Aminiyata ce Hausa Novel Complete
AMINIYATA CE
(Bazan barta ba)
MALLAKIN UMMU JUWAIRIYYAH (SahibarRoyal Star)
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Alhamdulillahi I’m back again
Wannan book sadaukarwa ne ga dukkan wata yar K’ungiyar Royal, love you guy’s to the moon and back
بسم الله الرحمن الرحيم
Page 1/5
_______________”Umma ki tayani murna Abbansu Nadra ya sake biya min school fees dina wallahi a karo mara adadi yau Umma I’m really happy, shi dai Abba baya gajiya, wai ni Umma me yasa Abbansu Nadra yake sona haka? Infact ba ma shi ka dai ba, Umma har da Mommyn Nadra tana matukar ji dani ko me yasa?” Cewar Khadija wace ta cika da murna sosai.
Wace ta kira da Umma murmushi tayi tare da ce wa “Khadija ke nan, to ke baki san abunda yasa iyalan gidan Alhaji ke sonki ba?, Ai baya rasa nasaba da soyayyar dake tsakaninki da Nadra, uhm Khadija kin san Nadra tana k’aunarki sosai ni gaskiya a tunanina Amintakan dake tsakaninki da Nadra shi yasa iyayenta suke k’aunarki” Umma ta fad’a ya yin da take kallon Khadija.
Littafan Hausa Novels Guda 1000 masu dadi
Matar Makaho Complete Hausa Novel
Hotunan Lalle Masu Kyau Kunshin Gam
Hajiya Gwale Hausa Novel Complete
Tsofaffafin Hausa Novels Watpadd
Khadija shiru ta yi tana nazarin maganganun mahaifiyarta, tabbas kuwa haka ne, domin Khadija da Nadra Aminan juna ne sosai tun suna yara, tare suke zuwa islamiyya haka ma a tare suke zuwa boko, komai nasu iri daya tamkar wasu tagwaye, Nadra da Khadija suna matukar son junansu sosai, duk da ce wa iyayen Khadija talakawa ne ya yin da iyayen Nadra masu arziki ne sosai, Alhaji Abdulsalam waton mahaifin Nadra hamshakin mai kudi ne sosai, ya yin da Malam Mustapha mahaifin Khadija tallaka ne, sai dai alhamdulillahi akwai rufin asirin Allah, wannan ke nan.
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
Kamar koda yaushe Nadra ta gama shiri sab a cikin uniform dinsu na makaranta, ta yi kyau sosai saukowa tayi daga saman bene zuwa down stairs, Mommy ce zaune tana kallo “My dear kin sauko ke nan? To a zo a yi breakfast ko?” Cewar Mommy, “no Mommy no need idan na je School za mu yi tare da Khadija” Nadra ta fada ya yin da take mikawa mahaifiyarta ta hannu “Mommy baki bani kudin P.T.A din ba” cewar Nadra, “Ai baki zan yi ko? Take it easy now” cewar Mommy.
“Okay to Mommy yi haƙuri” Nadra ta fada Mommy bata sake ce komai ba, mika mata kudin tayi, gani na yi Nadra ta bata fuska “what is it again? Me kuma ya faru?” Cewar Mommy, “to Mommy baki bani na Khadija ba” Nadra ta fada ta na mai bata cute face dinta, Mommy dariya ta yi ya yin da ta ce “ai na san za a rina, to ai ita ma ga nata ko?” Cewar Mommy ya yin da ta sake bata wasu kudin, Nadra dariya ta yi domin kuwa ta ji dadi sosai, “yauwa Mommy nagode sosai Allah ya biya, ni na tafi sai na dawo” cewar Nadra, “Alright my dear ki gaida Mamansu Khadija” ficewanta tayi ba tare da ta amsa mata ba.
Da sauri ta je ta rungumeta tamkar wadan da suka shekara basu ga juna ba, “Umma ina kwana” cewar Nadra tana dan rukusawa, Umma amsa mata tayi da sakin fuska “Nadra ya gida ina Mamanku fatan kowa na lafiya” cewar Umma, “Umma kowa lafiya kalau alhamdulillah” Nadra ta fada, “Umma zamu wuce sai mun dawo” cewar Khadija ta na mai rike hannun Nadra, da Allah ya kai ku lafiya Umma ta bisu, dukkansu gidan baya suka shiga ya yin da driver ya ja su, sai Excellent International school ya kaisu.
<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<
Firansu suke hankali kwance cikin Motar har suka kawo school, sosai suke maida hankali ga karatunsu sam basa saka wasa a karatunsu. Haka Nadra da Khadija suka cigaba da rayuwarsu in da kullum sai kara son junansu suke.
