Alhakin So Hausa Novel Complete
ALHAKIN SO
Page 1
Ina tsoron alhaki,ina mamakin wanda ba su d’aukeshi a bakin komai ba,wasu ba su san shiga hakin wani zai iya targad’a rayuwarsu ba.Wasu da dama suna gudanar da lamuransu ba tare da tunanin yanda za su riski gobensu ba. Allah ka mana tsari da shiga hakkin wani,ko da kuwa akan So ne.
Ba zallar soyayyar bane a ciki,har da k’addarori kala-kala,wanda nake fatan su ilimitar in sha Allah!
“Hasanata”
Ya kira sunanta cikin wani irin yanayi da ya saba ji idan ya na tare da ita,ya san ba za ta amsa ba,don kuwa tunda ta fito k’ofar gidan ta juya masa k’eya,ko kallonsa ta k’i yi.
“Fushi kike yi da ni ko?” Ya tambayeta, ya na lek’a fuskarta.
Nan ma dai ba ta juyo ba bare ta ba shi amsa.
Ya ce”wai ni ne ba kya so, ko auren?”
Ba tare da ta juyo ba ta ce”ka fi d’an dako sanin hanya,kai ne ba na so Yaya Abdul,na rasa yanda zan yi da kai,wallahi idan na ganka haushi nake ji sosai,kar ka sa ran zan so ka ko ka aureni,kuma idan ka aureni yanzu ka cuceni wallahi,ni ba zan yafe maka ba”.
Sai ta fara kuka sosai,ta saka hijjabin jikinta ta rufe fuskarta,tana ta yi.
Da k’arfi zuciyarsa ta fara bugu,wani abu ya zo ya tsaya masa a k’irjinsa, ya lumshe ido ya bud’e, ya na jin babu dad’i har cikin ransa,ya zai yi da rayuwarsa shi ma? Da ace shi ya sakawa kansa son yarinyar da tuni ya cire ya huta,ya na yi mata wani kalar so ba d’an kad’an ba,har ya na jin idan bai aureta ba ba zai sake samun wani farincikin rayuwa ba,kullum sonta k’ara samun wurin zama yake yi a zuciyarsa, duk kuwa da k’iyayyar da take nuna masa k’arara.
Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan
“Subhanallah!Don Allah ki fad’a min ta inda na tawaya,ki sanar da ni abubuwan da ya sa ba kya so na, ni kuma in har Ina da dama zan san yanda zan yi na gyara don ki so ni, ni wallahi ba zan jure rashinki ba”.
Ta tsagaita da kukan ta bud’e fuskarta,wannan karon ta juyo ta na kallonsa sannan ta fara magana
“Kai ka sanar da ni abin da ya sa kake so na,bayan na fad’a maka ni ba na sonka”.
Ya d’an cije leb’e ya na kallonta,tsananin burgeshi take yi,idan ya na kusa da ita numfashinsa har sark’ewa yake yi
Ya yi murmushin k’arfin hali ya ce” ni Allah ne ya dasa min k’aunarki a zuciyata tun kina y’ar yarinya,kuma komai naki burgeni yake yi.Kin ji nawa,ni ma sai ki fad’a min dalilin k’iyayyarki”.
Ta galla masa harara ta ce”ai kamar mu d’aya da Husaina,komai namu ma iri d’aya ne,me ya sa ba ka sota ba sai ni?”
Ya yi dariya ya ce”komai na ku ba iri d’aya bane a wurina,ke kin samu wani babban matsayi a fadar zuciyata, ita kuma matsayin y’an’uwantaka ne kawai ta samu a wurina.Kuma ba halinku d’aya ba,ke kin fi ta komai,kuma ni halinki burgeni yake”.
Ya kai k’arshen maganar ya na yi mata kyakkyawan murmushi,tsananin so da k’auna k’arara a idonsa wanda har kawo ruwa suke,idan kalar firar nan ta shiga tsakaninsu.
