Hausa Novels

Abul Khair Complete Hausa Novel

Abul Khair Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag; ABUL-KHAIR

 

 

 

TSARAWA DA RUBUTAWA DUK DAGA SALMEERT SANI SALMAN TRIPLE S° (ƳAR LELEN ROYAL STAR CE)

 

 

 

*WANNAN LITTAFIN NA KUƊINE KUMA WANDA SUKA FARA BIYA KAFIN A GAMA FREE PAGES, TO ZAI BADA #300, WANDA KUMA SUKA BARI HAR SAIDA AKA GAMA, TO ZASU BIYA #400*

 

 

 

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM, DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI, ALLH NA ROKIKA YARDA NA FARA LITTAFIN NAN A YAU RANAR 6 GA WATAN ZUL- HAJJI, ALLAH KA BANI IKON GAMAWA LAFIYA , ALLAH KA DAFAMIN A DUKAN LAMURANA , ALLAH KA SHIGEMIN GABA, ALLAH KA CIKAMUN KUMA DUKKAN BURIKA NA, NA ALKHAIRI*

 

 

 

 

*PAGE 1*

 

 

 

 

 

“””””””””””””””””””””””””””Ahankali kuma cikin isa da takama tare da izza , kyawawan Samarin suke saukowa daga mattatakan jirgin, So cute.

 

 

karasa saukowa sukayi, anan ne na shagala, domin a da , banga komai ma, kyawawan Samari ne, guda biyu masu masifar kama da juna, wanda ina da yaƙinin ko Iyayensu ba lallene, su iya banbancesu ba saboda masifar kamar da sukeyi da juna, kamar an tsaga kara.

 

 

Ahankali suka cigaba da tafiya cikin Kasaita da kwarjini tare da Haibar da take tare da su.

 

 

 

dogaya ne bawai chan ba tsawonsu dai-dai misali, sai dan jiki da suke dashi, wanda bawai jikine sosai ba, kawai dai su ba ramanmu ba kuma su ba masu kiba ba sosai, farare wanda farin nasu har wani jaja yake dashi, sai kwantacen sumar kansu da taji gyara, wanda har gyaran da akayi musu iri daya ne, kyakyawan cute lips dinsu na karewa kallo, wanda suke pink color, wanda ya yiwa , kyakyawan bakinsu ƙawanya, wanda sai kayi zaton tea spoon ma , bazai shiga ciki ba, saboda tsabar karantarsu.

 

 

sai kyakyawan hancinsu, da ya yi, baka’in dacewa da cute face din tasu, komai nasu kala daya , dan banbancin kadane, inda daya yana da gold eyes, dayan kuma nada blue, sai sumar kansu wadda ta daya, tafi ta daya yawa, amna har kayansu kala daya ne, hatta yanayin tafiyarsu ma kala dayane.

 

 

Karanta Littafin Bandirawo Hausa Novel

wasu manyan motoci naga sun nufa, wanda a kalla sunkai guda goma, ko wace kuma, an rubuta mata *ABUL-KHAIR*,.

 

 

 

wanda dukansu baƙaƙe ne, daya ce kawai fara wadda kuma itace tsakiyarsu tasha tinted , amma duka sauran goma sha huɗun, duk baƙaƙe ne.

 

 

 

shiga sukayi tare da haƙincewa a bayan motar, a hankali motocin suka fara tafiya domin barin Airport din, direct cikin garin na Damaturu , suka shiga, tafiya mai dan tsawo sukayi kafin su karaso, bakin tafkeken get din, Masarautar wanda sa ka kalleta, zaka gane cewa ba karamar Masarauta bace, Masarauta ce mai dinbin tarihi da dadewa, domin komai nasu na Al-adane , hatta ginin Masarautar na dane, domim gini ne na tubali .

 

 

 

a hankali motocin suka karasa shigewa cikin Masarautar da na karewa kallo .

 

 

 

bakin wani part , wanda tundaga waje in ka kalleshi kasan ba karamin kuɗi, aka kashe mishi ba, motocin suka tsaya.

 

 

daya ne, ya fara fitowa, ya shiga cikin part din, kusan 1 hour, kafin naji an kara bude kofar motar.

 

 

 

dayan ne, ya fito shima tare da nufar part din da dayan dan uwan, nashi ya shiga, a hakan yake tafiya kamar wanda kwai ya fashe mawa a ciki, sai wani yamutsa fuska yake.

