Aljanar Gidan Mu Hausa Novel Complete
Aljanar Gidan Mu Hausa Novel Complete
Daga Alƙalamin
_Sarat Alƙasum(Maman Nusaiba)_
JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION
Daga marubuciyar:
Amir da Amira.
Aljanar Jarumai.
Hafsat.
Ƙaddara ce.
Tani da Manu.
Rayuwar ma’aurata.
Sumayya baiwar Allah.
Abba ne.
And new book.
Aljanar gidanmu.
Ya Ubangiji yadda ka bani damar ɗaura Alƙalamina ka kuma bani dama da ikon sarrafa tunanina da baiwar da ka mini, ina addu’a ka bani ikon ɗauke shi lafiya, ya rabbi ka bani ikon rubuta abin da zai amfani Al’ummar Annabi Muhammad (S.a.w) Habibi ɗan gatan Allah shugaban duniya da ƙiyama. Allah ka ƙara mana lafiya da wadatar zuci ka hanemu ga aikata saɓo….
*WhatsApp number +966599791573*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
0️⃣1️⃣
Tsaye take a gefen babban titi tana rusar kuka, gefenta wata tsohuwa ce kwance tana rawar sanyi bakinta na haɗewa da labbanta saboda yadda jikin nata yake rawa sosai. Juyowa yarinyar ta yi za ta yi magana sai ta fasa ta mayar da hankalinta ga wata mota da take mata oda, tsayuwa ta yi tana Ƙifƙifta idanu tana jiran taga wanda zai fito daga motar…
Babbar motar ce fara sol ta yi parking a gaf da ita, direban dake a set ɗinta ya buɗe murfin motar ya fito fuskar shi na nuna fushi, yana zuwa bai tsaya yin komai ba ya kife yarinyar da mari ya kuma ƙara mata wani a ɗayan kuncin..
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza uku Hausa Novel
-
Doctor Eshaat Hausa Novel
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi Hausa Novel
-
Aure da haihuwa Hausa Novel
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya Hausa Novel
-
Gangar Shedan Hausa Novel
-
Angon mata biyu Hausa Novel
-
A gidan mu take Hausa Novel
-
Bafulatanar Rugga Hausa Novel
-
Matar yaro Hausa Novel
-
Mr Bello Hausa Novel
-
Mijin Buzuwa Hausa Novels
-
Gidan Uncle Complete Hausa Novel
-
Yar aiki return Hausa Novel
-
Raggon namiji Hausa Novel
-
Uncle Datti Jikina yake so Hausa Novel
-
Fataucin Mata Hausa Novel
-
Juhud Hausa Novels Complete
-
Moon Hausa Novels Pdf
-
Yarima Ashman Hausa Novel
-
Bandirawo Hausa Novel
-
Matar makaho Hausa Novel
Powered by: www.mynovels.com.ng
“Ke uban wa ya ce ki zo kan hanya ki tsaya? Dan uwarki ana magana kin wani tsare da manyan idanunki kamar wata maiya, to ki shiga hankalinki so kike ki ɓata mini suna a gari na ƙare rayuwata a gidan yari ko me?”
Shuru yarinyar ta yi ta zuba masa idanunta wanda ya ciko tam da kwalla, sosai taji zafin marin da ya mata hakan ya sa hawayen idanunta suka shiga zubowa jikinta nawa, da sauri ta sunkuyar da kanta tana goge kwallar data zubo mata tare da lumshe idanun nata, sai da ta jima kafin ta ɗago kai za ta yi magana taga ana ƙoƙarin buɗe motar daga set ɗin baya ta yi shuru tana kallon ƙofar..
