Almajirin Gidana Hausa Novel Complete

Almajirin Gidana Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Almajirin Gidana Hausa Novel Complete

ALMAJIRIN GIDANA*

 

 

 

*Writing By*

*Zee Elkasim (Mmn khady)*

 

 

 

 

*Daga Marubuciyar*

 

*Siyasa ko soyayya*

*Alhini*

*Gidan Asali*

*Halin Girma*

*Autar Hajiya*

*Zanen Zuciya*

*Yarinyar Baba*

*Auren tagwaye*

*Wata Uwar mijin*

*Ke Duniya*

 

And now

*ALMAJIRIN GIDANA*

 

 

 

 

.page 1

 

 

 

 

Da sunan Allah Mai rahama Mai Jin ‘kai.

 

 

 

 

Dan saurayine Wanda ashekaru bazai gazama Sha takwas zuwa Sha tara ba, zaune yake kan kujera ‘yar tsugonno a wani madai-daicin tsakar gida gabansa Kuma ‘yan kwarorin kwanonin wanke-wanke ne Wanda basu wuce kwara 7 ba, sai ‘yan cokulla Wanda suma ba yawane dasuba,

 

Hannunsa cikin robar ruwan dayazubama clean Yana wankewa sannan ya dauraye cikin wani ruwan daban kafin yakife cikin kwandon da aka tanada dan kife kwanonin.

 

 

Sallamar Mai gidan tasashi juyowa daga aikin dayake tare da amsa sallamar, fauziyya dake daki tafito cikin farin ciki Jin dawowar mijin nata, sanye take cikin Riga da siket na atamfa Wanda kalar atamfar da dinkin ba karamin fiddo da kyawunta sukayiba, cikin murna da farinciki ta rungume Salim “sannu da zuwa hubby,” tafada cikin nushadi yakara rungumeta tare da kissing kumatunta, yace “Nagode My wife”

 

Jikkar hannunsa ta karba sannan takama hannunsa suka nufi d’aki.

 

Sani Dake zaune Yana kallonsu duk abunda sukeyi kan idonshi, wani kululun bakinciki yazo yatokaremashi wuya,

 

Sauri yayi yanufi kofar fita daga gidan, zauren gidan yayi zaman dirshan yakalli kudu maso arewa yafara rizgar kuka kamar Wanda aka aikoma da sakon mutuwar uwarshi da ubanshi da duka danginshi lokaci daya.

 

Shikau abunda Salim da fauziyya keyi Yana bala’in batamashi rai, Yana masifar kishin fauziyya har cikin ranshi, baya kaunar yaga salim yayimata koda wani kallo Wanda yadanganci soyayya barantana Kuma akai ga yataba jikinta jiyake kamar ya had’iyi Zuciya yamutu,

 

Dafe kanshi yayi da hannu biyu dayakejin Yana barazanar tarwatsewa gida biyu saboda azabar ciwon dayake mashi,

 

Dagewa yayi iya karfinsa yabuga kanshi ga bango, Dan jiyakema kamar ba cikin hayyacinsa yakeba.

 

“Sani… Sani… Kusan sau ukku fauziyya tana kwalamashi Kira Amma bai amsaba, hanyar zauren tanufo tana Kara kwalamashi kira, sai lokacin yajiyota da sauri yanufi cikin gidan Yana goge hawayen dake kan fuskarsa, “gani aunty” yafada tare da saddar dakanshi kasa Dan bayaso su had’a ido da ita.

 

Kallonshi fauziyya tayi sannan tace “sani Wai meke damunka, kuka kayine?”

 

Saurin ‘kakaro murmurshi yayi Wanda Bai Kai cikina yace ‘yace “a’a aunty

Ruwan clean ne danake wanke-wanke- ya fallasamin a Ido shine nadan fita kofar gida ko yadan saki”

 

Tunda yafara magana fauziyya ke kallonshi tace “dama aikenka zanyi can shagon ka amsoma hubby lemu”

Wani kududun bakin ciki yaji yazo yamakalemashi a makoshi Dan jin fauziyya takira Salim da sunanda yatasana a rayuwarshi wato *Hubby* wlh dayanada Hali daya hanata fad’ar wannan sunan.

 

‘karbar kudin lemun yayi Yana niyyar fita, fauziyya ta kira sunanshi “sani”

Juyowa yayi yakuramata mayun idanunshi masu kama dana mujiya.

