Hausa Novels

Ana Zato Hausa Novels

 

INA farawa da sunan Allah mai Rahama mai jink’ai

Wannan lbrn banyi shi Dan cin zarafin wani,ko wata ba

Allah nake roko ya karemin kai Babana ya biya maka dukkanin bukatun ka na alkhairi

Adfat kune haske idanuna farin ciki Allah ya muku albarka yarana Fatima da Adam

Baxan mance daku ba Kawayen arziki Phattyta, farar mace fatima yahaya Oum najma Mzeeta Ummu suhaila(Sudan) MMN Abida fatima Abubakar MMN Amila Bilkisu M Amsoopy mum twins oum safwan Kai da duk matan  da ke cikin Mata masu gari na gaishe Ku

ATK’S  muna godiya da irin wahalar da kukeyi wajan turamana novels

Yan Uwana da kuke cikin taurari wannan page din naku INA jidaku har can cikin zuciyata

PAGE 1 to 10

“Innalillahi wa’innaillaihiraji’un” shine kalmomin datake fadi tana maimaita su,tare da dafe goshinta tana girgiza kanta.. “Innnalillahi wa’innaillaihiraji’un, Allahumma ajirni fi masibati wa’aklifni khairan minha” shine kalmar data dinga maimaitawa, Wata dattijuwa ce wacce bata wuce kimanin shekaru  Arba’in da biyar ba, take fadin wannan kalmar tana dafe kirjin ta da hannu, dago jajayen idanunta tayi wad’anda suka rine sukayi   jajir allamun tasha kuka ta d’agosu  ahankali ta kalli wannan d’an saurayin dake tsaye akanta, tasake dubansa dakyau girgiza kanta tayi akaro na uku sanan tace “Mansir dagaske kake fadi cewa Ashmat ta haihu?” Tana maganar tare da buga qirji allamun mamaki, kallon matsiyata yamata tare da kallonta sama da qasa  yace “Na ta’ba miki wannan qaryar ne umma? Na taba zuwa na miki wannan wasan ne? Ina tunanin a tsakani na dake babu wasa, tunda tsakanin uwa da ‘da ba wasa dan haka ni bazanyi wasa dake ba, kuma banga abinda zesa nazo na dorama matata,farincikin rayuwa ta wannan sharrin ba, Ashmat ta haihu yanzu haka tana gadon asibiti kuna iya zuwa ku dauki gantalalliyar ‘yarku da kuka cuceni kuka yaudareni batare dana sani ba.kuma sannan batare da nasan cewa tana dauke da cikin shege ba, cikin wanda bansan dashi ba yau watan mu biyar da yin aure ace harta haihu kaiiii!!!!!!! Wannan wanne irin cuta ne? Ko dik  dan ku mallaki dukiya kukai wanan, ko dan sabida mahaifina yasa kukai wannan? Haba!!! dan Allah bakuji kunya ba, bakuji kunyar rana irin wannan dazata zo na tinkare ku da wannan zance  ba? Atunani na ku din iyaye nagari ne masu tsantsar tabriya …. Allah ya isar mun, Allah ya isa macuta kawai,”

    Yana kai qarshen maganarsa yasa kai ze fice daga gidan  saiga wani dattijo yashigo fuskarsa dauke da murmurshi yace “Kaiiii babban baqo mukai agidan namu ashe laleh marhabun da Mansir ya kuke da…..! bai kai ga  qarasa. Abinda yake niyyar fad’i  ba Mujaheed ya ‘daga masa hannu allamun bayaso yaji abinda ze fadi yace “Ni Mujaheed zaku yaudara? Ku aura min ‘yarku da ciki ajikinta?” Hannu yakai ya daki gini seda ‘yan yatsuntsa suka fitar da jini suna zubarwa ya nuna wanan dattijon yana cewa “wallahi tallahi yadda kuka lalatamin suna dana mahaifina, koda yake bekai ga lalacewa ba tunda babu wanda yasan Ashmat ta haihu, dagani se mahaifina se ku, adangina ma babu wadanda suka sani se wad’anda suke cikin gidan mu….”

   Yafice yana huci ya shiga motarsa gudu yake sosai adaidai lokacin da ze isa asibitin kafin ya iso ya bude motarsa wani likitane ya shiga cikin dakin yana kallonta yana girgiza kai fuskarsa dauke da murmurshi yace mata “ya jiki?” Tace mishi ‘Ahh likita da sauqi idan ma zaku sallamemu

Idan ma zaku sallamemu yanzu ni innaganin zefi, “Zan sallame mana sallama ta har ..bari dai nai miki wanan allurar tukunna”

Saida ya mata allurar kafin yace ki d’auki danko ki Masa kallon bankwana ki Masa magana ko zuciyar zatayi sanyi kinji”

Yasa hannu ya mik’a mata jaririn da shima yakai hannu zai Masa allurar sai kuma ya fasa yana girgiza “No,I can’t he’s innocent” shiru tayi ta rungume yaron a kirjin ta …want hot smile doctorn yayi ya fara magana lokacin da ya lura allurar ya fara aiki sosai ajikin ta yasa hannu ya amshi yaron tare da cewa…

“Turoni akai na mikishi, wanda ina tinanin zakiyi bankwana da lahira har abada awannan lokacin kuma ma bari kiji infadi  wanda ya turo ni, ya fada mata sunan wanda ya turoshi yazo ya aikata mata wannan allurar, yana gama mata wannan allurar tafara ganin jiri, wani tunanine yafado mata a zuciyarta yasa kai ya fita yana waya saidai abinda ashmat bata saniba shine yana leken ta, “Tabbas!!! Nasan za’ai haka” tafad’i da karfi ta dauki takarda ta farayin rubutu, rubutu take sosai… Wannan takardar kamar dashi tazo a hanunta ba wanda ya lura dashi, dik zafin naqudar data keji haka ta ruqo wannan takardar da biro din ta shigo dasu..

    Dauka tayi tana rubutu tana ciza labbanta saboda radadi da zafin data keji a cikin jikinta, tanajin motsin shigowa tayi sauri ta ajiye littafin dake hanunta a gefen jaririn dake kusa da ita, bawata ce ta shigo ba face nurse faty wacce kawarta ce tun suna primary school, ita halin rayuwa ne ya hanata cigaba da karatu.. faty ko a yanzu ta zama nurse, wacce  ake kiranta da faty Afreen. Faty Afreen ce ta kalleta da fadin “kawata yaya kike ya gida ya jikin naki?” “Hmm jiki da sauqi amma waccan fa wacece? Ta nuna nurse Samira da suka shigo tare da faty Afreen “a’ah ba kowa bace yanzu zata fita” “owk toh bari ta fita senai miki mgn” Tinda samira ta fahimci cewar Ashmat naso tama faty magana se taqi fita tana tayin samo- samo ta koma can gefe yanda suke tunan bazata jiyo su ba hakan yasa Ashmat takama hanun faty Afreen tace mata innaso ki tabbatar cewa

“Duk wuya duk d’ad’i,Duk rintsi,ki tabbatar 

Wannan yaron ya rayu, akwai wani abunda na rubuta acikin takarda komai da komai da dik abinda ya sameni abaya dik yana cikin wannan takardar..”hannun faty ta kama,ta ta dauko takardar ta Sanya mata cikin tafin hannun faty ta rufe ta cigaba da cewa,

“Dan Allah dan girman Allah inaso kibawa d’ana idan ya girma, ki gaya masa cewa wannan shine abinda na bar masa, yayi hakuri da halin daze tsinci kansa, shima kanshi ze fuskanci qalubalen da ni kaina bansan iyakacinsa ba, amma ina masa addu’a Allah ya taimakeshi akan gaskiya , Allah ya cika masa burinsa na ganin ya kwatarmin haqqina da sauran ‘yan uwana baki daya ki karbi takardar nan dan Allah kinji” Kuma ki Masa Huduba da suna …..”ta rike cikin ta tana ya tsine fuska ciwon ya fara cin k’arfin ta hawaye suna bin kuncin ta, dakyar ta cigaba da cewa 

“Faty manna min shi a k’irjina na Masa Hudubar da kaina” duk jikin faty yayi sanyi ta rasa me zata cewa Ashmat sai d’aukar jaririn tayi tasa mata a k’irjin ta,wani kalar murmushi Ashmat keyi Wanda da ka gani kasan na dole ne tayi d’an ta Huduba a ta d’ago jajayen idanin ta,tace Ina son ka  Ashraf wanna shine inkiyar ka Dan Allah kawata karki bud’e takar dannan asalin sunan sa yana ciki na rubu….”ruko hannun ta faty tayi “Na karbi wannan amanar Kuma zan rike saidai kisani tare zamu raine shi,ni dake nasan cewa Dan nan namu ba ta hanyar sunnah kika samo Shiba Amma hakan ba yana nufin ki guje shi bane,inada tarin tambaya abaki saidai ba yau ba saikin samu isasshen lfy tukun”ngd kawata.ki rokar min su umma ya fiya kinji?”  Ungoo dai wannan takardar…

Maganar yana cije mata sai kara rufe hannun faty da takardar take. Samira na juyowa ta kalle su lokacin da take miqama faty takarda sega kira ya shigo wayar faty, faty na ganin numbern dake kiranta tace “Ashmat ki tsaya riqe takardar nan innazuwa  tana fita itama samira ta fita da allamun waya zatayi, dan ta kara shi a kunnen ta,tana magana k’asa k’asa ,Ashmat na ganin fitar datayi seta dauki ta kardar tasa acikin wandon d’anta Ashraf wanda ta  duqunquna shi  kafin tasashi acikin wandonsa saboda taga sanda samira take musu wani kallo ita kanta bata yarda da samira ba, anya samira bata daya daga cikin wadanda suke leqen asiri? Wa’danda aka turo su domin su illata rayuwar ta  su kasheta ita dai fatanta kar wani abu yasamu d’anta..

   Daidai samira na fitowa sai ga Mujaheed shima zai shiga

“Yace da ita “ina buqatar kibiyoni da yaron nan bayan na fita ki kula sosai, karki bari aganki ki boyeshi saboda kinsan asibitin nan naku akwai doka  dan haka ki boyemin dan, banaso kowa yasan cewa kin fita dashi inna fata kin gane?” “Karka damu sir! Komai zetafi yadda aka tsara insha Allah” yace toh shikenan.. yana shigowa Ashmat ta ganshi tayi murmushi tare da cewa “mijina kayafemin bancutar da kai ba kayi hakuri nayi hakan ne domin na rufa ma mahaifina asiri sannan na rufe wannan abun sanan kuma nakare daraja da mutuncin cikin gidan mu, hannu yakai ya shaqeta tare da zare idanu “ke harkin isa kice zaki kare mutuncin gidanku nikuma ki zubarmin da nawa mutuncin toh ma wanne mutunci kuke dashi acikin gidanku tukun, wanne mutunci kuke dashi? Ai bakuda mutunci matsiyata ne ku bakusan inda mutunci yake ba tinda har zakije kiyi cikin shege kuma kikaiwa wanin cikin acikin gidansa batare da ya sani ba mayafi wannan?, Wallahi na tsaneki Ashmat na tsani ganinki a rayuwata kuma sena zama ajalin rayuwarki..”. Zare ido take ahankali tana gwalalo idanu da dukkan allamu wannan riqon daya mata awuya ya shigeta sosai, jijjiga masa kai take allamun kasakeni ta furta da qyar, kayi hakuri kayafe min zanso ka zauna ingayamaka komai abinda ya faru “is too late banasonjin komai daga bakinki dan dik abinda ze fitoh daga bakinki karya ne, ke makaryaciya ce bakida gaskiya a rayuwarki komai naki qarya ne.. Ashmat nasameki ba virgin ba nayi hakuri na rufa miki asiri nace zan riqeki ahaka ba abinda ze sauya daga soyyayar danake miki sanan kuma bazan taba goranta miki wannan abunba banfadi ma kowa ba , meyasa baki fadamin ba? shin baki yarda da soyyayar da nake miki bane? Meyasa zaki min haka? kinsan mahaifina cikkaken dan siyasa ne wannan abunda kika mana ze zubar nana da kimar mu da mutuncin mu toh wallahi zanyi komai dan na riqe kima da martabar gidanmu kamar yadda kema kika wulakantani kika ci ammana ta domin ki boye wannan boyyayar mugun abu da kikayi sannan kuma ki rufe mutuncin gidanku ki kareshi dan haka nima zan kareshi…”

   Shaqe mata maqogaro yayi dan ya kasheta, yasa mata hannu a maqogaro tana nunfashi tana zaro idanu hawaye na zuba daga idonta tana furta “kayafemin zakayi dana sani watarana! Zakayi dana sani watarana!!… Daqyar maganar yake fito mata sabida yanda ya shaqe mata maqogaron sakinta yayi ya fice daga dakin ga baki daya.. ta shiga qaqari tana qaqari har  rai yayi halinsa anan gurin ta mutu… Bayan mutuwar ta da minti kadan sega faty tadawo cikin dakin, cikin hanzari tazo tana dubata tana tabata “Ashmat! Ashmat!!, Innnalillahi wa’innaillaihiraji’un Ashmat!!!, Ashmat meyafaru? Innnalillahi wa’innaillaihiraji’un”

   Fitan faty keda wahala sega samira tashigo dauke da wani zani a hanunta tasaka shi aciki ta dauki jaririn ta fice dashi, tafiya take cikin sanda ahankali ahankali wan dinsu da suka saka shiya hana agane cewa yaro na hanunta domin ta rufeshi acikin qirjinta tana tafiya ahankali..

   Cikin sand’a take takawa ta zaga ta baya ta wuce.. faty ta dawo daidai lokacin data shigo da doctors akan suzo su duba mata Ashmat suga yaya take ciki , rashin ganin jaririn yasa hankalinta ya tashi sosai seta tuna lokacin da Ashmat take nuna mata samira da dan ‘yatsanta cewa samira ta fahimci me suke nufi, window tashiga leqawa can ta hango samira cikin sanda tana tafiya da yaron ahankali ahankali… Fitowa tayi dagudu da sauri sauri tadauki waya ta kira mijinta “swthrt ka biyoni ,swthrt kabiyoni dan Allah innan zanfita daga asibiti.. yanzu da motata zan tafi zangaya maka dik inda muke dan Allah ka biyoni, wannan lamarin fa babbane,” “meyafaru faty ki fadi min meya faru mana? Meyake damunki inna zan biyoki kigayamin..” “No karka damu magana ne ka kirani kawai.. Nan danan ta shiga mota itama adaidai lokacin da samira ta miqama Ashraf jaririn a hanunsa ya sakashi cikin mota ya fita daga cikin asibitin.. yana fita faty tabi bayanshi, gudu yakeyi ba tsayawa gudu yakeyi gudu yakeyi itakan ta gaji bata saba gudu a mota irin hakan ba, mijinta tashiga kira yana dagawa yace mata “ganinan na fitoh kuna daidai inane inzo insameki” tace masa munan layin ‘yantifa tanan bayan wanan jan bankin, dan girman Allah kayi sauri wallahi bazan iya tafiyan ba gudu yakeyi sosai..” “wai waye wannan kigayamin mana dik kin rudani innafa driving ne meyafaru ne… “Swthrt kazo mana kawai karka damu abu ne very important, kazo kayi sauri, gudu taakeyi shima yana gudu har ya iso wajan yace kina inna ne tace gashinan mun wuce munanan anguwan ‘yandakau dan Allah kazo nikam nagaji zan tsaya inna tsaya kuma akwai babbar matsala wallahi anbani amana kar wanan amanar ta tafi takashe tana kuka tana gudu a motar  hakan ya sashi shima ya bita da gudu yana gudu har ya iso ya hango motarta daga can nesa yana zuwa yana tafiya yasa yakirata yana fadin “kidan tsaya ganin zan qaraso inna karasowa mushiga insha Allah u zan tarar dashi, hakan yasa tana tsayawa yazo ya shga ciki ta fita ta komawa wajan zaman baya ta rungume hannu akirji tana fadi “Innnalillahi wa’innaillaihiraji’un ya Allah yasa karsu tabamini wannan jaririn .. “meye haka? Shin waye shi? Meyasa zeyi haka da d’ansa na cikinsa, dik da nasan cewa Ashmat batada wani saurayina duniya se Ashraf batason kowa se Ashraf, 

batason farin cikin kowa sena Ashraf.. meyasa Ashraf zeyi haka dan kawai  ya mata cikin shege kafin su auri juna?” kuka takeyi sosai mecin rai.. Tabbas bazan taba mancewa ba Akwai lokacin da Ashmat tace min “dallah faty kiyi shiru mu munan muna tafiya muna bin mutun ki kalli abinda ya ke, gudu ya keyi fa kina nan zaki tsaya bamu wani labari daya riga ya wuce kimin shiru ni da Allah mu tafi kawai ko abinci fa banci ba kika dagoni.. kayi hakuri mutafi bazance komai ba arude nake shiyasa bazaka gane abinda nake nufi ba, bazaka fahimceni ba… Ashmat ta mutu, ta mutu ta bar duniya ta tafi Innnalillahi wa’innaillaihiraji’un meyasa ya kasheta meta masa shin akwai wani mummunan abu data aikata ne arayuwarta?, Ashmat fa saliha ce mahaddaciyar Al-qurani ce, Ashmat’yar baiwa ce.. macece mai hakuri da yawan ibada Ashmat ta kasance budurwa wacce rudin duniya be dameta ba kwata-kwata, Ashmat macece da bata zuwa party, Ashmat macece mai yawan sonyin ibada, karatun Al-qurani baya yankewa a bakinta, dik abinda takeyi tana yawan zikirin ubangiji, shin meyafaru ne? Garin yaya Ashraf ya mata ciki? Meyasa ya mata ciki awaje bata gaya min ba? 

“Ashmat tana fadimin sirrinta katina?’ …ko takanta bebi ba sedai ya juya ya buga uban tsaki ya kama gudu.. gudu yake shima Ashraf yana gudu.. idan suka lura cewa Ashraf nason ganowa suna binsa  abaya se su Dan sudanyi parking suyi basaja kamar zasuyi kwana su zagaya ta baya… Dan agaskiya mijin faty ya kware wajen driving.. Haka suketa gudu gudu har bayan sallahr   la’asr kafin ya tsaya yace “Gaskiya mu tsaya muyi sallah.. “toh yanzu muyi sallah akwai ruwa ne?” Akwai a mota na mana ya bata amsa, bafa motan ka bane mu tsaya muyi sallah kuma yana tafiya kacigaba da driving kawai dan Allah kacigaba ceton rai zamuyi kacigaba da driving karkace mu tsaya, mu tsaya a inna?  Lokacin da Ashraf ya lura cewa suna binsa seya canxa hanya yayi kwana ya canza hanya gabaki daya… Juyawan da zasuyi basu ganshi ba Ashraf babu allamunsa kawai se qura daya tada musu akan hanya…..

ANA ZATO

TAURARI WRITER’S ASSOCIATION

WRITING

BY

UMMU FU’AD(HUMKAM)

DAN ALLAH DUK WACCE ZATA KARANTA TA FARA TUN YANZU KADA SAI NAYI AYI TA CEWA NATURO,PLS ABUBUWAN DAYAWA

SHAFIN NAN SADAUKARWA NE AGAREKU MMN AMILA, MUM ISHAQ ,RAKIATAU NIGER , I LODIYU MY SO SOM

11 -12

Cikin Asibiti

Umma, mahaifiyar Ashmat ce ta shigo fusk a d’aure babu ko walwala, direct ta nufi gadon Ashmat da niyyar fad’a, turus ta tsaya ta jingina da bango. da hannu ta fara nuna inda taga an rufewa Ashmat fuska, bakin ta na ‘bari tana son yin magana Amma ta kasa,wata dattijuwa da suka shigo tare ta rungume ta tana bubbuga mata baya tare da cewa.

“Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun”

“Kiyi hakuri Bilkisu haka Allah ya nufa iyakan numfashin da Ashmat zatayi a duniya kenan,kiyi hakuri,a yanxu addu’ar ki kad’ai take buk’ata.

“Ayya Yaya shikenan,Ayya ya kashemin ita ko?”kafad’un ta rik’e tana jijjiga wacce take kira da Yaya cikin tashin hankali take maganar

“Hmmmm dama yace zamu gani wannan shine abinda zamu gani ashe bak’in ciki zai d’ora mana,Dan kawai bamu da gata?”shiyasa abubuwa ake mana haka?” 

“Wlh muna da mai k’arfi” kai ta shiga girgizawa  tana kuka mai tsuma zuciya ta, isa gadon da aka rufe Ashmat,hannu tasa ta yaye mata lullubin tana kallon kyakkyawar fuskar tilon ‘yar ta wani murmushi ta saki mai k’una yayin da hawaye ke zarya a fuskar ta, tace 

“Muna da Wanda yafi k’arfin kowa Ashmat, zamu k’ai k’arar sa  kotun da  babu cin hanci,Zan Mika dukkanin bukatun ki gurin sa”

“Ashmat saina k’watar Miki  ‘yanci” ta juya tana kallon yadda Samira ke faman bata hakuri tana cewa “ai tashin hankalin ma shine babu d’anta babu dalilin sa an sace shi,Kuma hajiya mijin ta fa baizo ba kiyi duk bincikenki ni nasan Wacce ta kashe ta,Dan kuwa naji lokacin  fad’a ya had’a su kuma a idona akayi”

“Hmmmm ‘yan nan ke nake sauraro fad’i abinda zaki fad’a Dan kuwa ni nasan mijin ta shine maka shinta”

“Wlh tallahi hajiya yau banga maigidan ta ba nidai da k’wayar idona Kuma anan nake tun safe, Nidai naji sanda, Ashmat ke cewa “Fatima mijinki ne yamin ciki Kuma wannan yaron na shine,na b’oyewa su umma ne kawai Dan na rufa muku asiri Amma ai kema kinsani tunda kin kama mu, sannan za’a karai tantancewa lokacin da ya girma”

“Haka dai naji tana cewa sai fatyn tace wlh ko zata rasa ranta sai ta salwantar da rayuwar su ita da d’anta,bazata tab’a bari sunan Dana mijin ya b’aci ba.lokacin da suka lura naji maganar da sukeyi faty tabar d’akin Ina ganin haka nima na fita da tsantsar mamaki,Amma bance komai ba sbd nasan yadda suke,na boye ta bayan k’ofar toilet batare da sun saniba, ,lokacin da na fito  shine naga abin mamaki”

“Bangane abinda kike nufi ba. Karki kuskura ki gayamin ansace wannan yaro wlh k’arya ne,k’arya kike?” Hmmmm naga nurse Faty dashi a hannun ta a lokacin da tabar d’akin nan cikin sand’a dashi a hannun ta,Dana tambaye ta sai cemin tayi shansa zayi,bankawo komai araina ba na shigo ina xuwa saina tarar da Ashmat ta mutu”. 

