Hausa Novels

Ahali daya complete hausa novel

Ahali daya complete hausa novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

AHALI D’AYA*

*_{auran bazata mapi k’ask’anci da wata irin rikitacciyar rayuwa mai d’auke da zallar k’iyayya}_*

 

 

 

 

_Written by_

*Mareeyeart lawal* 💞

 

 

 

 

_In dedication to my lovely ones_ 😍

 

 

_Bismillahirrahmanirraheem_

 

 

 

Page 1

 

 

 

Kyakykyawar matashiyar budurwa ce data amsa sunanta ajin karshe, wadda hutu dajin dadi y taemaka sosae wajen kara futo da asalin kyawun nata, shiryayyen bedroom ne da aka kawata shi tamkar a kasar Italy, komae na dakin Fari ne sol in aka dauke bedsheet dinta d yake Brown

 

Kallo d’aya zaka gane cewar bata cikin walwala kamar yadda yake a saman fuskarta

 

Fara ce sol doguwa ba kuma can can d’in nan ba, tana da Kyakykyawar kirar jiki irin ta matan da suka amsa sunan su na mata

 

 

Sanye take da tsadaddiyar abaya milk, ta yane kanta da siririn gyalen rigar, k’afarta Sanye da black hill shoe hannunta kuma rik’e da wayarta mae daraja ta farko

 

 

Zaune take gefan bed dinta tana danna wayarta, lokaci bayan lokaci tana duban makeken agogon dake manne a bangon dakin nata, mik’ewa tsaye tayi tana jan tsaki a karo na ba adadi

 

Kwan! Kwan!! Akayi knocking kofar ta, ta dago dara daran idanunta ta xubawa kofar kamar bataso ta bude bakinta cikin k’asa k’asa d murya tace “yess! Come in”

 

Murda handle din akayi, wata matashiyar budurwar da bata huce shekarunta ba ta bayyana, itama Kyakykyawa ce ba laifi

 

 

Shigowa tayi fuskarta washe da fara’ah tana kallonta kapun tace, “woow dear kinga yadda kikayi kyau kuwa? Gsky dole ma yayana y sake rikicewa idan ya ganki”

 

 

 

Tabe baki tayi tana mata wani irin kallo kafun tayi taku uku zuwa gabanta kamar baza tace komae ba sai kuma tace, “tun d’azu abie yake kirana, yy muhsin sai jiranmu yake kuma kinsan ni bansan ko ina ba a garin nan, zaman me kikayi fareeda?”

 

“Am sorry plz dear nad’an tsaya k’arasa wani d’an aeky ne”

 

“OK” abinda ta iya pada kenan ta d’auka key d’in motar ta tayi hanyar futa

 

 

 

Tafe suke itada fareedan tana ratsa falukan gidan har ta k’araso zuwa ga falon ammynta

 

 

Batare da tayi knocking ba ta murd’a marik’in k’ofar ta shiga

 

 

Shiryayyen parlor ne da aka k’awatashi da kujeru y’an gaske, da tumtum d carpet carpet tamkar a kasar larabawa

 

 

Daga chan kan crossing na hango wata matashiyar mata zaune gabanta bowl ne d’auke da fruits, tana ci tana kallon news channel, gefan ta kuma kaskone na turaren wuta yana tashin kamshy

 

 

 

Kallo d’aya zaka gane ba asalin bahaushiya bace, kamarta da yarinyar tamkar an tsaga kara

 

 

A kusa da ita yarinyar ta zauna ta d’auki inibi guda d’aya tasa a bakinta

 

 

Fareeda ma gefan ta ta zauna tare da russunawa tana gaishe ta.

 

 

Cikin gurb’atacciyar hausarta mara kyau ta amsa mata puskar ta washe da fara’ah.

 

 

Ta d’an tambaye ta y’an gidan su da lafiyar kowa na gidan kafun ta juyo da kallon ta ga tilon y’ar tata

 

Cikin harshen larabci take tambayar ta “ya akayi ne Arfah dama baki tafi ba?”

 

 

Yamutsa fuskar ta tayi batare da tace komae ba ta mik’e tace, “Ynx zamu tafi ammy”.

 

 

“OK habeebty ina phatan wannan karon komai yazo k’arshe kapun abbunki ya dawo”.

 

 

 

Kae kawae ta iya gyad’a mata ta sumbaci hannun ta tayi gaba

Fareeda ma bin bayanta tayi bayan tayi ma ammyn sallama

 

Da addu’a ta bisu, suka amsa ta da amin su duka

 

 

Gurin da aka tanada don adana motocin gidan ta nufa

Tamkar gurin Saida motoci hk aka jera motoci masu matuk’ar kyau da tsada da d’aukar hankali a gurin

 

Direbanta ya taho da hanzarin shi ya d’an russuna yana tambayar ta, “ranki shi dad’e ena………”

 

Da sauri ta katse mishi hanzari ta hanyar d’aga mishi hannu

 

Fareeda ce tace mishi, “karka damu malam saddiq ena ganin da kanta zatayi driving d’in”

 

 

“To to ba damuwa Allah ya tsare hanya ya kiyaye ya kaiku lpy ya dawo daku lpy”

 

 

A driver seat ta zauna Fareeda kuma ta kewaya gefan ta ta shiga

 

 

Nan danan mae gadi ya wangale mata get ta nufi hanyar futa a 360

 

Har zata huce su sai kuma ta tsaya, kusan ma’aikatan gidan maza ne a jere wajen d’akin mai gadin, duk addu’a suke mata ta adawo lpy

 

 

 

“Fareeda ena jakata”

Ta tambaye ta batare data kalle taba

 

Mik’o mata jakar fareedan tayi ta karb’a

 

Kud’i ta zaro masu yawan da ba tasan adadin suba ta mik’awa baba mae gadin

 

“ku duka wannan”

 

 

Tana fad’ar hkn ta huce batare data tsaya ko sauraron irin godiyar da suka soma jera mata ba

 

 

 

Wani hadadden eatry suka nufa Wanda da taemakon fareedan ta kaisu gurin.

Cikin takun ta daya ke nuna zallar aji da k’asaita ta shiga cikin k’awataccen gurin cin abincin

D’an tsayawa tayi tana bin ko ina na gurin da kallo step by step

 

A (V I P) table suka hango shi zaune yy odar drinks sae duba agogon hannunshi yake, da alamu shima zaman jiransu yake

 

 

Bata damu da irin mayen kallon da y’an gurin suke binta dashi ba ta nufi inda muhsin d’in yake Kae tsaye

 

Ta samu kujerar dake opposite d’in tashi ta zauna ta kuma d’ora k’afar ta d’aya kan d’aya

 

 

Muhsin da tun data tunkaro inda yake ya zuba mata idanu yana kallo sai kawai ya samu kanshi da sauke b’oyayyar ajiyar zuciya

 

 

“Barka da isowa sarauniyar mata”

Ya fad’a yana jifanta da wani irin miskilin kallo

Wani irin duba tayi mishi, ba laifi ya sake yin kyau fiye da da, sai dai fa ya d’an yi rama, ba tace komae ba ta d’auke idanun ta daga kanshi

 

Fareeda da take tsaye daga bayanta ce tad’an rankwafo ta kunnan ta tace, Arfah plz a d’an sassauta ma yayana”.

Wani irin murmushi tayi wanda ya kusan tafiya da muhsin da tun da tazo gurin ya kasa samun nutsuwa

 

 

K’asa k’asa da muryarta tace, “never mind dear koda yaushe kinsan ni ina aiwatar da abinda yake cikin zuciyata ne kadae”

 

“Na sani kam nidae fatana Allah yasa zuciyarki ta amince da yayana”.

 

 

Wani murmushin ta sake yi a karo na biyu ta kad’a idanunta tace, “kina son kanki da yawa Fareeda”

 

 

Yar dariyar fareedan tayi tace, “to ae dole ne bcs ur soo classy my frnd ynx dae bari nad’an baku guri koh?”

OK amma kada kije da nisa, in less than 20 mnt ma zamu gama komae”

 

“OK” shine abinda Fareeda tace tayi musu sallama tayi gaba

 

 

 

Ko bayan tafiyar tama shiru ne y biyo baya

 

Shi yana satar kallon ta ita kuma tana ta buga game a waya

 

After lyk 5mnt muhsin yad’an dake yace, me za’a kawo miki Arfah?”

 

“Ruwa” abinda ta fad’a kenan ba tare data d’ago ta kalleshi ba

“bazakici komai ba, ko snacks hk?”

“Noop ruwan ma is owk”

Ta bashi amsa a karo na biyu batare data d’ago ta kalle shiba

 

 

Duk da bae so hakan ba amma hk y kira waiter ya fad’a mishi abinda za suyi order

 

Shiru yaci gaba da wanzuwa a tsakanin su har aka kawo mishi bottle water d pizza da yayi order

Da kanshi ya zuba mata ruwan ya mik’a mata

 

Sai data d’anyi wasu seconds sannan ta mik’a hannu ta karb’a tace, “thnks”

 

Cupin ruwan ta ajiye tare da wayar tata sannan ta fuskan ce shi tace, “kace akwai maganar d zamu tattauna, gashi lokacin ka yana ta tafiya, ko daman ka kirani ne Don kawaii kayi ta kallo na?”

Har yanzu murmushi ne a saman fuskar shi yace, “eh ai ko bance miki komae ba iya ganinki danayi yanzu ma kin gama min komai, wllh arfah ban tab’a jin son wata mace a raena irin yadda nake jinki ba, ena sonki fiye da yadda kalmomin bakina zasu fad’a, amma bansan me yasa ba kin kasa fahimtar irin son da nake miki har yanzu, kin kasa ki bani cikakkiyar damar dazan nuna miki gundarin abinda yake cikin zuciya ta”

Shiru yad’an yi yana sake sauke b’oyayyar ajiyar zuciya kapun yaci gaba

“Arfah don Allah ki taemake ni ki sanar dani gundarin abinda yake cikin ranki, badon komai ba sai don nasan meye matsayi na a gurinki, idan kina lissafi yau auren mu saura wata uku ya rage, kuma har yanzu kin ki cewa komai, wllh fatima shirun nan naki yana k’ona nine can cikin raina, a kullum ena kwana ena tashi ne da fargabar rashin sanin hukuncin da zaki yanke game da hadin auren mu, wllh fatima rasa ki a gareni dai dai yake da babbar asarar rayuwa ta da bazan tab’a iya maye gurbin ta ba”

 

 

Mikewa tsaye yayi ya matsa kusa da inda take zaune yana kallon cikin idonta yana sake karfafawa kanshi gwiwa ya d’an rankwafo ta gaban ta, ya d’ora hannun shi saitin zuciyar shi, yayi narai narai da kwayar idon shi yaci gaba da magana

“plxxx arfah kice wani abu a gareni kiji tausayi na saboda zuciya ta tana gab da bugawa akan soyayyarki”.

Sai da ta d’an ja baya sannan ta d’ago idanunta ta kalle shi, gaskiyar abinda ya fad’a take gani muraran a kwayar idon shi.

Dauke idon ta tayi daga kallon shi da sauri, ta dauk’i ruwan daya bata ta ajiye ta kafa kai tana sha da sauri da sauri tana sauke ajiyar zuciya a jejjere.

Yaya fahad ne ya fad’o mata a rae, shine mutum na farko daya soma furta kalmar soyayyah a gareta, kuma shima har ynx bata san matsayar su ba

 

Idan har ta amince da soyayyar muhsin hkn na nufin ta watsar data fahad kenan.

Ga kuma mgnr da sukayi da ammyn ta, kuma ita har ga Allah a yau tazo ne da k’udirin tayi ma muhsin rashin mutuncin dako sunan ta bazai so ya sake tunawa ba, ta kawo k’arshen wannan had’in alak’ar tasu, amma da kalaman shi ya kashe mata kwarin gwiwar ta gaba d’aya, ya sanyayar mata da jiki.

Tabbas muhsin ya cancanci ta bashi duk wata dama, sai dai ita har ynx batajin soyayyar shi a cikin zuciyar ta ko kad’an kuma ko ba haka ba ita batajin zata iya auren shi ta zauna matsayin matar shi, ita a Yaya take kallon shi har yanzu.

“Wayyo Allah”. Shine abinda bakin ta ya furta batare data shirya ba.

“Arfah kina jina kuwa?'”.

Da sauri ta mik’e tsaye kamar wadda aka tsikara wa allura, ta d’auki wayarta da jakarta ta nufi hanyar futa daga gurin cin abincin.

Da sauri shima ya sallami masu gurin ya rufa mata baya, sai dai ko kafin ya futo har ta shige motarta tayi mata key.

A wajen wasu flowers ya zauna ya dafe kanshi da duka hannuwan shi, daman ya sani bazai tab’a samun arfah cikin sauk’i ba, saboda mace ce me matuk’ar jin Kae da izgilanci, shi a haka ma sai yaga kamar ta d’anyi laushi a kan yadda take da.

 

**********

 

B’angaren Arfah kuwa sai da ta d’anyi tafiya mai neesa sannan ta tsaya ta kira fareeda.

Ta d’anyi jiran ta na d’an wani lokaci sannan ta k’araso suka huce.

Kallo d’aya da fareeda tayi mata ta gane har ynx ranta a b’ace yake, don haka sai bata ce mata komai ba.

 

Wani irin gudu take shararawa dasu a tsakiyar titi na futar hankali.

Ita dae fareeda addu’a kawai take Allah ya kaisu gida lpy

Sai da suka zo daf da kwanar da zasu shiga anguwarsu ta soma slow a hankali.

Karaf!! Batare da zato ba bare tsammani ta daki wani mai napep daya shawo kwanar shima.

Take napep d’in ta hantsila duk matanen da suke ciki suka zubo k’asa wanwar.

Tsirarun mutanen da suke wajen ne suka d’auki salati kapun su taho da hanzari Don su kawo musu d’auki.

 

A gefe ta d’anyi parking ta kife kanta da sitiyeri, fareeda ma numfashi take mayarwa tana hamdala da Allah ya tak’aita.

Gurin har ya tara mutane ana ta hayaniya.

Wani mutumi ne ya kwankwasa mata glass.

 

Sai a lokacin ta d’ago, mutane sun taru sosai a gurin. “au bazaki futo ba ma kenan, kina kallo kin buge mutane Amman dan rashin mutunci kinja kinyi zamanki a mota, haba ku dinga yima kanku adalci mana”. Wani d’an dattijo ne yake mata wannan maganar.

A hankali ta bud’e murfin ta zuro k’afarta waje ta futo tana binsu da wani irin kallon k’yama.

Fareeda ma futowa tayi ta jingina da jikin motar.

Wani mutumi ne ya k’araso inda take tsayen ya soma mata magana, “dama haka kuka iya asararru, an tara muku dukiya har kun rasa ma yadda zakuyi da ita, shine kuke dakko motoci kuna taka talakawa bayin Allah, to wallahi akwai Allah munsan shi zai mana hisabi daku ranar gobe kiyama, gantalallu marassa tarbiyya”.

 

Tun daya soma mgn take kallon shi, duk daba wani jin hausa take yiba sosai Amman tasan ba magana mai dadi yake fad’a a kanta ba

Suma sauran mutanen gurin caaa sukayo masu da maganganu marasa dad’i.

Take kuma ranta ya kuma b’aci, komawa tayi cikin motar ta d’auko jakarta, Fareeda ta zagayo gefan ta tana tambayar ta cikin harshen nasara, “me kike k’ok’arin yi haka Arfah?”.

“Ki kyale ni Fareeda wad’an nan mitsiyatan mutanen, I know exactly what there problem is”.

Rik’e hannunta Fareedan tayi tace, “a’a Arfah ba haka zakiyi ba”, fizge hannunta tayi daga ruk’on da tayi mata tana jifan ta da wani mugun kallo.

Ita ma Fareedan zuwa ynz ranta ya soma b’aci da d’abi’un arfan Don hk a zafafe ta shige cikin motar.

Tana kallon yadda ta watsa musu tulin kud’in dake cikin jakarta (tamkar an watsama Kaji hatsi haka mutane suka hau rububi suna d’iba) “nasan wannan shine matsalar ku”.

Tana fad’ar haka kuwa ta baro su zuwa inda motar ta take, Ynx kam a hankali take driving d’in har suka k’arasa gida

 

 

Tana yin parking kuwa Fareeda ta futo kamar dama jira take tayi cikin gidan da hanzarin ta

 

Kae tsaye hanyar part d’in ammyn tayi, ita kuma arfah tayi nata part d’in.

 

Siririn gyalen kawai ta ajiye ta zare ribbom d’in data d’aure gashin ta.

Take kuwa gashin ta ma’abocin tsawo da santsi ya bayyana sai d’aukar ido yake saboda Gyaran da yasha.

D’aya daga cikin ma’aikatan kitchen d’in gidan da wani lokacin takan dan yi mata aiki ce data ga shigowar ta ta kwankwasa mata k’ofa, sai da tayi wasu sakanni sannan da kyar ta bata izinin shiga.

Gabanta tazo ta russuna tana tambayar ta, “ranki shi dad’e ko akwae abinda za’ayi miki”.

 

 

Kallon ta tayi daga sama har k’asa tana nazarin ta kapun ta buda bakinta tace, “me yasa yau ramlan bata zo ba?”.

Mai aikin ta sake russunawa sosai tace, “Neema ban sani ba gsky”

 

Wayar ta da take ringing ta d’auka ta zubawa ido tana kallo bata kuma d’aga ba har ta katse, haka akayi ta kira tana kallo har sai da aka jera mata missedcall kusan shida, sannan n daga k’arshen ta d’aga.

 

 

“plz Yaya ena d’an wani uzuri ne ynz, can we talk later?”.

 

Ajiye Wayar tayi bayan y bada amsar da bamu ji ba, har lokacin mai Aikin nan tana nan a durk’ushe inda take.

“ki had’a mun ruwan wanka”. Ta fad’a can k’asan muryar ta.

“to ranki shi dad’e ruwan kamar yaya?”.

Kwanciya tayi kan bed d’in tace, “kamar yadda ramlah take had’amun”.

“To ranki shi dad’e”.

Mai aikin ta pada ta huce tana patan a rabu lpy

 

After tyke 3mnt maid d’in ta sake dawowa tace an gama ranki shi dad’e.

Mik’ewa tayi ta nufi bethroom d’in, lumshe idanun ta tayi me aikin tana hamdala, don a yanzu kam an rabu lpy saura karo na gaba kuma

Ta dauk’i tsawon lokaci a ciki sannan ta puto d’aure da towel fari.

Fareeda ta iske zaune tana waya a saman doguwar kujerar dake d’akin, d’auke kanta tayi tana tabe baki.

Kai tsaye wardrobe d’in ta tayi ta dauko doguwar riga marar nauyi ta zura

 

Hot coppe d’in ka’idar da take sha duk farkon dare ta tarar a kan bed site drower.

Sai data soma gabatar da sallar magrib (Wadda duka raka’ah ukun cikin few seconds akayi su, kome aka karanta ma oho😂)

 

Coppe d’in ta ta d’auka ta soma sha, tana kallon Fareeda ita ma tayo alwalar ta soma gabatar da sallarta.

Sai dai akwae banbanci mai tarin yawa tsakanin tata data arfan, don ita har addu’ ah ma tayi bayan ta idar.

 

 

Haka suka ci gaba da zama babu wanda yace da d’an uwan shi kanzil, sai kallon kallo kawae.

 

 

Ko dinner ma yau ba tare sukayi ba, hasalima ita arfah bata ci komai ba ta kwanta.

 

***********

Washe garin ranar ya kama weekend.

 

 

Kiran sallar asubar farko Fareeda ta tashi, da kamar ta tashi arfah sai ta tuna ko lpy lpy suke ta tsani ta tashe ta da asubar fari irin haka.

Don hk sai kawai ta kyale ta

 

 

K’arfe 10:30 dae dae alarm ya tashe ta.

Fareeda ta kalle ta, ita har tayi wanka tayi break, amman don asara sai ynx ita take tashi.

Bathroom ta nufa, tana shirin shiga daya daga cikin masu aikin gidan kuma tana shirin futowa, cikin rashin zato bare tsammani sukayi karo.

Arfah ta dafe goshin ta da sauri, matar tayi saurin zubewa k’asa tana jera mata sannu da ban hak’uri, wani irin kallon tozarci da k’yama take bin matar dashi, kafin tayi mata alama da ta mik’e.

Tasss! Tasss!! Ta sauke mata tagwayen maruka a saman fuskar ta, “wace ce ke? Waye ma ya baki izinin ki shigo mun har bedroom d’ina? next time idan kina tafiya sai ki dinga lura da gaban ki mtss! Idiot”.

Hawaye ne suka sulmiyo ta saman fuskar matar da kad’an ya rage ta haifi kamarta. Har ta huce ta sai kuma ta dawo da baya, tana nan tsaye inda ta barta. “sannan ena mai gargad’in ki da kada ki sake wannar k’azamar kafar taki ta kuma tako mun room d’ina”.

Daga haka Bata ko sake bi ta kanta ba ta huce zuwa ciki

 

Fareeda da komai ya faru kan kunnen ta, ta mik’e matar tana futowa tayi saurin tarar ta tana bata hak’uri.

Matar ta share hawayenta tace, “kada ki damu y’ar nan, nima shishshigi na ne ya jawo mun, sbd ba nice mai aikin ta ba kema kin sani, gani nayi shiru shiru ramlan da take mata aikin bata zo ba, kuma gudun kar tayi laipi shine ni na amshe ta, ynz kuwa kinga saina kiyaye na tsaya iya matsayi na”.

Girgiza kai fareeda tayi ta koma ta zauna cike da mamakin hali irin na arfah.

 

 

 

 

_Comment_✍️

8/13/22, 8:47 AM – Merhreeyeart❤️: 🏡 *AHALI D’AYA*

*_{auran bazata mafi k’ask’anci da wata irin rikitacciyar rayuwa mai d’auke da zallar k’iyayyah}_*

 

 

 

 

_Written by_

*Mareeyeart lawal*💞

 

 

 

_In dedication to my lovely ones_🥰

 

 

 

 

Page 2

 

 

Fareeda tana kallon ta bayan ta futo wankan ma, abin haushi sai data gama gudanar da duk wani abu data keyi a kullum na safiyar Allah sannan ta zura hijab ta fuskanci alk’ibla.

 

Tsabar takaici Fareeda bata san lokacin data ja tsaki ba ta mik’e ta fuce daga dak’in.

Kamar me yin adungure haka ta duddungura ta sallame, ko cire hijab d’in batayi ba ta fuce daga cikin d’akin a matuk’ar hasale, a hankali take ratsa guri guri na cikin gidan batare data tsaya ko lura da irin gaisuwar da ma’aikatan gidan suke mata ba.

Ganin ta kusa karad’e gidan kaf bata gan taba sai kawae ta nufi part d’in yaya fahad kai tsaye, idon ta ya rufe, ta manta da yadda kwana2 take ta kakkaucewa haduwar su, rabon ta da part d’in shi tun ranar daya furta yana sonta, sai gashi yau fareeda ta ja ta.

 

 

Ba sallama ba nck kawai kanta tsaye ta murd’a kofar ta shige.

Wooww wani irin parlor na gani na alfarma, da aka shirya shi da wasu irin Royal chairs masu matuk’ar kyau da tsada, zaune suke ita da fahad saman d’an madaidaicin dinning d’in dake arewacin parlor, hira suke shi kuma yana cin abinci, rabin hirar ma duk ita take yin abinta don shi sam hankalin shi ma baya kanta.

Ta juyawa kofar baya shiyasa sam bataji shigowar arfah ba sai ji tayi kawai anyi baya da ita.

Hantsilawa tayi daga saman kujerar tayi baya zata fad’i Allah yasa fahad yana kusa yayi saurin tare ta bataje kasan ba.

 

Da mamaki fareeda take kallon ta, “ni zaki ma haka arfah? Me nayi miki? Saboda kinga duk abinda kikeyi ena binki kamar hadimar ki”.

Wata irin harara arfah ta wurga mata kamar idonta zai fad’o kapun ta soma magana, “kin fi kowa sanina fareeda kin san abinda nake so da Wanda banaso, to how dare will u just hiss at me?”.

“OK! Haka ne? to shikenan yaa fahad zaka zama shaida, daga yau zan tafi bazan sake dawowa gidan nan ba wllh tunda har arfah zata iya rufe ido ta manta da amincin dake tsakanin mu farat d’aya tayi mun rashin mutunci irin wannan sbd tayi abinda bai kamata ba nayi mata tsaki!!!”.

