Abraham Hausa Novel
Tag: ABRAHAM
🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇
*First edition*
#NoorEemaan
*WATTPAD*
@NoorEemaan
Am back again🚴♀️ it has been a while now….
All characters and lifestyle in this story are all drawn from my imagination, any resemblance of story should be considered as a coincidence!
⚠Caution ⚠️
Wanna liittafin Hakkin mallakan NoorEemaan ne! Ban yarda a juya min novel ta kowacce siga ba, idan kunne yaji…
The writer of
Rayuwar faheemah
Mijin ammina ne sila
Kyautar koda
Papi ne and now 👇
ABRAHAM…
*Wanna book din na so yin shi a matsayin paid book, amma saboda yanda masoyana suke ta tambayar :Noor yaushe zaki fara mana sabon novel ya sanya zan sakar muku shi a free domin Jin dadinku my fans, comment dinku kadai nake bukata, sannan wattpad fans dina kada ku manta da following dina sannan voting nagode…
*( bari na Baku wani takaitaccen labari game da book din ABRAHAM dazan fara in sha Allah…*
*Few days back ina cikin keke napep zuwa gidan mu, kwatsam naji labarin yazo brain dina, it’s funny RIGHT? Yeah it’s! Ni kadaina murmushi na saki domin abin yazo min a bazata, buh trust me guys zaku ji dadin shi fiye da zaton ku, ku dai ku rikitani da comments dinku kana kuyi following dina a wattpad.)*
_In sha Allah daga yanzu har zuwa lokacin dazan ajiye alkalamina wanna emojis din grapes da strawberry (🍇🍓) zan dinga amfani dashi a dukkanin novel dina kamar yadda kuka gani a sama, Dan haka masoya matukar kuka gan wanna emojis din 🍇🍓 toh tambarin novel dina ne_
*Note*
_Wanna shine second to the last novel dina Dana Yi, so ina ƙara reposting ne, ba sabo bane_
https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din
In the name of Allah, most gracious most merciful
Chapter 1-2
IMO OWEERI STATE NIGERIA
_WORDBANK ESTATE_
Unguwar wordbank na daya daga cikin unguwanin masu hannu da shuni a jihar imo. Wani Had’add’en gidane mai sassa daban-daban na hango, Ana wa gidan lakabi da ABRAHAM MANSION, sannan shine gida mafi kyau, haduwa, hadi da girma a Unguwar wordbank din gabadaya, cikin wani sashe na gidan na nufa….
Wata farar matashiya ce tallafe da katon cikin ta wanda yayi girma sosai, fridge ta nufa domin dauko Eva table water sakamakon kishirwan da take ji, balle murfin ruwan tayi ta fara sha, lumshe ido tayi kewar Mijin ta na nukurkusanta, Sosai take bukatar ya dawo, sai da ta shanye duka ruwan kana ta cilla Goran cikin dustbin, hanyar part din su ta nufa domin dauko wayar ta saboda ta yi Kiran mijinta, mutum mafi soyuwa a duniyar ta gabadaya baya ga iyayen ta, miskilancin sa kadai da ta tuno ya sata sakin murmurshi, she loves everything about him…
Har ta gifta sitting room ta dawo da baya sakamakon muryar mummy(madam Gloria) dake tashi, wani mugun murdawa dan cikinta yayi sakamakon abinda kunnuwanta suka jiyo mata…
“Sarah (babbar aminiyar madam Gloria) bazan taba bari wanna damar ta wuce ni ba, dole ne na salwantar da Nonye da Abinda ke cikinta, wanna aikin kuma zamu yi shi cikin daren yau kafin dan taurin ran ya dawo, domin matukar ya dawo komai ya lalace min , kin san cewa yana da wayo sosai basai na gayamiki ba, Dan haka ki shirya karfen biyun dare zamu aikata lahira, sannan na fasa ihun kukan mutuwar ta da safe, bayan na gama da ita, sannan a hankali zan aika Abraham lahira shi ma, daga nan dukiyar ABRAHAM ya dawo mallakina kaf, abinda na dade ina buri Kenan” madam Gloria ta fada da yaran igbo tana sakin dariyar zallan mugunta.
Nonye dake tsaye a bakin kofa ta saka dukkanin hannayenta ta rufe bakinta, sakamakon kukan dake k’ok’arin kufce mata, sosai zallan al’ajabi ya kamata, da mutum ne ya gayamata cewa madam Gloria nada irin wanna mugun halin sai inda karfin ta ya kare, amma gashi da kunnuwanta taji, azahiri ba wai a duniyar mafarki ba…
Kokarin barin bakin kofar take domin wani mugun duhu ke kokarin ratsa idanun ta, burinta ta isa dakinta domin Kiran Abraham ko da ita da Dan cikin ta basu rayu ba, amma zata so Abraham ya san da wacce yake zama, sai dai tana daga kafa daya tayi luuuuu zata fadi, sak’amak’on haka kofar ta girgiza, a kuma daidai lokacin ne madam Gloria da aminiyar ta Sarah suka kai idanun sa ga kofar a firgice, domin basa son kowa ya San da nufin su har su aiwatar dashi
Ta bangaren Nonye kuwa zaro fararren madaidaitan idanun ta tayi cikin tsananin tsoro da rudewa, domin Sam bata so su san cewa tana labe, hakan yasa ta aro jarumtar ta tsaya kan kafafunta, maimakon ta nufi dakinta sai tayi hanyar waje domin yafi mata sauki bacewa ganinsu…
tana fita waje su madam Gloria na bud’e kofar sai dai wayam basu ga alamun mutum ba…
Kallon juna suka yi, kana suka sake janye idanun su, cikin rashin yarda madam Gloria tace” kawata Sarah anya babu wanda ya mana labe kuwa“ ta tambayi Sarah da yaran igbo.
