Hausa Novels

An cuci Hijabi Hausa Novel Complete

An cuci Hijabi Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

ANCUCI HIJJABI*

 

*True life Story*

 

*deena m usman*

 

 

 

 

 

 

TALENTED* _WRITERS_ _FORUM

*had’in kanmu shine alfaharinmu*

 

 

 

 

 

 

*Writen by

fayeeeeeeex m usman*

 

 

 

 

 

 

 

*godiya ga allah mad’aukakin sarki da yabani damar fara wannan labarin lpyh,inaroqan allah da sunayanka tsarkaka akan kanufeni da rubuta alkairi duk abin dayake sharri sarki ubangiji kar kabani ikon rubutashi…Allah kayi salaty da sallama da masoyinmu Annabi muhammad S.A.W

da iyalanshi da sahabbanshi damu al’ummarshi*

 

An cuci Hijabi

 

*ban tsara lbrin dan cin zarafi ga kowaba,gargad’i banyarda ajuyamin lbr takowacce sigaba wanda kuma yayi shida Allah*

 

 

*pg1*

 

_kotun ta yi tsit, kowa ya yi jigum, ana sauraran abinda xai fitodaga bakin alkalin wanda yasunkuyar da kansa yana rubuce-rubuce,Lauyoyi dasauran ma,’aikata wadanda suke da alhakin zama akotun sbda sauraron shari’ah, kowanne yana xaune amazauninsa daya dace dashi,haka y’an kallo wanda zuffa tagama wankesu,hakama yarinyarda ake gudanar da shari’ar a kanta al’amarin yan ba kowamamaki shiyasa indai mutum yakalli fuskokin kaso tara cikingoma na mahalarta kotun sai kaga kowa cikin matsananciyar damuwa musamman wadanda abin yashafa, iyayenta da yanuwanta knan.mai shari’ar wanda ake da sunan hafiz adam ilyasa yadaga kansa hankaliyadubi wacce ake ka ra tana tsaye inda aketsaida wad’anda ake tuhuma .har yanzu dai Hijjabinne ajekinta,idanunta sunyi jajawur kanta sunkuye dagaba d’aya hankalinta atshe yake gawani ciwon kai da yatasota agaba gamatsanan ciyar da muwar da tabi ta addabeta ,kotun tacika maqil har wajan kotun mutanene atsatsaye,domin ko kai bad’an garin maqarfi bane sai kaje wannan shari’ar dan kaga yacce lamarin zaikaya,alqalinne yaqara d’ago kansa akaro na biyu, “malam Kadija Ibrahim kinji abun da ake tuhumarki akai nacewa kina d’auke da juna biyu?”shiru kotun taqara d’auka dan kowa ya tsayar da hankalinshi guri guda danjin abinda zaifito daga bakin wacce akeqara shiru tai dan bata iya tunanin zata iya had’a ido da jama’ar kotu,alqalinne yaqara kallonta akaro na biyu,”malama khadija haryanzu kotu ketake sauraro kifad’amata dalilin faruwar haka.”nima bansan dalilin faruwar hakanba,dif kaji kotun taqata yi na yacce Khadija tayi mgnar tata adaqile.alqalinne yace akaro na Uku,”Malama Khadija bayacce za’asameki da juna biyu kina y’a mace kice bakisan yadda lamarin ya kasance gurin faruwarshiba.wasu irin zafafan hawayene suke zuba daga kuncin Khadija,ahankali ta iya bud’e ido tare da qare kallon wad’anda suke mazauna kotun,idanuntane suka sauke akan Ummi wacce tazabga tagumi tana