Alkalamin Kaddara Hausa Novel
[08/09, 12:31 am] +234 803 192 1625: *AƘALAMIN ƘADDARA…!*
(Zanansa baya gogewa)
True life story
*MALLAKIN*
*_ZAINAB CHUBAƊO_*
DA
*_HAFSAT HAFNAN_*
*_Da sunan Allah mai Rahama maijin ƙai, salati da ɗaukaka su tabbata ga manzon tsira Annabin mu Muhammad(s.a.w) Ya ubangiji yanda muka fara Wannan rubutu lfy Allah Ka bamu ikon saukeshi lfy🤲_*
*_GARGAƊI bamu yarda wani ko wata su sarrafa mana wannan littafi ta kowace fuska ba Ba tareda amincewar mu ba🙅♀️, wannan kasheɗin kan me uwa dawabi ne Especially ɓarayin Youtub Masu cida gumin mutane😡_*
01
*SHIMFIƊA….📜*
___Sanya take cikin Uniform ɗinta na makaramta wanda ya kasance me Launin kalar Ruwan Ƙasa, a hankali take takawa sabida murɗawan da cikinta keyi tana tafe tana cije leɓe sabida azaban ciwon da Maranta ke mata jinda tai ƙafarta na neman riƙewa ne yasa ta jingina da ƙofar wani gida tana sauke numfashin Azaba.
Ta ɗan jima a tsaye gurin sannan tacigaba da tafiya har lokacin bata dena datse bakinta da haƙoranta ba, a daidai wani garage ɗin da ake gyaran motoci ta tsaya tana ƴarfe hannu sabida juyawan da cikinta keyi wani farin mota ta gani a fito da shimfiɗar dake cikin motar an ajiye a ƙasa da alama wanketa za’ayi, da sauri ta nufi gurin tana cizon baki ta ɗauki ɗaya cikin capet ɗin motar ta nufi ƙasan wani bishiya ta ajiye sannan ta zauna don bazata iya tafiya ba kuma.
Juyi ta farayi dataji abin yafi ƙarfinta se kawai ta fashe da kuka Tana Ƴarfe hannu, gabaɗaya litattafan cikin jakarta duk sun baje a ƙasa daga gefanta.
Daga ɗayan ɓangaren kuma Bayan matashin ya gama wanke motar tayi fees da ita se ɗaukar idanu take gwanin shi’awa, sega wasu matasa waƴanda bazasu wuce shekaru 35 ba su biyu sun nufo gurin me wankin motar, da alama dai a cikinsu akwai mamallakin motar
daga yanayin tafiyarsu kaɗai zaka fahimci baƙine a unguwar sabida ƙasaitarsu da kuma yanayin tsarin shigar dake jikinsu
Daga kallon farko idan kai musu zaka fahimci kyau da kuma tsarin da Allah yayma halittasu, amma sedai ɗaya daga ciki yafi ɗayan yawan yalwar Gashin kai da kuma sajen gefan fuska, inda shikuma ɗayan yay masa fintinkyau a hasken fata da kuma dogon Hanci, suna ƙarasawa gurin Me dogon hancin sosai ya dubi matashin yace “nawa ne kuɗin ka” matashin yay ƙasa da kai yace “dubu biyar ne yallaɓoi” bece komai ba ya zaro Dubu goma ya bashi, godiya ya shiga yi masa a madadin ya amsashi se kawai ya dubeshi a karona biyu tun zuwansu gurin yace “ina capet ɗin can site ɗin?” zaro idanu me wankin motar yayi Nan take ya fara kame-kame don wllh besan inda yake ba, shidai kawai yasan ya fito dasu ɗazu kafin ya fara wankin Motar.
A fusace yay kansa ze rufeshi da Masifa ɗayan ya riƙe masa hannu yace “Look Faizak you have to control your self malam!” tsayawa yay cak lokaci guda kuma ya fara firzar da zazzafar iska daga bakinsa, Murmushi Ya kuma saki sannan yajawoshi zuwa baya yace ” Don Allah ka rage yawan fishi akan abinda bekai ya karowa ba aboki, Rayuwar duniyar ma gabaɗayar ta ai ƴar haƙuri ce.” ya faɗi hakan yana kallon tsakiyar idon Faizak ɗin
Tsaki Faizak yaja sannan ya kalleshi pink lips ɗinsa har wani tattarewa suke sabida fisata yace “Amma Moha why ze bari capet ɗin ya ɓata bayan kai kanka kasan kaf motocina nafison wan……..kasa ƙarasawa yayi sabida hangota dayayi ta ƙudindine akan capet ɗin, kallon direction ɗinda Faizak ɗin ke kallo Moha yayi kafin ya Ankara har Faizak ɗin ya nufi gurin.