“abinda nake hasashe Kenan” Sarah ta amsawa madam Gloria
“tabbas akwai wanda ya mana labe, masu aiki basa shigowa nan sai idan za su yi aiki ko shirya dining table, shiyasa na zabi mu yi maganar a nan, amma zo muje in gani …” madam Gloria ta fada tana nufar part dinsu Nonye….
Sai dai sama da kasa ta duba babu Nonye babu alamar ta, sosai hankalinta ya tashi kana zarginta ya tabatta.
A haukace ta nufi compound din gidan ta tambayi mai gadi ya sanar da ita cewa babu jimawa yaga ta fita…
Ai bata jira mai gadi ya karasa jawabin sa ba ta koma ciki ta dauko key din mota ta fito, kana ita da Anty Sarah suka fada ciki ta bawa motar wuta suka bar gidan a guje, shi dai mai gadi da kallo ya bisu kana ya tabe baki ya koma bakin aikin sa….
Bayan sun fito babban titi ta latsa wani number, bayan seconds biyar kacal aka daga… “hello Emma mu hadu a junction yanzu”
Daga dayan bangaren saurayin da aka kira da Emma ya amsa hadi da kashe wayar, wanda kallo daya mutum zai masa ya fahimci cewa shi din tantiri ne…
mintuna goma kadai suka kawo Emma Junction din, kasancewar ya San motar ta hakan yasa kai tsaye ya shige gidan Baya motar, yace “madam Gloria meye labari ne”? Ya tambaya cike da nuna shi din Jan wuya ne”
“babu labari mai dadi Emma, sanin kanka ne cewa duk sanda na kira ka aiki za ka min, ba kuma yau ka fara min aiki ba, in fact babu lokacin bayani” ta karasa tana fisgar motar da gudu, tayi driving mai nisa kana ta hango wata kamar Nonye tana sauri tamkar ba mai ciki ba, gudu ta kara har ta cimmata…
Nonye dake a rude ta waigo Jin karan mota a bayanta saidai wadanda ta hango ya sanya hantar ta kadawa, hakan kuma yasa Dan cikin ta wani tsalle
“get in the car” madam Gloria ta fada a kausashe hakan kuma shine karon farko data fara bayyana wa Nonye asalin kalar ta da tarin tsanar da take mata, domin dukkanin abinda ya shafi ABRAHAM tana adawa dashi
Sosai hankalin Nonye ya tashi, gashi shida na yamma ta kusa, ba tare da ta tsaya wani tunani ba ta fada dajin dake gefenta ta fara hudu, tana fatan ta tsira daga kaid’in madam Gloria.
Da gudu Emma da madam Gloria suka rufa mata yayinda anty Sarah ta shige motar, hakan nan take Jin wani yanayi a tare da ita mai kama da tausayi…
Sosai Nonye ke gudu tana kuka, yayinda su madam Gloria ke bin ta a baya a kokarin su na kamota, sun yi gudu mai nisan gaske har karfin Nonye ya fara karewa hakan yasa ta fadi ruf da ciki yayinda ta buge kafar ta a katon dutsen dake gefen ta, zafin daya ishe ta ne ya sanya ta saki karan azaba, kokarin mikewa take amma ta kasa sakamakon nauyin da cikin ta yayi, gashi ya dunkule waje daya, tana cikin wanna halin ne su madam Gloria suka cimmata…
Cikin kuka mai matuk’ar ban tausayi tace “please don’t kill me” (na roke ku Karku kashe ni)
Daf da fuskar ta madam Gloria ta karasa kana cikin tsantsar mugunta tace “don’t worry Nonye darling bazan kashe ki a nan, saboda haka relax ok” ta karasa tana shafa gefen fuskar ta cikin mugunta kana ta fashe da dariya, can ta dinke fuskar ta ta kalli Emma tace “daukota mu bar nan kafin duhun ya kara yawa” tamkar kayan wanki haka Emma ya sabe ta a kafada ko tausayi babu, Nonye kuwa shiru tayi sai hawayen dake zuba a fuskar ta, karfin ta ya Kare gabadaya, a halin yanzu tafi tausayin dan cikinta….
Bayan sun fito titi Emma ya wurga ta a bayan mota , madam Gloria kuwa ta mika mishi bandir din yan dubu daya ya tafi cike da mata kirari….
*2:00am*
Ko ina da haske a gidan tamkar rana,
tsaye madam Gloria take a kan Nonye, macece mai matsakaicin tsaho hadi da kiba, fara ce irin farin inyamurai nan (igbo). Ta sha kitson twisting kananu, tana sanye da short skirt hadi da farar singlet Wanda hakan ya taimaka kwarai wurin bayyana katon tumbin ta. Ido ta Kurawa Nonye da a shekaru bazata wuce shekara ashirin da shida zuwa da bakwai ba, sosai Nonye ke cikin mayuwancin hali da katon cikinta dan wata Tara da kwana biyar, juyi take tana zub da kwalla masu zafin gaske saboda azaban da take fama dashi, magana takeson yi amma ta kasa furta ko da kalma daya ce, sai bakin ta dake motsi, ga cikin sai wani motsi hadi da juyi yake sosai, wanda hakan ke nuni da cewa dan cikin ya galabaita yana bukatar shakar iskar duniyar mu.
