Amfanin Lalle Guda 30 A Wajan Dan Adam
2: lalle yana maganin ciwon hakori da warin baki da kuma tsatsar dake jikin hakora…idan aka dafa lalle da ruwa sai aringa kuskure baki dashi. Sannan a samu garin lalle da kanunfari da gawayi adakasu tare aringa goge baki dashi yana kara karfin hakora sosai.
Duba Hotunan Lalle Masu Kyau anan
3: lalle yana maganin ciwon kafa musamman irin kakannimmu da iyaye jijiya ta rike gwiwa za’a kwaba lalle a kunsashi a gwiwa sai a rufe da Leda ko babdeji abarshi Na tsawon awa biyu ko daya sannan a cire, bayan ancire sai ‘a samu albabulnat adafashi a ruwan zafi sai a samu towel aringa dannawa a kafar sai ahada ruwan kal da zaitun asa garin lalle ahada sai a ringa shafawa a kafar yana maganin sosai domin mungwadashi.
4:lalle yana maganin cin ruwa Na kafa idan aka lalle da ruwan kal ko afram sai asa a kafar.
5:lalle yana maganin ciwon huhu idan aka samu ganyen danyen lalle guda uku 3 sai a dafashi sannan asaka sugar ko Zuma asha yana maganin ciwon huhu.
6:lalle yana maganin warin kashi da xakaji mutun yana wari da tsami idan akaje wanka sai aringa dafa lalle yana kara wanke jiki dashi yana maganin warin kashi sosai.
7:lalle yana maganin jiri(ajijiya) da mutun yakeyi idan aka dafa lalle asaka Zuma maikyau asha.
8:lalle yana kara karfin farce da maganin tsagewar hannu ( Dan uba) idan aka yawaita lalle a hannu ko kafa.
9:Ana Shankar lalle a hanci yana buda kwakwalwa..
10:Ana samun ganyen lalle guda uku ko biyu a jika a Kofi a idan yajuku sai asa sugar asha amma ba’a karasha sai bayan kwana biyu yana maganin ciwon koda.
11:Ana dafa lalle da Zuma mai kyau aringa sha yana maganin hawan jini da bugun zuciya wallahi angwada angani.
12:Ana shafawa kuna lalle idan mutun ya kone ko yaji rauni sai a samu kal tuffa a goga agun sannan a barbada garin lalle akai kunar xai kame sosai.
13:Ana samun ganyen lalle guda 20 sai a samu ruwa cikin kwanon San ruwa daya sugar gram 10 ko 20 ajika a ruwan a ringa sha tsawon kwana 40 yana maganin kuturta insha Allah.
14: yin lalle a kafa yana budewa mace kofofin jini, musamman macen da jinin al’ada yake mata wasa wata biyu ko uku sannan yadawo to wallahi yin lalle a kafa tana magancewa basaikin he Neman maganiba kugwada.
15: lalle yana maganin kurajan jiki daji ( Cancer) idan aka hada lalle da man shanu aringa shafawa a jiji.
16:lalle yana maganin ciwon Mara ko cikin lokacin da mace take jinin al’ada idan tasamu garin lallen saita kada aruwa tasha.
17: asamu ganyen lalle guda 3 da furan lalle da Zuma ajika su akofi da ruwan zafi asha yana maganin mura.
18:a hada garin lalle da kal aringa shafawa akai yana maganin ciwon kai.
19: idan mutun yana habo jini yana ta zuba yaki tsayawa sai a kwaba lalle a Dora akan hancin insha Allah jinin zai tsaya.
20: matar auren da tafiya budewa zata samu lalle ta kwaba da ruwan dumi ta saka agabanta Na tsawan awa biyu sannan ta cire tawanke da ruwan dumi yana matse mace sosai.
21:lalle yana maganin rauni Na ciwon sugar idan mai ciwon sugar yaji rauni yakan Dade bai warkeba to idan aka kwaba lalle akasa agun zai warke insha Allah.
22:a dafa lalle tare da ruwan kal sai aringa shafawa a baya yana maganin ciwon baya ko kiringayin irin yanda shafawa idan kai yana ciwo.
23:ana shawa jariri lalle idan anhaifeshi kafin aimasa wanka ashfa masa lalle Na tsawon mintuna biyar ko uku yana maganin cututtuka.
24:Shafa man lalle a karaya yana hade karaya akwai man lalle.
25:ana hada lalle da man wardi ko man lalle ashafawa me cutar barin jiki.
26:ana hada lalle daman kahhh poor ba kafurba sai anja kahhh poor yana maganin sanjin kashi.
27:ganye lalle guda biyu da ruwa Rabin Kofi da sugar tea spoon asha yana maganin shawara.
28:lalle yana Magani karyewar gashi asamu garin lalle kwatan Kofi da garin habbatussauda cokali 3 da cokali 3 Na ruwan dumi ko a tafasa ashafa akai Na awa 3 ko 4 sannan a wanke…..idan kuma gashi bashi da karfi sosai sai a sai asa lalle Rabin Kofi da cokali biyu Na wardi sai ruwa kramin Kofi sai ashafa Na awa 1 ko biyu sannan a wanke.
29 Ana hada lalle da Zuma ashafa agashi yana gyara gashi sosai.
30:Ana hada Lalle,Zuma,Manja,Hulba Da kwai Ashafa ajiki sannan ayi steaming da ruwan zafi (aturara jiki) yana yaran jiki sosai.
31: ana shafawa gawa lalle yana gyarata…..
Wannan faida Dan Allah idan ka karanta to kawatsama duniya domin anfanuwar Alummar musulmi…
thanks you so much we do appriciat
Alhamdulillah.
Allah yasaka da alkhaire, mal.za’a iya fada min WASU littafin da Samu WASU bayanai game da Islamic chemist da sauran Su .