Afnan Hausa Novel Complete

Afnan Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tun daga kasa Alhaji Faruk Muhammad ke jiyo sautin muryar yarshi daya tilo da yake so da kauna tana kuka kamar wacce take rera waka.

 

 

 

Alhaji Faruk matashin mutum ne dan kimanin shekara arba’in da biyar yana zaune tare da matarshi Hajiya Khadija da yar su Halima (Afnan) ,sai kuma dan dan uwanshi da ke dake gurinshi Abduljalal suna zaune lafiya cikin so kaunar juna .

 

 

 

Alhaji Faruk na zaune a bakin gado yaji burum an banko kofar dakin shi ,yarinya ce yar kimanin shekara goma zuwa sha daya ta shigo dama yasan ba wanda zai shigo haka sai Afnan,bata dawani tsayi sosai sannan kuma baza a cemata yar lukuta ba kuma za’ace mata siririya ba.

 

 

 

Tana zuwa ta fada jikin mahaifin nata tana sake fashewa da kuka kamar wata karamar yarinya yar shekara biyar ,shafa bayanta Alhaji Faruk ya fara ya ce “Mai ya faru da Mamana ne? waya taba mun ita, Yayanki ne? da sauri ta daga kai yace to me ya maki ?.

 

 

Afnan na kara shigewa jikinshi kamar wata mage ta turo baki ta ce “Abu ba shine ba zai fita nace zan rakashi asibitin wai baza shi dani ba na fiye yawo”ta sake saka kuka.

 

 

 

Alhaji ya ce “kashh amma Yaya bai kyauta ba, rabu dashi muma zamu fita ne muje gidan Nanne banda shi”yayi maganar cikin sigar lallashi.

 

 

 

Cikin murna Afnan ta mike tsaye tana tsalle kamar ba ita ba ce take kuka yanzu ,zuwa tayi ta rungume Abu dinta ta ce “ina sonka Abu bari inje in sako hijab”jikin ta har bari yake tsabar zumudi sai murmushi yake ya ce “To uwar azarbabi bari sai na fara yin wanka…..”

 

 

 

Ai bata jira ya karasa ba ta fyalla a guje sai dakin ta dake kallon na Abun nata ta shiga direct wadrobe dinta ta nufa.

 

 

 

Tsaya wa tayi tana kallon jerin hijabanta tunani ta fara wajen minti shida chan ta dauko wani peach hijab mai hannu dogo har kasa.

 

 

 

Dakin Abu Afnan ta koma ba tare da tayi sallama ba ,Ammi da ta dawo daga gidan Yayarta ne tsaye ita da mijinta a gaban mudubi tana fesa mashi turare.

 

 

 

Ta waiga ta kalli Afnan da tayi dare dare a kan gado harta dauki system din Abu .

 

 

 

Ammi tace “Afnan” a hankali ta dago kanta hararar ta Ammin tayi ta ce “Bana ce maki in zaki shiga guri ba kiringa yin knocking ko sallama,amma ina”.

 

 

 

Kwal kwal Afnan tayi da ido ta ce “Kiyi hakuri Ammi bazan sake ba ,sauri nake kar Abu ya tafi ya barni ”.

 

 

 

Girgiza kai Ammi tayi ta ce “Karma ki gyara ma kicigaba kuma tsaya kiji duk saurinki sai ya ci abinci zaku fita”.

 

 

 

Alhaji Faruk ne ya ce “Kai Khadija ki mata hakuri bakya ganin yarinya ce ”

 

 

 

Galala Ammi tayi tana karewa Abu kallo ta ce “Haba Alhaji Afnan dince zaka kirata da yarinya shekara goma in bata gyara ba sai yaushe zata gyara ? ”.

 

 

 

Abu bai sake cewa komai ba yayi shiru dan ta wannan bangaren Ammin Afnan ta fishi gaskiya.

 

 

 

Kallon Afnan ya yi ya ce “Mamana taso mu muje muci abincin”tasowa tayi daga kan gadon ta zo kusa dashi kama hannunta yayi suka nufi kasa inda Hajiya Khadija ta mara masu baya zuwa dining dinsu dake kasa serving nasu bayan su gama cin abincin ne ya mike ya kallon Hajiya Khadija yana murmushi irin nasu na manya ya ce “To Hajiya zamu wuce sai mun dawo”.

 

 

 

Ammi ta ce “Adawo lafiya, Allah ya tsare hanya, ka gaishe da Nannen.

