Hausa Novels

Aisha Indo Hausa Novel Complete

Aisha Indo Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Aisha Indo Hausa Novel Complete

Page 1*

*__________* Tinkim wani kauye ne dake wajen jihar Zinder ,a kasar Niger ,kauye ne wanda kusan zan iya cewa tsaka tsakiya yake tsakanin Nijeria da Niger.
Kauyen yanada kyau da dadin zama,mutanen garin akoy karamci da son bako,gidan Ado Mai saida kifi kowa yasan sa a kauyen,tunda ya taso yake sana’a saida kifi,har ya zama samari ,ya hadu da kuluwa mai bakin masifa,kowa yasan kuluwa da masifar ta,hakan yasa duk wanda yake son ta da aure yanzu ne zakaji an zuge shi.ace Masa ai batada da’a bata san darajan yan Adam ba,masifafa ce,sai kaji an fasa auren. kauyen auren wuri ake ma yarinya daga kin kai shekaru sha uku sha hudu yanzu za’a aurar dake,yayyin da kuluwa saida takai shekaru goma sha takwas kafin Ado mai saida kifi ya gani yace yana so kuma yana iyawa Saida akasha duru kafin a bari ya aureta.

 

Littafan Hausa Novels Guda 1000 masu dadi

Matar Makaho Complete Hausa Novel

Hotunan Lalle Masu Kyau Kunshin Gam

Matar Yaro Hausa Novel

Hajiya Gwale Hausa Novel Complete

Gyaran Nono a sari data

Tsofaffafin Hausa Novels Watpadd

 


