
Abinda ka shuka Daga Prof Malumfashi Ibrahim
Tag: ABIN DA KA SHUKA (1)
Daga Alkalamin Farfesa Malumfashi Ibrahim
Wurin da nake zaune, wuri ne da ban taɓa tunanin zan zauna a wurin ba. Wuri ne da ban taɓa tsammanin cewa wata ran zan kasance a cikin irin wannan hali ba. Dube ni cikin ragga, cikin mummunar kama, cikin mutanen da a lokacin da nake cikin ganiyata, in an ce su taka inda nake zaune, sun gwammace a kai su gidan kaso. Amma ga shi yau ni ne maƙwabcinsu na kusa da kusa.
A koyaushe na dubi inda nake zaune da abin da ya kawo ni wurin, sai in ji maƙoƙona ya gwame tamkar an sanya mani goruba biyu da ƙarfi a cikin maƙogoron. Ni ne yanzu cikin gidan maza tare da riƙaƙƙun ‘yan fashi da waƙanda aka yanke wa hukuncin kisa. Ni ma ga ni ina jiran alƙali ya yanke mani hukuncin da ya dace da ni, ko dai a sake ni ko a kashe.
Ehhh a kashe ni, saboda wai na yi kisan kai, amma sai na ɗauka cewa, ni ai adalci ne na yi ba akasin haka ba. Me ya sa za a yanke mani hukuncin da bai dace da ni ba. Me ya sa ?
Bugun da aka aiko mani da shi a tsakankanin ƙafafuna shi ne ya dawo da ni cikin hayyacina. Ban san lokacin da na yi zambur, na rarrafa zuwa wata kwana da ke cikin ɗakin da muke kulle ba. Na ɗaga kai sama ina mamakin wannan shuri da aka yi mani.
A daidai wannan lokaci ne na ga Masta, haka dai na ji suna kiran sa, ya sake tsayawa a gabana tamkar sojan da ya kada abokin hamayya, yana ta zazzare idanu kamar wanda zai cinye ni ɗanye. Ya sa ƙafafu ya shiga shuri na tamkar Okocha da tamola. In na yi nan, ya bi ni, in na yi can, ya sake bi na, tun ina kauce wa, har na gaji na laƙume a can ƙuryar ɗakin. Ya ko shiga shirga man ƙafarsa kamar wanda aka yo wa wahayi, sai da ya ga cewa ban iya komi sa’annan ya daka man tsaya.
Ni dai na ɗauka cewa na isa lahira tun da daɗewa, domin kuwa na yi zaton cewa walakiri ne ya yi man tsawa. Can sai na ji ya ce da ni, ‘ba za ka ba mu labarinka ba, ba za ka gaya mana abin da ya kawo ka gidan maza ba?’ A nan ne na gane cewa ashe dai a duniya nake, domin ban taɓa jin inda aka ce walakiri da Hausa zai yi magana da mu ba a ranar lahira.
Zafin taka ne da tsawar da yake man ta sa dole na soma tunanin yadda zan bayyana musu irin halin da nake ciki da irin abin da ya kawo ni wannan matsayi. Da na ga ya taso man afujajan sai na ɗaga hannayena sama ina roƙonsa da ya yi man rai, zan magantu. Ya ja da baya ya sami wani tsohon bokiti da muke fitsari a ciki, ya halbe shi zuwa wani ɓangaren ɗakin, aka tare, aka shirya masa, ya kama wuri ya hakimce.
Na dube shi, na sake dubar sauran abokan zaman namu, na yi ajiyar zuciya, kana na shiga ba su labarin abin da zan iya tunawa.
Na ce da ‘yan jarun ɗin da muke tare da su cikin murya mai ban tausayi da kyarma. ‘Labarin da za ku ji, labarinsu ne, labarina ne, labarinku ne, labarin duk wani mai hankali ne. A kullum na tuna da labarin nan sai na ji cewa wai shin ma mene ne amfanin rayuwa? Mene ne amfanin zuwana duniya tun da kuwa zuwan zomo na yi, na shigo da gudu, zan fice da gudu. Ba wai nufina ba ne na ce ban ƙaru da zuwa wannan duniya ba, ko kaɗan.