Da sauri yake tafiya yana zuwa gurin ya daka mata wata uwar tsawa wadda tasata miƙe da sauri manyan idanunta duk sun soye sabida mugun ciwon da Mararta keyi, tun kafin ta ankara tuni ya sauke mata wani lafiyayyen mari wanda yasa ta saki wani wahalallen kuka me sauti. Fincikoshi Moha yayi cikin yanayi na fusata yace “amma kaidai anyi Mugu wllh Faizak why are you slap her? Me tamaka don kawai ta zauna a saman wannan banzan capet ɗin motan naka?” cikeda hasala yasa hannu ya janye capet ɗin datake kai ta faɗi a ƙasa, se’a lokacin Moha ya fahimci she’s on her period sabida yanda duk jikinta ya lalace da jini.
Wata uwar ƙara Faizak ya saki lokaci guda kuma yayarda capet ɗin sabida jinin daya gani duk ya lalata capet ɗin, wata Uwar harara Moha ya watsa masa sannan ya isa dabda inda ta ƙudindine tana kuka kasa mata magana yayi don wllh besan abinda Zece mata ba, fararen idanunsa ne suka sauka akan Bulugul maram ɗinta dake ƙasa cikin littattafan ta.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ɗauki littafin ya buɗe nan take Sunanta ya baiyana a Saman littafin Kamar Haka *_KHADIJAH MUHAMMAD MAI-YAƘI_* ɗan jim yayi kaɗan cikin cool Voice ɗinshi yace “Khadijatou” ɗagowa tayi idanunta na tsiyayar da hawaye, da sauri tayi ƙasa da manyan idanunta sabida kwarjinin dayay mata murmushinsa dake ƙara masa kyau yayi yace “kiyi haƙuri kinji?” ɗaga masa kai kawai tayi amma har lokacin bata dena kukan datake ba, “zaki iya tashi?” ɗaga masa kai tayi still batai magana ba, tausayinta yaji ya mugun kamashi don haka yace “daure ki miƙe tsaye kinji” ya faɗi hakan yayinda yake ƙoƙarin kwashe mata litattafan ta ya zuba mata a jakar.
Ƙoƙarin miƙewa ta farayi mararta yay wani irin murɗa mata nan ta zube ƙasa Sumammiya, gabaɗayansu zaro idanu sukayi except Faizak wanda gabaɗaya takaicin Moha ya hanashi magana
Kallonsa ya mayar kan me wankin motar yace “pls ko kasan gidansu ne?” da sauri ya ɗaga masa kai yace “nasanta a can ƙasan layin nan gidansu yake” wani dogon fasali Moha yaja sannan yace “ok Don Allah barin baka kuɗi kaje chemist ka siyo min abu” takarda ya ɗauka a cikin littattafanta yay rubutu kaɗan sannan ya miƙa masa yace “kayi sauri pls” karɓa yayi ya tafi da hanzari
A fusace Faizak yace “tunda naga kai baka da niyar tafi ka tsaya se wani kallonta kake waikai tausayi toni wllh kaga tafiya na, baran tsaya ka zubar mana da class ba malam” yana kaiwa nan ya ɗauka kapet ɗin se wani yamutsa fuska yake ya jefashi cikin booth sannan yama motar key ya barsu nan, yana barin gurin sega Me wankin Motar ya dawo da ɗan babban leda a hannunsa pad ce a ciki se drip da kuma Allura suna nan zaune sega me keke napep, tareshi Moha yayi sannan ya kalli matshin yace pls muje ka rakani gidansu
Kinkimarta yayi kaman baby dama ba nauyi ne da ita ba suka shiga cikin keken, sam be damu da yanda duk ta ɓata mishin farin wandon jampan dake jikinsa da jini ba suna zuwa ƙofar gidan ya kalli me keken yace “ka jirani don Allah idan na fito seka maidani Janbulo” ɗaga masa kai kawai yayi sannan ya kinkimeta already wannan matashin ya shiga gidan ya sanar dasu, tare suka fito da Abbanta wanda kana kallonsa zakaga kamar da suke da ita banbancinsu kawai tafi Baban nata farin fata ne kawai,
Cikeda damuwa baban yace “sannu yaro ku shigo daga ciki mana” be wani shiga yay da ita har cikin wani haɗaɗɗen falo wanda aka tanada don baƙi, Shimfiɗeta yayi a hankali sannan ya buɗe ledar kayan asibitin ya fara haɗa alluran yayi mata sannan ya saka mata drip ɗin shima, a hankali take sauke numfashi idanunsa ne ya sauka akan cute read lips ɗinta da suka ƙara ja sabida kukan datasha, ajiyan zuciya ya sauke sannan ya maida kallonsa ga Mom ɗinta dake tsaye damuwa ƙarara a saman fuskarta yace “Hajiya an gama ba wata matsala kuma again insha Allah” godiya suka dinga masa sannan ya miƙe yay musu sallama ba tareda ɗayansu ya tambayi sunansa ba……..