Murmushin mugunta madam Gloria ta saki, ganin hakkan ta yana daf da cimma ruwa, Anty sarah dake gefenta ta share kwallar tausayin Nonye, ta sani cewa duk muguntar ta, bazata iya kallon mace mai tsahon ciki a halin nakuda ba tare da ta taimaka ko sausauta mata ba, kusan awa goma Kenan da Nonye ta soma nakuda saboda tsananin tsoron da firgici, Sannan bata isa ta hana madam Gloria aikata komai ba, duk da kasancewar Anty Sarah kawa ga Madam Gloria, amma a gidan take zama permanent, tana kuma a matsayin kukun su ce, wanda madam Gloria ta tsara hakan ne gudun kada ABRAHAM ya fahimci wani Abu a tsakaninsu, sosai Anty Sarah ke Rayuwa a gidan tamkar a gidan su. sannan ta San cewa idan ta nuna wani yanayi na tausayi ga Nonye dake kwance, ba shakka madam Gloria xata iya mata komai, domin tasan cewa anty Sarah ta gama sanin dukkanin sirrin ta….
Da murnushi mugunta kan fuskar madam Gloria ta juyo ga anty Sarah, k’ank’ance ido tayi, kana cikin son gasgata abinda take karantowa a fuskar anty Sarah tace ” SARAH! ba dai tausayi nake gani shimfud’e a fuskaar ki ba, yau she kika fara Tausayi? Domin tun zamanin yarintar mu ke din ba mai Tausayi bace”(ta tambayeta da yaran igbo)
Saurin sanja fuska Anty Sarah tayi, wanda da a ce madam Gloria ta lura da ta gano abinda takeson gani din. “ko daya bana tausaya mata, ranar da muka dade muna jira ce fa tazo, haba kawata sai kace baki sanin ba ” Anty sarah ta fada tana sauke boyayyen ajiyar zuciya, tana fatan kada madam gloria ta gano ta…
Murmushin jin dadin madam gloria ta saki, mayar da kallon ta tayi ga Nonye, ta kara galabaita sosai gwanin tausayi ga cikin daya tsananta motsin da yake, gashi tana son magana amma ta kasa…
Babu zato, babu tsammani madam gloria ta dauki pillow ta shiga dannawa a fuskar Nonye da dukkanin karfin ta, shure_shure Nonye ta dinga yi da kafafun ta saboda sosai madam gloria ke cigaba da danna pillow a kokarinta na kashe Nonye, Anty sarah ta dauke fuskarta, karon farko da ta ji wani mugun tausayin Nonye, sannan tayi nadaman biyewa kawarta…
A yau taji tana tsanar halayenta, domin har da gurbataciyyar shawarar ta a kisan da madam gloria ke kokarin yi wa Nonye
miye laifin nonye? yarinya mai kirki da faram faram da jama’a….
Sai da Nonye ta daina motsi kana madam Gloria ta d’auke pillow’n daga fuskar ta, sai dai me duk da cewa Nonye ta mutu, numfashi ya bar gangan jikin ta, amma sosai dan cikinta ke motsi….
Salon na daban ne,
Comment dinku kadai zai sa na cigaba da ABRAHAM…
Noor Eemaan🦋
I’m selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I’m
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
Sunday 19 December
8:46pm
[03/10, 9:58 pm] +234 816 362 6370: 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇
ABRAHAM
🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇
*First edition*
*WATTPAD*
@NoorEemaan
ELEGANT ONLINE WRITER’S ✍️📚
https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din
Chapter 3-4
(Not Edited)
Sosai tsoro ya bayyana a fuskar madam Gloria, domin abu ne wanda bata taba gani ko ji ba, ta yaya dan cikin Nonye ke motsi bayan ta mutu? Sosai murnan cikar burinta ya ragu
Mai da kallon ta tayi ga Anty Sarah data yi mutuwar tsaye, sosai nadama da tsoron Allah ya rufe ta, domin abinda ke faruwa yanzu ikon Allah ne mai yin yanda yaso.
“Sarah kina ganin abinda nake gani kuwa ko mafarki nake yi?” madam Gloria ta fada a rude, tana jijiga anty Sarah
“ba mafarki kike yi ba kawata, da gaske ne, amma ga shawara daya” ta fada tana satar kallon madam Gloria, fatan ta ta amince da tunanin daya zo zuciyar ta yanzu, domin ta hakan ne kadai zata samu sasaucin tsantsar mugunta da suka yiwa Nonye.
“meye shawarar ki Sarah fadi ina jinki” madam Gloria ta fada a kage.
“mezai hana mu fita da ita ta kofar baya inda ba security sai ki kira Emma ya hayo mota daga nan mu kai ta asibiti ayi operation kana a ciro dan cikin kafin gari ya waye mun dawo, idan ba haka ba matukar mutane suka Lura da dan cikin Nonye na motsi za a samu matsala domin abinda bakya so ne zai faru, ma’ana Dan Abraham zai rayu” anty Sarah ta fada tana fatan kawarta ta amince.
