Hausa Novels

Al’amin Dagash Hausa Novel Complete

Al’amin Dagash Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Dattawa ne zaune kan wasu lumtsa lumtsar kujeru masu ɗaukar hankali wanda dagani ba tambaya office ne, Da alamu ɗayane yakawo wa daya ziyara Dan daganin yanayin farin ciki a fuskar su zaka tabbatar da suna matukar murnar ganin junansu, ALHAJI SU AD BABANGIDA shine mamallakin wannan katafaren office yayin da Abokinshi Alhaji Ɗan Asabe yakawo masa ziyara bayan tsawon shekarun dasukayi basuga juna ba , Sosai Alhaji Su’ad yaji daɗin ganin Amininsa, Yake tambayar sa” yanzu dai kadawo Nigeria ba maganar komawa Spain ko”?

 

Alhaji Ɗan Asabe yayi murmushi irin nasu na manya yace “sosai ma maganar danake maka ayanzu ma haka families ɗina suna nan Nigeria , Kaga kuwa ai dagaske nake faɗa maka ban fada maka bane saboda ina so na baka surprise ”

 

Alhaji Su’ad yace “kai amma naji daɗin dawowar ka kusa dani Abokina ,kuma tabbas ka shammace Ni” Cikin murmushi Alhaji Dan asabe yace “oh really ?”

 

Alhaji Su’ad yace “yes I mean it Kuma saina rama” yafaɗa yana murmushi shima ,

 

Alhaji Su’ad yace” yanzu bawannan ba a wani state kake “? Alhaji Ɗan Asabe yace” kana nufin zanyi nisa dakaine Impossible my friend , Surprise nakeson nabaka nima anan kano na gina gidana ,”

 

Alhaji suad cikin tsananin farinciki yace” kai amma naji dadi so yanzu kawai katashi muwuce gidana muje kugaisa da su hajiyar kafin sai muwuce naje naga gidan naka ” Alhaji Ɗan Asabe yace” hakan ma yayi abokina kasa mu duniyafa irin wannan Hutu haka “?

 

Ahaji Su’ad yayi dariya yace har nakaika kaga yadda ka ajiye wani uban tunbi Alhaji ” Sukayi dariya gabadayan su kafin nan Alhaji Su’ad yaɗauki abinda zai ɗauka suka fito a office ɗin,

 

Secretary ɗin sa yayi saurin durkusawa sir bade har katashi ba ? Dan na ga time beyi ba”?

 

Ahaji Su’ad yace “natashi yau ga key nan take care of the office” I have a special guest today yafaɗa Yana nuna masa Alhaji dan Asabe ” Cikin girmamawa secretary yasake dukawa yagaida Alhaji ɗan Asabe Secretary yakarba yace “ok sir ”

 

Masu tsaron lafiyarsa suka karbi jakar zuwa mota ,

 

Suka fita kowannen su yayi wajen motarsa yashiga , Security din alhaji su’ad sukayi saurin bude mishi kofan motar Driver yaja sukatafi Alhaji Su’ad ne yafara gaba kafin Alhaji Ɗan Asabe yabi bayansa suka haura titi , Wani mansion building Suka nufa wato gida ne nagani Wanda nimai rubutu bazan iya misalta shiba saboda ya wuce tunaninmu gaba ɗaya Saidai gareku masu karatu kuyi iya kokarin wajan ganin kun hasko wanann gida cikin zuciyoyinku yayin karatu ,

 

Iya tsaruwa ya tsaru nera tayi kuka wajen Dankara wannan gida Masha Allah, Megadi ne yabuɗe gate da sauri yana wa Alhaji sannu da zuwa , ta hanyar Daga masa hanun cikin jinjinawa ”

 

Yashige ciki Alhaji Ɗan Asabe ma yabishi zuwa parking lord , Atare aka buɗe musu kofar, Alhaji Ɗan Asabe ya tsaya ya ƙarewa gidan kallo tsaf tunda yake arayuwarshi baitaba ganin tsarin ginin daya mishi kyau irin wannan ba ,

 