Wani babban mutum ne ya fito tare da wata ƴar yarinya mai kimanin shekaru 13 tana riƙe da ƴar Teddynta, idanunta ne ya sauka akan yarinyar da taga an mara ta yi saurin sakin hannun mahafinta ta isa gurin yarinyar ta tsaya, a sanyaye takai hannu ta shafa gefen fuskarta da shatin yatsun direbansu yake kwanta tar.. “Ki yi haƙuri zan rama miki marin da ya miki kinji.” Yarinyar ta faɗa ta ƙara da cewa” Ya sunanki?”
Ajiyar zuciya yarinyar ta sauke ta buɗe idanunta akanta sannan ta ce” Na gode sunana Amra.”
Murmushi Yarinyar ta yi ta kamo hannun Amra da yake ɓace da taɓo ga dauɗa data kwanta amma bata ji kyamarta ba ta riƙe hannun nata tana shafawa ta ce” Sunanki mai daɗi ni kuma sunana Afra amma ana ce mini Auta dan ni ce Auta a gidanmu, kuma z.. Bata ƙarasa maganar da take son yi ba mahaifin nata ya iso gurin tare da fisge hannun Auta daga na Amra ya ce” Auta me ya sa bakya ji ne? Yanzu wannan ƙazamar yarinyar kike taɓawa ko ba ki ga yadda take da datti ba? Kalle ta fa sai wari take.”
Amra ta kawar da kanta gefe ta durƙusa a gaban shi ta ce” Ranka ya daɗe ka taimaka mana kaga Mamata can a kwance bata da lafiya bamu da gurin kwana ko abinci da ƙyar muke samu muci, ka taimaka mana na kaita Asibiti” Ta faɗa tana riƙe ƙafafunsa.”
Cikin azama ya buge ta ta yi baya ta faɗi. “Ƴar matsiyata ni za ki taɓawa jiki ɗan uwarki kinga na miki kama da matsiyatan mutane irin ki? To ba zan taimaka ba ɗin ko an faɗa miki kuɗin a banza nake samun su da zan ke yiwa kowa hidima kamar ban san ciwon kaina ba? Ke kuma ki fice mu tafi gida” Ya faɗa yana damƙar hannun Auta da ta yi tsaye baki buɗe tana kallon Mahaifin nata..”
“Waiyo Allah! Daddy don girman Allah ka taimaka mata kalli fa yadda Mamanta ke rawar sanyi, haba Daddy me ya sa ba za ka taimaka mata ba kuma har kake dukanta? Ni dai ka barni na tashe ta sai mu tafi” Auta ta faɗa tana mintsinin hannun Daddy da yake ƙoƙarin janyeta daga gurin..
“Ke ba ki da hankali za ki taɓa jikinta? Wannan fa tsami take ki rabu da ita mu tafi gida” Cewar Daddy yana ƙoƙarin janta.. Fir Auta ta kafe ta ce ba fa inda za taje sai ta tashi Amra dake ƙasa a yashe, haushi ne ya kama Daddy ya ɗauke cak ya sata a cikin mota yana ta masifa. Da sauri Auta ta buɗe schoolbag ɗinta ta fito da biskota gida uku da kuɗi ta dubi Daddy ta ce” To ka bari na bata wannan tun da ba za ka taimaketa ba.” Dafe kai Daddy ya yi bai kuma ce mata komai, ganin haka ya sa Auta ta balle murfin motar ta fito da gudu-gudu ta iso inda ta bar Amra zuwa lokacin ta tashi tana kusa da Mamanta tana rusar kuka. “Amra! Ta kira sunanta da ɗan ƙarfi ganin hankalinta baya inda take. Juyowa ta yi tana kallon Auta bata amsa ba sai binta da kallo da take.. Murmishi Auta ta yi ta miƙa mata kayan hannunta ta ce” Ki yi haƙuri da abin da suka miki Amra Allah zai saka miki ga wannan kici wannan kuɗin kuma ki kai Maman naki Asibiti kinji” Ta faɗa da muryar tausayi.”