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza 3
-
Zuciya ta
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi
-
Aure da haihuwa
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya
-
Gangar Shedan
-
Angon mata biyu
-
A gidan mu take
-
Bafulatanar Rugga
-
Matar yaro
-
Mr Bello
-
Mijin Buzuwa
-
Gidan Uncle Complete
Powered by: www.mynovels.com.ng
Jinjina kai madam Gloria ke yi cikin gamsuwa domin ta yarda da shawaran Kawarta dari bisa dari, babu bata lokaci ta kira Emma ta sanar dashi abinda take bukata, mintuna ashirin kacal ya kawo Emma unguwar wordbank, Kiran madam Gloria yayi yace ya iso, ta fada masa cewa ta Bude kofar baya ya shigo domin su biyu baza su iya daukar Nonye ba
Bayan su ukun sun fita da Nonye cikin sanda suka saka ta a mota Emma na mata kirarin har ta cika aiki ta masa banza domin yanzu damuwarta a cire dan cikin dake ta motsi, har Emma zai ta da mota anty Sarah ta fita tace ta manta Abu, cikin Sauri ta koma ta shiga dakin Nonye da Abraham wasu abubuwa wanda Allah kadai yasan me ta dauka, cikin wani Jakarta ta saka kana ta fito ta fada mota, ta tarar madam Gloria na mitar basu da lokaci fa, me taje dauko wa ne? Hakuri kadai ta bata domin bazata so ta San abinda ta dauko ba….
Bayan sun isa wani karamin asibiti inda da
farko likitan yace sai anyi bincike, hankalin madam Gloria ya tashi abinda tayi gudu Kenan shiyasa basu je babban asibiti ba, take ta siye likitan da makud’an kud’ad’e inda ya amince, aka shigar da ita aiki bayan sunyi gwaji ya tabbatar musu da Nonye ta mutu
Cikin awa daya aka ciro lafiyayyun kyawawan y’ay’an cikin Nonye maza biyu , dayan sak ubansa tamkar yayi kaki, dayan kuma sak Nonye.
Masu iya magana sun ce zakaran da Allah ya nufa da chara ko ana muzuru Ana shawo sai yayi…
Sun kansu likitocin Sun Jinjina ikon Allah, domin abu ne wanda bai taba faruwa a asibitin su ba, a cire rayayye daga matacce, gasu kuma yan biyu…
Su madam Gloria sun kansu sun girgiza da abinda ya fito a cikin Nonye, yayinda hankalin ta ya kara tashi, fatan ta kadai a fito da yaran ta shake su har lahira, yayinda anty Sarah ke tunanin hanyar tsiratar dasu….
Likitoci suka fara aikin dinka Nonye yayinda
Nurses suka yanka cibiyar su hadi da goge jikinsu da olive oil aka nade su a wani babban towel domin babu kayan saka musu, bayan komai ya kammala, anty Sarah ta saci jiki ta je wajen babban likitan tana kuka tace ya mata Alfarman tseratar da Rayuwar yayan, domin madam Gloria bazata bari su rayu ba, da fari likitan bai amince ba, amma ganin yadda take kuka bilhakki da gaske ya sanya shi amincewa, kana yace zai ajiye record din komai daya faru a yau din saboda ko da bincike ya taso watarana, take anty Sarah ta amince
Y’ay’an aka bata, likita yasa nurse ta bi da ita ta wata kofar inda ma’aikatan asibitin kadai ke bi har ya sadata da bakin gate, direct tasha ta nufa inda ta ji conductor’s suna Kiran garuruwa masu yawa, ta rasa wanne zata shiga daga karshe taji anje GOMBE sauran mutum d’aya
Babu bata lokaci ta fada ciki, duk da bata San ko ina a arewancin Nigeria ba, amma ta San cewa yaran zasu yi nesa sosai da madam Gloria ta inda bazata taba kawowa ranta cewa suna arewa ba, duk da bata San abinda likitan zai fada mata game da yaran ba, bata kuma damu ba tunda burinta ya cika ta tseratar da Rayuwar yaran…..
Likita ke tsaye gaban madam Gloria yana sanar da ita cewa yaran sun mutu sakamakon ruwan haihuwa daya shiga kansu inda basu Lura da wuri ba, sosai murmurshi ya bayyana a fuskar madam Gloria wanda bata San cewa ya subuce mata ba, take Likita ya gasgata maganar anty Sarah ya kuma godewa Allah daya bata yaran ta tafi dasu, ganin duk ma’aikatan na kallon ta ya sanya ta ankara da abinda tayi, sai tayi saurin sanja fuskar ta zuwa ta zallan damuwa inda ta Riga ta makaro, tabbas madam Gloria ta cika shu’uma.
“Likita Allah ya jikan su, amma bazan iya kallon yaran ba, da wanne zan ji da mutuwar Nonye ko da rasa Y’ay’an dana saka ran zasu maye mun gurbin Nonye” sai ta saka kuka kana ta cigaba “a binne su kawai a makabartan asibitin nan, amma bazan juri ganin gawar su ba” ta karasa tana sakin sheshekan kuka…
Biyar saura na asuba aka basu gawar Nonye suka saka a mota, sai a lokacin madam Gloria ta Lura babu anty Sarah amma bata tsaya neman ta ba, domin bata so gari ya waye basu koma gida ba, a cewar ta Sarah zata zo gidan tunda ba bakuwar ta bane….
Wanna karan da kyar Emma da madam Gloria suka shigar da Nonye, suna yi suna hutawa har suka kaita dakin ta, hadi da rufe ta da bargo, falo suka fito ta sallami Emma ya tafi, kana ta koma dakin ta, tana fatan gari ya waye sosai domin yanzu karfe Biyar da mintuna ashirin ne.
