Hausa Novels

Amfanin Kubewa Ajikin Dan Adam

Amfanin Kubewa Ajikin Dan Adam:

 

 

 

 

 

 

Mutane da dama suna amfani da kubewa a matsayin miya ba tare da sanin tarin amfanin ta ga jikin dan Adam ba.

 

Bincike ya nuna kubawa na dauke da sinadarai kaman haka:

 

Calories

Carbs

Protein

Fiber

Magnesium

Folate

Vitamin A

Vitamin C

Vitamin K

Vitamin B6

 

Wassu sinadaran sun hada da sinadaran kare cells da kuma lalata ta guba a jiki kaman:

 

– polyphenols

– flavonoids

– isoquercetin

– Lactin

 

Ga kadan daga cikin amfanin kubewa a jikin dan Adam:

 

1- Kara Karfin Gani.

Kubewa yana taimaka wajen kara karfin gani. Ko mai karatu ya san dalili, sabida yana dauke da sinadaran Vitamin A da carotene.

 

2- Yana taimakawa masu juna biyu:

Kubewa yana matukar taimakawa masu juna biyu wajen inganta lafiyarsu da kuma na jaririn da ke ciki, domin kubewa na kunshe da dimbin sinadaran Vitamin B da ke samarwa da kuma inganta sabbin kwayoyin halitta na gina jiki da. lafiyarsa.

 

3- Yana rage hadarin kamuwa da ciwon koda.

Wani bincike da aka gudanar a jamiā€™ar Jilin ta kasar Sin ya tabbatar da cewa, yawan amfani da kubewa na matukar rage hadarin kamuwa da ciwon koda.

 

4- Yana taimakawa masu cutar Asthma.

Kubewa yana maganin cutar wahala wajen fitar da numfashi wato Asthma, saboda sinadarin Vitamin C da ke tattare ta ita.

 

5- Ana amfani da kubewa wajen maganin cutar siga wacce ta zamo ruwan dare a tsakanin al’umma a yanzu. Tana dauke da sinadarin fibre a cikinta, wanda ke taimakawa wajen daidaita yawan siga a cikin jikin dan Adam.

 

6- Inganta Lafiyar Uwar Hanji.

Kubewa na inganta lafiyar hanji da tumbi ta hanyar fitar da sanadaran da ka iya lahani ga hanji ko tumbin. Kuma sakamakon haka ne, ta ke maganin kumburi da cushewar ciki wanda kuma ke rage karfi ciwon siga ko ma maganinsa.

 

7- Kubewa Na Kara Karfin Garkuwan Jiki.

Yawan amfani da kubewa na kara bunkasa tare da karfafa garkuwar jikin dan-adam. akwai wasu Sinadarai dake cikin kubewa masu matukar amfani a garemu da suka hada da, Bitamin C da ‘Calcium’ da ‘Magnesium’ dake taimaka wa wajen yaki da kuma fatattakar duk wata cuta da ka iya kai wa jikin mutum farmaki.

 

8- Yana maganin karancin jini.

Yana matukar maganin karancin jini a jiki domin kubewa na kunshe da sinadarin Iron sosai. Kuma yawan amfani da kubewa na sanya idan ka ji rauni jini ba zai zuba da yawa har ya yi wa mutum lahani ba.

 

9- Gyaran Fata.

Ga mai son kara inganta fatan jikin sa ya yi laushi da santsi kamar yaukin kubewar toh ya lazumci amfani da ita.

 

10- Rage Hadarin Kamuwa Da Ciwon Zuciya.

Kubewa na wannan aiki ne saboda wani sanadari da take kunshe da shi da ake kira ‘soluble fibre’ a turance, wanda ke taimakawa wajen rage ‘cholesterol’ wanda hakan ke rage yiyuwar kamuwa da ciwon zuciya.

 

Lafiya uwar jiki

Leave a Comment