Allah ya yi man dukiya gwargwado, na kuma kai matakin shugabanci a cikin gwamnati a fadar Shugaban Ƙasa, kafin na yi ritaya. Allah ya yi mani albarkar ‘ya’ya, domin kuwa ya ba ni har shidda, ‘yan mata. Su ne kuwa matsalata, su ne suka sa man kansar zuciya da baƙin cikin da har abada ban taɓa mantawa da shi.
Wallahi ba wai ina baƙin cikin da Allah ya ba ni ‘ya’ya mata ba ne, maimakon maza, ko kaɗan, sai dai kullum na tuna da labarinsu, sai in ji cewa ai saboda su ne nake cikin wannan kakabi da tunani, kila da maza ne da ban yi wannan juyayi ba. To amma da yake ba mazan ba ne, matan ne, sai na fahimci cewa labari ne da ba zan iya kimshe shi a cikin ƙirjina ba, domin kuwa shaƙarar da yake yi man ko da igiyar sarƙafe mutumin da ake so kashewa ce aka lanƙaya man, to sai haka.
Na yi ajiyar zuciya, na sake dubar su, na ci gaba da zancena.
ABIN DA KA SHUKA (2)
Daga Prof Malumfashi Ibrahim
Ni ma na ruga in ga ko zan cimma masa da gudu, ina, ya sheƙa, ya shige wata kwana, ga shi cikin duhu, dole ta sa na dawo gida da ɓacin rai.
Ita kuwa ɗiyar tawa ko da na shiga gida tana wurin wanka, na jira ta fito, ina cika ina batsewa. Ta fito, na kalle ta, ta kalle ni, na kasa cewa uffan, ta sa kai ta wuce ɗaki ta yi kwanciyar ta.
A wannan dare na kasa cewa da kowa uffan, domin kuwa ai an gama ruguza mani irlina. Ina amfanin tsaron da nake ta yi shekara da shekaru. Ina amfanin fursunan da na sa waɗannan yara ciki, in har a cikin gidana za a ci mini mutunci!
Ina cikin wannan turaddadi ne rannan na ji Dije, ɗiyata ce ‘yar shekara 21 tana gaya wa yarta Maimuna, yadda malaminsu na Kemistire ke ba ta ajiyar makullin Laboratore a lokacin tana makarantar Sakandare ta kwana, ta ajiye, sai ta bari kowa bai ganin ta, sai ta shiga Laboratare ta kulle, shi kuma malamin sai ya faki idon kowa, ya lallaɓa zuwa inda take, ya ƙwanƙwasa, ta buɗe, su kulle, su yi ta gwaje-gwajen jin dadi.
Yadda take bayyana wa ‘yar uwar yadda suke sheƙe ayar ne ya tayar mani da hankali. Da suka shiga shewa kuma da buga hannaye, sai na ji na ƙume har cikin zuci. Na shiga tunani, ashe ni tsaron banza nake, tuni an gama nome man gonar da nake dako.
Amma abin da ya fi ban haushi da takaici shi ne abin da ya faru shekarar ta da ta wuce, wata rana da yamma, wanda kuma shi ne ya kawo ni nan wurinku, ba don na so ba. Ga yadda abin ya faru.
Wannan ƙaddararrar rana, na dawo daga masallaci ne da la’asar, na iske Jamila, ɗiyata ce ‘yar shekara tara da haihuwa, almajirin da ke zuwa yi wa matana wanke-wanke ya ratsa ta, jini na kwarara, tana kuka, yana ihu, ganin cewa ga ni, ga shi. Da na damuƙi wuyar rigarsa, na fyaɗa shi a jikin bangon zauren, sai dai na ji ƙum, in duba haka kwanya ta barbazu ko’ina, almajirin nan yana kwance kamar tukunyar ƙasar da ta faɗo daga sama, ya karairaye, tuni ya shuri birji.