Takaici duk ya rufeta,ta sake had’e rai ta ce”ni ko matsayin y’an’uwantakar ya kusa b’acewa a idona,na kusa cireka a jerin y’an’uwana,saboda ba na k’aunarka”.
Yanzun ma murmushin ya yi ya ce”ki cigaba da yi min rashin kunya,sai na saka an dawo da auren nan sati me zuwa,na ga yanda za ki yi”. Ya k’arashe maganar cikin son janta da wasa
Sai ta juya kawai za ta shiga gida.
Da sauri ya ce”ki na shiga zan biyo bayanki,na fad’awa Mama yau rashin kunya kika yi min”.
Ba ta ko saurareshi ba,don ta san ba zai iya kai k’ararta ba,ta shige gidan ta bar shi tsaye ya na murmushi.
Sai da ya ga shigarta gida sannan ya tada babur d’insa ya bar k’ofar gidan.
Sai da ta tsaya a zauren gidan ta saita kanta,kafin ta shiga da sallama.A tsakar gidan ta tadda Mama da Husaina zaune akan tabarma suna shan iska
Babu wanda ta yiwa magana,ta shige d’aki ta kwanta. Babu jimawa Husaina ta bita d’akin, gefen katifar da take kwance ta zauna,cikin damuwa da lamarin y’ar’uwarta ta ce” Hasana lafiya kuwa? Ko yau ma fad’an kuka yi?”
Hasana ta juya mata baya, ba tare da ta amsa ba.
Ta sake cewa”ni kam ban ga abun k’i a jikin Yaya Abdul’aziz ba,amma duk kin d’auki karan tsana kin d’ora masa…”
Kafin ta k’arasa,Hasana ta tashi zaune a fusace ta ce”to ki ce ya dawo kanki mana! Tunda ke yayi miki ai sai ki aureshi kawai”.
Husaina ta yi murmushi ta ce”ni ba manufata ba kenan,kuma ai ya san da ni ya ce sai ke.Allah dai ya rufa asiri”.
Ta tashi ta bar mata d’akin,ta na ayyana abubuwa da dama a zuciyarta.
Ita kuma kamar jiran fitarta take yi,sai ta cusa kanta a cikin filo ta fashe da kuka sosai,wani irin k’una take ji a zuciyarta,ta rasa wanda za ta fad’awa dalilin da ya sa ta ce ba za ta auri Yaya Abdul ba,kowa ya k’i ya nutsu yayi hasashe akan lamarin,sun zama makafi,sun zaka kurame,su na k’ok’arin tursasata ta yi abin da za a ji kunya da tsanarsu daga k’arshe.Babu me jin ra’ayinta,su farincikin Abdul kawai suke so,ita ko ta mutu babu wanda ya damu. A yanzu za su ba shi farinciki,amma gaba kad’an ta na da tabbacin shi zai fi kowa kasancewa a k’unci,ta san dole zai yi nadama da da-na-sani,idan abin da suke ta b’oyewa ya fito fili,ta na ji a jikinta a ranar za ta zab’i mutuwarta a maimakon rayuwa.
Kuma ta na ji a jikinta a ranar zai tsaneta tsana ta har abada,shi ya sa tun yanzu take so ya yi nesa da ita kafin me afkuwa ta afku,amma da yake shi kansa ba ya ja,ya kasa ganewa,ya mayar da kanshi dolo,kuma dak’ik’i. Kamar yanda d’an’uwansa ya mayar da ita dak’ik’iya a shekarun baya.
******
Tsaf ta fito cikin shirinta na doguwar riga da hijjabinta har k’asa,matashiyar buduruwa y’ar kimanin shekaru ashirin da biyu,ta kai duba ga mahaifiyarta da ke hada-hadar d’ora girkin dare,ta ce”Umma na tafi”.
Daga y’ar rumfar da take ta ce”Sumayya kar ki yarda ki kai magriba,ni ba dan kin shirya ba ma ai da bari kika yi sai gobe,yamma ta yi”.
Ta ce”Umma ba jimawa zan yi ba Allah”.
Ta ce”a dawo lafiya, Allah ya tsare”.