*WASHEGARI*
Kamar yadda madam Gloria ta fada karfe shidan safiya ta gwala ihun mutuwar Nonye
sosai take kuka tana birgima a kasa tamkar gaske, hakan yasa ma’aikatan gidan suka shigo part din halin tashi, suma kuka suka saka sakamakon Jin abinda madam Gloria take fada, “ewooooo Nonye yata kin tafi kin barmu, tayaya zamu kasance cikin farinciki bayan babu ke, kin tafi kin barmu da son(ABRAHAM) ya zamu yi da rashin ki, bayan kece cikon farincikin mu, mutuwa kin min yankan kauna ” sosai take maganganu cikin fitar hayyaci kai ka rantse da gaske take
Kowa na gidan yaji mutuwar Nonye matuka, domin macece mai son kowa, bata raina mutum komin kaskancin sa, haka zalika tana da son mutane sosai…
Kamar yadda yake a al’adar inyamurai idan mutum ya mutu basa binne shi a take, mortuary ake kai shi zuwa wasu lokuta kafin ayi bikin binne shi, hakan yasa madam Gloria da ta sanja shiga zuwa bakake tare da wasu yan’uwan su.
Haka al’adar su take idan anyi musu mutuwa komai na jikinsu yana kasancewa baki ne har izuwa wasu kwanaki.
*GOMBE STATE*
Bayan anty Sarah ta sauka a garin GOMBE ta shiga raba Idanu domin babu inda ta sani, ga yaran Allah ya basu wani mugun hakuri domin har yanzu basu yi kuka ba, daga karshe ta yanke hukuncin fara tafiya, tayi tafiya mai dan nisa kana ta shiga wani layi, gida na hudu idonta ya sauka a kai, haka kawai taji gidan ya kwanta mata a rai, shiga gidan tayi inda ta tarar da wata k’yakyawar yarinya fara sol hadi da iyayenta dake zaune a gefen ta suna hira cikin annushuwa
Da kallo duk suka bi anty Sarah ganin ta shigo musu babu sallama, “lafiya baiwar Allah” uban yarinyar ya tambaya a tausashe.
Jim anty Sarah tayi domin bata ji ko kalma daya daga abinda yace ba, dan haka tace “please can I use your toilet? Am really pressed”
Duk shiru suka yi domin babu mai Jin turanci cikinsu gwara-gwara baffa ya fahimci kalmar toilet din cikin abinda tace Dan haka yace “shalelen baffa zuba mata ruwa a buta”
Take yarinyar ta yi yanda yace kana ta kalli anty Sarah tace “gashi”
Amsar butar tayi, duk da a yawan lokuta idan fitsari zasu yi basu fiye amfani da ruwa ba, shiga bandaki tayi da jariran inda babu wanda ya lura cikin su Baffa cewar yarane sabuwar haihuwa a hannunta
Ta kai mintuna biyar a ciki kana ta leko ta kofar langa-langan inda ya huje ta ga baffa da Inna(matar baffa) sun shige daki, ya rage saura k’yakyawar bafulatanar yarinyar nan mai suna Aysha, ita ma daga karshe mikewa tayi zuwa nata dakin, duk anty Sarah na kallon su…
Ganin babu kowa a tsakar gidan ya Sanya ta ajiye jakar hannunta hadi da jariran a kasa cikin bandakin, kana a hankalin ta Bud’e kofar cikin sanda ta fito, sai da ta je soron gidan ta fara sauri-sauri gudu-gudu domin barin Layin…..
Ga wacce take bukatar ayi adding dinta a group chat this num👇
07082281566
NoorEemaan 🦋
I’m selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I’m
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[04/10, 10:59 am] +234 816 362 6370: 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇
ABRAHAM
🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇
WATTPAD
@NoorEemaan
ELEGANT ONLINE WRITER’S 📚✍️
https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.
Chapter 5-6
Sai da anty Sarah ta fito babban titi kana hankalin ta ya kwanta, ba tare da ta bata lokaci ba ta nufi tasha domin hawa mota da zai sadata da asalin kauyan su, Sam bata damu yamma tayi ba, haka zalika bata damu ko jin tsoron tafiyar dare ba, duk da yanda ta kai ga tsanar zaman kauye amma shine waje da zai sa hankalinta ya kwanta, domin bata son abinda zai sake hada ta da madam Gloria, ta kuma sani cewa har abada zasu da sauran kwannciyar hankali, domin kashe rai ba abun wasa bane.
Fatan ta daya mutanen nan su rike yaran amana, kuma in sha Allah zata yi kokarin sada Abraham da y’ay’ansa a lokacin daya dace matuk’ar tana raye, hawayen nadama ne ya saukar mata tuno cewa sune silan mutuwar Nonye, yanzu meye ribar su?
*GOMBE*
Baffa ne ya fito daga daki inna na biye dashi, “indo! Indon Baffa!!” baffan ya kira ta yana lekan Dan karamin dakin ta
“na’am baffana” ta fada cikin murya kasa-kasa wanda ke nuni da bacci ke shirin daukar ta.
Fitowar ta yayi daidai da dariyar da Baffa ya saki, kana cikin tarin kaunar tilon ‘yarsa yace” shalelena ba dai bacci kike shirin yi ba ga magriba ta gabato”
“wallahi baffana bacci nake ji sosai” tafada a shagwabe tana dago lumsasun fararren idanunta da ya dan rine kadan sak’amak’on baccin da take ji.
