Gyaran Jiki

Amfanin Kanunfari Wajen Gyaran Mace

Amfanin Kanunfari Wajen Gyaran Mace

 

 

 

 

 

 

 

 

 

KANUMFARI

 

Kanunfari kaɗai kika riƙe zaki samu canji a aurenki ƴar’uwa. Kanunfari yana da powers da shi kaɗai zai iya miki maganin abubuwa da yawa na matsalolin da ya shafi jikinki. Ba wai a shayi ko girki bane kaɗai yake da amfani ba. Mai wuyan shine bama iya jure aiki da abu kullum kuma bamu san hanyoyin sarrafashi ya zama effective ba.

 

Kadan daga cikin amfanoninsa:

 

1. Yana hana warin gaba. yana sanya ƙamshin gaba, yana kuma matsesa.

 

2. Yana wanko ciwukan da suke tattare da wurin, yana ɗauke da antibacterial properties da suke kashe vaginal infections.

 

3. Yana saukar da diabetes, yana hana samuwar cholera. Yana bayar da ƙarfin ƙashi. Sannan yana boosting immune system.

 

4. Yana rage zafin ciwo da kumburi. Da kuma ciwon kai mai tsanani.

 

5. Yana taimakawa wurin samun kuzarin sex da saukar ni’ima sosai.

 

6. Yana rage warin baki yana iya curing gembon ciki (mouth ulcer). Yana warkar da ciwon haƙori.

 

Zaki iya hadiyan kanunfari ko kuma ko ki tauna shi. Sannan zaki iya diban shi ki zuba a ruwa ya kwana ki rinƙa sha kofi ɗaya da daddare kafin ki kwanta ko da safe kafin ki ci komai. Yana cleansing jiki da matse farji da kashe cutuka fiye da tsammaninki. Yana ƙara miki dadi most of maganin mata dashi a ciki.

 

Sannan ga mai fama da diabetes ko mai son rage kiba su jika shi tare da cinnamon (girfa) su rinƙa sha.

 

Yanda nake nawa haďin da nake sha ko da safe ko yamma kullum:

 

Ina samun ruwa a gora sai na zuba kanunfari, na zuba busashshen na’a na’a (mint), na saka girfa (cinnamon) sai na watsa Habhan ko Habbahan (cardamom). Ƴar’uwa to wani lokacin sai ina yi ina yin tsallaken ranaku. Saboda zai ƙara miki ni’ima sosai, sha’awa, ga kashe cutuka marasa adadi har da asthma yana ragewa. In kina Numfashi zaki ji iskan numfashinki na da daɗi. Haka nan bake ba warin gaba sai dai kiji wata na ƙorafi.

 

Mai wuyan shine ki san sirrikan sarrafa kanunfari da abubuwan da ake sarrafata. Ba wai yin tsugunon hayaƙinta tare da bagaruwa bane kaɗai amfaninta a’a akwai wasu wallahi da yawa da masu baku magani kaɗai suka sanshi. Wannan kuma ya rage ga mutum ya je ya nemo sirrikan kama mijinsa da shi ya rike.

 

Ƴar’uwarku Sadeeya Lawal Abubakar.

2 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!