Kukan Jamila ne ya dawo da ni cikin hayyacina, na dube ta, na ga yadda jini ke zuba daga matuncinta, sai na tabbatar da cewa ya kassara ta, kassarawa ta har abada. Ban san lokacin da na shiga tattaka sauran abin da ya rage ba na jikin wannan almajirin.
Ban tsaya na dubi fuskokinsu ba, amma da alama labarin ya ratsa su, da na ji ba su ce da ni komi ba, sai na ci gaba da labarina.
Na san dai mun isa caji ofis, sai karakainar zuwa kotu, daga can kuma sai nan inda nake tare da ku, sauran abubuwa kuwa ban san yadda aka yi ba, kuma ba su dame ni ba.
Dariyar da suka kwashe da ita, ita ce ta fi damuna, domin da alama sun ɗauka na taɓu ne, amma sai na yi biris da su, na koma cikin wani sabon tunani.
Yanzu in an yanke mani hukuncin kisa shi ke nan? To amma wannan daidai ne? Idan ba daidai ba ne to laifin wane ne? Nawa ko na ɗan almajiri? Sai daga baya ne na fahimci wani abu, ashe tsaron ‘ya mace ba shi ne magani ba! Ashe ni ban ma iya gadin ba. Ashe dai idan ka ci amanar wani, sai an ci taka!
Can sai na ji wata murya na ce da ni. ‘Amana!’ ‘Amana!’ ‘Amana!’ Wannan shi ne ya fi damuna. Can sai wata muryar daban da waccan da muke zance da ita ta ce da ni, ‘ka ɗauka za ka yi wa Allah wayo ne! Ka ɗauka cewa ƙoƙarinka ne zai kare ‘ya’yanka mata daga faɗawa tarkon maza! Ka manta cewa kai ma ka shiga gonar da ba taka ba! Wanda ya ratsa hurumin wani, me zai hana a ratsa nasa hurumin!
Wannan murya ta sake razana ni ƙwarai da gaske. Can kuma sai na ji wata muryar na faɗa cikin sauri. ‘Amana!’ ‘Amana!’ ‘Amana!’ ‘Cin Amana!’ Nan take sai na tuna da abubuwa biyu a rayuwata, na gan ni a lokacin da nake hedimastan firamaren ƙauyenmu, a lokacin da na kulle Hajara a ofis, na yi mata fyaɗe. Yarinya ce ‘yar shekara tara da haihuwa. Iyayenta suka nemi su tada ƙura, mahaifina ya rufe maganar da yake shi ne hakimin garinmu, dole ta sa iyayenta suka bar garin, saboda kunya.
Nan take sai na ji jikina ya fara tsima, na soma makyarkyata. Can kuma sai na gan ni kwance da Mariya, wata budurwata, a cikin falon mahaifinsu. Shi ma mutum ne kamar ni, mai tsananin kiwon ‘ya’yansa, wanda ya sa ni kuma na nemi sai na yaga masa rigar mutunci, a lokacin ina cikin gayar samartaka. Na kwanta da ita ne a cikin falonsa domin kawai in nuna masa bai isa ba. Na kuma tabbatar masa hakan, domin kuwa ya iske ni da ita, turmi da taɓarya a falonsa, ban damu ba, nan na bar shi yana ta ihu da kuka, ni kuwa ina dariya, na cimma burina.
Ashe ban sani ba da sauran rina a kaba. Ko kafin na gama wannan tunani, sai na ji wata muryar na ce da ni. ‘Cin amana!’ ‘Rikon amana!’ ‘Ramuwar gayya!’ ‘Tashin hankalin rayuwa!’ Haka dai abubuwa suka dinga yawo a cikin raina. Na tuna da ɗiyata Halima da Maigadi Mati, can kuma sai na ga hotona tare da Mariya. In sake dubawa kuma sai na ga ɗiyata Jamila da ɗan almajiri, sai kuma na gan ni tare da Hajara a cikin ofis, ina yi mata fyaɗe, tana kuka!