Yau ma kamar kullum Nadra shiri ta yi cikin uniform ta sauko kasa “Mommy na gama shiri, to yau wa zai kaimu makaranta since har yanzu Baba driver bai dawo ba” cewar Nadra ya yin da ta bata fuska, “Hhhhhhhhhh” Mommy dariya ta yi tare da ce wa “to sannu rigimatu ai yau since Baba is absent kamata ace medullar oblongata dinki ya shaida miki ni din ce zan kaiku” cewar Mommy tana kallon y’arta ta, Nadra dariya ta yi sosai sannan ta ce “to Mommy ke da kanki zaki kaimu yau kuma?” “E mana ko kuma da matsala ne?” Cewar Mommy, “A’a wallahi ba matsalar komai” Nadra ta fada ta na mai yin murmushi.
Fita su ka yi zuwa parking space, suka shiga motar nan Mommy ta jasu as usual gidansu Khadija suka fara nufa, koda suka je Nadra da sauri ta sauko daga cikin motar tun kafin Mommy ta ida parking, gaida Umma tayi in da Umma ta amsa mata da murmushi da sakin fuska, ita ma Mommy saukowa tayi suka gaisa da Maman Khadija cikin mutunci nan fa Nadra ta ce da Ummansu Khadija “Yauwa Umma don Allah ina son mu yi magana dake”………
<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<
“To y’ata gani ina jinki” cewar Umma, “Umma don Allah so nake yau ki bar Khadija ta kwana a gidanmu gobe zamu je bukin Birthday din Salma diyar kanwar Mommy” Nadra ta fada, “Au to ai Nadra ba komai da gidanku da nan gidan ai duk gida ne ba komai na amince ta kwana din, Allah yasa mudace” cewar Umma ta na mai yin murmushi Mommy ita ma murmushi tayi.
Ita kuwa Nadra sosai ta ji dadi yau Khadija zata kwana a gidansu, nan dai suka shiga motar Mommy ta jasu sai a harabar makarantarsu ta saukesu, ajin da naga an aka rubutawa S.S 2 blue naga sun nufa, ba tare da bata lokaci ba nan da nan suka fara karatu domin kuwa tuni Malaminsu har ya fara karatu domin kuwa son so makara yau din nan…..
MINIYATA CE
MALLAKIN UMMU JUWAIRIYYAH (SahibarRoyal Star)
ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Alhamdulillahi I’m back again
Wannan book sadaukarwa ne ga dukkan wata yar K’ungiyar Royal, love you guy’s to the moon and back
بسم الله الرحمن الرحيم
Page 6/10
___________Karfe 2:00 dai-dai aka tadasu basu fi minti biy’ar ba sai ga driver ya zo d’aukansu da yake yau bazasu kai Khadija gidansu ba direct unguwarsu Nadra ya nufa dasu wato Arkillah, koda suka isa gida Mommy bata nan ta fita unguwa nan dai suka cire uniform dinsu suka shiga yin assignment dinsu.
>>>>>>>>>>>>>BAYAN SHEKARA BIYAR<<<<<<<<<<<<
“Don Allah Faruk ka yi haƙuri, wallahi mun riga da mun yi alkawari da Khadija rana daya za mu yi aure ka kuwa ga bai kamata na sa’ba alkawari ba, pls Yaya Faruk” Nadra ta fada kamar za ta yi kuka.
Faruk sa bo da tsananin haushi ko tanka ta bai yi ba ya tashi ya tafi abun shi, ita kuwa Nadra bata ji dadi ba amma ya za ta yi gaskiya ita bata ganin za ta iya sa’ba alkawarin dake tsakaninta da aminiyarta ba.
Yau kwana biyu ke nan Faruk ya daina kiran Nadra ko ta kira shi baya daga kiranta, Nadra abun na matukar damunta a gaskiya ta na son Faruk fiye da tunanin mai tunani amma gaskiya bata ji za ta iya barin Khadija ba, ya ma za ta yi aure ta bar Khadija, khadijar da ko saurayi batada a gaskiya sai dai su yi aure a lokaci daya.
<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<
“Ku dai ga yanzu ku din ba yara ba ne ba, don Allah Khadija ku tsaida miji a muku aure, wallahi aure shi ne martabar mace kuma shi ne mutuncin y’a mace, fine kun gama karatu har aiki kun fara to me yayi saura banda aure iyeee?” Cewar Mommy rai a matukar bace, “don Allah Mommy ki yi haƙuri in sha Allah very soon zamu tsaida miji” Khadija ta fad’a a ladabce.
“Okay to shi kenan Khadija Allah ya baku na gari, don Allah kar ace sai mai kudi pls” Mommy ta fada, “in sha Allah Mommy karki damu” cewar Nadra, Mommy hararanta tayi ba tare da ta sake ce komai ba.
Nadra hannun Khadija ta ja suka fice dakinsu.
