Tunatarwa

Abun Al’ajabin da ya faru a garin Bajoga da ke Gombe a Nigeria

 Abin al’ajabi ya faru a garin Bajoga.

.

Daga Bappah Haruna Bajoga

.

Wani abun al’ajabi ne ya faru a nan cikin garin Bajoga, a unguwar Bage dake a karamar hukumar Funakaye Jihar Gombe. Wata matace tana kwance a dakin ta da sassafe ta rufe kofar dakin sai kare ya shigo gidan, bai zame ko ina ba sai a dakin nata, kuma dakin a rufe yake amma Karen ya tura kofar ya shiga daki, ita kuwa tana kwance tayi tsammanin ma Akuya ce.

.

Data mika hannun ta don ta Kore shi sai Karen ya kama hannun ta ya ciza yaki sakewa, sai ta fara ihun neman dauki tana Kiran abokiyar zaman ta (Kishiyar ta), to amma ita abokiyar zaman nata tana bacci. Sai daya daga cikin ‘ya’yan gidan yaji ihu sai ya nufi dakin yadikkon nashi, sai ya samu hannun Matar a bakin Karen yaki sakewa, jini sai zuba yake tayi, ita ma abokiyar zaman nata sai ta farka. Taji hayaniya sai ta nufi dakin abokiyar zaman nata sai taga ana ta kokawa da Karen da ba a ma san daga inda ya taso ba, amma Karen yaki ya sake hanun nata, ya daddatsa mata yatsu bakin shi duk jini, cikin dakin ma jini. Sai aka samu nasara ya sake hanun nata sai ta shiga dakin abokiyar zaman ta a rude amma kuwa abin mamaki Karen nan ma sai ya bita, kuma fa babu Wanda Karen yake bi sai ita matar daya farwa din. Daga karshe da matar ta samu nasara sai ta sake shiga wani dakin na daban, sai suka rufe dakin ta ciki, sai Karen ya juya ya fice daga gidan, kuma ba a San daga inda Karen ya taso ba, da aka fita waje aka tambayi mutanen da suke zaune a layin unguwar kowa sai yace shi fa bai ga wani kare ba, wannan batu na al’ajabi daya faru a gidan marigayi Alhaji Haruna Dendele dai a yanzu shine ake tattaunawa a garin, musamman ma a Unguwar bage da abun ya faru.

.

Malama Fati Sambo Bajoga ma’aikaciyar hukumar jinkai ta Social welfare a karamar hukumar Funakaye jihar Gombe ta shaidawa manema labaru ta hannun daya daga cikin jami’an kungiyar marubuta ta Arewa Media Writers na yankin ( Bappah Haruna Bajoga) yadda aka tafi da matar Asibitin Bajoga, da kuma yadda aka kaita babban Asibitin gaba a cikin fadar jihar Gombe don yi mana aiki. Wannan shine takaitaccen abinda ya faru a Bajogan kenan da a yanzu ake ta fadin ra’ayoyi mabambanta. ALLAH yayi mana tsari da fitintinun rayuwa, ya raba mu da sharrin dukkanin halittu wasu halittu baki daya.

Leave a Comment

error: Content is protected !!