Kannywood News

Allah ya sakawa yan Arewa ana ta kashe su an rasa mai magana Hadiza Gabon

Allah ya sakawa yan Arewa ana ta kashe su an rasa mai magana Hadiza Aliyu Gabon

 

 

 

 

 

 

 

 

“Allah Ka Saka Wa ‘Yan Arewa, Ana Ta Kashe Su An Rasa Mai Magana”. Inji Hadiza Gabon.

 

 

 

Daga Zaharaddeen Gandu

Fitacciyar Jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood Hadiza Aliyu Gabon, ta nuna ɓacin ranta fili game da yawan kashe-kashe da ake yi a Najeriya, musamman anan yankin Arewa.

 

 

 

 

Tarihin Aisha Aliyu Tsamiya

Jarumar dai ta wallafa wani gajeren saƙo da ta rubuta a shafinta na Fezbuk, Jarumar ta yi Allah ya isa kan wannan kashe-kashe da ake yi wa yankin Arewa, kuma babu mai iya tsawatarwa.

 

 

 

 

Hadiza Aliyu Gabon ta bayyana cewa, “Yaro ɗaya aka kashe a Lagos an fita nemar masa haƙƙinsa, ba maganar jam’iyya ko addini ko jinsi, amma mu ana ta kashemu an rasa ko masu magana, Allah ya saka mana”.

 

 

 

 

Tarihin Hadiza Aliyu Gabon

Kashe-kashen da akai na baya bayan nan dai, shi ne na wasu matafiya kusan aƙalla 40 da yan bindiga suka cinnawa wuta a cikin mota, suka ƙone su ƙurmus.

Leave a Comment

error: Content is protected !!