Yana fitowa ya shiga cikin keken suka kama hanyar jan-bulo, tafiya kaɗan sukayi kasancewar babu tazara sosai tsakanin Rijiyar zaki da kuma jan-bulo ɗin, a bakin wani kantamemen gida me Adaidaita Sahun ya tsaya sannan Moha ya sakko ƙofar gidan yaɗan kalla sannan ya zaro 1k ya miƙa masa yace “nagd sosai ” juyawa yayi ya fara takawa a hankali cikin takunsa me ɗauke da nutsuwa ya shiga cikin gidan kai tsaye, a farfajiyar gidan ya haɗu da Hajiya Fatima ƙanwar Mahaifiyarsa wadda suke kiranta da Ammi
murmushi ya sakar mata yace “Ammi noi chamri?” kallon galala tayi masa sannan tayi dariya tace “jam Alhamdulillah Moha ya aiki?” kansa a ƙasa yace “lfy lau Ammi
Shafa kansa yayi yace “Salti fa ?” she’s upstairs cewar ammi ɗan jim yayi kaɗan sannan yace “barin shiga ciki” murmushi Ammi tayi tace “to bokan turai gobe dai zanzo Asbitinku fatan zaka haɗani da Dr.kazim ɗin base nasha wahala ba” murmushi kawai yayi sannan yce “bakida matsala Ammi.” part ɗinsa ya nufa kai tsaye tareda raba kansa da kayan jikinsa ya faɗa toilet, be jimaba ya fito ɗaureda towel tsadadden lotion ɗinsa mallakin companyn Olay ya fara shafawa, seda ya kammala tsaf sannan ya kalli makeken agogon bangon dake maƙale jikin bangon ɗakin, ɗan siririn tsaki yaja kaɗan sabida ganin lokacin sallar la’ar ya wuce sosai wata lallausar hallabiya ya ɗakko a cikin closet ɗinshi ya saka sannan ya tada sallan.
yana idarwa ko tasbihi kasayi yayi sabida gajiyan dake jikinsa, ga wadda ya kwaso a Hospital be huta ba Faizak ya ƙara masa wata se gashin sun ƙare dayin faɗa, wani gajeran Murmushi ya Saki a ransa yana mamakin Zafin rai irin na Faizak kan lallausan gadonsa ya hau ya kwanta tareda tunanin hanyar dazebi wajen Sauyawa Faizak Halaiyyar sa ta Saurin fishi akan abinda bekai ya kawo ba, wayansa ya jawo yaga tarin miss call ɗin Aminin nasa wani dogon Fasali yaja sannan yasa wayar a silent don yasan Faizak ze sake kiranshi.
Ɓangaren Faizak kuwa sanye yake cikin wata lallausar Riga Armless fara sol da ita me ratsin Sky blue a jikinta, hakanne ya bashi damar sanya treequarter wanda ya baya dogayen beautiful legs ɗinsa fitowa
wani siririn baƙin Silifas ne a ƙafarsa wanda ya fito da harken fatar ƙafan sosai, a nitse yake takawa cikin izza da taƙama harya isa cikin katafaren falon gidan wanda aka ƙawatashi da kujeru na alfarma haɗe rai yayi sosai donshi dama ba gwanin fara’ah bane, Salma ce kawai a Falon tana danna system ɗin dake gefanta da alama wani mahimmin abin takeyi a ciki se kuma me aikinsu Talatu wadda ke ƙoƙarin sa turaren wuta a burner.
Can ƙasan maƙoshinsa yay sallama tareda zama bisa ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun da sukama falon ƙawanya, ɗagowa Salmah tayi tana murmushi tace “ya Faizak wllh kaman kasan inason ganin ka dama.” fararan tsimammun idanunsa ya zuba mata ba tareda yayi magana ba, marairaice masa tayi kamar zatai kuka tace “uhmm ya Faizak please I need some money kaji” kawai dakai yayi gefe yace “me zakiyi da kuɗi Salmah?” washe baki tayi sannan ta gyara zama tace “shoping zanje” ajiyar zuciya ya sauke cikeda gundira da maganganunta yace “naji send me your account number Insha Allah I will send it to you” tsalle ta doka tai hugging nashi tace “thank you yayah”.
