Abu Zayad Complete Hausa Novel
BISSIMILLAHI’RRAHAMANIRRAHIM.
LITTAFIN ABU ZAYAD QIRQIRATA CE BATA WANI BA DAN HAKA BANYARDA AJUYAMIN LABARI BA HAR SAIDA IZINI NA, BANYANR DA KUMA AMAIDA SHI NA SAURARO BA SAI DA IZININA SBD HAKA A KIYAYE.
*Page 1_2*
Gudu takeyi sosai iya qarfinta acikin dokar daji gaba jeji baya daji, tin tana gudun iya qarfinta harta gajiya tafara d’aga qafa da qar sbd qatoton cikin dake manne ajikin ta, kuma duk da haka baisa tafasa gudun ba domin ga dukkan alamu gudun ceton rai takeyi domin kuwa tana wanan gudun tana juya bayanta tana hangen wasu mutane akan dawakansu da suke riqe da mugayen makamai suna binta suna so su kamata, ko da kuwa suka ga sun kusan kamata sai suka sauqa daga kan makamansu suka ci gaba da binta da gudu, ita kuwa baiwar Allah d’in babbar macace dan da alamu zata kai shekaru 40 ta gaji Sosai ga mararta da take mata ciwo Sosai tini tafara bleeding jini yafara bin qafafunta ita sbd tashin hankali bata ma san halin da take ciki ba, qara juyawa tayi ai kuwa taga saura qiris Dakarunan su cin mata addu’a tashiga yi azuciyarta ciwon mararta kuwa qaruwa taji yanayi har taji baza ta iya d’aga qafafunta ba dan haka tafadi a gurin amma ta qoqarta ta tashi taci gaba dayin rarafe acikin dajin, domin bazata iya gudu ba ko tafiya ma baza ta iya ba, gashi batason acutar mata da abunda ke cikin ta, suna qoqarin harbin ta da kifiya ta hango wata duhuwa da sauri ta rarafa ta shige cikin duhuwar, su kuwa mugayen suna harbin kibiyarsu, kifiyar tatafi ta caki wani ice, nan fa hankalin su ya tashi ganin matar ta ‘bace ‘bat a gabansu.
Nanfa suka shishiga dubata acikin duhuyoyi dake gurin, ita kuwa matar tana shiga cikin duhuwar na quda ta tirniqeta gashi bata ta’ba haihuwa ba arayuwarta asalima bata san yanda ake haihuwar ba domin bata ta’ba tsayuwa akan mai na quda ba, amma haka ta jure duk wahalar da take ciki har tahaihu ba tare da tayi ihu ba, dan kar su jiyota kawai Allah take ambato, aikuwa ta haihu lafiya domin kuwa kukan jaririnta taji yafito lafiya idanunsa bud’e ras sai callara qara yakeyi, cikin murna takai dubanta izuwa gabanta inda jaririn yake, tana godewa Allah,
Su kuwa wa’yanan mugayen kukan jaririn suka fara jiyowa acikin dokar dajin amma sun rasa ta ina kukan yake fitowa dan haka suka rarabu suna neman matar hankali tashe domin basa qaunar tahaihu so sukeyi suka sheta ita da abunda ke cikin ta.
Ita kuwa matar d’an tinani ta tsaya yi ta tuno wata rana da taji wata in go zama tana fadar yanda ake yanke cibiya, dan haka takama cibiyar tayi yanda taji ingozamar ta fad’a ta yanko ice mai kaifi abanta ta yanke cibiyar tana kuka, sanan ta gogewa jaririn jiki da gaganyakin ciyayi dake gurin, tacire mayafinta ta nanad’eshi aciki, sanan tayanki bakin mayafin ta sa tsinin itace ta ‘bula hanunta ta dangwali jinin gurin tarubuta ABU ZAYAD a jikin farin mayafin da ajami, sanan ta kama hanun jaririn nata ta d’aure masa, ta kuma yankar wani mayafin ta ‘bulla jikin jaririn nata ta dangwali jininsa tarubuta wani suna da wani yare wanda nima Mummyn Minal bansan me tarubuta ba, ta d’aurewa yaron nata a goshin sa, tana cikin haka taji ana cewa ga gurin da kukan yaron yake fitowa kunga jini a qasa, mu qarasa suna gurin qilla ta haife cikin jikinta dan haka dole mu kashesu.
Tana jiyowa qarar sautin takunsu, gashi bazata iya guduwa ba sbd jiri takeji dan haka ta d’auki d’anta ta rintsa ido ta wullashi bayan duhuyoyin da take tinanin qila ruwa ne agurin.
Tana wullashi kuwa suka qaraso gurin, d’aga ta sukayi cak suka ga ba cikin dan haka suka bata wani mugun mari suna tanbayarta ina abunda ta haifa amma ina kafin ta basu amsa ta sume, dan haka suka shiga neman jaririn amma Ina basu ganshi ba, Dan haka suka dawo suka caca’beta suka bar gurin da ita.
Shi kuwa Jaririn tana wullashi sai kawai ya kifu akan bayan wani qaton zaki dake shan ruwa a wani babban tafki dake
gurin, zakin nagama shan ruwan ya d’ago ya girgije jikin sa irin yanda dabbobi keyi memakon yaron yafadi sai ma mannuwa abayan zakin ya dad’a yi Zaki kuwa yayi tafiyarsa yabar gurin cikin sauri.
Ku biyoni muji ina zakin zekai yaron.
Shin ita kuma matar ina zasu kaita??
Littafi na ABU ZAYAD na kud’i ne 200 kacal ba dogon ‘bata lokaci ki biya kud’in ki kisha karatu, zaku samu free page zuwa 9-10 daga zaran na gama Free page kuwa wa’yanda suka siya su zasu sha labari sbd haka idan kina buqata kiyimin magana ta 09065120158
Dan Allah dan Annabi ki tura awasu groups d’in
Comment.
*ASSATAGAFIRULLAH WA’A TUBU ILAIKA*