Hausa Novels

Amrah Macijiya Hausa Novel Complete

Amrah Macijiya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

AMRAH MACIJIYA

 

By Rabeauty

 

*In the name of Allah, the most beneficent, the most merciful.

*Seeking for guidance and protection of Allah as i am going to start ❤️

Ya Allah!!!

Guide my heart, and protect my hand to the end of this book, AMEEN.

 

💫 Page 1💫

Kano state.

A wani kauye Wanda ake kira da tigadam, wata yarinya na hanga a bakin rafi xaune tana kallon ruwan rafin duka duka yarinyar baxata wuce shekaru goma sha biyarba,tashi tayi tana karewa gurin kallo, koh ina bishiyoyine koraye 🌳🌳masuban sha’awa, hanyar gida ta nufa kallo daya xakayiwa tafiyar ta kasan cewa wannan yarinyar ba cikakkiyar mutum bace sbd yanda take wata irin lankwasa, iskace tayaye mayafinda ta rufe fuskarta dashi,subhanallah, wannan irin kyau haka, yarinyar kyakkyawa ce kyan karshe idanuwanta Green ne gata fara kal yanda take da kyau xakasan cewa ba mutum bace,girgixa naga tafarayi Wanda ya matukar bani tsoro kafin kiftawar gira naga ta rikide ta xama shirgegiyar macijiya Green 🐍🐍🐍 sai sheki takeyi, cikin kauyen ta nufa tana kaiwa gurin wata kofa ta girgije ta xama mutum, da sallama ta shiga gidan, wata yar tsohowa dake bakin murhu tana ixa itace ta amsa, hade da fadin “wai ke AMRAH ba daman ayi miki fada saiki dau fushi ki wani fita dg gida kamar wata iska, waima daga gidan ubanwa kike? Karasuwa AMRAH tayi tana murmushi Wanda yakara fito da kyanta, tace” haba gwaggonah bafa fushi nayiba kawai dai fita nayi har kigama mitanki sannan na dawo”cikin kwantarda murya gwaggo tace “yar jikalle kinsan dai banason yimiki fada kece bakyayin mgn, dan Allah kikiyaye abunda xaisa na miki fada kinji, toh gwaggo inshaa Allah xan kiyaye, yawwa yar albarka, tashi tayi ta kara share gidan, ita kuma gwaggo tana kwashe abincin a cikin langa, ta xuba musu sauran a cikin kwano.

Bayan sungama Cin abincin saiga harira kawar AMRAH tabiyo mata su tafi islamiya, gaida gwaggo tayi sannan ta kalli AMRAH tana cewa “lalle AMRAH bakima shiryaba kuma kinsan yau malam abu ne xaiyi mana karatu kuma yace uku tayi mana cikin aji gashi ynx har 3:30 kuma nasan kafin mu isa hudu tayi kuma……. Xancenne ya makala sbd wani irin kallo da AMRAH tayi mata shiya hakana ka rasa xancen sbd tana balaaa’in tsoron idanun AMRAH shiyasa bata fiya kallon taba sbd idanunta green neh kuma kwayar idanunta farine ita harira har tunanin take anya AMRAH mutunce kowa, tashi amrah tayi ta shiga dakinsu batafi 5 minute bah ta fito cikin shirin islamiya, muntafi gwaggo, Allah yatsare gwaggo tace, Amin ta amsa hadi da Jan hannun harira suka fito suna isowa bakin soro ta dakko nikabinta ta saka sbd yadda idanuwanta suke, ba Wanda yataba ganin complete face dinta daga gwaggo sai harira, sbd duk Wanda yayi toxali da kwayar idanunta toh sunansa gawa, duk kauyen ba Wanda yataba ganin idanunta dg hancinta sai bakinta kawai mutane suka gani, suna isa malam abu ya tsakar dasu wai sunyi latti baxasu shiga ajinba, harira tashiga bashi hkr ita kuma amrah koh kallo be ishetaba abunda ya kara harxukashi kenan kuma yau yadau alwashin sai yaga fuskarta, harira kadai ta shiga aji ita kuma amrah yace tarage tsawonta a cikin rana, bayan yagama karatu ya fito ya nufu inda take ya shauda mata bulala koh gixau bata yiba ya kara shauda mata still bata mutsaba abun ya kara harxukashi yaci gaba da dukanta saida ya gaji Dan kashi ya kyaleta, ita kuma amrah idanunta sun kara rikidewa sun xama green sosai, hannu yasa ya taxge nikabinta da sauri yaja Baya sbd toxali da yayi da idanuwanta nan danan jikinsa yafara makarkata yama kasa mgn,ita kuma ta kafeshi da idanunta, da sauri yabar gurin, harira na karasowa ta kama hannunta suka nufi gida.

