Crypto currency

An cire manhajar Pi Network daga Playstore

An cire manhajar Pi Network daga Playstore

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Pi network

Shafin dandalin manhajojin wayar android mallakar kamfanin Google wato PlayStore ya cire Application din PI Network daga cikin Kasuwar sa.

 

Biyo bayan Bincike na gani da ido a yanzu haka babu manhajar a shafin na Playstore.

 

 

Ku karanta Abunda ya kamata ku sani game da Crypto Currency

Shin me hakan yake nufi? To ga bayanin dalla-dalla.

 

1. Ita mas’alar cire application daga PlayStore idan muka duba irin wannan yanayin zamu iya cewa kodai su masu PI din ne zasu sauke shi domin yi masa gyara, wannan kuma tsohuwar hanya ce da ake updating na applications yanzu directly ake yi.

 

2.Ko kuma, su shafin ne na PlayStore suka cire application din sakamakon wata matsala.

 

3.Wannan kuma ba wani abu bane da za’a damu, naga tuni wasu sun fara musayar maganganun na Shirme, masu yi don raha ni ban damuwa da hakan, amma masu daukar zafi to za’a yi amfani da raunin ku wajen tunzura ku.

 

4.Idan suka ga dama zasu iya cewa ba zasu kai application din su kowanne application store ba (Playstore ko Appstore), suyi hosting nashi a site nasu, a rika saukewa daga can.

 

Shikenan fa. Ƙarfi da yaji yanzu idan kana son gano weakness na mutum ka taɓo shi da maganar PI, wannan ai sakarci ne!

 

Ni a wannan shafin ban yarda mabiyansa su rika zama marasa wayewa ba game da duniyar ilimin fasaha, kimiyya, Kiripto, zamantakewa a Duniyar metaverse ba.

 

Mustapha Gfatu

(Dan Fafutuka)

 

 

Pi network

Leave a Comment

error: Content is protected !!