Abinda Umar Hashim Yace Game da Mutuwar Sani Garba SK

Abinda Umar Hashim Yace Game da Mutuwar Sani Garba SK

Tag: sani sk

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Umar Hashim ya wallafa wannan maganar ce a shafin sa na Facebook ga abinda yace:

Marigayi Sani Garka SK na daga cikin Jaruman fina-finan Hausa da ya jima ana mirginawa da shi, domin ya faro tun daga wasan dabe sannan ya ta6o Television kadan da kuma inda ya dauki mafi rinjayen lokaci wato Home video.

 

Bayan kwarewa da iyawa Sani yana daga cikin Jarumai ma su tarbiyyya wato Discipline wajan gudanar da sana’arsa ta film, misali, yana kiyaye lokacin zuwa aiki in an gayyace shi sannan bai cika korafin a yi maza a sallame shi a location ba kamar yadda wasu Jarumai kan yi musamman in sun ga sun sami daukaka, kazalika da wahala ya sami sa6ani da Daraktansa ko sauran Jarumai ‘yan’uwansa a location.

 

Sani ya sami kyakkyawar shaidar iya mu’amala da abokan Sana’a kwarai da gaske.

 

Ni a karan kaina babu abin da zan ce da rayuwar Sani SK sai San barka domin sun taso a wannan masana’anta tare da su Alasan Kwalle kuma suna daukata a matsayin yayansu a rayuwa.

 

 

 

 

Umar Hashim Na Murnar Cika Shekaru 13 Da Aurensa

Zan iya tunawa wata shekara mun kai ziyara Junhuriyar Niger domin gabatar da wasa a babban dakin taro na kasar wato Pale de congre, inda aka sami sa6ani wajan biyanmu hakkinmu, dan haka ba wai su Ali Nuhu da Halisa da Biba da sauran matasan wancan lokacin ba, a, a hatta Ni kaina duka mun rikice muna neman rigima da wadanda suka gayyace mu, amma Sani SK kadai Allah ya sanyawa nutsuwa inda ya dinga kai mari yana kai gwauro sai da ya ga ya dinke 6arakar.

See also  Mansura Isah Kammala Iddah Ga Yanda Aurenta na Biyu Zai kasance

 

Ta fuskar Sana’a kuwa SK kwararre ne kamar yadda kowa ya shaida, ya iya action film musamman a shekarun baya, sannan ya iya comedy bayan kwarewarsa a sauran 6angarori.

 

Na tabbata kyakkyawan halin Sani ne ya sanya abokan Sana’a suka dinga dawainiyar kula da lafiyarsa a lokacin da ya shiga rashin lafiya.

 

Tsohon Malamin makarantar Islamiyya Kuma Sha’iri wanda ya yi fice wajan kasidar yabon Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam. Allah ya jikansa ya gafarta masa.

 

MALAM IBRAHIM MANDAWARI (MAI UNGUWA)

 

ALLAH YAGAFARTA MAKA SANI

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top