Hausa Novels

Ana barin halak Hausa Novel Complete

Ana barin halak Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Alhamdulillah! Alhamdulillah dukkan godiya ta tabbatar ga Allah Ubangijin da ya halicci marubuci, tsira da aminci su kara tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad S.A.W da iyalan sa da Sahabban sa da tabi’ai har ya zuwa kanmu.

Ina rokon Allah yanda na fara rubuta wannan littafi ya sa na gama cikin koshin lafiya Ubangijin al’arshi ya dafa Mani ya taimaka Mani. Alkairan da suke ciki Allah yasa su isa gare ku sharrin Allah ya kore.

 

Addu’a ta musamman ga ahalina, *_Banu Umar_* Ubangiji ya cigaba da kawo zaman lafiya hadin kai tare da yalwar arziki.

 

*Littafin sadaukarwa ne ga mahaifi na*

 

Misalin ƙarfe daya da rabi na rana ne, kowa ka kalla a cikin jami’ar harkar dake gaban shi yake, wasu fita neman abinci, wasu kuma alwala suke a masallatai domin daura sallar azahar amma yawancin hakan yafi kasancewa da musulmai dake makarantar, su kuwa kiristoci neman abinci suke domin yawancin su ajujuwa zasu koma zuwa karfe biyu, wasu kuma tafiya suke gida Kasancewar sun gama abinda ya kawo su yau, haka nan wani bangare kuma karatu suke, kowa dai ka kalla da abinda yake aikatawa.

Gungun samari ne guda biyar suke takawa a hankali, saidai hayaniya dake tashi a bakunan su ne yasa kowa yake maida hankalin sa zuwa gare su, kaf cikin su babu mai sama da shekaru ashirin, sai dai a ido kai tsaye bazaka yanke masu wannan shekarun ba, sai dai zuciyar ka ta kawo maka zasu iya kaiwa 25yrs haka, domin kuwa masu lafiya ne sannan kuma ya hadu da girman jiki wannan dalilin yasa kowa yake masu kallon shekarun su masu yawa ne, idan ba bude baki akayi aka furta ba bazaka gane ba kai tsaye.

Tafiya suke cigaba dayi inda suka nufi Masallaci fitowar su daga lectures kenan ko abinci basu ci ba suka nufin masallacin domin an kirayi sallar azahar.

Duk wani temple ko kujera da suka wuce sai an daga hannu ana “five stars” ba tare da walakanci ba suke daga wa kowa hannu cikin Faran faran kuma suke cigaba da tadin su na abokai.

Group din mata kam sai dai su nutsu domin kuwa five stars basa daukan wargi ko kadan.
Haka dai suka ringa tadin su har wajen yin alwala da aka tanadar a masallacin suka daura alwala sannan suka nufi masallacin daidai lokacin kuwa aka tada salla inda suka hau sahu guda su biyar din ,kowa ya gansu gwanin sha’awa.

Amma hakan yana zuwa ga wanda bai taba zuwa masallacin bane ko kuma zuwan shi shine karo na farko duk wanda yake zuwa masallacin nan yasan haka suke jera sahu, abu ne mai wahala kazo ka same su ba sahu guda ba sai dai idan sun zo sun tarar sahu bai cika ne dole wasu su cika sahu wasu kuma su tayar a baya, amma idan ba haka ba sahun su suke sakawa sabo su biyar sannan wasu su cika ta sahun da haka aka idar da salla nan take kuwa aka fara watse wa a masallacin domin yawancin malaman aji gare su haka ma daliban wasu kuma sai yamma zasu shiga dalilin da yasa suka fara zaro takadda kenan domin yin karatu.

Five stars kuwa kallon kallon suke kasa kasa kowa yana gimtse dariyar da take cin sa a rai.
Daya daga cikin su ne yaja karamar tsaki ”Mtsw” da alama dai wa shi suke ma dariyar dan haka ne ya kara tsume fuskar sa tare da lumshe kwala kwalan idanun sa masu ɗauke da kyakkyawan kwayar ido.

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan

Daya daga cikin su ne ya dafa shi sannan yace ”Haba guy kai kenan baza ku taba shiri da Aunty Rahinah ba kullum cikin abu daya kuke kamar kaji, kuma duk idan aka biya laifin ka ne, yanzu sabida nasan dan ita zata shiga class ne duk kabi ka shiga wannan damuwar! Why? Nidai a ganina Bai kamata ba malamar ka ce dole ka girmama ta ka kuma bata mutumcin ta ba wai kullum kuyi ta wasu abu kamar yara ba, now u r matured ya kamata idan an girma a san an girma dan Allah! Yana gama wannan maganar ba tare da ya jira amsar su ba yace ”guys mu wuce pls Aunt Rahinah ta kusa zuwa five mints y saura.”

Yana magana duk suka mike banda wanda duk jikin shi yake a sanyaye. Cikin kwaɓe fuska Mahbub yace ”wallahi Allah baka jin magana ina ce yanzu na gama yi maka magana akan irin abinda kake bashi da anfani wai miyasa baka ji ne kam?”

Dan murmushi matashin saurayin yayi tare da shafa sumar kansa daga keya zuwa goshi sannan cikin zazzakar Muryar sa yace ” ina Rahinah ce? To kuje kawai ba yanzu zan shiga ajin ba!

Gaba-daya zaro ido sukayi inda Mahbub yace ” Rahinah kai tsaye babu wani sakaya wa kai kam yaushe zaka yi hankali ne iye?”