A hankali take sakkowa daga saman steps ɗin cikin shiga ta alfarma, sanye take cikin wata dakakkiyar shadda irinta mutanan sinigal wadda tasha wani siririn aiki tun daga wuyan rigar har zuwa ƙasanta, hannunta kuwa a jere yake da zobuna gold ƙirar Dubai hakama ƙaton bangles ɗin dake ɗaure a jikin tsintsiyar hannunta.
fuskarta ɗauke take da wani ƙayataccen Murmushi wanda ya taimaka waje ƙara fallasa sirrin kyanta, Hajiya Halima kenan Mahaifiyar Faizak da Salma haka kuma mata ga Ambasada Me ritaya Alhaji Abubakar Mahe, Faizak na ganinta ya miƙe yay hugging nata shafa kansa tayi cikeda so tana me ƙara yalwata murmushinta fiyeda na farko
shagwaɓe fuska yayi kamar ba wannan matashin saurayin ma’abocin zafin rai da izzah ba yace “Mamie I’m hungry!” sumbatar goshinsa tayi sannan tajashi zuwa daining aria ta zaunar dashi sannan ta zagaye ta fara serving ɗinshi with so much love and caring sabida yanda take mugun jidashi, a haka ya gama cin abincin sannan ya miƙe ya zagaya gefanta ya Sumbaci kumatunta yace “I love you Mamie na” murmushi ta saki itama tace “I love you more sweetheart ” harya kai tsakiyan falon sannan ya tsaya tareda juyowa yace “Mamie when pops ze dawo daga Germany?” “maybe tomorrow insha Allah ” Cewar mamie
Wani haɗaɗɗen murmushine yay escaping cute pink lips ɗinsa wanda ya ƙara fitoda sihirtaccen kyanda yake dashi yace “kai I’m so happy wllh, dole in shiryama Pops abu na musamman wanda zanyi welcoming nashi dashi” juyawa yay da sauri ya fita zuwa part ɗinshi, salla ce kawai ta fito dashi amma abin mamaki sam be haɗu da Moha a masallaci ba har akayi sallan isha, maine falo ɗinsu ya koma yay dinner with Mamie and Salmah sannan ya wuce part ɗinshi
Wanka ya kumayi sannan ya fito ya gama shafe-shafansa yasa turaruka masu sanyin ƙamshi, wasu lausasan pj-mas ya sanya a jikinsa sannan yabi lafiyan gado
kafin ya kwanta seda ya ƙara trying number ɗin Moha Amma still no answer, nan take seyaji yana zargin kansa tabbas yasan Moha fishi yake dashi akan abinda ya aikata ɗazu, “toma wai meye matsalar Moha akan marin dayayma yarinyar?” Zuciyar Faizak ta aiyana masa hakan a dedai lokacin dayake gyara kwanciyarsa, wani siririn tsaki yaja tareda Ajiye wayar a saman bedside drower, cikin kasalallen yanayi yay switching ƙaramar fitilar dake jikin gadon ɗakin yay duhu,
Duk yanda yaso yay bacci cikin sauƙi se abin ya fara neman gagaransa, haka ya dinga tuka da warwara akan yanda ze Shawo kan Moha a haka bacci me nauyi ya samu Nasarar ɗaukanshi cikeda tarin mafarkai kala-kala, koda ya farka nazari ya dingayi a kan mafarkan dayakewa kallo a matsayin marasa makama Ballantana tushe, tsaki ya kuma ja sannan ya koma baccinsa bayan yayi addu’ar da Sunna ta koyar, be jima da komawa baccin ba ya farka a firgice duk ya haɗa uwar zufa, bottle water ɗin dake ajiye bisa bedsite ya ɗauka tareda buɗewa ya kafa bakinsa ya fara sha yana sauke numfashi Akai-akai, Tamkar wanda ya ya Fafata gudin tsere da ingarman doki maji ƙarfi ……….
Tafiyar ta musamman ce tai daban da wadda mukai a mutuncin ƴa mace 🙅♀️
Sedai fa wannan karon littafik paid book ne, 300 naira zaki biya ta wannan account number ɗin:0249313050, Mustapha Hafsat, GT bank.
Seki turo da Evidence of payment via this number : 08102777485
Allah ya hore muku abin biya don Alfarmar manzon Allah 🤲
Comment
And
Share fisabilillah
H/z ✍️
[08/09, 12:31 am] +234 803 192 1625: *ALƘALAMIN ƘADDARA…*
(zanansa baya gogewa)
True life story
*MALLAKIN*
*_ZAINAB CHUBAƊO_*
DA
*_HAFSAT HAFNAN_*
*02*
___A Ɓangaren Khadjiah kuwa sai da misalin Ƙarfe biyar da rabi na yamma ta farka, ta tashi alokacin tuni karin ruwan da akasa mata ya kare.
