaka shi ya tsane ni saboda kaf gidannan babu mai masifar kallon mutum irina gani baƙa kamar gawayi don haka shi ko kallona bai san yi.
Ina shiga Kaka ta gimtse fuska ta ce”Innalillahi wa inna ilaihi raji’Un yanzu tsabar baƙin ciki tun kafin abani tsaraba ta kika zo salon ki cinyemin duka?to wallahi ahir ɗinki mara kunya ɗazu ba ke ce ki ka badani acikin mutane ba wai ƙwalliyata bata yi ba,tunda ta inya mura ta yi ƙyau aini ba dole bane sai na yi”.
Ko ɗago kai baiyi ya kalleni ba na ce”Yaya Bilal sannu da dawowa”.na faɗi hakan bakina yana kakkarwa kamar zuciyata zata fito haka na keji saboda tsoron yaya Bilal.
A hankali ya tashi ya fita baice min ƙala ba,na kalli Kaka inji ko zata yi magana sai kuwa ta ce”soja na don Allah ka ɓoyemin tsaraba ta da ƙyau eh ka yi ƙyaun kai da baka zauna wannan ƴar baƙar ta cinye min ba”.
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza 3
-
Zuciya ta
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi
-
Aure da haihuwa
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya
-
Gangar Shedan
-
Angon mata biyu
-
A gidan mu take
-
Bafulatanar Rugga
-
Matar yaro
-
Mr Bello
-
Mijin Buzuwa
-
Gidan Uncle Complete
Powered by: www.mynovels.com.ng
Ko da yazo wucewa ta kusa dani wani ƙamshin turare me mayen ƙamshi ne ya tafi da numfashina na lumshe idanuwa na ina jin ƙara son Yaya Bilal har cikin ƙoƙon zuciyata.
Kaka ta ce”to wannan kallon da ki ke bin namiji dashi fa,kin san dai ko a ƙafa aka ɗaura ki bazai kalleki ba,don matar soja ta dabance ba irinki ja’ira ba.”
“haba Kaka tunda na shigo ki ke ta zagina gaskiya Kaka ki daina wannan abinda ki ke yi wallahi wannan abin ba dai dai bane,yanzu idan kina faɗar haka a kusa dashi ƙara jin haushina zaiyi kuma kinfi kowa sanin yadda ya tsaneni”.
Sai na faɗi hakan kamar zanyi kuka ta ce”Haba ƴar baƙa aike mijinki ma na dabanne wallahi don ke har kin fisu ƙwari ma da kuma hazaƙa,naga ƙwanan nan ma zaki yi saukar alqur’ani kinga kuwa kina da baiwa da yawa”.
ƴar dariya na yi na ƙwanta kan cinyarta ta ce”yau naga ta kaina Ni Fatima wannan ƙarfaffar yarinyar zata karyani kowa ya hutu,kinyi wa iyayenki guda 12 asara.Yar dariya na yi sannan na ce”gaskiya Kaka kin iya haihuwa yanzu har ƴaƴa 12 ki ka haifa a cikinki?gaskiya kin zazzagu”.
kamar kaka na jira sai kuwa ta ce”Hmm iyayenku ai su sunƙi zazzaguwar ita wancar yellow ɗin kamar ɗorawa ita ta haifawa malik yara biyar,ita kuma waccen sadakar yallan ta haifa mishi uku,ita kuma inya mura wato uwarki ta haifa masa huɗu,to duk sayi sa gama don ni dai babu ruwana ato aura zansa ka ya yi ƙwanan nan”.da mamaki na ke kallon kaka don ita daman haka zancen ta ya ke da kun fara abin arziƙi idan har bakayi da gaske ba zai kuma na tsiya.
Zumɓuro bakina na yi na tashi na tafi sai kuwa ta ce”wallahi kin zunɓurawa inyamura mai baki kamar na shantu,ato ke Allah ya dubeki da baki yi wannan shegen bakin ba kamar ƙofar gari.ta gyara zamanta tana cigaba da cin goronta.
Ranar ɗaurin aure da wuri muka shirya mu ƴan matan gidan duk anƙwan shadda fara mukayi,iyayenmu kuma skye blue,samari kuma arsh sukayi.
Wajen Kaka na shiga ina zuwa naga ta yi baƙi ɗakinta cike da mutane amman maza ma sunfi yawa wasu pan gidanmu wasu ba ƴan gidanmu ba.