sharar hawaye, ko mamaki babu kana ganin Ummi kasan y’ar uwace agun Khadija na yacce suke kama kamar an tsaga kara,akusa da’ita kuma ga mahaifiyarsu mai suna Mariya tayi jigum dan ita idonta yagama bushewa dan arayuwa batata6a tunanin faruwar haka ga y’arta Khadija ba,koda’ike ba’ita kad’aiba hatta jama’ar gari yara damanya maza da mata baita6a tunanin faruwar haka ga Khadijat ba,hakan yasa kowa nacikin kotun wasu kuka suke wasu kuma sai cewa suke,arayuwa duk abin da d’an Adam zaiyi bazai tsiraba yanzu,sharri yatshidaga kan kowa ya dawo kan Khadijat baiwar Allah,wasu dai cewa suke to koma Khadijat nada ciki to fyade akamata,shirun da kotun ta d’auka yai matuqar tsayi dan kawo akwai abin dake saqawa azuciyarshi,hatta alqalin tausayin yarinyar yake dan yasan yarinyar bazatata6a iya aekata abun da’ake zarginta da shiba,daqyar akasamu alqali yai qoqarin maimaita tambayar da yaiwa Khadijat har sau hud’u, “Malama Khadija kuto haryanzu kefa take sauraro.tuni hawaye sungama wanke fuskar Khadijat,ahankali taqara d’ago fusakarta akaro na nabiyu da jayan idanunta tafara mgn tanakuka,”Yamai girma mai shari’a tabbas ina d’auke da cikin shege ajikina,abin daya rage daku shine kazarta da hukuncin da Allah yace aewa duk macan data aekata Zina,nafad’a tunba yanzuba ni Khadijat na aekata Zina kuyanke hukunci akaina daide yacce shira’a tatanada,kudaina 6atawa kanku loqaci kudai 6atawa jama’a loqaci,kuna yawo dani agari kuna jimin fushin iyayena akan abun da banji banganiba,kusan kuna zaluntata kuna shari’a dani akan abin da bansan dashiba kutaima keni ku’agazamin kuyanke hukuncin Zina akaina tunda kunce ita na aekata atunanina wannan shine mafita.durqushewa tai aqasa tasaki wani kuka maisauta daban tausayi,take kotun ta cika da haniya kowa yana fad’ar albarkacin bakinshi,kamar filin yaqi haka kotun ta hargitse bada kamar Ummi da mahaifiyarsu wanda Ummi kuka take kamar ranta zai fita,naganin y’ar uwarta acikin wannan masifar gashi bata da damar tai makonta,kan Khadijat ne yafara saramata sakamakon hayaniyar da kotun tacika dashi,alqaline ya buga gudumar shari’a,adaide da loqacin da Khadijat tazube aqasa sunan sumammiya,mai makon Kotu tayi shiru sai wani irin hayaniya taqara kaurewa,dasauri jami’a an tsaro sukayo kan Khadijat dan kai mata agajin gagawa,atake alqali yad’aga shari’a zuwa watan 13gawatan october,nan gari ya d’auka jama’ar gari aka hargitse ko wanne lungu da saqo nagarin idan kashiga maganar ake gida dawaje manya kai harma da yara,zancan ne yabazama ko’ina nagarin Khadijat tace tana d’auke da cikin shege duk wanda akaji haka abakinshi zaginshi ake ta uwa ta uba domin jama’ar gari sun san wacece Khadijat Ibrahim,batayadda za ai ace ta aekata wannan alfasha wannan sharrine tsantsa_ …

