A’indo Tantagariyar Yar Aiki

Bafulatana

A’indo Tantagariyar Yar Aiki

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tinkim wani kauye ne dake wajen jihar Zinder ,a kasar Niger, kauye ne wanda kusan zan iya cewa tsaka tsakiya yake tsakanin Nijeria da Niger.

 

 

Kauyen yanada kyau da dadin zama,mutanen garin akoy karamci da son bako,gidan Ado Mai saida kifi kowa yasan sa a kauyen, tunda ya taso yake sana’a saida kifi, har ya zama samari, ya hadu da kuluwa mai bakin masifa, kowa yasan kuluwa da masifar ta, hakan yasa duk wanda yake son ta da aure yanzu ne zakaji an zuge shi.ace Masa ai batada da’a bata san darajan yan Adam ba masifafa ce, sai kaji an fasa auren.

 

 

kauyen auren wuri ake ma yarinya daga kin kai shekaru sha uku sha hudu yanzu za’a aurar dake, yayyin da kuluwa saida takai shekaru goma sha takwas kafin Ado mai saida kifi ya gani yace yana so kuma yana iyawa Saida akasha duru kafin a bari ya aureta.

 

 

Bayan anyi Aure kuluwa tana masa ladabi da biyaya da duk wani abinda ya danganci sauke hakki ne na mijin ta saide fa ko kadan batada hakuri, idan ya mata abinda bashi ba,yanzu ne zata juye masa buhun bala’i.

 

 

 

A haka suke zaune,yau dadi gobe ba dadi,Ado yanada daidai abin rufin asirin sa domin dai abinci bai gagaresa ba, sanan sutura batafi k’arfin su ba, da sauran abinda ba’a rasa ba,saida sukayi shekara daya kafin Allah ya Albarkace su da samun yan tagwaye duka mata.

 

 

masu matukar kama da juna, kyawawa dasu bazaka taba gane su ba,ranar suna za’a sa musu sunan su na hassana da husseina anma Kuluwa ta zuba masifa dole fa sai ansa ma daya sunan mahaifiyar ta da ta rasu.

 

 

Allah ya jikan Mahaifiyar ta itama masifafa ce ta bugawa a jarida, dan kuluwa dai gado tayi.

ba yanda Ado ya iya yace”tayi hakuri asa musu hassana da husseina sai a dinga Kiran Hassanar da sunan A’indo anan kawai ta yarda, aiko akasa ma hassana sunan A’indo.

Tunda suka taso halinsu yadan banbanta, a halayen su kadai zaka iya banbanta su, dan ko mahaifin su saide ya Kira da sunan su tukon yake ganewa, mahaifiyar su kadai take ganesu,watarana anma ranar da suke jin iskancin sai suyi kicin kicin ko kai waye bazaka ganesu ba.

 

Karanta Yar Aiki Return

Husseina mafadaciya ce ta gidan gaske, yanzu ne ta zage ku danbata da ita bata wargi kai ko fada taga anayi idan taga ba’a danbata ba yanzu zata saye fadan ayi da ita, gata tantiriya.

‚Äč

 

 

Name: [ A’INDO TANTAGARIYAR YAR AIKI ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: November, 2021

 


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.