Yakalli Abokinshi Alhaji Su’ad “Yace gaskiya Su’ad kagina aljannar duniya” Murmushi Alhaji Su’ad yayi yace “Ɗan Asabe kenan ai lefinkane dazaka Gina gidan naka baka neme niba”? Company na ba abin da ba ayi na harkar gine gine da kawata gidaje kai harma da abinda ya kunshi furniture’s ”

 

Duk yawancin state din kasannan muna da branch a can kaga ko a wani gari kakeson gini baka da matsala I can do every thing for you amma kaki kasanar dani zaka dawo kasar ba ”

 

Alhaji Ɗan Asabe yace” kasan wai duk Dan inbaka mamakine nayi hakan ”

 

Alhaji Su’ad yace “well not too late , zamuyi magana yanzu dai mushiga ciki ka huta tukun” Atare suka shiga ciki Alhaji Ɗan Asabe bai sake tsinkewa da lamarin gidan ba seda suka shiga ciki,

 

Iya haɗuwa koina ya haɗu agidan nan Alhaji Dan Asabe se santin gidan yake ,

 

A wani haɗaɗɗan falo suka zauna , Alhaji Su’ad yaɗauki wayarsa yashiga Dan nawa Bayan andaga yace” uwargida rangida wacce yakira da uwargida tace ” ya akayi daddyn Al’amin ya office ɗin”?

 

Murmushi yayi yace” Gani a falo nida baƙo kizoki ga surprise be jira tasa ke cewa komai ba yakashe wayar tare da kallon Alhaji Ɗan Asabe yace yanzu zata fito ,

 

Yasake dailing wata number Daga can aka ɗauka yace amarya bakya lefi kokin kashe Ɗan masu gida , Murmushi tasa ke mishi kaman yana ganinta tace” kai daddyn Afnan wannan kirari haka ” Yayi murmushi yace x Gani afalo kifito kiga surprise tace ” OK on my way ”

 

Murmushi Alhaji Ɗan Asabe yayi yakalli Abokin nashi yace “kai Abokina an girma asan girma mana wannan kashe murya a waya haka “?

 

Murmushi Alhaji Su’ad yayi yace “har nakai ka ” Kai ai matsorocine gashi ka kasa ajiye mata biyu saboda kana tsoron hajiya sadiya ,

 

Gaba ɗaya dariya sukayi kusan ” atare suka shigo cikin falon amarya da uwargidan

 

Cikin mamaki hajiya Aisha tace” kai wata sabon gani wanake gani kaman Alhaji Ɗan Asabe,?” Dariya Alhaji Ɗan Asabe yayi yace “nine dai uwargida sarautar mata ba gizo idonki yake miki ba , munsa meku ƙalau tace “lafiya ƙalau ya iyalin amma dai dasu kazo ko”? kafin yabata amsa daddyn Al’amin yabata amsa yace “aitare suke yadawo Nigeria” Mom din Al’amin kai amma naji dadi shine hajiya sadiya bata nemeni a wayaba” Alhaji ɗan Asabe yace “tanason tabaki mamakine ” mom tace ” aikuwa zamu haɗu ne” sukayi dariya tace ” ya yaran nawa ” yace ” suna lafiya ” duk zasu zo ai ”

 

Ya kalli hajiya zabbau yace “kaga amarya agurin Abokina Cikin dariya itama hajiya zabbau tagaisheshi tare da tambayar shi ya iyali”

 

Kafin yan mintoci ancika gaban Alhaji Ɗan Asabe da kayan ciye ciye , Sallama sukaji kowa yamaida hankalin sa Ga bakin kofa ,

 

Wow wani hallita nagani Wanda akalla dai zan iyacewa wannan halitta bazai wuce jinsin larabawa ko India ba Dan gaskiya ba kyarya wanann matashin saurayin ya haɗu bakarya dogone fari yana da fadi ga dara daran ido masu matukar Jan hankalin Ga kwantaccen saje ɗaya kara wa fuskarsa kyau da kwarjini ,

 

Yana sanyene cikin wasu haɗaɗɗun kaya masu tsadar gaske wandon Jean’s ne black da kuma light blue shirt ,, Kansa ɗauke yake da kwantacciyar gashi kaman dai na larabawa ko India ,yayinda ba rabo da askin zamani akansa , Tsayawa misalta muku irin haɗuwar gayen tamkar kasawa ce agareshi ,gareku masu karatu ,

 

Fuskarsa ɗauke da farin Glass Wanda baka rabashida shi ,kasancewar sa na likita , Cikin murna ya rungume dadinsa Saiku rantse sun Daɗe ne basu haɗu ba

 

Daddyn Al’amin yace “yadai son ya aikin yanaga kadawo dawo da wuri “?