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
_haka kotu tabaje kowayai waje anan jama’a suka tsaya kowa yana tofa albarkacin na kinshi,Ummi da mahaifiyarsu Mariya wacce suke cema Amma sune qarshen futowa daga kotun da tafiya suke kamar masu tausayin taka qasa,har yanzu Ummi kuka take dan takasa saita tunaninta,dasauri wani matashi wanda ake kira da Imran yayo kansu,cike da damuwa yake duban Ammi,”Ammi dan ALLAH Dan Annabi kidaina sa damuwa aranki kunsan duk wuya mune da nasara sabo dako tantama babu kunsan Khadijat bazata ta6a iya aekata alfahasha irin wannanba.cikin damuwa Ammi takalli Imran cike da mamaki,”Imran nafi kowasanin wacece Khadijat domin nasan bazata ta6a iya aekata hakanba amma abun da yaban mamaki bakaji abun da tafad’a yanzu akotuba?.wani murmushi takaici da qarfin hali Imran yai,”Ammi aewannan duk 6acin raine amma kab jama’ar gari da Al’ummar da sukasan wacece Khadijat wllhy baza suta6a iya yadda akan Khadijat zata aekata hakaba,haba Ammi sai kace bakisan wacece Khadijat ba. girgiza kai Ammi tai ceke da damuwa,”shikenan allah yashige mana gaba. Amin Imran yace,kallon Ummi yai wacce duk mgnar da suke tanaji tsananin tashin hankalin da takecikine yahanata mgn,”haba Ummi maiye zafi komaifa yai zafi maganinshi Allah,tabbas nasan dole kishiga qunci na sharrin da akaiws y’ar uwarki,to wllhy baki kad’aiba kinga duk mutanan dake filin kotun nan jinjina lamarin suke domin abune ma wanda yuwuwarshi qaryane.sai yanzu Ummi ta iya qarewa inda take Kallo mutane ne tamqam awajan kamar shari’ar wani baban mutum ake a njra,tafiya sukayi su Ammine agaba Ummi na bunsu abaya,dasauri jama’ar dake wajan suka hau d’agamasu hannun samarin wajan kuma nafamar cewa,qaryane wllhy wannan bakomai bane illa hassada yarinya mai matuqar kamunkai za aewa wannan sharri aewannan abun tatsuniyace,haka jama’ar_ garima suke fad’a…

 

 

 

 

 

 

*to masu karatu bara nai burki* anan ko?

 

 

 

 

 

_kubiyoni_

 

ANCUCIHIJJABI

 

 

*TRUE LIFE STORY*

 

 

 

 

 

 

Talented* _Writers Forum

_had’in kanmu shine alfaharinmu_

 

 

 

 

*mai imani dole za’ajarabashi harkanshi ya kulle ya gaza bud’eshi idan yai hqr* _asannu zaiga sakamakonshi musali ganinan zan maye maka_ *gurbinshi,zansa kai murna_karkai_kuka_dakai zan* _zauna hawaye inshare_

 

 

 

 

*pg2*

 

 

 

 

 

 

 

_azaune take Ummi na kusa da’ita wasu irin hawaye masu quna da d’aci na qara ziyartar kuncinta, “yanzu Ummi mai zanyi wanda zai wankeni daga idon Abba da Ammi,da jama’ar gari?Ummi bansan mai nayiwa_ _masa ba ya min wannan aeka aekar ya cutar dani,ya lalatamin tanadin dana dad’e inawa kaina ya cuceni ya zalunceni tsakanina dashi saide allah yasa’isa”wani irin arnen_ _kuka Khadijat ta arce dashi wanda ya qara tayar da hankalin Ummi,qara matsowa tai kusa da ita kasan cewar da tana daga gefentane,dafa kafad’ar yayar tata tayi kafin tace, “aunty ki kwantar da hankalinki tunda kece dagaskiya,kuma ita_ _qaddara bata wuce kan kowa,na tabbata jama’ar gari bazusu ta6a amincewa da wannan abinba,suma su Ammi tsananin tashin hankaline yasa suka fara zargarki,dan haka ina roqanki kiyi hqr ki nutsar da hankalinki wajan fad’amin wanda ya aekata_ miki hk,domin _musamu abun da zamu tunkari su Abba dashi”

