Amfanin Citta (Gingger) A Jikin Dan Adam
CITTA: Citta na daga cikin abubuwan da ake amfani dasu wajen girkin abinci da kayan shaye-shaye kamar sobo.
Yana da kyau ayi amfani da CITTA wajen abinci domin taimakon lafiyar jiki.
AMFANIN CITTA:
(1) citta na taimakawa wajen kare ka daga kamuwa da sanyi.
(2) Citta na taimakawa wajen dauke zafin cuta (antianalgestic)
(3) Citta na taimakawa wajen gudanar da yawan siga cikin jiki
(4) Citta na taimakawa wajen kawar da zafin kirji da zuciya
(5) Citta na taimakawa wajen rage kiba.
(6) Citta na taimakawa wajen kare ka da kamuwa daga cutar ”ALZHEIMER”
(7) Citta na taimakawa wajen habbaka gunanar jini a jiki (blood circulation)
(8) Citta na taimakawa wajen rage azabar ciwon ASMA
(2) Citta na taimakawa wajen warkar da cutar daji (cancer)
NB: Domin samun cikakken amfanin citta, sai ayi amfani da danyen cittar.
AMFANIN CITTA ❄
◾ citta tana karawa maza da Mata ni’ima.
◾ citta tana wanke ciki da hanji domin jini ya rinka gudana cikin yanayi mai kyau.
◾ citta tana kare mutum daga yawan yin hudu/fidda iska.
◾ ibn sina yace: citta tana taka muhimmiyar rawa wurin gyara makoshi , ta kuma bada kariya daga kamuwa da ciwon Kai, citta tana bada kariya ga kwayoyin cutar da ake Shaka ta hanyar iska.
◾ citta tana sa jiki yayi zafi
◾ tana magance yanar Ido.
◾ wadda ke sanya mutum ya rinka ganin biji-biji to a nan mutum yana iya rinka cin citta ko a matse masa ruwanta sai a rinka digawa a idon.
◾ tana Kara ni’ima, tana Kara ruwan maniyi ( sperm)
◾ tana bada kariya daga kamuwa da ciwo.
◾ tana sa jini ya rinka gudana cikin kyakkyawan yanayin.
◾ shan ruwan citta yana magance ciwon zuciya, ya kuma sa mutum ya rinka yin numfashi yadda ya kamara.
◾ ruwan citta yana magance rudewar jiki, da kuma fitar da iska.
◾ ama amfani da citta gurin maganin Tari.
◾ ana hada garin citta da zuma a rinka sha don karawa Mata ni’ima da kuma kuzari.
◾ ana hada garin citta da zuma a rinka shafawa a gabobi don magance ciwon gabobi, ama kiran wannan hadin ( paste)
◾ taba maganin masassara da mura.
◾ ama amfani da citta gurin magance rikicewa al’ada.
◾ ama amfani da ita gurin magance wannan tsotsewar jiki.
❇ SA KISHIYA TAGUMI ❇
wannan hadin yana sauko wa mace ni’ima maigida zai ji baya gajiya da Kai miki ziyara.
➡ kwakwa.
➡ dabino.
➡ madara.
ki markada kwakwa da dabino ki tace sai ki zuba madarar peak ki rinka sha Zaki ga abin mamaki
♻ RADADI BAYAN GAMA JIMA’I ♻
wannan matsala na addabar wasu daga cikinsa Mata ba kuma sai sabbin aure ba, har tsofafin hannun, wannan matsalar tana Hana Mata jin dadin jima’i , domin magance wannan matsala sai a nemi
♻ garin hulba.
sai a tafasa sai ki rinka Kama ruwa bayan nan kuna sai ki hada
♻man zaitun da man ridi
ki rinka shafawa a gaban ki, shima namijin zai rinka shafawa a gabansa.
♻ KARIN RUWAN NONO ♻
a dafa furen zogale da zuma, wannan hadin yana Kara ruwan nono sossai.
➡ hulba
➡ sabara
sai ki hadasu ki tafasa ki zuba zuma a ciki ki rinka sha za’a samu ruwan nono.
❄ GA MACEN DA TAKE DA HAWAN JINI LOKACIN DA TAJE DA JUNA BIYU ❄
➡ na’a-na’a
➡ zogale
➡ tafarnuwa
➡ lemun tsami.
zaki hade su guri daya sai ki tafasa ki matsa lemun tsami a ciki ki rinka sha, insha Allah
,
{ lafiya }
AMFANIN CITTA {GINGER} GUDA11
GA KADAN DAGA CIKIN AIKIN TA
1 Citta tana maganin cutar sanyi.
2 Tana sanya kuzari ga jiki.
3 Tana maganin kasala.
4 Kwantar da jijjiyoyin jiki.
5 Rage maiko da kunburin jiki.
6 Ragi zafin cututtukan jiki.
7 Tana maganin ciyon gabobi.
8 Dauki zafin kirjin mutum.
9 Temakama gudanar da jini.
10 Temakama karfin jiki.
11 Warkar da cutar daji.
note -Akan daka citta a rika sanyata a shayi ko miya ko dahuwa.
Leave a Comment