MOMEE GOMBE
Maimuna Abubakar (An haife ta a 28 Yuni shekarar 1997). wadda aka fi sani da Momee Gombe ta kasance fitacciyar jarumar fim kuma ‘yar rawa a masana’antar shirya finai-finai ta Kannywood. Haifaffiyar jihar Gombe ce da ke shiyyar arewa maso gabashin Nijeriya.
Tarihin Rayuwa
Momee Gombe ta yi daukacin rayuwarta ne a garin Gombe. Ta yi karatunta na firamare da sakandaire duk a can.
Aiki/Sana’a
Momee Gombe jarumar fina-finai ce kuma tana daya daga jaruman da tauraronsu ke haskawa a yanzu kana kuma suke bada gudumawa a fannonin nishadi ta hanyoyi da dama.
Daukaka
Jarumar takasance tanada ra’ayin Zama Jaruma tun tana yar’karama amma bata samu cimma hakanba saboda auren datayi dawuri. Bayan fitowarta daga gidan aurene ta shiga harkan fim da taimakon shirya finafinan nan Auwal Mu’azu dakuma fitacce matashin mawakinnan hamisu Breaker.
Tafara sanuwa a video Waka da ake daurawa a manhajar YouTube. Inda jarumar tahau video Waka da jarumai irinsu Adam a Zango, Hamisu Breaker, Garzali Miko, Kabiru Kb International, Musbahu anfara dasauransu.
Sannan takara sanuwa a Shirin datayi kamarsu “kishin mata” da “asalin kauna” dakuma rawar data taka a Shiri mai suna “Ango” Tareda fittaccen Jarumin nan Adam A Zango.
Jarumar Kara matukar sanuwa a video wakar “Jarumar mata” sabida yaduwa da wakar tayi a yankin Afrika.
Karanta tarihin: Hafsat Idris
Lambobin Yabo
Maimuna Abubakar ta Ambaci Jarumi Adam a Zango a matsayin Mai Shugabanta Kuma Mai bata shawara Gameda abinda yadace, Takuma ambaci sunayen mutane dadama inda tace sun nada gudumawa Kuma sun taka rawa wajen daukakarta ciki harda Hamisu Breaker, Sunusi Oscar 442, Auwal Mu’azu dakuma Adam a Zango daga karshe Kuma tace “tanada burin Zama Babbar Jaruma a masana’antar ” Kuma “tana da ra’ayin taimakawa marayu da marasa
Momee Gombe kamarde saura Jaruma takasance tanada shafuka a Instagram, Twitter dakuma Facebook dakuma mabiya dadama.
Slm ina miki fatan alkhairi tarida samun cikar burinki na alkhairi
Allah ya kare jaruman knewood