tsagaita kukanta tayi tabi qanwar tata da kallo tana nazarin kalamanta dan tasan kokasheta za’ayi bazata iya_ _cewa ga wanda ya mata wannan ta asarba,hawaye ta sharce,tare da fara mgn cikin in’ina,”ban_ saniba Ummi wllhy _bansaniba idan nace miki ga wanda yamin wallhu wal azim namiki qarya,nidai kawai amatsayinki na y’ar uwata Ummi_ _ki’agazamin wajan ceto rayuwata,da wanne abun zanji da cikin dake d’auke ajikina wanda bansan ubansaba,ko kuma da rashin farin cikina kokuma da fasa aurena da’akayi”Dum!Ummi daji gabanta yayi wani mugun fad’uwa najin Khadijat ta ambaci_ _farin cikinta,kuka Khadijat taci gaba dayi,ita kuma Ummi zamewa tai,dan tana matuqar mamakin y’ar uwar tata nacewa batasan Uban cikin dake jikintaba,ganin da sukayi anyaye labule shine ya dawo da_ _kowacce cikin hankalinta,tare da maido kallonsu kan wanda ya bud’e labulan,Ammi ce tashigo rannan nata ad’aure ba alamar fara’a bare annuri,take gaban kowacce yafara dukan Uku_ Uku, _daga gefansu tasamu gu tazauna d’auke ke kallonta tai daga kansu tamai dashi kan qofar d’aki, “Khadijat kaf duniya baki da kamata,domin ko_ _bakomai nice,wacce ta jure wuya dad’i wahala azaba duk nashanye,na d’au cikinki wata d’ai d’ai har tara da ankwanaki,ranar da zaki zo dny wato ranar sa zan haifeki_ , _nari nagama cira rai da rayuwa,domin aloqacin ina tunanin mutuwa itace mafi sauqi agareni,amma cikin nasara ta Ubangiji,na haifeki,bayan na haifeki wahala bata qareba,nice cinki nice_ _shanki domin abincinki ta jikina kike samu,nice wankanki samiki kaya kula da damuwarki dasauran aeyukan da uwa kewa d’anta,daga haka harkikafara_ taka wani mataki _narayuwa,nanma aeki bai qareba kullum cikin fargaba nake,kullum idan nai salla ina saki cikin addu’ar allah ya tsareminke domin duk wata uwa burinta bai wuce d’anta yafi nakowaba, nai qoqarin saki atuba ta gari tare da kaikawo akan tarbiyarki,domin burina_ _kullum bai wuce na kaiki d’akin mijinki lpyh”shiru Ammi tayi tare da maido kallonta kan y’ay’an nata,wad’anda suka jeru kusa da juna,tunda tafara mgn suka tattara hankalinsu gabad’aya_ _akanta,”Khadijat kinsan kice wadda nakeso fiye da Ummi karki manta yacce nake alfahari dake agaban mahaifinku da bainar jama’a harso nake acemin Maman Khadija,amma yau shine Khadija za’awayi gari_ _kina d’auke da juna biyu Khadijat,wanda bashi da Uba,shinni Mariya ina zansa kaina wacce irin qaddarace wannan tatasoni agaba yazanyi da rayuwata,gashi nayi nayi kifad’amin wanda ya miki aeka_ _aekarnan Khadija kinqi,Khadija anya kuwa kina naiman gamawa da duniya lpyh kuwa?anya kina naiman yarda Iyaye da albarkarsu kuwa??kode kina_ _d’aya daga cikin mutanan da iliminsu bai qaresu da komaiba?karfa kimanta duk wata uwa idan zatama y’arta fad’a Khadija dake take misali,karfa kimanta kaf garin_ ( *MAQARFI* ) _bayarinyar da take da iliminki na addini,kokinmanta yacce jama’a suke yabankine?amma yai Khadija kece akaje har kotu dake akan kina d’auke da cikin da bashi da Uba, tabbas Khadija idan lamamarinnan yakasance gske ,zaki fawa kanki tarihi da zuri’arki da iyayanki dan _jama’a_ zasu dunga kiranki,da wacce ta yaudari jama’ar gari,dan wasuma_ cewa zasu dungayiMuna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [An cuci Hijabi Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!