Bayan anyi Aure kuluwa tana masa ladabi da biyaya da duk wani abinda ya danganci sauke hakki ne na mijin ta ,saide fa ko kadan batada hakuri ,idan ya mata abinda bashi ba,yanzu ne zata juye masa buhun bala’i…..
A haka suke zaune,yau dadi gobe ba dadi,Ado yanada daidai abin rufin asirin sa,domin dai abinci bai gagaresa ba,sanan sutura batafi k’arfin su ba,da sauran abinda ba’a rasa ba,saida sukayi shekara daya kafin Allah ya Albarkace su da samun yan tagwaye duka mata,masu matukar kama da juna,kyawawa dasu bazaka taba gane su ba,ranar suna za’a sa musu sunan su na hassana da husseina anma Kuluwa ta zuba masifa dole fa sai ansa ma daya sunan mahaifiyar ta da ta rasu,Allah ya jikan Mahaifiyar ta itama masifafa ce ta bugawa a jarida,dan kuluwa dai gado tayi……
ba yanda Ado ya iya yace”tayi hakuri asa musu hassana da husseina sai a dinga Kiran Hassanar da sunan A’indo ,anan kawai ta yarda,aiko akasa ma hassana sunan A’indo.
Tunda suka taso halinsu yadan banbanta,a halayen su kadai zaka iya banbanta su,dan ko mahaifin su saide ya Kira da sunan su tukon yake ganewa, mahaifiyar su kadai take ganesu,watarana, anma ranar da suke jin iskancin sai suyi kicin kicin ko kai waye bazaka ganesu ba.
,,,,,,,,,, Husseina mafadaciya ce ta gidan gaske,yanzu ne ta zage ku danbata da ita,bata wargi kai ko fada taga anayi idan taga ba’a danbata ba yanzu zata saye fadan ayi da ita,gata tantiriya .yayyin da Hassana A’indo ta hada kusan duka A’indo dai itama tana masifar ,saide akway ta da wauwta irin ta yan fari,ga tsiwa,ga karambani,kome ita ta iya,ga karambani yi ba’a sa ta ba,ga keta,uwa uba kauyenci saide matsoraciya ce ta gidan gaba, tunda suka taso kowace da burin ta ,A’indo batada buri sai taje birni aikatau,ita duk yanda take ganin yan mata daidai ita na kauyen in sunje aikatau wasu har a wuleliyar mota ake kawo su,to sai ta d’auki wanan tasa a ranta cewar Yar aiki baban matsayi ne da ita ,wanda ko a birinin da wuya a samu mai matsayin Yar aiki.
Sun adabi mutanen gari,kowa fata yake suyi auren nesa,saboda duk kyansu ba Mai zuwa wurin su saboda masifa irin tasu da ta uwar su,a yanzu haka sunada kusan shekaru goma sha bakway anma ba mijin aure Mahaifin su har ya gaji ya zuba ma sarautar Allah ido,A’indo kuwa a kauye ba Wanda baisan sunan ta ba,da ta biyo guri kace sai kinyi A’indo sai tace Tantagariyar Yar Aiki ba.”
Ana cikin haka kanwar Mahaifin ta tazo daga birni wada take a birnin zinder tana zuwa ta samu yara ta d’auke su ta kaisu Aikatau a birini duk wata ana biyan iyayen su,itama tana samu.
A wani zuwa ne da tayi A’indo ta aza bala’i itama fa sai taje aikatau dinnan,ba yanda Mahaifin ta ya iya yace suje ,wata kila ta samu miji ita in ta fita daga kauyen tunda dai wanan kauyen ba Wanda ke son su da aure,suna kuka haka suka rabu ita da yar uwarta Husseina,tun daga lokacin da A’indo ta tafi husseina ta Kara zama masifafiya,ta adabi mutanen gari tace ai ta dalilin su yar uwarta ta tafi,saide fa tace itama dan lokaci take jira,anma in lokacin yayi duk inda yar uwarta ta tafi a birni itama sai ta bita.
Ranar da aka shigo birni da A’indo duk Wanda ke cik’in motar Saida ta cika cikin sa da dariya,ana tsakar tafiya ta fido kanta ta window mota tana ihu wai ga bishiyoyi can na gudu,akayita dariya.
kusan gidan biyar aka kaita aikatau anma duk inda taje sai tayi ta’asa,su korota.
A karo na shida ne aka kaita gidan wani dattijo Alhajin Sanmani Hamshak’kin Dan kasuwa ne Mai kudi,yayan sa biyar Mata biyu Maza uku.
Alhassan shine da na farko dan kimanin shekaru talatin da biyar a duniya (35years) Yan biyu ne yar uwar tagwaitakar sa bata zo da rai ba sai shi,a yanzu haka yana kasar waje aiki yake sodja ne baba na kasa da kasa Wanda duniya keji dashi kuma take takama dashi,saboda ilimin sa kwazo ,basirar sa,uwa uba yasan kan aikin sa .baya dariya ko kadan,babu Wanda zaice ya taba ganin dariyar sa,saide murmushi , murmushin ma iyakar sa lebo . Mai bi masa shine idrissa dan kimanin shekaru ashrin da biyar,sai khalipha dan kimanin shekaru ashrin da uku suna karatu,sai halissa Yar shekara ashrin da biyu tayi aure a Niamey shekara biyu da ta huce,sai auta khalissa, yar kimanin shekaru goma sha bakway su suna karatu ne.
Sai mahaifiyar su Hajiya saude datijuwa Yar kimanin shekaru arba’in da biyar.
Katon gida ne sosai tsarare ,Wanda aka kashe masa naira wajen tsara sa ,ginin ma ginin turai ne, yan aiki gidan kusan ma’aikata goma sha tara ne,kowace da ranar aikin ta, bayan masu gadin gidan da masu tsaron lfy masu gidan su ba’a sasu a lisafi ba,Hajiya saude duk masu gyaran falon da ake kawo mata Sam bata wani ganin kyan akin su ita tafi so in ta fito falo taga ko Ina kal kal yana walkiya,hakan yasa tasa a Nemo mata Yar aiki ta kauye a cewar ta su suka fi aiki domin basa Wasa da aiki suna sakin jikin su suyi aiki basa gajiya.
Hakance yasa Anty najin irin Yan aikin da Hajiya keso ta kawo A’INDO gidan yau ai tun a k’ofa ta tatare siket zata arta a guje Saida Antyn tata da ta gane nufin ta ta rike hanun ta kam,tayita lalaba ta sanan suka shigo..
*_________* “kefa kikace shi, gashi kuma na so miki na dubu hudu da dari biyar cassss.”
Cewar A’indo.
Hajiya tace uban waye yace miki kwali shine kati,Nima ai nice da shirme da na aike ki,kuma in banda hauka wa ya taba kiwo ki sayi wanan uban bubun igiyar wai Zaki fara dan tare ,dan tare saikace wata amarya,yanzu kin min asara mitssss,”dan Allah Hajiya gobe ma ki aike ni na samu canji na sayi dusa ko ta naira ashirin ce na fara dan tare,kafin nan da shekara in rago na yazo