Ta amsa da amin, ta na ficewa daga gidan,idan ka kalli fuskarta za ka ga damuwa k’arara,don a cikin zuciyarta ba ta son fitar, don dai ya zama dole ne
Sai da ta d’an yi nisa da gidan sannan ta ciro wayarta a jaka,ta yi d’an danne-danne ta kara a kunne
“Na fito” Ta fad’a bayan an amsa kiran da tayi,sannan ta ce ok ta katse kiran ta mai da wayar jakarta,ta cigaba da tafiya.
Ta na isa bakin titi,ta doshi wata bak’ar mota,ta bud’e ta shige gabanta ya na fad’uwa,don ta na fargabar wani ya ganta.
“Hmmm!” Ta sauke ajiyar zuciya,bayan ya ja motar sun fara tafiya.
Khalid ya yi murmushi ya na wani lumshe ido ya ce”matsoraciya”.
Idonta ya ciko da k’walla,kamar za ta yi kuka ta ce”Allah na fara gajiya da wannan rayuwar,don Allah ka aureni mu huta,ni fa ina fargabar ranar da asirinmu zai tonu”.
Ya jinjina kai,ya ce”saura kad’an,ki k’ara hak’uri don Allah kin ji Sumayyata,komai ya kusa zuwa k’arshe”.
Ta ce”don Allah wannan ya zama na k’arshe, sai kuma idan mun yi aure ka ji?” Ta kai k’arshen maganar ta na rausayar da kai,wai ko zai tausaya mata.
Sai kuwa ya b’ata rai,ya nemi gefen titi ya faka motar ya ce”fita”.
Ta kalle shi cikin kid’ima ta ce”saboda me?”
Ba tare da ya kallleta ba ya ce”ki fita na ce,ba na buk’ata”
A sanyaye yayi maganar,shi ya sa ba ta tantance a wani yanayi yake ba
Don haka murya na rawa ta ce”amma ba fushi kayi ba ko Yayana?”
A tsawace ya ce”fushi nayi,kuma babu ni babu ke har abada!”
K’irjinta ya shiga bugu,idan da Kalmar da ta fi tsana ita ce ta rabuwa da Khalid,saboda idan ba shi ta aura ba ta san ta na cikin matsala,tunda ta riga ta ba shi kanta sau babu adadi,don haka take taka-tsantsan da b’acin ransa,kuma take yi masa duk abin da yake so,a k’ok’arinta na lallab’ashi ayi auren,don gudun tonon asirinta.
“Don Allah ka yi hak’uri, ni fa ba da wata manufar na fad’a ba”. Ta yi maganar da murmushi, ta na son mai da abun wasa.
Ya yi mata wata kafirar harara kafin ya ce” idan kin ga da takura fa babu dole,tsaf zan k’ara gaba,ai babu dole a lamarin,idan kin ga na buk’aceki sai kin san yanda kika yi kika b’ata min rai ko? Idan ban da k’addara ma ta shiga tsakaninmu ni me zan yi da y’ar talakawa irinki?”
Ita dai ta yi shiru ba ta sake magana ba,duk da maganganunsa sun yi mata zafi.
Da haka suka k’arasa gidanshi da suka saba zuwa su aikata masha’arsu,ba tare da sanin wani nasu ba.
Sai bayan sallar isha’i,ya dawo da ita gida,k’irjinta sai bugu yake,ta na jin ranta a jagule,kamar ta fi kowa shiga tsananin rayuwa. Kud’in da ya mik’o mata ta saka a jakarta ta fito daga motar.Ko ta kan sallamar da yake yi mata ba ta bi ba,ta wuce ta na waige-waigen unguwar tasu
A sanyaye ta yi sallama ta shiga gidan,Umma ta amsa ta na shirin shiga d’aki ta ce”sai yanzu ko?”
Ta ce”ban samu abun hawa bane a k’afa na dawo”.
Umma ta ce”to ya jikin nata?”
Ta ce”da sauki”.