 

Kafin yaba daddynsa amsa yakai kallonsa kan Alhaji Ɗan Asabe yace” lah daddy yaushe kazo wallahi bangankaba”? Yatashi daga jikin daddynsa yafada jikin Alhaji Dan Asabe , Shima dariya yayi tare da rungume sa yace surprise nakeson Baku kaida dadynka son ,”

 

Al’amin yayi murmushi yace am Glad to see you dad “you are welcome ”

 

Alhaji Dan asabe yace me too my son , thanks for welcoming your dad” Murmushi Al’amin yayi Yace “daddy zayyad fa tare kuke yace ” no shisai next week zai gama abin da yakeyi kaima Kasan da yazo kaizaifara nema ”

 

Al’amin yace I no that dad Allah yadawo dashi lafiya nasan shima bazai faɗa min zai zo ba saida naganshi tunda muke waya bai ce yakusa dawowa ba ”

 

Ya tashi yakoma inda mom ɗinsa take ya kwantar da kanshi akan cinyar ta , Yakai kallonshi kan hajiya zabbau yace” sannu da gida ummy “ciki ciki ta amsa mai inda sabo yasaba da wannan hali irin na matar ubansa ” hakan baya damun sa ,

 

Sam bata ƙaunarsa kamar yadda shima mom ɗinsa bata kaunarta da ita da yaranta itama haka ta tsani Al’amin sosai kamar ta shake shi.ya mutu haka takeji ,

 

Mom ɗin sa ta shafa kansa tace “kaci abinci kuwa son”? Yace “no mom wallahi yunwa ce tadawo dani gida by this time around ”

 

Daddy dake jin hirarsu yayi murmushi yace” to ai lefin kane son tun yaushe naketa baka shawarar kayi aure kafito da matar dakakeso kaki”

 

Alhaji Ɗan Asabe yayi murmushi yace ” yishiru Ɗana tunda Ga daddynka nan zan baka kanwarka Suhaila kaje kaganta kushirya kanku”

 

aiba Al’amin dayayi mutuwar zaune ba harta dady da mom saida suma suka kalli juna Dansanin halin Ɗan nasu ba irin mace da ba a mishiba amma yaƙi ya nemo da kansa ma yaƙi ,

 

Al’amin tashi yayi daga jikin mom ɗinsa ya wuce part ɗinsa, shiru batare da ya tanka ba , Ganin haka Yasa Alhaji Ɗan Asabe murmushi yace “au kunya nabaka ma “?

 

Murmushi Alhaji Su’ad yayi yace “kai amma kuwa naji dadi wannan Abu kaga tuwo na maina kenan ” sukayi dariya ,

 

Mom tace “kai amma Abu yayi dad’i wallahi Allah yasa Albarka aciki , Sukace “Amin” hajiya zabbau ce kaɗai bata tankaba Dan ita bataso hakaba”

 

Al’amin yafaɗa kan Royal bed dinshi tareda sauke ajiyar zuciya

 

TUNA BAYA*

 

Alhaji Su’ad Ɗan Asalin garin kano ne anan aka haifesa Maihaifinsa Alhaji Yusuf yakasance yagaji sarauta gaba da baya amma kasancewar Alhaji suad bashida sha’awar sarauta , Yasa bayan rasuwar mahaifinsa se bai karbi sarautaba yabawarwa ƙaninsa Wanda a yanzu shike da wannan sarautar ta kano gaba ɗayanta ,

 

Alhaji Su’ad su biyu iyayensu suka Haifa Wanda Alhaji su’ad shine babba sai ƙaninsa musa wato memartabar sarkin kano kenan na yanzu , Alhaji Su’ad da musa suna matukar son junansu sosai Dan aure ma rana daya sukayi abinsu Alhaji Su’ad sukawuce kasar Spain da amaryarsa inda anan yake kasuwancinsa , Aisha sunan matarshi yar asalin kasar Libiya zamane yadawo dasu Nigeria kuma abuja anan suka hadu da alhaji suad har Allah yakaisu Ga aure