Rabi’u daudu ne ya shigo falon domin shine kukun gidan,dan daudu ne in yana abu kai kace mace,yanda yake rangwada har yafi macen,lokacin da A’indo tazo baya gidan ya tafi hutu,ya iya abinci kwarare ne hakan yasa Hajiya ta kasa rabuwa dashi jiya dadare yazo ,yaji labarin A’indo kaf,ya kawo ma hajiya juis ya tarar da zancan da suke,kugu ya Kama da hanun sa daya,bayan ya aje ma Hajiya juis din,yana wani karairaya,yace”ahhh Allah daya gari banbam casss makuwa,aheee ya fada tare da tura duwawu baya,ya kada idanu tare dayin farin ya tafa hannu ya rike haba tare da cewa Hajiya me kala kala,keko hajiya me ya kaiki kwaso wanan yau Allah na tuba mutum gashinan kamar ka zuba a guje,anma kekam anyi asara ,kin bata mana sunan mata wly,kin bada mu mata,hahhh yau ni Hajiya me ya kaiki kwaso wanan jabu ki kawo mana gida,yanzu ke in banda lalaci a aike ki sanyan katin waya ki kwaso kwalin waya ki kawo,tab Hajiya sannu Ashe kina fama.”
Ya fada yana maganar mata tare da juya kugu,yayi fari sanan ya rike haba yana Kare ma A’indo kalo.”
galala A’indo tayi tana kalon sa ta Kama haba tace”tab ashe dai hajiya taron mahaukata Kika kawo a gidan nan,tab ashe ban gama kalo ba,yau Allah na tuba ya aka iya dani ma bare kuma ga wani.”
tace tare da juya kacokan hankalin ta ga Rabi’u daudu .
Yamutse fuka Rabi’u yayi,Alamun dai ransa ya bace,yace”ke bari gani na haka wly yanzu zan tube mu kwashi yan kalo ehhhe ni Zaki kira da mahaukaciya sanan ki kira ni da wani ba wata ba,yau Allah na tuba ai kece mahaukaciyar baba ma kuwa .”
“Kai ni karku cikani da surutun banza,ai dukan ku ragaitatu ne,ke kuma taraki nake ,Allah duk ranar da kika cikani sai kinbar gidan,haba yarinya gakinan shiriritata,ba kimtsi ,na fara yarda kinada tabin k’wak’walwa.”
“Hahhh wly Hajiya kin canka daidai ,marar hankali ce lamba daya ma kuwa,cewar A’indo tana washe baki .
Sakaka Rabi’u daudu yayi yana kalon A’indo yace”hahh wly Hajiya kina fama,wanan kam ta zare sai ankawo mai rukiya .”
Yana gama fadar haka ya kama hanya yayi tafiyar sa, yana tafiya irin ta mata yana kada kugu,baki a sake A’indo take kalon Rabi’u daudu har yabar harabar falon,ta tuntsure da dariya ,sanan ta kara gusowa wurin Hajiya tace”Hajiya wanan anma haka haka ne ko? dan wly naga Alamun shima sha tara ne,to in ba sha tara ba wane mutum ne duba fa hajiya A’indo tace tana koyon tafiyar Rabi’u daudu Hajiya tafiyar sa wane namiji zaiyi wanan tafiyar in ba haka haka ba ,to aradu Hajiya bani kadai ke bukatar magyarin mutum ba,wly wanan ma yana bukata.”
Kuma Hajiya dan Allah kice ma Alhajin gidan nan ya dinga tafiya a hankali,in ba haka ba yayi Bari dan naga cik’in sa ya kusa haihuwa,Kinga ranar ma ya Fado anma dai ya’yan basu mutum ba ko?
Da Allah Hajiya ki dinga cewa ya dinga tafiya a hankali,in zai fita gidan nan kiga Yana sauri,Kar yaje ya barar da Yan cikin,Kinga ku rasa yaran ku Dan Allah ki masa magana cewar A’indo domin itafa har ga Allah dagaske take ,dan ranar ma saida ta tambayi daya daga cik’in masu aiki cewar wai yaushe Alhaji zai haihu.
Saboda Alhaji yanada kyau saide katon ciki garesa,Wanda Yana tafiya cikin na rinjayar sa
Mugun kalo Hajiya ta jefeta dashi tace”wai A’indo yaushe zaki nutsu kiyi hankali, kuma mijin nawa kike ma haka wly ki kiyayeni zan saba miki.”
“Jiya ko shekaran jiya insha Allah,zanyi hankali hakiya.taba hajiya amsa tare da kamewa tsam.”
Kada kai Hajiya tayi ta tashi tabar mata wurin.
Ko akanta A’indo zama ma tayi a falon ta fara kalon wani American film da akasa, waro idanu tayi ganin wasu maza biyu suna fada a tv dayab ya zaune dayan yanata dukan sa,aiko me A’indo zatayi bayan aza hannu bisa kai ta kwala wata Kara da duk wani na cik’in gidan yaji,tace”Wayyo Allah dan Allah kuzo Kar ayi kisan Kai,Hajiya kuzo ku raba wly zai kashe shi,Hajiya Jin wanan ihun ta aza wasu ke fada da gudu gudu ta fito a firgice,Suma sauran jama’a gidan hakan suka garzayo a guje suna isowa falo suka iske A’indo ta aza hannu bisa kai tana sheka kuka,ganin an kashe wancan mutumin na Tv ,aiko kowa yayi cirko cirko da idanu aka zuba ma A’indo idanu cik’e da takaici,Dan sun lura da Tv ne take ,Hajiya da karasowar ta kenan tace “su waye ke fada kuma,A’indo fuska shabe shabe da hawaye,tace sai yanzu zakuzo bayan an gama yin kissa,ku yanzu gidan nan sai a kashe mutum bakuzo kun cece shi ba,ai gashinan sai kuje ku d’auki gawar kuyi mata jana’isar.”
Ni bara naje nayi Alwalla muzo muyi zaman makoki,nasan yanzu mutane zasu fara taruwa,ta fada tare da share hawayen ta tayi gaba tana cewa “Allah jikanka Hanmma.
Ahhhhh yau ni naga kala kala ni Rabi’a kekam Allah shi kwashe maki Albarka yanzu saboda Allah a TV ne ake wanan abu kika cika mana gida da kuwa,kekam anyi asara cewar Rabi’u daudu.”
ya fada tare da wani botsarewa ya turo kirji.
Cik’e da takaici Hajiya tace”A’indo bazan iya dake ba ,wly,ki tatara ki koma inda kika fito tun kafin kisa min hawan jini,in ba iskanci irin naki ba abinda ke Tv zakizo ki hana mutane kwanciyar hankali,to ni bazan iya ba tunda bazaki ki natsu ba.”
waro idanu A’indo tayi tace “haba hajiyata,aradu nidake mutu ka raba,kuma ai nayi haka ne dan a taimaki rai tunda naga ana gida guda.”
Uban waye yace Miki da gaske ne,wanan Tv ne wanan film ne,abinda kike gani ba dagaske bane wasan kwaykwayo ne kuma ma mu ke ganin su su basa ganin mu.
” La Hajiya yi hakuri ban sani ba anma daga yau zanyi hankali,dan Allah kiyi hakuri ,wly wanan gidan yanda kika san kanin uwata bazan iya rabuwa dashi ba.”
tausayi taba hajiiya Hajiya tace “naji shikenan anma karki kara irin haka.”
Yauwa Hajiya ta wo ke wo ke,nidake mutu ka raba takalmin kaza,Yan bakin ciki saide a mutu ehehhh ”
Ta fada tare da kalon Rabi’u daudu.”
Ahheee riiiii kom,anyi a banza wai ance da makaho ga ido yace a’a wari suke,yau Allah na tuba mai jiya taci bare yau,akace in da ranka kasha kalo,shidai dan kauye a ko ina sai ya nuna halin sa,kedai kin baro mata,gaki mace har mace anma ba gyara sai sakarci,kai wly mu mata an cuce mu.”
” Garjeje sangameme lukucece,tukeke,mumukeke rusheshen kato dakai kana Kai kanka jinsin mata,tab anma kam Allah dai ya shirya cewar A’indo.”
“Ke ki kiyayeni ,wly sai na tube mu ba hanmata iska dan ba ta Ido ce dani ba wly”
“Kai bana son shanshanci kuje ku bani wuri bazan iyaba Hajiya tace tare da barin gurin .”