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Bayan sallar isha’i amrah ta fice daga gidan gwaggo ma bata saniba, hanyar da tasan malam abu nabi ita ta nufa ta haye saman bushiya tana jiran isowarsa, aiko ba’a dadeba saigashi yabiyo da yar fitilarsa, aiko tayi sauri ta diro daga kan bushiyar rabin fuskarta rufeda Green din mayafi, yana isowa ya tsaya yana yadata da fitilarsa gabansane ya fadi dashi ya xata aljanace amman saiyafi fuska ya basar hadi da cewa “ke malama jayemin akan hanya tayi mishi banxa aiko yahau xaginta, amatsayinsa na malami amman yana xagi, can kuma yace waike wace irin dabbace, a harxuke tace” MACIJIYA 🐍”hade da yaye mayafin fuskarta, tashiga yin wata irin jijjiga nan take taxama shirgegiyar macijiya🐍 green sai sheki take, nan take malam abu yafara fitsari a wando, wata irin dariya ta sheka da ita sannan tace” malam abu kayi kuskuren dukana da kuma xaginta, a yau dinnan xan kasheka kuma ynx, kafin yayi mgn tayi sufa ta laulayeshi tashiga sararsa ta Ko ina ihu yake amman ita koh a jikinta saida ta tabbatar baya numfashi sannan ta kyalesa, a takaice dai ta kashe malam abu, anan tabar gawarsa tayi ficewarta xuwa gida.

AMRAH dai muguwace ta karshe amman bata fiya kisaba sai idan antabota, tohfa koh waye yatabota xata kashehe illa mutum biyu,Gwaggo da kuma harira”.

 

💫Rabeauty 💫

[16/08, 10:01 am] +234 907 976 8094: 💫AMRAH MACIJIYA 🐍🐍🐍💫

 

By Rabeauty 🥰💫💫💫💫💫💫

 

Page 2

Labarin mutuwar malam Abu ya riski kowa dake kauyen, hankalinsu ya matukar tashi dasu kaji cewa macijine ya kashe shi.

A fadar mai gari kuwa kowa ya taru ana jiran iliya mai macixai yaxo, yana isowa a kace ya bude macixai nai a duba bakin su aiko aka duba amman sarar batayi kama da bakin macixanba, haka aka taro akayiwa malam abu wanka da sallah aka kaishi makwancinsa.