“Abinda yasa na k’ara tabbatawar kaina faty ce tayi kisan shine,wannan” ta d’ago hijabin faty dake kusa da kan Ashmat ta mik’awa umma.shiru umman tayi tana sak’e sak’e acikin zuciyar ta”

“Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun,Fatimar ta sace ‘dan aminiyar ta?”eh!lallai duniya tazo k’arshe wannan shine Ana zaton Ashraf, ashe bawan Allah bashi bane,yanxu ya zayi kubamu gawar ta mutafi “

“Assalamualaikum”sallamar wani hamshakin d’an majalisa mai suna Alh Mu’azzam Musa mutun ne shi, mai d’umbin al’umma Dan siyasa mai tausayin talakawa, dattijo mai ilimin addini,Shararren d’an siyasa,saidai burin sa aduniya yadda zai taimaki talaka, da yadd talaka zaiji d’ad’i ya huta,mutum mai adalci,

“Wa alaikumussalam”Sannun ku ,Ya mu kaji da hakuri duka mutanin da ke cikin d’akin suka amsa

Gaisawa sukayi ya wuce gurin Ashmat Yasa hannu ya bud’e mata iya fuska,girgiza kansa yay,hawaye sun cika Masa ido hankie ya fitar ya goge fuskar sa

Muryar sa na rawa yace”Ina Dr inason ganin sa” ok sir let me go and call him”

Wata kujera dake d’akin Abban Ashmat ya ajiye Masa akan ya zauna yace 

“Ka zauna malam ni hakan ma yamin ngd”ba yadda baiyi akan ya zauna a kujerar yak’i hakan yasa Abban Ashmat zama.dr na k’arasowa “Alh Mu’azzam Musa ya mik’a Masa hannu akan suyi musabaha shikuma ya k’asa mik’awa,Saida yace 

“Assalamualaikum ka bani hannun ka Musa mu ladan juna”sannan ya yarda sukayi musabaha ya cigaba da cewa angama binciken?”

“Eh!rankai dade minyi iyakan binciken mu ba abinda Tasha ko makaman cin sa,saidai kujewar da tayi a wuyar ta ga dukkan alamu shaketa akayi, sannan mun tarar da hijabin faty agurin” wacece faty”d’aya daga cikin ma’aikatan mu rankai dade”okay shikenan?” 

“Ba shikenan ba Dan kuwa ni har yanzu wlh Ina kokonto matu’kar gaske ace faty ce ta kashe Ashmat,a yau dinnan Ashraf ya gaama ikirarin kashemin diya Dan haka shi nake zargi Kuma saina k’watar mata ‘yanci kota halin k’ak’a” inji Umman Ashmat tana magana tana kuka

“Hmmmm koma waye wlh sai ya d’and’ank irin abinda taji a yau dinnan”ko da kuwa d’an da na haifane wannan shine adalci ….

Ku fito da gawar muje ayi mata sutura ,har yakai bakin k’ofa yadawo “Ina shi Ashraf din yake yanz”Abban Ashmat ne yayi magana cikin sanyin murya,yace “nima inata Kiran layin sa baya tafiya,ya kamata ace dashi aka sallaci mai d’akin sa”

“Hmmmm suspect na farko kenan,Ina ita Fatimar take ki kiramin ita” sorry sir itama bamu ganta ba,saidai mai gadi ya tabbatar min da cewa ta fita da gudu a motar ta,shi kansa ya tsorata da yanayin ta,Dan kullum saita sallame shi kafin ta wuce”

“Hmmmm dukkan su zasuyiwa hukuma bayani dalla dalla wlh”

Yana gama magana ya fita rai abace ya shiga motar, direct k’ofar gidan sa ya nufa inda mutani suka cika babu masaka tsinke,anan gidan sa dake G.R.A ya nimi alfarma azo da Ashmat,babu musu aka taho da’ita suka shirya ta…

Lokacin da suka gama shirya Ashmat mum din Ashraf banda kuka da addu’a ba abinda takeyi,tana mtukar k’aunar Ashmat kamar yadda take k’aunar Ashraf,haka aka fitar da’ita suka sallace ta,sannan suka mik’a ta gidan ta na gsky.

ANA ZATO

WRITING

BY

UMMU FU’AD

PAGE12 – 20

Lokacin da duka dawo Alh Mu’azzam ya Shiga cikin gidan ta kasa ta’aziya sannan ya fito, tunda ya zauna yake  tunani a cikin ransa tabbas wannan karan sai nunawa ashraf da fatima sunyi babban kuskure wajan kashe,Ashmat….

“Bangaren su Faty kuwa suna can jejin Hankalin su yayi matuqar tashi gashi jeji ne basu san hanya ba, shiru sukayi suna kallon junansu, faty ta kallesa tace “yanzu ya zamuyi?” Yace 

“Wannan qurar da. ya tada,to shi zamubi, kisanya ido a dik inda ya wuce zakiga qurar ya tashi ki rinqa lura da kyau kema, dik inda kikaga qura ta saman nan yana haurowa toh ,nan hanyar yabi dan haka nan zamu bi, kinga bari musa kai mufara da sunan Allah, Bismillahi ya fad’a ya danna key yafara bona  wuta, 

Aiko cikin hikimar ubangiji se gashi yana hango bayan motar sa suka cigaba da gudu, yana gudu har suka bar garin baki d’aya suka shiga wani garin,tafiya suke! Sosai ba wanda ya tsaya tsakaninsu, 

Ashraf ma bashi da niyyar tsayawa seda suka wuce garuruwa uku wajan k’arfe hud’u duna tafiya akan hanya, sun shiga wani irin jeji tafiya suke sosai segasu a wani rugan fulani, rugane can suke hangowa me nisan gaske tafiyan, suna kan tafiya se motarsu ta tsaya cak mai ya qare, kallon juna suka shigayi 

“Innnalillahi wa’innaillaihiraji’un” faty man mu ya qare” ya fada , karka damu ai munada qafafun mu mufita mu bishi a guje karka yarda ya tsere mana dan girman Allah, yace faty gudu fa kikace? 

“kwarai ma kuwa riga da wando ne a jikina kai ma riga da wando ne a jikin ka, dan haka Bismillah kawai,”toh shikenan muje, suka fara binshi da gudu, suna gudu yana gudu, yana tafiya beko waiga bayanshi sabida shi alokacin burinshi yaje ya ajiye jaririn da  yaji gabaki daya ya dena kuka tin, jarinrin na kuka har ya dena kuka hakan yasa ya tabbatar wa kansa cewa jaririnan ya mutu dan haka gwara yaje yayi sauri ya ajiyeshi inda ma baza’a taba tsammani ba  kuma baza’ayi tinani ba,

 shiyasa ya yanke hukuncin zuwa dashi jejin da basu ma san me ake nufi da cikin gari ba, balle suyi yunkurin ZUWA dashi, rayuwar su dai daga jeji sai jeji, hakan yasa ya rinqa gudu, gudu yakeyi gudu yake suna binshi a baya, sunyi gudu sosai faty ta kasa qarasawa se haki take tana buga qirjinta ta dafe qirjinta da hanunta tana cewa “Innnalillahi wa’innaillaihiraji’un” bazan iya katafi kawai kabarni anan ,Adam k’irjina, da marata suna mij matsanancin ciwo’

“Dan Allah ka bishi, kayi sauri ka bishi, yace faty amai fa kikeyi amman ma gashi kaman da jini jini, ba damuwa ba matsala bane kaidai kawai kabi bayansa  da gudu nace maka , kabishi dan Allah katafi kabishi kawai, tana magana tana rikr mara 

Yaace “Shikenan, ya fara gudu yana binshi itama ta fara ahankali dan tana jin jiri sosai a jikinta yana di banta, gashi qafarta tanajin danshi-danshi dake dake fita daga cikin jikinta, ta kasa tsayawa dik wannan abun datake ji tacigabata da tafiya, tadanyi gudu ta tsaya ta cigaba da tafiya hakan yasa har Allah ya taimakesu sukaga yayi parking a kofar wani gida ya dauko jaririn acikin mota ya ajiye musu shi, yana ajiyewa ya shiga mota ya tafi da gudu da niyar komawa inda ya fitoh seda ya tabbatar,

 Ashraf ya bar wajen kafin yaje yasa hannu ya dauki jaririn, shiru yayi yana kallon yaron dan babu ko alamun nunfashi a jikinsa “Innnalillahi wa’innaillaihiraji’un” shine kalmar da ya dinga furtawa ahankali ya fara tafiya yana komawa inda suka ajiye motar su cikin hikimar Allah juyawar da zeyi seya hango wani ….

Rafi da ruwa agurin haka yasa yaje wannan rafin ya tsugunna ya dibi ruwan wannan rafin ya diga ma yaron akan labban bakinsa amma inna, ko motsi beyi ba ya dibi ruwan ya watsa masa se yaron ya tsandara ihu kuka kawai ya keyi ba sassauta wa. Ya nata kuka sosai hankalin sa yayi matuqar tashi tabbas yasan wannan yaron ba abinda yakeji se yunwa , mezasu basa?shin mezasu bashi? Kai!!!! Ya salam ya furta ya cigaba da tafiya yana kan tafiya se suka hadu da faty a hanya ta nemi guri ta zauna saboda yanda takeji jikinta babu lafiya ..

     Kallon juna suka shigayi shida ita yace “faty kinga yaron nan yinwa ya keji”

“Na watsa masa ruwa yayi motsi amma kinga yanzu ko motsin bayayi yaronan kada ya mutu, karban jaririn tayi ta rungumeshi a cikin jikinta “ya salam mezan masa yanzu, shin mezan bashi, bakinta ta kai kusa da bakinshi allamun tanaso tayi kissing dinsa taji cak ya cabe bakin yana tsotsa yanata tsotsa, ya sake ya qara tsandara kuka hakan yasa hankalinta ya tashi matuqa tace a motana akwai madara, akwai kayan tea danake ajiyewa mutafi.. yace toh inna ruwan dazamu bashi?

Tace akwai ruwa acikin motana abayan booth nake ajiyewa mubashi haka”

“Amma ai faty ruwan sanyi ne, kanaso ya mutu ne? Dan Allah ka riqeshi mu tafi kasamin shi abayana, tsugunnawa da zeyi ya samata shi abaya seyaga qafarta jini,

 saboda fararen Kaya ne ajikinta, yace faty me nake gani a qarqashin kafarki kaman jini?dan Allah ka saka wannan ba matsala bane innaga cikin dake jikina ne ya fita batare da mun sani ba, kasakamin wannan yaron, amana aka bani nagaya maka bazan iya ba bazan iya cin amanar kawata ba aminiyata wacce ta sakani farinciki a lokacin da kowa ya gujeni, wacce ta soni a lokacin da kowa ya qini ni., kamin wannan dan na rasa dana ko ‘yata wanda karamin cikin da watanshi uku ne, ni bazan damu ba akan wannan daya riga yazo duniya,

” kuma shikenan ta mallaka a rayuwar ta, gashi ta koma ga mahallicinta, idan ya mutu bazan yafewa kaina ba, yace toh shikenan yasa mata dan abaya ta riqeshi da zanin da aka lullubeshi ta goyashi suka tafi cikin mota, tasha wahala matuqa domin hanyarsu ta tafiya seda qafarsu ta huje.. 

wata qaya ta tsoke mata takalmi ta shiga har cikin qafarta, daqyar mijinta Adam ya cire mata yana cire mata suka kama hanya suka cigaba da tafiya ahankali ahankali har suka qaraso cikin motar madarar ta dauka ta dauki cup ta hada masa, sedai babu feeder da hannu ta tare masa tana basa amma inna be iya sha ba hakan yasa  ta juyar dashi ta dureshi, tadinga dura masa madarar nan tin yana kuka yana sha har seda yayi shiru, 

“Wasu zufa ne ya keto masa daga goshinsa hakan yasa ta gane ya koshi, sannan bacci me dadi ya kamasa ta rungumeshi akan qirjinta… Awannan lokacin ne ta daga ido ta kalli mijinta tace

” Megidana ya zamuyi da wannan jaririn…  Tabbas ina son sa. ina kaunar sa.sedai abinda baka sani ba shine samira taji lokacin da Ashmat take bani ajiyar wani  takada”

“Zaro ido Adam yayi had’i da dafe k’irji alamun tsoro, yace Takarda kuma? Kinga abinda ta rubuta aciki? Wlh k’arya take bani bane”

Da sauri Faty ta juya  ta yi masa kallon tuhuma kafi tace

“Bangane bakai bane” hannun sa yasa ya bugi goshin  sa “mtsww wlh baby duk NA rud’e ne,amma Dan Allah kamar yadda tace miki karki bude to ki cika alkawari kinji”

“Kada ka damu insha Allah Dana San inda yake zan baka ajiyar sa dan sai kafi adanamin ita dakyau”

“Yauwa tawan hakan ma zayi” wata nannuyar ajiyar zuciya ya sauke a ransa yana fad’in duk lokacin da takar dannan ta shiga hannu na bazaki sake ganin ta ba,babu wanda ya isa yayi zatona bare ma har ya tonamin asiri…..

Hannun sa ta rike “Babyna me kake tunani haka naga kayi shiru” a’a ehm! Inatunanin wannan jaririj ne”

“Hmmmm gsky abin tunani ne, Ya zama min dole na gujewa wannan garin dole mubar wannan garin kodan sabida dana ya rayu…

 Wannan dan nawane nizan shayar dashi nono na sannan na bashi tarbiya kamar nina haife sa, baxan taba bari ya gane shidin maraya ne ba, dan Allah megidana ya zamuyi da wannan yaron awanan jejin gashi yanzunan har yamma ta sake yi.. kasan ko bamu fadi ma kowa ba za’a neme mu ba’aganmu ba..  

GASHI man mu ya kare ya zamuyi?”

 hmmm Innnalillahi wa’innaillaihiraji’un Adam ya furta tare da girgiza kansa, wannan wanne irin bala’i ne metayi mishi hakan ne yake nema ya kashe mata ‘da … Ba komai bane se dan karya lalata sunan gidansu ne yasa yayi haka bayaso ace ya mata cikin shege wannan shine dalilin da yasa ya keso ya hallaka wannan jaririn, kyakyawa dashi , jaririn da besan komai ba,kawai kawoshi duniya akayi amma akeso a wahalar dashi tinyana cikin tsinmansa..

    Insha Allahu rabbi nayi alkawarin koda zan rasa komai dana mallaka arayuwata sena bashi kariya iyakar bakin qoqarina har sena cika mata burinta amma abu daya dayake damuna acikin zuciyata shine, takar darnan datace tabani da sirrinta da yake ciki gaba daya,bsannan kafin lokacin ta gaya min cewa zata bani wani abu amana ne kar na bude kar kuma na karanta dan girman Allah se har ta haihu abinda ta haifa na bashi dan tasan cewa tabbas za’a bibiyi rayuwarta, za’a kasheta baza su barta araye ba  saboda wannan abunda ta aikata ze lalata sunan mahaifin sa da siyasan sa dan haka bazasu  taba barinta araye ba ,zasu  kasheta..  Nima nadaukan mata alkawarin bazan taba bude wannan takardar ba harse sanda danan ya girma sanan nadauka na basa lokacin inya dauki mataki zanji abinda kecikin takardar nan.. sedai kashhh!!!! Tayi shiru tare da share hawayen dake gangaro mata… Babu takardar nan babu labarinta banganshi ba alokacin danashiga har na dagata inna tinanin Ashraf ya dauka Innnalillahi wa’innaillaihiraji’un kawata shikenan baza abi miki haqinki ba, baza a bibiyi wanda ya kasheki ba mekika masa arayuwa haka?. Hmmm matata ya muke ciki? Ya kamata musan abinyi dan ni inna fada maka bazan bari danan yayi rayuwar maraici ba kamar yanda nayi ba kasan dai banida uba banida uwa inna zama ne awajan wan babana ba irin azaban da be gana min ba ba irin wahal halun da bansha ba dan ayanzu ya nemeni ya rasani wallahi na tabbatar baze taba damuwa ba kuma baze taba dana sani ba, dangin mahaifiyata kuma zanje garesu zan kuma gaya musu cewa zanyi tafiya ne me nisan gaske ballallai nadawo yanzu ba… sabida nasan tabbas zasu bibiyeni zasu bibiyi rayuwata akan wannan  takardan, Ashraf se inda qarfinsa ya qare  dan seya karbeshi idan yasan yana wurina sedai matsalar daya nikaina bansan inda takardar take ba ayanzu ballantana nasa ran zan ganta har indauketa ni fatana shine Allah yasa basu dauki wannan takardar ba idan sun dauki wannan takardar gaba daya kashin mu ya bushe…

TAURARI WRITER’S ASSOCIATION

WRITING

BY

UMMU FU’AD(HUMKAM)

21-23

Adam banda Susa k’eya ba abinda yakeyi ga wasu zafafan zufa da suke keto masa,badan  hankalin  fatima atashe ya keba tabbas zata hango damuwar dake fuskar mijin ta k’warai da gaske.

Shirun da yayi yasa ta cigaba da cewa “My honey ya zamuyi gashi  kamar magrib tayi gurin ya fara duhu, bansan yadda zamuyi ba,gsky inajin tsoro gashi marata ciwo take min matuk’a”

“Innalillahi ya zanyi yanxu baby ki nutsu dakyau kinsan wannan jejin sunan sa k’are kukan ko?” Ahankali ta d’aga masa  kai alamun eh! Hannayen sa ya dafa kafad’unta d’ayan hannu yana share mata hawaye dake bin kuncin ta,

“Ki daina kuka ba abinda zai same mu da ixinin Allah.kiyi shiru muyi tunanin mafita” wace mafita ce  a yanxu da gari yayi duhu kawai ka k’yaleni kila  ta wannan hanyar ne  nima zan koma ga mahaliccina” 

“Dan Allah karki k’ara furta irin wannan kinji  muna tare dake,duk wuya duk d’ad’i,baxamu tab’a rabuwa da juna ba,tare zamu raini boy har ya girma muyi masa  aure  kinji”

Wani k’ayataccen murmushi ta saki tare da rik’e hannayen sa tana kallon yadda duk ya rud’e ahankali ta furta 

“I NA sonka miji na, dalilai dayawa yasa nake k’aunar ka,kai adaline,yanxu anan jejin zamu kwana?” 

“A’a akwai wasu bukoki Dana gani lokacin da muka taho, INA tunanin mutafin gurin nasu mu kwana idan Allah ya kaimu gobe sai Musan abinyi ko?”

“Ban yarda ba ka dauki wayar ka kakira  Mana Ashaf yazo ya d’auke mu kawai Dan Allah” lallai NA yarda  da cewan da akeyi  mata ba kuda hankali,banda abinki a nan jejin zamu kwana?”

“Baby kalli can kamar mutane ke xuwa da ruwa a jarkoki ko?” Eh! Haka ne,ki jirani anan ina zuwa bari naje gurin su ko zasu d’an taimake mu”OK adawo lfy,Allah yasa adace”ameen”yace

Ya.kama hanya da gudu yayi tafiya mai nisan gaske kafin ya isa  gurin su suna ganin sa kowa ya fito da makaman sa

“Malamai Ku tsaya niba mugu bane,kada ku cutar dani,wlh banzo gurin ku da niyyar cutarwa ba,hasalima taimako nake nima agurin Ku”

Wani jibgege mai Suna burguji yace “idan ma da cutarwa kazo me zaka iya mana kaga  wannan saman  jakunar to man petir  ne acikin sa Wlh sai mu babbake ka”

“Alhamdulillah,waiyoo dadi,yanxu na tambaye Ku mana” Dan Allah zaku iya saidamin dashi?”

“Eh!to zamu iya Dan Dana SBD matafiya cikin sahara muke siyowa anan muke saida musu,Saidai gaunati bata yarda  da yin hakan ba”

“Ku yarda dani wlh Maine yakaremin a mota ga matata ba lfy hari b’arin ciki tayi ku biyoni zaku fi gasgantawa”. Ka wuce gaba muna biye dakai….

Tafiya sukayi mai nisa kafin suka  k’araso inda  Faty take a lokacin ta gama baiwa  Ashraf madara  kenan saiga su,ta tsorata matuk’a da hannu Adam yake  nuna mata cewa ba komai ..

Kallo d’aya Burguji ya mata, ya kasa d’auke idon  sa gareta shiru yayi yana naxarin…can yace 

” Falmata bakya tsufa ne?Ashe zamu ganki araye,Allahu akbar ,kai Gujiko ga falmata yar gidan Sarki Mahmoud….

“Yeeeeee da gudu suka k’arso suna zuwa  suma  kallon mamaki  suke. Yadda Faty sak  Sarauniya Falmata…

“Allahu Akbar, yau masarautar ….” da hannu Faty ta masa alama da kayi shiru,hakan kuwa akayi 

Adam yace bangane abinda kuke  nufi,Wannan fa mata tace sunanta fatima ba Falmata,Dan Allah karku kwacemin ita wlh a yanxu Nafi bukatar ta fiyee da komai,kawai Ku d’auki jaririn kuyi tafiyar ku” hahaha wannan alama ne da yake nunamin baka da gsky Burguji yayiwa yaran sa alama da hannu su d’auke Adam ,cak  duka daga shi, su Dan yi tafiya kafin suka tsaya …

Burguji yace “Falmata kibiyo ni, mu koma gida  sarki ya makance SBD rashin ki masarauta sunyi kewar gimbiyar su,shin daga kike haka?” Kayi hakuri sunana Fatima sunan Dada ne Falmata itace ta haifeni”

“Alhamdulillah hiyeee kinga  tsaya bari NA rubuta miki komai acikin wannan da kin koma gida ki bata tabbas zata nemi gida  awannan lokacin masarautar ta yana jiran gimbiya Falmata,hannu tasa ta amshi wannan kwalin 

” Dan Allah ya sunan masarautar Dan Dada bata tab’a fadimin ba,Kisha kurumin ki bazata so kisani ba Sunan masauratar ya fadi mata

(Fatima bataso kusan sunan masarautar SBD tsaroo)

“Ido naga ta zaro tana masa  kallon mamaki” k’warai kuwa Dan haka muna jiranta NA rubuta komai harma  da yadda zata shigo ,kedai kawai ki tabbatar kin bata wannan sak’on”

“Insha Allah zan bata Saidai mai ya k’are mana bamusan yadda zamuyi ba”

“Kai Ku dawo dashi” Adam da yafara sakin fitsari a wando cewa yake …

“Ngd!ngd da Baku cutar min daita ba” hmmmm yanxu ma saimun fitar daku wannan jejin zamu dawo ka d’auki wannan jarkan ka duddule ta yadda zata isheku,bana bukatar godiya kaidai nayi yadda muka  umar ceka”

Hakan kuwa akayi bayan sungama Adam ya tada mota suna tafiya Burguji da tawagar sa suna binsu abaya…

Ashraf ne ya fito wanka hannun sa rik’e DA towel yana share jiki..wayar sa dake ringing ya d’aga PAPI ya bayyana ajikin screen kirjinsa ne ya buga 

Hannun sa NA karkarwa ya d’aga “Aslm papi” Duk inda kake kazo gidan su Ashmat kasa me ni gobe da safe idan Allah ya kaimu”kitt ya kashe wayar 

Yadda Ashraf yaji mortar Papi yasan ba lfy…..”hmmmm waya  ya d’auka ya dialing number Samira ,ringing daya  ta daga 

“Samira inafatan komai yana tafiya yadda muka  tsara” don’t worry sir,komai yana tafiya daidai da yadda muka tsara,akwai wani abun farin ciki da ya faru sir”menene wannan? “Adam yamin text yanxu wai yana so mu hadu dashi gobe insha Allah” OK! Duk yadda kukayi ki sanardani kinji”

“Angama sir” Saidai fa Ashmat ta mutu”Jimmm yayi k’irjin sa na bugawa yace “wannan shi yafi dacewa da’ita,ke dai  ki hanzarta tura Salamatu k’auyen su,ki bata kudin da nabaki sannan ki tura mutanen ki su rik’a monitoring d’inta kar asamu matsala ” Angama sir”yauwa ya batun hijab din kinsa  agurin kuwa?”hmmmmm sir Ai komai ya tafi fiye d yadda muka  tsara Dan kuwa harda Zoben Nan dake hannun ta,dama yau tacire shi da zata sawa  wata mata hannu,tana ajiye shi ni kuma NA d’auke batama gane ba har wannan abin ya faru”