Rabi’u saida yayima A’indo kalon sama da kasa,ya wani tabe baki irin na mata ,ya rike jalabiyar sa da hannu daya ,ya rike kugu da hannu dayan ya juya yayi tafiyar sa yana kada kugu.”
A’indo ta kece da dariya ta fita tayi ficewarta.”
Bayan kwana biyu A’indo ce zaune sai durzar kuka take baji ba gani,bini bini ta rike ciki duk Wanda ya tambaye ta lfy bata ko kula sa,Saida aka fada ma Hajiya sanan tace a Kira ta taji abinda ya faru,tana zuwa wajen Hajiya ta tsaya sai zare zaren idanu take,kamar wada tayi karya Hajiya tace”A’indo me ke damun ki naji ance kinata kuka.”
Share hawaye A’indo tayi tace”yau Hajiya ba dole nayi kuka ba,ace kwana hudu mutum yana aje kahi a cik’in sa,tunda nazo banyi kahi ba,ace gaba-daya wanan katon hirgegen latsetsan gidan babu masai “A’indo ta fada tare da matse fuska .
“Ikon Allah to ke A’indo basu nuna Miki wajen kashin ba.”
Tab Allah ya tsari kakana habu anma wly ku yan binin nan akoi ku da Almabazaranci ,yau in banda waouwta irin taku wanan randar k’yakyawa ita za’ayi kahi wanan ai hede asha ruwa,jiya ma can ciki nasha ruwa na ,na kohi wly zar dadi ”
Innalillahi wa’ina illaihi Raju’un nikam Saude naga takaina A’indo a wanan farin abun Kika sha ruwa?
“Hahhh Hajiya yau ni ina ruwa na,tsab nasha kayana na kohi,yanzu dai hajiya ki taimaka min da inda zani nayi kahi dan wly tun jiya nake jin ana mun kidan danbagalaje aciki matse fuska tayi sai ji kake buuuutt ta buga tusa.
*__________* anma gaba-daya A’INDO a tsorace take,bata kara tsurewa ba saida suka shigo falo,dukawa tayi tace in ta taka fashewa zaiyi,sai kace gilass ,ba yanda Antyn ta batayi da ita ba akan ta tashi anma Ina,to tun anan Hajiya saude da duk a gaban Idanun ta abun ya faru ita da yaranta suka kece da dariya ,sukaji A’indo ta shiga ransu.
Bayan Hajiya ta musu tambayoyi tace Antyn ta tafi aba A’indo d’aki daya a cikin na masu aiki har ta kwana biyu sai ta fara aiki ta gani in ta iya ,sai ta dinga gyaran falo hadi da guga.
Bayan an Salami Anty ,A’indo tasa Hajiya saude tayi tagumi tana kalon ta,Saida Hajiya saude ta tambaye ta lfy ?
budar bakin A’indo sai cewa tayi kinyi kama da matan Aljanna,yau me zasuyi in ba dariya ba,Hajiya tace “akaita d’akin ta ta huta kwana biyu acan ma ta buga kauyanci.
Saida tayi kwana biyu ana nuna mata ayukan da zatayi.a ranar kwana ta uku ce Hajiya tace a kirawo ta,tana zuwa Hajiya tace “so nake yau ki gyara min falon Nan yayi haske sosai,har yayi walkiya, washe baki A’indo tayi tace”angama hajiya, dariya Hajiya tayi ta bar mata falon,itako taje ta debo ruwa da sabulun guga da abun guga. Ta zauna
*_________* zaune take tayi baje baje a tsakar falo,Sai gugar tiles take,bayan ta gama guga da ruwa da sabulu sai ta kuma d’auko Mai na gyada uban mai yauwa,sai ta zuba a hannuwan ta ta murza sai ta shafa a tiles din kai kace mutum take shafa ma,da taga kamar shafawa ,da hanunta hakan zai bata mata lokaci sai ta d’auki Mopper tana dangwalo man dashi tana gogawa a tiles din,anma a zaune take yi ,saide ta dinga jan jiki tana gugar ,”ai wly Hajiya yau sai ta bani k’yauta,dan tsab zan goge mata falon nan sai yayi kal kal yana walkiya,duba fa har kalon kaina nake a ciki tamkar madubi, ci gaba tayi can ta tsaya ta murguda baki,sanan ta tafa,tace “ayariye nanaye ayariye, ayariye nanaye ayariye,ga saurayi na samu ayariye,wakarta take tana tafawa tare da rike kugu,duk wanan abun a zaune take,domin tales din ko ba’a goge ba idan bakayi taka tsantsan ba yanzu ne zakasha kasa, to bare kuma ga aindo tana kara shafa masa mai ,falon duk yayyi walkiya,tsabar Man gyada da ta goge falon dashi,bayan ta gama taji cikin ta na kugi”hahhf wly dan Albarka yunwa yake ji tace tare da shafa cikin ta,yau dama cin kwai da biyar,da ledar biredi daya,da ferpesun yan ciki Wanda ma ko cika kwanon nawa baiyi ba,me zasu min,yau nida ko a gida malmala hudu nake cinyewa badan ta isheni ba,yau Allah na tuba wanan abincin na yan birni mai zaimin,ai wly bazai min komai ba,da rarafe ta rarafa tayi kitchen abinci ta loda tuli guda Wanda mutum biyar sai suci su koshi,anma ta tashi dashi idan ka ga cin da take ka dubi jikin ta kai kace wata katuwa zaka gani,anma kuma abun mamaki siririya ce,anma ba can ba,ita ba doguwa ba,ita ba gajera ba.
Ni kaina nayi mamakin ci irin nata,Hajiya ce ta fito ta sauko daga matatakala tana kwala Kiran Aindo ,anma sai me tana saukowa daga matatakala sai ji tayi kamar an d’auke ta an yado,wata kara ta saki wanda ya tada Hankalin Yan gidan suka fito gaba-daya ,anma duk Wanda ya shigo falon saide kaji suuuuuuu ya fadi,wasu kuma kamar an jefo su haka zakaji suna faduwa,harda yan aikin gidan,dukan su daga mai rike kugu sai me rike kafa,wasu kuma reran suke kwance,daya saman daya a hankali Aindo ta fito ,kamar yanda ta fita,wato da rarafe,har ta karaso falon ,ganin mutanen gidan duk zazaune wasu a k’wankwance ,wasu na hawaye ,sai zama itama tayi ta aza hannu bisa kai ta kece da kuka,”yiiiii yiiiiii,Allah jikan ka hanma Allah jikan ka hanma,Wayyo Allah bango ya fadi.
Gaba-daya sai suka tsaya suka zuba Mata,ido duk da sunajin radadin faduwa da sukayi, Hajiya ce tayi k’arfin halin cewa”ke wai lfy waye ya rasu mutane na cik’in wani hali kizo kina mana kukan mutuwa.”
tsayar da kulan Aindo tayi ta zuba ma Hajiya idanu,tace”to ba zaman makoki kuke ba,in ba hanma ya mutu ba ai bakunzo kuyi wanan zaman ba ,harda masu kuka,yiiiiii Allah ya jikan ka Hanma , Alhaji ne ya fito yana cewa wai lfy ko ” waro idanu hajiya tayi tana cewa Alhaji karka karaso Kar ka karaso akoi matsala a kasa.”
“Nikam Hajiya kinada shirme watarana kema me kuke yiiii ai bai gama fadar abinda yake shirin fada ba sai ji kake suuuuu ya jibgo kasa sai saman Hajiya,wata Kara sukayi a tare ta wahala,anma Hajiya tafi cin wahala ,me Aindo zatayi in ba dariya ba harda rike ciki,sanan tace”Alhamdulillah ashe ba mutuwa akayi ba,kardai kuma faduwa kukayi,to ku dama in Banda abunku da waw ta irin ta yayan farin wa zai taka wanan guri ba tare da ya bushe ba,woooo wooooo Alhaji Alhaji yasha kasa