Nan take ni ma na shiga kuka. ‘Yan jarun suka sake fashewa da dariya, ganin ina rusa kuka tamkar yaro. Can sai muryar nan ta sake dawowa tana ce da ni, ‘maciyin amana’. Na sake fashewa da kuka mai tayar da hankali.
Dubawar da na yi haka, sai na gan ni gaban alƙali, na waiga haka cikin tsoro, sai na ji wata muryar ta ce da ni…Kama tadinu….
Mun kammala.
[16/10, 5:44 pm] +234 706 387 8558: ABIN DA .muke tare da su cikin murya mai ban tausayi da kyarma. ‘Labarin da za ku ji, labarinsu ne, labarina ne, labarinku ne, labarin duk wani mai hankali ne. A kullum na tuna da labarin nan sai na ji cewa wai shin ma mene ne amfanin rayuwa? Mene ne amfanin zuwana duniya tun da kuwa zuwan zomo na yi, na shigo da gudu, zan fice da gudu. Ba wai nufina ba ne na ce ban ƙaru da zuwa wannan duniya ba, ko kaɗan.
Allah ya yi man dukiya gwargwado, na kuma kai matakin shugabanci a cikin gwamnati a fadar Shugaban Ƙasa, kafin na yi ritaya. Allah ya yi mani albarkar ‘ya’ya, domin kuwa ya ba ni har shidda, ‘yan mata. Su ne kuwa matsalata, su ne suka sa man kansar zuciya da baƙin cikin da har abada ban taɓa mantawa da shi.
Wallahi ba wai ina baƙin cikin da Allah ya ba ni ‘ya’ya mata ba ne, maimakon maza, ko kaɗan, sai dai kullum na tuna da labarinsu, sai in ji cewa ai saboda su ne nake cikin wannan kakabi da tunani, kila da maza ne da ban yi wannan juyayi ba. To amma da yake ba mazan ba ne, matan ne, sai na fahimci cewa labari ne da ba zan iya kimshe shi a cikin ƙirjina ba, domin kuwa shaƙarar da yake yi man ko da igiyar sarƙafe mutumin da ake so kashewa ce aka lanƙaya man, to sai haka.
Na yi ajiyar zuciya, na sake dubar su, na ci gaba da zancena.
“Ni dai Allah ya sa mai tararrabar ‘ya’yana ne, ba na son wani namiji ya nemi isa gare su. Ban taɓa yarda da wani namiji ya kusance su ba, balle ya shige musu cikin rayuwa, ya lalata mani su. A kullum sai dai a kai su makarantar boko da Islamiyya a dawo da su. Idan aka yi hutu kuwa suna zaune gida tamkar masu fursuna.
Ba abin da na ƙi a ce wani ya taɓa matuncinsu, ba gaira ba dalili. Kullum fatata ita ce in kai su ɗakin mazajensu, sumul ƙalau. Ban san dalilin da ya sa nake cikin wannan damuwa ba, amma abu ne da yake tare da ni da daɗewa.
Amma da yake ta Allah sai ta kasance, duk da irin wannan tsaron nawa, rannan da misalin ƙarfe tara na dare, na ji ana ta nishi a bakin garejin gidana, an kuwa ɗauke wuta, haskawa da nake yi haka sai ga maigadina Mati, taushe da Halima ɗiyata, ‘yar shekara 18, ba su san ina wurin ba,suna ta al’adar nan ta zakara da kaza, ko kafin na dawo a husace ɗauke da takobi, shegen ya sauka daga kanta, ya ruga. Ni ma na ruga in ga ko zan cimma masa da gudu, ina, ya sheƙa, ya shige wata kwana, ga shi cikin duhu, dole ta sa na dawo gida da ɓacin rai.
Zan Ci Gaba
Leave a Reply