Na gaishesu na kama hanya zan fita sai naji kaka na ce wa”ƙwaji shasha Salisu ba yanzu ka gama yimin ƙwatancenta ba?ka ce inya maka iso kana sonta kuma tazo kabarta ta fita,to wallahi ni babu ruwana gwara ma ku sasanta tun yanzu don wallahi na gaji da kallon ƴan matan gidannan yara sunkai talatin duk ƴan mata,wannan ma idan kana da hawan ruwa ai sai ya tashi”.
ni dai ranar kunya ta isheni azuciyata na ce kaka kenan ɗazu ta gama faɗar munyi kaɗan yanzu kuma ta ce wai munyi yawa,kaka kenan babu mai iya mata sai ita.
Shima wanda ta kira da Salisu ɗin kunya sosai ce ta kama sa,ya kama rufe fuska,ni kuwa ɗan satar kallonsa na yi sam wallahi baiyi min ba ni wallahi ko da ma ace ya yi min ni yaya Bilal na ke so.
Da sauri na yi hanyar sashensu Rashida sai ga Salisu ya biyo ni a baya yana yimin magana,ban iya wulaƙanta ɗan adam arayuwata don haka na juyo muna cikin gaisawa sai ga Yaya Bilal ya fito daga cikin sashensu ya yi bala’in yin ƙyau cikin shaddarsa ruwan arsh,ta zauna sosai a murɗaɗɗan jikinsa mai ƙyau da tsari,kaf gidanmu babu wanda ya yi fari da kuma ƙyau irin na Yaya Bilal shine ya yo asalin kakanmu,kuma Yaya Bilal yana kama da babanmu wato alhaji abdulmalik.
Ayanzu yaya Bilal soja ne yana a matsayin Admiral ana ce masa Admiral Bilal Mohd.in kiyarsa Admiral B.
Gaba ki ɗaya hankalina da nutsuwata duk yana kan Yaya Bilal,Salisu yana ta zuba surutunsa dai daga baya ya gane ce wa hankali na yana wani wajen ba wajensa,mamaki sosai ya ke ganin wanda na ke kalla tabbas idan baiyi ƙarya ba yasan wannan yaya na ne kuma yasan ɗa ne ga yayan mahaifina amman ya aka yi haka na ke ta kallonsa lallai aƙwai lauje cikin naɗi a wannan lamarin,don ruwa baya tsami banza sosai Salisu yaji haushin wannan lamarin ya juya ya tafi don shi tunda ya ke bai taɓa buɗe bakinsa bama ya ce,yana son wata ƴa mace ba sai akan Khairat amman ta wulaƙanta sa haka.
Anyi bidiri sosai aka saki kiɗa amman iya mata ne kawai ƴan uwan Mama suma sunyi na su al’adun na inyamurai,ashe abin ya zaunawa Kaka a ƙoƙon zuciya ta shige ɗaki ta fara kuka wiwi,ashe lokacin Kishiyar mama na ta ganta wato Hajiya Iklima ta biyo kaka don salon gulma tana tambayar kaka abinda ya faru,haba daman kaka na jiran ƙiris ta ƙara volume ɗin kukanta tana tirje tirje kamar ƴar yarinya ƙarama,ta ce wa mama iklima ta je ta kirawo mata malik da sauran ƳaƳanta.
Duka iyayenmu maza suna babban farlon gidan ana hira ta zumunci,sosai hankalinsu ya tashi maxa goma ɗinnan duk suka taho daman biyu ne mata ƴaƴan kaka goma maza,nan fa kaka ta shiga gaya musu wai tana ji lokacinda aka ce a ƙara volume tunda masifaffiya ta iso.
*Miss green ce*
ABIN CIKIN ƘWAI…!*_
📃Littafi na 1
By
*Ummu maher(Miss green)*
*GAWURTATTU 5*
———————–
*wattpad user name*
—————
*Arewa book user*
——————–
*Sirrinmu* manzon Allah (s.A.W) ya hanemu da gujewa mazajenmu a shimfiɗa yin hakan babban laifi ne kuma tsinuwar mala’iku za ta tabbata akanki. ——————————–
3 4
.. .Dukansu suka haɗa baki wajen ce wa “umma lafiya me ya faru?”.kukan ta ƙara fasawa tana ce wa”yanzu har lokacin wulaƙanta ni agidannan ya yi?gaskiya zan bar muku gidannan ku zauna ku da matanku tunda haka kuka zaɓa”.
dukansu shiru suka yi sai malik ne ya ce”Umma ki faɗa mana abinda ya faru,don mun shiga cikin duhu wallahi”.