Rarafawa tayi har ta fito waje duk sunyi sake suna kalon ta,har ta fita tana fita tayi ajiyar zuciya tace “wai Alhamdulillah Kai anma nikam wly yar baiwa ce na iya dabara, bari na fita na nemo magyari ya gyara su wai likita shine magyari ,da gudu ta fita tabar gidan,tana fita ta gyara d’aurin kugun da tayi,da dankwalin ta tayi ture kaga tsiya, zane daban riga daban dankwali daban,Yar kauye sak ga wata kwaliya da taci kaf ta rikita fuskarta da wata rikitaciyar kwaliyar ta.bazaka taba gane yanayinta ba,wani ta hango yana tafiya,gyara tafiyar ta tayi,Dan wai Kar ya rainata ,dan tasan mutan birni da raina yan kauye,tace”Kai dan mutume kai tsayawa yayi,ganin kamar dan birni ne wayaye sai tace”ke Aindo kema fa yanzu kinada matsayi karki manta a bini kike,kuma kowa da aikin sa yake tinkaho,to aike baban aiki ma gareki dan haka karki kwafsa,duk ita kadai take maganar ta cik’in Zuciyar ta,yamutse fuska tayi kicin kicin Kai kace mai jin kashi mutumin Yana kalon ta tsoro ma ta basa tsayawa yayi har ta karaso yaji ikon Allah ,tana wani Fadi tana kumbura,ta karaso tace “hi gaye wai irin na Yan birni ya kake dan Allah a Ina ne ake zuwa a d’auko mai gyara mutum idan ya lalace.”
Kalonta ya tsaya yi ,sai ganin ta murguda masa baki yayi,aiko ransa ya baci yace
“Ke Dan kin raina min hankali kinsan ni waye zakizo kazama dake wa ya sani ma ko mahaukaciya ce zakizo kina wani tambaya ta kodan kinganin a kasa,to ni dan Minista ne,motata ce ta samu matsala badan haka ba ke kin isa kimin banzan tambayar ki Yar kauye kawai.”
Tunda ya fara magana Aindo take masa gatsine tana murguda masa baki,tace “mtsss Ashe ma ba wani matsayi ne da uban naka ba,ina wani gadara a aikin masai ko me,yau Kai uban naka ma aikin kwasar Kashi yake ko,to bara kaji ni sunana Aindo ya a gurin ado Mai Saida kifi ubana babu wanda bai sanshi ba,uwata kuma babu Wanda baisan kuluwa Mai bakin masifa ba ,nikuma matsayina wly in kaji sai ka sara min,to matsayin da na taka ko wa yaji sai ya saramin.”
” Meye matsayin ki ya katseta ganin Alamun kamar batada hankali?
Niko keda matsayi,domin ni tantagariyar Yar aiki ce,Mai zaman kanta.
Kuma kaf wanan k’asa babu Wanda baisan A’indo Tantagariyar Yar Aiki ce ba.”
Sakin baki yayi sakaka yana kalon ta duba da yanda take zare zaren idanu tana kade Kaden idanu ya tabatar masa dacewa wanan batada hankali,shiko a duniya in akoi abinda yake tsoro to mahaukaci ne,domin tun Yana yaro wata mahaukciya ta taba fashe masa Kai,aiko ganin zare zaren da A’INDO takeyi yasa ya tsorata,tare da hada wani yawu makwat,ja da baya baya ya farayi adan tsorace tana binsa,ganin da yayyi kamar zata kamo sa yasa ya arta a guje,itama da gudu ta bisa,tare da ihu bisa hanya,tana cewa”wayyo jama’a ku kawo mana agaji gudu take tana waywayawa, duk a tunanin ta ko wasu suka biyo su,sosai take tikar gudu har ta fita daga unguwar,can ta tsaya tana haki,ta juya ta buga tsaki tace”mtsssss ashe ma bahon ba komai ba ya gani yasa ni inata tikar gudu kamar wata mahaukaciya ”
Saida ta gama gararanmar ta a gari bata samu mai gyaran mutum ba kamar yanda tace,tukon ta dawo gida can wajen yanmma,a lokacin tuni doctor yazo ya duba mutan gidan,inda akayi sa’a basuji rauni ba…..
tana dawowa ta shigo falo,ta kalli Hajiya dake zaune ta washe baki tace”wo wo Hajiya yau anji jiki aradu,Ashe manya ma na faduwa.
Kallon ta Hajiya tayi rai a bace tace “yanzu ke A’indo haka ake aiki so kike ki nakasa mu,wa yace miki ana zuba man gyada ayi guga?
“Yau Hajiya ke kikace falon yayyi walkiya har sai ya koma tamkar madubi,to shine Naga Man gyada kadai zaisa d’akin yayi walkiya,kuma ke Hajiya banda shirme irin naki,Aou na manta ashe ke baba ce,to Hajiya in banda wauwta irin ta yayan fari me ya kaiki taka gurin ba tare da ya bushe ba.”
Sake da baki Hajiya ta tsaya tana kalon A’indo wada take magana tsakaninta da Allah , Hajiya tace nice “mai wauta irin ta yan fari, kuma uban waye yace miki man zai bushe?wai anya A’indo kinada cikak’en hankali kuwa?
“To wly Hajiya nima haka ake cewa a kauyen mu inajin dai sai an kawo mai gyaran mutane ya bincik’e ni ya gani dan wly ko a kauye haka ake cewa banda shi.
Sauke ajiyar zuciya Hajiya tayi kawai A’INDO ta Shiga ranta ne da yau sai tabar gidan.”..
“Jeki ki huta gobe an nuna Miki aikin.”
“Yau Hajiya wane hutu zanyi inajin yunwa.”
“Je ki zuba abinci can kitchen .”
Hajiya tace Dan ta dan fara jin tsoron A’INDO.
Anma Hajiya langa nan zan cika dan wly tunda nazo gidan nan ban taba koshi ba.”
“Kije ki zuba iya cinki.”
Hajiya tace tana mamakin irin ci irin na A’indo
Bayan kwana biyu Hajiya ta Kira A’indo tace tazo taso mata kati na waya A’indo ta amshi dubu biyar Hajiya tace kiso min na dubu hudu da dari biyar,ki d’auki dari biyar,din kisha halawa.”
Kai Anma Allah zungura Miki Albarka Hajiya wly,Bari naje na sayo Miki.
Da gudu ta fita.”
Hajiya ta girgiza kai tace “Allah ya shirya,tana fita kofa da gudu har taje bakin hanya akoi wani shagon waya,Nan ta nufa to,A’indo dai batasan meye katin waya,itadai ta taba ganin gidan waya wurin Yar aikin gidan Hajiya da zuba kayan kwaliya a ciki,A’indo tace meye sai tace mata ai gidan waya ne ,to shine ta rike,dan ta manta abinda Hajiya ta aiketa siya tana zuwa tace”mai shago abani gidan waya na dubu hudu da dari biyar.”
Waro idanu Mai shagon yayi yace gidan waya kuma”
Murguda baki A’indo tayi tace “kaga Malam ka bani gidan waya meye na wani tambaya,baga irinsa ba ba can na gano ta nuna wani kwali.
Yace”Au kwalin waya zakice ,yau ai ba’a saida kwalin waya,saide ,in wayar Zaki saya….
” kaga Malam wly banzan gusa anan ba sai ka bani kwalin nan na dubu hudu da dari biyar casssss ma kuwa.” ta murguda masa baki,ganin yayi bari kaway ya amshi kudin ya bata, dan ga dukan alamu batada hankali.”
“Kawo kudin to na baki.”
“Hahhhh kaji dan rainin hankali cewar ta, ta kunto kudin da tayima kuli ta basa,kuma ka bani canjina eheee kar ayimin halin bera.”
Bata yayi dariya kunshe a bakin sa,Saida ya bata tace “yauwa dan gari,a haka dai gaka kamar ka waye anma katon bakauye ne kai,way Malam dan Allah na tambaye ka mana?
” Inajinki”
“Dan Allah Ina ake saida igiyar kaba ta d’aure awaki da raguna ?
“Kije can ga wani tsoho can zaune sune yake saidawa.”
” Kai anma wly Allah ya maka Albarka ta kunto wata tsohuwar naira biyar dinta a zani tace”gashi ka fida nera biyu kaban naira uku canji na,na baka kyauta halak malak,saboda ka nuna min wurin Saida igiya.”
“Kada kai mai shagon yayi yace a’a jeki nagoda.”
” Inba shirme irin naka ba wa yake kin k’arbar kudi,ai sai kayi ni na tafi,tafiya tayi taba tsohon dari biyar din duka tace” baba ka bani wanan igiyar ta dari biyar.
“Kai yata duk ina zaki da wanan igiya.”
“Dariya tayi tace “baba ka bani.”
“Yanzu ko yata ,ni ai na ma saida bari na baki,duka ya zuba Mata a buhu ya bata, ta jawo kayanta tana waka har ta karaso gida duka mutanen gidan kalon ta suke,babu Wanda ya d’auke ta mai hankali.
Karasowa falon tayi ta aje buhun kusa da Hajiya tace”wai Hajiya na gaji wly.
Kallon ta Hajiya tayi tace”keko meye wanan Kika jajubo a buhu.?
Washe Baki A’indo tayi tace Hajiya ai igiya ce”
“A’indo igiyar me kuma me zakiyi da ita?
“Hahhh Hajiya ai dan tare ne na fara ,gobe ma zan tafi na sayi dusa in kika Kara bani wani ragowar canji ko ta naira ashrin ce.”
“To naji me zakiyi dasu ?
Cewar Hajiya da ta fara tsoron Al’amarin A’indo.
“ai Hajiya kiwo zan fara Nan da shekara nake so na sayi Rago guda daya ya fara haihuwa,shine nake so na tanadi dusa da igiyar.”
” Waro idanu hajiya tayi tace”wai ni kam A’indo bakida hankali ne ?
“A to wa ya sani Hajiya sai an Kira mai gyaran mutane ya duba ni dan nima banida tabaci ”
“Uhum naji Allah ya kyauta bani katin wayar ni.”
ai kuwa Naso miki mai kyau Hajiya bara ki gani,nan ta zaro kwalin waya ta bata,.
Amsa hajiya tayi ta duba tace me zan gani niko Hajiya,duba kwalin tayi bayada komai kwongo ne,Hajiya ta zaro Ido tace A’indo meye wanan shine katin wayar A’indo.?
Hahhhhh kaji Hajiya da wani shirme kuma to meye in ba shi ba …………….
Aci gaba da gashi