Yaɗauketa sukayi kasar Spain Yayinda musa kaninsa shikuma yake kano da Amaryarsa zulai ,

 

Hajiya Aisha matar Su’ad shekararta ɗaya ta haifo kyakkyawar ɗan ta mekama da ita ba abin da yabari nata komai da komai dan yafita ma kyau nesa bakusa amma seya ɗauko jikin daddynsa komai na daddy ne amma kuma fuskar da farin na momy ne ranar suna yazo akasawa yaro suna Al’amin yan Nigeria sunzo ciki kuwa harda matar musa wacce itama tazo da katon cikinta koyau ko gobe

 

Sunyi murna sosai da samun wannan kyauta daga Allah yabasu , yayin da suka shiga tarairayar ɗansu sun shagwaɓashi sosai har abin yayi yawa , , Dan acikinsu bamai son yaga bacin ran dan nasu shiyasa kome yayi dai dai ne ba mai mishi faɗa Mom din Al’amin hajiya Aisha macece kyakkawa ajin farko acikin mata sai dai kash takasance bata kaunar talaka a rayuwarta taɗauki tsana ta daura akan talaka ,bataso taga wani ya raɓesu itada mijinta da ɗansu dan ita aganinta talaka ba mutum bane saboda batasan talauciba a rayuwarta ta taso cikin kudi tayi aure cikin kuɗi,

 

Wannan halin nata ne hakama mijinta Alhaji Su’ad shima bayason mutane kokaɗan shiyasa idan yasa kafa sukabar kasar bazai sake waiwayowaba sai yaga dama , Haka suka hadu suka Gina rayuwar ɗansu kwalli ɗaya a duniya wato Al’amin, Al’amin yana da shekara goma aduniya daddynsa yakara aure da kanwar abokinsa zabbau wacce auren za a iyacewa na kaddarace dan yadda suke soyayya da mom ɗin Al’amin bazaka taba ɗauka zemata kishiya cikin sauki haka ba , Mom din Al’amin tayi baƙin cikin auren mijinta uban danta kwalli daya aduniya , amma dayake shidin namijin duniyane yanuna mata yana bukatar ganin yara kanana ne agidansa ,

 

Itakuwa mom din Al’amin tana haihuwar sa batare da tayi shawara da mijinta tasa aka juya mahaifarta dan ita acewarta haihuwa matsalace tunda Allah yabata wannan ma Allah yara matashi , Lokacin da Alhaji Su’ad yaji labarin abinda tayi shine yakudiri aniyar hukuntata , Ta hanyar kara aure wanne shine sanadiyar kara auren Alhaji suad

 

Yatare da amaryarsa zabbau sosai suke zuba kishi da hajiya Aisha kwatakwata bajituwa a tsakaninsu ,

 

Musammam ma da zabbau tabude ido taga yadda Alhaji Su’ad yaɗauki son duniya yaɗaurashi akan Al’amin wannan Abu na matukar damunta ,

 

Cikin ikon Allah kuwa zabbau tasamu ciki kuzo kuga kaɗaɗi da iyayi Alhaji Su’ad kuwa yashiga riritata sosai dan a yanzu ba abinda yafi bukata irin yaga yatara zuria , Sai daifa babu abinda ya ragu nadaga son dayakewa matarshi mom din Al’amin wannan yasake saka tsanar mom din Al’amin azuciyar kishiyarta hajiya zabbau,

 

Al’amin ba abinda yabari na gadon halin iyayensa danshi harma yafisu akidar tsanar talaka gashi ana mugun tsoronshi ko a school kashiga hanun click ɗinsu baza kasha ba dan zaiyagaka Kane kuma agaban mutane ,zai wulakanta ka ,ko kai wanene ,

 

Su ukune abokan juna Wanda suma iyayensu Masu kudine sosai suma suna zamane acan Spain ɗin , Alhaji Dan asabe babban abokin dadyn Al’amin ne kuma makocinsa anan kasar Spain , Sun shaku sosai komai nasu tare sukeyi haka ma ‘ya’yansu basa rabuwa , Alhaji Ɗan asabe yana ɗaya, hajiya sadiya itace uwargidansa yaranta biyar biyu maza uku mata , Zayyad Abokin Al’amin na ƙud da ƙud shima shine babba agurin su sai kaninsa mas’ud sai kuma sai mebinsa suhailat sai ƙannanta biyu ,

