Abu Rasheed Hausa Novel Complete
Tag: ABU-RASHEED
Zainab Habib(Mom Islam
_Ga masu so a tallata musu hajarsu suyimin magana ta nan 08141799224_
_Bismillahar rahmanir rahim_
*Ƙauyen Ƙauran Domawa*
_Dake cikin garin saminaka_.
9:am 23/6/2022 Thursday.
p 1-2
Yarinya ce ƴar kimanin shekaru goma da aihuwa , hannunta riƙe da tulu tana tafiya tana ƴan wake-waƙenta ,
Da sallama ta shigo gidan nasu daya kasance ginin ƙasa wanda ke ɗauke da ɗakuna huɗu ,ɗaya na Goggo Amina ,ɗaya na Inna Laure , ɗaya na baba ,ɗayan na kwananta tana isowa da ruwan data ɗibo ta kawo gaban Inna Laure ta ajiye tare da cewa “Inna ina tuwon nawa ?”
Inna Laure ta galla mata harara kafin tace “sai da kika gama yawon barkancin naki zakizo kina tambayata abinci ?”idan baki ɓacemin da gani ba wallahi sai na cire miki ƙafa ”
Goggo Amina dake keɓe baki tace “kema kika kulata ta gaji munafurcinta ta ƙyale mutane ,
Shigowar baba ne yasa ko wacce tayi tsit sai suka hau cewa ” Hasina ƴar albarka maza jeki rumfa ki ɗauko tuwo kici ,kasancewar baba yazo ɗaukar wani abu ne yasa bai sauraresu ba tunda bashi da saurin fahimta ya fice .
Inna Laure ta danguware mata kai kana tace “kije ki dakamin yajin can ƴar iska “.
Hasina ta miƙe tana share hawayen dake zubo mata , ta ɗauki robar da barkono yake ciki ta juyo a turmi ta ɓare magin dake ciki guda ɗaya tasa gishirin data gani a ciki tahau daka ,tanayi tana atishawa ,kafin ta gama dakan yajin duk tasa a hancinta , ihu tasa kasancewar ta gurza hannunta a ido tare da yin tsalle tana cewa “wayo Allah Ummana yaji a idona ”
Babu wanda yayi yunƙurin kulata bare su nuna sun ganata , har ta gama kukanta ta share hawaye suna zaune .
Bayan ta kammala dakan ne takawo gaban Inna Laure tace “gashi Inna ” batare da ta ɗago ta kalleta ba tace “ki ɓacemin da gani ”
Hasina ta fice da gudu kai tsaye gidan ƙawar Ummanta ta shiga , da sallama a bakinta tana shiga ta tarar da ƙawar Umman tata a gindin murhu tana sakun ɗanwake , dama sana’arta kenan kullum da safe .
Tana ganin Hasina tace “ƴar Umma ina kika shiga ne kwana biyu banajin ɗuriyarki ?” Hasina tahau goge ido tana cewa ” ba Inna Laure da Inna Amina bane suka yimin duka shekaranjiya ba ,jiya kuma suka ɗoramin tallah har tirai biyu , yau kuma Inna Laure taban dakan yaji har yana shigemin ido , suka hanani abinci ” ta ƙarashe maganar tana kuka ,
Cikin tausayawa ƙawar Ummanta da ake kira da Inno ta kamo hannunta kana ta zaunar da ita tace …
Karanta littafin Gidan Uncle Hausa Novel
Hasina na fita baba ya shigo hannunsa riƙe da ledar taliya guda biyu , cikin fara’a su Inna suka tareshi tare da ce masa yau zamuci daɗi ”
Baba na faɗaɗa fara’arsa yana waige ,sunsan wa yake dubawa sarai babu wacce ta kulasa , sbda baiji ɗuriyata bane ya sashi cewa ” wai ni ina Hasina ne ?” Inna Amina tace “cewa tayi ita bazataci tuwo ba sbda bashi ka bayar a dafa a gidan ba ”
Cikin ƙunar rai baba yace “wato Hasina ta ɗauko ruwan dafa kanta ,ita ba ƴar kowa ba amma ta dinga zaɓen abinci ?” yanzu ina ta shigane wai ?”baba ya tambayesu cikin ɓacin rai .
Inna Laure tace “ai bazata wuce gidan Inno ƙawar uwarta ba tunda acan suke kitsa munafurcinsu ”
Ran baba a ɓace yace “tashi Laure ki kiramin ita ” Inna Amina tace a’a malam ka bari dai ta shigo aja mata kunne yin hakan zai iya janyo maka zagi a gari ”
Baba yace “to shikenan amma ai wannan tozarci ne “,
Yana rufe baki Hasina ta shigo abinka da yaro da taci abinci a gidan Inno ko goge baki batayi ba ,
Tun daga nesa baba ya fara ɗura mata zagi yana cewa “kinaso kiyi halin baƙar uwarki mai baƙin hali ,kinaso ki mayar dani matsiyaci ne ehe ?dahar zakice baki cin tuwo ?Hasina ta sanya hannu a baki alamun mamaki cikin tsoro tace “wallahi baba ba’a ba… yazo inda take ya ɗauketa da mari wanda sai dataga giftawar taurari ,kafin yace “matsiyaciya kusa mata tuwo ina kallo taci “.
Jikin Inna Amina yana ɓari ta nufi gurin ɗumamen tuwon ta sako mata har guda huɗu ,ta zubo miya koriya shar wacce babu tabbacin akwai manja a cikinta bare magin kirki “zoki ɗauka ” Inna Amina tace kasancewar itace da abinci kuma itace amarya .
Jikin Hasina na karkarwa ta ɗauko tuwon baba na zaune ta fara ci , kasancewar ta fara ƙoshi ,yasata ci kaɗan kana tace “ta ƙoshi ”
Baba ya zaro mata ido tare da cewa “ko zaki amayo dashi sai kin cinye ”
Dan kinga kece kaɗai ƴa a gidannan shine kike yiwa mutane iskanci ,suma basu cire rai da aihuwaba tunda Allah ne bai basu ba ,ni bazanyi miki goyon da za’azo ana zagina ba dan haka ki kula da rayuwarki ,idan kin munafurcesu kanki kikayiwa ,bayansu baki da wasu iyayen da zaki sanar ma damuwarki ” baba ya ƙarashe maganar yana sanya hannu a cikin aljihunsa ya fito da naira hamsin yace “ayi cefanen taliya ”
Inna Amina ta karɓa kafin tace “,tunda kin ƙoshi tashi ki siyomin manja na talatin maggi dunƙule na goma farin magi na ashirin inada goma gashi maza ina jiranki ”
Hasina ta wanko hannu zata fice taci baba yace….!
Kinson jin ƙarashen labarin ? da nace bayan sallah zanyi posting sakamakon mutane da suka matsamin yasa na saki littafin yau ,ina fatan masoya littafaina zaku nunamin love ta hanyar siyan littafina .
*Wannan littafin na kuɗi ne akan sassauƙan farashi ,normal 200 vip 500 special 1k zaki turo da kuɗinki ta wannan account ɗin 3175689751 Zainab Habibu first bank shedar biya ta wannan number 08141799224 ko kuma katin hoton katin mtn ta wannan number 08141799224 , ga masoyana da basayin whtsapp akwai group dana buɗe wanda zandinga yi muku posting ma’ana ƴan facbook , ƴan Niger kuyimin magana in faɗa muku inda zaku biya nagode.*
MOM ISLAM
Leave a Comment