Yaune mukayi finel exam d’immu, kowa kagani fuskarshi fes yana murna daganan hotuna mukayita d’auka har wuce k’arfe biyu narana muna ta chashewa a school daganan, direban su Zahra dayazo d’aukarta nabisu saboda ta rok’eni akan inje yayansu ya had’a mata k’warya-k’waryar faty, na taya murna iyasu ‘yan gida da k’awayenta.

A chammade ansha shagali har k’arfe biyar na yamma, sannan muka samu kammu a d’akinta muka yada zango, wash Allah na wallahi yau duk nagaji! Huumh kede bari ai inaga yau indanna kwanta bazan iya tashi ba.

Yawwa nik’o dama inason, muyi magana dake, Humaira zama na gyara sosai nace inajiki, my Zahra “Wainiko wannan matar yayannaki haka takeyi miki irin wannan cimmutunci? Amma kuma kike k’yaleta, da baiwafa ta kiraki amma baki tankaba kuma wannan Wanda yazo ya wucemu, inace shine yayannaki?”

Huuuuumh bazaki ganeba Zahra, kamar ya bazan gane ba? To ganar dani. Zahra zamfad’a miki komi koda de sirrinane amma kema kinzama wata b’angare na rayuwata saboda a yanzu duk fad’in garin lagos banida wasu makusanta kamar ku biyu keda Anty Billy, kuma nima nagaji da shirun ina buk’atar shawara da mafita ta yadda zamb’ullo ma al’amarinnan saboda nima ba dabba bace mutumce kamar kowa.

Idanuwa kawai Zahra ta zuba min tana kallona, tab’ata nayi nace yanaji kinyi shiru ne? Bakomi kawai sauranki nakeyi, domin nak’osa naji me zakice min. Yanzu zakiji komi kuwa.

Kamar yadda kikasani sunana Aisha Umar gwaram, da mahaifina da mahaifin Yaya Aliyu uwarsu d’aya ubansu d’aya, daganan ta kwashe tarihinta gaba d’aya har zuwa aurensu da Haidar ta fad’awa, Zahra tokinji yadda komi yakasance kinji koni wacece Zahra don haka yanzu meye mafita?

“Kuka sosai Zahra takeyi” tab lalai Indo kinga rayuwa wallahi bantab’a tsammanin akwai irin wannan rayuwar azahiri, nayi tsammanin saide a littafai ko fina-finai, “aiduk abinda kikaga anayi a littafai da fina-finai majority suna faruwa agaskene tabbas hakane amma fa da banyarda ba saida naji tarihinki gaskiya yakamata wahalarki ta k’are hakanan.

“Shawarata yanzu itace Aisha dole kitashi tsaye ki amshi mijinki ahannuki lokaci yayi da zakidena yiwa wannan sakaryar bauta, yanzude dolene mufara jawo hankalinshi zuwa gareki. Taya kenan eh kamar yawan kwalliya bakince kuna dad’ewa baku had’u ba? Eh to yanzu yakamata kullum ak’allaku had’u kamar sau uku koma fiye da haka, kamar yaushe da yaushe?

“Kamar da safe kafin yafita zuwa office yazama dole ki d’auki wanka najan magana kizo ki gitta ta inda dole zaiganki, kuma kikasance ma’abociyar k’amshi koda nasanki inde tananne banida haufi dake yanzu tashi muje gurin me gyaran Kai, daganan zamu biya wani guri dake kai Zahra yanzufa yamma tayi kuma kinsan dole inkoma inyi girki, tsaki zahra taja tace ai wallahi duk abunnan ma dayafaru laifinkine gakide ahaka kamar wayayya amma muguwar bagida jiyace ke.

“Dariya nakamayi nace bakiji nid’in ‘yar k’auye bace kinga kuwa ai dole inyi k’auyanci ko? Ai wallahi ingaya miki yau ba inda zaki saimunje ammaki gyara na musamman saboda sonike kafin jarrabawar mu tafito, ace lokacin ansamar min baby, idanuwa Indo tazaro tace tab wallahi kimfi k’arfina,

Matsoraciya kawai yoni innice ace inada miji kusan shekara hud’u tab ai wallahi da tuni nayi wuf da shi dariya sosai Zahra tabani sannan muka mik’e muka fito, sallama mukayiwa Mommy mahaifiyar Zahra mace me kirki sosai da sanin yakamata.

“Turarukan Humra tabani masu masufar k’amshi tmda wani had’in sabulu irinna shuwa dayake mommyn shuwace, godiya sosai nayi mata sannan muka fito, tsakanin gidansu Zahra da gurin saloon d’in ba wani nisa ak’afa muka k’arasa shagon.