Fuuuu!! Ta nufi hanyar futa daga parlon, da sauri fahad yabi bayan ta yasha gaban ta, “wai meye haka kukeyi ne fareeda? Me yasa har yanzu baza kusan kun girma bane?”.

Idonta ne ya tara hawaye tace, “kana kallon irin abinda arfah take yimun yaa fahad, kullum tana kaskantar dani kamar ta fini da wani abun, dame ta fini kyau gata asali ko ilimi? To akan me zan ci gaba dayin shiru tana kaskantar dani kullum”.

Hannun ta ya rik’o ya zaunar da ita saman d’aya daga cikin kujerun falon, ya juya zuwa ga arfah, tana tsaye yadda ya barta sai dai fa duk jikinta da alamu yayi sanyi.

Hard’e Hannun shi yayi kawae ya tsaya yana kallon ta, shi kanshi al’amarinta wani lokacin yakan bashi mamaki kamar wata me ifritae, yaa shagala da kallon ta ta yadda har ya manta abinda ya kawo shi gurinta.

 

Sai data mik’e hanya sannan ya farga yayi saurin dakatar da ita ta hanyar rik’o hannunta da yayi, ta fuzge hannun ta da sauri taci gaba da tafiya, rufa mata baya shima yayi cikin saurin.

 

Wani irin k’ululun bak’in ciki ne ya tokare zuciyar fareeda, kamar ta tashi ita ma ta bi bayansu takeji.

Bayan kusan minti 2 da futar su sai gasu kuma sun sake dawowa taren, ita tana gaba shi yana biye da ita, sai yanzu na lura da kammannin shi sosae.

Fari ne sol tamkar yadda arfan take, kyakkyawa kuma na gaske da ya isa ya shiga gasar sarakunan kyau, dogo ne mai matsakaicin k’ibar jiki.

Sanye yake da jallabiyya ash colour data sake futo da asalin kyawun kalar shi.

 

A kujerar dake nesa data fareeda ta zauna, shi kuma ya zauna saman d’an k’aramin table d’in dake kusa da inda arfan take zaune.

Shiru sukayi su duka sae sautin kukan fareeda daya ke futowa kad’an kadan, wanda kusan da 2 takeyi.

 

Fahad hankalin shi nakan arfah da tayi mirsisi ta share maganar da sukayi a waje.

Sai data d’auki tsawon lokaci kafun ta bud’e bakinta da kyar tace, “kiyi hak’uri”.

Kallon ta fareeda tayi kamar ma ba ita tayi maganar ba, la shakka Fahad ne yasata ta bata hak’urin nan, Don hk sai kawai ta mik’e ta fuce daga d’akin.

 

Babu wanda yayi yunk’urin dakatar da ita har ta fucen, ita ma arfan mikewa take shirin yi Fahad yayi saurin dakatar da ita, a kusa da ita yayi masauki yana bin kwayar idon ta da kallo.

“Arfah me yasa kike yimun haka ne? Sbd Neema kin tsaneni bakya son ganina koh?”. Cikin harshen larabci yake mata wannan maganar.

“tabbas dani na d’orawa kaina soyayyarki to da tuni na dad’e da cire ta na jefar nima na huta, to sai dai kash hakan bayin kaina bane, soyayyarki tun bansan kaina ba take d’awainiya dani, ina ganin kamar zan iya shanyewa a lokacin da naji labarin sa ranar ku da muhsin, sai dai hakan ya gagare ni, ni kad’ae nasan yanayin da nake ciki kwana2 nan da kika b’oye kanki a gareni”.

Hada hannuwanshi 2 yayi alamun roko yace, “Plzz arfah ko baki amince da soyayyata ba ki dinga bari ina ganinki ko gaisawa ma mu dinga yi, tunda yanxu nasan yazame mun dole na hak’ura dake, Amman Don Allah kada ki datse igiyoyin zumuntar da take tsakanin mu arfah, don ni yanzu na hak’ura dake nasan hakan shine k’addara ta”.

Maganar shi ta k’arshe ta matuk’ar sanyayar mata da jiki duk da yadda taso ta dake amman sae ta kasa.

Idon ta ya ciko da hawaye ta d’ago da kyar tana kallon shi.

“ban tab’a jin k’iyayyarka a raina ba ko dede da second, hasalima Idan ka d’auke abie da ammiena babu Wanda nakeji a raina kamar ka, kasani akwae shak’uwa mai tsanani tsakanina dakae, bansan yadda zanyi bane abun ya zomun wani banbarakwae da naji babu zato ka nuna cewar kana sona, na kasa amincewa da gaskiyar cewa yayana yana sona yayana da nake d’aukar shi tamkar uwa d’aya uba d’aya……. ”

Sai ta kasa k’arasawa saboda wani irin kuka daya taho mata.

 

Shi kanshi da da dama da kukan zaiyi ko yaji sauk’in abinda yake ranshi, shi a yanzu babban abinda yake d’aga mishi hankali shine auren ta saura wata 3, ada akwai Kyakykyawar gaisuwa ta mutunci tsakanin shi da muhsin amma a yanzu ko ganin shima baya son yi, gaisuwar ma dakyar yake tsayawa suyi.

“Innalillahi wa’ inna ilaihi raji’un, allahuma ajirni fil musibati waklifli khairan minha”.

Abinda ya fad’a kenan ya dafe kanshi da hannuwan shi 2

 

 

Sun d’auki tsawon lokaci a haka, sai dan sautin kukan arfah da yake tashi kad’an kad’an a parlon.

Mikewa tayi daga k’arshe duk da yadda take ganin uku uku ta nufi hanyar futa.

Da kyar ta iya kai kanta saman aikuwa a k’arshen stairs din ta zube tana sauke ajiyar zuciya.

Dai dai lokacin da fareeda ta futo da jakar kayanta, ta ganta dafe da k’arfen benen, har zata karasa gareta sai kuma ta tuna da kalaman da taji fahad yana fad’a mata, take wani bakin cikin ya sake lullub’eta taji tamkar ta shak’e ta ta mutu kowa ma ya huta.

Muryar fahad daya biyo bayanta taji yana fad’in, “subhanallah arfah me yake faruwa? fareeda kina kallon yanayin da take ciki kuma”.

Da sauri ta saki jakar hannun ta tare da saisaita yanayin ta ta nufi arfan da sauri, sai dai kash ko kafun ta k’arasa ma tuni fahad ya isa yayi mata kyakykyawan masauki a jikin shi yana tambayar ta, “meye ne ya same ki baby?”.

Ta kasa magana ma sai jujjuya kanta da take kawae, taimaka mata yayi ganin yanayin jikin nata na sake ta’azzara kamar ciwonta zai tashi, suka nufi part d’in ta yana rik’e da ita.

Wannan abu daya faru yafi d’aga hankalin fareeda fiye ma da abinda taji d’azu.

Bayansu tabi duk jikin ta a sanyaye, iya k’ok’ari fahad yayi wajen ganin ciwon ta baiyi nasarar tashi ba, ya samu jikin yayi sauk’i batare da wata matsala ba, bayan wasu yan mintina da kanshi ya had’a mata tea ya bata a baki da d’an chips, shima dakyar taci sai wani lallab’ata yakeyi ita kuma tana ta wani nannarkewa. Wanda fareedan take ganin kamar da gangan ma take yin hakan.

Daga k’arshe dai bedroom d’in ta ya rakata da taimakon shi kuma ta kwanta saman bed d’in.

 

Ya juya zai futa sukaci karo da ammie zata shigo, yanayin yadda ya ganta kad’ai ya bayyana mishi tasan halin da arfan take, a gigice take tambayar fahad, “me ya same ta fahad, me yasa Baku huce clinic ba ko ka kirawo likitan ta, kasan yadda ciwon ta yake inya tashi baya mata da sauk’i”.

“cool down ammie ba ciwon ta bane ya tashi kawai dai stress ne, kuma Ynx ma ta dawo normal”.

Karasawa tayi jikin gadon ta rungumo ta jikin ta tana tambayarta “habeebty fad’a mun ina ne yake miki ciwo? Fahad nidae ka kira mun doctor shuraem kawae”.

“Babu komai fa ammie ta dawo normal yanxu bacci kawai take buk’ata”.

Noop I will not believe you fahad zaka iya b’oye mun saboda kada hankalina ya tashi, ai fareeda ta fad’a mun komai, Plzz fahad ka kira mun doctor shuraem kawae”.

 

 

Kallon fareeda yayi suka had’a ido sai ta marairaice, “naji tsoro kada wani abu mummuna ya same ta shiyasa na kira ammien”.

 

D’auke idon shi yayi daga kanta yana sake jin tsanar ta a ranshi fiye da kima, gaba d’aya shi daurewa kawai yake mu’amala da ita Don shi sam batayi mishi ba gaba d’aya halinta na muna fukae ne a cewar shi.

 

Wayarshi ya d’auko ya kira doctor shuraem d’in don hankalinta ya samu kwanciya,

 

Kamar yadda fahad ya fad’a mata haka doctor shuraem ya tabbatar mata da ingancin lafiyar ta.

 

Sai lokacin hankalin ta ya kwanta ta kira abbie ta sanar dashi, yaso ta had’a shi da arfan ma suyi magana saboda yafi samun nutsuwa sai dai ta tabbatar mishi da bacci takeyi amman data tashi zata kira shi.

 

 

Yinin ranar duk haka suka yini suna tattalin ta da nuna mata kauna, fahad in banda masjid babu inda yaje yana ta gadin ta, data motsa shima zai motsa yana tambayarta yadda take ji.

Fareeda kam bak’in ciki kasa barin ta zama yayi a d’akin, sai a lokacin ta sake tabbatar da lallai bata da wayo, don ta kira ammie ne saboda ta nisan tata da fahad sai dai hakan baiyi wani a’mfani ba, k’arshe sai suka had’u ma har ammin suna tattalin ta da nuna mata k’auna.

A daren ranar fareeda ta tafi, duk yadda ammie taso ta hak’ura sam fareeda tak’i. Ganin ta hak’ik’an ce sai kawai tasa fahad ya kaita gidan madadin driver.

Sosai ammie had’a mata sha tara ta arzik’i kamar yadda daman ta kanyi mata a duk lokacin da tazo ta kwanan musu 2 zata koma gida.

Fahad badon yaso ba ya tafi ya kaita gidan Don shi tafiyar second d’aya ma baya son ta had’a su.

 

Zaune take saman gadon ta mik’e k’afafun ta, sanye take da pink night gown y’ar k’arama data tsaya iya k’aurinta, gashin kanta a d’aure a k’eyarta sai d’aukar ido yake, gaban ta d’an k’aramin bowl ne me d’auke da fruits, sai faman yamutsa takeyi ammie na zaune a gefan ta tana lallab’ata ta daure taci.

Cikin siririyar muryarta mai cike da shagwab’a tace, “Allah ammie na k’oshi in na kuma ci zanyi amai ne”.

“haba sweetheart yunwa fa zai dame ki cikin dare idan baki ci ba”.

Juwaya tayi ta kwanta tana ta yamutsar fuska “d’auke bowl d’in ammie tayi ta d’ora saman drower tace ,”to tunda baza kici ba ki tashi kiyi sallah kuma d’azu abban ku ya sake kira yana son yaji yanayin jikin naki”.

Mik’ewa tayi zaune tare da jawo wayarta zata kira shi, ammie tayi saurin kwace wayar a hannun ta” “maganar sallah fa nayi miki”.

 

Sai ta sake shagwab’e fuska, “ammie bani da lafiya ne fa”.

“Ok tunda baki da lafiya baza kiyi sallar ba kenan?”.

“to ai in na tashi jiri nake ji, plz ammie ki bani naji muryar abbie na”.

 

“Allah ya shirye ki baby ni bansan ranar da zaki girma ba, salla dai itace cikon addini” ta fada tare da mik’a mata wayar, ita kuma ta mik’e zata tafi.

“Plzz ammie ba yanzu bafa ki bari nayi bacci mana”.

 

Hararar ta tayi tace, “zaman me kuma zan ci gaba dayi? Ai kin warke baga shinan ma har zaki iya magana sosai ba”.

Sai ta soma bubbuga k’afa, “Allah ammie yanzu duk bakya ji dani kamar da, ni na k’agu hutu na ma ya k’are na koma schl”.

Dariya ta d’anyi tana kallon ta kafun ta girgiza kai tace, “ni dai har yanzu bansan ranan da zaki girma ba baby, Jiya ma kina ta bacci na shigo d’akin nan”.

Zata sake yin magana wayar ta ta d’auki ringing, ai da sauri ta d’aga ganin mai kiran nata.

Murmushi kawai ammie tayi ta fuce daga d’akin. Ita kam sosae ta d’auki lokaci tana waya da abbie d’in, daga yadda ta zage yau tana ta yi mishi hira ya sake tabbatar da ingancin lafiyar ta, daga k’arshe sai jin saukar numfashin ta yayi tayi bacci, koda yayi hasashen agogon Nigeria sai ya tabbatar da lokacin baccin ta yayi don daman yasan bata huce hakan.

 

*********

A cikin kwana ki biyun nan na sake fahimtar irin asalin tsantsar gatan da take dashi a gidan, on Monday fahad kacokan ya bada uzuri a gurin aeky don kawae ya zauna tare da ita, kulawa iya kulawa, haka gata ma iya gata, duk abinda take so a gidan to shi suma suke so, haka duk abin da ta tsana suma basa k’aunar ko had’a hanya dashi su sake, ta b’angare d’aya ne sukayi burus da ita shine maganar auren ta da muhsin, wanda tun farko sunsan ta tsani wannan had’in auren, Amman suka share ta, ba don komai ne ba kuma sai dan wata manufa tasu daban daban da suke so su cimma, ko meye wannan manufa?

 

 

Wannan kenan

 

******** *******

 

kamar yadda sunayen mu suka banbanta haka halayen mu ma suka banbanta, haka tsarin gudanar da rayuwar mu ma ya banbanta, akwae tazara mai nisa tsakanin yatsar tsakiyar yatsun mu da d’an k’aramin yatsan mu na hannu.

 

A lokacin da wani yake d’and’anar Zuma wani na can yana shan ruwan mad’aci.

D’an k’aramin madaidaicin gida ne me d’auke da ciki da falo maki manta guda2 sai fallen d’aki guda 1 da kuma sitting room Wanda k’ofarshi ta futa har waje, tsakar gidan shimfidar babbar tabarma guda1 sai d’an k’aramin kitchen da toilet guda2 na wanka dana masai.

 

Safiya ce misalin k’arfe 6:30 tsit gidan yake bakajin motsin komai sai sautin daddad’ar muryar shi da take tashin rera karatun alk’ur’ani mai girma cikin suratul a’araf.

 

A hankali na nufi inda wannan ki’ra’ar take tashi don ganin mai wannan murya tamkar balaraben k’asar saudiyyah.

 

Fallen d’aki ne mai d’auke da y’ar k’aramar katifa irin ta y’an makaran ta, sai drower da akwatin kayanshi guda1.

Siminti ne shimfid’e k’asan d’akin a share tadal tamkar a yada tuwo aci.

Ya shimfid’e darduma daga d’an gefan katifar yana zaune sanye da dogon wando na wani yadi mai sauk’in kud’i da farar singlet.

Abun dazai burge ka da wannan matashi shine duk wannan karatun yanayin shi daka ne, wato memorization.

Alarm d’in wayarshi ne ya dakatar dashi ta hanyar bada sauti.

Sai Ya jawo wani d’an k’aramin littafi da biro yayi d’an rubutu ya mayar saman drowar dake d’auke da tarin littattafai na addini dana boko, ya kuma dakatar da alarm d’in daga bada sautin.

Sai daya mik’e tsaye na samu nasarar k’are mishi kallo.

Kyakykyawan saurayi ne dogo ma’abocin k’irar k’arfi, kalar fatarshi choculet irin mai hasken nan, fuskarshi zagaye da irin d’an siririn sajen nan da matasa kanyi ado dashi, fuskarshi sai futar da annurin haske take da wani irin kwarjini na musamman.

 

Futowa yayi zuwa tsakar gidan nasu yana mik’a tare da salati, tsintsiya ya d’auka ya d’an tattaro d’akin shi duk da ba wani datti yayi ba sannan ya sake futowa tsakar gidan, share shi yayi tass! Ya wanko toilets d’in ya sharo kitchen d’in su nan ma ya goge.

Agogo ya sake dubawa, bakwai da y’an mintina har rana ma ta soma hasko tsakar gidan nasu.

Ruwan wanka ya had’a Sharp Sharp, duk yadda ya tsani yin wanka da ruwan sanyi haka ya zuba ya nufi bayin dashi, yana shirin shiga mahaifiyar shi ta bud’ e k’ofar d’akin ta ta futo. Kyakykyawar bafulatana fara tana yanayin kamanni da farouk d’in sosai, sai dai ita fara ce tas, duk da halin matsi na rayuwa da suke ciki Amman hasken fatar ta bai gushe ba.

Dawowa yayi ya d’an Russuna ya durk’usa yana gaishe ta cike da tsantsar ladabi.

Ta amsa shi cikin sakin fuska tana tambayarshi khadija bata tashi bane?,

“eh ummi banji motsin taba ina tunanin ko har yanzu jikin nata ne”.

“A’a to su kuma su haseena fa, bana son saukarcin banza fa da wofi, nufinsu yau baza suje makarantar ba” ta k’arashe fad’a tana nufar d’ayan d’akin da yake jikin nata tana fad’a, Shi kuma ya shige wankan shi.

 

Bai wani dad’e sosae ba ya futo yana d’an karkarwar sanyi ya shige d’akin shi, ummi dake durk’ushe a tsakar gidan tana fafutukar hura wuta tace, “wai wanka kayi da ruwan sanyi farouk? Madadin ka bari gashi ina ta sauri na hura wuta, gawayin ne ma bashi da kyau sosae”.

“ai sauri nake ne ummi kinsan kuskure kad’an yanzu sai su wulak’anta mutum”. daga cikin d’akin ya bata amsar.

Tace, “haka ne kuma muna fatan wannan karon Allah yasa a dace”.

“ameen ya fad’a daga cikin d’akin”.

 

Sauri sauri ya shirya ya futo tsakar gidan sanye cikin k’ananun kaya masu sauk’in kud’i, hannun shi rik’e da envelope da wayarshi y’ar k’arama.

Zuwa sannan ummi har ta d’ora tukunya a wuta, wata matashiyar budurwa da bata huci shekara 19 ba tana durk’ushe tana wanke wanke yayinda d’ayar kuma mai bi mata ke jan ruwa a rijiya.

 

Duk gaishe shi suka soma yi

Ya amsa su yana tambayar “Zahra da safiyyah fa?”.

“Zahra ta shiga band’aki safiyyah kuma tana d’aki itama bata da lafiya”.

“yaa salam” ya fad’a yana girgiza kanshi kawai.

“ka bari kawai farouk ni har bansan ma yadda zanyi ba wllh, kana kallo babanku kasuwa ta tsaya cak, abincin mu ma idan muka dafa yau shikenan ya k’are, balle aje ga batun magani ko chemist, kai wannan rayuwa Allah yayi mana maganinta”.

“ameen y fad’a yana gyara tsayuwar shi, to ni zan tafi ummi nasan baffa bai tashi ba ko? Allah dai yasa yau mu samu abinda zamuje nema, idan mukhtar me chemist ya futo zanyi mishi magana yazo ya duba khadija da safiyyan”.

“ai baban kuma tun asuba daya futa masallaci bai dawo ba, kasan yaune sadakar 7 ta malam Musa, ni fa banason bashi farouk ka kuma san babu yadda za’ayi mu iya biyan shi a halinda muke ciki dae yanzu”.

D’an murmushi yayi yace, “kada ki damu ummi Jiya ae nakaima Sulaiman babbar wayata anjima ma zan karb’o kud’in ta”.

Shiru tayi fuskarta bayyane da alamun damuwa tana kallon shi.

“kada ki damu ummi lafiyar su ai ta fiye mun wayar muhimman ci, ni na huce ummi kada nayi late sai Allah yayi mun dawowa”.

“OK farouk Allah ya yanke maka yasa k’arshen wahalar kane yazo”.

“Ameen ummi nagode sosae sai na dawo”.

Adawo lpy yaya Allah ya bada sa’a, su haseena duk suka bishi da wannan addu’a.

Ya amsa su da ameen ya huce.

 

Kamar yadda yayi alk’awari kuwa sai daya soma biyawa ta shagon mukhtar d’in sai dai ya tarar dashi a rufe, don haka sai kawai y huce gidan mukhtar d’in yayi mishi bayani sannan ya huce.

 

 

 

Basu fi mutum shida ba ya tarar a wajen, yayi musu sallama suka gaisa ya koma gefe ya zauna yana ta ambaton Allah.

 

Ba’a soma gudanar da interview d’in ba sai wajen k’arfe tara, zuwa lokacin tuni mutane sun cika gurin.

Babu abinda yafi d’aurewa farouk kai kamar yadda aka ajiye su suda suka fara bada sunan su a gurin aka shiga kiran Wanda suka zo daga d’eshi suna hucewa.

 

A k’alla an kira sama da mutum 15 suna zaune, wani saurayi da yake d’an nesa dasu ne ya matso kusa da farouk d’in yace, “me yake faruwa ne naga an tsallake mu?”.

“wallahi muma dae bamu sani ba Amman bari na tambayi me kiran sunan ai gashi nan ma tahowa”.

Wani shima cikin su ne yake wannan maganar tare da mik’ewa ya nufi mutumin, “mallam lafiya naga an tsallake mu bayan tun sassafe muke anan”.

“yauwa daman zuwa nayi don nayi muku bayani sai dai kuyi hak’uri an riga an gama d’aukar adadin ma’aikatan da ake buk’ata sai dai ku tara wani lokacin”.

 

Wani irin rass! Farouk yaji a lokacin da ake yi musu wannan bayanin tamkar saukar guduma.

 

“innalillahi wa’inna ilaihi raji’un ya shiga fad’a yana k’ok’arin mik’ewa daga kan kujerar da yake zaune, bai tsaya ko sauraran cece kucen da wasu daga ciki suka tsaya yi ba ya nufi hanyar fucewa daga ma’aikatar batare dako waige ba

Tafiya yake zuciyar shi cike da tarin tunaninnika barkatai, shi yanzu bai masan yadda zaiyi ba wata k’ila bashi da rabo ne a aikin gwamnati, don wannan shine kusan karo na 6 daya tafi neman aiki kuma duk bai samu ba, k’asar nan ta zama kawai waka sani ne waya sanka. “Sana’a wahalar samu, Aikin ma wahalar samu, ko ya ake so mu matasa muyi da rayuwar mu?”.

Shi kad’ai yake wannan maganar kamar wani tab’abb’e. Shi a halin dayake ciki ma yanzu ko kud’in motar dazai koma gida ma bashi dashi.

Haka ya mik’a hanya yaci gaba da tafiya duk da nisan da yake tsakanin gidan nasu da inda yaken, tafe yake yana ta karanta wasik’ar jaki wani zancen ma a fili yakeyi batare daya sani ba.

 

 

 

 

 

 

_Comment_✍️

8/13/22, 8:47 AM – Merhreeyeart❤️: 🏡 *AHALI D’AYA*

*_{auran bazata mafi k’ask’anci da wata irin rikitacciyar rayuwa mai d’auke da zallar k’iyayyah}_*

 

 

 

 

_Written by_

*Mareeyeart lawal*💞

 

 

 

_In dedication to my lovely ones_🥰

 

 

 

 

Page 3

 

 

 

Da sallama ya shiga cikin gidan nasu, bai tarar da kowa a tsakar gidan ba don haka kai tsaye ya shige d’akin shi, zama yayi a gefan katifa ya had’a kai da gwiwa.

Ummie ce ta lek’o d’akin tana, fad’in, “haba ni naji sallama kuma na futo banga kowa ba, ashe kaine ka dawo? ta k’arashe fad’a tana k’arasa shigowa cikin d’akin nashi.

 

D’ago kanshi yayi yana kallon ta ta zauna ita ma a gefen shi tana dad’a nazarin shi. Yadda taga yanayin shi kadae ya bata amsar tambayar da tazo zata mishi.

 

Don haka sai bata tambaye shi komai ba ta fuce daga d’akin, bata jima ba sai gata ta sake dawowa da d’an madaidaicin flask ta ajiye mishi a gaban shi, “ka daina wannan tunanin haka farouk Kaci abinci, Allah yana sane dakai shi kad’ai kuma yasan abinda ya tsarawa rayuwar ka nan gaba, farouk ina ji a jikina kai d’in zaka zama wani abu saboda gwagwarmayar da kasha a rayuwa, kai dai kaci gaba da addu’a kawai”.