“To matarka ce inya mura ita ce ta ɓata min rai,wai ga masifaffiya nan ta iso,don ubanta gidan inyamurai ne nan da za ta tara mana ƴan bariki suna muskuta ɗuwaiwaka kamar gidan maguxawa?to wallahi ni nagaji xan barmuku gidanku”.sai ta fashe da kuka sosai har da majina,Hajiya Iklima ta ce”kaka don Allah ki yi haƙuri ki daina kuka”sai kuwa kaka ta Juyo a fusace ta ce”indai na kuka ko?tunda ba uwarki ce taka kukan ba ai dole ki ce haka?ni tashi ma shi ki barni in yi magana da ƴaƴana bana son bare awajen.
wani malulun baƙin ciki ne ya cika zuciyar Hajiya iklima ta Kalli fuskar hajiya kaka ta harareta,ita ta rasa wacce irin mata ce ba ta ɗaukar zuga ko kaɗan,amman ta yi alƙawarin muddin tana raye sai ta haɗa Hajiya kaka da dukkanin surukanta ta zama ita ce ta gaban goshi.
Tashi ta yi ta fita tana mai ƙara jin haushin cin fuskar da Hajiya kaka ta yi mata,sai kuwa kaka ta ce”to as dai a fita don bana son ina shawara da ƴaƴa na a zo asakamin idanu irin na fulanin daji”.
wannan magana da kaka ta faɗa ba ƙaramin mugun haushi ya bawa Hajiya iklima ba,don tasan sarai da ita take don asalinta fulanin daji ce,don itama kafin ta bari a aurota ba ƙaramin gwagwarmaya aka sha ba.
“Umma insha Allsh daga yau Zulaihat ba xa ta ƙara yi miki wani abu da zai ɓata miki rai ba,yanzu ma ba sai anjima ba za ta baki haƙuri”,yana faɗar hakan ya yi saurin fita.
Usman autan Hajiya kaka ya ce”gaskiya umma ki daina yi wa wannan baiwar Allahm haka,gaskiya ba a ƙyauta mata wallahi saboda ita ba yaranmu ba ce sai kuma ace za abi a tsaneta”.
“ah lallai ƙanin Zulai ka ce kaima an jiƙa an baka,kamar yadda sukayi wa ɗan uwanka a da cen baya,yanzu kuwa Allah ya dawo min da hankalin ɗana jikinsa,yanzu muna nan da kai za kaga caccakar da zai yi musu shegu masu cin arziƙi,tunda suka zo ina kula dasu babu abinda suke sai dafa nama daga an sauke wancen a ɗora wannan,ɗana yana ta kawowa suna cinyewa”.
dukkansu shiru sukayi har Alhaji Aliyu wato babban ɗan ta don shima ba’a bar matarsa ba,don haka haƙuri kawai ya iya bawa Hajiya kaka yaja bakinsa ya yi shiru.
A ɗakinsa ta samesa yana kaiwa yana kawowa hannayensa ya rungumesu a baya,sallama ta yi ta samu waje ta zauna kanta a ƙasa sai ta ji ya ce cikin zafi”Yanzu Xulaihat abinda ki ka yi wa mahaifiyata ya yi miki daɗi kenan? ki tara ƴan uwanki suna zagar min mahaifiya ta to wallahi ba zan lamunta ba,kowa ya haɗa kayansa ya barmin gidana don ba zan lamunci cin fuskar kowaccenku akan mahaifiyata ba.
Muryarta na rawa zata yi magana da sauri ya ɗaga mata hannu ran tsohon soja ya tashi ya fita yabar mata ɗakin,ya koma wajen mahaifiyarsa ya cigaba da lallaɓa ta,don yana fatan ya gama da ita lafiya.
Kuka sosai ta yi awajen kafin ta tashi ta fita,tana tunanin ta yadda za ta gayawa ƴan uwanta wannan maganar garinsu da sai a yini a kusan ƙwana ana tafiya sannan sai da yamma ta yi sannan za a ce su koma da yamman nan ko kai amarya ba ayi ba sunga gida.
Ɗaki ta koma tasha kukanta sosai,a hankali na buɗe ƙofar ɗakin mahaifiyata halin dana ganta a ciku shine ya ƙara jagula min tuna nina,na ƙarasa kusa da ita hankalina atashe ganin fuskarta ta jiƙe sosai da hawaye cikin daburce wa na ce”Mama lafiya me ya faru da ke?”