 

“Meya sameka agoshi Naga ya kumbura” tajeho mashi tambayar idanunta akanshi.

 

“Uhe eh uhum dama lokacin da ruwan kumfa clean yashigarmin a ido Ina niyyar fita shine na buge da bango”

 

“To Allah ya sauwa’ke sani karika kula Dan Allah idan kana aiki, kullum Kai idan zakayi wanke-wanke sai ruwan clean yashigarma a ido kamar wani ‘karamin yaro, kayi sauri Dan Allah kakawomin lemun hubby zaici abinci Yana bukatar lemu a kusa”

 

“To” yafad’a tare da ficewa daga gidan zuciyarshi na tafarfasa jiyake kamar yaje yarufe Salim da duka Dan duk fadi’n Duniya ba Wanda yatsana kamar Salim.

 

Bayan mintina dabasu wuce glbakwaiba sani yadawo da Leda d’auke da lemun Coca-Cola, sallama yaketa kwadawa Amma shiru ba amsa haka yasa yanufi dakin Kai tsaye ya yaye labulen, fauziyya ce zaune tad’an kwanto jikin Salim tanata zubamashi shagwaba, shikuma Yana aikin rarrashi kamar wata yarinyar goye,

See also  Taswirar Kaddara Hausa Novel

 

Karin wasu littafai da zaku so

Karar fad’uwar ledar lemunda sani yasawo yadawo dasu cikin hayyacinsu, saurin rabata da jikishi Salim yayi tareda bin sani da kallo Wanda shima su yake kallo zuciyarsa na tafarfasa, sunkai tsawon minti 2 haka kafin sani yasaki kabulen dakin da karfi yayi baya, yanufi wurin wanke-wankensa hawayenda ke makale a idonshi suka cigaba da zubowa, ahaka ya karasa wanke-wanken ranar ko abinci bai tsaya karba ba yabar gidan.

 

 

 

 

 

 

 

*Tofah Reader’s Ina fatan kungane waye sani Kuma waye Salim, Kuma wane matsayi fauziyya take wurin Salim, kubiyoni Dan Jin yanda labarin zai kasance, idan Naga yasamu karbuwa gareku zancigaba idan Kuma Naga akasin haka zakuji shiru kawai*

 

Wannan somun tabine daga cikin labarin *ALMAJIRIN GIDANA*

*ALMAJIRIN GIDANA*

 

 

 

*Writing By*

*Zee Elkasim (Mmn khady)*

 

 

 

 

*Daga Marubuciyar*

 

*Siyasa ko soyayya*

*Alhini*

*Gidan Asali*

*Halin Girma*

*Autar Hajiya*

*Zanen Zuciya*

*Yarinyar Baba*

*Auren tagwaye*

*Wata Uwar mijin*

*Ke Duniya*

 

And now

*ALMAJIRIN GIDANA*

 

 

Page 2

 

 

 

 

 

Fauziyya da kanta tazo ta d’auki lemun da sani yasaki a kasa ta kalli Salim tace “hubby narasa mai ke damun sani, ace kusan tsawon wata biyu Yana aiki a gidannan amma kullum sai ruwan omon wanke-wanke yashigar masa a Ido, yaufa baka ganiba wlh yanda idanunsa sukayi ja, Kuma yaje fita ya buge da bango, bakaga yanda goshinsa ya kumbura ba”

 

Tunda fauziyya tafara magana salim ke kallonta saida takai Aya sannan yace “ba dole ruwan omo yashigar masa idoba, aikine yakeyi Wanda bana jinsinshiba, kyau ace namiji kamar sani Yana kasuwa Yana neman na kanshi baya Zauna agida yanayima mata bautaba”

 

“Haba hubby yanzu idan sani yabar gidannan yazanyi da aikace-aikacen dayake tayani, Kuma idan ba saniba banida d’an aike kariga kasani, ni wlh baniso kana maganar barin sani a gidannan”

 

Murmushi Salim yayi tare da shafa gefen fuskarta yace “to ai shikenan amaryata Kuma Uwar gidana, yanda kekeso haka za’ayi”

 

“Nagode hubby, bari nahad’ama ruwan wanka tunda kagama cin abincin”. Daukar kular abincin tayi da plate din takai kitchen, robar abincin sani tagani ajiye yanda tazubashi ba’a taba ba, cike da mamaki tace “sani baici abincinba, ko lafiya oho, hmm nasan zai dawo”