 

Zayyad shima rayuwarsu ɗaya da Al’amin shiyasa abotarsu tazo ɗaya , Àl’amin yana da shekara shabiyu aduniya yayi haddar alkur’ni dasauran littafai na addini masanin kur’ani ne sosai sai dai yasani amma baya aikidasu , Sai dai akwai sallah akan lokaci dan gaskiya duk shakiyancinsa Allah bebashi ikon wasa da sallah ba yana kokari sosai wajan kiyaye dokokin ubangiji akansa ,

 

Yana shekara 25 years yazama babban likitan mezaman kansa Wanda kosu acan kasar Spain din suna alfahari dashi sosai, Kusan shekara takwas dafara aikinsa kafin kafin suka koma Nigeria gaba ɗayansu , Suka bar Alhaji Dan Asabe acan da iyalanshi danshi yace bayanzu yake da burin dawowa kasarsaba

 

Al’amin tunda yadawo yafara aiki a Asibitinsa Wanda burinsa kenan amma hakan baisa yadai na business ba tare da daddynsa ko ina yana nan yana neman nakansa sosai , Hausawa sukece kabi fadin malam amma karkabi halinsa Dan Al’amin kam ba abinda bayasha na su giya da duk kayan maye , Kwararrene a wannan gefen ,kuma wai yana mazaunin babban likita , Baya Neman mata sosai budurwasa ɗaya Victoria wacce akecewa vicy , Daga ita baitaba sanin wata ‘ya maceba aduniya ba Saboda shi Allah yayishi mutunne mai kyama sosai , Itama dakyar tashawo kanshi ,tahanyar shayar dashi desire tablet , Ba a hayyacinsa ya kusanceta , a lokacin da yafarka yaga abinda yafaru , Bakaramin duka yawa vicy ba saida tayi jinyar jikinta sosai , Itakuwa kaman mayya taki rabuwa dashi , Yazama tundaga wannan lokacin suke muamala kamar mata da namiji , har wa yau ,

 

Daddy da mummy duk sunsan halin da yake ciki , Duk sunsan komai suna gudun bacin ranshi ne Da kuma soyayyar da suke masa wanda basa iya tsawatar masa ,gudun bacin ransa , Shiyasa kawai kullum acikin yi wa Al’amin addua suke , Ba irin macen daba a kawo mishi yazaɓa ba Dan yabar gurba tacciyar rayuwar dayakeyi amma yaƙi dainawa , Sunsa mishi ido sunkuma bishi da addua

 

Al’amin da zayyad da kuma Faisal abokaine sosai waɗan da halinsu yaso ɗaya , Banbancin kawai su basuda daure fuska sabanin Al’amin da kullum fuskarsa kaman baitaba dariya ba Sam baya da sake fuska ga gudun raini , Ko Vicky ma ita take binshi amma baitaba nemanta da kanshiba danshi aganinshi ko matarshi bata isa yabitaba ballantana ita yar bariki , Victoria ga balain tsoron Al’amin take sosai saikace ubanta , Zayyad ma yana Neman mata sosai kuma hausawa hakama faisal Duk kanwa jace ,shiyasa abotarsu tayi daidai ,

 

Baba musa (sarkin kano) ƙanin Alhaji Su’ad ne baitaba haihuwar ɗa namiji ba shiyasa yake kiran AL’AMIN da Prince

 

Shikuwa Al’amin shima kaman ubansa idan akwai abinda yatsana baiwuce Akirashi da Prince ba Saboda kwatata ba tsarin sarauta a plan ɗinshi , Gashi kuma duk families din ba ‘da namiji saishi kaɗai, Hajiya zabbau Amaryar dad ɗin Al’amin itama ‘yaya mata take ta Haifa harsu hudu Allah baibata namijin data keso ba wannan yasaka mata tsanar Al’amin da mom ɗinsa a zuciyar ta ,Sosai ,

 

Wannan kenan kadan daga cikin tarihin wannan families ɗin

 