Sosai taji dad’In jikinta don akalla ta share kusan mintina biyar da farkawan amma bata ji wani ciwon ciki ya sake mintsinanta ba.
Duban Mom d’inta tayi wacce take zaune tana kallon yadda take ta k’ok’arin tuttura kayan marmari abaki, daqyar take iya sha kasancewar bakin nata babu dad’I.
“Momy ina yake ? “.tayi mata tambayar tana me tsareta da fararen idanunta da suka rine don wahala.
“Shi wa kenan?”.
Kamar zatayi kuka tace”wanda ya nuna mun tausayi karara, wallahi Momy in kika ga yadda ya marairaice ke kya ce ko ciwon ajikinsa yake amma wannan abokin nashi bashi da tausayi kona k’wayar zarra, Fad’a gareshi beda kirki ko kadan, Ni har naji ma na tsanesa wallahi…” tana kaiwa nan amaganar nata ta rushe da kuka.
Cike da mamak’i Mummy tace”a’a Khadija nifa ban son Shagwab’a, ba Daddynki ne zaune anan ba balle ki tasashi gaba da tijara, me aka miki kike wannan kukan ? ”
Jan majina tayi tace”Wai fa akan shegiyar capet d’in motarsa ce ya rufeni da fad’a, capet d’in dama yayi kama da fatar rakuma shine aka yi mun wulakanci akansa, Momy hadda Marina fa yayi akansa..”
Kuka ya sake cin k’arfinta…kama baki Mom tayi sannan tace”kema me yakaiki daukar masa Capet tun farko kika kwanta akai ? “…Nan ta kwashe yadda sukayi ta gaya mata..
Ita kanta Momy ko kadan bata ji dad’In abunda Faizak yayi wa d’iyar tata ba amma tafi ganin Laifin ita Khadijar data shiga gonarsa….Momy tace”Gobe ma ki k’ara neman fad’an dayafi karfinki se an miki wanda yafi wannan….”…cike da d’acin Rai tayi saurin taran Numfashinta”haba momy meyasa kike gayamun ba dad’I ne ? don kawai na kwanta akan capet d’in motarsa shine ya bashi damar marina ? bai fa tsaya a iya fad’a ba ce miki nayi Marina yayi ! Mom he slapped me ” ranta ya sake mugun b’aci sanda ta tuno wannan moment d’in da Faizak yake marinta wanda tunda tayi wayau ba’a tab’a daga hannu an mareta ba sai dai fad’a kasancewar ita d’in ‘yar gata ce, ‘ya kwara daya kwal da Allah ya azurta MR & Mrs Mai-Yaki da samin haihuwarta..
Ajiyar zuciya Momy ta sauke sannan ta mike tana fad’in”Look Khadija bani da lokacin dramas naki, kibari in daddynki ya shigo sai ku cigaba da shirmenku kamar yadda kuka saba.”
Tana gama fad’in hakan tasa kai zata bar dakin, da sauri Khadija ta sakko daga kan gado ta nufeta ta rungumota ta baya gami da fashewa da sabon kuka tana fad’in”Momy bazan tab’a yafewa *FAIZAK* wulakancin da yayimun ba inba takowa yayi har zuwa gabana sannan ya duk’a har kasa ya nemi gafarana ba..” dayake taji sanda Moha ya ambaci sunansa hakan yasa bata manta ba, ta haddaceshi tsaf kuma bazata tab’a manta da sunan, shi karan kansa da kuma wulak’ancin da yayi mata wanda ya tsaya mata arai ba..
Sosai ta bawa Momy tausayi don yadda take kukan kadai ya isa kasan abunda aka mata ya bakanta mata sosai, Fuskantarta tayi sannan ta shiga lallashinta har tayi shiru sannan ta saukar da ajiyar zuciya tace”Da kin bi maganata da baki Fita ba balle hakan ta faru dake, ke kanki kinsan duk sanda lokacin al’adarki ya zagayo kikan wahala sosai har ki Fita hayyacinki, nace miki Khadija ki hakura da zuwa islamiyyar nan yau har kidan samu lafiya zuwa gobe kya je amma kika k’iya, to gashi ke baki ma kai ga karasa islamiyyan ba kika had’u da me maganinki..”
“Momy ina cikin wa’enda zasu Musabaqa na Wannan shekaran to taya kike son inyi wasa da wannan damar ? Karfa ki manta ance duk wanda yazo na daya za’a biya masa kudi yaje aikin hajjin bana..”