 

Hannu biyu yasa ya share hawayen daya taru a idanun shi batare daya bari ummie ta ankara da abinda yayi ba ya mik’e ya fuce daga d’akin.

Wanko fuskar shi yayi ya sake d’auro alwala ya dawo.

 

Ummie ce tace, “ka tashi Kaci abincin farouk”.

 

Gayara kwanciyar shi yayi yace, “ummie kin manta yau Azumi nake?”.

 

Dafe kanta tayi, “ohh! Na manta wllh Shap, mukhtar fa yazo yayi ma khadija test, sannan kuma yasa mata drip leda 2”.

 

Mikewa yayi zaune yace, “yauwa dama har test d’in nace ya musu don a sha magani a kan ka’ida, malaria ne ko?”.

Take yanayin fuskar ta ya d’an sauya tace, “ehh! Safiyya dae malaria ne khadija kumaa laulayi take……..”.

 

Da wani irin mamaki ya mik’e zaune yana kallon mahaifiyar tashi.

“ka bari kawae farouk ni kaina wllh Don bakaji yadda naji ba lokacin da mukhtar ya fad’a mun, ashe daman rabo ne yayi sanadin auren nan nasu, banda haka ace Aure ko wata biyu bai rufa ba ya mutu ita kuma tana da ciki”.

 

 

“Hakane kam ummi daman waman k’adarallahu hakk’an k’adrihi, mu d’auki hakan a matsayin k’addarar ta, in yaso sai a kira shi yuseef d’in a fad’a mishi kawai gudun samun matsala”.

 

Ai wannan ya zama dole, baban kuma daya dawo zai je ya samu mahaifin shi da zancan, bama son ko sisin shi don Allah bai hana mu yadda zamuyi mu kula da ita ba, amma dae yasan da cikin”.

 

 

“Hakane kam”. Ya fad’a tare da komawa ya kwanta.

 

Ita ma mik’ewa tayi ta fuce daga d’akin zuwa nata d’akin.

 

*******

 

Zaune yake a saman dakalin k’ofar gidan su misalin k’arfe biyar da rabi na yamma.

 

Kamar yadda yake bisa al’adarshi wato ambaton Allah a duk lokacin daya kasance shi d’aya.

 

Zahra da ramlah da suka dawo daga makarantar islamiyya suka yi mishi sannu da hutawa sannan suka shige gidan nasu.

 

Ya dade zaune a gurin yana gaisawa da tsilli tsillin mutanen da suke hucewa a anguwar tasu, wanda yawancin su y’an anguwar ne, da suke dawowa daga kasuwa.

 

 

Da d’aya da 2 suka d’an soma taruwa a gurin daya zamto musu tamkar majalisa idan sun dawo daga kasuwa.

 

Hira sukeyi irin ta matasa masu ji da tashe kuma akan lokacin su, farouk dae nashi sauraro kawae idan sun sako shi iya kaci yayi murmushi ko y’ar dariya kawae.

 

Wata matashiyar yarinya ce da bata huci shekarun k’anwar shi Zahra ba, taci uban bilicin duk ya b’ata mata fuska da bak’ak’en kuraje tazo ta tsaya a gurin su tana magana.

 

Hankalin shi baya kansu don haka bai san abinda suke tattaunawa ba.

Khaleed ne ganin Hankalin shi ya tafi ya d’an taboshi yace, “ya dae man ko azumin ne na ga miskilancin naka yau ya zarta na kullum”.

 

D’an murmushi yayi yace, “wllh ko d’aya kawai dai yau jina nake”.

Wani daga cikin su ne ya Cafe cikin shak’iyan ci yana fad’in, “ka sani ko tunanin gimbiyar tashi yake?”.

 

Duk dariya sukayi, Khaleed yace, “haba farouk ne fa, ku sauya batu dae”.

 

“Owk to abin ne kenan?”. Wani cikin su ya sake fad’a

 

“Humm na fahimci so kuke dai ku kore shi”. Khaleed ya sake fad’a.

Murmushi shikam kawai yayi, Sulaiman yace, “yanzu dae sadiya tana magana farouk”.

Shi sai yanzu ma ya lura da ashe ita ce daya d’ago idon shi ya kalleta.

 

Banza yayi da ita har Saida Khaleed yace, “kaifa take jira farouk, ka d’an tashi mana kasan komai yana buk’atar sirri”.

 

Kallon ta ya sake yi a karo na 2 ya wani tsare gida kafun yace, “kina iya fad’ar abinda ke tafe dake”.

 

Yadda yayi mata maganar sai da taji shakku ita kanta ta diririce.

“umm dama assignment na kawo kayi mun”.

 

Sai daya sake d’aukar lokaci don tsabar takaici ma rasa abinda zaice mata yayi sai can dai dakyar yace, “kije ki kaima saddiq mana ni banjin zan iya”.

Hucewa tayi tana d’an zunb’ure zunb’ure da baki, don ba haka taso ba sam,

Khaleed ne yace, “yarinyar nan tana son had’a hanyar ta dakae farouk, kai kuma ni har yanzu bansan irin kaba”.

 

Baice mishi komai ba ya share don shi a ganin shi komai ma dama ce ta lokaci, a halin da yake ciki d’innan bai tab’a marmarin soyayyah bama bare akai ga batun wani Aure, kuma shi anashi ganin meye amfanin kace kana son mutum idan har ba auren shi zakayi ba.

Mikewa yayi jin an soma kiran sallar magrib.

Sallama yayi musu, khaleed yace, “zaka futo ne anjima?”.

“anya kuwa? Gsky banjin zan iya futowa yau, gurin salis kad’ai zan iya zuwa sai mukhtar Don yau da wuri zan kwanta”.

“owk to sai Allah ya kaimu gobe kenan? Dama wata anguwa zaka rakani da”.

“wata yarinyar ka gano kenan?” Farok ya tambaye shi yana kallon shi.

 

“Ai kaima farouk kasan kwanan zancen, ni wllh lamarin ku mamaki yake bani kai son mata shi kuma aminin naka gashi nan dae” ….. Wani cikin su ya k’arasa fad’a yana dariya.

Shima farouk dariyar yayi ya karasa shigewa cikin gidan nasu ba tare daya kuma ci gaba da sauraron suba.

 

Khadija ya samu tana durk’ushe a k’ofar toilet d’in su tana kyalaya amai, duk ta futa kamannin ta.

Sosai yaji tausayin ta a ranshi ya kewayeta yana mata sannu ya d’auki buta don gudanar da abinda yake gaban shi.

 

 

Da daddare duk suna zaune a tsakar gidan nasu in aka d’auke khadija da take kwance har lokacin.

Maraji’ar karatun su sukeyi su matan tare da ummie, Yayin da shi kuma yake zaune kusa da mahaifin shi ya tattara duk wata nutsuwar shi yana sauraron baffan nashi.

D’an bafulatanin mutum ne ma’abocin kyau da cikar haiba, mutum ne ma’abocin nutsuwa da cikar kamala.

 

Magana ya soma yi cikin kwantaccen sauti inda yace, “wato farouk abin da nake son na gaya maka shine, maganar zaka fudda rai da neman aiki sam bata taso ba, dole haka zaka ci gaba da lalubawa har Allah yasa a dace, domin kuwa babban kuskure ne fudda rae da yanke tsammani daga rahamar ubangiji, don haka duk yanayin da zaka tsinci kanka na matsi da kuncin rayuwa to kada ka tab’a yanke k’auna daga rahamar ubangiji.

Allah yana sane dakai kuma shi yasan abinda ya tsarawa rayuwar ka anan gaba, sannan zaman hakan ma bazai yiwu ba, don haka gobe in Allah ya kaimu ka futa kaima neman na kanka kamar yadda kowane matashi yake k’ok’arin yi, duk k’ank’antar sana’a kada ka raina ta, kada ka dubi irin yawan ilimin da kake dashi girman kai ya rud’e ka Kaji koh? A haka har Allah yasa ka samu abinda kake son”.

” To baffah insha Allah zanyi abinda kace, nagode sosae”.

 

“yauwa farouk Allah yayi maka albarka, naji abinda kayi d’azu a gurin maman ku, Allah ya shi maka albarka ya haskaka rayuwar ka”.

 

“Ameen baffa”. Ya fad’a tare da mik’ewa ya shige d’akin shi.

 

 

Allah sarki farouk

 

 

To cikin kwana kin kuwa farouk bai sake zama ba yasoma bulayin neman Aikin da zaiyi ya dinga d’an samun d’ari da kwabo amman ya gagara, in ya futa tun safe haka zaiyi ta bulayi har ya gaji ya dawo gida.

 

Ganin ya jera sati yana wannan buga bugar ba nasara sai kawai ya hak’ura ya fawwalawa Allah.

 

Ummie ma ganin abin sai dad’a yin gaba yake sai kawae ta kira yayanta da yake garin Abuja ta sanar dashi komai da suke ciki, da yake akwai Kyakykyawar fahimtar juna a tsakanin su da shak’uwa (ita ce dae daman bata son sanar mishi komae, indai ba irin haka ta k’ure mata ba)

Yaji dad’i sosae da take sashi cikin lamarin ta kuma yayi mata alk’awarin yana nan zuwa cikin satin da zasu shiga amma ko kafin yazo ya karbi accnt yayi mata trnspr ta y’an kudade masu nauyi. Wanda dasu ne suka siyi y’an kayan abincin da zasu ci na kwana2, aka kuma kai khadija asibiti don tana fama da laulayi mai tsanani.

An basu gado sosae ake kuma kula da ita, kamar yadda sukayi tunani kuwa, yuseef baizo ko dubata ba amman ya amsa cewar eh cikin dake jikinta nashi ne Wanda daman su abinda suka fi ji kenan.

Ranar wata Litinin kuwa Abubakar yayan ummie ya diro garin na kaduna, lokacin da yazo bai tarar da kowa a gidan ba sai farouk don yaran duk suna makaranta ummie kuwa tana asibiti gurin khadija.

 

Bayan ya huta farouk da kanshi ya kaishi har asibitin da aka kwantar da khadijan.

Wadda Kyakykyawar kulawar da take samu gurin likitocin tasa ta warware sosae sai abinda ba’a rasa ba, zuwan nashi ya musu dad’i sosae musamman ummie.

 

 

Bayan ya duba jikin khadijan bai tafi ba sai da ya siya musu duk wani abu da yasan zasu buk’ata a asibitin.

 

Tare suka tafi da ummie shi kuma farouk ya zauna anan.

 

Sun tattauna batutuwa masu matuk’ar muhimmanci game dashi kanshi da rayuwar shi, kuma yaji haushin yadda bata tab’a fad’a mishi duk wani hali na rayuwa da take ciki har sai abin ya tik’e irin haka.

 

Ita dai hak’uri kawai ta bashi don daman tasan zaiyi fad’a in yazo.

Kwanan shi d’aya y juya bayan ya tabbatar da a kaso d’ari na matsalolin su, 70 sun tafi.

Maganar aikin farouk kam yace sai dai in zai bishi Abuja in 2 weeks ma zai soma aiki, amman kuma farouk d’in yace, shi dai yafiso anan garin kadunan ne, shi kuma abubakar bashi da ido anan d’in don haka sai ya samo mishi mafutar tuk’in napep.

Hakan kuwa yayi ma farouk d’in dad’i kwarai da gaske.

 

 

**********

 

 

To kun san ance waiwaye adon tafiya.

 

 

B’angaren Arafah kuwa cikin satin abbie d’in ta ya dawo.

Tana tsaye a k’atotuwar harabar gidan nasu, tayi matuk’ar kyau cikin wasu tsadaddun riga da skert wanda suka amshi jikin ta kwarae.

 

Shi da fahad ne suka futo daga motar.

Bafullatani usul kai inka ganshi baza kace ma ya haifi kamar Arfah ba saboda hutu dajin dad’in daya ratsa shi, da gudu ta nufe shi kamar wata y’ar k’aramar yarinya tanayi mishi oyoyo.

Rungume ta yayi shima yana fad’in, “oyoyo babie ner”.

Fahad ne yace, “babie fah kace abie? wannan k’atuwar ce babie”.

Da sauri ta d’ago kanta tana kallon yaa fahad d’in kafun cikin shagwab’ar ta tace, “abie ka ganshi ko?”.

Shafa kanta yayi yana fad’in, “rabu dashi Arfah daman shi bai iya komai ba sai jan rigima”.

Hucewa gaba fahad d’in yayi yana murmushi dan shi komae nata burgeshi yakeyi, kama daga maganar ta, tafiyar ta, dama yadda take koman ta yana matuk’ar d’aukar hankalin shi, tare suka jero ita da abban nata tana fad’in, “kasan wani abu abie?”.

Ya girgiza mata kanshi tamkar yadda takeyi wasu lokutan, murmushin da yake k’arawa fuskar ta kyau tayi kafun tace, “I soo much miss u”, shima murmushin yayi yana sake jin ta a zuciyar shi yace, “I miss u too mamana”.

 

Ci gaba da tafiya sukayi har zuwa part d’in shi tana fad’a mishi yadda tayi kewar shi har suka isa parlon nashi, a gefan shi ta zauna har lokacin hira takeyi mishi irin wadda ba kowa takewa ba sai mahaifin nata, idan kuka ganta bazaku tab’a cewa tana magana irin haka ba.

Sosae yake sauraron ta tare dayi mata tambayoyi sosae akan karatun ta, yaji dad’i da yaga tana concentrating yadda ya kamata. Sunyi hira sosae kafun Daga k’arshe dae tafi ta barshi don ya huta,

 

 

Cikin satin taci gaba da rayuwa cikin tsantsar farin ciki har y’an gidan sun shaida hakan, don su kansu ta daga musu k’afa daga duk wani rashin mutumci da take takawa a gidan.

******

 

Ranar wata Litinin da safe ta tashi daga bacci kamar koda yaushe, bayan ta gama gabatar da duk wani abu da takeyi wanda take d’aukar shi wajibi duk safiya,

Futowa tayi sanye da wasu shu’uman riga da wando, rigar iya cinya, tsaye tayi a kitchen d’in gidan tana k’are ma masu aikin kallo d’aya bayan d’aya kafun ta soma magana, “wace ta san gidan su ramlah?”.

Wata daga cikin ma’aikatan gidan tace, “ni na sani”.

 

Sai data sake shan k’amshi sannan ta kuma cewa, “me yasa in tazo sai bayan kwana 2 take sake zuwa? “.

Ta sake tambayarsu har lokacin tana binsu d’aya bayan d’aya da kallon kyama da k’iyayyah”.

 

“Wllh nidai ban sani ba ranki shi dad’e amman idan zani gida weekend zan biya ta gidan nasu sai na dubo miki meye matsalar”.

 

“Noop! Idan kinje ma kawae ki sanar da ita taci gaba da zama na koreta daga Aikin”. Ta nuna wata cikin su da bata kai su shekaru ba tace, “ke saiki maye gurbin ta, daman kinsan dokoki na ko?”.

Sosae jikin matar yayi sanyi tasan maybe itama k’arshen aikin ta a gidan ne yazo, lahaula wala k’uwwata illah billah.

“bakya jina ina magana ne?” ta fad’a cikin d’an d’aga muryarta kad’an (Don dama ita bata magana da k’arfi)

“Yi hak’uri ranki shi dad’e, eh nasani insha allahu kuma zan kiyaye”.

 

Tsaki taja tare da fucewa daga kitchen d’in.

 

Sosae jikin su yayi sanyi suka kuma tausaya ma ramlam don yarinya ce me nutsuwa ga hankali, gata da hak’uri da biyayyah, irin yadda Arfah take wulak’antata a gidan idan tazo hutu amman tayi hak’uri ta jure, ko su bata zama ta tattauna dasu, abinda ya kawo ta kawae take, a wasu lokutan sai dai aga ita kadai tana share hawaye.

 

 

Ita kuwa koda ta futa kai tsaye part d’in ammien ta ta nufa, sai da ta tsaya ta d’an yi knocking,

Ammien ce ta bata izinin shiga sannan ta bud’e k’ofar ta shiga. Ammie tana zaune ta rangad’a kwalliyar ta mai kyau irin ta manyan matan da suka isa, zama tayi a k’asan carpet d’in tare da d’ora kanta a saman k’afafun ammien.

“Barka da safiya Ammie” , ta fad’a kamar bata son bud’e bakin ta.

Shafa kwantaccen sumar kanta tayi tace, “barka da safiya habeebty fatan kin tashi lpy?”.

 

Yamutsa fuska tayi kamar wadda taci mad’aci kafun tace, “ammie ba lafiya ba cox Jiya banyi bacci ba sosae, ina ta tunani”.

 

 

Y’ar dariya ammien tayi kafun ta kuma cewa, “tunanin meye haka kuwa zai hana mamana bacci?”.

 

Sai ta mik’e sosae tana kallon mahaifiyar tata ganin ta d’auki abun kamar wasa, “Allah Ammie da gaske nake, ina ta tunani akan yaya fahad ne, kunce bake kika haife shi ba, to waye ya haife shi?”.

 

 

Take walwalar dake saman fuskar ammien ta soma b’acewa, sam batayi tunanin abinda Arfah zata ce ba kenan, “wannan wani abu ne daya shud’e tsahon lokaci mai tsayi, kuma ban son tuna shi a halin yanzu, kamar yadda nasha fad’a muku ke dashi fahad d’in, shi d’an yayata ne dake can k’asar Egypt garin Cairo”.

Shiru Arfah tayi kamar me nazarin wani abu kafun ta kuma cewa, “to amma ammie kema y’ar can asalin garin cairon ce? Kuma meyasa bamu tab’a zuwa ba, Wae ina familyn ki dana abbie suke ne, ko kuma kamar yadda naji wasu mutane suna fad’a muma daga sama muka fad’o?”.

 

Maganar ta ta farko ta ba ammien haushi, amman kuma wadda tayi daga k’arshe sai ta bata dariya.

 

“wai sai zuwa yaushe zaki daina damu na da wannan maganar ne? Ke kin tab’a ganin Wanda suka fad’o daga sama da idon ki?”. Duk cikin harshen larabci take mata wannan maganar.

Sosai ta shagwab’e fuska tace, “I’m sorry mum, nima mantawa nayi”.

 

Sun d’an yi shiru kowa da abinda yake sak’awa a ranshi kafun daga k’arshe arfah ta tashi ta nufi dinning tana bubbud’e warmers d’in data tarar, abinci ne kusan kala nawa Amman duk ba wanda yayi mata a ciki, don haka sai ta nufi kitchen d’in da kanta don bada order.

 

Ranar ammie gaba d’aya rasa walwalarta tayi, arfah ta taso mata da tsohon mikin dake cikin zuciyarta tana rayuwa dashi tsawon shekaru.

 

Ahalin ta, Ahalin mijin ta sam wani abu ne da bata san ta tunga tunashi, kuma bata tab’a tunanin irin rainon da sukayi ma arfah zata dinga damun su da irin wad’annan batutuwan ba, gashi yanzu ita abubuwa duk sun jagule mata, tafi kowa tsanar had’in auren muhsin da arfah, amma kuma bata da yadda zatayi ta raba su, kuma ko a fuskar ta baza taso jafar yasan da abinda ke rantan ba.

 

Da yammacin ranar arfah ta shirya cikin doguwar riga ta atampa, ta yane kanta da d’an siririn gyale, hannun ta rike da wayarta da mukullin motar ta, sabuwar mai aikinta na binta da jakar ta a baya.

 

Wayar ammie ta kira ta sanar da ita zata d’an futa zuwa gidan su fareeda, amma ba dad’ewa zatayi ba.

Kashe Wayar tayi bayan sunyi sallama ta mik’awa mai aikin nata.

 

Sai da sukaje har gaban motar da zata futa da ita sannan ta mik’a mata jakar.

Har tasoma yima motar key sai ga ammie ta futo da saurin ta tana kiran sunan ta tare da dakatar da ita daga shirin tada motar da takeyi.

 

Ta jikin windown motar ta tsaya tana kallon tilon y’ar tata tare da fad’in, “arfah baza kiyi driving d’in motar nan ba yau”, sai ta kwalawa saddik kira, “saddiq! saddiq!!”.

Wanda ta kira da saddiq d’in ya taho da hanzarin shi tare da russunawa yana amsa kiran nata, “gani hajiya”.

 

 

“ka kai arfah gidan su fareeda, kada ka yadda tayi driving da kanta”.

 

Russunawa ya sake yi yace, ”an gama ranki shi dad’e”.

 

Kallon ta arfah take duk ranta a b’ace, ganin ranta ya b’aci sai ammien ta dafa kafad’ar ta tace, “I’m sorry habeebty nima banson duk wani abu dazai b’ata ranki, Amman ba yadda na iya bazan iya hak’uri da rashin kiba, kuma fareeda ta fad’a mun ko ranar da kuka futa d’in nan sai da kika kusa accident Allah ya tsare, don haka kiyi hak’uri yanzu saddiq d’in ya kaiki”.

Bata ce da mahaifiyar tata komae ba ta futo ta koma gidan bayan kamar yadda ammien take so, amma fa a ranta ita kad’ai tasan abinda ta shirya da zarar ya kaita gidan su fareedan.

 

(wani abu da yake bibiyar rayuwar arfah shine, duk lokacin data tuk’a mota da kanta sai tayi accident, ko ta buge mutane, kuma mutanen ma irin wanda ta tsani had’a hanyar ta dasu wato poor people, talakawa)

 

 

 

 

 

 

 

 

_comment_✍️

8/13/22, 8:47 AM – Merhreeyeart❤️: 🏡 *AHALI D’AYA*

*_{auran bazata mafi k’ask’anci da wata irin rikitacciyar rayuwa mai d’auke da zallar k’iyayyah}_*

 

 

 

 

_Written by_

*Mareeyeart lawal*💞

 

 

 

_In dedication to my lovely ones_🥰

 

 

 

 

Page 4

 

 

Tunda suka soma tafiya bata d’ago kanta ba har suka isa anguwar su fareedan.

Horn yayi mai gadi yazo ya bud’e mishi get kasancewar duk sun sanshi saboda dad’ewar da yayi yana aiki a gidan alhaji ja’afar d’in.

 

A gurin da aka tanada don adana motocin gidan yayi birki, babban gida ne kwatankwacin gidan su arfah.

Bayan yayi parking saddiq da kanshi yazo ya Bud’e mata murfin motar.

Sai data gama shan k’amshin ta sannan ta zuro k’afafun ta data sakaye su cikin wasu irin takalman fata masu tsinin dunduniya.

 

Mik’a mishi hannu tayi a lokacin data gama tsayawa kan k’afafun ta.

Ba musu ya Mik’a mata key d’in ta huce zuwa cikin gidan.

Ta part d’in aunty ta soma biyawa (wato amaryar baban su muhsin d’in)

 

Tana kitchen a lokacin da arfahn ta shiga, y’ay’anta k’anana guda2 da suke kallo a falon suka nufi cikin kitchen d’in a guje suna kwala ma auntyn kira.

“mamie kizo kinyi bak’uwa, wannan k’awar auntie fareedan daya muhsin zai aura ce tazo”.

 

Da sauri auntyn ta futo don ta gane abinda yaran suke nufi, a zaune ta same ta k’afar ta d’aya kan d’aya tana kad’awa. “lah ashe kuwa da gaske ke d’in ce”.

Dan murmushi tayi suka soma gaishe da auntyn, auntyn ta amsa mata cikin sakin fuska, sun d’an yi shiru kafun arfah ta tambaye ta, “ina su rufaeda?”.

“Au nan kika soma shigowa kenan? Rufaeda suna chan part d’in mama”.

“eh biyowa nayi mu soma gaisawa dama kafun na shiga cikin”.

“kai amma fa naji dad’i sosae babie, yaushe rabon ki da gidan nan? Inaga fa tun kafun a tsaida maganar auran ku keda muhsin”.

 

Rasss! Gabanta ya fad’i, ita mantawa ma take da wani mutum Wae shi muhsin balle a kaiga tazo mujitan wata maganar auren shi.

 

Shiru tayi batare da tace da ita komai ba, ta d’an zauna jimm kafun ta mik’e don ta huce.

 

“a’a badai har zaki tafi ba? To d’an jirani na minti 2 ina zuwa”. Auntyn ta fad’a tare da shigewa bedroom d’in ta da sauri.