Bata iya ce wa komai ba ta tashi ta fita,binta na yi da kallo ina hasashen abinda ya faru tabbas hajiya kaka ce ba wani ba,don tun ina ƙarama na sha kama mama tana kuka kuma ba kowa ne musababin kukanba sai hajiya kaka,sam bata san mama na ban san abinda ta yi mata ta tsaneta haka ba.nima bani da zaɓi daya wuce in fito daga ɗakin don haka na yo waje don ƙawayenmu duk sunci ƙwalliya don kai amarya,ina fitowa Rashida ta ce”lafiya naga fuskar mama duk ta canza?ko ke ce kika yi mata wani abin”.
“hmm Rashida ni kuwa me zanyi wa mama da za ta yi fushi dani haka?kawai dai kin san tsakaninta da hajiya kaka ina ganin wannan ne amman ba ni ba ce.”
“kin san Allah Khairat matar nab gaba ki ɗaya ta ishemu a gidannan,ni na rasa dalilin daya sa duk iyayenmu suke cikin gidannan kamar dole,ita kuma ba bari take a zauna lafiya ba,kullum sai faɗa ni wallahi matar nan ma na matsu ta margaya mu huta da jarabarta.
Saurin rufe mata baki na yi na ce”wallahi Rashida ki kiyayi wannan bakin na ki kinsan dai matar nan kakarmu ce,babu yadda zamuyi da ita suma iyayenmu haƙuri suke da ita,muma ya kamata muyi haƙurin ko?”
Iman da Salimat da suke juyo hirar da su Khairat suke sai kuwa suka ce”Hmm Rashida wallahi ki cigaba da maganarki kada ki biyewa wannan wacce bata san inda ya ke mata feeling ba,don haka ko muma wallahi mun tsaneta wallahi tunda bata san iyayenmu mu ma dole ne mu tsaneta”.
ni dai fitowa na yi babban hall ɗin da ake hidimar bikin abin mamaki duk babu ƴan uwan mama na awajen abin ya ɗaure min kai sosai,yanzu fa na gansu awajen amman har na nemesu ban gansu ba.
Aranar dangin mama na duka suka koma ba tare da sun tsaya sai washe garin ba,hankalina ya tashi sosai na fito na yi sashen hajiya kaka,tana zaune ita da wata ƙawarta Hajiya Inna,na gaisheta tana tsokana ta tana ce wa saura na mu muma,kunya ce ta rufeni sai kuwa na ji Hajiya kaka na ce wa”Hmm Hajiya Inna kema dai kya faɗa wallahi wataran idan na ga yaran nan suna shiga suna fice agidannan su kusan ashirin duk ƴan mata,sai in shiga ɗaki inyi ta kuka sai ta buɗe injirnta ta ce”kinga duk inda na yi ƙashin wuya saboda yarannan duk dun tsotseni wallahi”.
duk da ina cikin tashin hankali sai da na yi dariya sannan na ce”Hajiya kaka kina da masaniyar dangin mamana duk sun bar gidannan acikin wannan daren ko kai amaryar basu yi ba sunga gidan brother”.
“brozo na ce ungo ƴar nema. to sai me don sun bar gidan ai ni sauƙina ne don wallahi idan na fito naga waɗannan samudawan mutanen har zazzaɓi na ke wallahi don ni bana son ganin ire iren inya murai sam agidannan itama uwar taki darajarku take ci wallahi da tuni ta daɗe da barin gidannan”.
Da sauri Hajiya Inna ta kalleta ta ce”haba Ramatu ashe har yanzu baki manta da wannan abin ba?Har sun tara zuri’ah Da Ɗanki yanzu da aurensu ya kai shekara 30 Fa amman ai yakama ta a manta da komai tun sanda malik ya auro yarinyar nan shekararta 13 har yanzu da take kusan shekara 43,amman ace haryanzu ba a manta da komai ba?gaskiya bai kamata ba Ramatu ki sani kema fa ɗiyanki suna gidan miji fa?bakya tsoron ayi musu haka?don Allah Hajiya Ramatu wannan abin ya wuce in banda yarinyar nan tana da haƙuri ne da irin ƴaƴan yanzu ne da babu abinda zaisa ba zasu yi miki rashin kunya ba,don kin zagar mata uwa a gabanta.
Har hawaye ya fara wanke min fuskata na tashi na fita daga ɗakin,wai ita hajiya kaka me take so ne da mamana?wacce irin tsana ce haka”.
ji na yi kamar na buge da abu da sauri na juyo saboda buguwar da goshina na ce”wash”.
sosai gabana ya faɗi ganin Yaya Bilal,da sauri na take xan gudu ya janyo bayan rigata tas tas ya kifamin maruka har biyu,na dafe ƙuncina hawaye na ƙara fitowa a idanuwa na ya ce”stupid girl kawai ke bakya kallon gabanku ne da zaki bugeni?to wannan shine last warning matuƙar na biyo hanya to ki kada ki biyo don na tsani kallon wannan dirty face ɗin ta ki,don haka ki kiyaye.”
maimakon ya bani haushi sai ma ya ƙara burgeni sosai,abin tausayi wato shi so hana ganin laifi.