Itama Amra murmishin ta yi ta miƙa hannu ta amsa sannan ta ce” Na gode Auta kina da kirki ba zan manta dake ba a rayuwata.” Jinjina kai Auta ta yi ta ciro zoben dake hannunta mai kyau ta kalli Amra ta ce” Bani hannunki nasa miki zobe ina so ki za ma Ƙawata.” Ba muso ta miƙa mata hannunta wanda ƙuraje ƙanana suka fito a yatsotsin nata wasu har sun yi ruwa kuɗa nata bin hannun. Cikin tausayawa Auta ta kalli hannun ta ce” To ki riƙe karki saka tun da naga ƙuraje sun fito miki ki sayi magani kisha sai su mutum zan ke sawa direba ya biyo nan dani dan nake ganinki.” Jinjina kai Amra ta yi tana zubar da hawaye da ƙyar ta ce” Na gode Ƙawata.” Ba komai Auta ta ce kana ta miƙe ta mata bye bye sannan ta koma cikin motar direba yaja suka bar gurin….
Sai da taga tafiyar su sannan ta miƙe da ƙyar tana dafe kwankwasonta da yake mata zafi. “Wash Inna ƙila ƙashin kwankwasona ya karye” Ta faɗa tana buɗe kwalin buskotar..
Ɗago da kan Inna ta yi tana jera mata sannu ta tashe ta, kafaɗarta ta shiga ta taimaka mata ta miƙe. Napep ta tsayar ta ce masa ya kaisu kyamis mafi kusa, kallon Amra mai Napep ɗin ya yi yana done hanci, tsaki yaja yana ce mata taya zai dauketa tana tsami salon ta kashe masa kasuwar shi ga mota da mutane biyu.. Kuka Amra tasa ta durƙusa ta ce” Ka taimaka ka kaimu kaga Innata bata da lafiya magani zan sayo mana ko nawa kake so zan baka ina da kuɗi.”
Wani kallo ya kwatsa mata ya yi gaba abin shi..
Kuka sosai take tana riƙe da Inna sai neman faɗuwa suke, sai da ta gaji da tsayuwa sannan ta samu wani ya daukesu ya kaisu kyamis….
Tun da suka bar gurin Auta ta murtuke fuska tana kumbura baki, shi ko Daddy ko a jikin shi sai ma faɗa da yake mata akan biskotanta da ta bai wa Amra….
Suna zuwa gida Auta ta fito a guje ta nufi ciki tana kuka..
Kicibus ta yi da Fadila da ƙawayenta biyu sunsha kwalliya suna wani ɗage kai..
“Ke dalla can jaka daga gidan uban wa kike yanzu?
Auta ta tsayar da kukan da take ta ɗago kai tana saba baki ta ce” Anty Daddy ne.”
“Kuma dan Daddy ne ya sakaki kuka sai ki shigo mana afujajan kamar wadda ta gudo daga Dawanau? Nifa kin sani bana son iskanci za ki wuce ko saina bangajeki daga hanyar? Ta faɗa tana nuna mata hanya..
Wani kukan Auta ta kuma sakawa tana sakin schoolbag ɗinta a ƙasa ta kuma ƙarawa kukanta sauti.. Tass tass ƙaran marin ya daki dodon kunnen Direba da yake ƙoƙarin shugowa da ƴar Teddyn Auta. Waro idanu ya yi yana ja da baya jikin shi na rawa..
“Kai kuma munafiki uban me ka shigo yi cikin palonmu? Cewar Fadila tana jefa masa gorar ruwan da tasha rabi ta bar rabi..
Kuka Auta ta Ƙwalla tana riƙe kuncinta cikin jin zafin marin ta sunkuya ta ɗauki schoolbag ɗinta tare da nufar hanyar cikin palon, har ta kusa kaiwa palo ta dawo ta isa gurin direba ta amshi ƴar Teddynta, kallon Fadila ta yi ta ce” Muguwa azzaluma Allah ya isa ban yafe miki sai na faɗawa Daddy” Tana faɗin haka ta kwasa a guje ta shiga ciki.”