Bata jima ba ta dawo da wata y’ar k’aramar jaka ta kayan cosmetics ta mik’awa arfahn.

“Gashi wannan irin kayanku ne na y’an mata”.

Da arfan kamar bazata amsa ba sai kuma tayi murmushi ta amsa batare data yi mata godiya ba ta nufi hanyar futa.

 

Part d’in su fareedan ta shiga (da yake dama gidan mata 2ne)

 

A b’angaren su bata tarar da kowa ba na gidan sai ma’aikata da suke d’an karakainar su a tsakanin parlon da kitchen d’in gidan.

Wayarta ta d’auko har zata kira no fareeda sai kuma ta tuna da wani abu ta fasa, no mama ta kira wato (maman su fareeda d muhsin din)

Ta kuwa yi sa’a don bugu uku ta d’aga, “kin k’araso ne babie?”.

Tayi mamakin yadda maman tasan da zuwan ta, amma kuma data tuna da ammie sai mamakin nata ya gushe.

“eh amma ba kowa a main parlor”.

 

“Kada ki damu babie ki hauro sama kawae”.

Mik’ewa tayi ta nufi saman kamar yadda maman ta bata umarni.

A zaune ta iske ta saman kujera.

Hamshak’iyar mace ce data gama jik’a da naira da hutu, gami da gayu tamkar ammien ta, sai faman zabga k’amshi take, tana ganin arfahn ta mik’a mata hannu alamun ta k’araso gareta.

 

Babu musu ta isa gareta tare da k’arasawa ta zauna gefan ta.

 

Sosae tayi farin cikin ganin ta don har ta manta rabon dasu had’u, babu b’ata lokaci kuwa aka soma gabatar mata da drinks kala_kala.

“kice yau kin tuna da mamanki”.

Maman ta fad’a tana kallon ta.

D’an murmushi tayi tana wasa da zara zaran yatsun hannun ta, yayinda kanta yake a k’asa.

 

“Ina kika baro sofiyyan? Kwana2 itama bamu had’u ba”.

“tana gida”. Ta fad’a tana tsiyaya ruwa a cup.

 

Hira maman take mata sosae cike da salon jan hankalinta zuwa ga wani abu da kuma nau’i na bugun ciki.

 

Tana jan hankalinta zuwa ga muhsin, sannan kuma tana son taji yadda alak’ar tasu take tafiya a halin yanzu, don shi ta bakin shi ba’a jin komai.

Ita ma kuma arfahn hakane, tunda maman ta tsunbulo maganar yaa muhsin ta sauya fuska, a gurin maman take jin ashe ma yayi tafiya baya k’asar, koda taga maman tana son taji ta bakinta ne sai kawai ta nuna mata ai Sun mayi sallama dashi kafun ya tafi.

 

D’an k’aryar data fad’a wa maman, sai da taji dad’i a ranta ba kad’an ba don ko ba komai ai tagane ai suna tare da juna.

Abinka da wayayyun mata kuma tuwo na maina, sam babu ruwansu da batun wani surukuta balle wata kunya da sam bata cikin tsarin su.

Arfah ta d’an dad’e anan b kamar a part d’in aunty ba, kafun daga karshe ta tashi don ta tafi.

 

Ita madai kamar aunty kyautar kayan cosmetics tayi mata da sauran tarkace na y’an mata.

 

Da kyar take tafe da ledar don ba yadda zatayi ne da a ta faki ido ta ajiye musu kayan su.

Har wajen motar ta ta rakota sannan ta koma, tana matuk’ar k’aunar Arfahn har zuciyarta take jinta kamar y’ar ta.

 

Arfah tana shirin shiga motar sai ga saddiq ya taho da hanzarin shi yana mata sannu da futowa, ya bud’e mata gidan baya, wani irin mak’askancin kallo tayi mishi kafun ta soma magana, “kana tunanin zan iya kuma had’a tafiya ta da talakan mutum kamarka?”.

 

Russunawa malam saddiq d’in yayi tare da shanye b’acin ran maganar data gasa mishi yace, “kiyi hak’uri ranki shi dad’e hajiya ce ta bada umarnin kada a sake a barki ki tuk’a mota da kanki……”

 

Kamar jira take yakai k’arshen maganar tashi ji kakake tass! Ta wanke shi da lafiyayyen mari, “kai ka isa na fad’a ka ja?”.

 

Runtse idon shi yayi zuciyar shi tana mishi wata irin suya, bai tab’a jin nadamar aiki a gidan alhaji ja’afar ba sai yau, yarinya k’arama y’ar cikin shi zata d’aga hannu ta kwad’a mishi mari irin haka ba don kuma yayi mata komae ba……

 

Bai sake ce da ita komai ba ya mik’i hanyar futa daga gidan.

Abinda ya faru kusan akan idon ma’aikatan gidan ne da su fareeda da futowarsu kenan daga garden.

 

Har zata shiga cikin motar sai ta hango su fareedan suna tahowa.

 

Tsayawa tayi ta hard’e hannuwan ta a k’irji tana kallon su, wani irin d’arrr fareeda taji a lokacin data sa idon ta akan arfahn, tayi wani irin mugun kyau fiye ma da lokacin data baro ta a gidan su.

“shegiya kamar ita tayi kanta”.

Sam batasan maganar tata a fili tayi ba har Saida taga rufaeda ta mata kallon bazata da mamaki.

 

Sai tayi saurin wayancewa ta hanyar yin murmushi ta d’ora da fad’in, “kin gane arfahn ce badai kyau ba da iya dressing”.

 

Gyad’a Kae rufaedan tayi tace, “haka ne kam amma auntie kema fa kinsan ai dole auntie arfah tayi kyau in kikayi duba da cewa mamarta Arab ce, kuma ko a cikin Arab d’in ma ita d’in mai kyau ce”.

 

Zancen sam baiwa fareeda dad’i ba don haka sai bata ce komai ba har suka k’arasa gurin da arfahn take tsaye, a zahiri fareeda sam bataso kula taba, don tanason rama abunda tayi matan, kodan tasan cewa a rayuwa bata fita da komae ba, sae dae kash a halin ynz lokaci ya k’ure mata don tana buk’atar kusanci wajen aiwatar da kud’irin ta, don hk sai nan take ta sauya yanayin ta.

 

Da d’an hanzari ta k’arasa suka rungume juna kamar ba komae, ita arfah tun da abun ya faru ma ta d’auke shi a matsayin ya huce.

 

(banbancin halin fareeda da arfah shine, ita fareeda macece mai matuk’ar kyashi , hassada, da kuma makirci, ta kasan ce mace mai matuk’ar son kanta, kuma bata yafiya, kowanne k’aramun kuskure a gurin ta zaka biyashi da tsada, amma kuma ta kasance mae matukar kirki ga mutane, duk k’ank’antar ma’aikatan gidan su ko k’ask’ancin su bata tab’a yi musu koda kallon banza, balle a kaiga rashin mutumci irin na arfah, while arfah ta kasance mace marar mutumci, da zata iya taka kowa, kuma tana da izza da jin kai na k’arshe, amma kuma bata da rik’o sam, dg inda tayi mk abu aka jima to kuma ya huce, sannan bata d’auki abun duniya komae ba, amma pa ta d’auki duniya komae)

 

 

Rufaeda ma rungume ta tayi tana y’ar dariya cikin farin cikin ganin ta, “nafi wata 3 rabon dana ganki auntie”.

Murmushi arfahn tayi, fareeda ta Cafe zancen cike da kissa tace, “really? To ai kuwa bazaki kuma koda rabin wata 1 daya ma baki ganta ba, don bikin ta da yaa muhsin ya kusa ckn satin nan, kinga zaki dinga ganinta akan kari kenan”.

 

Kallon ta kawae arfah tayi batare da tace komai ba.

 

 

Tana tsaye jikin motar ta fiye da minti uku sai sauraron hirar da rufaedan take mata kawai take, har lokacin fuskar ta washe da fara’ah.

 

Agogon hannun ta ta duba tace, “to nidae I’m about to go, yaushe zaku shigo keda salma d’in?”.

 

“next week insha Allah” rufaedan ta fad’a kanta tsaye

 

D’an zaro ido arfahn tayi tace, “gurin ammie dae zakizo ko? Don We will be back to schl end of dis week”.

Da sauri fareeda ta kalle ta tace, “kina nufin hutun mu ya k’are?”.

 

Kallon ta arfahn tayi tace, “ki lissafa mana ki gani”.

 

Shiru fareedan tayi ta tafi dogon nazari, ita a iya lissafin ta akwae sauran sati 2. Hankalin fareeda ya tafi ta lula cikin dogon nazari…..

 

Rufaeda kam ta baiwa arfah tabbacin zuwa cikin ranakun kafun su koma.

 

Duk jikin fareeda yayi sanyi lokaci guda ta zama sukuku, har arfah tayi musu sallama ta tafi jikin ta duk a salube yake, ya akayi har hutun su ya tafi batare da ta aiwatar da abinda ya dace ba.

 

 

Yau batayin gudun ma sosae, Tafe take slowly tana bin wakar hip hop ta turanchi cikin nutsuwa, dae dae inda zata karya kwanar da zata hada ta da titin anguwar su unexpected kawae taci karo da wata mota itama ta karyo kwanar, tayi saurin juya akalar motar ta don ta kauce wa motar, sai dai cikin rashin tsammani ta kwashe wani mutum a mashin shi kuma ya daki wani mutum dayazo tsallakawa, take mutumin ya fad’i k’asa mai mashin d’in kuma yayi taga taga Allah ya tak’aita bai fad’a kan mutumin ba.

 

Mutanen gurin suka d’auki salati, “hasbunallahu wani’imal wakeel” take duk sukayo kan mutumin daya fad’in suna k’ok’arin d’aga shi.

 

Kife kanta tayi da stiyerin tana sauke ajiyar zuciya a jejjere.

 

Tayi kusan minti biyar tana dafe da saitin zuciyar ta har y’ar k’aramar hayaniya ta soma tashi a gurin,

 

D’ago kanta tayi ta tadda cincirindan jama’a ana ta jajantawa, tsaki taja tare da dukan sitiyerin da hannun ta tana fad’in, “I hate dis people, bana son su, kamar yadda suma basa son mu, amma meyasa! meyasa!! meyasa!!! kullum nayi driving sai na had’u dasu a hanyataa”.

Duk cikin yaren larabci take wannan mgn.

Ganin hankalin mutane ya soma dawowa kanta sai nuno motar da take ciki ake ana magana, sai ta maida Hankalin ta kansu, kasancewar glass d’in mai duhu su basa ganin ta amma ita tana kallon su tar.

 

Magana suke da ba tasan me suke tattaunawa akai ba Amman tana iya gano mutumin da aka buge durk’ushe yana hawaye yayinda yake tsintar wani abu a k’asa yana zubawa a cikin wata y’ar bak’ar leda da take hannun shi.

Wani irin yanayi taji Wanda bata tab’a jin irin saba, har batasan lokacin data futo daga cikin motar taba.

A hankali tamkar wadda akayi connctng da magnet haka ta dinga tafiya har ta k’arasa inda mutumin yake, kusan mutanen gurin duk ita suke kallo, yayinda ita kuma hankalinta yake kan mutum guda a gurin, durk’usawa tayi a gaban shi tana kallon shi har lokacin, dattijo ne daya kusa tasamar ma Shekaru 60 a duniya.

Kallo d’aya zaka gane yadda gajiya da wahalar rayuwa ta futo a jikin shi, wani kod’ad’d’en yadi ne a jikin shi daya ji jiki sosae, k’afar shi kuma slifas ne daya sid’e duk an d’ad’d’aure shi da leda.

K’afar shi da me mashin d’in nan ya daka sae zubar da jini take alamun yaji rauni sosae, amma ko lura da hakan baiyi ba sai tattare shinkafar shi data zube yake yana zubawa a leda.

Tafi minti 2 a durk’ushe gaban shi tana kallon shi, duk mutanen gurin sunyi shiru suna jiran suga abinda zatayi.

 

 

Farouk daya nufo gurin tun daga nesa ya hango tarin mutane, kasancewar ba fasinja ya d’auko ba har ya gifta ta gurin a cikin napep sae kuma ya dawo da baya ya tsaya, baya hango komae sbd yawan mutanen gurin, sai masu maida zance gasunan kashi kashi. Jinjina Kae yayi yace,

“ooh su kuma mutane basa rasa abin kallo, ko meya faru anan kuma?”.

 

Wani matashi da yake kusa dashi yace, “wllh wata yarinya ce ta haddasa accident kaganta can ma ta futo ko a jikin ta.

 

“girgiza Kae farouk yayi, ya juya don a ganin shi baiga amfanin tsayuwar ba, har yy gaba sai dai kamar wanda aka dakatar sai ya samu kanshi da sake dawowa, take ya soma kutsawa ta cikin mutanen har ya dangana da inda mutumin yake, ita kuma tana durk’ushe gaban shi ta juya ta yadda bazae iya ganin fuskar ta ba, tsayawa yayi yana k’are mata kallo da son ganin fuskar ta, karo na farko a rayuwar shi daya tab’a kallon wata mace irin yadda yayi mata, magana takewa mutumin da baisan ma me take cewa ba, don ko shi wanda yake gaban nata bayajin yanajin abinda take fad’a.

 

“wanene kae? Bakaga akwae ciwo a jikin ka ba?”.

 

Karo na farko a rayuwar ta data tab’a yiwa wani mutum magana cikin kwantaccen sauti irin haka, a cikin irin mutanen data tsana.

 

Tsayawa yayi cak ya d’ago da idanun shi ya kalleta, wani irin duba na tsana da k’iyayyah.

 

Sai da taji wani shork lokaci d’aya tayi baya tamkar wadda aka jonawa lantarki, still kuma idon ta a kanshi tana ci gaba da kallon shi.

 

 

Maganganu mutane sukeyi Wanda sam hankalin ta baya kae, abu d’aya da taji daga k’arshe shine kalmar, ” wannan ai rashin imani ne, ku kyale mutum yana zubar da jini haka kuna kallon shi haba!”.

 

Da sauri ta juya da baya wanda hakan ya baewa farouk damar ganin fuskar ta, ya lumshe idon shi kwakwalwar shi ta tafi dogon nazari da tunani, a ina yasan wannan fuskar? A ina ya tab’a ganin wannan fuskar?.

 

Ita kuwa motar ta ta koma da sauri ta zaro kud’i masu matuk’ar yawa da ba tasan ma adadin suba ta dawo.

 

Har lokacin farouk yana tsaye sae dae yana jingine ne a jikin wata mota, shima kamar ance ya kalli fuskar mutumin sae kawai yayi gamo da mutum tamkar baffan shi, take abun yayi mishi yawa a kwakwalwa, ga wannan matashiyar yarinyar kuma ga wannan dattijon, kafun ya farfad’o daga tunanin daya soma tafiya, saiga yarinyar ta sake dawowa da uban tulin kud’i,

 

A hankali take takunta cikin zallar aji da izza har ta sake dawowa gaban mutumin, Kud’in ta d’ora mishi a tafin hannu batare da tace komae ba ta mik’e da niyyar tafiya,

 

Sai dae taku 3 tayi ta tsaya sakamakon kiran sunan ta da taji anyi, “Fatima”. Kafun ta juyo mutumin ya d’ingisa k’afar shi ya tsaya a gaban ta, kamo hannun ta yayi yana kallon ta ido cikin ido ya d’ora mata kud’in a tafin hannun ta kamar yadda tayi masa, “wannan kud’in naki babu abinda zaiyi mun, kamar yadda kika ganni a wannan talaucin, to a cikin sa nake son na k’are rayuwata, bana buk’atar wani abu daya futo daga hannun ki, ko ja’afar mahaifin ki, balle a kaiga sofiyyah mahaifiyar data haifeki”.

 

 

Zaro ido tayi, ta d’an yi baya still idonta akan mutumin, zuwa yanxu ma ita ta fara jin tsoron shi, ta kalli hannun ta ta kalli mutumin.

 

Mutumin yayi wani murmushi mae ciwo yace, “kwarae kuwa wannan sak’one na baki musamman har zuwa ga mahaifiyyarki sofiyyah data kasance ummul aba’isin rusa dangatakar jini guda! *AHALI D’AYA* saboda wani kyallin duniya, dattin duniya mae k’arewa wato kud’i, kuma kamar yadda tayi mana muna nan muna addu’a itama sai ta d’and’ana irin abinda muka d’and’ana a rayuwa, insha Allah sai ta kurb’i irin madarar bak’in cikin da muka kurb’a, don ubangiji baya goyon bayan zalinci, kamar yadda yake addu’ar wanda aka zalinta bata da hijabi”.

 

Yana gama fad’in haka ya juya yana d’igisawa ya isa ga ledar shinkafar shi ya D’auka ya mik’i hanya.

 

A gurin ta zamo tamkar robbot, har ya kul’e ta kasa koda daga hannun ta balle takae ga yin wani kwakwkaran motsi ko yunk’urin barin wajen, waye wannan mutumin? Me yasa yayi mata magana haka a cikin taron mutanen nan? Taya akayi ma yasan abbie da ammienta ne? Me ammie tayi da yake ja mata wannan jafa’in?

Wad’annan tunanikan su suka taru suka cunkushe mata kwakwalwa har ta d’auki lokaci mae tsawo bata sani ba, a hankali mutanen gurin suka soma sulalewa suna barin wajen har ya zamana saura ita da farouk kawae, da shima lokaci d’aya ya tsinci kanshi a irin yanayin da ta tsinci kanta.

 

Farouk baisan taba, bai san mutumin ba, amma abu daya kawae daya sani shine sunan sofiyyah da ja’afar, domin kuwa a iya tsawon rayuwar shi da ummie da baffan shi ya fahimci ja’afar da sofiyyah wasu mutane ne da ko sunan su ba sa son tunawa, a wasu lokutan ummie har hawaye takanyi idan ta tuno da wani abu daya shude lokaci mae tsayi a tsakanin su da sofiyyah, takance sofiyyah itace silar lalacewar rayuwarsu, kuma ita ta jefasu a halin da suke ciki yanzu.

 

 

 

Daga k’arshe Arfah Zubar da kud’in tayi a gurin sannan ta juya ta nufi motar ta, yau wani abu ya sameta Wanda kwatankwacin shi bae tab’a samun taba a rayuwa.

 

Shi Farouk kam daya fita yin neesa a duniyar mafarkin sae da ta tashi motar ta sannan ya dawo hayyacin shi.

 

Hucewarta kawae ya gani a guje tamkar zata tashi sama, yabi bayan motar tata da kallo, sae ya juya kawae zuwa ga napep d’in shi tamkar wanda aka zubarwa da laka, sai dae karaf idanun shi suka tariyo mishi wannan tulin kud’in data zubar.

 

Hankalin mutane har yanzu bai Kae kaiba, shima har yayi tunanin ya huce kawae sai kuma zuciyar shi ta bashi wata shawara, bak’ar leda ya D’auka ya zuba kud’in a ciki ya ajiye a cikin napep d’in shi ya nufi hanyar gidan su, don yau yaga abinda sam bazai iya ci gaba da aikin ba.

 

A 360 taci gaba da jan motar har ta k’arasa gidan su.

 

 

Koda tayi parking ma bata b’ata lokaci ba ta futo tayi cikin gidan da saurin ta, kai tsaye part d’in ta ta nufa ta shige cikin d’aya daga bedrooms d’in ta ta murzawa kofar key, saman bed ta fad’a rigingine tana sauke ajiyar zuciya.

 

 

A halin da take ciki ynx tana buk’atar privacy, shiyasa tana jin ana knocking ta share, tasan ma bazae huce yaa fahad daya ga shigowar taba.

 

 

 

 

 

 

 

 

*_comment_* ✍️

8/13/22, 8:47 AM – Merhreeyeart❤️: 🏡 *AHALI D’AYA*

*_{auran bazata mafi k’ask’anci da wata irin rikitacciyar rayuwa mai d’auke da zallar k’iyayyah}_*

 

 

 

 

_Written by_

*Mareeyeart lawal*💞

 

 

 

_In dedication to my lovely ones_🥰

 

 

 

 

Page 5

 

 

Tunanika ne barkatae suke neman su caza mata kwakwalwa, tayi zurfi sosae ta yadda har batasan lokacin da fahad ya shigo d’akin nata ba, sai ji tayi kawae yana jijjiga kafafuwan ta da suke zube a k’asa.

 

Mikewa tayi firgigit tana kallon shi tare da sauke tagwayen ajiyar zuciya, durkushe yake a gabanta yana kallon ta cikin son nazarin yanayin ta.

Ita kam d’auke ido tayi don gujewa kallon kwayar idanun shi.

“meya faru dake ne arfah? Naga kin shigo a sukwane kuma kin rufe kanki”.

K’asa tayi da kanta tare da dafe kanta da hannuwanta duka, yadda tayi d’in ya tabbatar mishi akwae damuwa babbah a tattare da ita, to amma meye damuwar tata, zama yayi sosae kusa da ita ya kira sunanta cikin kwantaccen sauti, “arfah” shiru tayi mishi, bae hakura ba ya sake kiran nata a karo na 2, “Plzz arfah ki fad’a mun mana ko meye, ko nine na sakeyi miki wani laefin?”.

Mik’ewa tayi tsam ganin zai dameta da tambayoyi taje jikin windown d’akin ta tsaya tare da hard’e hannuwan ta duka ta zubawa window ido.

 

Rufa mata baya shima yayi still ya tsaya a jikin windown ya zubawa fuskar ta ido, Kae tsaye bazae iya fassara yanayin fuskar tata ba.

Magana yake ci gaba dayi mata amma tayi tamkar ba da ita ma yake mgnr ba, ganin da gaske bazata ce komae a gareshi ba sae kawae ya zubawa sarautar Allah ido, kusan minti 10 suka d’auka a tsaye kafun ta juyo don barin gurin, da sauri fahad yasha gabanta tare da kiran sunanta, “arfah”. Bata amsa ba amma ta d’ago ta kalleshi, had’a hannuwan shi yayi duka 2 ya soma fad’in, “plzzz arfah wae me yasame kine, da fari kin dawo kin rufe kanki, na shiga damuwa sosae a gigice fa na samo spare key Allah yasa ma abie yana gari, ynz kuma kinyi shiru da bakinki? Shin da haka muke dake? Meyasa bazaki saki jiki dani mu koma kamar yadda muke a da ba? To a rayuwa ma waye kike dashi wanda zaki iya fad’a ma damuwarki bayan ni? Idan kika cire su ammie, meye laifin da nayi miki? Saboda kawae nace ina sonki arfah? To shi kenan tunda hakan laefi ne, sae nace na janye, me zae sa bazaki saki ranki komae ya huce ba?”

Sai ya durk’usa a gabanta bisa gwiwowinshi, “arfah kada kiyi saurin manta alk’awari mana, karki manta YAYA fahad d’inki da irin rayuwar da kukayi dashi a baya tun lokacin k’uruciyarki, yayanki da kika fi kowa kusanci dashi, yayanki da bacci ne kad’ae ke raba ku, yayanki kuma komanki a lokacin……

“har a yanzu ma matsayinka bae sauya ba ko dede da second a cikin zuciya ta, kana nan a matsayin komae nawa yayana, best friend d’ina”…… Ta fad’a cikin katse shi daga fad’ar maganar da ya d’auko d’in.

 

D’irkusawa tayi a gaban shi tasa hannu ta share hawayen ta tana girgiza Kae.

“sam bakayi min laefin komae ba, matsala ta a yanzu ko Kaji nasan bakada maganin ta, don haka ka kyale ni kawae yadda ka ganni…….”.

Mik’ewa yayi tsaye sosae yana ci gaba da kallon ta, “Idan har da gaske ina nan a matsayina ban sauya ba, to ki fad’a mun meye damuwarki a yanzu”

Kallon shi tayi ido cikin ido 4 a while kafun ta d’auke idanun ta da sauri tana sake share hawayen dake zuba daga idanun ta.

“kamar yadda n fad’a maka matsayinka bai sauya ba tabbas amma akwae wani abu da bazae tab’a gushewa ba har k’arshen numfashin mu, soyayyarka tana nan a kwayar idanunka bata huce ba, ni ina ganin ta a duk lokacin dana kalleka, to meyasa zakayi mun karya”…….