“kinga ki danyi hakuri kiyi sallah idan yaso sai ki kwanta, zo mu zauna a tabarma kafin ayi kiran”
“toh Baffa bari nayi fitsari Ina zuwa” tafada tana daukar buta domin shiga bandakin.
Inna dake garken dabobbi tana tasar nonon shanu ta saki murmushi hadi da girgiza kai, domin sosai indo da Baffa ke kaunar juna wani zubin ‘yar kallo take zama…
Kafar hagu indo ta saka a bandakin bakinta dauke da addu’ar shiga bandaki, sai dai addu’ar makalewa yayi sak’amak’on abinda tayi tozali dashi a kasan bandakin, shin mafarki take ko gaske? Ko ko shin aljanu ke kokarin bud’e mata ido?
Sanin cewa bata da mai bata amsa ya sanya ta kwala ihu daya yi matukar gigita su Baffa, hankali tashe suke nufi bandakin dan ganin abinda ke faruwa, ya kuma saka Indon su ihu…
*IMO STATE *
Zaune madam Gloria take sanye da bakaken kaya kamar yadda yake al’adarsu idan anyi musu rasuwa, idanunta sunyi luhu² sakamakon kukan karyan da take yi ba dare ba rana matukar a idon jama’a ne, sosai mutane ke tausaya mata, domin har tafi iyayen Nonye nuna mutuwar ta girgiza ta…
Wata yar’uwar su ce ta kalli madam Gloria hadi da cewa “Gloria kiyi hakuri hakan nan, sannan ya kamata zuwa yanzu ki kira ABRAHAM domin ya sani, saboda babu amfanin cigaba da boye masa”
Wani kuka madam Gloria ta saki har da majina tace “tayaya zanyi in sanar da dana wanna mummunan labarin? Banason hankalin shi ya tashi” ta karasa cikin kuka tana bubbuga kafafunta a kasa, riketa duk sukayi suna bata hakuri hadi da karfafa mata guiwan ta kira shi kan cewa ya dawo gida amma kada ta sanar dashi mutuwar Nonye sai idan ya dawo kasar.
Tana Jan majina ta fara dialing number’n shi kana ta daidaita muryar ta…
*KOREA*
Kwance yake gefen beach a wani had’add’en kujera sanye da boxer, sai sunglass dake manne a idanun sa, haka zalika sauran mazan sanye suke da boxer musamman masu shiga ruwan yayinda matan ke sanye da bikini wanda daga kirjinsu sai al’auransu ya rufe. Kyakyawane, chocolate color mai haske, yana da kirar nan da akewa lakabi da *giant* sai had’add’en six-packs dinsa idaunsa bai fiye girma ba, amma suna da matukar jan hankali, hancinsa dogo ne mai dan kauri, yana madaidaicin lips daya kara fuskar tasa kyau ainun, akwai wani karamin dankunne a kunnensa yayinda ya rataya cross + a wuyansa wanda hakan ke nuni da cewa shi din mabiyin addinin chirista(Christian) ne.
Burinsa yanzu ya gama abinda ya kawo shi kasar nan ya tafi domin yayi kewar gida sosai, kasancewar agajiye yake dawowa ko damar Kiran nonye da mummy baya yi, dan karamin tsaki yaja wanda sautinsa bai fito ba sai labb’an bakin sa ne suka motsa.
Haka kawai yake jin ranshi ba dadi, latsa wayarsa yake kokarin yi Kiran madam Gloria ya shigo, yaji dadi sai dai Sam babu alamar hakan a fuskar sa, domin shi mutum ne miskili da zurfin ciki wanda kai tsaye mutum bazai iya karantar abinda ke fuskar sa ba.
Latsa kore yayi hadi da kara wayar a kunnensa “good evening mummy, I was trying to call you guys now” ya fada da turanci.
Daga bangaren madam Gloria kuwa sosai ta daidaita muryar ta kana tace ” yes son! Ya kamata ka zo kawo gida hakan gobe, idan yaso ka koma daga baya” ta fada masa da yaren igbo
“mummy is everything alright? How’s Nonye and my baby doing?” kit madam Gloria ta kashe wayar ta, domin batasan sauran amsar bashi ba.
Haka nan yake Jin cewa there’s something wrong Dan haka babu bata lokaci ya shirya kana yayi booking flight Inda yaci sa a samun jirgin da zai je Nigeria, amma sai karfen taran dare.
Dan haka gida ya dawo ya shirya cikin wasu had’add’un kaya da ganinsu kadai zai tabbatar maka da tsadar su, wayoyin sa hadi da system dinsa kadai ya dauka kana ya tura sakon Gmail ga company daya zo takanas domin su cewa akwai dalili mai karfi daya sanyashi komawa kasar sa, amma zai dawo as soon as possible, daga nan filin jirgi ya koma domin zuwa lokacin takwas ta wuce, ba kuma yaso yayi missing flight.
*NIGERIA*
IMO STATE
Bayan ya sauka a airport ya kira lambar driver gidan hadi da sanar dashi yana Airport, babu Jimawa yazo amma wanna karon driver’n bai yi masa surutunsa irin yanda ya saba ba, hakan ya dan bawa Abraham mamaki domin yasan driver akwai surutu sosai, amma Sam bai nuna ba
Tafiyar mintuna ashirin ya sada su da Abraham mansion, sauka yayi, bai jira driver ya Bude masa ba, direct ya shige general parlour sai dai abinda ya gani ya sanya gabansa fad’uwa sosai domin a iya saninsa a kuma al’adar su ta igbo sai idan mutum ya mutu ake sanya bakakken kaya irin haka, toh me yasa duk suka sanya bakin kaya? Waye ya mutu? Yayi duka tambayar a ransa yana bin fuskar kowa da kallo
Da sauri madam Gloria ta taso, ta isa gareshi kana ta fashe da kuka sosai tace….