“Wow! Good job Samira dame  zan biya ki ne?” Ka aureni shine burina”

to fa masu karatu Sark’ak’iyar YAWAN SHARHI YAWAN TYPING

shin kun yarda Samira ta auri Ashraf

BY

UMMU FU’AD(HUMKAM)

24

“Hmmm Samira kenan, a gsky zuciya ta mutum d’aya tak take so,bazan iya had’a ta da kowa ba,har abada,kuma sanin kanki ne ni ba irinki nake so a matsayin Matar aurena ba,Sam bakya daga cikin jerin Matar da nake da burin aura,kuma wlh tallahi daga rana irin  ta yau karki sake furta min irin wannan kalaman idan kuma kink’i to kuwa bazaki k’i gani ba”

Ya katse wayar tare da Jan wata doguwar tsaki “banda wauta irin naki nasan cewa mugayen halayya gareki kuma NA aure ki?Allah ya kiyaye wlh gwara NA mutu babu aure,wawuya kawai”

Shikadai ya keta magana ,har ya sa wata jallabiya ash color ya kwanta Saidai me da ya rufe ido Barci yayi awon gaba dashi ,cikin Barcin  ba abinda yake gani sai Ashmat tana nuna masa wani gida tana cewa 

“My honey wannan shine gidan,wlh shine kayi agaji Dan Allah” firgit ya tashi yana kalle kalle, ya tsorata matuk’a shiru yayi yace “gsky ne banyi addua ba NA kwanta Barci dole NA rika mafarki masu abin tsoro”

Washegari misalin k’arfe bakwai NA safe su Adam suka shigo  gida  

“Kai Alhamdulillah, gsky munji  jiki sosai my man” ai kinfini ma jin jikin bari NA sirka MUKU ruwa KI masa wanka to kawai tace ya tafi  toilets ya hada mata ruwan wanka tace 

“Kaga bari nafara yiwa Ashraf sannan sai nayi nawa ko?”  Eh! Gsky kuma hakane ki masa saiki taki daga baya” hannu tasa ta d’auke shi xuwa toilet,ahankali tafara cire masa kaya har taxo  wandon sa, tana cirewa takar dar ya fad’o tayi saurin d’agawa takaishi d’aki ta aje …

Sannan tadawo ta fara masa wanka…Saida ta wanke shi Tass ta d’auki towel ta nannd’e shi aciki suka taho d’aki mai ta shafa masa,acikin Kayan da suka fara siya ta d’auko  guda ta sanya masa yayi kyau matuk’a ,

Ta fito parlour da murmushi d’auke a fuskar ta tace”My man kalli yaron nan sai kace kaga yadda yayi kyau masha Allah “hannu yasa ya amshe shi da murmushi ” gsky ina son Ashraf fatima,yaron ya shiga raina dayawa,Allah ya raya shi bisa tafarkin addinin Muslunci?”ameen mijin Allah yaba shi ikon cikawa mahaifiyar sa burin ta”Hmmmm ai babu takardar kinga kuwa ba maganar wani buri,ni dama  Wlh banason tashin hankali”to albishirin ka naga takardar acikin wandon sa, gsky Ashmat tayi dabara da yanzu  sunsan cewa takardar NA cikin wandan sa NA tabbata bazasu bari ba”

“Kai alhamdulillah kina nufin takardar yanxu haka tana hannunki?” Eh!tana hannun na,amma Kai zaka rik’e ta SBD ni mace ce kuma inada  rauni,Dan Allah ko bayan raina  ka tabbata ka damk’a masa wannan takardar ahannun sa”

“Karki damu my baby zan tayashi wannan yakin  amatsayina NA mahaifi” peck ta manna masa tare da cewa ina zuwa  bari nayi wanka saina d’auko ma takardar ko?”

“Eh!gsky ki hanzar ta Dan akwai maganar da nakeso muyi” baka da matsala bani 2hours zan fito” tana gama magana tayi kamar ta shiga toilet saina ga tayi kwana ZUWA library dinsu ta kulle kofar ……

“Gefen Ashraf kuwa tunda ya tashi ya shirya yana fitowa gidan su Ashraf ya nufa direct…”

Lokacin da ya isa k’arfe goma da Rabi NA Safiya_ya samu dumbin mutane a k’ofar gidan  daga cikin su akwai mahaifin sa, kowa NA masa ta’azziya ganin haka yasa Alh Mu’azzam mik’ewa ya nufe shi,

“Ashraf NA ganin mahaifin sa ya rissina da niyyar gaishe shi hannu ya d’aga masa tare da cewa 

” bana bukatar gaisuwar ka”yana magana a fusa ce,Ashraf ya kama hannun sa ya fizge yana nuna shi da d’an yatsa …

“Me ka aikatawa Matar ka? Wani irin laifi tayi maka da zaka mata wannan mummunar sakamako,eyee ka fadimin” da Saudi Abban  Ashmat ya shiga tsakiyar  su, ya rik’e hannun alh  Mu’azzam zuwa cikin gida tare da Ashraf suna shiga yace.

“Alh shin kanada wata shaida da nuna cewa d’ana Ashraf shine ya aikata wannan? Shin bazaka rufawa  ‘Yar asiri ba? Kodai.kafin so kowa yasan cewa ta mutune ta hanyar haihuwar ‘Dan da ba’asan mahaifin sa ba? Nasan cewa kai din adaline da’ace muna samun shuwagabanni irin ka da wannan k’asar tamu ta gyaru,ban tab’a ganin shugaban da yake ziyartar talakawan sa ba kamar ka.kaifa kasan cewa shaida ya nuna mana fatima aminiyar tace ta ka sheta”

“Malam Safwan bank’i batun kaba,amma ya fadamin Inda ya shiga yinin jiya har ya kwana baixo Anyi jana’idar Matar sa dashi ba” Yana gama magana motar police NA parking yace 

“Yauwa officer Ku tafi  dashi office dinku Ku tabbatar kun jigata shi sannan ban amince da zuwan kowa gurin saba har saiya ya shirya fadin gsky, ku gana masa axaba ta yadda ko.d’aga hannayen sa bazai iyaba idan ya shirya fada mana gsky Ku kirani”

“Pls Papi Dan Allah,nine fa Ashraf d’an da kafi so” Yi mana shiru kana tunanin soyayyar da muke maka zai rufe mana ido mu goyi bayan. K’arya?Wlh muddin kana sa saka hannu acikin kisan  Ashmat to kaima a kashe ka wannan shine adalci,yadda nake mahaifiyar ka haka wannan” ta nuna Umman Ashmat “haka itama take Uwa ga Ashmat Dan haka inspector Ku tafi dash “

“Duk hankalin mutane yadawo Kansu MUSAMMAN yadda Alh Mu’azzam yana kallo a ka tafi da Ashraf,shi yasa talakawan sa ke matuk’ar kaunar sa.

Ana tafiya da Ashraf shima ya shiga motor suka wuce ciikin hanyar su na tafiya saiga wata tsohuwa tukuf ta rik’e icce aka tana tafiya dakyar har sun wuce yasa driver dinsu ya koma baya …

Ya fito murmushi ya saki yace ” inna sannu inayini”da murmushi itama tace lfy klau yaro “yauwa inna Dan Allah kizo ki Shiga NA kaiki gida “

Ido ta zaro tare da hura masa goro a fuska tace “Aniya bi aniya kawai.nashiga motar ka salon kamin fyad’e ina tattalin budurcina” dariya maganar ya bashi ganin a k’alla zatayi shekaru saba’in da doriya take maganar budurcina,

“Haba Inna wlh bazan cutar dake ba ki yarda dani mana” Niii a’a kwarankwatsam bazan Shiga ba salon yadda kake lashe baki kamar tsohon maye nima ka lasheni “ya salam yanxu dai baba kawo iccen NA rakaki ko?” Eh! NA yarda amma da sharadin daga bakin k’ofa zaka tsaya,Dan bana so mutanin angwa suga kafito daga gida na su d’auka kwarto NA Kawo, alhali so nake nasamu Yaro saurayi NA aura mu durji soyayyar mu”

A kafadar sa ya sanya iccen yana dariya yace “To Inna ainima saurayine” ni Dan Allah kadaina kirana da inna,wannan ai salon ka kashemin kasuwa ne,dubeka wai wani inna saika ce tsohuwa”Sorry t….”ohni lantana naga takaina kai wai meye haka zakiyi magana kawani turo baki wai ,soru salon iskanci”

Shaidai  dariya yake suna tafiya mutane sai kallon sa suke wasu na gaisheshi itako Sai mita take wai yaga diri ya like to Wlh kwalelensa ….har suka iso k’ofar gidan yace 

To baba gashi ta amshi iccen tana cewa “Yaro kasan me Wlh nakamu da shaukin Sonka?” Ido ya zaro yana mata kallon MAMAKI” dalla  rufe ido kana wani zaro ido, kodai nayima yarinta ne”ta k’arasa maganar tana wani juyi tare da d’aga masa gira “Ah wanene nima sonki nake yanxu dai tunda naga gida yau xanfara ZUWA zance,ga kudin zance NA fara biyanki”

“Amshe kudin tayi ta watsa masa banason komai naka,kai kadai nakeso kuma wlh muddin kace baka sona kashe kaina zanyi” ta k’arasa maganar da kuka  shiru yayi yana kallon ikon Allah wani dabara ya zo masa ….

Wayar sa ya Ciro yace zo ma kigani photo zamuyi aiko ta daka tsalle Saida zanin jikin ta ya cire ya rage daga ita sai wata katuwat skirt mai hade da bante …yana gama daukar su yace 

“Masoyiya Zanin naki ya fadi” subhanallah Wlh bansaniba ohni lantai salon naje NA TADA maka hankali kamin fyad’e,har Zata d’aura zanin ta galla masa harara”haba masoyiya miye NA hararan,rufe idon ka nadaura zani”tafukan hannun sa yasa ya rufe 

“A’a Wlh nKi wannan ma salon tuzairaine kana lekomin skirt ta nan hujin” hahaha to na cire hannayen kinga NA rufe idon da k’arfi”

“Saida ta tabbatar ya rufe kafin ta Daura zanin” to bude NA daura”hmmm kumafa kinyi kyau “hahaha Dan ma banyi wanka ba,da zakajira ai sainayi wanka NA fito ko?” Yauwa gsky kije kiyi zaki kara kyau 

Tana juyawa ta rika tafiyar yanga da silifas din ta da ya sud’e ta Shiga gida ..

Yana ganin ta shige ya cilla mata kud’i saiga speaker da kansa yana gudu yana jiya da baya ko zata fito…..

Saida ya tabbatar bazata Ganshi ba ya tsaya ya kira driver dinsa yaxo ya d’auke shi

Bayan Fatima ta fito wanka saiga Adam ya SHIGO yace  “Baby ina takardar nan yake Dan gwarama mu adanashi dakyau”

Auho gashinan dama jiranake ka shigo  saina baka”ta d’auki takardar ta mik’a masa ..

.

Wani hot smile Adam yayi ganin shafin farko an rubuta I LOVE YOU SO MUCH MY SON

ANA ZATO lbr cike da sar`kak’iya Zalunci fyad’e Mulki da sarauta k’arya da cin amana  uwa uba kisan kai

Page 25

Hannayen sa ya d’ora kan kafad’un ta yana mata wani killer smile,itama Murmushin tayi tana  ta d’ora tafin hannun ta saman nasa tace “Mijina Shalele na,shin kana buk’atar wani agareni? Umarni kawai zaka bani cikin nuna isa da tak’ama,sbd kaine shugaba,kaidin miji nane wanda aljanna na k’ark’ashin k’afar ka, shiyasa nake jin tsoron bacin ranka,kada kak’i d’agamin domin na wuce”

“Haba dai Matar so,aini tuni na d’aga, Allah ya miki albarka ked’in kin cika mace tagari mai tsananin biyayya saidai ….” Shiru yayi yana shafa fuskar ta yana murmushin da ka gansa  kasan baikai cikin zuciya ba,fatima kuwa da sauri  ta juyo gare shi tana cewa “Sai dai me mijin,kayi gaggawar sanar dani,Dan na roki ya fiya agare ka”

Ta k’arasa maganar tana d’aukar little Ashraf  kamar yadda naji tace dashi..

Kallon ta Adam yayi yace” meyasa kika d’auke shi bayan yana Barci”SBD na k’ara  tofa masa addu’a Allah ya karamin shi”Karki damu d’awainiya nane na Baku dukkanin kulawata ki kwanta bari na siyo.mana abincin ko ?” 

“Eh!to kayi hakuri na yau SBD yadda nake jin jikina ba d’ad’i bazan iya girki ba,dan Allah ka yafemin kaji” tana maganar cikin shagwab’a tare da rausayar da kai”bayan ta ya d’an buga  yace na hakura baby na INA ZUWA”har ya kai bakin k’ofa zai fita  Tayi saurin cewa 

“_Takardar dake hannun ka amana ce agaremu nasan cewa ni macece kuma mai rauni yasa na baka koda bayan raina ka tabbatar da cewa takardar nan Ashraf kad’ai zai Karanta,kayimin alkawarin bashi kariya?” Insha Allah Matar so nayi alkawari”OK u can go ” 

Tunda Ashraf ya Shiga gidan kaso ba abinda ya fara tunawa sai toilet din sa Wanda a girma yayi ukun d’akin aka sashi  shiru yayi yana nazari wani k’ato da ka Gandhi kasan irin rik’akkun ‘yan daba ne,da wata iriyar murya mai tsoratawar yace 

“Kai Yane naga kana wani eh!basarwa,ya juya  ga mutanen da ke binshi abaya kud’an sashi yaji eh!wasai had’i da welcome kun gane ai”

“Sai Guxungu” suke fadi d’aya daga cikin su ya shak’o Wuyar rigar Ashraf cikin isa da tak’ama Ashraf yace shin kunsan  koni d’an waye”Dalla Malam bamu tambayeka wannan ba”gwaf suke buge mishi baki da Saida ya fashe yana fitar da jini,Hannu yasa yana sharewa ya cigaba da cewa Nine nan d’a ga maigirma speaker Alh Mu’azzam Musa”baki suka bud’e gaba d’aya suna cewa laaaa gsky Anyi asaran kudin Tara kai ga ubanka Malam mutumin kirki mai taimakon talakawa amma anyi  rashin sa a kai kuma kazama d’an ……”kafin suka rasa dukan su suka hau kanshi da duka suna fadin  sannu da zuwa  eh ahaaa,aito  wlcm ne,idan zasu d’ago daga dukan da suke masa sai suce “eh!” Sannan xuba masa duka suna cewa “Ahaaa”

Saida suka masa litis dukan sakwaran afawa yayi laushi sosai ko iya d’aga KAFA ba yayi saiga masu aikin gidan prison yazo ganin yadda suka masa ya tsorata matuk’a yayi saurin juyawa office Dan ya kira ogan su “Guxungu ya zaro wuk’a a kasar wata dotse yana cewa ” Yane kawai kace musu Mishkila akasamu eh!ka Suburbud’omin zagi,nikuma na Samface ka da mari,idan kak’i fad’in haka eh!cikin dare zan xungura ma wannan wukar eh!acikin ka,na zakuloo hantar ka,a gasamin Na eh!Murzata abakina,Iyaka  aita shari’a daga k’arshe ace anyanke hukincin kiss eh!ta hanyar rataya,hahaha yoo dama mutuwar nan fa dolen eh gyatumar mutum ya maragaya hahh”_ Ya Allah kudubi yadda yake ambatar mutuwa batare da yaji ko d’ar na imani acikin zuciyar sa ba,saima dariya da yake shin atunaninku wannan laifin iyayen sane da basu bashi ilimin addini ba,ko tarbiya ne basu dage a kansa ba,Ya taso cikin angwa baisan xuwa massalaci ba tun yana d’an shekara bakwai shi zai fita ya nemo yayi tallan pure water a titi,ahaka zai samu abinda zaisa abaki,to shi mahaifin sa babu ruwan shi da ciyar da gida iyaka dai ya bada na dare shima ba kullum daga ya dawo uwa zata ce Audu d’an ban hamsin na siya k’annen ka Alala suci yunwa sukeji,zai d’auka ya bata bubu ruwan ta da inda ya samo kud’in_ kuma baxa ta tambaye shi saidai ta washe baki tana cewa yaron kirki shiyasa nake sonka_

Gobe idan ya fita baisamu ba,saiyaji bazai iya zuwa gida a haka daganan tunanin sata zaifara to dama baki koyar dashi cewa sata ba abu bane maikyau,Daga yakai 15yrs kwace bada shiba, satan kayan mutane bada shiba,daga haka zai fad’a hannun muyagun abokai sufara gwadamar yadda ake shan sigari shikenan kuma.Ya ke Uwa kisani cewa ‘Ya’yan nan amana ne Allah ya baki kuma zai tambayeki ranar gobe k’iyama,k’iyama k’iyama,Wallahik azeem zaizo karkiji anata ambaton kice har yanzu?lalala Zaizo wlh awani hali zai riske ki?zai risken?zai riski yaran ki?kina da yara baki damu da janyo su jikin kiba? Shin kinsan cewa a halittar yaranki akwai wanda yafi Sha’awa mace ko na miji kin taba tunanin tsaya tsam kiyi wannan tunanin kuma wai sunanki Uwa ga yanmata agabankj wancen tafi rawar kai amma baki d’auka komai neba,Na tausaya miki wlh,Shin kina d’aukar yaranki kawai ki kaisu wajan wasan yara kuje shopping koda ice cream ne kawai ki saya musu ku xauna kuna hira cikin jindadi sannan ku dawo gida? Kinsan hikimar haka?to bari kiji samari sun gane cewa Mu hausawa bamu damu da irin wannan ba,da sunfara soyayya da yarinya saiya nuna mata tace miki gidan kawar ta zasuje tayi assignment kin sake baki ta fita, ya dauke ta zuwa Sahad farko tana fara ganin wurin zata fara cewa Wow!gsky ya had’u Murmushin cin nasara zai fara yace saima kinga ciki, naga saurayin da ya kashewa budurwar sa 300 ita kuma sai yauki take a dole sunzo shoprite, iya ice cream ya siya mata,plz Uwa ki duba ki mik’e Sannan bazaki fadi ba dan kince yaran ki I love you,ina son ka Musa sbd ka iya kaxa da kaxa”

Ya k’arasa maganar yana lashe wuk’ar da ke hannun sa da harshe ya maida shi k’asan dutse,Murmushi ya fara ganin su officer sun k’araso Kai yadai me suka ma?”laaa bakomai bugewa nayi da jikin wannan bangon gsky da zafi”

“OK!sorry anjima zanzo na kiraka da akwai maganar da zamuyi ” to!kawai yace ya zaun Dan jiri yake gani …

Bayan sallah Isha’i Fatima ta fito cikin wasu sleeping dress dinta red gashin ta da yasha gyara ta juyo dashi kafad’ar ta takama da red ribbon sai k’amshin humrar UMMU FU’AD ke tashi tunkafin t k’araso k’ashin shu’umar humra ta fara kawowa Adam gaisuwa…lumshe ido yayi tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya …

Idon sa a rufe ya bud’e hannayen sa yana cewa Oyoyo Matar so k’arasowa tayi tare da shigewa cikin jikinsa ajiyar zuciya ya k’ara  a karo na biyu yana cewa inason wannan k’amshin ko da cikin bacin rai nake Dana jiyo k’amshin ki sai naji zuciyar ta sanyaya”hot hug ya bata yana cewa Matar so menene sirrin dake cikin wannan k’amshin Dan tabbas irin naji ajikin…….ash……”

Shiru yayi yana wani nazari can kuma yace Ashwariya A film din……”hahaha a film din Adam da Fatima ko?”Dan naga alama ka Lula dayawa”gsky na Lula har naso na saki layi ko ?”kama saki layin ai “ammm ai kece kinsan sirrin yadda zaki sacewa mutum zuciya …

Harbin bindiga yasa shi yin shiru, Fati kuwa fitsari ta sake a zaune tsabar rud’ewa harbi a kumayi a karo na biyu bullet ya fasa  glass din window,

” innalillahi wa Inna ilaihi rajiun “shine Kalmar da Adam ke fadi bugun k’ofar da ake musu yasa su yin shiru Faty ta rik’e Adam…

” Fatima kizo ki bude k’ofar da hannu ki ko kuma muyiwa gidan nan wanka da alburushin mu”Daga waje ake fadin haka,kuka fatima take tana cewa Kar su rabani da amanata,amanata,little yarona,ayya ni fatima waiyoo, Addu’a zamuyi kinji bari na bude musu “Kai ta Shiga girgixawa tana zubar da  hawaye harda majina ” karka bud’e kashe mu zasuyi kabari Dan Allah karsu illatamin yaro”Idan ban bude zasu kuma yin harbin  kuma bamusan ta inda  zasuyi ba kar ya samu little Ashraf “Da sauri  tace ” na na …na ya…r….da”

“Am…..amma ka tsaya na b’oye d’an amana a backyard saika bud’e musu” wai bazaki bud’e k’ofar bane?ko dai mu bud’e da kan mu” Da hannu yayiwa d’aya da cikin magana ya fasa glass din window 

Adam najin sun fara fasa glass yace d’auko d’an amana hannun ta na b’ari tana kuka ta d’auko magana  take dashi kamar wacce ta zauce”nayi ma addu’a karka damu kaji bafa komai neba kawai dai Wasane kuma Munyi bak’i karkayi kuka zasu rabamu kayi shiru ko da harbina sukayi kaji ko d’an amana”kamar ya San me take cewa ya tab’e baki xaiyi kuka tayi saurin. Hade  bakin su guri  d’aya yayi shiru tace 

“Kayi shiru d’an amana kar suji kukan ka” d’akin Adam suka shiga wardrobe dinsa ya danna da k’arfi saiga wani d’akin ya bayyana babu abinda d’akin ya rasa kallon tuhuma takewa Adam yace ki Shiga ki aje shi ki.fito kanta  taji ya fara harbawa tsabar mamaki da tambayoyi abakin ta masu yawan  gaske ,amma tayi shiru 

Da sauri ta fito ya rufe suna gama rufewa barayin har sun shigo d’akin hannu suka fara mik’a Mata ,,kawai kibamu takardar da Ashmat ta baki babu abinda zamu miki

“Wani takardar?” Mari babban cikin su ya wanka mata Saida ta d’auke wuta kuncin da ya Mara ta rik’e tana cewa to Ku kashe ni tunda Baku yadda da abinda nace ba,

Wani marin zai kuma Adam ya tare  hannun ya nuna shi da yatsa karka fara tab’amin mata wai kai wani irin banzane maza irina ya kamata ka Tara Dan fada ba mace ba “

“Hahaha hahaha” dariya kawai suke lokaci guda suka gimtse fuskar kamar basune sukayi dariya yanxu ba

“Ka gayawa Matar ka tabamu takardar ” Babu wani takardar “Adam ya basu amsa.da hannu ya nunawa ya ransa su dake shi,su ka fara dukan sa Fatima tana kuka tana basu hakuri amma sunki saima dariya da ogan. Yake yana lashe baki …..