Ta shige d’aki,kai tsaye kwanciya tayi rigingine,hawaye su ka ce salamu alaiki. Ita kanta ta na jin tsanar kanta a cikin zuciyarta,ta na mamakin dalilin da zai sa Khalid ya k’i aurenta har kawo iyanzu,ta na fargabar tonuwar asirinta kafin ayi auren,don ta na da tabbacin iyayenta ba za su yafe mata ba.
Sai da ta ji Umma ta k’walla mata kira,sannan ta tashi firgigit,ta zuge jakarta ta fito da kud’in da ya bata,dubu biyar ne cif,ta je wurin tsohuwar akwatinta,ta d’aga k’asan kayanta ta had’esu da sauran kud’in dake ajiye a wurin,har zuwa lokacin ba ta daina wahaye ba.
********
Wani matashi ne,zaune a madaidaicin falo,waya rik’e a hannunsa,a zahiri wayar yake kallo,amma a bad’ini hankalinsa sam ba ya kan wayar,tunanin yanda zai yi ya samu dubu goma kafin dare kawai yake yi,ko yanzu kiranta ne ya sa shi d’aukar wayar,amma ya kasa bin kiran,don bai san amsar da zai ba ta ba
Ya na matuk’ar son Zainab,amma ita Allah ya yo ta me masifar kwad’ayi da son kud’i,ita kuma ba y’ar kowa ba. Babbar damuwarsa ma bai ga d’ugon son shi a idanunta ba,muddin ya ga ta na kwantar masa da kai to ya san kwanan zancen, duk kuwa ranar da ta kalle shi ta fad’a masa kalmar ‘I love you’ to nan take wani ciwon kai yake rufto masa,don kuwa ya san tabbas ba zai bar gidan ba,sai ta tambaye shi wani kud’i,ko kuma ya siya mata abu me tsada.
Shi d’in ba wani me k’arfi bane,adaidaita sahu yake ja shi ne sana’arsa,amma a hakan yana iya k’ok’arinsa na ganin ya faranta mata,ya na yi mata hidima ko da shi zai kwana ya wuni da yunwa.
K’arar shigowar sak’o ta wayar ne ya sa shi firgita,ya kalli wayar da sauri. Ita d’in ce dai kamar yanda yayi zato
_’Lallai ma Abdallah! Ina ta kiranka ko? Ni da ma kati za ka turo min na d’ari biyar,ba wata uwar za ka yi min ba’_.
Da sauri ya saki ajiyar zuciya bayan ya gama karanta sak’on,cikin farinciki yayi mata replay da fad’in
_Yi hak’uri sarauniyar mata,ba na kusa da wayar ne,wane ni da share matata? Matsayina bai kai nan ba.An gama,yanzu zan turo miki’_.
“Wajibina ne na tura miki ai” Ya fad’a a fili
“Me za ka tura?” Mahaifiyarsa ta fad’a,ta na k’arasowa inda yake.
Ya sosa kai ya na murmushi ya ce”uhm,wasu hotuna ne”.
“Allah ya baka sa’a” Ta fad’a ta na zama,don ba ta yarda da shi ba
Da d’ari bakwai ya tashi yau d’in, don haka ya d’auki d’ari biyu ya bata,sauran kuma na siyan kati ne.Ciki kuma ko oho!
Ya na fita daga gidan ya tura mata, babu jimawa sai ga wani sak’on nata ya shigo,yayi zaton ma za ta ce ya shiga ne,ko kuma tayi masa godiya,sai ya ga tuni ne take yi masa kan dubu goman da ta tambaye shi jiya
Ya had’iyi wani yawu,ya shiga adaidaita ya ja, da bismillah ya hau aikinsa.
*Labarin nan me b’angare uku ne,da b’angaren Hasana da me sonta yayanta Abdul*
*Da b’angaren Sumayya,da wanda take so Khalid*
*Sai kuma b’angaren Abdallah me adaidaita sahu na Zainab me son kud’i*
*Ina fatan za ku bi ni,don jin sak’onnin da nake son isarwa*
08028966015
Leave a Comment