Kanbu! Ni ki ka cewa muguwa? Zan dawo na haɗu dake yau zan ga mai rabamu dake a gidan nan, ba dai Mommy bata nan ba zan yi maganinki” Cewar Fadila tana girgiza jiki ta yi gaba suka bi bayanta.. Tana zuwa saitin mai gadi ta ce” Kai kuma Ɗanladi sai na sa Daddy ya koreka daga aiki tun da in na ce ka wanke mini mota ba za ka yi ba ko?
Haƙuri ya shiga bata amma taki ko kallon shi ta shige mota ita da ƙawayenta, kiɗa suka konna kana taja suka bar gidan a guje kamar za su tashi sama…
Misalin ƙarfe 11pm na dare Daddy na zau ne yana duba wata jarida, Fadila dake gefe ta kunna kallo ta kawo MBC2 tana kallon wani American film ana ta nuno wasu masoya suna rungume da juna, Auta dake kan stamp ta rafka tagumi tana kallonsu…
Da fito ya sanyo kai cikin palon, shi kuma na bayan shi ya shigo yana waka da turanci kiɗa na tashi a cikin wayarsa..
“Oh my god! Daddy yaushe ka shigo gari ne ba ka faɗa mana ba?” Cewar Sudas yana miƙawa Daddy hannu.
Dariya Daddy ya yi ya ce” My Son’s ai dama surprise na muku daga ina haka?”
Wani juyi Sauban ya yi tare da yin rawa ya iso gaban Daddy ya bashi hannu suka tafa, kallon su Auta ta yi sai kuma ta yi saurin saukowa tana murna ta nufo su. Tana zuwa saitin Fadila tasa ƙafa ta taɗeta ta faɗi tim a ƙasa. Sudas ya yi saurin juyowa ya ce” Kai Auta bi a hankali mana har kina faɗuwa.”
Kallon Fadila Auta ta yi bata ce komai ba ta miƙe ta isa gurin Sudas ya ɗaurata akan cinyar shi ya yi yana shafa guiwar hannunta da take mata zafi…
” Sannu Auta Mommy bata dawo ba?” Cewar Sauban yana danna wayar shi…
Bata cewa kowa komai ba har suka gama surutun su suka rabu da ita…
Miƙewa Fadila ta yi ta wuce ɗakinta, Auta ma ta miƙe ta nufi ɗakinta. Tana hawa kan stap taga ƴar Teddynta tasa hannu ta ɗauketa ta wuce ɗakinta…
Tana shiga ta faɗa kan gado sharar hawaye…
Ƴar Teddynta ta rungume tana ci gaba da kuka har bacci ya kwashe ta..
Bata fi minti goma da soam bacci ta farka, saukowa ta yi daga kan gadon riƙe da ƴar Teddynta ta buɗe ƙofa ta fita..
Ɗakin Fadila ta nufa tana mutsitsika idanu, tana isa ta shiga buga ƙofar da ƙarfi tana faɗin” Anty Fadila ki buɗe mini ƙofa.”
Cikin bacci Fadila taji ƙaran buga ƙofar ta miƙe, a fusace ta nufi ƙofar ranta na tafasa, tana buɗewa ta faɗo ɗakin ta takure a guri ɗaya..
Galala ta saki baki tana kallonta, wani ɓakin ciki ne ya rufe Fadila ta janyo cazar wayarta ta soma tsula mata tana faɗin” Dan uwarki uban me za ki mini a ɗaki ni z.. Bata ƙarasa ba taji an yi caraf da hannunta an zafga mata wani gigitaccen mari wanda ya yi sanadiyar ɗaukewar jinta da ganinta na wani dakikun…
_*Maman Nusaiba ce*_


Name: | [Aljanar Gidan Mu Hausa Novel Complete] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |
Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV
Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi

Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi

Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram

Leave a Comment