Wayar da ke cikin aljihun sa tafara ruri alamun ki ra da sauri ya d’aga ” A’a har yanzu “to oga angama yace tare da kashe wayar yana dariyar  mugunta 

Adam da suka masa litis duka harda kan bindiga ko hannun sa basa motsi ogan yace Ku bank’are Mun ita hahaha oga muma zabamu rabon mu ko?” Dolene ai kuma kunsan  shigar bullet Zan mata na  fice abuna hahaha” yana magana yana cire belt da doguwar wando y rage daga shi sai boxer. Adam da yake gefe rintse ido yayi ko magana ya kasa yana kuka fatima tana kuka tana cewa 

“Kuji tsoron Allah ni Matar aure CE,” Hahaha Saduji KAFA ji  wai Matar aure ne ya liliyo ashar ya maka mata “kai kusa tayi shiru “

Mari kowannen su ya bata kafin suka sake cire belt dinsu suka Shiga jibgar ta,tun tana kuka har tayi shiru jin haka yasa ya d’aga musu hannu da su ky’aleta hakan kuwa akayi ..

Dariyar mugun ya fara yana matsowa inda  take gashi dama Kayan jikin ta babu murfin kasa,…..)

ANA ZATO lbr mai cike da tausayi zalunci Kisa fyad’e saurata mulki soyayya

“Mumini zaiyi burin haɗuwa da Allah a lokacin mutuwarsa, kuma shima Allah zai yi burin haɗuwa dashi, domin haƙiƙa shi muminin ya ƙarar da rayuwarsa ne wajen yiwa Allah da manzonsa biyayya ne dalilin hakan sai yasa Allah maɗaukakin sarki yayi masa kyakkyawar tarba”

“Sannan ba ya ke tawa wata mace haddi kawai dan son abin duniya,Wanda idan kanwar sa ce yaga zawa haka tabbas shidin nasan sai inda k’arfin sa ya k’are …

“Amma kuwa wanda ya ƙarar da rayuwarsa wajen saɓawa Allah da manzonsa, to haƙiƙa yana cikin haɗari da fargabar da bai taɓa shiga cikin irinta ba anan duniya”

“Manzon Allah (S.A.W), yace: shi mumini idan mutuwa ta bijiro masa, lallai ana yi masa bushara da samun yardar Allah da karamarsa ne, babu wani abinda yafi soyuwa a gareshi face sai abinda yake a gabansa, yana son haɗuwa da Allah, kuma shima Allah yana son haɗuwa dashi”

Bukhari ne ya ruwaito”ta k’arasa maganar idaninta na zubar da hawaye bayan hannun ta tasa ta goge tacigaba da cewa

“Dan…..” Kafin ta k’arasa taji ya rumgume ta ihu tayi niyyar kurmawa yasa hannu ya to she mata baki Adam na ganin haka ya fara ja da mazaunan shi har yakai toilet yana shigo ya daidai lokacin da Yake kokarin rabata da Kayan jikin ta Adam yace ga takardar’

“Girgiza masa Fatima take tsabar bakin ciki ta kasa cewa komai kuka yaci k’arfin ta dariyar mahaukata suka fara suna cewa shegen bakaso na fada rijiyar ka ko?kafi kai kad’ai kaita  wurga kwallo Dan ashana kawai sukayi ficewar su

Wani irin kuka mai tsuma zuciya da ban tausayi fatima ta saki tana cewa ” Adam baka kyauta min kana tunanin zan barshi ya ketamin haddi? Meyasa bakayi amfani da kwakwalwar kanka ba a matsayin ka na namiji,haba yanxu ya zanyi?me zamce?ta yaya zamu gane makashin Ashmat?wace irin hanya zanbi Dan sanin mahaifin D’an amana,wlh ka cuceni nayi Dana sanin baka yarda ta, ada na d’auka nidin mai rauni ce,nice bazan iya jure wahala ba. Na d’auka duk abinda zasu maka baxaka tab’a yarda kabasu wannan amanar ba,Ashe na tafka babban kuskure a rayuwa ta Dana yarda dakai,,wallahil azeem daga rana irin ta yau bazan sake yarda da kowa ba akan yarona”

A wahalce ya nuna kansa  da d’an yatsa yana cewa “Harni bazaki….” Eh har kai,ta fadi cikin tsawa ga mida kuka ,Kaine ma farkon Wanda bazan k’ara yarda dashi ba inaso kasan cewa wlh ka bani MAMAKI matuk’a da har zaka d’auki abinda zai taimaki dumbin mutane ka damk’awa mugaye axzulumai Ashraf ne ya turo su Dan su wulakan tani  kuma tabbas shine maka shin Matar sa,mutum ne shi mai fuskar biyu,mai son zuciya bayan ya lashe zumar ta batada amfani a gareshi shiyasa ya kashe ta”

“Fatima ki d’auko d’an amanar ki” da k’afa ta rik’a ja har ta isa bakin wardrobe d’in saidai tayi-tayi ta bud’e ta kasa bud’ewa babu yadda bata gwada ba amma fir yak’i budewa…

“Killer smile Adam yayi yana cewa ” Akwai security ai yan mata idan ba ni bane wlh ko zaki shekara bazai bud’e.ba ki zo ki taimaka min na tashi saina bud’e SBD Yaro na nasan yanxu haka yana jin  yunwa”

“Ni d’in mai biyayya ce  agareka mijina kayi hakuri ka yafemin bisa  lafazin danayi Mara d’ad’i dazu agare ka,duk da cewa raina yana bace ha Yar yanxu amma ka yafemin karkayi fushi dani tunda bansan lokacin mutuwa ta ba”

Anan fatima ta nuna mana yin fad’a da miji  har kiyi fushi batare da kin nimi yafiyar sa da kuma bashi hakuri babbar illane gareki,wasu matan na tafka babban kuskure da ya ka mata ace duk mace tagari yasan cewa aure ibada ne,mai tattare da kalubale,hakurin nan dai shi zamu yi

Da kyar ya iya mikewa ya ya tura saiga wardrobe din ya shige ciki da sauri ta Shiga ta d’auko jaririn ta manna masa kiss a goshi  ya fara kuka kamar yasan wacce zata bashi abincin sa …

Kallon Adam tayi tana cewa “kaga yana kuka ko?tambayar mu yake meyasa zamu bayar da wasiyyar mahaifiyar shi?meyasa?meyasa?” Ta k’arasa maganar tana kuka mai cin rai…..

Wani d’aki babban mai makeken gado mutum d’aya na hango kwance yanata juyi sai cewa yake lantai nima inasonki,bazan miki fyad’e ba sunnah zan raya dake “shiru yayi yana kallon p.o.p dake Saman d’akin bakajin k’arar komai sai na AC idanun sa a rufe ya jingina bayan sa jikin gado ..ga dukkan alamu tunani kawai yake ….

Ahankali ya fara bud’e ido ya mika hannu zuwa kan wani drower dake jikin gadon ya kunna Radio kuka jiyo da saurin ya fara waigawa ko zaiga mai kukan kusa dashi ….

Ya jiyo D’an jarida yana cewa Inna ya sunanki?” Sunana Lantai babyn Dan saurayi”Tofa yanxu me yakawo ki gidan radio Humkam me kike bukata “Dan Allah Ku taimaka min wlh na kamu da shaukin son sa tunda na hadu  dashi,yaro kasan wlh mutumin kirkine shi,ko da zanina ya fadi a gabansa baiyi yunkirin yimin fyad’e ba,tun daga wannan lokacin nayi shaidar sa,idan har baizo gareni ba tabbas zan kashe kaina wlh” to ya sunan sa”d’an gayu”haka ake kiransa”a’a nice dai nake kiransa da haka”kinada phote sa?” Eh!inada shi”Dan jaridar ya sauke ajiyar zuciya yace Alhamdulillah komai xaizo da sauki  INA fatan kin taho da photon”ai wlh yana nan gurina bai bace ba”ta nuna masa cikin Zuciyar ta da d’an yatsa “hahaha gsky ne inna karki damu yanxu ki tafi gida zamu bada cigiyar sa insha Allah zai zo” kuka ta saki tana cewa “d’an gayu wlh ina sonka burina muyi aure kaxo gareni ko na kashe kaina”

“Masu sauraran mu Dan Allah duk Wanda yasan wani mai suna d’an gayu ya Samar dashi cewa wata tsohuwa” mari ta gaurawa d’an jaridar Saida ya rik’e kuncin sa ta cigaba da cewa”wlh kana kara kirana da tsohuwa saina cirema yan maraba kalleni dakyau idan kuma ka k’arya ka kuma fadi kaji wannan Marin da nama kadan kaji”Shiru d’an jaridar yayi yana mamakin wannan mata anya mutum CE”

“Alh Mu’azzam dake zaune ya nata sheka dariya harda rik’e ciki saiga Hajiya Zainab ta shigo jikin ta d’auke da Kayan Barci tace 

” Alh lfy kake dariya haka?”hhhhhhhh wlh dole na dara ya bata lbrn duk yadda sukayi da lantai har kunna radion da yayi,ya fito da photon da ya musu ya nuna mata,mezatayi banda dariya tana cewa to kai yanxu ya zakayi 

“Zan aure ta kamar yadda take so gsky na tausaya mata awannan shekarun nata” hmmmm haka ne indai irin tane ka auro Dari baxanji komai ba”ngd yace ya d’auki waya ya bar d’akin a parlour   ya zauna kan  3siter wata number ya dialing ringing d’aya ya d’aga yana yi masa sallama daga d’aya bangaren ya amsa tare da gaisuwa bayan sun gaisa yace “rankai d’ad’e Dan Allah  INA bukatar Form din takardar senator wannan karan mai girma governor INA fatan zakabani damar  siya.

“No need to say it out pls,  zan baka kuma Kaine za kaci,SBD kai d’in jajir tacce ne musamman idan na duba yadda kake d’awainiya da talakawa jiya naji ka tafi kauyen Kiru har ka taimakawa wa yanda iftila’in gobara ya afka musu, tabbas ko takarar Gauna ka fito mutanen garin  nan zasu Mara ma baya,kamar yadda ka saba taimakon xaurawa yau naji wata mata tana niman d’an gayu ya zakayi da’ita” Insha Allah zakace kuma ni  zabin Allah nake nima akan dukkan lamura na,batun wannan Matar kuma ni da kaina zan aure ta”Meyasa?ka San ta ne?”Sirrin zuciya ta ne wannan”OK! Sannan batun takarar  governor kuma shima na kusa xuwa gurin insha Allah “Alh  Mu’azzam kasan fa ba jam’iyar d’aya da kai ba,meyasa bazaka dawo  T G T  (Tallafi Ga talakawa)ba?”

“kayi hakuri rankai Dade bazan iya barin  A D T(Agaji dan talaka)ba sbd  irin hidimar da jam’iyar tamin”Gud  mu had’u dakai a gurin babbar Malam Zayyanu Dan ya duba mana ya fitowar taka zai kasance “Hmmmmm aini tuni na tashi tsaye rankai dade wlh na Dade da Sallama lamura na ga  Wanda baya gyangyad’i bare Barci,Allah  (S.w.t) yana cewa  ya Ku wad’anda sukayi imani!Ku bi  Allah da tak’awa.sannan kasani akwai lokacin da bawa  yake kusanci da ubangijin sa sosai  wannan lokacin shine time dinda  kayi sujjada yana dakyau ka tsananta addu’a a wannan lokacin Dan kusa kake da ubangiji,INA Kara tunantar damu muhimman cin tsayuwar dare (kiyamul lail)  Ita sallan dare tana sanya ka kusa da ubangijin halittu,sallan dare lokacine na amsa addu’a,akwai boyayyar lada ga Wanda yake tsayuwar dare,” Thank you Mu’azzam ya batun son Nasa  ankawomin shi yanxu haka yana government house tare dani,idan kai baka son sa Ni ina so dama kasan NADIYA har ciwo tayi lokacin auren sa,tanajin mutuwar Matar sa,ta sake yimin magana Dan haka zan had’a su aure badan komai ba sai Dan manufata,Wanda ba lallai kasani ba”

“Manufar ka ai shine had’a xumunci” ni da kai munsan haka,amma dagani har mahaifiyar sa munfi so ya dubo gidan talakawa SBD a taimaka musu,sannan yaron nan kisan kai yayi amma ka goyi bayan sa,meyasa?bama son auren,money marry money” Mu’azzam yanxu kana nufin bazaka bari ya auri nadiya ba?”Ban isaba SBD Nadiya ‘yata ce  ko gobe kana iya daura  musu aure rankai Dade,bazan tab’a ka ma sirikina ba koda na zama governor “hahaha lallai na yarda kai d’in babban k’waro tunda kayi saurin gano logo na” Hmmmm siyasa kenan,rankai Dade Ina baka hakuri lokacin da zan kai kukana gurin mahaliccina yayi dan yanxu 3:am sai gobe idan Allah yasa muna numfashi kayafemin idan nayima laifi SBD bansan lokacin da mutuwa zata riske ni ba,saidai na kasance duk k’arshe addu’a ta INA cewa ALLAHUMMA A INNI ALA  GAMARATIL MAUT

“Shiyasa nake son ka SBD kai ne me fadimin gsky komai Dacin ta babu ruwan ka da mulkina” ai rankai Dade tunani ya kamata mu rik’ayi Duk izza da murlkin fir’auna ina yake yanzu? “Ina k’aruna yake? Idan ma kana jin kanka kai din wani babbar kwarone ya kamata murika komawa muna duba tarihin wadanda suka gaba cemu” hakane ngd sai Munyi waya “

Suna kashe waya  ya fad’a toilet yayi alwala yana zuwa ya tarar  da momy ta idar da sallah tana jero addu’a hawaye na bin fuskar ta,murmushi yayi yana k’ara godewa Allah da ya bashi mace ta gari mai yawan ibada 

 

gidan su Ashmata 

Umma tana zaune banda tunanin mutuwar ‘diyar ta ba abinda take, Abba yace kiyi hakuri Bilkisu komai zai wuce,Allah yajikan Ashmimin Abba,tace Abba rayuwa da mutuwa duk suna hannun Allah kawai kai bawa  kaxama mai YAWAN zikiri da tasbihi sannan ka zama mutum na gari,Dan kuwa abincin tsutsane kai watarana,wannan lamari yana matuk’ar bani tsoro bilki,SBD tun ranar da Yarinyar ta gamu da wannan jarabawar farin. Ciki ya kaurace man”to Malam tambayst shine INA jaririn wa mata ciki?waya ka sheta?meyasa danayi waya da’ita take cemin kar na yarda dashi?wanene ,shi d’in?

nima tambyar da nake kenan wanene maka shin ki Ashmat m,Ashraf ne ko Adam Dan gashi yanzu nadiya  ta SHIGO,hmmmmm kadan kenan daga cikin sark’akiyar ana ZATO mai wuyan fassarawa

PAGE 27

Ashraf zaune a wani k’ayataccen parlour fadi MUKU kyansa zai cika min d’an karamin littafin nan nawa batare da na gama ga dukkan alamu charting yake yana murmushi wajan voice ya danna yana cewa 

“Na fadi miki zan fito kuma za’a rufe babin Ashmat da shegen d’an ta,hahaha” itama ta maido masa da voice kamar haka

“hmmm ai wlh bantab’a sanin kai mugu bane sai wannan karan gsky ka matuk’ar bani mamaki duk soyayya da kukeyi da Ashmat ka mance” fita daga charting yayi ya dialing number ta ringing d’aya ta d’aga yace 

“Har gobe ina son Ashmat,irin son da bazan. Tab’a yiwa wata ‘ya mace ba,Ashmat macece ta gari mai yawan ibada,wata biyar kad’ai mukayi inuwa d’aya hmmmm” hannu yasa ya share hawayen da ke zubo masa ya cigaba da cewa ….

“Dolene yasa na aikata haka SBD taci amanar k’au……

Shigowar Nadiya yasa yayi shiru tare da katse wayar ” Murmushi tayi gami da zama kusa dashi har suna gogan jikin juna ….

“Nadiya me kikeyi haka?” Shagwabe fuska tayi tana cewa nidai ina fata ba kana magana akan wannan shegiyar Matar taka bane ko? Dan Wlh na tsaneta,I hate her” 

“Hmmmm Nadiya ta Riga da ta mutu ” Nafi kowa farin cikin mutuwar ta Dan kuwa Hmmmm bama ita ba Wlh duk macen da tayi gigin zuwa gareka da sunan so tabbas daga ranar sunan ta GAWA” Ta k’arasa maganar tana tauna cingam tare da huro kwai cikin kwarewa ta k’ara  duban sa dakyau 

Ta lumshe ido tace “Muna  da kudi,muna da  mulki, idan ka mance Grany  dina shine Sarkin Daura sannan dad d’ina governor anan Nasarawa Brother din mom Governor a katsina,hmmmm Dan haka wannan karan babu Wanda ya isa  ya hana aurena dakai,saidai idan bana numfashi Wanda a yanxu dai kam nasan da saurana tunda ko furfura ban fara ba”

To fa kasurgumar jahila a tunanin ta mutuwa bata d’aukar yara ne sai manyan  wannan kuskure ne babba …

© Fatima ce  ta Zaune tayi ta gumi wani shu’umin murmushi tayi tare da ‘Yar k’aramar dariya tsam ta mik’e tana cewa Umma ta lokaci yayi da zan san ahalinki,lokaci yayi nima xanga gata na duk da cewa nidin…..shiru tayi ta k’arasa d’akin da Adam yake a kwance yana waya,yanajin bud’e k’ofar ta ya katse kiran….

A gefen katifa ta zauna tare da kiran sunan sa “Mijin,lokaci yayi da Zan baza ma niman dangin mahaifiya ta sannan ina so kayi aure,idan na same su Zan ne meka insha Allah ngd da kulawar ka gareni” kallon ta kawai yake ya rasa abinda zaice …..

Wayar sa ya d’auka ya mata transfer d’in kudi ya cigaba da cewa “bazan

..

.. 

 . Hanaki ba Dan tunkafin ki aureni sai da mukayi yarjejeniya Dan haka INA miki fatan alkhairi,na so ace kibari.na samu lfy mutafi tare amma ..bakomai Allah ya cika miki burinki na alkhairi kinji” ameen kawai tace ta tashi ta d’auki d’an amana ta Goya duk abinda zata bukata ta d’auka…..lokacin da ta fita tasa kaya a motar maigadin gidan su ta kira sukayi magana….

Ya fita saiga shi yadawo tare da Matar sa da  yarinya suka Shiga motar ya Shiga gurin zaman driver ……

Adam banda cizon lips d’in sa ba abinda yake ganin kira nata shigows wayar sa ba sassauci yasa shi d’agawa cikin zafi yana cewa 

“Me kike bukata kuma daga yau banason na sake ganin kiranki cikin waya ta,SBD dama wannan takardar shine tsorona kuma babu su a yanzu suna gurin ki”

“Na sani amma nima basa hannu na suna gurin oga Dan kuwa nasan yanzu ya konata da hannun sa,kasan me?Ya fito yanzu haka yana government house tare da maigirma governor,kaga  shikenan zance ya mutu “

“Ni ba abinda ya shafeni, da damuwa na guda  wannan takardar kuma babu” to wai kodai Kaine ka d’irkawa Ashmat ciki?” Samira” ya kira sunan ta cikin tsawa yana cewa ” karki k’ara gayamin wannan magana idan kuma kinki hmmmmm” kayi hakuri Adam,amma ina Fatima take” tana d’aki  tana ta kuka wai ita  amanar ta ….ko kallon ta banyi ba”OK! Ka kula da kanka karka tab’a bari ta gane wani Abu tattare dakai”Insha Allah hakan zanyi”

Suka kashe wayar a tare ya kira Fatima ringing d’aya ta d’auka yace 

“Kuna inane yanzu” Ga mu nan Mun kama hanyar Wani k’auye mai suna kabi acikin garin inda wa ta katse wayar …

Shiru yayi yana naxarin maganar ta “hahaha wato na biyoki idan Zan sha wahala”….

Wacece fatima me take boyewa mijin ta, waye  maigadin gidan ta, shin ina ta nufa me zai faru da rayuwar Little Ashraf?

_PAGE_ 28

WACECE FATIMA

Falmata dai itace mahaifiyar Fatima, asalin falmata haifaffiyar Kasar Niger ne,acan wani gari da ake kira da AGADEZ falmata itace babbar ‘ya Ga sultan of AGADEZ.Sarki Sanusi Muhamdou shine mahaifin falmata,yana da mata hudu, mahaifiyar Falmata mai suna RAKIATAU itace ta hud’u a gidan Sultan Sunusi,duka matan sa ba Wacce ta tab’a haihuwa RAKIATAU na zuwa Allah ya albarka ce ta da samun juna biyu, hakan ya matu’kar ta yar da hankalin sauran matan matu’ka musamman uwar gida,Sultan kuwa har walimah Saida ya kira… RAKIATAU ta sha tsangwama wajan Yan uwan ta,dik yadda zasuyi Dan azubar da cikin nan sunyi Amma inaa  Allah ya kare Saida ta haihu ta haifo ‘yar ta santaleliya sak mahaifin ta,murna gurin Sarki ba’acewa komai sai hamdala.falmata ta taso cikin tsana da tsangwama acikin gidan su ,a lokacin ta zama cikakkiyar mace sultan ya sa ranar da za anada ta a matsayi. Tambura(princess) matan sa suka je gurin wani malami mai suna Akiluu aikin ka kamar yanka wuka hakan yasa suka tabbatar Masa da cewa suna so yayiwa falmata jifa da zata mance komai sannan yasa ta tsani duk wani Abu  da ya shafi dangin ta da k’asar ta.sannan ya makantar da’ita. hakan kuwa a kayi bayan sundawo suka sa wasu daga cikin hadimai da su d’auki falmata suka wota garin Kano su ajiye ta a jeji,hakan kuwa akayi lokaci guda aka nimi falmata a masarauta aka rasa.hankalin Sultan ya balain tashi…yaci Kuka sosai ya bada cigiya tare da makudan kudi ga dik wanda ya kawota shiru..

Lokacin da hadimai suka kawota wannan ruga da aka ajiye little Ashraf anan suka aje falmata.cikin ikon Allah saiga Alh usman  da babbar aminin sa,Kuma d,an uwan sa Alh Sagir sunzo wajan fulani da suke musu kiwo zasu koma gida.saiga falmata tana kuka, lokaci guda sukayi magana 

“kaga wata kyakkyawar fuskar tana kuka” jin maganar su yasa ta d’ago jajayen idanin ta dan ta kalle su amma INA duhu kawai take gani

“Alh Sagir yace wlh wannan ko aljanace Bismillah zanyi kawai na taba ta,idan bata bace ba,to nasamu mata,idan Kuma ta bace to saina hakura”Dariya Alh Usman yayi yana cewa nadai samu mata karma mufara Yar haka da kai”kee ya sunan ki?” Shiru bata basu amsa ba,Alh Sagir yayi Bismillah y tab’a mata hannu yaga bata bace yayi  hamdala yana murmushi ya koma motar da niyyar d’auko mata ruwa Alh usman yayi saurin cewa “Ina son ki Dan Allah ki fadamin sunanki,kuma ina rokon ki da kisoni kinji?”kai kawai take girgizawa tana magana da frenchtan nuna Masa bakin ta da cikin ta,cikin Fransanci tace “kabani ruwa, inaso nasha”Sam baigane abinda tace ba saima dukan goshin sa da yayi ya ce “Ohni Usman ga ranar french yayi nak’i tsayawa a makaranta na’iya kullum idan malamin yaxo saidai na dira ta window na gudu gashi ranar amfanin ta yazo, min”yana cikin tunani saiga Alh Sagir ya zo da ruwa ahannun ta yasa ruwaa ta kafa baki bata cire ba Saida ta shanye  “cikin yaren french yace 

,Ya sunanki “tayi shiru ta kwance wani kulli dake  zanin jinkin  ta na  saiga wasu zobuna guda biyu da ‘yan kunnen a zurfa an rubuta Falmata, ta Mik’a Masa ya amsa yana murmushi ya duba yace “kenan falmata shine sunanki?” Amma ya naga kamar bata gani” yake cewa Alh usman nima haka na lura saidai wlh ko kurma ce Kuma makauniya to Ina son ta Kuma ina k’aunar ta,Kuma duk rintsi da zafin kishi irin na hajiya Rahama bazai hanani auren ta ba”hmmmm wannan tawa ce Dani t dace ba kai ba tunda kana da mata ni Kuma tawa Allah ya mata rasu…..”kafin y k’arasa falmata jiri ya debeta tayi luu zata fad’i dukan su suka kai hannu da niyyar rik’e ta ta fada jikin Alh Sagir

29

“Inna lillahi wa inna ilahi rajiun,me ya sameta haka,ko dai za muyiwa su Innawuro magana ne?” Alh musa ya had’e fuska yana jin zafi a zuciyar shi da Falmata bata fad’o jikin sa ba .yace 

“Ba zamu tambaye su ba,Dan Wlh banaso su rabani da’ita kawai ka sata  a motar,Watakila Yunwa take ji” haka ne”Ko NA  taimaka maka”a’a bar ta kawai”alh sagir ya fadi tare da Dora ta bisa  kafad’ar sa zuwa ciki motar…….