 

 

Ya amsa da “Zataji yaja Afnan suka fice”

 

 

*GIDAN NANNE*

 

 

“Ahhh ga manya baki ga manya baki ga takwara ga takwara”wata tsohuwa ce zaune akan wata kayatacciyar kujera mai kyau ta dai-dai zaman mutum biyu sai murmushi take tana yake baki.

 

 

 

Da gudu Afnan taje ta fada kan jikinta Nanne ta ce “ke ke Yar’nan dagani karki karasa mun yar kafartawa”.

 

 

Tashi Afnan tayi tana chuno baki gaba mutanen falon suka sheke da dariya wanda ya dada bata ma rai.

 

 

 

Nanne ce ta janyo ta jikin ta tana fadin “Rabu dasu dama so suke suji kanmu kuma baza suji ba,yanzu ma kuskure ne,murmushi Afnan tayi ta ce “Yauwa tsohuwas tawa”

 

 

 

Murmushi Abu yayi anan ne ya gaishe da mahaifiyartasu Hajiya Nanne yake tambayar ya jikinta ,nan yar autarsu Maryam da ta zo daga gidanta bayan ta gaishe da Yayan nata ta kalli Afnan ta ce “Hajiya Afnan ba magana ko?” dauke kanta Afnan tayi tana cuno baki gaba wanda ya riga ya zame mata jiki tsabar shagwaba.

 

 

 

Abu ya ce “Ahh ke kuma Maryam meya hadaku da mutuniyar ki ?, yau kin taro match ba gola”

 

 

 

Maryam ta ce “ohhhhh ni nama manta alkawarin dana mata cewar zan aika mata da chocolate ,ai sai amun hakuri gashi nazo da chocolate din”

 

 

 

Ai tuni Afnan ta tashi daga kwanciyar da tayi akan cinyar Nanne ko bari batayi ba Maryam din ta gama rufe bakinta ba ,ta je gurin Aunty Maryam ta ce “ina chocolates din Aunty?”

 

 

 

Maryam ta banka mata hararar wasa ta ce “Baki gaisheni ba zan baki abuna”.

 

 

Da sauri Afnan ta ce “Aunty Ina wuni”nan Maryam ta kyalkyale da dariya ta janyo hand bag dinta ta kwaso chocolates din kala kala,su Snickers ne ,bounty ne da sauransu ta mika mata kafin kiftawa da bismillah ta sha chocolates sun kai biyar zata bude ta shidan ne, Aunty Maryam ta kwace tana fadin “Ta isa haka abarwa anjima kuma” hade rai Afnan tayi ,sai kuma ta hade hannayenta biyu alamun hakuri ,ta marairaice fuska ta ce “Please Aunt one moreeee” da kyar ta lallabata ta kara mata guda daya”.

 

 

Chan Afnan tana ta waige waige ta leka chan ta leka chan fridge dake falon ta nufa ta bude ta hau dube dube chan idonta ya sauka akan wata damammiyar fura da nono hannun tasa ta dauko .

 

 

 

Dawowa tayi gurin su Nanne ta zauna a gefen ta ta ce “Tsohuwas wannan fura da nonon fa?”

 

 

 

Nanne ta ce “Ohhh ni na manta ma,naki ne dazu na zauna na dama maki da hannu na dan nasan zaki so shi,nasa maki fridge dan yayi sanyi”.

 

 

##########

 

 

“Nikam Yaya in tambayeki Ina wannan tsohuwar surukarki tana nan har yanzu da wannan halin nata?”.

 

 

 

Hajiya Zainab ta ce ”Hmm kijiki kema Nafisa mai hali dama baya fasa halinsa ai ba a chanjawa tuwo suna ,ni wallahi nagaji da ita so nake kawai ta sheka ma,ta dauki son duniya ta dorawa waccen shegiyar yar mai idanuwa kamar na mayu ke kya zata a kanta aka fara haifar mata jika in kika ga yadda take yin nan nan da ita sai kinsha mamaki ita da uwarta ni kuwa da yata kota mu ba ayi,shi dama waccen gantalallen tun yaushe suka asirce mini da ,kafin yazo gurina ma ana dadewa ,sai nayi magana sai ya wani ce aiki aiki saboda shi ya kawo aiki”.

 

 

 

 

*MORE COMMENT*

*MORE TYPING…….*

 

 

 

~Addeejeeh~

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.