Ƙamshin tureransa ya ƙi barin wajen sai da na ɓata minti kusan talatin sannan na tashi na tafi,wajen daya mareni ɗin na shafa hannayensa duk sun fito a kumatuna,ina ta shafa wajen maimakon inji haushi a’ah daɗin marin ma naji don ko babu komai ko madubi na k
Da sauri Hajiya Inna ta kalleta ta ce”haba Ramatu ashe har yanzu baki manta da wannan abin ba?Har sun tara zuri’ah Da Ɗanki yanzu da aurensu ya kai shekara 30 Fa amman ai yakama ta a manta da komai tun sanda malik ya auro yarinyar nan shekararta 13 har yanzu da take kusan shekara 43,amman ace haryanzu ba a manta da komai ba?gaskiya bai kamata ba Ramatu ki sani kema fa ɗiyanki suna gidan miji fa?bakya tsoron ayi musu haka?don Allah Hajiya Ramatu wannan abin ya wuce in banda yarinyar nan tana da haƙuri ne da irin ƴaƴan yanzu ne da babu abinda zaisa ba zasu yi miki rashin kunya ba,don kin zagar mata uwa a gabanta.
Har hawaye ya fara wanke min fuskata na tashi na fita daga ɗakin,wai ita hajiya kaka me take so ne da mamana?wacce irin tsana ce haka”.
ji na yi kamar na buge da abu da sauri na juyo saboda buguwar da goshina na ce”wash”.
sosai gabana ya faɗi ganin Yaya Bilal,da sauri na take xan gudu ya janyo bayan rigata tas tas ya kifamin maruka har biyu,na dafe ƙuncina hawaye na ƙara fitowa a idanuwa na ya ce”stupid girl kawai ke bakya kallon gabanku ne da zaki bugeni?to wannan shine last warning matuƙar na biyo hanya to ki kada ki biyo don na tsani kallon wannan dirty face ɗin ta ki,don haka ki kiyaye.”
maimakon ya bani haushi sai ma ya ƙara burgeni sosai,abin tausayi wato shi so hana ganin laifi.
Ƙamshin tureransa ya ƙi barin wajen sai da na ɓata minti kusan talatin sannan na tashi na tafi,wajen daya mareni ɗin na shafa hannayensa duk sun fito a kumatuna,ina ta shafa wajen maimakon inji haushi a’ah daɗin marin ma naji don ko babu komai ko madubi na duba zan ga tafin hannayensa a kumatuna.
Ban samu kai amarya ba don har sun tafi,sashen Anty ƙarama na je matar baba usman ƙaramin ƙaninsu babanmu.
Turaren wuta ta kunna a burner mai shegen ƙamshi ta kalleni da fara’arta ta ce”ah wata sabon ganin yaushe rabonda na ganki a sashennan har na manta?”
Ɗan murmushi na yi na ce,”to maman arman gani na zo”.da mamaki ta kalli kuncina ta ce”ikon Allah ke kuma Khairat wani mugunne ya mareki haka?”.
ɗan shafa wajen na yi na ce”am daman faɗuwa na yi ɗazu”.
“ƙarya ki ke wallahi Khairat ba faɗuwa ki ka yi ba ki faɗi gaskiya dai?wannsn marine ga yatsu biyu biyar nan sun fito raɗa-raɗa.
Hawaye ne ya fara fitomin na saka tafin hannuna na rufe don kada ta gani,janyo ni ta yi ta rungume ni sannan ta ce”ki faɗa min gaskiya Khairat nasanki da haƙuri da kawaici waye ya mareki haka?”.
ban sanda na ce mata ba”maman arman yaya Bilak ne ya mareni waidon na biyo hanyar da ya ke”.sai na fashe da kuka don ban san abinda yasa Yaya Bilal ya tsaneni ba”.?
“caɓɓi jan lallai yaron nan ba shida mutunci yanzu shi ne ya yi miki wannsn marin na cin kashi da wulaƙanci.? Da sauri na riƙe hannayenta na ce”don Allah maman Ammar kada ki faɗawa kowa wannan maganar wallahi ina sonshi bana son tun yanzu ya ce ina haɗasa faɗa da ƴan uwa.
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
Yayi kyau sosai