Dan tsaki kawai yaja kamar ba dashi ake maganar ba ya ciro wayar shi tare da fara dannawa.

Cikin kufula Faruk yace guys mu wuce kawai remain 3 mints yaushe zamu jira shi yana bata mana lokaci da abinda ya taka tun da kuka ga haka, kunsan shi ungulu ne baya jewar banza dan haka mu wuce kawai.”

Yana fadin haka duka suka fita daga masallacin tare da fara saka takalman su Mahbub kamar yayi kuka haka yake ji, ya rasa wannan taurin kan irin na abokin shi, ya rasa wannan bakin gaba dake tsakanin Aunt Rahinah da abokin nasu yanzu miye amfanin rashin shiga ajin fisabilillahi?

Haka suka fice daga masallacin kamar Mahbub ya jawo shi amma shi ko kallon shi bai daga kai yayi ba balle yasan yana yi.

Tsawon kamar minti arba’in da shigar ta aji tayi nisa sosai da koyar wa Mace mai natsuwa da kamala kyau tare da aji fara ce sol mai madaidatan ido fuskanta dauke da annuri wanda kai tsaye shi ba murmushi ba haka kuma ba wai ta tsume bane! Ajin yayi tsit da alama suna matukar gane abinda take koya masu din idan tayi explaining musu abu kadan sai ta juya kuma kan allo ta rubuta musu ta sake juyo wa taci gaba.

A hankali yake taka corridor din ajujuwan zuwa cikin ajin babu wani alamar tsoro a jikin shi ko wani ɗar! Shirun da ajin yayyi ne ya saka duk wani taku da yayi sai anji sawun shi.

A hankali ya shigo hannun shi rike da waya sai hannun rigar jamfar da ya nade kanshi babu hula sai tarin sumar da ta sha gyara tana ta yalki da daukar ido, daliban da a kalla zasu kai hamsin kowa idon shi ya mayar kansa yana mamakin jan magana irin na wannan saurayin, ko da yake ba yau suka saba ganin haka ba dan har Allah Allah suke ta Aunt Rahinah ta shigo domin su buga karamar drama dinsu da shi.

Boyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke sannan tace cikin harshen turanci ”Fu’ad get out of my class” shiru ajin yayi kamar babu abu mai rai sabida yanda fuskar malamar kai tsaye ya nuna matukar asalin bacin ranta! Kamar ba da shi take ba haka yayi domin kuwa sunkuyar da kanshi yayi yana danna waya abinshi.

Kama kai kawai Mahbub yayi yana jinjina taurin kai da rashin ta ido irin na Fu’ad.

Cikin hasala Rahinah ta kara magana cikin tsawa ”I said get out of my class”

A hankali Fu’ad ya mike tare da saka idon shi cikin nata yayi mata wani irin kallon da ita kawai ta fuskanci abinda yake nufi sannan ya fice.

Yanzu ma dai ajiyar zuciyar tayi tare da gyara wuyan ƙaton hijabin dake jikin ta ta koma ta cigaba da koyar wa! Dama tana addu’ar Allah yasa kada ya mata tijara a gaban yan aji dan tasan zai aikata.

Haka ta gama koyar War ta na awa uku cir sannan ta sallami yan ajin itama ta fice.

Ita ta fara fitowa kafin daliban Fu’ad na zaune kan dakalin kofar ajin cikin dan daga murya yanda ita kawai zata ji yace ”Da kika Kore ni mutuwa nayi? To ina ce gani da rai na garau babu abinda ya same Ni?”

Bata ce masa komai ba kawai ta wuce domin bata da lokacin shi a yanzu amma zai yi bayani ne dalla dalla a lokacin da ya shiga hannun ta!

Caaa abokan nashi suka yi mishi duk da idan da sabo sun saba da wannan lamari to amma kullum cikin yi mishi fada suke baya ji musamman Mahbub da ya kasance mai sanyin hali tare da bin duniya a sannu. Haka suka yi ta mishi amma ko a jikin shi basu ishe shi kallo ba.

Kasancewar basu da wani aji ya saka su tinkarar ma’ajin motoci, a kullum Faruk yake fara ajiye wa sannan Haidar sai Khalid sannan Mahbub sai ya wuce gida. Kaidar su kowa shi zai tuka kanshi zuwa gida sannan wanda za’a sauke ya kara karban motar har sai ya rage daga shi sai Mahbub.

Da haka dai suka shisshiga motar Faruk yaja suka bar cikin makarantar. Kamar yanda suka saba kullum haka suka yi ya rage daga shi sai Mahbub kawai.

Shiru su kai babu wanda ya ce uffan sai da abin ya ishi Fu’ad sannan yace wai me ke damun ka ne guy?

Karamar ajiyar zuciya Mahbub ya sauke sannan yace ”damuwar ka mana Sameer menene amfanin fada da Rahinah miye amfanin yiwa Rahinah rashin kunya matsayin malamar ka take bayan wannan matsayin..! Ya isa dan Allah cewar Fu’ad yana daga wa Mahbub hannu. Inda wannan ce matsalar insha Allahu na daina ka ma daina damun kanka kaji? Gaya min matsala ta gaba! Yayi maganar yana shan kwana da motar.

Dan girgiza Mahbub yayi a ranshi yake fadin bazaka canza ba Fu’ad.

Matsala ta biyu kuma game da dad ne…!

 

 

Leave a Comment

error: Content is protected !!