Matar musulmace amma ba ba hausa bace, donko hausa bataji shagone babba sosai me b’angarori da yawa, akwai gurin gyaran kai da gurin wanki k’afa dana kwalliya gurinde ba abinda basuyi Wanda yadanganci gyara jiki.
Littafan Hausa Novels Guda 1000 masu dadi

Matar Makaho Complete Hausa Novel

Hotunan Lalle Masu Kyau Kunshin Gam

Matar Yaro Hausa Novel

Hajiya Gwale Hausa Novel Complete

Gyaran Nono a sari data

Tsofaffafin Hausa Novels Watpadd

Dayake matar customer su Mommynce Zahra tayi mata bayanin gyaran jiki za’ayimin dana kai, cewatayi mushiga cikin wani d’aki wanda aka zagaye shi da labule matar da kanta tayimin, kaina akafara gyaramin Dana bud’e kannawa duk saida sukayi ihu saboda yawan sumar kannawa gata irin ta fulaninnace me shegen santsi, kaina baya buk’atar relaxer kawaide tayi amfani da mayuka masu masifar kyau da tsada ne, atakaicede ammin gyara sosai fatata dataji wanki da kaya had’a had’e sai faman santsi takeyi ga wani shek’i da ta d’auka kamar Katab’ani jini ya fito.

Mune ba mubar wurin ba sai waje takwas na dare, daganan direbansu ya d’aukemu zuwa wani k’aton shop wanda shagon ba komi suke saida waba sai English wear’s masu masifar kyau, todama bare kunsan sune kayan ‘yan garin.

Nan danan Zahra tashiga loda min kaya iri-iri idan ta d’akko wasu mani kunya matake bani ince karta d’auka domin bazan iya sawa ba sunyi k’anana da yawa, tsaki kawai takeja, saida ta lodi kaya masu yawa sosai sannan mukaje gurin biyan kud’i atm d’inta kawai ta mik’a aka cire kud’in aka samana kayan abayan mota.

Namma mub’ata lokaci sosai don har after ten muna wurin, daganan bayan mungama muka tafi ahanyane ta bani wani had’in man shafawa tace mommynta ke saidasu matan aurene kawai ke amfani dashi shima sai idan zaka kwanta tare da mijinka, mommyn batasan kinada aure ba shiyasa bata had’a miki da shiba amma inna koma zanfad’a Mata komi nasan itama zata taimaka mana.

Shiru kawai nayi saboda bansan abinda zan sakawa wannan baiwar Allah dashi ba amsa nayi nace god………… Katseni tayi da sauri tace bana son godiyarki ki rik’e kayarki.

Don Allah Zahra karki hanani gode miki saboda kimmin abubuwa da yawa arayuwa, ko yayane kibari nagode miki koda nasan banida abinda zansaka miki dashi, bana buk’atar godiyarki madam, abu d’aya nake buk’ata a wajeki.

Da sauri nace ki fad’i komeye shi inde har befi k’arfina wallahi nayi miki alk’awarin baki shi.

Murmushi Zahra tayi sannan tace bakomi nake soba illa inaso kiyimin alk’awarin, zaki dage kibi shawar-warinmu gurin ganin kin k’wato martabarki, sannan kuma kiyimin alk’awarin saka wa’innan kayan da muka siyo keda komi ma wanda zaiwo da hankalin mijiki zuwa gareki saboda inason kafin mukoma school ki sauke mishi wannan hayak’in dake kanshi.

Doguwar ajiyar zuciya naja sannan nace bakomi Zahra nayimiki alk’arin insha Allahu zanyi iyakar bakin k’ok’arin, kawaide kitayani da addu’a, insha Allahu zantayaki da addu’a sosai tawan, Amaryar Aliyu Haidar A Squar tak’are maganar da tsokana.

Sanda muka shigo cikin bareck d’in shad’aya saura kwata na dare ak’ofar plat d’inmmu suka ajiyeni Emeka dake zaune kambenci ak’ifar plat d’in shine yataso yana mana welcome yad’aukar min kayana yashi dasu sannan mukayi sallama dasu Zahra, saida naga sumbar cikin bareck d’in sannan na nufi cikin gidan………..,…………

*Gashinan de ba yawa mutara a next pege domin jin yadda zata kaya karkubari abaku labari domin yanzu za’afara wasan ammafa innaga ruwan comments ngd*

 

*_Assalamu alaikum ‘yan’uwana masoyana masoyan book d’ina Ina yiwa kowa da kowa barka da salla Allah ya mai-maita mana yakaimu ta bad’in bad’ad’a da rai da lafiyar mu da wa’inda suka kirani da wa’inda sukayi min tex kaidama wa’inda basu kira ba duk Ina gdy Allah yabar zumunci, ngd sosai UMMUHFADIMA tanayiwa kowa fatan alkhairi_*

Pege 45-46

*K’AUYEN GWARAM*

Tun daga ranar malam sada yadage ya hana idonshi barci, yanata k’ok’ari akan Baffah saboda abun na matuk’ar damunshi.

Baffah ma tunda yafarko daga suman da yayi tundaga nan bekoma dai-dai ba yawan shurunshi sai yak’aru fiye da da, yanzu saide kaganshi ya zauna yayi tagumi,

Yau dayake juma’ace bayan sundawo daga masallaci, Malam sada yashiga gidanshi, yace ina zuwa malam Ummaru, “to yace yasamu guri ya zauna kan dakalin dake k’ofar gidan, be dad’eba saigashi ya fito rik’e da rubutu acikin k’warya ya mik’awa Baffah amsa yayi yana jiran yaji k’arin bayani.

Kasha mana maganin meye? Had’a fuska yayi yace kana tunanin zan cutar da kaine? Umbazaka sha ba bani kayana, ya ida maganar yana kai hannu zai karb’a, a’a yi hak’uri abun bekai chamba Baffah ya fad’a yana kai maganin abakin shi, saida yasha sosai sannan ya cire daga bakin shi yana mik’awa malam Sada k’waryar, kauda kai yayi yace aiduka zaka shanye shi, bece komi ba ya kuma kaiwa bakinshi saida ya shanye shi tas sannan ya mik’a mishi k’waryar.

Amsa kawai yayi yajuya zai shige gidanshi saurin rik’oshi Baffah yayi yace haba Malam Sada fushin kuma na meye? Inde maganinne aide nasha ko.

Eh kasha ainaji kana yimin wasu tambayoyi ne kasande bazan iya cutar da kai ba ko? Eh nasani kayi hak’uri bari inje insamu in d’an kwanta saboda inajin kaina kamar yana d’an juya min. To jeka Allah yasawwak’e da ameen ya amsa sannan yamik’e yanufi cikin soron gidanshi yana had’a hanya, da kallo Malam Sada yabi shi yana me matuk’ar tausaya mishi mutum har mutum amma gaba d’aya yazama wani iri saboda illar sihiri, girgiza kanshi yayi yana menemawa d’an uwannashi amininshi kuma mak’ofcinshi lafiya.