 

Inda ruwan gidan yake tanufa tacika bucket takai kewaye, sannan takoma d’aki tace “Hubby ga ruwan wankan can nahad’ama”

“To my wife sai muje ki tayani wanakan dan kinsan yau na matukar kwaso gajiya”

Murmushi tayi tace “to muje Mana, ai sainayima wankanma duka Dan banason abunda zai wahalarmin da Hubby na”

 

 

Da sallama Sani yashigo gidan saboda wata mashahuriyar yunwa data addabeshi, da dai baiyi niyyar Kara dawowa gidanba a yau saboda bayason ganin bakinciki, saikuma yaga yunwa na niyyar illatashi, Kuma yasan yanzu Salim yabar gidan saboda haka yadawo gidan cike da farinciki Dan yasan zasusha fira shida fauziyya saboda idan Salim bayanan shine abokin firarta, Kuma idan suna fira jiyake kamar ansakashi aljanna saboda tsananin farinciki har mantawa yake da duk wani bakin cikin rayuwa.

 

Ganin yayi sallama kusan sau 2 ba’a amsamashiba, sai karar ruwa yakeji a toilet ya tabbatarma kanshi da wanka takeyi, saboda haka ya nufi kitchen ya dauko robar abincinsa yafito da niyyar zuwa inda yasaba zama a gidan, dai-dai lokacin Kuma Salim yafito daga toilet shida fauziyya suduka d’aure da towel jikinsu da lema Alamar wanka sukayi, juyowa sani yayi Aiko idonshi ya sauka kan fauziyya dake Daure da ‘karamin towel Wanda baigama rufe cinyoyintaba, a matukar firgice Sani kebinsu da kallo da mayun idanunshi, Nan take zuciyarshi tarinka harbawa da sauri da sauri, wani abu mai Kama da madaci yataso yazo ya tokaremashi makoshi, miyan bakinshi gabaki daya yakafe, kanshi yarinka juyamashi duk illahirin jikinshi kyarma yake, hakan yayi sannadiyyar fad’uwar robar abincin dake hannunshi wacce Nan take ta tarwatse abincin Kuma ya zube a kasa.

See also  Macen Sirri Hausa Novel Complete

 

 

Salim na ganin haka yakama Hannun fauziyya, baizame ko’ina ba sai kurya ya zunar da ita gefen gado, sannan yasako jallabiya yadawo tsakar gidan da niyyar yayima sani wulakanci dan baiji dadin yanda ya riskesuba, Amma Yana fitowa sai ya iske Sanin baya tsakar gidan, har kofar gida ya leka Amma baiga komai Kama dashiba

[8/4, 7:30 AM] Zee Elkasim: Dawowa Salim yayi ranshi a matukar bace ya iske Fauziyya zaune inda ya zaunar da ita ta buga uban tagumi, kallonta yayi yace “Fauziyya korar sani zanyi daga gidannan”.

 

Arazane ta juyo ta kalleshi “hubby, saboda me? Me yayimaka? Haba hubby gaskiya baikamata ka koreshiba Babu laifin zaune babu na tsaye”

 

“Dole yabar gidannan tunda ba gidan ubanshi bane”

“Haba Salim akanme zaka daga akan sai sani yabar gidannan Alhalin bayimaka wani laifiba” tafad’a a hasale, “Ni gaskiya hubby bazan yarda ka koreshiba, idan Kuma yazama dole saika koreshi to kagayamin laifin dayayima”

 

Banza Salim yayi da ita yacigaba da shirinsa, kananun Kaya yasanya wandon jeans sai shirt polo milk colour, kafarsa sanye da bakaken takalmi ba karamin kyau yayiba, makullin mashin dinsa roba-roba ya dauka, yafita yabar gidan batareda yakara Yima Fauziyya wata maganaba.

 

Jiki a sanyaye Fauziyya ta d’auko wani sassayan lotion akan mirror tashafama jikinta, sannan tashafa farar fowder da man lebe, wasu riga da siket ta sanya na English wears marassa nauyi ajikinta da ana zafi dukda marece yayi,

Ba karamin kyau Fauziyya tayiba, dukda kasancewarta gwana a fagen makeup Amma yau batayiba, hakama kayan data sanya ba karamar muhimmiyar rawa suka takaba wurin fitoda illahirin surar jikinta, tabarma ta dauko da pillow ta shimfida tsakar gidan cikin inuwa ta kishingida duk jikinta a sanyaye.