Ya kwantar da’ita ya juya wani rafi dake kusa da rugan ya debo ruwa mai sanyi,ya yayyafa mata,firgit ta tashi tana Sosa ido tare da wata katuwar hamma. Hot smil Alh sagir yayi lokacin da ya tuno da Kindirmo da su Ard’o suka basu tare da manshanu mai yawa, yasa bakin robar swan Saida ya cika ta dam sannan ya jijji gata. Ya mik’awa Falmata a hannun ta,aiko tanajin roba kamar ta ruwa ta kafa kai jin kindirmo ne yasa tayi murmushi ta cigaba da yasha….

Tunda ta kafa baki bata cire ba,Saida ta shanye …. Ta kuma yin murmushi da yake k’ara fitowa da kyanta .

Alh Musa da driving kawai yake amma hankalin sa na gurin Falmata har suka iso gida….suna shiga duk Wanda ya d’ora idanin sa akan Falmata sai ya ruga da gudu 

Sbd Falmata Farar mace CE sosai,ga ta siririya,gashin kanta mai ywa gashi bak’i tana sanye da rigar gidan sarauta ajikin ta..

Lokacin da Gwaggo lantai ta hangi Falmata da gudu ta ruga hr zanin ta ya fad’i tana cewa 

“Duk Wanda yaga tsirara na  shida Allah” amma bata fasa gudun ba har ta isa  k’urya d’aki tana haki tare da rik’e k’irjin ta

Alh musa ne ya shigo hannun sa rik’e da Zani yana dariya yace 

“Gwaggo ga zanin ki,Dan Allah ki fito Matar da zan aura ne,NA Kawo miki ita,kiganta…..”

“Musa Wlh ka fita ido na  tahm,hauka kake?nace hauka kake zaka d’auko aljana kace ita zaka aura, yau zan ga abinda ya kashe kaka ta Juma,Musa ina Sagiru yake? Gani nan Gwaggo Dan Allah ki fito kinji”

“Niii na fito taji Dadin cinyemin Hanci Dan NA lura tunda ta shigo dogon hanci NA   kawai take kallo,ja’ira”

“Gwaggo Dan Allah muka ce ki taimaka mana” a hankali Gwaggo lantai ta fito tana lekawa ko xata ganta…ganin parlourn ba kowa sai Alh musa da alh sagir yasa ta fito.

“Duk Ku taho kuyimin bayanj  dalla  dallan inda kukayi wannan mummunar gamo da aljana” Gwaggo ba fa aljana bace, mutum ce, kamar kowa”karya kuke wannan ko acikin aljannun ita sarauniya ce,acan  dan haka kuyi gaggawar komawa da’ita inda kuka d’auko ta,tunkafin su fara niman ta” Alh sagir yayi shiru yana naxari yadda zai b’ullowa mahaifiyar shi,wani dabara yazo masa yayi saurin cewa

“Gwaggo kince kina so kiyi aure,kuma d’an saurayi,sannan kyakkawa ko?” Eh kuma ina nan inajiran sa zamu hadu watarana “

Shiru sukayi na wani lokaci alh Musa yace “ai gwaggo mahaifin falmata shima yaro ne kuma kyakkywa”  da gaske kake?”eh!har munyi magana dashi amma kin ga baxai yuba sbd

30

kince musu aljannu,kinga kuwa babu sauran zance”kai dalla ga fara baxan tab’a son wannan aljanar ba,bare kuma ubanta,Ku hanzar ta d’aukar Ku har gidan nan da’ita Ku tafi can bakin rafi Ku sake ta za kuga ta b’ace”

Alh sagir yayi saurin cewa “Gwaggo Dan Allah ki tausayawa zuciya ta ki taimakamin Wlh zuciya na zata  iya bugawa idan babu Falmata” Au Sagiruu kaima to dawa zanji Musa yace yana son ta kaima kace kana sonta  anya kuwa? Ba aljannun ne suka shiga jikinku ba? Ku biyo ni”

Tana fitowa babbar parlor taci karo da Falmata “Wa innahu Sulaimanu,ya Allah waiyoo ni lantai kee ja’ira koma gurin ku mana,tuff tuff aniya bi aniya tuff-tuff” ta rika to fa yawu …

Alh sagir yace Gwaggo kiyi hakuri makauniya ce,kuma kamar ma batajin Hausa”Ina ji amma ba sosai ba”

Falmata tayi magana cikin sanyin murya,a Saba’in Gwaggo lantai ta arta da gudu tana cewa kunji ko har maganar ma ba irin namu bace “tunda Lantai tabar gida a wannan ranar ,ta koma asalin gidan iyayen ta da taga gada Dan tace muddin suna so ta koma to saidai Falmata ta bar gidan….

Anyi  gurmuzu sosai tsakanin har  Saida wan mahaifin su ya shiga zancen inda yace ita Falmata ta zabi Wanda takeso aciki,Alh Sagir ta zab’a,hakam baiyiwa Alh Musa dadi ba tun  daga wannan lokacin ya kullaci Dan uwan sa…

Bayan auren su da shekaru biyu Falmata ta haifo yarta kyakkawa tana saukowa duniya ita kuma ta fara wani matsannancin ciwo hakan ya dagawa kowa hankali gashi Duk maganin da aka bata  indai ya shafi laluran ta sai fatar jikin ta su fetso da wasu irin kuraje masu fitar da ruwa mai wari,dole aka hakura har lokacin ta yayi tabar jaririyar diyar ta mai suna fatima 

Kowa a familyn yaki amsar fatima SBD diyar mayya suke kiran ta,Alh Sagir ya ajiye komai nasa  yaje kauye ya d’auko Abuwa tazo suna  renon fatima tare,,lokacin da fatima takai shekaru biyar  shima rai yayi halinsa,rikon fatima ya koma gurin Alh Musa,lallai fatima tasha wuyar rayuwa kowa ya tsaneta barin ma lantai gashi mahaifin ta ya bar dumbin dukiya amma government school aka sakata a nan ne ta hadu da Ashmat kusan kullum daga makaranta sai sun so gidan su Ashmat umma ta basu abinci sunci sannan fatima ta kama hanyar gida…kowani Yaro da babba a gidan Alh Musa a motar ake  fita dashi Duk inda zashi banda fatima abinci ma sai kowa yagama ci sannan ita take samu taci 

.

Akwai wata mai Suna Sajida da Maryam sune  aminan Falmata tun zuwan ta garin Kano,a hannun Sajida Alh sagir ya bar rigar Falmata da suka fara haduwa da’ita da yan kunnen ta,Ya bar mata wasiyyar cewa lokacin da fatima ta mallaki hankalin ta,yana so ta bata wadannan Dan sune  shaidar mahaifiyar ta,hakan kuwa aakayi”ta damk’awa fatima sune  ranar auren ta,lokacin da Fatima ta gama secondary school alokacin Adam yaron Sajida ya gama jami’a kuma Alh Musa yace iya inda  zai iya daukar nauyin Fatima kenan Dan haka aure zai mata.

Sajida NA jin haka tasamu kakar su fatima Malam jaxuli ta sanar dashi bukatun ta,kwarai ya amince kuma ya d’auko wata paper ya mika mata tana budewa tags wasiyyar alh sagir ne da yake cewa yan so Adam ya auri fatima Dan yasan zai kula masa da’ita SBD tunda aka haifi Fatima Adam yana dawowa makaranta gidan su fatima zai nufa yaje suyi ta renon ta,tare da Baban ta,idan kuwa tana kuka  shima ya rika kuka kenan har sai tayi shiru,shakuwa ce mai karfi a tsakanin su,

Tana gama karantawa tayi murmushin jin dadi tace “Baba kasan halin Musa tabbas kamar yadda ya fada sati mai zuwa zai aurar da’ita ga Me angwa SBD rashin mutunci,Wlh ko NI nan aure na ya mutu bazan auri me angwa ba bare kuma fatima”

“Karki damu yau za’a Daura auren fatima da Adam,sannan nasa ansiyo mata form na school of Nursing,Dan nasha tambyar ta saitacemin shi take so,batun Musa kuma ki kyaleni dashi yau zai ji Daura auren da azahar inyaso bikin mubari sai ta gama karatu ko?”

“Eh hakan ma yamin dadi ngd sosai Allah yakara maka lfy Baba” amin yace,tana fita ya kama hanya zuwa gurin lantai ya kora mata bayani…cewa tayi batasan wata fatima ba Dan haka ya kyaleta …

A wannan rana aka Daura auren Adam da fatima Saida ta gama karatu sannan akayi biki ta tare gidan mijin ta…

wannan shine tak’aitaccen tarihin fatima,wacce a yanzu naji tana cewa driver ya kaisu airport Saudiyya zata

31

Da saurin driver ya juya yana mata kallon mamaki Hajiya saudiyya fa kika ce,umara zakije ne naga kin d’ebo KAYA dayawa irin haka”

“Yan uwa  akwai kudi na tura muku sannan zaku daina zama acikin gari saidai inason duk k’arshen sati zamu waya daku duk abinda yake faruwa Ku sanar dani,sannan inaso ka dibo wad’anda kasan cewa duk wuya duk dadi baza suci amanar ka,ka sanya su lura da Adam…xaka tafi gidan Gwaggo lantai da gidan Momy Sajida inaso ka sanar da kowa hatsarin nayi kuma na mutu..akwai gawar da tayi  accident a can asibitin mu,kamar yadda Safnah t fadi min zaku had’u da’ita  a bakin hanya motar nan zaku maidata Mara amfani,sannan kaima da Matar zakuyi  hakuri ne,kamar dai yadda kuka shirya xa d’an raunata Ku,Kayan jikinka sai any age wasu guraren ka tabbatar sun yarda cewa motar ta k’one kuma wannan Matar itace nii fatima”

“Ranke d’ad’e angama da wannan batun ai tuni kawai kedai yanzu airport din xan kaiki ko?” Hmmmm duk cikin takun basaja ne siyan tickets da nayi,ba jirgin da zan hau,Mu cigaba da tafiya akwai Wanda yake jirana shima wannan salon taku ne …kaga ana xaton nayi hatsari na mutu…shikenan an shafe babin rayuwa ta,ni kuwa inacan ina renon yarona”

“Hahaha gsky Hajiya wannan takun saike” uhmm yi shiru kawai ga Adam ya turomin sak’o “FATIMA meyasa zaki tafi a lokacin da nake son Gina sabuwar rayuwa tare dake,kuma kika iya tsallakeni a halin rashin lfy,meyasa kuka fifita kawa akan mijinki,ina baki umarni da ki dawo idan kuma kika tafi to abakin aurenki,kije na sake ki saki d’aya”Innalillahi wa inna ilaihi rajiun” shine kalmomin da ta rik’a furtawa tana nanatawa har Saida taji sanyi acikin zuciyar ta …

“Kayi hakuri Adam amma bazan iya dawowa,muddin suka gano gsky ga me da takardar nan kasheni za suyi,ko kuma suji lbrn little ASHRAF bazasu tab’a barin Mu a Raye ba”

“tayi kuka sosai sbd k’aunar da takewa mijin ta,gashi rabuwar su yazo mata baka tatam.ba tare da ta shiryawa hakan ba.

Murmushi tayi lokaci guda ta fashe da dariya ta d’auko wayar …

” Hajiya kina da abin mamaki,yanzu yanzu kina kuka,kika juya murmushi,lokaci guda kuma sai dariya,miyee sirrin ne”

“Wannan tambyar fa?” ta cigaba da baiwa little madara sai da ta gama ta d’auko wayar ta tafara rubuta text kamar haka….

_Hmmmm kowanen Ku kar nake kallon sa,duk wani takun Ku acikin tafin hannu na kuke yin sa,Wlh kunji  NA rantse yanzu aka fara wasan xantafi amma Ku saurari dawowa ta a lokacin da d’an zaki ya girma….mijina kana tunanin ban fara zargin ka bane?kallon ka Kawai nake,naki nuna maka ne Dan karka  gane,shiyasa nayima basaja.wannan takardar da NA baka ,chemistry din Ashmat ne tun muna SS3 yake guri na.Ku saurari fitowar real book a gidan jaridu na safiya,ba wai ina nufin gobe ba a’a Ku dai  Ku tabbatar ko wace safiya kuna Karanta jaridu Dan tana iya zuwa muku nan da 3months,Nadiya naga sak’onki ta WhatsApp dama na Dade da sanin kema da sa hannunki a Kisan Ashmat,hahaha ASHRAF,ADAM MIJINA,NADIYA,SAMEERA,ina gaisuwa,nice dai fatima Sagir ‘Yar mayya_”

Tayi marking number Ashraf  Dana Adam ta tura musu Nadiya kuwa ta Facebook ta tura mata,tana gamawa ta kira Safnah ringing d’aya ta d’aga tana cewa

“Wlh fatima sun jiga ta gashi bazama a gane kamanni ba gashi komai ja motar su ya k’one yanzu ya zayi” Innalillahi wa inna ilaihi rajiun ayya kuma kikace Matar tana manne da baby?” Eh!tare suka k’one sai wani shima sauran dai baxamu iya ganewa ba yanzu nasa  ankira road safety nasan suna  zuwa asibitin Mu za kaisu ni kuma na rika da na k’ona sark’ar da kikabani gasu a hannu na wadannan keys din dasu zan nunawa Adam ko?”hahaha Safnah har kin fini shiri,shikenan ngd,kiyi kokarin sanar dani duk abinda ake ciki”OK shikenan,

Wani cikin jeji fatima ta rika nuna musu sunyi tafiya mai TSAYI kafin  tace  Ku tsaya,wata motar ta taho daidai inda suke ta tsaya Fatima ta bude ta shiga  suka zuba mata kaya,kallon Wanda yake driving tayi..

“Ashe ka shirya” hmmm nakai 1hour anan ina jiranki Dan tun jiya muka iso kasar nan bisa umarnin ki ranke dade”ngd sosai da kulawar ku, lokacin da na duba wannan rubutun naka daka bani a lokacin naji ina sha’awar ganin yan uwana musamman danaji kana cewa nidin jinin sarauta ce …..”

“K’warai kuwa daga  yau nasan nagama arziki a duniya ngd da baki wuce kai tsaye ba,Dan zanfiso ace da kaina na fara shiga dake masarautar Agadez”

©tunda text ya shigo wayar ASHRAF ya keta tunani to wani takarda ne  fatima take nufi,shi lamarin  ya d’aure masa kai,”

Fita yayi daga  gurin message ya dialing number Samira ringing d’aya ta d’aga tana cewa”Yanzu nake  shirin kiran ka”Samira kinsan wani takardar da fatima take magana akan sa?” Shiru Samira tayi kafin  tace  “takardar kuma gsky bansaniba,me ya faru?” Yanzu Fatima tayimin text cewa wai takardar da nasa azo a amsa bashi bane ta bayar wani ne daban,ni kuma Wlh ban tura kowa ba”ka kira Nadiya ka tambaye ta,ka Santa sarai wajan rashin mutunci,kuma banda abinka  dana  San da batun takardar zan fadi maka Musan abinyi tun…..Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.. Number motar fatima ake nunowa a breaking news,ya salam fatima naso muyi magana”

“Kafi  kowa sanin Nadiya shegiya ce  ina zaton itace ta had’a wannan hatsarin da fatima tayi” katse wayar yayi yana kokarin dialing number Nadiya saiga Alh Mu’azzam ya fito cikin wasu dakakkun shadda da suka sha aiki tun daga sama har k’asa …murmushi yayi Wanda ya k’ara fito da kyansa yace..

“Son yau nefa daurin aure na,amma naga ko wanka bakayi ba” Dady ka tafi kawai Dan yanzu haka gurin jana’iza Zani na kawar Ashmat fatima”

32

Fatima kuma gsky ya kama ta mutafi tare bari na kira mai girma Gauna ya amshi auren ba sai na tafi gurin ba,Abu mafi muhimmanci shine zuwa gurin Jana’iza”

Suka fito tare suka shiga motar zuwa family house din su Fatima wani abin mamaki sai ga Gauna da sauran mutane agurin,speaker yayi mamaki k’warai sai da Alh Musa ya sanar dashi cewa ‘yace a gurin sa jika  a gurin Lantai

Adam yayi kuka kamar ranshi zai fita can ya dan jingina kan sa,ajikin bango har aka fito da gawar cikin makara suka sallah ce su.

K’warai a yau Alh Musa da lantai sunji mutuwar fatima amma lantai k’ek’ashe ido tayi tana cewa Yusrah ‘Yar Alh Musa “Yusrah ki goga min barabad’a bakin mana” harda eye shadow duk ta sa ….

Alh Mu’azzam ya kira Alh Musa suka magana sannan ya bukaci a gayawa lantai tayi hakuri bazai iya auren ta ba SBD wasu dalilai …

Alh Musa kuwa cewa yayi ai sungano Alh Mu’azzam na da aljannu masu  duka da zama macijiya idan dare yayi”aiko lantai tace bada’ita ba …

A kwana a ta shi ba wuya gurin Allah yau kimanin shekaru uku da rasuwar Ashmat da fatima 

Anyi auren Nadiya da ASHRAF,Safnah kawar fatima da Adam,lantai kuwa ta nan haka kurum yau taji tanason fita  ahankali take taka tafiya tana reran ‘yan wak’okin ta…..

Saiga wata jeep ta tsaya wasu k’arti guda uku suka fito d’ayan hannun sa rik’e da hankie ya rufe mata baki suka sata cikin motar su ka ja motar da gudu ….

Waya ya d’auka na hango Sunan da OGA Sanusi ya dialing number Saida tayi ringing har  ta katse ba d’aga ba,tana yankewa wata kiran ta kuma shigowa,ya d’aga da farin  cikin sa yace “ina fata kunsamu” k’warai ma kuwa Mun samu  kuma da ka ganta zatakai 80yrs d’in “good job Ku kaimin ita  gidana zan taho yanzu” angama oga ,yanzu saura mutum ashirin da biyar ko?”eh!muna bukatar yara ‘yan wata uku mata guda biyar,Yan 10yrs biyar,yan mata virgin biyar,sai tsoffi guda  uku sannan yara maxa yan 7yrs guda uku,

“Ku kula sannan a yanzu munfi bukatar tsoffin tunda dasu muka fara wannan itace ta biyu saura uku” angama OGA”

Lokacin da suka ajiye lantai gaba d’ayan su fuskar su a rufe take dishi dishi take gani dakyar ta iya furta “Dan Allah karkumin fyad’e nikam guda nawa duniyar ta ragemin,kubarni na fasa yin auren tuntuni d’an gayu ma yasani”

“Hahaha!to banda abinki Gwaggo me  za muyi dake ware kawai” suka rufe d’akin suna dariyar lantai da take cewa kar su mata fyade..

Suna saiga wata motar ta fito cikin wasu gayune guda hudu,suka kin kimo lantai suka wurga a baya sunyi tafiyar awa hudu kafin suka isa wani gida,anan ma waya sukayi sannan suka aje lantai fitar su ke da wuya saiga wata motar irin ta daxu ta shiga gidan su uku nan daukar lantai sukayi sunyi tafiya cikin kasurgumin jeji KAFIN suka ki ta waya  sai ga wani  attajirine ai d’auke da murmushi ya karaso yana cewa 

Aikin Ku yayi kyau Ku samin ita  a mota,suna  saka lantai yayi wani shu’umin murmushi yaja motar tafiya yayi mai nisa sannan ya tsaya a bakin wani tafkeken gida  wasu remote ya fitar saiga get ya bude,ya sake dannawa get na biyu ta bude Saida ya danna sau biyar kafin yayi parking,cak  ya d’auko lantai bayan ya shafa mata wani abu a fuska yana murmushi ….

Bai aje ta a ko inaba sai kan tafkeken gado Mao fadi da yasha kwalliya….

Wani d’an k’aramin tukunyar k’asa ya d’auko yana murmushi, yasa hannu a ciki ya Ciro wata farar Leda da aka kulle  ruwan wankan gawa acikin ya zuba mata a gaban ta, ya shiga kiran ….

K’iri k’uuuuu,guso,k’iri k’uuuuuuuuuuuyana zuba ruwan ajikin sa ya cigaba da cewa 

“Bazanyi sallah ba,bazanyi wankan tsarki ba, har sai kuncika arba’in k’iri k’uuuuuuuuuuuuu” ya k’ara zuba ruwan sannan ya afkawa Lantai amma saida  ya tabbatar yasa security

Har ya gama abinda zaiyi lantai tana kwance kamar gawa yana gamawa haka ya sanya hannu ya kwashe duk kazantar da ya zuba mata  har na cikin jikin lantai. ya zuba cikin wannan tulun ya tura shi  k’asar gado yana murmushi……

CIKIN gari

Gaba d’aya yan gidan su Alh Musa sun bazama niman Lantai duk inda suka San tana zuwa sun tafi amma babu ita hankalin su ya matuk’ar tashi musamman  da suka tuna wannan lokaci da muke ciki.na kiddanaping, da fyde_ Alh Musa ya rasa yadda zaiyi ya fiddo waya  ya dialing number Speaker …

Alh Mu’azzam na zaune kan wata 3siter lafiyayya hannun sa rik’e da cup na shayi yana kurb’a yaji k’arar wayar sa,hannu ya kai zai d’auka  sai kuma ya fasa, ya tashi da niyyar shiga bathroom d’insa Dan azaton sa Hajiya ne Momyn Ashraf  sai yaga Alh Musa,da sauri ya d’aga yana karawa a kunnen sa tare da doka sallama …..

“Wa’alaikumusssalam, rankai Dade,ina yini,ya iyalan” Alhamdulillah ya gida,da gwaggo?”a taimake Mu kamar yadda ka saba Dan Allah…Gwaggo lantai ta b’ata bamu San inda take ba,Dan Allah…”

” Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, tayi me? Ta b’ata tun yaushe KENAN?” 