_A GASKIYA COMMENT DINKU YANA KADAN HAKAN KE SANI RASA KARFIN GUIWAN TYPING DAN ALLAH IDAN KUN KARA YAWAN COMMENT ZAN DINGA YI MUKU KODA BAYAN KWANA DAYA NE, IF POSSIBLE KULLUM, DOMIN INA DA AIKI SOSAI NAKE DAUREWA NAYI MUKU DAN HAKA KUMA KU FARANTA MIN DA COMMENT DINKU_
Noor🦋
26/12/2021
9:41am
I’m selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I’m
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[04/10, 11:00 pm] +234 816 362 6370: 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇
ABRAHAM
🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇
*First edition*
*WATTPAD*
@NoorEemaan
ELEGANT ONLINE WRITER’S 📚✍️
https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din
_note wanna ba sabon typing bane, reposting nake, so duk mai so ya fara bi yanzu ba sai nayi nisa ace daga farko ba_
Chapter 7-8
Yana shirin yin magana Kenan yaji muryar madam Gloria na fadin
“son munyi rashi, munyi rashi babba, Nonye ta tafi ta barmu, tafiya ta har abada, Nonye is gone for ever son” ta karasa tana fadawa jikinsa hadi da rungumeshi, yayinda sautin kukan ta ya karade gabadayan falon.
Tamkar wanda aka watsawa barkono haka ya runtse idanunsa, ji yayi gabadaya dakin na juya masa, sosai gabansa ke faduwa tamkar zata Faso kirjin sa ta fito
Nonyen sa ta mutu, ta tafi, tafiya ta har abada? abinda madam Gloria ta fada ya Shiga dawowa kunnuwansa , a karo na biyu madam Gloria ta kara cewa “ta haifi yan biyu wanda suma a take suka mutu, wayyo ni Gloria ya zanyi da raina” wanna karon k’wak’walwar Abraham ce ta daina gane komai sak’amak’on abinda madam Gloria ta kara fada, wanda ya sanya guiwowin sa yin Sanyi har ya gaza daukar gangar jikinsa, tilas ya sulale kasa, gabadaya jikinsa ya dauki rawa tamkar wanda yake cikin kankara, sabanin hakan gumi ne ke keto masa, na zallan tashin hankali, ga gashin kansa sun mimmike, duk da cewa babu ko digon hawaye a jajayen idanunsa, amma dole dukkanin wani mai tausayi da imani ya tausayawa halin da Abraham yake ciki a yanzu.
Rikeshi madam Gloria tayi tana kuka hadi da bashi hakuri, ko kala ya gaza furtawa domin nauyi da labb’ansa suka yi, hannu biyu ya sa ya rike kanshi dake barazanar fashewa, haka ya kasance cikin wanna halin fiye da awa uku kuma ko motsi bai yi ba, banda zuciyarsa dake bugawa da sauri² mutum zai yi tunanin matacce ne….
*GOMBE STATE*
Ba tare da su baffa sun lura da jariran dake kasa ba suka riketa hadi da cewa “aysha lafiya meya same ki, yi magana meya same ki aysha? ” suka fada a tare suka duba jikinta…
Idanunta ta runtsa, sakamakon hakan hawaye ya zubo kan kyakyawar fuskar ta, hannu ta mika ta yiwa su baffa nuni izuwa ga kasan bandakin inda babies din ke kwance wanda zuwa yanzu sun fara mutsu² sak’amak’on sanyin ruwan bandakin daya fara ratsa ta cikin towel din zuwa fatar jikinsu, a tare suka zaro idanun su ganin abin al’ajabi, da ba dan kada su kara firgita tilon diyar su ba, da ihun suma zasu zunduma, a take kuma k’wak’walwarsu ya tariyo musu sanda anty Sarah ta shigo da farin towel din nan, amma basu taba tunanin cewa abu mai rai ne a ciki ba, a tunanin su ko wani kayan ta ne bata son ajiyewa a waje shiyasa ta shigar dashi bandakin.
Sosai mamaki da al’ajabi ya rufe su, babban tambayar su anan shine menene dalilin ajiye yaran da anty Sarah tayi? Domin basu ga alamun tabin hankali ga anty Sarah ba, bare su ce rashin cikakken hankali ne ya sanya ta manta yaranta a Bandakin, shakka babu wanna babban al’amari ne ya shigo cikin Rayuwar su…
Baffa da tausayin yaran ya gama rufe shi ya tsunkuya, amma gabansa na faduwa, amma ya dake, domin abu ne wanda bai taba ji ko gani ba ne ya ratsa gidan sa, sosai ya dake gudun kada ya kara firgita su Inna, addu’a dauke a bakinsa ya hade yaran a jikinsa, kana ya kalli su Inna yace “ki dauko jakar nan ku fito daga bandakin hakan nan” ya fada yana barin bandakin, sai a lokacin indo ta Bude idanunta dake ziraro da hawayen zallan tsoro, cikin tsoro Inna ta sanya hannu ta dauki jakar hadi da riko hannun indo suka fito daga bandakin….