 

Sake Zama yayi sosae a gabanta, lokaci d’aya shima idanun shi suka soma sauya kala daga Brown hazel to dishi dishin red, abubuwa da yawa suna damun shi a rayuwa kuma baisan yadda zaiyi ba, matsayin da yake ciki yanzu dae dae yake da a dakeka a hanaka kuka, daga k’arshe ita da take lst hope d’in shi gashi itama zai rasata, sosae hawaye suka soma silmiyowa daga cikin kwayar idanun shi, “I luvs you, I really do tabbas Idan nace babu soyayyarki har ynz a cikin zuciyana to na fad’i k’arya, amma pa kamar yadda na fad’a miki ni na hak’ura dake, idan har hakan zai sake kawo mana dawwamammen zumunci na har abada, Idan har hakan zai faranta ranki ki komawa asalin walwalarki”……. Ya k’arasa fad’a cikin karkarwar murya.

Had’e kanshi yayi da gwiwarshi kawae yana jin yadda bugun zuciyarshi yake dad’uwa

 

Itama kallon shi kawae take cikin matsananciyar damuwa kafun taci gaba da magana, “wannan shine kuskurenka, kuma shiyasa bazaka tab’a ganina yadda kake so ba, meyasa kake saurin yanke k’auna? Meyasa zaka hak’ura ka barma yaya muhsin dukkan nasarar bayan kaine kasha wahala wajen yin campaign d’in? ”

 

Wannan karon cikin hargitsatstsen yanayi yake kallonta, “me yasa zakice haka bayan nidake duk munsan gaskiyar cewa muhsin kike so…..”

“kada kace haka don Allah, kada ka sake fad’a, kunnuwa na bazasu iya d’auka ba, idan har da gaske soyayyah d’aya ce, kuma zuciya ma d’aya ce, to duk ni nawa suna gurinka yaya fahad”

Wannan karon ya kasa gasgata cewar ba maparki yakeyi ba, ya kasa yadda da maganganun da arfah take fad’a zahiriyya ne, sai ya had’a hannuwan shi a karo na 2 yana kallonta yace, “don Allah arfah na rok’e ki kada ki k’arasa hargitsa mun tunani na, kina fad’a mun abinda yake k’arya Don kawae naji dad’i a raena? Me yasa zakimun haka?”.

Hannunta ta d’ora a saman nashi taci gaba da magana tana kallon idanun shi, “sam ba k’arya nake maka ba, wllh a yau ina fad’a maka ainahin abinda yake cikin zuciyata ne, Kae nake so yaya fahad ba yaa muhsin ba, dakae kad’ae nake son na rayu, bawani can daban ba”…….

 

Yadda yake kallonta ya kasa koda k’ifta idanun shi, yadda yake sauraron ta d’in nan wani irin tashi hankali yake sake shiga, ji yake kamar tana jik’a shine da ruwan dalma yana narkewa.

 

Sosae ta sake matsowa kusa dashi kamar zata shige jikin shi tana dad’a k’ara sautin kukanta, “don Allah yaya fahad ka taimaka ka kawo mun k’arshen maganar auren yaaa muhsin d’in nan, wllh zan iya mutuwa Idan aka aura mun shi ko na kashe kaena…….”.

 

 

 

Da sauri ya dakatar da ita ta hanyar d’aga mata hannu, “enough plzz ki dena magana irin haka don Allah, kunnuwana bazasu iya d’auka ba”.

Kanta ta kwantar a gefan kafad’ar shi tana sake fashewa da wani matsanancin kukan, a hankali ya zame kanta cikin hanzari ya fice daga cikin d’akin, wanda saura k’iris suci karo da ammie da duk wani abu ya faru a cikin kunnenta. Da sauri tayi baya, wanda da yana cikin cikakkiyar nutsuwarshi daya ganta.

Murmushi tayi tana tunanin abu na gaba dazae biyo baya a cikin ranta, don tayi alk’awarin indae tana raye saita karya alk’awarin ja’afar akan arfah, da wata wasiyyar banza ta abokin shi wato baban muhsin daya rasu, ta kuma lashi takobin idan har fahad bae samu arfah ba to lallae muhsin ma bazae same taba.

(ko burin ki zai samu cika kuwa sofiyyah)

 

Ranar arfah tayi kuka sosae kamar ranta zai fita, har ammie da take kallonta cikin cctv taji tsoron kada ciwonta ya tashi.

A daren ranar sae da sukayi video call da fareeda, ta bata labarin duk yadda sukayi da yaa fahad d’in.

Da arfah zata lura da tagane tsantsar tashin hankalin da fareedan ta shiga a lokacin da take bata labarin ya zarce na al’ajabin labarin da take batan.

Sosae kan fareedan ya kulle har ta rasa shawarar da zata baiwa k’awar tata kamar yadda ta buk’ata, to amma da yake ta kasance makirar mace ajin k’arshe sae tayi mata alk’awarin kawae gobe zata shigo, sosae arfah taji sanyi a ranta, koba komae tasan fareeda zata kawo mata shawara cikin sauk’i, kamar yadda ta kwantar mata da zuciya da mayaudaran kalamanta.

 

Ranar tayi bacci mae dad’i har fiye ma da tsammaninta.

 

 

 

Yayinda fareeda ta kwana bata runtsa ba saboda tashin hankali da bak’in kishi, ita ta d’auka maganar soyayyah tsakanin arfah da fahad ya huce tamkar ayi ruwa a d’auke, ashe su a cikin zuciyoyin su bae huce ba, ita suka bari tana ta haukarta.

Tayi kuka har ta godewa Allah, ta kumayi alk’awarin indae bata samu fahad ba, to arfah ma bazata tab’a samun shi ba, saboda ta dad’e tana dakon soyayyar fahad a cikin zuciyarta tun batasan kanta ba, kuma ta dad’e tana nuna mishi alamu amma duk ya share kamar bai gane abinda take nufi ba, har yanzu ta kasa gano Makusarta kota inda ta gaza da fahad ya kasa karb’ar ta a yadda take.

Yadda ta kwana bata runtsa ba haka ta samowa kanta mafuta akan damuwar ranta, a daren ta tambayi wani friend d’in ta d’an makarantarsu, ya kuma tabbatar mata da akwae sauran 2 wks a hutunsu, to lallae akwae abinda arfah take shiryawa data b’oye mata, murmushi tayi a fili ta furta, “nasanki arfah nasan komai naki, I know exactly how to destroy u, ammie ganinan zuwa gareki.

Take ta kyalkyale da wata iriyar dariya don ita harta hango yadda zata tarwatsa komae.

 

 

************

 

 

To b’angaren farouk kam baiyi birki a ko’ina ba sai a k’ofar gidan su.

 

Bai shiga cikin gidan ba sai daya soma shiga masallacin anguwarsu ya sauke faralin sallar la’asar data same shi a hanya, bayan yayi alwala da butocin nan masallacin.

 

Da sallama ya shiga cikin gidan nasu kamar yadda ya saba, khadija dake zaune a bakin kitchen ta amsa shi tana yi mishi sannu da zuwa, babu laefi ynz jikin nata da sauk’i har takan futo ma ta kamawa ummie girki kamar yadda ya sameta ynx.

D’akin shi ya shiga direct yayima wad’annan kud’in Kyakykyawan b’oyo sannan ya futo.

A k’ofar D’akin nashi ya zauna yana tambayar khadija, “ina ummie?”.

Khadija tace, “ta tafi gidan mallam kasan yaune sunan auntie Aisha”.

“ah aysha kara haihuwa tayi? Ya tambaye ta da alamun mamaki”.

Murmushi tayi tace, “eh ae kasan wancan babyn kwanan shi 30 ya rasu”.

“ayyah to Allah ya raya mata wannan, Wae me ake dafa mana ne yau patient koda yake ai kin warke ma”.

Y’ar dariya tayi tace, “ummmm yaya bazaka gane bane wllh ynz warin tattasan nan da naji kad’ae zuciya ta tashi take, ni dama zaka taimakeni ka k’arasa mun don Allah”.

Dariya yayi yace, “yarinya ni zakiyi ma wayo ba? Ga kinan ina ganinki ras dake, to da a gidan mijinki ne fa, wazai k’arasa miki?”.

Dariya take amma ambaton mijinta da yayi take yanayin fuskar ta ya sauya har farouk ya lura da hakan, shi kanshi subul da baka ne sae daya fad’a ya tuna gangancin maganar da yayi, gashi yanzu tana cikin farin ciki ya b’ata mata rae.

 

Matsawa yayi ya janyo kayan miyar da take gyarawan yace, “kawo dae badon halinki ba na tayaki”.

Yak’e tayi mishi don ko murmushin ma ta kasa ta mik’a mishi turmin don ta gama gyarawa ma.

Jajjagen ya soma yana janta da hira cikin dabara har ta koma cikin farin cikinta.

 

A hankali ya sauke b’oyayyar ajiyar zuciya, yana hamdala data saki ranta don ya tsani ya ga ta kule a cikin D’aki tana kukan nan, abune ya riga ya faru ba yadda zasuyi.

 

Ko daya gama Jajjagen ma ci gaba da tayata hira yayi yak’i futa duk da kiran da khaleed yake tayi mishi a waya amma ya share, har sae da su Zahra suka dawo daga makaranta sannan ya fuce ya barta tare dasu don yasan ko dramar su kad’ae bazata barta wani tunani ba.

 

A k’ofar gidan su ya samu khaleed d’in inda suke zama ya cika yayi fam, zama yayi gami da dafa kafad’ar shi yace, “ya ta samu ne man? Irin wannan kira da kake ta danna mun ashe kana kusa ma?”.

 

Hararararshi khaleed d’in yayi, farouk ya kyalkyale da dariya, “ka kuwa iya harara wallahi kamar mata, ko y’amma tanka suna harararkane in kaje zance?”

Duk yan majalisar tasu suka kyalkyale da dariyar suma, wani cikin su yace, “tab khaleed! Gsky yau farouk ya cika wasa”, yana gama fad’a suka sake kyalkyale masa da wata dariyar.

Khaleed kam sake dakewa yayi, Sulaiman ya kalleshi yace, “yanzu Kae farouk banda abun kana Wanda ba soyayyar yake ba, ana kallon soyayyah me yakawo wani maganar harara kuma”. Farouk kam murmushi yayi wannan karon yana kallon fuskar Khaleed d’in.

Khaleed dae Duk yadda yaso ya dake kasawa yayi sai da yayi dariyar

Wani cikin su ya sake fad’in, “Khaleed kenan wai Kae da Farouk zakayima zuciya? To wllh ka buga don bama zaka iya ba”.

Farouk dafa shouldar shi ya kuma yi yace, “kayi hak’uri Khaleed bawae da gangan nak’i futowa a lokacin da ka kira niba akwae wani uzuri da nake ne a lokacin”.

 

“ai ni babu abinda zaka cemun, Allah ne yayi zamu had’u ma da tuni na tafi daman kai indae aka had’a abu dakae, hummm!”.

 

“baka yadda da abun dana fad’a ba kenan khaleed?”.

“shikenan ya huce in anjima da daddare sae muje”.

 

Shiru Farouk d’in yayi kamar me nazarin wani abu, ganin haka Khaleed d’in yace, “ko hakan baiyi maka bane?”.

Girgiza Kae yayi, “a’a yayi indae bae Kae k’arfe tara na dare ba”.

“wane irin k’arfe tara na dare kuma muda zamu je Shap Shap”.

“owk to Allah ya nuna mana lokacin”.

Sulaeman ne bayan sun karkare magana yace, “nifa bazan gaji da fad’a ba wllh har ynz mamakin ku nake, shi kullum cikin yin budurwa, kuma bazashi zance shi kad’ae ba, kai kuma yadda na fahimta ka tsani ma had’a hanya da mata wai anya ma kana k’alau kuwa?”.

 

Wani irin kallo farouk yayi mishi kamar zaice mishi wani abu sai kuma ya fasa.

Khaleed ne yace, “kufa kuna da matsala Sulaiman ba dama kuga mutum cikin farin ciki sai kunsan yadda kukayi kuka dagula mishi rae, yanzu wannan maganar meye amfanin ta”.

“to meye laefi a cikin maganar danayi yanzu ae gaskiya ne amma in kunji haushi ku gafarceni”.

Sulaeman d’in ya fad’a a d’an zafafe.

Khaleed zaiyi magana wani cikin su yayi saurin tarar numfashin shi, “ya isa haka don Allah, ya huce tunda ya nemi afuwarku, ni nasan zolayane kawae irin na Sulaeman bada wani abun ya fad’a ba”.

Duk shiru sukayi kamar ba sune yanzu suke dariya a gurin ba.

Farouk ne ya mik’e tare dayi musu sallama ya shige gidan su.

Yana zama a gefan katifarshi wayar shi tana ring.

Sulaeman ne yake kiran don haka sai ya d’aga, “Sulaeman yae akwai wani matsalar ne”.

“a’a meyasa ka tambaya”

“ba komae kawae naga yanzu muka rabu ne”.

“ba wani abu bane na kira kane kawae saboda na dad’a baka hak’uri akan abinda ya faru d’azu, kayi hak’uri dan Allah ni bada wani………”

Da sauri Farouk ya katse shi, “au wae saboda haka ka kirani? Sulaeman kenan tun muna yara fa muke tare, halinka ba wanda ban sani ba kamar yadda kaima nawa b wanda baka sani ba, wannan maganar ta huce don Allah”.

 

Murmushi sosae Sulaeman d’in yayi sukayi sallama suna jin dad’in yadda ako da yaushe suke fahimtar juna.

 

 

****** *******

 

Da dare misalin k’arfe goma da rabi, Farouk ne kwance saman katifar shi, ya tsurawa silin ido, abin daya faru d’azu ne yake dawo mishi daki daki, daya runtse idon shi babu abinda yake gani sae hoton fuskar ta, da yanayin yadda take tafiyar ta cikin izza da k’asaita yadda take magana tana juya ido da kuma yadda take motsa bakinta, Kae yadda take yin koman ta ma.

Samun kanshi yayi dayin murmushi lokacin daya tuno yadda ta ruk’o damun kud’in nan ta kaewa mutumin nan, da alamu mutumin nan ya santa sosae, to amma me yasa mutumin yake mishi kama da baffan shi.

Zunbur yayi ya Mike kamar wanda aka tsikara da allura.

Lallae ko shakka babu baffan shi zai san mutumin nan, kuma ya naji ajin shi suna da alak’a, to ita kuma yarinyar fah? Idan har mutumin yana da alak’a da ita da iyayen ta, su kuma suna da alak’a da mutumin, kenan suma suna da alak’a da ita kenan?

 

 

 

 

 

 

Plzzz fans kuyi hak’uri naji wasu suna tambayar novel ranar talata

Kar ku manta ranakun post sune

 

_litinin_

_laraba_

_Juma’ah_

 

 

 

 

 

 

 

 

_Comment_ ✍️

8/13/22, 8:47 AM – Merhreeyeart❤️: 🏡 *AHALI D’AYA*

*_{auran bazata mafi k’ask’anci da wata irin rikitacciyar rayuwa mai d’auke da zallar k’iyayyah}_*

 

 

 

 

_Written by_

*Mareeyeart lawal*💞

 

 

 

_In dedication to my lovely ones_🥰

 

 

 

 

Page 6

 

 

 

Lallae ko shakka babu ita d’in mahaifinta wani ne a k’asar nan ko shakka babu, nazarinta ya soma tun daga yanayin jikin ta, da natural skin d’in ta data nuna zallar hutu da gogewa, ga exclusive atamfar da take jikinta, takalmin k’afarta, agogon hannun ta, wayarta mae matuk’ar tsada da ko a masu kud’in garin nasu ma ba kowane ya mallakawa d’an shi ba tukun (don shi kanshi a ntwrk ya tab’a ganin companyn wayar) sannan ga yadda tayo ambaliyar wannan uban kud’i, daga k’arshe akan motar da take hawa ya k’ark’are duk wani tunanin shi, mota ce ta millions of naira,

 

To waye mahaifinta kenan?

 

Shi dae tun da yake ko mae kama da ita bae tab’a gani a social network ba, duk da yadda y’ay’an y’an siyasar k’asarmu da masu kud’i ke baja kolin hutu nansu a mabanbantan gurare na kasashe daban daban ita bai tab’a katari da mai kama da ita bama.

Shiru yayi yana dad’a dulmiya cikin tunanin ta, ga kyau, ga aji, ga kud’i, ga wayewar da a kallo d’aya zaka iya gani.

Lallae ta had’a komae har da abin da mutane da dama suka rasa a rayuwarsu.

To amma kyan halaye pha? Don yanzu ba kyan ba kyan halin, don shi a rayuwar shi sam bai ba kyau tasiri kamar yadda ya bawa tarbiyar mace da ilimin ta na addini da kyawawan halayen ta ba.

 

 

Mtsss! Yaja tsaki a fili yace, “to meye nawa ma na damuwa da tunanin ta”. Wayar shi ya duba, 12 har da y’an mintina bai kwanta ba sae ya futo ya d’auro alwala, ya soma gabatar da nafilfilin shi.

Bae samu damar kwanciya ba sae k’arfe 1 da y’an mintina.

Sae muce asuba ta gari farouk.

 

 

 

****** ******

 

 

 

Da asuba ma koda ya tashi ya gabatar da sallar asubah sae ya koma ya kwanta.

 

Da safe su Zahra har suka gama hayaniyar shirin makaranta suka tafi bae futo ba, kuma basuji sautin k’ira’arshi ba kamar kullum, tun lokacin suke mamakin jin shirun nashi sae tambayar juna sukeyi “ko yaa farouk lafiya?” har suka tarkata suka tafi schl hankalin su yana kanshi.

 

Goma da rabi ummie suna zaune a tsakar gida ita da khadija suna d’an hirarsu ta rayuwar yau da kullum, khadija take cewa, “ummie wae yaya farouk lafiya yake kuwa?”.

Ummie tace, “me kika gani”.

“a’a jin shi nayi dae shiru har yanzu bae futo ba”.

Shiru ummin tayi don tabbas duk ranar da yayi irin hakan to ba lpy ba.

 

Sai ta Mik’e da kanta ta lek’a d’akin nashi, yana kwance ya lullub’e har saman kanshi da bargo.

K’arasa shiga ummie tayi tana kiran sunan shi, “Farouk! Farouk!!”

Jin bai amsa ba sae hankalinta kuma yad’an tashi, bargon ta janye a hankali tana lek’en fuskar shi tana sake kiran sunan shi.

 

Bacci yakeyi sadidan. D’an bubbuga gefan hannun shi tayi, sai gashi ya motsa a hankali tare da ambaton sunan Allah.

 

“haba farouk ka tashi mana, wannan wane irin bacci ne yau kakeyi ko baka da lafiya ne?”.

 

Mik’ewa yayi zaune tare da lalubo wayar shi ya duba time, “Kae har lokaci ya tafi haka”, ya fad’a yana Mik’ewa tsaye daga saman katifar.

 

 

Kusan a tare suka futo da ummie, wanke fuskar shi yayi ya zauna a kan tabarmar da suka shimfid’a a tsakar gidan nasu tare da gaishe da ummien, ta amsa shi tana tambayar lafiyar shi don yana dad’ewa baiyi irin wannan baccin ba, yawan ci ma sai in bashi da lafiya ne.

 

D’an shafo kanshi yayi yace, “ummie lpy qalau nake fa kawae gajiya ce”.

 

“farouk ka fad’a mun gaskiya dae in bakajin dad’i, nasan halin miskilancin ka gwara a tari ciwon tin daga masomi basae yaci k’arfin ka ya kwantar da Kae ba”.

Dan murmushi yayi yace, “Allah ummie qalau nake kawae y’ar gajiya ce kamar yadda na fad’a miki”.

 

“to Alhamdulillah yauma kana azumin ne? Koda yake nasan ma babu fashi”.

 

Murmushi wannan karon ma yayi.

 

Sun d’anyi shiru kafun khadija ta soma gaishe shi, ya amsa ta yana dad’a tambayar lafiyar jikin ta.

 

Ummie tace, “ta warke wannan sae abinda ba’a rasa masu juna biyu dashi ba, wannan kuma sai an rabu shima za’a rabu dashi”.

Shiru yayi yana dad’a jin tausayin khadijan a ranshi, shi duk matar da akace tana da ciki haka kawae sae yaji tana bashi tausayi, haka kuma data zama uwa zai dinga ganin ta da wata k’ima ta daban, don yasan zama uwa ba k’aramun babban abu bane.

 

Yana zaune yayi shiru kamar babu kowa a tare dashi, ummie suna ta hirarsu ita da khadija wadda shi dae yanajin sune kawae amma sam hankalin shi baya tare dasu.

 

Bae tab’a jin haka ba, bai san ma ko ana jin hakan ba, amma shi a yau ya tsinci kanshi a cikin tunanin wata dumu dumu, karo na farko a tarihin rayuwar shi, ayi ta tunanin mutum daga kallo d’aya kuma a damu dashi, to me hakan yake nufi.

Shi dae gashi da kallo d’aya daya yima wannan yarinyar da har yanzu ko sunan ta ma bai sani ba, bai masan ko zai sake ganin taba, yazo yayi bacci rabi da rabi saboda tunanin ta,

Ganin zata dami rayuwar shi sai kawae ya mik’e ya soma shirin futa aiki.

Wanka yayi ya shirya kamar kullum cikin kayan shi masu sauk’in kud’i da kyau, amma pa sun amshi jikin shi sosae Kae kace wasu tsadaddun kaya ne yasa.

 

Suna zaune a inda ya barsu, khadija tana tsintar shinkafa ummie kuma tana gyaran salad.

Durkusawa yayi a kusa da ummie yace, “ummie ni na futo zan huce amma inaga yau sai magrib zan dawo tunda ban samu damar ma yin aikin sassafe ba”

Ummie tace, “ai yau da gobe sae Allah kuma jiki da jini, ni dae abinda nake so ka maida hankali sosae kuma ka dinga ajiye wani abu madadin balance, tunda kaga Kae ba haya faces bane zuwa nan da shekara sae kaga ka mallaki gidan ka d’an k’arami, kaga daga nan sae maganar aure, kaema kamar yadda duk rabin abokan ka sukeyi, ka mallakin naka iyalan, fatana dae Allah ya had’a ka da mace ta gari wadda zata share maka hawayen ka”.

 

 

Shiru yayi kamar wanda ruwa ya cinye, har sae da khadija ta d’an saci kallon shi, yana durk’ushe kamar me tunanin wani abu.

“Wae farouk kana jina kuwa?” muryar ummie ta katseshi daga d’an k’aramun tunanin daya soma tafiya.

Mik’ewa tsaye yayi, y’an kud’in da sukayi saura a jikin shi ya ciro ya ajiyewa ummie a kusa da ita, “gashi ummie ni na tafi”.

Kud’in ta duba tace, “farouk ai daka bar Kud’in ka don ba abinda muke buk’ata ko wani abun ba sai kayi dashi ba”.

 

“ba wani abu ummie ku ajiye ae wani abun zai iya tasowa, ni dae sai Allah yayi mun dawowa”, ya K’arasa fad’a yana yin gaba.

Ummie ta bishi da addu’ar Allah ya tsare, khadija ma haka, ya amsa su yana fucewa daga gidan.

 

Ummie tabi bayan shi da kallo cike da tausayawa, wato a duniya Allah ya sani tana tausayawa rayuwar farouk, duk y’ay’an ta ba wanda yake mata abinda farouk yake mata, ya kasance d’aya tamkar da dubu a gareta , mutum neshi mai matuk’ar hak’uri, juriya, yakana, da kawaeci, ta sani Shekarun shi sunkae, a matuk’ar takure yake amma in ba ita data lak’ance shi ba babu wanda zai iya shaida hakan. (Allah ya tallafi rayuwar ka farouk).

Ta fad’a a fili, khadija ta amsa mata da ameen.

 

 

 

**********

 

 

Zaune take a saman balcony na babban falon gidan su, taci kwalliya cikin wata doguwar riga data fidda salsalar shep d’in jikin ta gaba d’aya, kanta a b’ude yake gashin kanta ma’abocin tsawo da santsi yasha gyara sai d’aukar ido yake, ta tufkeshi a k’eyarta.

D’an madaidaicin table d’in dake gabanta cike yake da abinci kala kala kamar zata iya cinye su Duka, d’aya daga cikin masu aikin kitchen d’in gidan su ce durk’ushe a gabanta tana jiran umarnin ta, Yayin da ita ta d’ora kafarta d’aya kan d’aya tana danna wayarta kamar wata sarauniya.