*KATSINAN DUKKO*

Wata arniyar motace naga tayi parking ak’ofar shagon tabawa me abinci, wata farar macce ce tabud’o k’ofar motar ta fito tana wani yayya mutsa fuska, oooooooh hajiya Zeee kina wuta fa wannan arniyarfa wani kallon nafik’arfinku naga tana bin ‘yammatan da suke Mata kirarin naga tabisu da shi, Niko nace tofa ikon Allah kuko daga ganin hajiya guda ta tsaya amotar ta sai kufara yimata irin wanna banbad’anc……. Ban kai k’arshen maganar da nakeyi ba naji wani saurayi yana tambayar su Suby wai wannan ba wannan ‘yar k’auyen bace? Huuhm kaide bari kawai Ziko wallahi ita ai ingaya maka yanzu Abuwa tashigo gari sosai saboda tashigo bariki da k’afar dama.

Bansan sanda na aza hannu akaba nace tab bade abuwar Gwagwgo me k’irar maza ba ta gwaram?, suka amsa min da cewa itafa, aida sauri nayi cikin shagon domin na k’ara k’are mata kallo, aikode ita ce amma saide wannan Fara ce tas domin har wani kashe ido takeyi, sannan ga ‘ya’yan banki atare da ita duniya sabuwa.

Magana suke da hajiyar k’asa k’asa sannan naga ta d’ebo d’auri-d’aurin ‘yandubu dubu ta mik’awa tabawa tace gashinan duk, yanda kukayi ki kira saboda ni daganan ma Abuja zamu wuce tare da Hajiyata domin tanaso waita nunani agurin k’awayenta.

To shikenan Allah ya kiyaye hanya Hajiya Zainab, amma zaki biya ta gida ko domin kindad’e baki jekika ga Haruna ba domin ko d’azu kafin nafito saida yake tambayana wai yaushe zaki dawo, mitssss toke mekikace mishi? Yoni mezance mishi kuwa, zageshi nayi tas saikace yabani ajiyarki.

Mitsss kimmun dai-dai bar sakaran niyanzu banida lokacin shi ke bama shiba ni duk wani namiji yanzu baya gabana, maza mezasubaka umbanda wahala sai su d’irka maka ciki, amma hajiyoyi fa ga dad’i ga nera kibari kawai, dariya sukayi harda tafawa, _wa’iyazu billah Allahumma ajirnifiii masibati wakkalif’ni khairaan minhaa ya Allah katsare mana imanin mu damu da ‘ya’yanyemmu da dukkan zuri’ar musulmi, wannan wacce irin musibace dake faruwa, me ‘yar’uwarki mace zata iya yimiki mezaki samu agareta ummbanda tarin zunnubai Allah shirya duk masuyi yasa subari kafin lokaci ya k’ure musu ameeeeen_

*GWAGWGO*

Adai-dai lokacin da Abuwa tasamu duniya take bachaka da ita itakuma Gwagwgo tanachan durk’ushe gaban bokanta tana begin d’in bokanta akan ya binciko mata halin da ‘yarta take, madubin tsafinshi ya d’auka yayi surkullenshi, saiga Abuwar acikin wani ma haukacin falo zaune tsakiyar manyan hajiyoyi sunsata atsaka, itako saifaman dad’i takeji.

Ai Gwagwgo bata san sanda ta fashe da kuka ba tana rok’on boka akan ya taimaketa ya binciko Mata inda ‘yarta take saboda wallahi ninasan farrak’u akayimin da ‘yata saboda umba haka bayadda za’ayi Abuwa ta manta dani, ‘yarki tana garin Katsina a wata unguwa mesuna tudun ‘yallihidda, wajen masallacin idi, daganan duk Wanda kika tambaya gidan tabawa me abinci yasani, ammafa duk abunda kika taras baruwana karkiyi kuka dani kiyi kuka da kanki, babu ma abinda zantaras sai alkhairi “shikenan kitafi rauhanai sukareki” duk’awa tayi har k’asa tace godiya nake me taimakona akan komi dabaka daban San yadda zanyi da rayuwata ba.

Hahahahahahahaha wata mahaukaciyar dariya yarink’ayi kamar zaifasa kogon dutsen, tashi kitafi kina cikin kariyar mu harki dawo ga wannan kiyi amfani dashi dai-dai sanda zakigana da ‘yar taki, “godiyanake” wa’iyazu billah.

*LAGOS*

Kaina tsaye nashige cikin falon saboda kwata-kwata bantsammani ganin wani acikin mutanan gidamba, turus naja na tsaya saboda ganin megidan danayi saifaman kai-kawo da yakeyi acikin falon, k’arar bud’e k’ofar danayi ce ta ankarar dashi da sauri ya juyo yana, kallona.

Ko k’ala bance mishi ba na cigaba da tafiya abina, keeeeeeeeeeeeh wata irin tsawar datasa saida nafurgita yadaka min daga gidan ubanwa kike? Kuma wane tsinanne ne yasauke ki amota? Duk da cewa na tsorata da yanayinshi kuma na firgita matuk’a amma duk da haka sai kawai nadake kwata-kwata ko afuskata ban nuna mishi cewa natsorata ba,.

Juyowa nayi fuskata dauke da wani murmushi wanda yafi kama da kai asuwa, wai badake nake magana ba saina tattakaki agurinnan, ok Ashe dani kake nayi tsammanin dakanka kake magana saboda banji kakira sunanaba; eh dakaina nake magana kinsan aini ma haukacine.

Sorry nibance ba amma koma daga Ina nake ai inaga bakada matsala da hakan ko saboda ba ajiyeni kayi bako sannan kuma bakowa bane ya saukeni ba sai masoyi abin k’aunata yaro sabon jini fil aleda wanda nizan b’are abuna, ba second hand ba, mesona tsakani da Allah duk dakasancewa ta ‘yar k’auye, ta idasa maganar tana cigaba da tafiyarta zuwa d’akinta ko waigowa batayi ba saboda wani mugun tsoro ganitake kamar zai ma k’areta. Tab yanzufa za’afara wasan kude kubiyini karku Bari abaku lbr………………

*pls kuci gaba da hak’uri Dani de komi yakusa zama normal ngd gashide na dawo da k’arfina insha Allahu ammafa yawan comments d’inku shine zai bani k’arfin gwiwar yimuku typing kullum yawan comments yawan typing ahaaaaaaa*

 Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Aisha Indo Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

4 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!