“To amma ai da lafiya ake komi ko ? Kuma naga dai rabonka baya tab’a wuceka, in har Allah yace kina da rabon zuwa to ko baki je musabaqar ba se kika Allah ya nufeki da zuwa aikin hajjin..” kwantawa Momyn nata tayi ajiki tana jin duk wani kalaminta na ratsata, cike da fargaba tace”Maman Khadee pls can i say something ?” Haka take gaya mata wani sa’in in iskancin nata ya motso…”ina jinki ” dagowa tayi tana murza yatsun hannunta idanunta na kallon kasa ta lagwabar dakai gefe tace”akan wannan maganar tamu ne…don Allah ki yarda inyi auren kinji Maman Khadijah ? Allah inayi ciwon cikin nan zai bari….” wani irin tsawa Momy ta doka mata don ta tsani jin wannan batu ” _*Khadijatul Khairiyya*_ wallahi ki Fita daga idona! Na gaya miki bazakiyi auren nan yanzu ba se kin digirgire ! wai meyasa bakya jin magana ne ? dududu nawa kike da har kika soma tunanin aure ? Me kika sani akan aure ey Khadija ? ki gayamun wani hukunce hukunce kika sani akansa ? Sannan wasu sharudd’an ne kika sani ? ”
Momy tayi tambaya tana watsa hannu a iska, turbuno baki gaba Khadija tayi sannan tace cike da wauta da yarinta”Ni abunda na sani agame da aure! Ana dafawa megida lafiyayyen girki ne, amasa wankin kaya da yi mishi wanka kamar beby, ata riritashi ana shagwab’ashi, sannan ka dunga kula da hakki’nsa wannan shine aure !”
Murmushin takaici Momy tayi tace”Wani hakk’in kike nufi ban gane ba ? Cike da kunya tace”kai momy meyasa kike pretending kamar baki sani ba ?….”ina fa na sani ? Ni ban sani ba yanzu nake daukar lacca awajenki dai “.
Bud’e baki tayi tace”kai Momy to taya akai kika haifeni ? Nifa kin gane abunda nake nufi kawai waskewa kike….”
“Kinci gidanku wato Khadija zancen da kuke zuwa jiyowa kenan agidan Ladiyo keda Zara’u ko ? tana zama tana baku labarin yadda sukeyi ita da mijinta shiyasa kema kika bijiro mana da batun a aurar dake haka ne ? to bud’e kunnuwanki kiji dakyau dake da Ladiyo akwai banbanci sosai, ba daya kuke ba, ita d’in ‘yar gargajiya ce shiyasa tayi auren wuri, Ke kuma d’iyar wayayyu ne dole ki maida hankali kiyi karatu kafin kiyi aure, kin ganni nan saida na zama proffessor kafin na auri ubanki shima alokacin prof ne, kinga kuwa dake dasu da banbanci sai kin zama mu koda baki kai matakin proffesor ba kafin mu bari kiyi aure..”
Kuka ta fashe mata dashi me daga hankali tace”shiyasa ai kuka gama tsofewa baku haihu da wuri ba, Ni d’in ma Allah ne ya taimakeku in ba haka da watakila baku same….” da sauri Momy takai hannu ta bige mata bakin tace”Zanci kutumar ubanki in kikace zaki gayamun ba dad’i, mu muka haifeki ba kece kika haifemu ba, Na fada bazakiyi auren yanzu ba sai lokacin da muka gamsu da karatunki! Kuma daga yau kika sake zuwa gidan Ladiyo ban yafe miki Nonona da kika sha harna tsawon shekara daya da watanni shidda ba ” tana kaiwa nan ta kada kai tabar dakin, kuka Khadija ta fashe dashi tana fad’i da karfi”wallahi se kun aurar dani donni bazan tab’a kaiwa irin shekarun daku kuka kwashe ba aure ba! kuma ni nake jin wannan azabar ciwon cikin baku ba, ni kadai nasan halin da nake tsintar kaina aciki in ya taso mun, baku sani ba Shiyasa kuka hanani auren bayan kun san ance yin auren shine mafita, da zarar mace tayi haihuwa daya in aka dace sai aga ciwon maran ya rabu da ita har abada..” tsagaitawa tayi tana jan majina, can ta cigaba”haba ciwon ciki sai kace me nakud’ar haihuwa ? Yo! to ku aurar dani inje in tayin me gaba dayan kuma me dalilin mana in san nakudan gasken nakeyi, kuma ko badon wannan ba *NIMA MACE CE* ku kyaleni inje inji abunda matan aure suke ji, Ladiyo tace babu wahala kuma babu azaba sai dad’in da akeji, to wai Momy bak’in cikin samin jindadin kuke mun ko menene yau ina son in sani ?”