 

Ta d’auki tsawon lokaci a gurin bata motsa ba har maid d’in gwuiwowinta suka sage ta zauna sosae, gashi ba abun ka tafi ba ka tafka laifin da za’a yima rashin mutumci koma ayi maka sanadin aikin, (su kuma abinda ya rik’e su a gidan shine, Kyakykyawan biya da ake musu da kuma kyautatawar alhaji ja’afar da taimakon shi garesu, akwae wani lokaci da bazata tab’a Mantawa ba, sun shiga matsala a sanadiyyar gidan haya da ake musu wulak’anci, a k’arshe alhaji ja’afar ya siyi gidan ya mallaka musu ita da mijinta, to bama wannan me aikin kadae ba kusan haka yakewa duk ma’aikatan gidan, wannan shine dalilin daya sa suke iya jure kowani wulak’anci da k’ask’anci na tilon y’ar shi arfah, kuma hadda suna hadani da kusan rabin rayuwar ta ma yanzu ya karkata ne zuwa k’asar da take karatu indae ba hutu tazo ba irin haka, sannan mahaifiyar ta sofiyyah sam bata da irin halin ta, ita bata d’auke su ma mutane ba, iyakarta dasu umarni ne, kuma muddin ka kiyaye zaka ji dad’in zama da ita)

 

“ooooh wae abincin ma umarni na kike jira?”.

 

Arfah ta fad’a a lokacin data ajiye wayarta tana kallon mai aikin, “I’m soo sorry madam am really sorry”, mae aikin ta fad’a tana k’ok’arin soma saving d’in ta, jikinta har rawa rawa ma yake.

 

A d’an madaidaicin tray ta had’a mata komae da komae tare da fad’a mata, “maddam ur breakfast is ready”.

 

Sake ajiye wayar ta tayi ta kalli tray d’in ta kalli mae aikin, daga kallon da tayi maid d’in ta gane she’s in trouble, to meye kuma batayi dae dae ba.

 

Matsowa kusa ta kumayi ta russuna, “is there something wrong maddam”.

 

Harararta tayi cikin izza da ginshera tace, “ke bak’uwa ce a gidan nan?”.

 

Da sauri matar daba wani gane hausa sosae take ba ta girgiza kanta, “a’a madam”

 

Da hannu tayi mata alamar ta dad’a matsowa kusa.

 

Ta k’araso cikin dar dar da zullumi, kafun ta ankara sai jin saukar yatsu biyar tayi a fuskar ta, “dama haka ake saving d’in brkfst dina?”.

 

Da sauri mai aikin ta sake russunawa tana dada bata hak’uri.

 

 

Sai ta d’auki k’aramun plate ta soma hada mata cikin tsananin tsoron kada ta kumayin wani kuskuren dan batasan hukuncin da za’a yanke mata ba kuma.

 

Tana cikin zubawa da yake arfahn hankalinta yana kai sai ji tayi kawae tace, “is ok, u can go”.

 

Da saurin ta kuwa tayi gaba tana sauke ajiyar zuciya da hamdala, da Allah ya tak’aita abun ya tsaya iya haka.

 

 

 

Cikin nutsuwa da yauki takecin abincin kamar bataso, nasan shima da son samu ne wani zata sa ya tauna mata shi.

 

 

Bata wani ci na kirki ba ta ture table d’in tare da juya kujerar da take kae, wayarta da take hannun ta ce tayi ring, fareeeda ce, don haka da d’an hanzarinta tayi picking, “kina ina ne dear nazo fa tun dazu”.

 

Wani murmushi ne ya subuce ta saman fuskar ta, daya kara mata kyau tace, “owk ki sameni a balcony na middle parlor, opposite to part d’in abbie”, I can see weather u can find me”.

 

Tana gama fad’a ta ajiye wayar saman cinyarta tare da kwantar da kanta jikin kujerar da take kae, yayin data lumshe fararen oily eyes d’in ta.

 

 

Tsayuwar mutum da taji a kanta yasa tayi saurin Bude idanun ta batare data shirya ba, tana shirin zatayi magana sukayi 4 eyes da yaya fahad.

 

Take ya sakar mata murmushin sa mae tsada yana jawo kujera d’aya ya zauna kusa da ita, “barka da safiya miss arfah”.

Ya fad’a har lokacin idon su cikin na juna.

 

Saita lumshe idanun ta tare da motsa labbanta, baiji abinda tace ba amma ya gane ta amsa shine.

 

 

Sun danyi shiru babu Wanda yace ma wani kanzil a cikin su kafun fahad yace, “yaushe zaki koma UK ne”.

 

 

“end of dis weekend” ta bashi amsa har lokacin idonta a lumshe.

 

Shiru ne kuma biyo baya kafun ya sake mata wata tambayar, “kenan kusan tare zaku tafi da abbie?”.

 

 

 

“wata k’ila” ta sake fad’a mishi kai tsaye.

 

“to bikin ki da muhsin fa, wata nawa ya rage?”

 

 

Babu shiri ta mik’e zaune tana bin shi da wani irin kallo daya kasa fassara shi lokaci d’aya.

 

Murmushi yayi mae ciwo, baice komae ba sai kallon ta kawae da yake yana dad’a jin yadda zaiyi missing d’in ta harta cikin jinin jikin sa, ji yake kamar yayi hauka idan ya tuna yana gab da rasa ta gaba d’aya.

 

“kiyi hak’uri arfah, Jiya munyi magana ta rashin fahimta dake, abinda nake nufi is clear, kuma idan kikaji dalilae na zaki amince”.

 

 

Sai ya tsaya yaja dogon numfashi kafun yaci gaba, “idan kika duba arfah zakiga cewa maganar auren ki da muhsin ba wae kai tsaye aka k’irk’ire ta ba rana tsaka, a’a ta faro ne tun kafun rasuwar alhaji umar (wato mahaifin su muhsin, aminin abbie)

 

Mutumin nan tun kina k’arama yake matuk’ar sonki da d’an shi muhsin, kuma har ya rasu yabar duniya da wannan burin a ranshi, da Allah baiyi rabon shi zai k’ulla ba, to kinga ashe shima abbie d’orawa yayi.

 

Sannan wani abu na 2 daya kamata kiyi dogon nazari akae, a rayuwa abbie fa bashi da kamarki, duk duniya baya son abinda zai tab’a ki komae k’ank’antar shi, shine dalilin da yasa yafiki son duk wani abu da kike so, kuma ya tsani duk wani abu da kika tsana.

Abinda nake son na fahimtar dake anan shine, akwae dalilin da yasa abbie yakeson yi miki dole akan auren muhsin duk da yasan yadda bakyaso.

 

Idan kika duba arfah, abbie yayi miki dukkan wani gata kuma bae tab’a yi miki dole akan komae ba, kin rayu tamkar zinariya, ya jik’a ki da gata na gaske da acikin y’ay’an masu gata ma zaki iya kasancewa a sahun gaba, to kinga ashe a duniya ko wuta yace ki fad’a bai kamata kiyi mishi musu ba, balle yana da k’imar da bazaki tab’a yadda ja inja ta had’a kuba……..

 

 

 

 

 

 

_fans afwan kwana 2 ina samun matsalar network kuma wattsapp d’ina baya responding_

 

_Duk da hk ina ganin comment d’in ku, kuma hakan shike k’aramun karfin gwiwa, phatan zamuci gaba da tafiya tare👍_

_Thnks alot_

 

 

 

 

 

 

 

 

Comment✍️

8/13/22, 8:47 AM – Merhreeyeart❤️: 🏡 *AHALI D’AYA*

*_{auran bazata mafi k’ask’anci da wata irin rikitacciyar rayuwa mai d’auke da zallar k’iyayyah}_*

 

 

 

 

_Written by_

*Mareeyeart lawal*💞

 

 

 

_In dedication to my lovely ones_🥰

 

 

 

 

Page 7 _(seven)_

 

 

Idan kikayi wani abun arfah nakan dad’e ina mamaki, amman idan na zurfafa tunani sai na ga abinda kikayi fa iya gaskiyar ki kenan, kuma ko nine a irin k’adamun da kike Kae irin abinda zanyi kenan, gaki da kyau, ga gata gaba da baya na uwa da uba sannan ga kud’i an tara miki, kinga a rayuwa baki da wata matsala da zata hanaki yin yadda kike so, sab’anin wasu y’ay’an dako d’aya a cikin abubuwan da kika mallaka basu rab’a ba, hatta ni da nake miki wannan maganar kuwa.

 

Shiru yayi yana dad’a nazarin fuskar ta don ya gane yadda ta karb’i zancen, idon ta yana kanshi amma bazae iya fassara yanayin data ke ciki ba Kae tsaye.

 

Sai ya sake kwantar da murya sosae yaci gaba da fad’in, “da wannan nake rok’on ki don girman Allah ko a fuska kada ki yadda abbie ko ammie su gane cewar har yanzu bakya son muhsin, so d’aya a rayuwar ki ki kyautata musu ta hanyar nuna musu cewa sun isa da rayuwar ki, kuma kin basu dama su yanke miki ko wane irin hukunci da suka ga yayi dae dae dake da rayuwar ki, tunda kinsan bazasu tab’a cutar dake ba, maganar soyyayyar dake tsakanin mu kuwa ina so ta zamo tarihi, ki D’auka ta huce kamar yadda na d’auka, zanje nayi addu’a arfah, kema ina son kiyi kuma ki nemi zab’in Allah, daga k’arshe ina fatan zakiyi mun Kyakykyawar fahimta, ki karb’i muhsin don soyyayyar dakike ma mutane 2 nan da baki da tamkarsu, ki karb’i soyayyar muhsin don shawarar da d’an uwanki, masoyinki kuma babban abokin ki yayanki ya baki, lastly kiso shi kuma ko Don albarkacin soyyayyar da mahaifin shi ya nuna miki da yana raye”……

 

 

Sae yayi shiru tare dasa hannu ya d’auke hawayen da suke shirin zubo mishi, kafun ya mik’e gently ya soma tafiya, sai dae taku uku yayi kacal ya kasa yin gaba sakamakon ruk’unk’umeshi da tayi ta baya, tana fashewa da wani irin kuka mae rad’ad’i da shiga zuciyar mai sauraro.

 

Sun d’auki kusan minti 3 a haka tamkar wad’an da aka dasa a gurin babu Wanda yake ko cikakken motsi a tsakanin su.

 

 

K’arar sakin tray da sukaji cikin kunnuwan su shi yasa farouk saurin cire hannuwan ta daga jikin shi ta baya, tare da share hawayen da suka rufe idanun shi, kallon kallo sukayi shi da fareeda data ci burki tamkar mutum mutumi tana kallon su cikin wani irin mabayannin tashin hankali daya kasa b’oyuwa a saman fuskar ta.

 

A hankali ya kewaye ta batare dayace komae ba ya bar gurin. Arfah kuma ta durk’ushe a gurin tana wani irin jan numfashi.

 

 

Da hanzari fareeda tayo kanta tare da rungumota jikinta tana kiran sunan ta, a hankali tayi wata magana k’asa k’asa tare da dank’e hannun fareedan sosae, kafun kuma numfashin ta ya d’auke d’if.

 

 

Tsabar rud’ani fareeda rasa yadda zatayi ma tayi, gashi wayarta ta baro ta cikin jakarta, daman suna gama waya da arfan kitchen ta nufa saboda ko break bata tsaya tayi ba ta taho da zumud’in yadda zata soma aiwatar da shirin ta, sai kuma tayi mugun gani, (to mugun gani mana ta samu arfah rungume da masoyin ta suna kuka ita dashi, kuma babban abin bak’in ciki saboda son junan su, wata irin zuciya data d’ebe ta, tasa ta sakin trayn hannun ta babu shiri a lokacin).

 

Wani irin tsaki taja a fili cike da jin ninkin tsanar arfan a cikin zuciyar ta. Badon gudun fad’awa matsalar da zata toni asirin taba data watsar da arfahn anan ta mutu ma kowa ya huta.

 

Tsaki ta kumayi a karo na 2 ta ajiyeta a saman tiles d’in gurin tayi hanyar part d’in ammie a gigice kamar gaske.

 

Sai dai tayi rashin sa’a don ammien bata nan, sai ta juya akalar ta zuwa ga part d’in fahad direct.

 

Bata tsaya neman izini ba kawae ta fad’a cikin parlon, baya parlon, kasancewarta ba bak’uwa ba a gidan sai kawae ta nufi bedroom d’in shi.

 

Tana murd’a mabod’in k’ofar shi kuma yana futowa daga bathroom fuskar shi duk alamun ruwa haka idon shi har lokacin da alamun kukan yake.

 

Da wani irin jirkitaccen kallo ya bita don ko arfah bata mishi irin wannan kutsen, kafun ya fad’a abinda yayi niyya ta dakatar dashi ta hanyar fad’in, “yaya fahad arfah! Arfah tana can ciwonta ya tashi…… “.

 

Ai bae bari ta k’arasa ba ya ture ta yayi waje a sukwane.

 

Tana kwance a inda fareeda ta barta babu inda yake motsi a jikinta.

 

Cak ya d’auko ta ya nufi part d’in ta, fareeda na biye dasu a baya duk ta gigice kamar irin har zuciyarta d’in nan.

 

Likitan ta ya kira kusan 4times baiyi picking ba, duk sai ya kuma shiga rud’ani gashi shi ba likita ba bare ko taimakon gaggawa ne ya soma bata, gashi baya son a d’agawa su ammie hankali don har gargad’in fareeda yayi akan kar ta fad’a musu.

 

Sai safa da marwa yake a d’akin lokaci bayan lokaci yana d’auke hawayen dake zubo mishi, daga k’arshe ma sae ya samu guri ya zauna yadinga kuka kamar wani mace.

 

Duk wata dabara sai ta kwace mishi ma. Aftar lyk 10 mint sai ga kiran doctor shuraem d’in.

 

Da saurin shi kuwa ya d’aga, “afwan injiniya ka kira lokacin ina d’an wani uzuri ne”.

“OK ba damuwa jikin patient d’in kane fa yau ya tashi, kaganta ma wallahi tun d’azu ko motsi batayi”.

 

“ya salam! Yanzu kuna ina ne? Ina phatan dae bakuyi gaggawar kaita asibiti ba?”.

Fahad yace, “ai ni tunanin hakan ma baizo mun ba muna gida, plzzz doctor kada ka b’ata lokaci kazo yanzu”.

“owk ganinan zuwa”.

 

Daga haka duk suka ajiye wayoyin, sai lokacin hankalin farouk ya d’an kwanta kad’an, don yasan da ikon Allah da doctor shuraem ya k’araso ne.

 

*************

 

Doctor shuraem yayi duk wani abu don ya samu numfashin ta ya dae dae ta, kuma alhamdulillah yanzu ta dawo hayyacin ta, sai dai yasa mata oxygen don ta taimaka mata zuwa nan da good 15 hours,tare da surkud’a mata allurar bacci.

 

 

Aikuwa ba b’ata lokaci wani irin bacci mae k’arfi yayi awon gaba da ita.

Zama doctor shuraem yayi bayan komae ya dae dae ta ya fuskanci fahad sosa,

“ko zan iya ganin hajiya sofiyyah mamanta?”

Shiru fahad ya d’an yi kafun yace,”gaskiya yanzu dae bata nan, amma likita akwae wata matsala ne?”.

 

“babbah ma kuwa”, likitan ya fad’a tare da soma harhad’a kayan shi.

 

Fahad ne cikin damuwa da son jin matsalar da likitan ya ambata yace, “to amma likita me zai sa bazaka iya fad’a mun ba? In yaso zan iya isar da sak’onka gareta idan ta dawo”.

 

Murmushi likitan yayi ya saci kallon fareeda data zabga uban tagumi kamar me tunanin wani abu amma duk kunnuwan ta suna tare dasu.

 

Sai ya kalli fahad d’in yace, “kayi hak’uri engineer bawae bazan iya fad’a maka bane, a’a akwae sharrud’an dana tab’a gindaya mata ne wanda in aka bisu yadda ya dace zata iya rabuwa ma da ciwon ta warke gaba d’aya, to amma yanzu naga kamar ba’a ma amfani da wad’an can dokokin nawa, saboda yanayin ciwon is now increase with almost 20 percent, that’s ya zama 50 percent out of hundred, rayuwar ta tana cikin risk idan har matakin baiyi decreasing ba, don haka nake son don Allah a kiyaye duk wani abu dazai b’ata mata rae har ya kawo tashin ciwon nata, saboda shi ciwon *ZUCIYA* da kake gani bawae k’aramun ciwo bane da za’a dinga wasa dashi”.

 

“Ina phatan kuma zaku bamu had’in kae wajen taimakawa rayuwar ta arfah”.

 

“Insha Allah” fahad ya fad’a. Daga nan kuma sukayi Sallama da likitan zai huce, kallon fareeda yayi data tafi wani mugun tunani da k’ulle k’ullen sharrin ta.

“y’ar uwar likitoci yae, yaushe zaku koma k’asar kune, kinsan fa keda patient d’ina nan ba k’asar ku bane bak’i ne”.

 

Murmushi tayi mishi kawae wanda ya matuk’ar bashi mamaki kuma har ya tafi da al’ajabin abun a ranshi.

Ya dad’e yana neman hanyar da zaiyi mata magana, ya kuma dad’e yana neman shiga a gurin ta amma kallon arzik’i bai tab’a had’a shi da ita ba, doctor shuraem tun daya d’ora idanun shi a kanta shekaru uku baya ya kaimu da k’aunarta sosae a ranshi, yabi duk hanyar data dace don ganin ya sameta abun ya faskara, sai yanzu ma daya dad’e da soma cire ta daga zuciyarshi sae gashi yau ya fara jiyo k’amashin nasara.

 

 

Har sukayi sallama da fahad ya shige motarshi yana al’ajabin fareedan, karo na farko tayi mishi murmushi mae ma’ana, yaji shi kuma har cikin ranshi.

 

Fahad ko daya koma bai shiga bedroom d’in ba saboda wanzuwar fareeda a gurin sai yayi zaman shi a parlourn.

 

 

Wayar ammie ya kira a lokacin har sun d’auko hanyar dawowa gidan ita da abie.

 

“fahad muna hanya ina fatan dae komae lafiya?”

 

Ta fad’a mishi cikin harshen larabci.

 

Sai ya amsa mata da, “to ammie sai kun k’araso kawae, bawani matsala babba bane, kawae jikin babynki kine yau ba dad’i”.

 

A kid’ime ta soma jero mishi tambayoyi, “meya sameta fahad? Kuma tun yaushe ne? Amma ba jikin nata bane ko? Ka kira likitan ta kafun mu k’araso”.

 

Wannan maganganu data jero shi ya janyo hankalin abbie shima ya soma tambayar meya samu arfahn.

Duk lokaci d’aya suka firgice, da kyar fahad ma ya samu yayi musu bayanin da suka fahimta.

 

Tafiyar mint 30 suka azalzali drivern abbie yayi ta a cikin 15 mint.

 

Fahad yana kwance a saman doguwar kujerar dake parlorn sai gasu sun shigo afuja’atan har had’a baki suke wajen tambayar, “ina take”.

 

Mik’ewa yayi zaune yanayi musu sannu da zuwa tare da nuna musu k’ofar bedroom d’in yace, “tana ciki bacci ma takeyi doctor shuraem yazo ya duba ta har ya tafi yace………”.

 

Ai babu Wanda ya jira jin k’arshen zancen nashi a cikin su.

Sukayi cikin bedroom d’in nata da sauri.

 

Fareeda tana zaune a gefanta har lokacin tayi nisa cikin duniyar tunani, sai kawae ta gansu unexpect.

 

Bacci takeyi sadidan.

Kusa da ita abbie ya zauna tare da kamo tafin hannun ta yana kallon fuskar ta cike da so da tausayawa.

 

Itama ammie kusa da abbie d’in ta zauna tana amsa gaisuwar da Fareeda take mata, sai lokacin alhaji jafar ya Ankara da wanzuwar ta ma a gurin.

Russunawa tayi sosae ta gaishe shi, ya amsa had’e da d’ora tambayar garin ya akayi ma ciwonta ya tashi, duk shiru sukayi daga fareedan har fahad.

 

Shima bai kuma tambaya ba sai ya d’auko wayar shi ya kira likitan nata, sun tattauna sosae akan matakin ciwon nata wanda shi bae tab’a sani ba.

 

Sosae ranshi ya b’aci yaita fad’a akan b’oye mishin da akayi da kuma yadda aka karya dokar likitan.

 

Babu wanda yace mishi kanzil a cikin su har ya gama sannan fahad ya bashi hak’uri.

 

Wannan abun daya faru yasa ran sofiyya ya b’aci sosae, sai kawae ta d’auki jakarta tayi ficewar ta daga d’akin.

 

Da ido kawae ya bita batare da ya kuma cewa komae ba.

 

***********

 

 

Misalin k’arfe 9:35 na dare ya futo sanye da jallabiyya Brown colour data sake futo da kyaun shi na bafulatani usul, ta kuma b’oye Shekarun shi.

 

A hankali yake takawa har ya isa part d’in nata, ya tura kofar a hankali ya shiga, sassanyan k’amshin dake manne da d’akin ne ya soma yi mishi maraba.

Tana kishingid’e jikin tum tum d’in da aka k’awata parlorn dasu taci uwar kwalliya cikin wata doguwar riga d’inkin atamfah, sai ka d’auka irin matashiyar ce yar kimanin 25 years haka.

 

Cikin takun shi na nutsuwa ya isa gareta ya zauna a gefanta, wayarta ta jawo tashiga dannawa tamkar ma bata san da wanzuwar wani mutum a gurin ba haka ta share shi.

 

Shiru yayi kawae yana nazarin ta, a tsawon shekara 27 da sukayi tare da ita bae tab’a yi mata fad’a ta karb’i kuskuren ta ba, kuma koda sab’ani suka samu sae dae shi yaje don ya bata hak’uri Amman ita bazata tab’a neman saba, kuma idan yazo ma yadda tayi yanzun haka takeyi mishi. Shi mutum ne mae matuk’ar hak’uri, yakana da kawaeci irin na wanda jinin fulani ziryan yake yawo a jikin su.

 

Ajiyar zuciya ya sauke tare da zare wayar daga hannun ta yace, “ki tashi sosae nazo ne ina son muyi wata magana dake sofiyyah”.

 

Sai ta Mik’e zaune fuskar ta a d’aure.

 

Gyara zama yayi sosae ya fuskance ta, “shin nan gidan idan akace bana nan tunda ni ba mazauni bane waye shugaba?”.

 

Shiru tayi bata amsa shiba, kuma hakan bai dame shiba yaci gaba, “shin daman haka ya kamata jagora ya kasance, a matsayin ki na wakiliyata sofiyyah shin ya kamata ace abubuwa suna faruwa a gidan nan da bakisan da zaman suba? Shin bayan arfah kina da wata y’ar ne daban sani ba?, ki amsa mun tambayata mana sofiyyah”.

 

Kallon shi kawae tayi amma bata iya tace komae ba.

Sai yaci gaba da maganar shi, “nasan amsarki itace babu, to meyasa bazaki tattara attention d’in ki gaba d’aya a kan taba tunda kinsan ga yadda yanayin ta yake, gaskiya bazan b’oye miki ba sofiyyah sam banji dad’i ba, yarinyar nan kinsan duk duniya bani da kamarta, idan akace yau ta mutu…….. Idan akace yau babu arfah to bamu da sauran wani d’a ko y’ar da zamu ce tamu ce, kuma kinsani likita ya tabbatar da bazaki kuma aihuwa ba balle mu haifi wani, haba sofiyyah kiyi tunani da karan kanki mana, ya kamata a dinga sakaci da lafiyar ta, ace Wae har likita ya gindaya wasu sharudda dani ban san suba?, sannan idan muka ajiye wannan batun, a cikin gidan nan na bincika babu ma’aikata 2 maza, dana tambaya sai akace mun an sallame sune, meyasa? Shin kinsan dalilin da yasa nake tafe da sadiq driver kuwa? To banajin kaf cikin ma’aikatan nan za’a samu kwatankwacin sa a gaskiya da rik’on amana, amma sae naji labarin wai an kore shi, shin laifin me yayi da zafi haka da har za’a koreshi baza’a jira har Allah yayi mun dawowa nasan da matsalar ba? dama haka shugabancin yake ko?”.