Direct dakinsa baffa ya nufa da yaran, hakan yasa cikin muryar tsoro indo ta ce “wayyo baffa nah! kada ka shigar dasu dakin ka, Kar su cutar da mu, kila ba mutane bane, ni gaskiya bazan iya kwana a gidan nan ba, Dan Allah baffa ka fitar dasu daga gidan nan, muje mu nemi matar mu bata yaran ta ” ta karasa cikin zallan tsoro mai hade da kuruciya hadi da sakalci….
Itama Inna irin tunanin Indo ne a ranta na cewa
Yaran ba mutane bane, amma bata furta ba, sai sai tsaf baffan ya karance ta, hakan ya sanya shi sakin murmushi, ya kuma girgiza kansa, tabbas duk shekarun mace da kaifin tunanin ta namiji ya fita koda bai kai ta yawan shekaru ba, ba tare da kuma yayi magana ba ya ida shigewa dan karamin dakin sa, ya kuma san cewa zasu biyo bayan sa domin basu taba ketare umarnin sa…
Wata jibgegiyyar kodaddiyyar malum-malum baffa ya janyo cikin kayansa ya saka yaran a ciki ya lullube su kana ya kwantar dasu kan gado irin dai na kauyen nan, towel din ya fitar waje ya saka cikin roban wanki ya saka kilin da ruwa ya jika shi, kana ya saka kilin ya wanke hannunsa sosai sannan ya koma dakin….
Gyaran murya yayi hadi da mai da duban sa ga Aysha Indo yace “shalelen baffa ina so kwantar da hankalin ki, ta ina kike tsamanin zamu ga matar? Wacce hanya tabi? Ba mu sani ba, Allahu masani.
Sannan ba fa manta yaran tayi ba, ko mai tabin hankali ta san kaunar abinda ta haifa, Allah ka dai yasan dalilin daya sa ta ajiye mana yaran, wadannan yaran mutane ne kamar mu, ki cire tsoro a ranki kinji, Allah kadai yasan dalilin daya sanya wadannan bayin Allah shigowa cikin Rayuwar mu, ko nace kaddarar mu” ya fada yana nuna yaran kana ya cigaba “domin akwai gidaje bila adadin a unguwar nan, amma nan gidan yaran suka fado, Dan haka nayi alkawarin kula da yaran nan har sanda zan daina numfashi, ina fatan zan samu goyan baya daga gareku”
Jinjina kai inna ta yi, wanda tsoron ya dan ragu sak’amak’on maganganun da baffan yayi, zai kara magana yaji an kwala Kiran sallar magriba a wani masallaci hakan ya sanya shi barin dakin da sauri yana gayawa su inna suma su hanzarta yin alwala kada su rasa jam’i domin su kan bi jam’i domin masallacin yana kusa da gidan su, wanda baffa shine Limamun masallacin….
Bayan an iddar da sallah da kamar mintuna talatin baffa ya shigo hannun sa dauke da bakar leda, kallon inna dake kokarin yin tarke/talke yayi, Cikin sauri yace “da kin fara yi wa yaran wanka da ruwan zafin nan, idan yaso sai a sake dora na tuwon” ba musu ta ajiye kayan tuwon, wani tsaftataccen bokiti ta dauko ta juye ruwan, kana ta zuba wani, hadi da gyara wutan, dakin baffa ta nufa da bokitin, kana ta fito ta nufi dakin ta domin dauko roban wanka wanda tun na indo ne amma yana nan da sauran kyansa da sabunta(kun San fulani akwai iya ajiya🤩)
Sai da ta wanke roban wankan kana ta dan sirka ruwan zafin kadan, kan gado baffa ya zauna, jariran na hannunsa yayinda indo ke gefe tana raba idanu wanda zai tabbatar wa mutum cewa har yanzu tsoron bai barta ba.
Ledar da baffa ya kawo inna ta zazzage, kayan jarirai da na Sanyi, sabulun yara da so so, man shafawar su, mataji(comb) hadi da hular Sanyi. Ba laifi siyayyar tayi daidai talaka…
Sosai inna ta wanke yaran ta kuma gasa musu jiki sosai, sai a lokacin jariran suka canyara kuka tun lokacin da suka shaki iskar duniya….
A kuma daidai lokacin ne Indo taji wani mugu_mugun tausayin yaran ya ratsa jikinta, wani Sanyi ya fara ratsa ko wani huda na gashin jikin ta, sak’amak’on hakan tsikar jikinta ya fara tashi, haka nan ta ke Jin wani yanayin na mussaman kan yaran Wanda bakinta bazai iya furtawa ba…
Ajiyar zuciya ta sauke, kana ta mai da duban ta ga yaran Inda zuwa Yanzu Inna ta shirya su cikin kayan da baffa ya kawo, sunyi kyau sosai gwanin sha’awa, karon farko da Indo taji tana son daukan yaran ta rungume su, hakan yasa ta fara takawa domin isa garesu….
*yanzu Abraham ya soma, yawan comment dinku shi zai bani kwarin guiwar cigaba da typing, idan ba comment nima bazan yi update ba*
*Sannan mai son nayi adding dinta a group ta yi chatting dina up ta lambar nan*👇
NoorEemaan🦋
07082281566
Share fisabilillah
Comment
Vote
I’m selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I’m
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[…] Abraham Hausa Novel […]
[…] Abraham Hausa Novel […]
[…] Abraham Hausa Novel […]
[…] Abraham Hausa Novel […]
[…] Abraham Hausa Novel […]