 

 

 

Sani kuwa tun lokacin dayabar gidan da gudun tsiya yakoma gidansu, inda suke kwana shida ‘yan’uwanshi Almajirai, kan sosashiyar katifarshi ya kwanta ya kalli rufin dakin idanunshi na zubar da zafafan hawaye, ya Lula cikin kololuwar tunani, ba abunda ke addabar zuciyarshi sai tsantsar So da ‘Kaunar Fauziyya, sannan uwa uba Zazzafan kishinta dayake, baya ‘kaunar yaganta tareda Salim, bayaso yaga Salim yakai hannunshi a jikin Fauziyya jiyake kamar yasa takobi mai kaifin bala’i ya yanke hannunshi, saigashi yau yayi mugun gani Wai Fauziyya ce take wanka tare da Salim a toilet daya da soso daya da sabulu daya dakuma bikiti daya.

 

 

 

 

 

_Zee Elkaseem (Mmn khady) ce_

*ALMAJIRIN GIDANA*

 

 

 

*Writing By*

*Zee Elkasim (Mmn khady)*

 

 

 

 

*Daga Marubuciyar*

 

*Siyasa ko soyayya*

*Alhini*

*Gidan Asali*

*Halin Girma*

*Autar Hajiya*

*Zanen Zuciya*

*Yarinyar Baba*

*Auren tagwaye*

*Wata Uwar mijin*

*Ke Duniya*

 

And now

*ALMAJIRIN GIDANA*

 

 

 

 

*Duk wacce tasan tana karanta wannan novel d’in tayi joining a wannan group din, Dan girman Allah idan ba karantawa kikeba Kuma baki comment kada kishiga Dan kokin shiga zan fiddaki, Kuma bamu bukatar kome sai Wanda yashafi book din idan Kuma bashi zai kawokiba plz kada kishiga*

 

 

 

 

 

 

 

Page 3

 

 

 

 

Hawaye yacigaba da zarya kan fusakarshi wani na bin wani, tashi yayi zaune daga kwancen dayake yace “Fauziyya Ina sonki Ina kaunarki Kuma kota wane hali sai kinzama mallakina”

 

“Sani… Sani… Sani Wai mike damunka? Tun d’azu nake Nan inatama magana Amma kaki kulani sai wasu surutai kakeyi Wanda ni banganeba….

 

Firgigi sani yadawo daga dogon tunanin dayake dakuma surutan dayaketa zubawa mararsa kan gado,

Kallon Basiru yayi sannan ya goge hawayen dake kan fusakarshi yace “uhum ba kome Basiru”

Dafa kafadarshi Basiru yayi yace “tayaya zan yarda da ba abunda ke damunka bayan ga damuwa Nan ‘karara tare dakai, waini sani yaushe kafara boyemin abubuwan dasuka shafeka, nalura dakai tun ranar da kafara aiki gidan Fauziyya duk gaba daya kabi ka canja, narasa gane kanka”

See also  Jinkirin Aure Hausa Novel Complete

 

Murmushi Sani yayi Wanda bai Kai cikiba, sannan yatashi ya dauki buta yazaga kewaye yafito yayi Alwala yayi sallar la’asar,

 

Wata tsohuwar jaka gana yajawo yafara fiddo kayan sakawarshi a ciki, wani wandon jeans ya jawo da wata Riga mai kalar wandon ya kallesu kamar Yana nazarin wani abu a jikin kayan minti 2 kafin yayi wani irin wurgi da kayan zuciyarshi na tafarfasa Natsaneka Salim natsaneka bana sonka natsani duk wani abu daya fito daga hannunka”

 

Wasu riga da wando na yadi ya sanya kalar ruwan hoda, dukda kayan sunji jiki duk sun kod’e Amma wanke suke fess, dan ba laifi sani Yanada tsafta bama zaka kalleshi kakirashi almajiri ba.

 

Basiru ne yasake zuwa inda yake yace “Ina zuwa Kuma mutumina?”