 

B’oyayyar ajiyar zuciya ta sauke a lokacin daya Kae aya a zancen sa tasoma da fadin, “jafar sanin kankane cewa arfah ba dani kad’ae take rayuwar ta ba, ko ka manta ne cewa ta shafe wata 6 a k’asar England batare da tazo ko hutu gida ba? to ni taya zansan dawa dawa ma take huld’a kuma me sukeyi mata na b’acin rae da yake haddasa mata wannan matsalar?, ma’aikatan da kake magana akae kuwa ni d’aya nasani, shine Sulaiman a cikin masu watering d’in flowers ne kuma saboda na isa ne da yayi badae dae ba na yanke mishi irin hukuncin daya dace dashi, ko kuma yauma zaka nuna mun iyakar tawa ne”.

Sae ta soma kuka, “saboda kaga bani da kowa, ni ba y’ar k’asar ku bace shiyasa kake yimun irin haka ko ja’afar, saboda kaga na rabu da kowa nawa saboda kae shine yasa kake wulak’antani yadda kake so……..” ta Kae k’arshen zancen tana sake fashewa da wani Sabon kukan.

 

Murmushi alhaji ja’afar yayi yace, “ai kuwa bae kamata kiyi irin wannan tunanin ba tunda arfah jininki shine yake yawo a jikinta, kuma kinsan halin muskilancin ta, to har yanzu sai na fad’a miki adadin mutanen da take mu’amala dasu a UK, kuma tunda taje ciwo irin haka bai tab’a samun taba sai ta dawo gida ko kina tunanin bana biye da duk wani takun tane?, to har gurin da take yawan zuwa ma sae na fad’a miki, maganar family kuwa nima na rabu da nawa familyn saboda ke, saboda soyayyar da nake miki sofiyyah, ke kanki kin sani ina sonki fiye da komae dana mallaka a rayuwar nan, tunda na had’u dake wata mace bata tab’a burgeni ba bare har nayi tunanin d’ora idanu na akan wata, kina kallo har mace mahaifina ya auramun lokacin ina k’asar Egypt, irin yadda yayiwa ibraheem da khadija amma ina dawowa dake ko kallon fuskar ta banyi ba na sake ta kuma duk don saboda son da nake miki, bazan tab’a iya yin adalci tsakanin ki da wata matar ba, haba sofiyyah keda muka ajiye wannan maganar sama da shekaru 18 meye na dawo dashi kuma yanzu?”.

 

Kuka take sosae amma ta gasgata maganganun shi.

 

Sai ya rungumota jikin shi cike da kwantar da murya yaci gaba da fad’in, “kin isa dani da dukiyata har ma da ma’aikatan da suke aiki a k’ark’ashi na bana gida ba kad’ae har Wanda suke company na ma duk Wanda kika kora ya koru, kawae dae shi saddiq d’in ne banji dad’i da mukayi loosing mutum mae amana ba kamar shi”.

 

“to kayi hak’uri hubby na insha Allah hakan bazae sake faruwa ba”.

 

“ya huce matata farin ciki na”.

 

Duk sae sukayi dariya cike da so da kulawa sukaci abincin tare anan parlorn ta kamar yadda sukeyi a duk lokacin da yake gari.

Tare suka futo da ita.

Ita ta tsaya d’auko mishi wayar shi a part d’in shi.

Shi kuma yayi hanyar part d’in arfah, duk da bae dad’e da baro gurin tanba amma yana son sake ganin jikin nata.

 

Tana zaune a parlour ta d’ora k’afar ta saman glass center table dake gabanta, sanye take da doguwar riga blue da akayi mata ado da wasu irin stones masu walwali da d’aukar ido kanta babu d’an kwali as usual. Fuskar ta tayi fayau kuma ta dad’a haske kamar wadda tayi kwanaki tana jinya.

 

Hannunta rik’e da d’an k’aramun bowl dake d’auke da kayan fruits tana ci tamkar wadda akayi ma dole, ita kad’ae ce a parlourn hakan yasa tana ganin shi ta sauke k’afar ta kasa tare da ajiye bowl d’in fruit d’in hannun ta.

 

Take fuskar ta ta washe da fara’a ta yunk’ura da kyar ta mik’e.

Da sauri ya isa gareta tare da mayar da ita ya zaunar a saman sofa d’in, “ki zauna kawae ko baki ga har yanzu jikin ki babu k’arfi bane?”.

 

 

 

 

 

 

_afuwan fans har yanzu dae ena fama da matsalar network_

 

 

 

 

 

 

 

_comment_✍️

8/13/22, 8:47 AM – Merhreeyeart❤️: 🏡 *AHALI D’AYA*

*_{auran bazata mafi k’ask’anci da wata irin rikitacciyar rayuwa mai d’auke da zallar k’iyayyah}_*

 

 

 

 

_Written by_

*Mareeyeart lawal*💞

 

 

 

_In dedication to my lovely ones_🥰

 

 

 

 

Page 8 _(eight)_

 

 

 

Sae ta shagwab’e fuska, “abie naji sauk’i fa”.

Zama yayi kusa da ita yana dubanta yace, “nima ae bance bakiji sauk’in ba, kawae nafison ki huta sosae”.

 

Murmushi tayi tana sake jin k’aunar mahaifin nata sosae a cikin ranta, take maganganun fahad suka soma dawo mata daki daki, sai ta tafi yi musu fashin bak’i.

Har mahaifinta yayi ta magana ba tasan ma yanayi ba.

 

Shigowar ammie ne ya dawo da ita hayyacin ta daga d’an k’aramun tunanin data soma tafiya.

 

“Wae me yake damun kine mamata?, tun d’azu ina ta magana ina hankalin ki ya tafi?”.

 

Shiru kawae tayi har ammie ta k’araso kanta yana k’asa ta kasa furta ma komae, tana jin kamar ta futo ta fad’awa abie gaskiyar abinda yake cikin zuciyarta, to amma wani abu da batasan ko meye ba yazo yayi mata bake bake a saman mak’ogwaro ya hana numfashin tama hucewa yadda ya kamata.

 

Zama ammien tayi itama a kusa da ita suka sata a tsakiya.

Dafa kanta yayi tare da sake kiran sunanta, “Arfah idan akwae abinda yake damunki ki futo ki fad’a mana nida mahaifiyarki, tun wuri ma in wanda zamu iya magance miki shine muyi miki maganin sa da kud’in mu da jikin mu, domin kuwa a duk duniya bamu da kamar ki kema kin sani, idan bamuyi miki ba wa zamu yiwa?”

 

D’ago kanta tayi tana duban mahaifin nata, ji take kamar tayi hauka a duk lokacin data tuna da maganar aurenta a cikin zuciyarta.

 

Jinta shiru sai kawae ya d’ago fuskar ta, hawaye ne suke sauka d’aya nabin d’aya.

 

“yaa salam! Baby yanzu har akwae abinda zai dameki da bazaki iya bud’a baki ki fad’a mana ba?”.

Tab’e baki ammie tayi batare da tace musu kanzil ba daga shi har y’ar tashi.

 

Rarrashin duniya babu irin wanda baiyi mata amma tak’i bud’e baki tace komae, daga k’arshe ma sae ta b’ige da tambayar shi, “abie yaushe ne bikin yaa muhsin d’in?”.

 

Sai yayi murmushi irin nasu na manya yace, “yanzu maganar auren muhsin d’in ce duk ta saki cikin damuwa haka?”.

 

Sai lokacin ta samu kanta cikin rud’ani karo na farko kuma taji kunyar abin da tayi d’in a cikin ranta, tsabar diriricewa ma sai kawae ta hau girgiza Kae, hakan da tayi kuwa ya k’ona ammie sosae don bataso tace a’an ba.

 

Alhaji ja’afar ne ya kuma cewa, “saura sati biyar baby kinsan nayi cancelling komawa makarantar ki har sai bayan bikin ku keda muhsin d’in, sai ku tafi tare, shi zai zauna anan k’asar na tsawon sati uku kacal sae ya huce Italy inda yake d’an harkokin kasuwancin sa, ina phatan hakan da muka tsara yayi miki?”.

 

Wata irin zabura da tayi lokacin da yake wannan maganar ta zuba mishi ido kamar wadda aka turowa da sak’on mutuwa afuja’atan.

 

Har saeda ya juyo ya kalleta da mamakin yadda tayi d’in, sai lokacin ta waske ta hanyar fad’in, “da wuri haka? Na d’auka sae watannin da aka sa Sun cika”.

 

“eh to da hakan dae mukaso to sae kuma wasu dalilae suka taso da suka sa dole zamu dawo da bikin ayi shi cikin few weeks”.

 

Arfah kam dataji wannan labari tamkar saukar aradu sai ta sake lafewa a jikin abie d’in tana sake sakin wani Sabon kukan na tausayin kanta da rayuwar ta.

Cikin rarrashi sosae yake ci gaba dayi mata magana tare da nuna mata irin kyawawan halayen da muhsin d’in yake dasu, sannan ga wani advantage na 2 a auren yaron yana da rufin asirin shi dae dae gwargwado, kuma duk family d’in shi suna sonki kamar yadda shima yake sonki, zasu kula dake da rayuwar ki ko bayan ba raena nasan bazaki tab’a yin kukan maraici ba.

 

Ire ire wad’annan maganganun da yake sam ba fahimtarsu take ba tana dae sauraron shi, ammie kam mik’ewa tayi don bata ga amfanin zaman ta a gurin ba, tana jin zafin zancen nashi fiye da arfahn ma da yakewa maganar.

Shima mik’ewar yayi yace, “bari mu tafi gaba d’aya, ya duba agogon bangon dake mak’ale a parlon, lokacin baccin tama har ya huce”.

 

Da kanshi ya taemaka mata ta shiga har bedroom d’in ta, a gefan gado ya kwantar da ita yace, “kiyi bacci mae dad’i babie kinga fareeda ma tuni tayi baccin ta, ki ajiye wayarki a kusa ko zakiji wani abun na rashin jin dad’in jikin ki kiyi maza ki kirani ki ammien ki”.

 

Kanta kawae ta gyad’a mishi tare da kwanciya sosae akan gadon, don yau batajin zata kuma sake yin wani wankan saboda har yanzu idan ta mik’e tana jin jiri.

 

 

Daga k’arshe addu’oi ya tofa mata sannan ya sumbaci goshin ta ya fuce, bayan ya rage mata hasken d’akin.

Fareeda da tayi baccin lamb’o sai ta bud’e idanun ta jin fucewar abie.

 

 

Tsaki taja a k’asan zuciyarta, yau taji matuk’ar farin ciki da zancen mahaifin arfahn, anzo gurin da take son tuntuni aje, zanga k’arshen soyayyar nan taku laila majnun.

 

Sai ta saki murmushi a saman fuskar ta.

 

 

************

 

 

To farouk kuwa cikin kwanakin nan gaba d’aya ya sauya, haka kawae sae ya tsinci kanshi da rashin jin dad’in rayuwar shi.

 

Ga wani irin tunani na rashin tabbas daya sark’eshi, a wasu lokutan sae ana tsaka da hira dashi sae kawae ta fad’o mishi a rae, yakanji wani irin tashin hankali a cikin zuciyar shi game da ita, sai ya dinga jin kamar bazasu sake had’uwa ba, ganin duk wannan tunanin basune mafita ba sae ya sake ninka ibadun shi, kuma ya sake maida kanshi busy, har doguwar hirar dare yanzu yake zama cikin su sulaeman a k’ofar gidan su sulaeman d’in.

 

Wasu lokutan ma har sae ummie ta kira shi tana fad’an ina ya tafi gashi zasu kulle gida sannan yake tahowa.

 

 

Sababbun halayen nashi kuwa har sun soma damun ummie, har ta soma yi mishi fad’a akan ita fa bazata d’auki wannan gantalin ba shin ina ma yake zuwa? Ace tun safe mutum in ya futa yana kan kwalta banda sallah da cin abinci ba abinda ke tsayar dashi, kuma ace ya dawo gida lokacin da kowa yake sa hak’ark’arin shi ya kwanta sai kuma mutum ya sake yin gaba, to wallahi bazan d’auki wannan rashin hankalin ba gwara tun wuri ma ka watsar tunda ai da can ba hakan kake ba.

 

Ranar data titsiye shi da wad’annan maganganun sosae jikin shi kuma yayi sanyi, shi bae san yadda zaiyi da rayuwar shi ba, ya samu kanshi cikin jarrabawar rayuwa mae tsanani a cikin y’an kwanakin nan.

 

“kiyi hak’uri ummie insha Allah zan kiyaye”.

 

Abinda ya iya ce mata kenan, sai kuma itama ta sauko daga d’an hawa fushin data soma, har ya nufi hanyar d’akin shi sae tace, “bazaka ci abincin bane yau?”.

 

Sai data fad’i haka kuma sae ya tuna ashe ma baici abinci ba, gashi yana jin yunwar a cikin shi sosae, dawowa yayi ya shiga kitchen d’in yana tambayar ta inda ta ajiye mishi abincin.

 

Koda ya d’auko abincin ma sai yayi zaman shi akan dakalin kitchen d’in ya soma cin abincin, ba kowa tsakar gidan nasu sae ummie kad’ae da khadija da yake tsammanin bacci ma take, su Zahra kuwa suna ciki saboda wutar lantarki da aka kawo suna kallo.

 

Hira suke yi shida ummie jefi jefi, rabin hirar ma duk akan shirye shiryen bikin Ahmad abokin sune da xa’ayi cikin satin.

 

Ummie ce take cewa, “aikuwa yaron yayi k’ok’ari akwati biyar fa har da kid, ai abunda sukayi sam ba dattako a ciki, yaro yayi iya k’ok’arin shi amma ace basu gani ba”.

 

 

Farouk ne ya karb’i zancen nata da fad’in,

“gaskiya ahmad yayi k’ok’ari sosae kam ummie, amma basu yaba ba, wae daga k’arshe ma mahaifin yarinyar cewa yayi suzo su d’auki kayansu koshi zai had’a mata wanda sukafi wad’annan, mtsss! Wasu Masu kud’in ae akwae izgilanci kamar su sukayi ma kansu arzik’in”.

Farouk ya k’arasa fad’a cike da jin takaicin abun a ranshi.

 

Ummie kam cewa tayi, “Allah ya kyauta, ae matsalar auren y’ay’an masu kud’i kenan, su raina ka su raina iyayen ka, su kuma raena arzik’inka, farouk ni dae nafi son ka nemo y’ar talaka dae dae kae, wadda ta samu Kyakykyawar tarbiyyah, tasan yau da gobe iyayen ta duk abinda mukayi bazasu raina ba, muma baza mu raena nasu ba muyi abin mu tuwo na maena”.

 

 

Murmushi kawae yayi yace, “to ae ummie ita yarinyar tana son shi sosae, kuma ita bata da matsala dashi kwata kwata, kawae familyn tane kuma su d’in ma yana auranta zance ya k’are, to ya zasuyi da ita tun data dawo k’ark’ashin shi”.

 

Allah ya kyauta kawae tace, shima daga nan ya mik’e tare da ajiye kwanon abincin daya gama ci a cikin kitchen d’in, ya wanke hannun shi yace, “ummie sae da safe”.

 

“Toh Allah ya tashe mu lafiya Farouk, Neema zuwa zanyi na fatattaki masu kallon can naje na kwanta”.

Ta k’arasa fad’a tana mik’ewa tsaye tare da nad’e tabarmar da take zaune tana kiran sunan khadija da baccin ta yayi nisa tuni.

 

Har ya shiga d’akin shi ya kwanta sai kuma ya tuna da kifin daya siyowa khadija tun da rana.

 

Zahra ya kwalawa kira, ta amsa tare da zuwa da hanzarin ta ta durk’usa bisa gwiwowinta tace, “gani yaya”.

 

Ledar ya mik’a mata yace,

“ki ba khadija ko ummie”.

 

Karb’a tayi tareda yi mishi godiya ta fuce daga d’akin.

 

Shima komawa yayi ya kwanta ya d’ora da tunanin shi na k’a’ida, ya kasa mantawa da wannan yarinyar, ga uban tulin kud’in ta da yake matashi dasu suma sun dame shi, kullum dasu yake futa ko Allah zaisa yayi katarin had’uwa da ita, har bi yake ta hanyar da abin nan ya faru wancan ranar ko Allah zai had’a su ya dank’asu gare ta.

 

Abubuwa sun dame shi da yawa sai dae kawae Allah yayi mishi maganin su.

 

Ga yawan fad’uwar gaba da take damun shi, sai ya dinga jin kamar zaiyi loosing something very closed & important to him a lokuta da dama.

 

“ya Allah ka tsare mu dani da y’an uwana da iyaye na daga dukkan sharri da kuma abin k’i”.

 

 

******* ******

 

 

Washe garin ranar ya tashi da ciwon ciki da zazzab’i mae zafi.

Hakan ya hana shi halartar sallar asuba, aikuwa baffan su yana dawowa daga masallaci yayo d’akin shi Don yayi mamaki yau da bai ganshi masjid ba, a kwance ya same shi cikin bargo sae murk’ususu yake.

 

Ganin hakan yasa ya isa da hanzarin shi yana tambayar shi, “Farouk me yake damun ka?”.

Cikin rawar murya yake fad’in, “wayyo baffah, kaina, cikina mutuwa zanyi……..”.

 

Shhhhhh! “karka sake kirawa kanka wayyo Farouk, cuta ae ba mutuwa ba, ina mukullin mashin d’in ka yake?”.

 

Da kyar ya iya nuna mishi saman drower, aikuwa ya d’auko da sauri ya fuce daga d’akin, yana futowa sukayi kacib’us da ummie, sai ta tsaya tana fad’in, “ni fa ince daman naji kamar shigowar mutum kuma na futo banga kowa ba, sai kuma naga takalmin ka a k’ofar d’akin Farouk ina phatan dae komae lafiya”.

 

Huce ta yayi yana bata amsar, “Farouk ne bashi da lafiya……..”.

 

Ai kafun yakae k’arshen zancen tuni har ta shige cikin d’akin Farouk d’in, shi kuma wayar shi ya d’auko ya kira makwafcin sa mallam dauda, da yake d’an shi shima napep d’in yake ja kamar Farouk.

 

 

Aikuwa ba b’ata lokaci ya turo musu mukhtar d’an nashi, daman rabuwarsu kenan a masallaci.

 

Da mashin d’in Farouk sukayi amfani yaron ya tafi kaesu asibitin, tunda shi farouk anan anguwar yake ajiye napep d’in shi sab’anin d’an makwafcin nasu da yake baro nashi a can gurin gadi.

 

Su biyu suka tafi sae farouk d’in daya kasa zama ko a cikin napep d’in, sai murk’ususu yake yana faman ambaton sunan Allah, banda sannu ba abinda suke iya ce mishi don sun tsorata da yanayin jikin nashi duk jikinsu yayi Sanyi,

 

 

Wani private hospital mafi kusa suka kaishi, aikuwa suna zuwa aka karb’e su aka soma bashi taemakon gaggawa.

 

Gaba d’aya daga ummie har baffan sun kasa zama guri d’aya, sai safa da marwa suke a tsakanin d’akin da aka kwantar dashi.

 

Sai da akayi mishi test sannan aka soma yi mishi duk abinda suka ga ya dace da ciwon nashi.

 

Bayan d’an wani lokaci, baffah ne zaune a gaban likita yana yi mishi k’arin haske dangane da ciwon farouk d’in.

 

“wato baba yaronka yana da typhoid ne kun sani?”

 

“eh mun sani tunda yana motsa mishi lokaci zuwa lokaci”.

 

Likitan yace, “good to aikuwa baba typhoid yayi ma yaron ka kamu na hak’ik’a, shine ya haddasa mishi ciwon cikin nan da kuma wannan zazzab’in mae zafi, amma insha Allah mun shawo kan ciwon kuma indae zaibi sharud’d’an da zamu gindaya mishi zai zauna lafiya da jikin shi”.

 

“me zai hana likita, ai bin doka ma ya zame mishi dole, mu da muke da k’aramun k’arfi idan abun yayi gaba da haka ai sae dae muce lahaula wala k’uwwata illah billah kawae”.

 

D’an murmushi likitan yayi kawae, yayi musu y’an rubuce rubuce a takarda ya bashi.

 

Babu kud’i a jikin shi don haka da suka rabu da likitan sai kuma ya soma tunanin yadda zai samu kud’in da zasu sallami asibiti, ga dae resit nan a hannun shi na ubannin kud’i, to ubannin kud’i mana mutumin da yake ta abinda zaici.

 

D’akin da farouk d’in yake kwance ya dawo, ciwon ya lafa ba kamar d’azu da suka zo ba, ummie tana zaune a gefan shi tana tofa mishi addu’oi.

 

“Sannu farouk”, baffa ya fad’a lokacin da yake zama a gefan gadon.

 

Bae iya amsawa ba sai kallon baffan kawae da yayi.

Sun d’an zauna jigum tsakanin shida ummie kowa da tunanin da yake a cikin ranshi. Shi kuma farouk yana ci gaba da d’an murk’ususun ciwon kad’an kad’an.

 

 

Banda jera mishi sannu ba abinda sukeyi.

 

Inda Allah ya taemake shi Bayan wasu mintina ciwon ya lafa mishi gaba d’aya.

 

Sai lokacin hankalin su ya kwanta har ummie take tambayar baffah, “ko ya kukayi da likita?”.

 

Resit kawai ya mik’a mata, ta Karb’a tana karantawa, zaro ido tayi lokacin data ga yawan kud’ad’en da suka buk’ata, ko da yake tasan za’a rina tunda suka zo private hospital irin wannan.

Ajiye takardar tayi tana tambayar baffan, “ko a ina yanzu zamu samu kud’ad’en nan?”

 

Shiru duk sukayi suna tunanin mafuta.

Farouk da har bacci ya soma d’aukar shi sama sama yaji maganganun nasu, sai ya ruk’o hannun ummie kafun da kyar ya iya bud’e bakin shi yace, “ummie akwae kud’i a d’aki na a cikin wanda nake saving a banki ku d’auko ku had’a dashi sae ku biya kud’in asibitin”.

 

 

Shiru ummie tayi tana kallon shi cike da tausayi, hak’ik’a farouk ya zame musu komae cin su, shan su, rashin lafiyar su harma da nashi rashin lafiyar duk shine.

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’uun kawai take maimaitawa a cikin ranta, sam bata so da za’a tab’a wani abu a kud’ad’en nan ba, ko don shima ya tsira da abinda kowa yake tsira dashi wato muhalli.

A hankali tasa hannu tana share hawayen da suka cika idanun ta, sai ta mik’e kawae ta fuce gudun kada ta karyar musu da zuciya.

 

Ko a napep d’in ma banda kuka babu abinda takeyi har ta k’arasa gida.

 

 

Duk suna zaune a tsakar gidan jingum jingum babu wanda yaje makaranta a cikin su.

 

Aikuwa suna ganin ta suka kewayeta da tambayar ya jikin yaa fahad d’in?

 

“da sauk’i” ta basu amsa da kyar tana tambayar abinda ya hanasu zuwa makaranta gashi har lokaci ma ya k’ure.

 

Babu wanda ya amsa ta a cikin su, tasan kuma dalilin daya hana su zuwa makarantar, don haka sai ta huce su kawae ta shige d’akin farouk d’in.

 

A hankali take duba cikin kayan shi daki daki, sai dae ita bata ga kud’i ko naira biyar ba, sai ta ja ta tsaya kawae tana dad’a k’arewa d’akin kallo, tasan ma’ajiyar kud’in shi bata huce cikin drower da samanta ba, amma sae gashi abun mamaki ta duba har cikin jakun kunan shi babu kud’in.

 

Sae kawae ta yanke shawarar bari ta koma asibitin in yaso idan ya d’an ji sauk’i yadda zai iya magana sosae sai ya bata bayanin inda ya ajiye kud’in Kae tsaye.

 

 

Take tayi na’am da wannan shawarar, sae dae har ta futa sai kuma ta tuna da lallae suna buk’atar kud’in nan ko don abinda za’a patient zai buk’ata a asibiti.

 

Dawo wa tayi taci gaba da bincike d’akin mataki mataki har tazo inda katifar shi take, pillown daya tada kae ta d’aga, sai ga lodin kud’i sun bayyana cikin yeluwar leda.

 

 

 

 

Komawa tayi da baya tamkar wadda aka jonawa electric shock tana bin tulin kud’in da kallo, jikinta har rawa yake.

 

 

 

 

 

 

 

_comment_✍️

8/13/22, 8:47 AM – Merhreeyeart❤️: 🏡 *AHALI D’AYA*

*_{auran bazata mafi k’ask’anci da wata irin rikitacciyar rayuwa mai d’auke da zallar k’iyayyah}_*

 

 

 

 

_Written by_

*Mareeyeart lawal*💞

 

 

 

_In dedication to my lovely ones_🥰

 

 

 

 

Page 9 _(nine)_

 

 

 

Meya had’a farouk da irin wannan uban kud’in, shin a ina ma ya samo su?