Washe gari amrah tana daki tana bacci gwaggo ta shigo ta tayarda ita tana cewa”yar jikalle tashi Dan Allah na aikeki gidansu harira ki karbomin daudawa gurin innah”toh gwaggo ta tashi ta fito bayi ta shiga ta wanke fuskarta ta fito ta dauki mayafinta Green tasaka ta nufi gidansu harira, tana xuwa ta tararda harira na wanke_wanke gaisawa sukayi sannan ta nufi inda innah suka gaisa sannan tagaya mata abunda gwaggo ta aiko ta karba, bata tayi sannan ta fito xata wuce harira tace “amrah bayan la’asar xanxo mutafi rafi, toh kawai tace tafice daga gidan, a hanyarta ta komawa gida taga wasu samari su biyu suna mgn kuma akan mutuwar malam Abu ne, dan tsayawa tayi Dan taji me suke fada, dayanne yace” hmmmmm ni wlh wannan abun yafara bani tsoro ace anrasa gane wane macijine ke wannan kisan har yau”dayanne yadafa kafadarsa yana cewa “nima dai abun yafara bani tsoro, amma ai gobe ne maigari yace maccido maciji xaixo da kuma magani, kowa dake kauyen nan xa’a bashi yasha, duk Wanda a maciji toh yanashan wannan maganin xai fara rikidewa, kuma na rantse muddin wannan macijin ya kasance acikinmu toh wlh saina kashe shi har lahira wlh, gaban amrah ne yafadi saikuma naga tana wani shu’umin murmushi Wanda daka gani kasan bana alkhairi bane, gida ta karasa tana xuwa tabawa gwaggo daudawarta ta shige daki, da kallo gwaggo tabita sbd taga yanxu duk ta canxa kamar ba amrah taba, ynx mugun halin shiga daki tabijiro dashi, girgixa kai kawai gwaggo tayi ta tashi tashiga bayi, tana fitowa ta dauro alwallah ta nufo dakin, ta tayarda sallah, tashi amrah tayi itama tayi alwallah tayi sallah, bayan sun idar amrah ta juyo ta fuskanci gwaggo tace “waini gwaggo meyasa me gari xaice sai wani maccido maciji yaxo yabawa kowa magani, meyasa su baxasu yi bincikeba tukunnah ai…… Wani kallo da gwaggo tayi matane yasata kasa karasa xancen, waike amrah yaushe xaki fara tausayin mu ke kwata kwata bakida tausayi damuwar mutane bata damekiba, waini kam wace irin xuciyace dake, nidai nasan cewa baban ki da mamanki ba haka sukeba kuma nima dai ba halina kika biyoba, dan Allah amrah ki gyara kinji kuma gobe maccido xaixo da karfe biyar dan haka tun karfe 4:30 xamuje fadar mai gari kinajina, kai kawai ta daga.

Bayan sallar la’asar harira tayi sallama tashigo, gaida gwaggo tayi sannan suka fice xuwa rafi, suna tafe suna yar firarsu, can dai harira ta kasa hkr tace “waini amrah na tambayeki? Eh kawai tace, harira tace” wai meyasa naga tafiyarki ba irin tamu bace kina tafiya kina wani lankwasa kamar macijiya, dariya amrah tayi sannan tace “toh ai macijiyar ce” dariya harira tayi tace da baki fadaba wlh, shiru amrah tayi bata kara cewa uffanbah, suna isa bakin rafin suka xauna kafafunsu sukasa a cikin ruwan, wasu samarine su uku sukaxo wucewa dayanne ya hangesu yayi saurin tabo su yana cewa kai kunga wasu yam mata, dayan ne ya juyo yace kai ashe yau xansha dadina da yammatan nan, karasawa suka yi gurin su, da isarsu suka fara yimusu iskanci.

Harira ce tace da ganinku ba’a yankin nan kukeba Dan haka Dan Allah ku koma yankin ku, dariya suka sheke da ita dayan yasa hannu ya fixgo harira ya mannata da jikinsa ya shiga shinshinar wuyanta dayan kuma amrah ya cafko yana kokarin yaye mayafinda ta rufe fuskar ta dashi, amman yakasa wani wawan Mari yabata wadda saida gefen bakinta yafashe, harira kuma har sun kaita kasa suna kokarin daga mata riga, jin suka yi ance “ku kyaleta da wata irin murya” Wanda yamare tane ya juyo yace ke yimana shiru, kuma damun gama da ita kanki xamu dawo Dan haka kishirya, ya juya ga harira wadda tariga data sadakat sbd harya cire wando, hucin maciji suka ji a bayan su, ai da sauri suka saki harira suka juyo, wani irin raxanannen ihu suka saka a tare, sbd toxalinda sukayi da wata shirgegiyar macijiya green 🐍, harira mah tsoro ne yakamata nan tashiga neman amrah amma bata gantaba, jin sukayi macijiyar tace “saida nayi muku kashedi amma kukaki ji Dan haka dolene na kashe ku, kafin suyi wani yunkuri gaba daya tabi ta saresu nan take suka xube matattu a gurin, gurin harira tayo, harira koh harta juya xata fece taji tace” tsaya “ai da sauri ta tsaya, karasuwa tayi gurin ta, sannan ta girgije takoma mutum, ai harira na ganin AMRAH nan take ta sumee a gurin.

 

Rabeauty

*please vote, comment, and share *

 

 

 

Name: [My Novels (www.mynovels.com.ng)]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022

 


Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na TelegramPowered by: www.mynovels.com.ng

7 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!