“Tun da sassafe da ta fito bamu sake ganin ta ba” Ku Hanzar ta Kai report gurin ‘yan sanda”yallab’ai banasone hakan Dan bamu San ko masu  kidnapping bane” OK INA zuwa” ya katse wayar 

“Takaici ya kama Alh Mu’azzam yaja  wata doguwar tsaki tare da kiran D.P.O yana sanar dashi b’atar lantai,ya k’ara da cewa 

” duk Wanda kuka kama kar Ku mar na wasa SBD wannan sace sacen yayi yawa haba me mutane suke son zamane?tsohuwa irin lantai me zaku sata kuyi mata?”Fyad’e rankai d’ade Dan ko jiya ankawo mana wata dattijuwa mai shekaru saba’in a sume anyi mata fyad’e”

“Fyad’e?” Ya maimaita ya dukan k’irjkn sa da hannu

Kitt ya kashe wayar sa ,ya shiga safa da mare’s Number mai girma Gauna ya kira har ya tsinke bai d’aga ba,toilet ya fad’a da niyyar yin wanka amma batun wannan tsohuwa ya tsaya masa a rai matuk’a idanin sa suka kada sukayi jajir yama  rasa me zai ce ,

“Wannan wane irin musibane fyad’e wa tsohuwa?” Kasa wankan yayi yasa kaya ya nufi government house

Naso ganin fuskar wannan dattijo amma ina  ya hanani saima baya da ya juya da lantai a hannun sa yasa a bayan motar .

Kamar dai d’azu remote ya rika dannawa yana bud’e gate Din gidan har ya fita……gudu yake sosai kafin ya iso inda aka BASHI lantai ya m’ikawa wannan da yakawo mishi,ya canza motar ….

Ya shiga  gudu har ya iso bakin titi…..ajiyar zuciya yayi,da gefen ido ya kalli wayar sa,yasa hannu ya d’auka missed called da yawa ya tarar number mutum d’aya ya kira yana cewa da  ganinan zuwa na d’an fitane ..

Wad’anda suka d’auki lantai su suka dawo da’ita har kofar gidan mai angwa suka wurgata k’asa kafin suka tada k’ura …..bat suka bace a gurin 

Hankalin mai angwa ya tashi ganin lantai a kwance babu numfashi da SAURI ya dubi babban d’an yace 

“Ku taimaka min Mu shigar da’ita daga ciki saiku kirawo min Alh Musa” hakan kuwa akayi.. Da sauri  Matar mai angwa suka rufi akan lantai mai angwa yace kee Shamsiya kidan duba ta kiga ….

Ku taho mutafi,bayan sunbar d’akin wacce aka kira da shamsiya ta d’aga zanin lantai da sauri ta rufe  ganin duk ya baci da sperm ….

Tana fitowa Alh Musa na zuwa ..ya shiga d’akin tare da Dr Yusrah jkan lantai drip aka sa mata SBD yadda jikin ta yay zafi sosai ,ko gixau lantai batayi ba sai can cikin dare Ta fara motsi da k’afa  bakinta ma yana motsi…. Alh Musa ya kai kunnen sa daidai bakin ta yaji tana cewa

“Falmata ki yafemin,Yar mayya ki yafemin kiyafemin ” sai shiru yace Gwaggo sun yafe miki, ina kika shiga Gwaggo muna ta nima…..

“Excuse me Dad,Ruwan baya tafiya” ya d’aga ido ya kalli lantai ina  yace tare da rik’e hannun ta,

“Yusrah ki barshi kawai Allah ya yiwa Gwaggo cikawa”

…….

Gaba d’aya d’akin ya d’auka d Innalillahi wa inna ilaihi rajiun…..

Shiru Alh Musa yayi yana tuna haduwar su da safe da yaje gaisheta tana cewa 

“Wato Musa baxaku aurar dani bako? Kunfi so na mutu babu aure,Wlh burina a rayuwa shine na mutu cikin d’akin mijina,amma kun kasa fahimta ta,sannan Baku tsaya kun dubi uzurina ba,mahaifin Ku ya mutu da sauran kuruciya ta amma Sam kun hanani yin aure”

Tana magana hawaye na bin kuncin ta tasa hannun zanin tana sharewa , ta fyace majina   tare jikin zanin ta cigaba da cewa …

“Shin kun tab’a tsayawa Ku tambaye ni dalilin da yasa nake so nayi aure?” Nasha fad’i muku ni Aure zanyi da zaran na Kawo miji sai Ku ta baya Ku tsoratar dashi,ko kuja masa kunne ta yadda bazai sake gigin zuwa gurina bare ma nayi tunanin auren sa”

“Duk nasan komai Wlh nasan cewa Kaine ka hana d’an gayu ya aureni ka fadimin me kuka ce masa kai da Zaituna”

Saida Alh Musa ya Susa k’eya kafin yace “haba gwaggo me kuwa zamuce masa kina fa kallo har antaru yace ya fasa,nidai ina tunanin mutuwa ‘Yar mayya ce ya tada masa hankali kawai”

“Kaci gidan ku ,nace kaci gidan Ku zaka fad’i min gsky ko saina Mazga ma mari”

K’eyar sa ya k’ara susawa tare da sunkuyar dakai yace 

“Ce masa mukayi  kinada ciwon hauka kuma idan ya fi tashi cikin dare gashi komai kika samu kina rank’walawa mutum,harma  ki yanke mar jiki Dan duka kike sosai,kuma ko ina kika gansa saiki rika cewa ya miki fyad’e”

“Shine yace aikuwa haka kikace masa nace to kadan ma yagani”

“Hmmmm ai nasan ruwa bata tsami banza haka kurum bazai ce ya fasa.Musa yau na cire dukkanin kunya ta,zan gaya abin da yasa nake so nayi aure, MusaNi mace ce mai yawan bukata,bazan iya fadi muku ba, ya ka mata ku amfani da kwanyar ku,amma sai kurika cewa gwaggo me xakiyi da aure,ku mai kuke da aure?ka bani amsa mai kuke yi da aure?”

“Kiyi hakuri” ba batun hakuri bane yau rana ce da zan amayar da abinda na hadiya sama da shekaru 30.   kun tauyeni kun hanani aure,wai meyasa Ku ‘ya’ya kuke mana haka,ina nufin Mu mata,meyasa daga kawai kun d’an tasa shikenan bakwa k’aunar kuji iyayen ku  mata sunyi batun aure,ko haihuwa sai Ku nuna Sam bakwa so harma kurika cewa to ke me zakiyi da aure yanzu,muna da bukatar Mu,nima ‘yar Adam ce kamar Ku,yadda kuke da sha’awa nima inada shi”amma k’ir misisi kun hanani,Musa ko kasan  dalilina na komawa tsohon gidan mahaifana,bari na fadima ko da kuwa zaka tsaneni yau saina fad’a,na fake da Falmata ne kawai na koma can,Dan biyan bukatar kaina,kasan aminin mahaifin Ku sabitu, da yazo da batun aure na har k’ulle shi kukayi?”

“Eh kawu Sabitu na gane shi”

“Hmmmmm bayan ya fito ya zo ya sameni akan cewa tunda duk hanyar da nabi Dan nayi aure Kunk’i kuma ni INA fama da buk’ata yana da shawara,anan yamin shawarar na koma can gidan shi kuma kullum zai rik’a zuwa tunda shima ja’iran yaran sa duk Matar da ya aura sai ta fita”

“Wannan dalilin yasa nayi muku shiru akan batun aure” A lokacin da Sabitu ya mutu nayi kuka sosai sannan nayi Dana sanin rayuwar  da kukayi kullum sainayi kuka na duk’ufa rok’on Allah ya fiya”

“Musa ko kasan akwai balagar tsufa,naji wani program na Malam Ibrahim Khalil da yake yi a guarantee radio, inda zaka tsoho yaje ya niman auren budurwa ayita cewa tsofai-tsofai dashi,yayi jika da’ita,kaxa kaza.to Wlh shi kad’ai yasan abinda yake damun sa” naso ace kunji wannan program din”

 “Ina fata zaka barwa yaran ka wasiyya ko da ka mutu kar su hana mahaifiyar su yin aure kamar yadda kukamin har yakaini ga aikata zina,duk cewa nima inada laifi na biye kunyar naje na sabawa mahaliccina”

Ta k’ara sa magana tana kuka mai tsuma zuciya Alh Musa ma kuka yake dakyar ya iya furta ki yafemin zan cika miki burin ki …

“Na yafe muku,nima ka tayani rokon Allah ya yafemin laifi na”

Wani irin kuka Alh Musa ya saki yana cewa Inna bana CE zan cika miki burin ki ba?”

34

Mai angwa yace “Musa addu’ar ka,shi tafi bukata ahalin yanzu,Dan Allah kayi shiru” Baba Mudi Inna ta tafi tabar ni da abubuwa dayawa da zan ta tunani”kayi hakuri Allah yajikan ta da rahama,Allah yasa ta huta, Shamsiya ya kama ta ayi mata wanka a suturta ta ko?”

“Hakan zayi Ku Kawo mana likafani” Alh Musa ya d’ago jajayen idanun sa “Akwai likafanin da take ajewa duk Wanda ya mutu ta bada,gashi yau dashi za suturta ki Gwaggo”

Bayan hannun sa yasa yana share hawayen da ke zubo mishi ya tashi zuwa gida ya d’auko likafanin ya Kawo,text ya rubuta sannan ya tura shi ga duk contact dinsa..

Fatima dake zaune kan wata kujerar alfarma little ASHRAF na rik’e da alqur’ani a hannu na tana ce masa ….

“ASHRAF  ya Sunan ka?” Tunana Ashaf “menene buri Momyn ka?” Buyin mony ta rik’e gsky a duk inda nake nayi yaki da duk azzalumi na zama mutum kirki,kar nayi k’arya,kar nayi zagi,kuma ni jarumi ne,zanyi fad’a da koma waye Dan k’wato hakkina Dana monyna”

Murmushi tayi ta shafa kansa,wani Handsome guy ya fito yana murmushi shima ya shafa tukeken cikin ta da alamu haihuwa yau ko gobe  yace ….

“Mony Mu” ya fad’i kamar yadda ASHRAF yake cewa SBD tsamin baki 

“Nima na d’ad’e da hadda ce wannan amma kullum sai kin sa ya fad’a,fatima Dan Allah ki fadamin dalilin da yasa kike masa haka?” Hmmmm sirrin zuciya tane  kuma inaso ka rik’e wannan yan kunnayen da sark’a wacce Momy Sajida tabani shi,idan ASHRAF yayi aure kabashi a matsayin gudun muwa ta,Ba axurfa bane Gold ne,shine abinda Nafi so da k’auna gaba d’aya acikin abinda Allah ya MALLAKA min” 

Fatima ina ASHRAF ya  shiga” hahaha na tarbiyar tar d’ana muddin ya ganni  tare dakai to ya bar gurin shiyasa kana. Zuwa ya shiga ciki”

“Hmmmm ya ka mata ki…….” Yaji text ya shiga cikin k’aramar wayar sa,yayi saurin fitarwa yaga Baba Musa ..yace 

“Princess Baba Musa ne kila so yake na tura masa da kaya na gurin su ya kare ” OK ya kama ta ka tafi can Dan inason sanin yadda Nadiya,Samira,Salamatu,Ashraf ,Adam suke rayuwa,

Tsuke fuska yayi jin ta ambaci tsohon mijin ta

Ya bude text d’in ganin abinda aka rubuta yasa shi kasa cewa komai,dakyar ya iya furta ..

“Ina zuwa zan d’an ke waya”

Washe gari da safe bayan ankai lantai gidan ta na gsky sun dawo Alh Mu’azzam ya dubi d’umbin mutanin dake gurin ya fara  …

bude taro da bismillah sannan ya cigaba da cewa 

_Ya Ku ‘yan uwana Wlh Mutuwa gsky ne, gashi kuna kallo kuma a gaban ku,yanzu muka sanya ta cikin kabari muka juyo muka dawo,yanzu tana can.

“Mu tsaya kan kyakkawar d’abi’a SBD ita kyakkyawar d’abia tana Samar da gida a aljanna ,muyi rik’o da addinin Mu, riko bilhakki da gsky Allah  yana ce Lallai wadanda su kace  ubangijin Mu shine Allah,sannan suka tsayu kan addinin musulunci babu tsoro tare dasu,kuma baza suyi bakin ciki ba.Wad’annan sune ma’abota Aljannah,sune MASU dauwwama a cikin Aljannah sakamako ne ga abinda suka kasance suna aikatawa.Yaku iyalan wa nnan baiwar Allah da ta rigamu gidan gsky …”

“Ku sani cewa nata ya ja saura ni dake, da dakai yaushe ne zan mutu?” Da wani lokacin zan mutu?me zan kasance ina aikatawa a lokacin?karatun alqur’ani?tasbihi?sauraron wak’a? Nine duk wani wak’a da zai fito saina sanya  cikin waya  waya ta,shin  Gurin party naje?Karanta novel nake alhali banyi sallah ba?ke UWA mai shayarwa lokacin da kike  shayarwa shin bakin ki me yake furtawa ko dai wak’a kike d’anki,shiru kawai like yo ko kuma kina Tarawa kanki dumbin lada,hanyar ,yin tasbihi a lokacin? Ya kamata  Mu tuna wadannan,Dan Annabi Muhammad (S.A.W) yana cewa An kewaye Aljannah da abinda rai baya so, wuta kuwa ankewaye tane da abinda rai yake so,kunga kuwa Ashe sai Mun dage,muntashi tsayee “

Mu tashi tsaye wajan Neman ilimi Dan wajibine akan dukkan musulmi SBD falalar sa da muhimmancin sa yasa ubangiji ya sanyashi zama wata Hanya ta samun Aljannah. Allahumgafirlaha  wagafir zanbaha,Allah yasa ta huta …

Yana gama wa’azin sa ya fara bin duk Wanda yake zaune agurin da naira dubu biyar sai kunyi musabaha sannan ya mika musu kudin ….

Haka yayi ta rabawa har ya gama sannan ya shiga cikin gida ya musu ta’azziya ya fito..addu’a kawai ya kesha ya shiga motar suka wuce ..

Zabe nata motsawa a yau rage wata biyu cur hankalin duk wani d’an siyasa a tashe yake burin bai wuce  ace. Shine yaci ba,wad’anda suke kan Kujerar mulki basa son sauka akai,wad’anda basu hauba burin su shine su hau ko ta halin k’ak’a.inda ko wacce jam’iya burin ta shine ace ‘yan takarar tane suka ci wannan zaben,

Duk sun bazu sai kudi kowannen su yake sakewa wajan campaign. Honorable Saleh ya banya hankalin sa ya tashi Musamman da yaga campaign d’in abokin karawar sa Alh Mu’azzam Musa yadda ya Tara dumbin al’umma ga ruwan kudi da kaya da yake raba musu.shiru yayi yana naxari har ga Allah shi talakane hasalima bai aje komai ba sai gidan sa gashi baida wata hanya da zai samu kud’i …

Honorable Tasi’u Gauta ya kalli honorable Saleh yabanya yace “Nasan abinda kake tunani shine kudi,kuma idan baka  da kud’i babu inda zakaje Mutane kajine muddin baka  watsa musu hatsiba baxasu tab’a zuwa gurin ka ba,amma idan kana watsa musu hatsi sai yadda kayi dasu zakayi ta juya su kamar waina  a tanda “Dan haka ina  da mafita,ya matsa kusa dashi ya masa magana a kunnen sa,nidai banji ba,bare na rubuta,

A lokaci guda suka dara tare da tafa hannu ,

Motar suka shiga sunyi tafiya mai Nisan gaske kafin su kayi parking din motar sa a bakin wani Babban makaranta da ya Tara almajirai da yawa su kutsa can ciki saiga su cikin babban zaure malamin dake zaune cikin wasu Alkyabba saika ce  basarake ya d’aga ido ya kalle su ya cigaba da Jan carbin sunkai 30mints zaune batare da yace dasu kanzil ba.  

Saida ya gama ya shafa sannan ya mik’a musu hannu sukayi musabaha,honorable Saleh ya banya zai fara magana ya dakatar dashi hannu tare da cewa …

” na Riga nasan abinda ke tafe dakai,yanzu ka k’arbi wannan ruwan da kake gani Fitsarin jaki ne ka k’irga su guda nawa ne”guda takwas yauwa to Mu d’an shiga daga ciki dan ban akwai Qur’an kar abin yayi mana _

Can ciki suka shiga wani d’aki d nikaina Saida na tsorata ya d’auko wasu k’yalle farare guda goma ya bashi  tare da cewa …..

“Ko wani fitsarin jaki guda da muka baka dashi zakayi wanka ba sallah tsawon kwana goma kada ka bari iyalanka su ganka tsawon kwana goma,sannan wannan kyallen zaka hadu turmi fa tabarya da yara maza uku mata bakwai duka kar su wuce yan shekaru biyar zuwa yan watanni uku ,duk lokacin da kayi zaka kkwasomin komai acikin wa nnan farin kyallen ka Kawo min,sharad’i baxa kalli idon duk Wanda zakayi mu’amala dasu ba,ka rufe  fuskar ka,,ina fata kagane ga wa nnan kwandon acik zaka Tara har saika  gama sannan arana ta goma zakataho nan misalin shabiyu na dare,Sauran aikin ka barmin”

Honorable Saleh Ya banya yaji hanjin cikin sa ya kad’a yace “Malam wannan ai” Wanda ya Kira da Malam yayi saurin dakatar da shi da hannu yace 

“Kana son Mulki ko baka so?” Ina so amma ni addu’a akacemin kanayi banyi tunanin babban malami kamar ka da duniya ta sanka zaka sanin aikata wannan babban sab’o”

“Hahahahahahahà

35

“HAHAHAHA, Tabbas ka fad’i gsky ni dinnan kangarau ne na haddace alqu’arni sama da shekaru arba’in da suka wuce, sannan duk wani surkullena iya Amma sanin cewa ba Abu bane maikyau yasa ba nayi na rik’e koyarwa ta,da almajirai na,hmmm saidai babu wani kudi da nake samu daga Yan siyasa irin ku,hakanne yasa na bud’e buzu na,Dan haka kawai ka aikata abin da nace hakan ne zaisa ka kada abokin takarar ka Alh Mu’azzam, Kasan irin mu muna d’an basaja ne sbd ai yanzu Mata daku ‘yan siyasa bakwason zuwa gurin bokaye ko ba haka neba?”

“Subhanallah,malam boka kuma? Allah ya rabamu da zuwa gurin bokaye”murmushi mai sauti malam yayi a zuciyar sa yana cewa “ai dai zaku zo gurin manyan bokaye masu ci da rigar malanta”

“A fili kuwa sai cewa, Allah ya rabamu da sharrin bokaye,aini yau dinnan kan buzu Zan kwana ina maka istihara Dan muga suwaye agaban ka sa bayan ka,Saleh kana son mulki dai ko?”

“Malam inason mulki Dan mulki akwai d’ad’i Dan haka bani na amince zanyi muddin kanada tabbacin cewa zanci wannan zaben”

“Ka tafi kawai karka damu”to malam nawa zan bayar”abinda zaka bada sadakane kawai banason komai har sai kaci mulki”ok ngd!

Tunda suka fito Honarable Saleh yabanya ya dubi Honarable yace “gsky na tsorata matu’kar gaske da jin abinda yake furtawa”ka dai yanzu ka bar komai a hannun Kuzungu Dan ya shigo Nigeria tun jiya Kuma ya taho da wasu daga Niger Amma yanzu haka da kaga nadan ja gefe shi na kira ,kaga lokacin tasowar yara daga makaranta ya kusa”

Ok to Allah yasa adace,ni dama ‘yan mata ne yace ,yadda yan Mata da wasu iyaye kwadayin kudi ke gaban su,babu ruwan su da wani bincike sudai burin su diyar su tayi miji …

© Kuzungu ke tafe hannun sa Rike da su biscuits sweet da kayan kwalama na yara sai ga wasu yara su uku biyu maza daya yarinya Yar shekara hudu yayi saurin watsa Biscuits da motar na wasan yara a k’asa,mazan suna gani 

“Su ka ce mu gudu sace mu zayi karmu d’auka zamu zama doya”suka ruga da gudu suka bar Aisha a gurin sai tayi kamar zata tafi sai tadawo  har ta koma takai hannu zata d’auka Kuzungu ya fito yana mata murmushi yace 

“Yan Mata na k’ara Miki?ta d’aga Masa kai alamun eh!ya bare alawa yabata ta fara sha ya d’auke ta ya Dora kan cinyar sa ,tana Shan alawa ya fito da Yar tsana yana cewa

“Kinga baby  kinaso” ta sa hannu ta zata kwace ya sauke ta suka fara Yar tsere tana bin shi saidai ya bata haka yayi ta mata wayo har ta shiga cikin motar tana shiga taga kayan Wasa ko ta Ina ga biscuits dasu cheesee ko ta Ina 

Murna da farin ciki suka lullube ta,taashiga cin wannan ta aje Saida taking ta koshi ta juya da Yar tsanan ta,tana Mata rawa……

Tafiya sukeyi sosai har barci ya d’auke ta, Kuzungu na ganin   Haka ya d’auki hankie ya shafe fuskar ta dashi wayar dake hannun sa ya d’auka ya dialing wata number yace oga ga yarinyar na samo…Zan mik’awa  samual ita yanzu….

“OK ba matsala  ngd”

Yana mikawa samual,shikuma ya ba Tasi’u Tasi’u yaba Joseph,Joseph yana Ard’o,Ard’o ya Mik’awa Salele k’araga,shi kuma ya mikawa Honorable Tasi’u Gauta …

Tunda him Tasi’u Gauta ya rik’e yarinyar a hannu ya fito da waya daga cikin aljihun sa ya dialing number Alh Mu’azzam yayi ringing har ya katse bai d’auka ba,ko minti 2 baiyi da kira ba Ya biyo baya …

Yana d’agawa yace “da Girman kujerar gashi fa ankawo masa yarinya ta farko kamar dai yadda nayi ma bayanin da Malam Tsalha yayi,to yanzu zai fara lomar farko”

“Wa’izaubillah,inason ka sayan wannan biron ajikin gashin ta,CIKIN kitson zaka tura shi iya gurin camera zai zama a kasa yadda zai kwashe KO mai insha Allah saina Kawo karshen Siyasar Yabanya,kuma na k’ara uku akan wancan farashin matuk’ar kayimin aiki dakyau…”

“Karka  damu ai ban tab’a baka kunya ba” ya katse wayar yayi yadda Speaker ya umarce shi sannan ya shiga ciki parlour..