Ita dae tasan farouk baya sata kuma baya caca, balle tace na wasu ne ya d’auko ko kuma a gurin caca ya ciyo.

 

“Ohhh! Allah kada kasa yaron nan ya bijiro mana da abinda baza mu iya ba, Allah ka gani mu talakawa ne da muke neman cin yau da gobe duk a gurin ka Allah, Allah kada kasa zafin talauci ko wahalar rayuwa yasa yaron nan bama shi kadae ba har y’an uwan shi, su kauce hanya daga bigiren tarbiyyar da muka d’ora su akae na tsoron ka Allah”.

 

D’akin ta ta koma ta zauna bayan ta mayar mishi da kud’in yadda ta gansu, kuma Allah da ikon shi sae ga wanda tazo neman ma ta ganshi a inda batayi tsammani ba, daman rabon taga wad’an can d’in ne yasa da farko ma bata ga kud’in ba duk da gasu a fili.

 

Zama tayi shiru a gefan gadon ta ta lula tunani mae zurfi, tun daga yadda d’abi’un farouk suka sauya har zuwa yadda yake iya kae wani dogon zango a waje, a wasu lokutan ma gashi a zaune amma zatayi ta magana hankalin shi na wani guri.

 

Ganin wannan tunanin babu inda zae kaeta sai kawae ta mik’e ta soma shirin komawa asibitin.

 

A tsakar gida su safiyyah ta tarar kowa ya kama aikin shi, khadija kuma ta d’ora ruwan shayi a kurfoti.

 

A y’ar k’aramar kujerar dake tsakar gidan ta zauna tana tambayar dalilin daya hana ayi komae a gidan kamar yadda aka saba.

 

Duk hak’uri suka bata, sai kawae ta mik’e ta soma shirin komawa asibitin bayan ta had’a duk abubuwan amfanin da take ganin za’a buk’ata.

 

Ita da safiyyah (y’ar k’aramar k’anwar su farouk d’in) suka tafi saboda kayan da ta d’aukar mata.

 

Sun isa asibitin akan kari, amma sae data tsaya ta biya su kud’in su, sannan ta k’arasa d’akin da aka kwantar da farouk d’in.

 

Ta tarar su khaleed abokan shi duk sunzo duba shi da kuma sauran mutanen anguwa da ake zaune lafiya.

 

A gefan gadon ta zauna tana gaesawa da y’an dubiyan, inda suke dad’a yi mata ya mae jiki.

 

Har yanzu bacci yakeyi amma fuskar shi a yamutse kamar wanda yaci mad’aci.

 

Ta d’an dad’e a zaune kafun suyi musu sallama su tafi bayan sun harhad’a kud’i a tsakanin su suka dank’awa ummien.

 

Sosae tayi ta jera musu godiya da addu’a kala kala.

 

Bayan futar su da kad’an baffa shima ya tafi bayan ta bashi tabbacin ta biya kud’in asibitin duka da kud’in data samu a d’akin farouk d’in.

 

Sosae yaji dad’i kuma hankalin shi ya kwanta, don da duk a takure yake da tunanin inda kud’in nan zasu futo.

 

Toh farouk kuwa kusan kwanan shi 3 kenan a asibitin.

 

Alhamdulillah za’a ce don ya warware sosae a cikin y’an kwanakin, harma ya soma takura likita akan ya sallame shi haka.

 

A duk lokacin da yayi ma likitan wannan maganar yakan ce, “ka warke ne shiyasa har kake neman sallama, amma ranar da aka kawo ka banda mutuwa babu abinda kake kira”

 

Murmushi kawae farouk d’in yake yi idan likitan ya bashi wannan amsar.

 

Su sulaeman alk’awari ne kullum sai sunzo sunga jikin shi kafun su futa kasuwa.

 

Khaleed kam so biyu a rana haka yake zuwa baya ko gajiya, kuma duk lokacin dazae zo sae ya taho musu da kayan fruits, haka ma daga gidan su kannen shi sau uku a rana sae sun kawo musu abincin nan ko gajiya basayi, ummie ta hana su amma kullum ba fashi.

 

Su Zahra ma kusan zuwan su 2 asibitin, khadija ce tun data zo sau d’aya tayi ta shek’a amae saboda warin asibitin, ummie tace kar ta sake zuwa tunda ba dole bane.

 

Duk wannan abin da yake faruwa ummie hankalinta yana kan wad’an can kud’ad’en data gani ranar.

 

A wasu lokutan tana yawon yink’urin yi mishi maganar amma data tuna da a gadon asibiti suke saita danne ranta ta kyale har zuwa lokacin da zaiji sauk’i su koma gida.

 

Ranar daya kwana hud’u kuwa a asibitin, tun da yayi sallar asubah ya d’anyi bitar karatun shi na hadda kamar kullum, bai kuma komawa bacci ba ya hau harhad’a kayan su, ummie data kwana tare dashi tana kallon shi batace mishi kanzil ba, kafun lokacin da gari zaiyi haske sosae tuni kayan su sun dad’e a ready.

 

k’arfe 9 da y’an mintina fauziyyah ta kawo musu abin kari.

Kunun tsamiya ne su Zahra sukayi da jalouf d’in taliya data ji alayyafu.

 

Kunun tsamiyar kawae ya iya sha a ciki don daman shi tuntuni yasha ragowar tea d’in jiya dayayi saura.

 

Yana jin ummie tana yima safiyyah fad’a bai san dae ko akan meye ba kuma bai saka musu baki ba, tunda shi dama asalin shi ba mutum bane mae shiga abinda bae shafe Shiba, balle yanzu kuma ya lura y’an kwanakin nan ummien sae wani d’ad’d’aure mishi take, bai sani ba ko wani abun wani yayi mata, ko kuma bata jin dad’i ne kawae.

 

Yana gama shan Kunun sae ga khaleed ya shigo da sallama.

 

Farouk ya amsa mishi sallamar cikin sakin fuska sosae, sun gaisa da ummie inda yake dad’a tambayar ta jikin Farouk d’in.

 

“me jiki ae ya warke khaleed, yasu maman ku sukaje gida jiya, don Allah kayi musu ban gajiya in ka koma, ngd sosae”.

D’an russunawa ya sake yi yace, “ba komae ummie zasuji insha Allah”.

 

Safiyyah ma da take zaune gefan ummie ta gaishe shi, ya amsa ta yana ajiye food flask d’in daya ke hannun shi tare da zama kusa da Farouk d’in.

 

“yae! abokina naga ka samu fa kwana 2nan, ni sae naga ma har wani fresh kayi, ah lallae zaman asibiti ya karb’e ka”.

 

Hararar shi yayi tare da kai mishi duka ya kauce yana mishi dariya k’asa k’asa saboda wanzuwar ummie a gurin.

 

Sun dan tab’a hira sama sama, duk akan abinda ya shafe sune, kafun yayi musu sallama ya huce kasuwa, don daman bae wani sake ba.

 

Flask d’in ummie ta Bud’e, faten doya ne daya wadatu da busashshen kifi sai zabga k’amshi yake.

 

Tasan Farouk yauma baci zaiyi ba, don tunda ake kawowa ko d’and’anawa bai tab’a yiba.

 

Sae kawae taba safiyyah tace ta huce dashi gida k’arshen ta baza’a rasa me ciba.

 

Sunci gaba da zama jigum ko bayan futar safiyyan ma.

 

Gashi yau likitan bae zo da wuri ba sbd wani d’an uzuri daya tsayar dashi a government hospital, da yake yana aeky dasu a wasu lokutan.

 

 

Da wajen la’asar Farouk yana zaune saman sallayar daya idar da sallar, sae ga likitan ya shigo, yana ganin shima bae tambayi ba’asin komae ba ya rubuta musu sallama, sae dae ya kafawa Farouk tsauraran dokokin kula da kae.

 

Daga k’arshe a motar shi ya d’auko su ya Kae su har k’ofar gidan su.

Kuma ya karbi no Farouk acewar shi don su dinga sada zumunci lokaci bayan lokaci.

 

*********

 

Kwanaki suna ta shud’ewa.

Farouk dae tun washe garin ranar da aka sallamo shi daga asibiti ma ya futa aeky, don acewar shi baiga amfanin zaman da zaiyi ba.

 

Kusan har yanzu ummie taki sakar mishi, baisan dalili ba kuma koda wasa bai kawo a ranshi ko kud’in nan daya b’oye ta gani har ta sauya mishi haka ba, bai kuma tambaye ta dalilin sauyin daya gani a tattare da ita d’in ba, saboda shi mutum ne mae yawan yima mutane uzuri a rayuwar shi.

 

Yauma data kasance asabar tun da wuri ya fuce aikin shi, bai kuma tsaya karya kumallo ba har sae wajen k’arfe 1:30 daya tsaya yayi sallar azahar a masallacin anguwarsu.

 

Da sallama yauma ya shiga cikin gidan nasu, duk su zahra basu dawo daga makaranta ba, shiyasa gidan tsit daga ummie sae khadija da haseena da take zana jarrabawar su ta ssce, ita ma yau bataje ba saboda basu da paper.

 

Kusan atare suka amsa mishi sallamar.

 

Zama yayi a kan dakalin k’ofar d’akin shi yana yima ummie barka da gida.

Ciki ciki ta amsa shiyasa ma sam baiji abinda tace d’in ba.

 

Haseena da take zaune tana tsifa ya kalla yace, “akwae sauran abinci a gidan kuwa?”.

“eh Yaya ae har da tea ma na safe da baka shaba an ajiye maka a cikin flask”.

 

Sai ya gyara zama, “owk to kawo mun tea d’in na soma sha in yaso sae naci abincin daga baya”.

Rufe kanta tayi da d’an kwali, don tasan halin yayan nasu, yanzu in yaga k’wallin gashi ko guda d’aya ne sae yayi ta maseefa, kitchen d’in ta shiga bayan wasu y’an mintina sae gata ta sake dawowa da shayi a cup sae alala a flate.

 

“ngd haseena” ya fad’a lokacin da yayi arba da masoyin abincin nashi daya dad’e bae ciba.

 

Kusan shiru ne ya wanzu a gurin har zuwa lokacin da su Zahra suka dawo daga makaranta.

 

Aikuwa nan hira ta b’arke tsakanin su, don ma ganin shi a gurin yasa sun d’an nutsu da hayaniyar tasu.

 

Abun daya fi bashi mamaki shine yadda ummie ta d’auke wuta kamar bata gurin, bayan kuma yasan da ba haka take yi ba a duk lokacin data kasance a tsakanin su.

Daga k’arshe sae kawae yayi komawar shi aiki tun da yayi abinda ya dawo dashi d’in.

 

 

****** *******

 

 

Washe garin ranar suka tashi da d’aurin auren ahmad, wannan dalilin yasa tun da yayi sallar asuba bai samu zama ba suna ta hada hada shi dasu suleman da suka kasan ce manyan jiga jigan abokan ango.

 

Da misalin k’arfe 11:00 aka d’aura auren Ahmad da amaryar shi sadiya.

Can na hango tawagar su Farouk sunsha ankon shadda milk sae maik’o take yi.

Hotuna suke tayi inka hango Farouk yayi kyau sosae haka ma kamalar shi ta sake cika, yana tsaye daga d’an can nesa dasu rik’e da y’ar k’aramar wayar shi ko me yake dubawa?

 

Khaleed ne ya k’araso gurin shi yana fadin, “yae! Muzo mu tafi ko? Kasan anjima akwae reception pa”.

D’an yamutsa fuska yayi suka jera tare da Farouk d’in yana fad’in, “aeni ina jin dakyar ma in zan samu damar zuwan nan”.

 

Khaleed ne yace, “haba farouk ahmad ne fa, idan kayi mishi haka kuwa bazaeji dad’i ba, tunda Jiya ma kaga bakaje dinner ba”.

Mtss! “kaema kasan matsala ta d’aya ce khaleed”.

 

Khaleed ne cikin dad’a son nusarshe dashi yace, “Plzz Farouk muna bukatar mu mara mishi baya just once in your lyf kaje mishi reception d’in nan ko minti d’aya ma idan kayi faqat, amma ko ba komae zaiji dad’i”.

 

“Allah kana da matsala khalid, nifa nasan duk abinda kake yiwa da zuwa reception d’in nan, y’an mata ne fa ba wani abun ba, ni kuma bani da ra’ayin irin wannan rayuwar kaima ka sani, ni nasan yanzu b aure ne a gaba na ba shiyasa koda wasa ban tab’a kallon wata yarinya da fuskar soyayyah ba, hasalima ni ban taba jin wata a cikin raena……… “.

 

Sai kuma yayi shiru ya kasa k’arasa zancen tunowa da yarinyar nan da yayi.

Maganar shi kuwa sosae ta shigi khaleed, sae yayi shiru yana kallon farouk d’in da kuma tunanin abin daya katse shi daga k’arasa zancen daya d’auko d’in.

Sun isa inda khaleed ya ajiye mashin d’inshi, farouk ne yake tuk’a mashin d’in, shi kuma khaleed yana baya.

 

A gidan su farouk sukayi burki, sun tarar dasu hashim ma ashe tuni suma sun dawo sae kawae ya bud’e musu sittingroom suka shiga.

 

Aikuwa nan suka hargitse da hira kowa na fad’in abinda yake ranshi, farouk dae kamar yadda yake ba ma’abocin yawan hayaniya ba yana gefe.

 

Khaleed ma duk surutun shi yau kam shiru yayi,saboda shi a y’an kwanakin nan ma akwae abinda yake timing, kuma muddin yana so yayi nasara sae ya kama kanshi sosae a gurin farouk, shiyasa d’azu da sukayi wannan maganar jikin shi yayi sanyi matuk’a.

 

Yinin ranar tare sukayi shida farouk, ko gurin bikin ma basu koma ba, ragowar matasan duk sun tafi reception su kuma kowannen su yayi gida.

 

Kwance yake yanzun ma ya tsurawa ceiling ido, wannan sauyin da ummie tayi mishi ya dame shi matuk’a, yayi attempting zuwa ya sameta yafi sau hud’u, sae dae kamar Wanda ake dakatarwa daya mik’e ya futo sai kuma ya fasa.

 

Daga karshe sae kawae ya yanke shawarar ya zuba mata ido yaga iya inda abin zai tsaya, yasan indae wani laefin yayi ma ummie ta dad’e da yawa sati d’aya komae zata fad’a mishi laefin shi komae ya huce.
Littafan Hausa Guda 1000 Download
Itama a bangaren ta hakan ce ta kasance, ta kasa futowa ta tunkareshi da maganar kud’ad’en data gani tun wancan ranar, sae dae ta barshi a ranta cewa watak’ila tsoron jin amsar da zata biyo baya ne ya hanata.

 

Toh rayuwarsu taci gaba da tafiya cikin amincin ubangiji, kullum da safe farouk zai futa aikin shi bayan ya gama duk wasu abubuwa da yake yi a k’a’idarsu, idan ya d’anyi aiki duk inda aka ce 11 tayi to zae koma gida ne ya karya ya kuma d’an huta zuwa lokacin da zaeyi sallar azahar, sai yaci gaba kuma da aikin shi daga nan har isha.

Zuwa yanzu Tunanin fatima arfah ya zamto jini a jikin shi, kuma kullum yana tafe ne da saran zasu sake had’uwa ya dank’a mata sak’on kud’ad’en ta da kullum yake yawo dasu a cikin napep, yayinda suke ci gaba da rayuwa shida ummien shi Kae da k’afa.

 

Yau ma kamar kullum ya gama shirin futa aekin shi bayan yayi sallar zuhur, sanye yake da wani yadi riga da wando rigar iya gwiwar shi, duk da yadin mae sauk’in kud’i ne amma yasha wanki da guga, ya kwanta luf a jikin shi.

 

Gidan yayi tsit kamar ba kowa ma a ciki, k’ofar d’akin ummie yaje yana kiran sunanta, khadija ce da bacci ya soma d’auka ta jiyo maganar shi ta futo.

“ummie bata nan ne?”, ya tambaye ta.

“eh taje gidan aunty rufaeda, daga nan kuma zata biya gidan kawu mallam”.

 

Shiru ya d’anyi kafun ya nufi hanyar fucewa daga gidan.

 

Tafe yake yana addu’ar Allah yasa yayi gamon katar da yarinyar nan yau dae ya dank’a mata kud’in ta, koda yake dama ya dad’e yana wannan addu’ar a cikin ranshi.

 

 

*************

 

 

Kunsan ance waiwaye……..

Toh bangaren arfah kam tsiran kwana 2 da sukayi maganar nan ita da abie yayi tafiya k’asar Spain, sae dae tafiyar dukanta ta kwana 3 ce, shirye shiryen biki suke sosae a cikin gidan ba kama kafar yaro, kuma Gyaran jiki na gaske ammie tasa akeyi mata, in & out.

Abinka da y’an boko kuma surukan zamani, mama mahaifiyar muhsin d’in ce ma tayi musu hanyar mae Gyaran jikin, ta kuma jaddada mata tayi mata da kyau. Ita duk a ranta tayi amanna da cewar sofiyyah ta fita ma son taga anyi auren yaran.

Arfah Jiki yaji gyara kam, hakan ya sake futo da d’an asalin kyaun ta, sae dae zuciyar ta a cunkushe take hakan yasa saman fuskar ta sam ba walwala.

 

Fareeda hankalin ta har yanzu bae gama kwanciya ba musamman idan taga fahad da arfah Sun keb’e bata san me suke tattaunawa ba, hankalin ta yakan tashi.

 

Gashi a zahiri kamar babu komae a saman fuskar su, amma kuma tana jin tsoron yanayin kusancin su, tana jin tsoro kaddae arfah shigo shigo ba zurfi tayima su ammie sae biki ya kusa tabi fahad su gudu.

A kwance take amma lokacin da wannan tunanin yazo mata sai tayi zunbur ta mike zaune kamar mara gaskiya ta zubawa arfahn da take zaune kusa da ita tana operating system ido.

Jin kamar ana kallonta da tayi sae ta juyo da duban ta zuwa ga Fareedan, sae dae kamar ma ta tafi tunanin wani abun ne.

Sae ta kad’a hannun ta ya bada sauti a saman fuskar ta. Take kuwa tayi firgigit ta dawo hayyacinta, ta zubawa arfan idanu still tana kallonta.

“wannan kallon fa? Ko na sauya miki ne?”.

Sae ta sauke b’oyayyar ajiyar zuciya, “ko d’aya k’awata kawae ina tunanin ki ne a cikin zuciyata, kuma harga Allah ina tausaya miki ne, sae ta sake matsowa kusa da ita ta dafa kafad’arta , “nasan yadda zafin k’iyayyah yake, sannan nasan irin zafin da kike ji na auren ki da yayana tunda har yanzu bakya son shi, koda ace babu yaa fahad ma a cikin zuciyarki, balle k’iyayyar wanda yake cikin soyyayyar wani ba abu bace mae sauk’i, kuma bata tab’a gushewa”.

“Da ace yaa muhsin zai saurare ni arfah, da an soke auran ki dashi kin auri fahad tunda shine kike so, kuma kika fi dacewa dashi”.

Murmushi arfah tayi mae ban mamaki, tunda Fareeda ta soma maganar nan take sauraron ta kuma tana nazarinta, ta yadda da duk maganar da tayi mata saboda tasan ita d’in mae k’aunar tace, kuma tana jin takaicin abin itama a cikin ranta, to amma fa duk da haka bazata iya futowa ta fad’a mata gaskiyar abin da yake cikin ran ta ba, _and she will also lyk to surprise her_ don haka sae tace, “ki saki ranki Fareeda kamar yadda Neema nayi, domin kuwa har yanzu ban amince da auren yaa muhsin kamar yadda duk kuka d’auka ba, sai dae abinda nake shiryawa ko zae biyo bayan shirun nan nawa, sirrin mune nida yayana, mae k’auna ta kuma abin alfahari na”.

Ta karashe fad’a tana mae haskaka fuskar ta da wani Sabon murmushin.

 

 

Tashin hankalin da Fareeda ta kuma shiga har yafi na farko, lallae ashe tunanin ta gaskiya ne, to aikuwa ya zamo mata dole ta samo mafutar da auren nan za’a matso dashi ayi shi cikin kwanaki k’alilan kafun su sami damar aiwatar da k’udirin su.

Firgigit ta sakeyi a karo na 2 saboda d’an jijjiga kafadar ta da arfahn tayi, “Wae Fareeda ko akwae wata matsalar ne?”.

 

Mik’ewa tayi tsaye tana lalubar d’ankwalinta tace, “babu komae dear tunawa nayi da aikin da ammie ta bani d’azu ashe banyi ba, sae tayi hanyar futa tana fad’in ina zuwa minti 5 ynz zan dawo”.

 

Kae tsaye part d’in ammie tayi don da zafi zafi ake dukan k’arfe, a cewarta, sae data tsaya ta kuma saesaeta yanayin ta da tunanin ta inda zata soma shiryo zancen, sannan ta k’arasa.

 

Da sallama ta shiga parlon ammien, bata parlon don haka saeta zauna a kan d’aya daga kujerun parlon tana k’are ma komae kallo daki daki.

Tana son ta sanar da ammie zuwanta amma ta manto wayar ta a part d’in Arfah.

Zama tayi shiru tana sake jinjina al’amarin a cikin zuciyar ta,”lallae Arfah bata da wayo, a tunanin ta zata ce bata san yayanta ne a gabanta kuma ta kyale ta, ai in tasan abinda takeyi bazata tab’a futowa har ta nuna mata wata alamar k’iyayyah wa yayanta ba, balle har akae ga ta furta mata da kanta.

“a’a fareeda dama kece kuma kika zauna anan, ae da kin shiga neema wani d’an aiki na shiga yi”.

 

Ta k’arasa fad’a tana zama saman kujerar.

Fareeda kam sunkuyar da kanta k’asa tayi tana wasa da fingers d’in ta.

“munyi magana dake, kuma sae naji ki shiru kwana 2 ina phatan dae komae lafiya”.

 

D’an sosa gefan fuskar ta tayi sannan ta soma magana, “kamar yadda nayi miki alk’awari cewa zan fad’a miki komae dana sani game da arfah, to nima ammie ina son kiyi mun alk’awarin cewar zaki iya rik’e abinda zan fad’a miki yanzu a iya cikin ranki kuma bazaki tsani arfah ko ki k’untata rayuwar taba”.

 

Shiru ammien tayi tana kallon fareedan yayinda ta zak’u da taji abinda fareedan take son fad’a.

Sae ta gyara zaman ta sosae tana dad’a bada hankalin ta d’ungurun gum zuwa ga fareedan, “insha Allah fareeda nayi miki wannan alk’awarin”.

 

D’an b’ata fuska tayi irin abinda zata fad’a d’in ya dame ta sosae, “wato ammie abinda naji daga bakin arfah ya matuk’ar bani mamaki kuma ya d’aure mun Kae, da nima har nayi tunanin na b’oye miki kamar yadda arfahn tayi sae dae a yadda kika d’auke ni bazan iya cin amanarki irin haka ba”, sae ta d’anyi jim cikin maraeraece fuska kafun taci gaba da fad’in, “ammie arfah fa tana da wani da yake cikin zuciyar ta bayan yaya fahad, kuma akwae kwakwkwarar alak’a a tsakanin su har tafi ma wadda take tsakanin ta da yaya fahad”.

Wani irin kallo da ammien ta wurga mata tashi d’aya sae daya tsorata, ta d’an ji wani d’ar a ranta lokaci guda.

 

 

 

 

 

_fans kuyi hak’uri da jina shiru ranar litinin wllh na shiga wani muhimmin uzuri ne, kuma wanda nayi typing a lokacin bae huce readmore 2 ba nikuma nafison naci gaba dayi muku yadda muka fara, fatan Allah yasa mu dace duniya da laheera_

 

_sae abu na 2 da yake sare mun gwiwa, a duk lokacin dana ajiye duk uzurina nayi muku typing kuka gani kuma bakuyi mun comment sae naji gaba d’aya kwarin gwiwata ya sare, sae na dinga tuhumar kaena da laefin maybe labarin ne baiyi muku ba taya zan tabbatar da cewar muna tafiya tare?_

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Name: [Ahali daya Complete Hausa Novel (www.mynovels.com.ng)]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022

 


Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na TelegramPowered by: www.mynovels.com.ng

 

Leave a Comment

error: Content is protected !!