“Khadija ni kike gayawa wa’ennan maganganun don muna sonki da arzik’i ? ” momy ta furta tana k’ok’arin shigowa dakin da Muciyar da take nufin fara tuk’a tuwo dashi…Khadija na ganin shigowarta ta fad’a bandak’i asukwane tare da murza key, sai sauke ajiyar zuciya take tana gwaggwalo idanu waje don ba karamin tsoron duka take ba.
Momy tace”Zaki fito ki sameni ne kuma daddynki zai dawo zan fad’i masa irin rashin kunyar da kika tsiro dashi kwanan nan.”
Tana jin Fitarta ta bud’o kofar ta fito atsorace, cikin sanda ta nufi kofa ta rufe dakin kana ta koma ta zub’e saman gado gami da dora Filo akan cinyarta, Tunanin Moha ne ya fad’o ranta, se murmushi take ta saki tamkar wata sokuwa ko kuma wacce tayi gamo.
“Allah sarki me tausayina ! Allah yasa inna tashi aure in samu irinka wanda zai rik’a jin tsananin tausayina akodayaushe wanda kuma zai rik’a jiyar dani irin dad’in da Ladiyo take fad’ar ana ji in akayi aure ba tare daya nuna gazawarsa ba ! Ina son aure ko don ciwon maran nan ya rabu dani har abada amma gashi Daddy da Mommy basa so ” ta ida magana kwalla na zubo mata, ita fa tun sanda taji labarin ance wai idan mace tana yawan ciwon mara na al’ada to muddin tayi aure tayi haihuwar Farko to in aka dace ciwon na iya rabuwa da ita har abada, shine fa tabi ta kwadaitu da hakan ta addabi iyayenta akan su mata aure kota samu ta huta da azab’an ciwo duk wata domin kuwa in ya tashi zuwar mata bada wasa yake zuwa ba, yakan sa ta fita cikin hayyacinta ma…gashi iyayen nata ‘yan bokan bokoko ne, so suke sai tayi zuzzurfan karatu kamar dai su kafin su aurar da ita, balle ayanzu kallon yarinya sosai suke mata, dududu shekarunta 17 kuma acikin wannan shekarar ne zatayi Candy na Ss3.
Tare suka taso da ita da Ladiyo da Zara’u a unguwar, kawaye ne sosai amma Ladiyo ta basu kusan shekaru uku, sai dai baka ganewa don karamin jiki gareta, duk cikinsu Khadija ta fisu girman jiki, ga uban wautar tsiya, amma gara ita ma akan Zara’u, in aka gangaro kan Ladiyo kuma kankat kenan ba’a magana sai Lahaula wala kuwwata, wautarsu duk kusan daya shiyasa kawancen ma yazo daya.
Ita d’in ‘yar gargajiya ce, agidansu basa boko sai karatun addini, da zarar yarinya tadan tasa in har ta fara ganin al’adarta to zaiyi wuya tayi hailarta ta biyar agidan, don aurar da ita za’ayi cikin gaggawa kuma already an riga an miki miji ana jiran ne kawai ki k’yank’yashe kafin ajoneku, ahad’aki da kusan sa’ar babanki ko wanda yakusan sa’arsa.
To ita Ladiyo bata soma al’ada da wuri ba sai data kai shekaru 20 don har iyayenta sun fara tsoro ko lafiya ? amma dayake su d’in ba wani yadda da Zamani sukayi ba shiyasa basu je asibiti don adubata ba, sai aka shiga dura mata maganin gargajiya tare da zubawa sarautar Allah ido, ita kuma sam abin bema ba dameta domin idan taga yadda Khadija ke fama da rayuwarta dik sanda wata ya zagayo abun gwanin ban tausayi se hakan ya rik’a bata tsoro taji kawai ko anan gaba bata fatar tayi al’ada (awautarta kenan) amma ita Zara’u sam bata yi, da wuya ma kaji ta b’ata Fuska da nufin ciwon mara..
To sai data kai shekaru ashirin dinne cif cif sannan al’adar yazo mata, aranar taci kuka harta gode Allah don aganinta itama zata fara wahala kenan kamar Khadijah, sai dai wani ikon Allah tunda tayi ciwon maran sau daya bata sake ba har aka mata aure, ahalin yanzu tana da wata kusan biyar agidan mijinta Malam Manu me mata uku, itace cikon na hudu, kuma kasancewarta yarinya acikin matansa yasa yafi ji da ita yana riritata, ta gaban goshinsa, ga wani irin zumar da yake kwasa awajenta kasancewarta sabon jini shiyasa ya koma tamk’ar rakumi da akala awajenta, hakan kuwa ba karamin adad’i yake mata ba shiyasa take jin duk duniya babu wanda yakaita sa’ar Miji da moriyar aure, duk sanda su Khadija suka zo wajenta kwashe komai take da wanda yakamata abarwa ciki duk ta gaya musu shiyasa Khadija ta qara masifar kwadaituwa da aure!