<<<<<<<<<BAYAN WATA BIYU>>>>>>>>
“Wai ke Khadija sai yaushe zaki gabatar dani awajensu Umma pls Khadija make it snappy now, wallahi ina matukar sonki da aure ne my dear na fison nan da wata shida a d’aura muna aurenmu” cewar Safwan saurayin Khadija, “Laaaa Ya Safwan gaskiya ba yanzu ba don Allah ka d’an kara min lokaci pls” cewar Khadija ta na mai marairace masa fuska, “Khadija kamar ya ke nan ban gane ba? Ohh shi ke nan kin daina sona ko?” Cewar Safwan rai a d’an bace, “ayya Yaya Safwan ba haka ba ne ba, kawai ina son ayi bukinmu da Nadra rana daya ne”.
“Okay shi ke nan na fahimce ki, amma nan da wata nawa ke nan?” Cewar Safwan, “Uhmmmmm to Yaya Safwan nan da shekara daya fa?” Cewar Khadija, “Ohhh my God gaskiya nan da shekara daya Khadija an dade sosai don Allah nan da wata takwas dai” “okay to shi kenan tunda haka kake so” cewar Khadija, nan dai suka cigaba da firarsu ta masoya.
Nadra kam yanzu batada saurayi domin kuwa tuni Faruk ya rabu na ita a tunanin shi Nadra sam bata sonsa tunda bata son shi da aure, tuni har taga invitation aurensa ai kuwa a ranar da taga invitation shi sosai ta yi kuka kamar ranta zai fita, Mommy kuwa ba abunda tayi bata face gwai, ya yin da Khadija ce mai lallashinta.
<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<
Nadra kam sosai ta ci kukanta mai isarta don kuwa ko kadan bata ji rarrashin da Khadija ke mata, “Yanzu shi ke nan Khadija Faruk aure zai yi, kina ganin ya min adalci kuwa? Wallahi Khadija Faruk ya ci amanar soyayyata agareshi ya ci amanar soyayya….. Bata ida fad’a ba kuka ya ci k’arfinta.
“Don Allah Nadra ki yi haƙuri pls, don ALLAH ki yi haƙuri ki daina wannan kukan pls” Khadija ta fad’a kamar ita ma za ta yi kuka, da kyar ta iya tsaida kukan nata, nan Khadija ta ce da ita “pls Nadra ki shirya mu je in da Umma kwana biyu bamu je ba” “Haka ne kuma Khadija to je ki shirya ni haka zan je” cewar Nadra, “Okay to shi kenan.
Nan suka shirya suka je gidan Umma sosai suka wuni a gidan in da ita ma Umma nasihar ta guda shi ne suyi su fidda mijin aure lokaci na tafiya, ita ma dai nuna Mata su ka yi in sha Allah sun kusa fitar, nan dai ta musu fatan samun na gari mai albarka, da “Ameen” suka amsa mata.
<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<
“Don Allah Nadra naji wani zance ne daga bakinsu Ilham to shi ne nake son ki karyata min wannan zance din” cewar Minaufa kawarsu Nadra “Ina jin ki wane kalar zance ke nan?” Nadra ta fada tana mai son jin abunda Minaufa zata fad’a, ita ma Khadija sosai ta bada hankalinta.
“Wai ce wa su ka yi kin ce bazaki yi aure ba har sai Khadija ta samu miji sai kuyi aure a rana daya wai haka ne?” Minaufa ta fad’a tana mai son jin amsar da Nadra zata bata, “E mana sai kuma me?” Cewar Nadra tana mai hararan Minaufa, “Iyeeeee ashe basu yi miki karya ba, lalle ma Nadra waya ce miki har yanzu ana irin wannan amintaka, lalle sai yau na kara tabbata sam bakida wayo, ni yoo ko yan biyu ban taba jin sun ce za su yi aure a rana daya ba balle ku da ba yan biyu ba lalle yakamata ki yi tunani haba ku dinga bawa junanku shawara mana” cewar Minaufa rai a bace.
“Ke Malama ya isa haka nan”…. Cewar Khadija ita ma rai amatukar bace, “wai ina ruwanku da mu ne? Ina ruwanku da rayuwarmu wallahi idan baku daina sa muna ido ba to gaskiya zaku raina kanku ne don kuwa ba za mu yi muku mai dadi ba” cewar Khadija ta na mai watsa mata harara.
Ita ma Nadra kara mata tayi da ce wa “To sannu bakar munafuka to an ki ayi auren, nace an ki ayi auren ko zaki saka ayi d’ole ne, to bara na gaya miki wallahi Khadija *AMINIYATA CE* kuma bazan yi aure na barta ba kinji na gaya miki stupid kawai”…. Nadra ta fada ya yin da ta fice daga wurin a fusace, ita ma Khadija bin bayan Nadra ta yi, ya yin da suka bar Minaufa tana mai yin mamakinsu….
Leave a Comment