Honorable Saleh NA kwance kan wata 3siter ya taso da murmushin sa yana zuwa ya karbi yarinya shiru yayi yana kallon ta,ya d’aga ido ya kalli honorable Tasi’u Gauta yace 

“Na yarda  da kai,bazaka tab’a cin amanata ba,hakan nema yasa bana shayin fadima duk wani sirrin,Dan Allah ka rik’e min amana” karka  damu Wlh tallahi bazan tab’a fadima kowa ba,to banda abinka sirrin ka ai itace tawa, ta yama  zan fara fitar dashi bayan nasan kashina ya bushe”

“Kuma inaso ka bige wancan Speaker ka nuna masa kujerar Senator ba irin tasu bane,sannan nima ka maramin baya na zama Dan majalisa,hahaha ka ga ya tashi a tutar babu”

“Hahaha gsky kai kasan tuggu yanzu dai INA zuwa”

Ya shiga da’ita cikin wani d’aki  ya d’auko kwandon da Malam tsalha ya bashi,ya cire duka Kayan jikin sa ya d’auko Farar kyalle yayi yadda Malam tsalha ya sashi yana gamawa………

wanene kuzungu?meyasa fatima ta b’oye inda take?shin wata aura?wanene wannan alhajin da yayiwa lantai fyade?waya kashe Ashmat? Menene Ashmat ta rubuta acikin takardar?menene tsakanin Adam da Ashmat?wacece Salamatu da Adam yasa Samira ta koma dai’ ta k’auye?wanene ya tura Dr ya kashe Ashmat?shin Asirin wad’anda suka salwantar da rayuwar Falmata zai to nu?Wanene mahaifin d’an amana

Page 36

Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun tabbas mai Imani bazai tab’a aikata Zina har sai zare Masa wannan imanin,Dan kuwa da ace Honarable Saleh yabanya nada imani da Tausayi,bazai tab’a biyewa son zuciyar sa ba wajan sab’awa Allah…

Yana gama aikatawa ya tashi gaba d’aya babu ko numfashi a jikin ta,duk jini ya b’ata tashi da’ita Murmushi yayi ganin ya fara cin nasara ..

Yayi duk yadda Malam tsalha ya Umar ceshi sannan ya fito da ita…. Honarable Tasiu Gauta yayi saurin ta sowa daga inda ya amshi yarinyar yana cewa 

“Kamar fa bata numfashi”eh!nima haka nagani,ka tabbatar mutanen ka sun ajiye ta inda baza’a gansu ba”angama rankai dade duk yadda kake so hakan zayi..

Ya  fito da’ita zuwa cikin motar.tunda yabar gidan gudu yake sosai.yasa hannu ya cire biron da ke kanta Yana murmushin mugun ta ya zira cikin aljihu, kafin ya mik’awa musu,haka suka rika mik’awa juna har ta isa hannun kuzungu..shi Kuma ya kaita cikin gari yaaje Yana k’arawa motar sa.

©Mai girman gaune tsaye Yana faman safa da marwa hannaye hard’e da juna,wata jibgegiyar mace naga tana magana ahankali ga dukkan alamu hakuri take bashi.kamar tace ya k’ara fad’an 

“Shut up,Kina hauka ne?meyasa zaki bar Humaira ta fita batare da security ba.nace meyasa”ya k’arasa maganar yana shak’e  Mata wuya,dak’yar take cewa” my dear ya kake so muyi da rayuwar mu kullum muna k’ulle guri guda,idan ma zamu fita sai anhadamu da katti,bamu da ikon watayawa kamar sauran mutane meyasa?mu ba kifin gwangwani ba,Amma kullum a k’ulle muke,ko motar muka shiga k’ulle ta ake,shin tayaya Y’ay’ana zasu samu mijin aure ne?”

“Kuma….”kau kau… Marin da ya Mata shi yahanata k’arasa fad’in abinda tayi niyyar fad’i…..

Last warning wlh tallahi .mtswww yaja tsaki Yana kokarin Kiran Humaira… switch up yayi ta kira akashe,Hanakalin say ya k’ara tashi ya juya ta Kara kallon burkusheshiyar matar sa,yace 

“Hameeda kincuci kanki,kinsan muna da mak’iya, ga cases din raping yayi yawa a garin nan,shiyasa na Hana su zuwa ko’ina,Why?why? Idan hutawa kuke so ki fadamin mana,ku duba duk k’asar da kukeso ku tafi kuyi yawon ku acan but not in Nigeria bazan tab’a yarda ba,baki da aiki saidai ki zauna kina cin Burger,pizza, chocolate, cake,ko da yaushe bakin ki motsi yake,saikin zo tashi ki kama Nishi,”

Kamar an sake tsumashi ya cakumo luta-lutan Kuma tun ta,yace “muddin wani Abu yasamu ‘yata saina sace wannan kumatun”

Ya saki hannu ya fara dialing kiran Humaira wani ajiyar zuciya ya sauke jin ankira …

Tana ganin Kiran sa tace “Chuchu old man is calling fa?”Wanda ta kira da Chuchu Yana saka belt yace ki picking mana tunda mungama ….noo ya kyaleshi kawai yanzu Zan koma gida,Kuma make sure gobe kayi shiga Mata kazo Dan so nake mu kwana tare”

“Hahahaha shiyasa nake sonki wato irin ga aminiyar ki ta kawo Miki ziyara ko?”eh!mana 1week zakayi”Ahh ke fa bakyaji meye na kaini jinsin maza Kuma”hmmm kiyi hakuri Zinaru k’araga,Ina so ka,au ki samu Wacce kika yarda da’ita tsohuwa ki bata waya kii Mata bayanin komai  Dan zan kira ta naba mom suyi magana”

“Angama madam to ya mezan samu?”Mtswww taja tsaki tare da bud’e zip din jakar ta,bandir na kudi ta fitar  ta bashi tana cewa” kayi amfani Dani na baka kudi tsabar ka rainani”

“kee kina so ki kaini bango,Menene n

Haka bako lank’wasa a tsaye ki kam”sorry”tace ya d’auki zani yana d’aurawa a k’irji,Yana tafa hannu “wlh Humaira idan baki daina kaini jinsin ‘yan maza ba,sainayi tumb’ur mu daku”yadda yadda k’ara sa maganar yana Shirin figee zani shi yaba Humaira dariya,Saida tayi Mai isar ta kafin tace.

“Ga kudin nan ka…au ki amsa banason surutu”

“Eh!mana ai kudin mune ake satowa abaku,kinga kuwa dole na karb’a”harara ta doka masa “waye barawon Daddy?”ahhh ni bance ba,Yana magana irin ta Yan daudu Yana rik’e baki tare da buga cinya….

“KI bari na mutu Mata sukaini kabari”Oho ma nidai Ina jiran ka,gashi old man na k’ara kira”ki answer  mana,ke fa ‘yar yawa ce”Naji bazan amsa ba,nasan yanzu yasa wad’annan security d’in su nemeni,saina samu acikin. Su nayiwa wani aika-aika tukun zasu daina bina duk inda na tafi”

“Ke dai a sauka rab’ab’a” so nake nasa ‘yar bra dina karkimin lalata” mtswww taja tsaki tafi ta….

Da sauri ta shiga taxi ya kaita wani gida tana shiga matar gidan na D’orawa wata ‘yar shekaru da basu wuce takwas ba talla tana cewa 

“Lawazima ki hanzar ta kinji,ko dari uku kikayi ki dawo nasamu nakai Buhari shakatafi Kinga jikin nasa sai k’ara zafi yake sosai”Wacce ta kira da lawazima tayi nar-nar da fuska kamar zatayi kuka 

“Umman mu ki bani abinci naci kafin na tafi naga kin d’ora tukunyar kan icce har yanzu bata nuna bane?” Juyawa matar tayi tana share hawayen da ke fita daga idanon Saida ta daidai ta natsuwar ta sannan tace 

“Lawazima kiyi hakuri kinji bai k’arasa ba yi sauri ki dawo mu samu ko na kai Buhari ne Asibiti”to Umman mu …

Lawazima na fita ta shiga kitchen ta gyara murhu tafasar da tsinke shi takawo ta zuba cikin tukunyar ta d’ora leda a saman ta, sannan ta rufe .

Sallamar Humaira yasa tayi saurin fitowa daga kitchen bata gane ta ba, Humaira tayi shiru tana kallon cikin gidan tace 

“Aunty taimako zamuyiwa juna. Nida ke,inaso ki d’aukon kayanki kibani na siya guda d’aya zanbaki kudinki kinji, sannan wannan na jikina ki dibi wannan kwatar ko watsa ajikin ta sosai …..Zan baki dubu goma “

“Na’am dubu nawa kika ce”goma ko bazakiyi ba?”zanyi,wlh zanyi ayya Allah ngd maka yau Zan huta da bala’in Salele tana magana tana kuka

“Meyasa kike kuka? Wanene Salele?” Yar uwa ne Salele shine maigidan nan,ni Kuma Allah yayiwa mijina rasuwa shekaru uku da suka wuce….

Nike ciyar damu,nice uwa Kuma uba,munk’ara gurin wata biyu akan yadda muke bashi kudin haya,banida shi,na nima bansamu ba,d’an k’osan da nakeyi da safe Buhari ya cinye jarin,gashi sunce aiki zasu Masa saina kawo dubu dari da hamsin,kuka ya ci k’arfin ta …inaso suyi karatu babu dama,bamu da abinda zamuci tafasa shine abincin mu,burina da safe bai wuce nasamu naira talatin da sai suga na zuba cikin ruwan zafi su sha,wataran ma,bana samu ashirin da Zan siyi jarka ruwa,ngd Miki Allah ya rufa Miki asiri duniyar ki da lahirar ki, Allah yajikan iyaye da kakan ni”

Humaira da take zubar da hawaye ta kasa ko furta kalma guda ta dubi inda matar Nan ke rayuwa ginin k’asane Mai d’auke da d’akuna guda biyu,dayan d’akin gefen sa ya zube shi Wanda suke ciki babu ko ledan k’asa ,a hankali ta taka cikin d’akin babu katifa bare tabar ma sai wasu tsumma da matar take kira da sunan kaya,tana d’aga ido taga fallen Kano ne babu silif gashi duk ya hurhuje,har Rana na shigowa d’akin, ta kalli matar cike da tausayawa tana cewa

“Ai na kuke kwana?”a Nan muke kwanciya nida yarana guda shida”idan Ana ruwan sama ya kukeyi,a lokacin” Kinga wannan lungun?”ta nuna Mata bayan k’aure da duk  a bule yake tace anan muke haduwa mu rungume junan mu wannan k’aramin zamu sa a tsakiya mu rufe shi sbd kar ya kamu da ciwo”

“Ina kayan da zaki bani?” Ga su Nan ki zab’a da kanki” Humaira ta fara d’aga kayan tana dubawa duka babu Wanda bata d’aure wani gefe na Riga ko zani ba”

Ka sa magani tayi tana kallon d’akin “Yarinyar da ta fita ‘yar kice ko?”eh!itace ta biyar sunan ta lawazima sai Buhari,”

Suna cikin magana Buhari ya farka daga barci ya shiga kwarara amai babu abinda yake fita daga cikin sa sai ruwa cikin sa ya rik’e Yana cewa

“Umma cikina”ta rasa me zatayi ta ruga da gudu xuwa  tkitchen tasa wani b’ulalliyar kwando ta d’ebo Tafashiyar ta xuba a kwano ko gishiri babu bare ayi tunanin kuli-kuli ..

Tazo da shi,tarike kansa,zata bashi Humaira tace “what am I seeing”mutum zaici wannan?”innalillahi wa Inna ilaihi rajiun ” tayi saurin katse videon ta dialing number Dad dint Yana fara ringing ya d’aga ido yana kallon Speaker da yazo  yace,ga ta tana kirana, Alhamdulillah ka amsa hankalin Mu ya kwana ” Wlh tsoron d’auka nake kar ace.masu  kind kidnapping ne sukayi wuf da’ita”

“Noo insha Allah babu abinda ya same ta” Hmmmm Allah yasa”yana d’agawa kafin yayi magana tace  Dady I need your help, Dan Allah ka turomin wani security da yanzu  Angwan makara huta”Humaira dawa kike tare”Dady bari natura ma wani video Dana d’auka a gurin da nake Dan Allah ka Kawo musu d’auki bazan iya barin su ba,har sai naga Murmushi a fuskar su”Humaira ki dawo yanzu”no Dady I  can’t”

Ta katse kiran da sauri  ta kunna data WhatsApp ta shiga ta,turawa Momyn ta ,Dady,Da babban aminin sa Alh Mu’azzam,sai Nadiya”

Anyi sa’a duka suna online Dan tana katse kiran Gauna ya kunna data,Alh Mu’azzam kuwa yana jin Humaira klau take shima ya kunna…..

“Oh my God” Gauna ya fad’a ya nuna videon

©tunda kuzungu ya jefar da yarinyar nan tafiyar sa da kadan wani bawan Allah ya gan ta,kasa tab’a yayi Dan wannan babu tantama students d’in su ne da aka ce ta b’ata “Innalillahi wa ilaihi rajiun”wannan Kalmar yake ta fad’i da karfi 

” cikin k’ankanin lokaci lbr ya karade  ko ina yan jarida nan da nan suka cika gurin sai ga Mahaifiyar yarinya tazo tana kuka ta rungume ta ajikin ta tana cewa 

“Ya Rabbi,Innalillahi wa inna ilaihi rajiun ayya me kika musu,meyasa saike Zuhra,Dan Allah me zasu samu ajikin ki,ayya,Innalillahi wa inna ilaihi rajiun,Allah ya isa,Allah ya saka miki,Ku taimaka min mukaita asibiti”

Wasu mata suka rik’e yarinyar ita Kuwa albarkacin doguwar hijabin da tasa  taci Dan zuba da zanin jikin ta tsabar tashin hankali 

Maihaifin Zuhra yazo da mota suka sanya aciki  mahaifiyar sai kuka take tana fad’in “Allah Kaine gatan Mu,dakai muka mika kukan mu,ya Allah ka wulakan ta duk wani mai hannu cikin wannan, ka d’and’ana musu rad’ad’i da zafin da muke ji ayanzu”

Fuskar Zuhra ta shafa ta d’aga jajayen idanin ta,”Abban sadik Zuhra bata numfashi,ka duba kaga bata numfashi,me suka mata kuma bayan fyad’e? Kumfa ke fita ta hancin Zuhra,kai!kai! Wai ba gidan karuwa ne? Zuhra ‘Yar shekaru hudu?”

“Rahama Dan Allah ki yi hakuri Ku ihun nan bazai sauya komai ba,ki duba nan me yake zuba ta k’asan ta a haka,Rahama menene haka kamar mafitsarin Zuhra da gurin bayan gidan ta sun…..”

Ya k’arasawa kuka kawai ya fashe dashi yana  fad’in Wlh ban tab’a zina ba,ayya Innalillahi wa inna ilaihi rajiun , daidai Lon lokacin da suka I so asibiti….

Hmmmm sharhin Ku yanamin kadan gsky INA bukatar dogon addu a da sharhi ngd 

37

Yana kiran Alhaji mu’azzam amma be da gaba shikuma lokacin Alhaji mu’azzam ya shiga cikin Asibitin da buhari a hanunsa ya miqawa nurse shi yace ashiga dashi a bashi emergency treatment hakan kuwa akayi domin ganin speaker da kansa ya riqo yaron, yana tsaye a jikin motarsa sega abban zuhura ya taho da sauri, yana ganinsa yazo ya tsugunna kusa dashi yace ranka yadade anyi wa ‘yata fyade dan girman Allah ku kwato mana haqqin mu kusa a binciko masu yin wannan aikin, wannan abubuwan yayi yawa agari dan girman Allah ku tausaya mana mu iyayene kuma iyayene, ranka yadade zafin da mukeji idan akayi wa naka kaima shi zakaji dan  Allah dan girman Allah asa hukuma su kwato mana wanda yayi wannan aikin don Allah.. 

   Dazunan ma honorable saleh yabanya yace mana shima yadauki alkawari  ze mana ze bayyana dik wanda yayi wannan aikin dan Allah ranka ya dade ku taimaka mana kaga shi seya hau mulki, ku kuma kuna kan mulkin yanzu kune da mulkin yanzu dan Allah ku tausayawa rayuwar mu ku tausayawa rayuwar ‘ya’yan mu.. ‘Ya’yan mu suna cikin wani hali an mayar dasu tamkar wasu dabbobi, ba’a daukesu a bakin komai ba za’a dauqi ‘ya amata fyade azo a wurgar da ita.. Za’a dauki babbar mace amata fyade azo a wurgar da ita.. Ya zamuyi ne  bamusan wa’anda suke aikatawa ba amma kullun muna kai kukan mu ga Allah (S.W.A) daya tona asirin dik wani me hannu a ciki, dik maganan dayakeyi Alhaji mu’azzam be hanasa ba kuma bece dashi qala ba seda ya sauke ya gama tukunna yace dashi kuyi hakuri amma insha Allahu rabbi na muku alkawari zan binciko wannan koda ta qarqashin qasa ne, muje muga ‘yar taka.. Yana zuwa ya shiga yana ganin zuhura yayi shiru batare dayace komai ba idan be manta ba zuhura itace acikin wannan memory din dake jikin wannan biro din da aka basa.. Shiru yayi yana nazari kafin yace insha Allahu rabbi zata samu lafiya yanzu ai ta farfado ko?

   Eh ranks ya dade ta  farfado anma dai har yanzu batama gane wanda yake kanta, sedai anyi mata aiki kuma aikin biyu za’a mata yanzu anyi guda daya saura na biyun dayan ma sunce mana dubu dari biyu da hamsin ranka yadade daqyar muka samo dubu dari da hamsin shikuma dayan banu da halinsa.. Yace owk karku damu yanzu inna  likitan yake? Yace yana cikin office dinsa ranka yadade, toh mu tafi… ya kama hanya sukaje wajan likita suna zuwa likita ya tashi tsaye ahhh ranka ya dade da kanka , yayi murmushi yace eh gani da kaina, suka sha hannu yace kubani bill din wannan bawan Allah da kuma dik wani wanda mara lafiya da rashin lafiyarsa ya danganci fyade innason ku bani dan Allah bill dinsu gabaki daya yanzu da kuma account number dinku zanyi transfer din komai a kula dasu kyauta insha Allah inna buqatarsu yanzu..

   Cikin hanzari likitan yasoma fadin owk sir! Owk sir!! No problem sir yanzu zansa ahada da anhada xan turo ma sir, ko zaka dan abinan dina numbern da za’a turo maka?yace no problem ka rubuta, yana fada Abban zuhura na haddacewa akansa shikuma likita na rubutawa har ya gama sannan suka fita abban zuhura godiya yake masa nan da nan aka hada bill din aka tura masa sukuma nan da nan ya musu transfern kudin a lokacin…

   Wadansu na kuka agurin wadansu na farinciki banda addua ba abinda yake sha agurin  talakawa se hannu kawai yake daga musu.. Wani murmushi yayi da shikadai yasan sirrin murmushinsa..yana fitowa daga kudin ya dauki wayarsa 3misd calls na governa ya gani hakan yasashi murmusawa ya kira yana daukan waya governa yace mishi ba’aga humaira ba inna tinanin wadansu sunsa a kidnapping dinta bansan su waye ba amma wannan karon banason hukuma su shiga sena nuna ma wanda yayi kidnapping humaira shi karamin dan iska ne, karamin dan siyasa ne shi be san komi ba akan siyasa sena nuna masa cewa tinkafin a haifeshi muke cikin siyasa kuma muke cikin duniyar siyasa kuma mu mukasan tuggu da dik wani badaqala na siyasa dan haka inna zuwa governa  kawak ya kashe wayarsa, yana kashe wayar yayi dailing numbern Alhaji bara’u.. Alhaji bara’u yana dauka yace ranka yadade tasamu kenan yace eh kasan ai seta samu muke bibiyar irin layinku dariya Alhaji bara’u yayi yace ai shiyasa nake sonka ranka ya dade.. Yanzu meke faruwa? Wakakeso a kawar? Wa kakeso a kawo? Kuma wa kakeso a kwato? ” ‘Yata” ya basa  ansa

   Ehhhh!!!! Ranka ya dade ya fada da karfi tare da razana ‘yar ka?  tayaya hakan ya faru? Ranka ya dade bana baka rules ba? Na gaya maka yanda zakayi ka kare yaranan sabida yan siyasan nan sun sanya maka ido so suke su samu wani gaba da zasu ga illan ka.. Nasani sha kurumin ka yanzu aka kidnapping dinta dan haka innaso ka baza mutanen ka jeji da ko inna ka bazasu kuma inna buqatar inka ‘yata kafinan da awa hudu … 

   Dik inda kake tunani a baza ayi bincike iyakar bincike ka baza mutanenka a daga hankalin kowa amma inna fatan kagane yanda zakayishi cikin siyasa . bada sunana ba bada laqanina ba da wani abu kuma da ze sa agane ni bane innafatan ka fahimta abinda nake nufi..kwarai kuwa ranka ya dade karka damu yanzu zan baxa mutanena wasu su shiga gidan jaridu wasu suje gidan radio wasu suje gidan telebijin yanzu akafara wasan ranka ya dade insha Allahu rabbi muke da riban wanan wasan, kuma yanda election yamatso kusa inna me tabbatar maka kai zakaci nasara ranka ya dade, ba wanj agabanka ba wani a bayanka kai giwa ne ka taka dik wani wanda kakeso ka wuce girmanka ya wuce a tari gabanka sedai ta bayan ka, ta bayankan ma se idan kaso in bakaso ba kuwa kanagaine tamkar kana tafiya da bayanka.. Ranka ya dade badai mutun ba sedai Allah wanda kuwa ya nemi ya ja da kai mu munanan zamuja dashi kowaye shi a qasarnan..

   Gaba dai gaba dai ranka ya dade kaine governan mu yau kuma kaine shugaban qasarmu gobe,ba maza  a gabab ka, ina me tabbatar maka seka mulki wanan qasa tamu ko ana ha-maza ha-mata zamu tsaya mu kawar da wanda zamu kashe m tsaya  wanda zamu jefar  da wanda zamu jefar kuma mu kashe wanda zamu kashe kawai domin kai ranka ya dade karka damu kabamu ‘yan mintina kawai zamu kawo ma rahoto kuma zakaji zamu aiwatar sanan kuma zamu mannawa hhhh jam’iyun hamayya!!!

    Wadanda suke hamayya damu, wanene ze sace maka ‘ya ranka ya dade ka barmin komai a hannu na, ka kwanta kawai kayi bacci, Alhaji  bara’u bazan iya bacci ba senaga ‘yata acikin gidana karka bari suyi raping  dinta wallahi, wallahi karka bari a tabamin ‘yata kasan wannan abun shi yake yawo ko? Toh karka yarda Dan  zan iya aikata komai domin na kare iyalina, zanyi komai domin na basu kariya tare da kare mutuncin su, nakare musu dik wani abu daya dangance su ina son iyalina banason komai ya tabasu ballantana ‘yar dana haifa da cikina.. Wai ni!nii!!niii!!!!! Za’asa ayi kidnapping ‘yata God!!!  Nabarma komai a hanunka bara’u innajiran result idan result yayi kyau zakaga dakyau idan result yayi kyau zakaga ninkin ba ninkin acikin account dinka… Yayiiiiiii! Ogaaaa haka ya fada yana murna ya katse wayar..