CIGABAN LABARI

 

Al’amin yashiga tunanin maganar Alhaji Dan Asabe na wai zaibashi suhaila , Yarinyar da kokaɗan bata cikin tsarin matar dayake mafarkin mallaka Sai dai kuma bazai mishi musu ba ,

 

Turkashi

 

Washagari da safe bayan angama break fast Suna zaune afalo gaba ɗayansu mutan gidan sakamakon yau asabar daddy baya fita Al’amin kuma sai bayan la’asar yake fita hospital ranar week end,

 

Kaman daga sama sukaji karar jiniya Dad yayi murmushi yace” brother akwai zuwan bazata”

 

Al’amin yace “kaman daddy King ko”? Dad yayi murmushi yace ” Kafada sunan nan agabanshi, Baruwana kasan halinsa”

 

Mom tace aifa kasan shi ai kartasan dariya sukayi Dama akidarku ɗaya Al’amin yayi murmushi batare dayace komaiba ,

 

Memartaba Alhaji musa ne yayi sallama afalon yayan nasa , Alhaji Su’ad yatashi yace haba brother Aida ka aika saina zoma , “ai Allah yabaka tunda kai ke mulkanmu ,” Memartaba yayi murmushi yace “yaya kenan baka raboda tsokana” Al’amin yatashi yace” Welcome daddy ”

 

Memartaba yakai kallonshi kan Al’amin yace “common my Prince zo gurin daddy mana , Al’amin yayi murmushi yakarasa ga Memartaba ya rungumeshi yace ” ya naka aikin”? yace” Alhamdullilah dad ”

 

Yace “masha Allah adage da taimakon jama’a ,” Mom din Al’amin tace” su yallaɓai hankali yakoma kan ɗa , Ba a ma ganin kowa afalon sai shi kaɗai ” Murmushi yayi yace Kinga lefin uba Dan baiga mutane a falon saboda ɗansa yafaɗa yana dariya ” Daddyn Al’amin yace” faɗa mata dai”

 

Murmushi mom tayi Dan yadda kanin mijin nata yake nuna kulawarshi akan Ɗan tilon Ɗan nata abin yana mata dad’i sosai. Kiran Al’amin akayi awaya yasa yafita afalon , Memartaba yanemi guri yazauna yace “Yaya magana nazo muyi akan Prince”

 

“Bazai yiwu asamishi ido haka ba ba aure Bayan ba abinda yake nema a rayuwa bai samu ba yanzu yana cikin 37 years kenan a lissafina” Saboda haka nayanke shawarar haɗashi aure da yar uwarsa Aymana , Dad da mom suka kalli juna . “Wannan hukuncin dana yanke ne shine nazo nafada maka inji naku ra’ayin akan hakan” , Dad din Al’amin yayi gyaran murya yace “haba brother har akwai hukuncin da zakayanke akan al’amin yazama baiminba”? “ai Al’amin ɗankane Dan haka kasawa ranka aure kaman anyi angama Wannan kuma shine tuwo na maina yakalli mom din Al’amin yace” koba hakaba”? , “Itama cike da jindadi tace “hakan ma yayi kyau”

 

Dad ɗin Al’amin yace” amma wani hanzari ba guduba”, Nan yakwashe yadda sukayi da Abokinshi Alhaji Dan asabe yasanar da ,Memartaba

 

Murmushi memartaba yayi yace “wannan ai bawani abin damuwa bane tunda daman ai shi mijin mace huɗu ne “Wannan bakomai bane sai a aura mishi duka” , Mom tace “a ai gatan saiya mishi yawa , “ina lefin afara da ɗayar tukun na , idan ya iya rike ta sai akara mishi ,” takarasa tana dariya , Sosai maganarta yabasu dariya memartaba yace” wayafada miki Prince rogon namijine ai ko hudu akabashi a rana daya zai rike ballantana biyu” Dad din Al’amin yace” kai dai kana bin bayan ɗanka kawai” ,Sukayi dariya gabaɗayan su Mum ce ta kalli kofar falon taga Al’amin yayi mutuwar tseye Duk suka maida kallonsu gareshi ,

 

Tofa jama’a yanzu akafara wasan

 

Kubiyoni

Leave a Comment

error: Content is protected !!