Kallonshi sani yayi yace inafa zanje inda yawuce gidan Fauziyya, kasan duk garinnan banida inda yawuce nan”

 

Murmushi Basiru yayi yace “adaibi sannu da shigema gidan mutane kada asamu matsala, danni wlh bama zan iya aiki gidajeba na kwammace naje kasuwa nayi dako na samu na kashewa”

 

Rab’awa sani yayi ta gefenshi ya wuce, batare daya cemashi kome ba, shima Basiru bayanshi yabi domin tafiya sabgar gabanshi, idonshine ya sauka kan kayanda Sani ya jefar, kwalama Sanin Kira yayi Wanda harya Kai bakin kofa ya juyo,

Basiru yace “wannan ba kayanka bane anan?”

“Nawane banaso ka d’auka idan kanaso” baijira abunda Basiru zaiceba yafice daga gidan.

 

 

Kai tsaye gidan Fauziyya yanufa da sallama yashiga gidan, Fauziyya dake kwance a inuwa ta amsa sallamar tare da tashi zaune “a’a sani Kaine?”

 

“Nine aunty fauzy, sannu da hutawa” “yauwa sani, Amma sani Wai yau mike damunkane d’azu kawanibi ka firgice?”

 

“Bakome aunty ni kaina d’azu narasa miye matslata, Amma yanzu Kinga lafiya Lau nakejina, ga wani farinciki da annashuwa danakeji yanda kikasan anyi mani bushara da gidan Aljannah”

 

“Kai sani baka gajiya, waini sani Ina abokinka?”

 

“Wane kike nufi Basiru ko Tukur,?

Dariya Fausiyya tayi sosai Dan tunowa datayi da drama da akasha tsakanin sani da tukur din Wanda ada shine almajirinta, kafin sanin.

 

“Aunty Fausiyya ai bakisan wani abuba, Tukur fa yanzu yazama abunda yazama dan naji labarin Wai kwaya yake siyarwa”

 

“Kai Dan Allah” Fauziyya tafad’a tare da dafe kirjinta Alamar maganar ta razanata.

 

“Wlh kuwa aunty, Dan kafinma yatafi wlh sata yafarayi, tunda yayo sata shagon wani mutum aka kamashi akayimashi mugun duka yakara gaba, sai kwanaki nakejin labarin Yana siyo kwaya Yana siyarwa”

 

“Oh kace Allah ya tarfama garina nono daya rabani dashi”

 

“Kedai Bari aunty Fausiyya..

 

Sallamar Sadiya kawar Fauziyya ce ta yankemasu firar dasukeyi, da murna Fauziyya ta tarbeta tanayimata oyoyo.

 

Kallon ta Sadiya tayi sannan ta kalli sani dake zaune kallo daya zakayimashi kasan Yana cikin annashuwa da farinciki.

 

“Shigo ‘kawata” tafad’a tana nufar d’aki, Sadiya tabita tana waiwaye tana Kara kallon Sani,

 

Zama tayi kan kujera Fauziyya takwomata ruwa Mai sanyi daga cikin karamin fridge dinda ke dakin.

 

Kallon Fauziyya Sadiya tayi tace “kawata wanene wancan?”

Kallonta Fauziyya tayi tace *ALMAJIRIN GIDANA NE* dafe kirji Sadiya tayi tace “wancen katon shine Almajirinki Fauziyya, ko tsoro bakiji”

 

“Tsoron me zanji, iyakarsa shara da wanke-wanke sai aike idan yakama”

 

“Amma nikam gani nake kamar akwai ganganci d’aukar wannan katon amatsayin Almajiri, yo Fauziyya duka dame Kika girmeshi, Ni wlh danashigo zauren gidan naji firarku wlh nad’aukama Salim dinne, ke fauza ko rantsuwa nayi banzanyi kaffaraba nasan baki girmi wancan yaronba”

 

“Hmm ke nidai banison inskanci, wani Zaki dauka Salim ne, a’a kin manta, yanzu dai ya school?”

 

“Lpy lao wlh, nasameku lpy?” “Lpy lao” haka sukacigaba da firar yaushe gamo, sani Kuma ganin Fauziyya tayi bakuwa maimakon yatafi Amma saiya gyara zama Yana jiran tafiyarta sudasa firarsu, Dan ko Yana barin gidan sai Salim yadawo Shima badan ranshi yasoba.

 

2 thoughts on “Almajirin Gidana Hausa Novel Complete”

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top