   Ya na Katse wayar shima Alhaji bara’u ya shiga kiraye kirayen mutanensa yakira wanan yakira wanan

   Abinda ya bani mamaki

 shine Alhaji bara’u bashi bane yake fita yayi aikin kuma wa’anda yakira shima ba shi bane aqalla seda  akayi waya da mutane hawa-hawa wajan goma sanan akaje ga ogan shi kanshi ‘yan daban

38

Gaba d’aya mutanen Alh Bara’au sun ba zama niman Humaira, lungu da sak’o …

®cikin asibiti doctor’s sunyi iyakan kokarin su amma,ina Babu Zuhra,hakan yasa suka fito jiki a sanyaye,Dr imran ya kalli Abban Zuhra da ido ya masa alaman 

“Ka biyoni office” hakan kuwa akayi ya bishi cikin Hanzari musamman  yadda yake jin kirjin sa na bugawa sosai,

Ya kama handle d’in k’ofa zai bud’e ya sake jin fad’uwar gaba_hakan yasa shi Saida ya dafe  k’irjin sa da hannu, ya Kara’sa bud’e k’ofar da sallamar sa,Dr Imran ya amsa 

“Have a sit,Emm nace ba,kasan duk musulmi ya sancewa Allah zai jarabe shi dai ko?” Yes Sir! Pls go.street to the point”anyway ina mai baka hakurin cewa Allah yayiwa Zuhra rasuwa “

“What?? K’arya kake Wlh har ka isa  kana tunanin zan yarda  dakaine?yau Zuhra ta cika 4yrs ciff,kuma tacemin  zata bani mamaki,tace na siya mata gown,da teddy,kuma na siya yana gida jira kawai nake Ku fitomin da’ita naje na d’auko mata”

Ya fashe da kuka kamar Yaro yana rik’e kansa ,Dr Imran ya kalle shi cikin tausayawa “kayi hakuri lokacin ta ne yayi,kuma …”

“Kuma me?zaka ce” ya tashi yana nuna Dr Imran da ‘Dan da tsar hannun sa ” ‘yata akayiwa fyade shikenan wanda ya mata yasha,ko ajikin sa. yadda na d’an..dani wannan bakin cikin. Hmmmmmm”

Ya fasa  furta abinda yayi niyya ya buga teble d’in Dr ya fita cikin huci da jin haushi…

Momyn ,

Zuhra na zaune ta kalle shi,cikin muryar tausayi :”Abban Zuhra doctors din da suka shiga yiwa Zuhra Operation duk sun fito amma basu fitomin da’ita ba,kayi musu magana, inason ganin ta farka,Dan nasamu kwanciyar hankali, har na hada cake din birthday ko da bazata Ciba,wannan shine burin ta”hmmmm Rahama kiyi hakuri Zuhra kam addu’arki kawai take bukata a halin yanzu ba cake ba”hannun sa ta rik’o “me kake nufi,a’a nace a’a Zuhra ‘yata tana raye,shekarun Mu Goma sha biyar da aure Allah bai bamu haihuwa ba,kwatsam sai gani da ciki tunda na haifi Zuhra yau shekaru hud’u daidai ban k’ara haihuwa ba,Zuhra kad’ai gare ni Dan Allah kar ka cemin ta mutu”

Hannayen  ta d’ora a kan k’irji tana girgiza kai,lokaci guda take furta 

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, jiya ne kad’ai  bansamu zuwa school d’aukar ta ba,SBD bikin  Safiya,Zuhra na rasaki SBD sakaci irin  nawa, na barki da yaran da Kansu ma bazasu iya karewa. ba, akan biki,narasa gudan  jinina dana  d’ad’e ina kwanan Zaune, ina kuka da idanuna cikin dare,cikin sujjata yau narasa ki”

Abban Zuhra yayi saurin rik’e ta ,ya zaunar da’ita,sai ga kanin sa ya taho da motar suka shiga theatre room,yana ganin Zuhra kwance ya fashe da kuka,ya kasa ko tab’a ta,kanin sane ya d’auke zuwa cikin motar a hankali ya tako inda  Rahama ta tsuguna tana kuka mai cike da nadama,

Dakyar ta yarda ya sanya ta cikin motar,gaba d’aya ta zauce sai maganganu marasa dadi take furtawa babu addu’a ko kadan d ya fito daga bakin ta,

Abban Zuhra da ya fito ya shiga baya suka nufi gida….

Sun tarar har an had’a mata ruwan wanka,ita kawai ake jira, 

Wasu mata guda biyu suka suturta,lokacin da aka fito da’ita zaje ayi mata sallah Rahama ta rik’e makarar

“Ku barmin ita,ahaka zamuyi wasan Mu,Nafa ko ya mata yadda ,zata zama diyar kirki,kunsn burin ta?kawai ita, idan ta mutu ta shiga Aljannah,Kullum, sai tace zan shiga Aljannah idan banyi zagi bako momy? Zansha Bobo a Aljannah? Ai zan d’iba miki?” Hahaha daga kuka ta koma  dariya,dik  mutanin dake gurin sai da suka tsorata da irin  dariyar  Rahama,gashi ta rik’e makara GAM TAKI saki,

Matan dake gurin suka rik’e ta,tana musu dariya “Zuhra,yarinya mai tagwayen suna,Kece Zuhra,kece Saudat,agurin ,Dady kece Zuhra,agurin Momy kece saudat” wak’ar d takewa Zuhra shi ta rika yi tana sheka dariya,

Bayan an sallah ceta suka wuce da’ita zuwan gidan ta na gsky, Rahama ta fara dariya ba tsayawa tana kiran Zuhra,dankwalin kanta tayi wurgi dashi, Amaryar ta,MMN yara mazan da suke tare da Zuhra ta rik’e ta amma ina  ta fizge,ta ruga  da gudu,mata dayawa sunyi kokarin rik’e ta,amma ina  ta watsar dasu k’asa”,

Tunda ta fita gudu kawai take bata tsaya ba sai a wani jeji ta shiga d’aukar shara tana rungumar su a kirjin ta,

©MMN buhari zaune tana murmushi ganin Buhari ya farfad’o,gefen fuskar sa ta shafa tana fad’in “Alhamdulillah buhari,Allah ya baka lfy kaji,k’irjin ta,taji ya buga lokaci guda Tunanin Lawazima ya fad’o mata,Allah yasa kina lfy,lawazima,mayasa nakejin kirjina haka?ka mata yayi nayi murna amma yanzu akasin haka nakeji”

Lawazima kuwa nacan bakin titi da kayan talla babu wanda ya siya naira goma kawai tayi,shiyasa ta kasa zuwa gida,tana tunanin idan ta koma ba abinda zasu ci,gashi mahaifiyar tace takawo ko dari uku ne zasu kai buhari asibiti…tana cikin wannan tunanin saiga wani saurayi kyakkyawa ya kalle ta,

“Yan mata ya sunanki?”sunana lawazima” hiyeee suna mai dadi,ina zaki haka?”bako ina talla nake yi kuma ba’a siya ba,dan Allah ka siya ka bani kudin na kaiwa umman mu sbd takai buhari asibiti”ok zan siya nawa zan baki?” Dari uku ne,sai ka dibi kanwar ta dari uku”amma ya naga fatar bakin ki ya bushe haka sosai?yunwa kikeji?”ta daga masa kai hawaye na bin fuskar ta,yasa hannu ya share mata hawayen,hannun ta ya rike ta fisge ,murmushi yayi yana cewa 

Lawazima umman kice tace na kiraki Buhari ya mutu”a’a bai mutu ba,kadaina cewa ya mutu,nasani”to ko ki biyoni dan ki ganewa kanki”eh to na yarda mutafi nagani …

Tana tafiya kadan ta fara ganin jiri sbd yunwa ya riga yaci galabar ta,ga shi ko naira biyar tak’i kashewa burin bai wuce ta koma gida ba,yuuuuu zata fadi ya rik’e addu’a yaji tana karanta ahankali kamar yadda umma ta koyar da’ita 

Allahumma gafirzanbii wadahir qalbi wahasir farjiii,waiyo cikina” a take ta suma….wayar sa ya fitar ya dialing wata number ringing biyu aka daga naji yana cewa sir na samu,yanzu zankaiwa K’I SABO”

“Ok shikenan duk da dai nasan yanzu,ko da yake kaita din”

Humaira ce kwance tana tunanin aran ta,babu Wanda yasan inda nake sai mutum hudu,Dady, Dadyn,speaker, Yaya ASHRAF, sai aunty Nadiya,shin acikin su wazai sa a kiddanaping dina..

Kuma gashi inda suka ajiye ni gurine maikyau babu Wanda ya hantareni???ko ya tab’a ni,anya kuwa mai wannan kidnapping bashi da manufa?” To wai ma,wanene daga cikin su zai min haka, nak’i turawa mom nasan cewa tana can tana fama dasu meat pie d’in ta wayar ma ko ta Kansa bata. Bi  sai dare,dariya tayi da ta tuna yadda sukayi kafin ta amince ta fita,

Tafi kakeji yana tashi,ta ko’ina…..

39

“HAHAHAHA WOONI HUMAIRA tabbas duk Wanda yace Zan iya aika ta irin wannan za k’arya ta shi,Dady nasan yanzu kana can ka baza police lungu da sak’o suna nima na,inda hankalin su,bazai tab’a zuwa gidan gonar ka ba,ni Kuma Ina nan ciki,Ina shanawa ta”

Ta k’arasa magana tana d’ora d’aya kan d’aya,tana zura Hannayen ta,saman kushin,kai Chuchu,wai har yanzu kajin basu gasu bane?”kai na Abatauwa sai kije ki siya ,ki bani aiki Dan salon na tsufa ‘yan maza suce na mokad’e narasa mijin aure”

Yana bata amsa daga kitchen ita Kuma tana parlour juice ta d’an tsiyaya cikin glass cup, wato kasan me?”ank’i a sanin salon mugunta ki rik’a kaini jinsin da banawa ba”to I’m sorry,kinsan yanzu hankalin Dady ya tashi,sosai ya ka Mata mu kira shi,makudan kudi nake so,ta yadda Zan shiga k’auyu ka na taimake su, Chuchu wannan hanyar kad’ai ke gareni,bazan tab’a yarda ta kufcemin ba,na d’ad’e Ina shiryawa wannan ranar”hmmmm haka ne,Amma ita matar nan da kika bar Mata waya idan want Abu ya same ta Kuma fa?”

“Babu abi da zai same ta,Dan nasan Dady speaker zaije gidan, I’m very sure zai tafi,Kuma bazai tab’a bari hawaye ya k’ara zuba daga fuskar ta ba”

“Na San da hakan yanzu dai dame zamu fara aikin mu”ya k’arasa maganar yana aje plate na gasassun kaji da kifin ruwa,sunsha jajjagen tarugu da albasa har wani Mai suke,gefe guda ga lafiyayyan yaji da yasha Hadi,

Hannu takai zata figoo kaza Chuchu yayi saurin rik’e Mata hannu “haba mana Baby,ai kya wanke hannu,ko sbd wannan cuta covid19 da ake fama dashi”Au ni zaka gayaawa Corona virus,zaka gane shayi ruwa ne, Allah ya kaimu dare,dole ne mu bada social distance”

“Ehhm!uhhhm mubar zancen sa hannu”hahahaha yarinya da yau kin kwana a gefe sai gani sai hange”ai bance komai ba, gani nayi ya dace ace kin wanke hannun ki kafin kici wani Abu”malam kar ka rainani mana, Saida na wanke hannu na kafin na fito”

Ta k’arasa maganar tana hararan sa alamun taji haushi,yi hakuri yace suka cigaba da figar kaza.bayan sun gama tace ka kirawo mutanin ka,suzo suci kaza kafin mufara aikin mu”ok yace, ya kirasu suka shigo cikin parlourn kaji ta nuna musu tare da cewa 

“Banaso asamu matsala 1billion zaka ce,Kuma kayi Masa warning sosai tare da cewa kunsan inda yake aje wannan Stephanie d’in,Kuma yanzu haka iyayen ta,suna hannun ka,kar ya jinkir ta,turo wad’annan kud’in, sannan kuce Masa yaje angwan mesau babu kanwar mahaifiyar sa,tana gurin ku,karka jira amsar ka kashe wayar tare da cilli da sim d’in a k’asa,sai ka dawo,karka bari asamu matsala, sannan ka tabbatar ka isa wannan garin kafin ka kira,Chuchu ku kula sosai Kuna gama waya kubar gurin ku yarda sim kamar yadda nace karku k’ara ko 1minte a wajen”

“Inshallah ,zamuyi duk yadda kike so”good Allah ya taimake mu”ameen Amma kudin da muka nima Sunyi kad’an” chuchu basuyi kadan,saidai fa yan banza nan sun makemin baki Wlh naji zafi “kiyi hakuri ranks d’ad’e umarnin ki kawai muke bi……

” ya zanyi daku Ku hanzar ta zuwa Ku tabbatar sai kun shiga kauayen Katsina kamar dai yadda muka tsara hakan zakuyi”

Suna fita suka shiga motar gudu suke ahanya sosai….

Alh Mu’azzam ne zaune yana kallon video d’in Saleh yabanya cikin laptop dinsa…..

masu zaton Alh Mu’azzam ne to kin daiji cewa bashi bane

PAGE 40

Murmushi chuchun humaira yayi yana gyara daurin dankwali ya coke ta gaban goshi yana karka ce bako

“Ke ni dadi na rashin mutunci tunda kika ce gauna ya miki aure ya nuna miki baki kai ba,karatu zakiyi?”na fara jawo masa bala’i danni ba mulki bane a gaba na,ko kadan basu dame niba,amma nayi tattaki na cire kunya irin tamu ta mata,nace su aurar dani,suka min caaaa kamar zasu cinye nama ta,har dady na cewa ko zan mutu bazai aurar dani ba sai nagama degree gashi nan tunda na gama babu mashinshini,shi kuma girman kai ya hana shi samo min mijin aure”

“Har yana cewa kamar shi ace yana begging wani yaxo ya auri ‘yarsa never”hmmm chuchu saina sa dad yayi kuka da idanin sa,wlh ashiryee nake na d’auki ciki danni gsky banaso na mutu ba aure”yanzu zani Bautar k’asa anan zan sheke ayata”har kullum ina kan baka na kuma bazan tab’a gajiyawa wurin tunatar dake cewa ke musulma ce,mai rik’o da addini,meyasa kikeso ki kangare ne?” Dadyna sila,baka ga yadda Dadyn fareeda yayi ba a cikin littafin sune sila”

Duk ba wannan ba humaira kiji tsoron allah a duk inda kike,kisani yana kallon ki,meyasa duk lokacin da kika taho gurina muka gama mu’amala sai ki yita kuka?meyasa kullum a sujjadar ki ta karshe kike kuka?ke din mace ce mai kamun kai da rik’o da addini”

“Ya isa!banason jin komai daga gareka chuchu,iyaye na sun kasa fahimtar cewa halitta kowani d’an adama ta fannin sha’awa daban take,ya ka mata ace uwa zata fi kowa sanya ido gurin yaran ta,dan ta gano mai yawan sha’awa,amma momy babu ruwan ta”chuchu har yau ina bakin cikin wannan bak’ar alak’ar dake tsakanin mu,iyayen suna zaton aunty Nadiya ce mai rawar kai,sai suka fi sanya mata ido,ni kuma ko oho,basusan nice nan maiyin mummanar sab’o ba”

“Karki damu da zaran mungama wannan aikin zan san yadda zayi kiyi aure idan kina bukatar hakan insha Allah”hmmm Allah yasa,bari na kira su muji gurin da suke”

Ta kira yafi sau biyar basu d’aga ba,hankalin ta ya matuk’ar tashi,sai ga kiran su,tana d’agawa yace,

“Hajiya mun kira sau uku bai d’aga bamu san dalili ba,amma mun tura masa sak’o tare bukatun mu”ok kun dai cire sim din k?”eh!mun cire harda wayar ma nan muka bar ta”good ku koma otal d’in da na kama muku”karki damu wasu lokutan nakan rasa dalilin da yasa ko mune muka kira dady ta private number d’insa baya picking duk kiran da zakayi saida gaba yazo ya kira,abinda yasa nake mamaki shine duk irin aikin da yake ko taro suka tafi muddin muka kira ta private number zai d’auka,ko ya mana text,amma duk lokacin da muka kirashi bai d’aga ba zaka ga can anjima ya dawo ya gida bazai shigo ta main door ba sai ta baya,kuma bazai shiga d’akin sa direct ba sai…..”shiru tayi jin zatayi baram-barama.

©Tunda ya dauki lawazima a sume ya yayya fa mata swan water mai sanyi ta farka,lokaci d’aya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya,tare da dafe k’irji,abinci ya ajiye mata aiko ta sa hannu saidai abin mamaki,lawazima bata fara cin abincin nan ba saida tace bismillah,bayan ta kammala tayi hamdala tasha ruwa

Duk abinda takeyi yana kallon ta ba tare da yace  komai ba,har ya mik’a mata gurin wani, yana k’arban ta ya shafa mata wani farin ky’alle,shima ya mikawa wani har yakai gurin wani Alh Gambo,sannan ya yi tafiya mai nisan gaske kafin ya kaita wani gida,yana zuwa ya mik’a ta ga wannan dattijon da yayiwa lantai fyad’e ya juya da sauri….

Yana shiga da’ita cikin d’akin ya d’auko fitsarin jakin ya wanke jikin sa sannan itama ya zuba mata,tukunyar jar kasa ya kuma d’auko abin mamaki sai ganin k’yalle sama da ashirin aciki,ya fitar da daya wanda babu komai aciki,

Yakai ga aikata nufin sa ya shiga ganin lawazima ta koma abar tsoro da yaje sai yaji kamar an wanka masa mari,yayi hakan kusan sau uku,ana ukun ne,ya daina gani ya shiga lalube ba tare da yana gane komai ba,ya daki katon jikin gado…saida gwiwar sa ta fashe,waiyoo na shiga uku ya furta yana tab’a gurin…kaya ya maida,yanajin kansa na sarawa ya dauki lawazima yana layi da lalub’e ya fitar da’ita yana kiran Alh gambo,

Dake zaune can backyards yayi saurin tasowa ya karb’e ta…

Yana mik’awa Alh gambo idon ya bud’e ….wani irin kallon tsana yakewa Lawazima,cikin bacin rai yace ,”Aka sheta, kuma yanzu zaka basu umarni dan wannan ba mutum bace,dan haka nake so ku kashemin ita,sannan ku  nemo min iyayen ta,wlh sai nasa sun d’and’ani irin  rad”ad’in da nakeji a yanzu”

“Amma nace kisa fa kace””da kata banason jin komai shin ka mance abinda,Artii baguu,(india)yace ne?shin ka mance sharadin Cancanwa na (China) ya ce dam?wannan karan tsafin su ya nuna cewa muddin muka samu harka sannan bamu fad’a ciki ba,ya zamto kyallen ya bar tukunyar to na tabbatar wannan ya mutu,idan ba haka ba,dole ne na fad’i zab’e”

“Kai kasan zan iya yin komai sbd kujera ta,zan iya yin komai sbd mulki na,kana tunanin zan yi saka ci wani yayi zaton nidin nan banason kujera ta?”kayi hakuri duk na mance ne wlh. “karaf lawazima tace …Me ka mance,uncle….

Dan Allah ina uncle da yabani abinci?yace zai siyi kanwar duka yabani kud’i kuma saina ya samin wani farin kyalle,yana kai hannu ni kuwa mai wayo nace auzubillahi minasshaidanir rajeem,ai umma ta kullum tana koya mana addu’a kuma tace ana sace mutani a yanka su,ban sake sanin inda nake ba,kawai sai ga wannan,ta nuna wannan Dattijon da hannu,ya cire kaya nayi saurin rufe ido na,na fara fadin Auzubikallmatillahi tamat,mingadabihi wa’ika bihi,washarra ibadahi,wamin hamazati shayadin wa’anyahdarun,kuma ….”

“Keeee yimin shiru,Gambo ya ka mata  mu d’auki mata ki,yarinyar nan ta ganni,oh my god,”

©”Ya Allah lawazima kullum bayan sallah asuba saina taraku gaba d’aya munyi azkar,tun kina ‘yar shekaru uku nake koyar dake addu’a da yadda zakiyi su,sannan da lokacin sa zakiyi sbd,wannan yanayi da muke ciki,Allah ya kare ki,lawazima,gani nadawo gida dan na ganki,babu ke ba labarin ki” 

Ta fashe da kuka mai tsuma zuciya..

41

Cikin ta daya Farar ruri alamun yunwa takai hannu ta shafa, gaba d’aya ta manta da batun abinci sai yanzu ,da cikin ke sanar da’ita yana bukatar  ta Kai masa d’auki cikin gaggawa,amma ina ta kasa yin hakan SBD hankalin ya tashi rashin ganin lawazima, har mak’ota Saida ta dudduba ko zata ga lawazima,duk Wanda ta tambaya sai yace rabon sa da’ita tunda rana.

Wanda ya mik’awa Lawazima har juya zai tafi Dattijon ya sake Kiran sa Rai abace,

“naso ka sanar dasu cewa su kashe ta, sannan baza ta tab’a samun sallah ba,su bar ta agurin ta zama abincin” namomon jeji,Ina fata ka gane”angama rankai d’ad’e indai wannan k’aramar k’waron ne kada hankalin ka ya tashi,ita d’in banza mun gama da wad’anda suka fita,masu ji da kansu ga kudi ga mulki,bare wannan talakar banza”

Murmushi Dattijon yayi tare da jinjinawa Alh gambo da hannu,yasa ta a motar,gana daya lawazima ta tsorata, musamman da ya wanka Mata wasu zafafan marin da ya Mata kafin ya Sanya ta a motar,ya fara gudu har ya isa ga,wani.dan daba shirgege ya parking motar a gefe, ya fita sunyi magana da shi sosai kafin ya mik’a Masa ita,Alh gambo na tafiya ya fara marin lawazima…

“Dan Allah kayi hakuri nibanyi komai ba”ya k’ara Mata wani da Saida ya fasa Mata baki,jini na fita Amma ko ajikin sa,kanta ya buga da wata bishiya…tayi wani razananniyar k’ara sa yasa ta fad’i warwas babu … numfashi,hannun ta ya d’aga ,ya tabbatar ta mutu,yasa kafa ya ture ta ta gangara ,yayi wuce war sa…..

© Humaira ce zaune tana shek’a dariya ganin damin kudi agaban su,ta kalli Chuchu da ya shigo gidan a matsayin kawar ta,tana cewa

“Wlh ban d’auka dad zai bada kudin Nan cikin sauki haka,Amma daga kiran na biyu Yana dagawa ya amince,yanzu yadda zanyi na fita daga gidan Nan shine tashin hankalin,Amma Naji Yana cewa zai raka president wani taro America ranar Sunday ni Kuma Monday Zan fara aikina insha Allah”

“Ok Allah ya kaimu ,ni dai tunda an samu waccan sai Amin ‘yar taimako”ya k’arasa maganar yana kashe Mata ido

Speaker zaune a Asibiti Yana tausayin Mmn Buhari na rashin ganin lawazima,gefe guda Kuma Yana ayyana irin abinda zai aikatawa Honarable Saleh yabanya …

Lawazima na kwance fuskar ta ya kunbura,babu alamar numfashi, cikin ikon Allah sai ga ruwan sama Yana sauka batare da hadari ya hadu ba,jin saukar ruwan da tayi a jikin ta shi yadawo da’ita daga doguwar sumar da tayi,a hankali take son bud’e idon ta Amma Ina ta kasa,ta yunk’ura zata tashi saiga wannan kyakkyawar saurayin mijin fatima,akan doki,shima ruwa ya Masa duka.

Tun daga nesa ya hango mutum a kwance hakan yasashi tahowa Dan yaga waye, lokacin da ya iso hannu kawai lawazima ke iya d’aga Masa ….

Da sauri ya sauka daga kan dokin ya d’auke ta,sanin cewa jejin nada matu’kar hatsari yasa Shi d’ora ta saman dokin ya fara gudu,ganin numfashin lawazima kamar zai d’auke ya sa shi tsayawa da dokin bayan sunyi tafiya Mai nisan gaske,Dan a lokacin hasken torch light kad’ai suke gani ko.alamun tsoro babu a tattare dashi….

Wani bargo ya shimfida tare da kwantar da lawazima,”Innalillahi wa inna ilaihi rajiun”shine kalmar da yake maimaitawa,wasu zafafan zufa  ya share da hannun sa,duk da irin sanyi da ake a wannan jejin……

3 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!