 

 

 

Wow Ashema a waje banga komai ba, dan saida nayi mutuwar tsaye nayi saboda, ganin tsabar haɗuwar part din , wani kofa naga ya nufa, binshi nayi a baya domin ɗauko rahoto.

 

 

wai ashe bedroom ne, karewa bedroom din kallo nayi, shima ɗindai ya hadu bed din, kuwa yasha shimfiɗa ta Alfarma, irinta gidan Sarauta.

 

 

 

bathroom ya nufa direct, da chan kofa naji ana cewa , “Twins bari na haɗa make hot water, kaga garin da akwai Sanyi, kuma kaga yanayin jikinka bakajin dadi”ya fada yana wucewa .

 

 

bakin bed din ya zauna yana fitar da numfashi , da dan karfin ga bugun zuciyarshi da yake bugawa , da dan karfi.

 

 

minti kadan , naji ana cewa “Khair! Khair!! taho kayi wankan”, ya fada yana fitowa daga bathroom din.

 

 

 

kamar bazai tashi ba kafin ya mike a hankali, saida yazo kusa dashi kafin, ya juya blue eyes dinshi tare da cewa “thanks”, a hankali wanda indai ba kana kusa da shiba, to bazakaji ba, girgiza kai kawai *ABUL* ya yi, yana jinjina wannan miskilancin irin na *KHAIR* wanda ko Mahaifinsu da yake Sarki baya wannan takamar.

 

 

 

 

saida ya share kusan 30 minutes, kafin ya fito, sumar kannan mai tulin yawa tana zubar da ruwa, kan kujerar dressing mirror, ya zauna tare da fara goge kanshi da towel din, da ya naɗo sumar kanshi da ita.

 

 

 

Abul ne, ya shigo bedroom din, hannunshi rike da wasu kaya wanda ba wasu masu nauyi bane, sosai wanda kuma kalla daya ne da na jikinshi.

 

 

ta mirror Khair ya kalleshi , ajiye kayan ya yi, gefen bed din tare da matsawa kusa da shi, towel din da yake a kanshi ya Ansa, ruwan da yake a kanshi ya shiga goge mishi , sai da ya gama, tas kafin ya shafa mishi, lotion saida ya gama, kafin ya dauki hand drea, ya fara busar mishi da gashin kanshi.

 

 

 

tayashi ya yi, ya gama shiryawa tas , kafin su fito Abul rike da hannun Khair , fita sukayi daga part din, wani part suka nufa, wanda yake dan nesa kaɗan da nasu.

 

 

 

Wata tsohuwace, zaune sai masifa, takewa wasu Kuyangun da ke, zirga-zirga a parlour, ”shegu, ni kuyi sauri ku kawomin Abinci naci, kar na mutu, ace tun dazun baza’a kawowa mai rai Abinci ba, sai nasa Abdul-jabaru, ya koreku duk an kawo wasu tunda kudai Salamanmu ne, ” ta fada tana wurga musu harara.

 

 

 

suna shigowa naga Khair yadan, saki fuskarshi, Masha Allah , duk da ba dariya ya yi, ba amma sosai ya yi kyau.

 

 

“a’a, kunga dan Albarka ina kake a ciki, karaso nan, dama tun dazun nikeson zuwa gurin Abdul-jabbaru dan ya kiramin kai, ashe kana kusa ma”, ta fada tana washe hakoranta .

 

 

 

matsawa kusa da ita Khair , ya yi yana cewa, ” Ayya , sai kuma gani nazo”, ya fada fuskarshi babu yabo ba fallasa.

 

 

 

 

 

*********************

 

 

 

 

zaune suke sun hada kai da guiwa, su ba kuka suke ba amma yanayinsu ya baiyana halin da suke ……………………..

 

 

 

ga wanda zasu fara biyan kuɗinsu to zasu iya turowa ta wannan account number din

 

 

1499884120

Umma salma sani.

Access bank.

 

 

ko katin MTN ta wannan number

 

 

07033371851

 

 

 

 

ku tabbatar kun turomin shaidar biyanku ta hanyar yomin screenshot, sai ku turomin.

 

 

 

 

 

 

Salmeert Sani Salman (Ƴar lelen royal star ce)

Leave a Comment

error: Content is protected !!