Jiwo muryan Zara’u tayi tana gayar da Momy dayake kicin d’insu atsakar gida yake, ba wani kudi garesu ba se rufin asiri, wato bazaka dai kirasu da talakawa ba haka kuma bazaka sakasu asahun masu kudi ba…Tana kallon Zara’un ta taga sanda ta russuna tana gayar da ita abakin kicin d’in tare da tambayarta Khadijan, ba tare data sake dubanta ba tace”ki shiga tana ciki ai kin san wata ya zagayo tana nan tana fama amma da sauki, kije in kin fito ina son ganinki ”
Amsawa tayi da “to Momy” sannan ta mik’e ahanzarce tayi ciki.
Tun kan ta kariso Khadija ta mik’e ta bud’e mata kofa, tana shigowa se kuma ta tsaya turus tana kallon Khadijar da tayi sheme sheme asaman gado kamar ba mara lafiya ba.
Murmushi tayi tace”Ke yana kallo haka meya faru ? ”
“To ai gani nayi lafiyarki qalau yau, nida nake tunanin zanzo in taras kin tara mana mutan unguwa agidan se kuma na ganki garas dake ? Wallahi ba don nasan dai Momy bazatamun k’arya ba kai dana ce watakila date d’in abun ne ya canza…”
Dariya sosai Khadija tayi da maganarta sannan ta mik’e ta jawota ta zaunar da ita abakin gadon tana fadin”Ke maganin abun na samu wallahi ”
Zara’u ta gwalo idanu waje tace”ke da gaske ? Ko sun yadda zasu miki auren ne ? ” siririn tsoki taja gami da tab’e baki tace”wa’ennan mutanen ne zasu min aure ? ai dana bi gari ina rarraba goro da alawa, ke karin ruwa akamun kuma naji dadinsa sosai kamar an ciremun ciwon gaba daya, ke in har basu mun auren anan kusa ba to agaskiya shi za’a ta kira ya cigaba damun karin ruwan duk wata..”
“Wanene shi d’in ?” Khadija ta bata labarin Moha da Faizak, sosai Zara’u taji haushin abunda Faizak d’in yayiwa aminiyar tata hadda cin alwashin sai sun rama duk sanda Allah ya sake hadasu, abangare daya kuma se taji kawai Moha ya mata..
Sai kusan magrib tayi haramar tafiya sai shushe shushe take, Khadija tace”kedai Zara’u naga ranar da wannan ciwon shoshe shoshen zai rabu dake don naga abun naki sai dad’a gaba yake ?” Dariya sosai tayi tace”sai randa nayi aure ! Aranar da *NIMA* na zama *CIKAKKIYAR MACE* mijina shi zai yayemun wannan ciwon shoshe shoshen ta hanyar yawan yi mun tausa da matse matse ” ta ida magana tana dariya tare da jefa babbar ‘yar yatsarta abaki ta shiga tsotsa, girgiza kai Khadija tayi tace”ke wautarki ma me lasisi ce, tsotsar yatsarki kadai ma in aka bakki da ita ba lalle namiji ya kalleki ba balle har yayi tunanin ajjeki agidansa, don Allah Zara’u ki girma mana ”
“Karki damu nan da dan lokaci zan dena, kin san tunda Ladiyo ta gaya mana yadda ake tsotsar ayabar megida tun asannan na soma jarabawa don in saba sabida banason abin yazo ya zamar min sabo nan gaba, so nake in zama espat kafin nan kin gane ai…” se dariya take kamar wawiya, juyawar da zasuyi sai ganin Momy sukayi abakin kofa tana kallonsu ranta na mugun suya, Fuskan nan ahad’e tumuk! Ashe kakaf taji duk batsar da suke tayi, tuni suka dauke dariyarsu kowanne gabansa na fat fat…………..
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza 3
-
Zuciya ta
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi
-
Aure da haihuwa
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya
-
Gangar Shedan
-
Angon mata biyu
-
A gidan mu take
-
Bafulatanar Rugga
-
Matar yaro
-
Mr Bello
-
Mijin Buzuwa
-
Gidan Uncle Complete
Powered by: www.mynovels.com.ng
Comment
&
Share
Fisabilillahi🙏🏻
H/Z