Hausa Novels

Alamomin Shafar Aljannu

Alamomin Shafar Aljannu

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

ALAMOMIN SHAFAR ALJANU

********

Yadda zaka gane cewa Aljanu sun shafeka, ko kuma sun shafi waninka.

 

Duk wanda yake biye da ZAUREN FIQHU zai ga wani lokacin muna yin zurfafan bayanai game da lamarin Shaitanun Aljanu masu shiga jikin Bil Adama, har wasu suna ganin kamar ba haka bane.

 

Amma daliban ZAUREN FIQHU na whatsapp sun sha saurarar Audio na wasu rukiyyoyin da aka gabatar anan..

 

Yau kuma in sha Allahu zaku ji bayanin alamomin da ake gane shafar Aljanu ajikin mutum.

 

Wadannan alamomin sun kasu zuwa gida biyu. Akwai na fili, akwai kuma wadanda bassu faruwa sai alokacin barci.

 

ALAMOMIN ‘BOYE:

****

1. Bushewar idanu : Zaka ga mutum ya kwanta akan shimfidarsa amma barcin ba zai zo masa ba, sai Chan tsakiyar dare ko kuma wajen Asubah.

 

2. Yawan farkawa daga barci A FIRGICE!! . Wani zaka ga kusan duk minti talatin sai ya farka, ko Qasa da haka.

 

3. DANNAU: Mutum yana kwance zai ji wani BAQIN ALJANI yazo ya danneshi. Zai yi ta EEHU!!. Amma babu mai jinsa.. Wani lokacin wasu sunfi yinsa da safe bayan sallar asubah.

 

4. MAFARKAI MASU FIRGITARWA: Kamar kayi mafarkin an biyoka za’a yanka ka, ko kuma mafarkin fadowa daga wani tsauni, ko kuma kaga hallaka Qarara, idan ka farka zaka ji jikinka duk zuffa!.

 

5. MAFARKIN NAMUN DAJI : Ganin miyagun dabbobi amafarki kamar macizai, Karnuka, Kyanwa, Rakumi mai fada, Damusa, Saniya, ‘Bera, suna bin mutum zasu kamashi. etc.

 

6. Tauna acikin Barci. (kaji mutum yana barci amma yana taune-taune).

 

7. Dariya ko Kuka, ko Eehu acikin barci.

 

8. Kaga mutum yana barci amma ya tashi tsaye yayi tafiya, sannan ya dawo ya kwanta alhali ko farkawa bai yi ba.

 

9. Mafarkin afkawa cikin ruwa, ko Jini, ko wani mummunan rami.

 

10. Mafarkin Matattu, ko ganinka a MAQABARTA, ko wajen yanka dabbobi, ko kwata, ko Juji, ko tsakiyar Daji mai duhu.

 

11. Mafarkin Gajerun Mutane, ko dogaye tsola-tsola. Ko farare Sol, ko bakake WULUK, masu ban-tsoro.

 

12. Mace ta rika yin Mafarkin wani namiji yana zuwa yana saduwa da ita, bisa siffar Mijinta, ko saurayinta, ko mahaifinta, ko dan uwanta, etc.

 

13. Namiji ya rika mafarkin wadansu mata suna zuwa masa suna kwanciya dashi.

 

14. Mace ta rika mafarkin haihuwa ko ta rika ganin jarirai ana kawo mata tana shayar dasu amafarki.

 

ALAMOMI NA FILI

*******

1. CIWON KAI : Marar jin magani. Ko an sha magani ba zai dena ba. Kuma gobe ko jibi ma sai ya dawo.

 

2. FADUWAR GABA : Kaji Qirjinka yana bugawa FAT! FAT!! FAT!!! (kamar zai fashe).

 

3. JUYARWA daga bin Allah ko duk wani abinda ya shafi addini kamar Zikirin Allah, karatun Alqur’ani, da sauran abinda Allah yake so, kai kuma sai kaji baka so.

 

4. BAQIN CIKI : Haka kawai babu wani dalili sai kaji ranka yana ta baci, kana jin haushin kowa da kowa ba tare da wani dalili ba.

 

5. RIKICEWAR TUNANI: Kaji kamar komai ya chabe maka. Ka rasa yadda zakayi.

 

6. Rashin lafiyar wata ga’ba. Amma likitocin zamani sun gama bincike sun kasa ganowa ko magance chutar.

 

7. Rikicewar Jinin haila. Rashin zuwansa akan lokaci ko kuma zuwansa fiye da kima.

 

8. Yawan zubewar Juna-biyu. Ko kuma rashin samunsa kwata-kwata.

 

9. Jin kamar tafiyar kiyashi ajikinka ko yaushe.

 

10. Jin maganganu masu tsoratarwa ba tare da kaga mai maganar ba.

 

11. Jin tsananin sha’awar aikata sabon Allah. Kaji kamar ana ingizaka.

 

12. Yawan mantuwar karatu, ko rashin fahimtarsa. Wato toshewar basira, alhali da chan ba haka kake ba.

 

13. Yawan jin waswasi ko kokonto ayayin tsarki ko alwala ko Sallah.

 

14. Yawan Kuka ko dariya ba tare da wani dalili ba.

 

15. Jin Kasala mai tsanani tare da nauyin jiki yayin Sallar farillah ko karatun Alqur’ani mai girma.

 

16. Tsoron shiga cikin jama’a, ka rika jin kamar zasu hallaka ka, alhali kuma ba haka bane.

 

17. Idan kina tafiya ki rika jin kamar wani yana binki a baya.

 

18. Yawan Qiyayyar juna atsakanin ma’aurata. Idan mijinki baya nan kiji kina mutukar sonsa. Amma da zarar ya dawo sai ki rika ganinsa kamar dodo, ki rika jin baki son ganinsa ko jin maganarsa.

Leave a Comment

error: Content is protected !!