Aneesah Romantic Love Novel
Bismillahir Rahamani Rahim
1&3
Wasu yara ne Zazzune suke saman tabarma ana cin abinci wata yar Matashiyar yarinya ce bazata wuce shekara sha shida aduniya ba zaune take saman kujera ta ɗura kafa ɗaya saman ɗaya fuskar ta babu rahama kallon su take ɗaya bayan ɗaya sannan tace “ina Auwali yake”!?.
Jikin su ya fara rawa ɗaya daga cikin su yace”Allah ya kara maki lafiya Aunty wallahi yana gidan admu me shago.
Wani dattijo ne ya shigo cikin gidan yana gyara murya Yatsine fuska tayi tace “wai kai Baba me yasa kullum kake abu irin na yan yara wallahi shiyasa bana son ina zaune kake shigowa.
Tooo bismillah yanzun zaki fara yi mani wa’azi to ba zanyi Sallamar ba tunda kinga ina kyale ki ko shegeyer yarinya mai kama da aljanu wallahi dan dai cikin ƴayana ke kawai ce Allah ya ɗura mani sonki to ina uwar ki.
Ɗauke fuskar ta tayi tace”to wallahi ba zan daina fada maka gaskiya ba ko ka gyara ko kamar ma ka gyara na dai fada maka.
Cikin takaici ya wuce cikin ɗaki saboda ba zai iya sa ina sa da ita ba.
Wata yar budurwa ce tashigo cikin gida ta hango ta burki ta ci tace “yau na shiga ukku na to yanzun ku me za’a ce mani, karaso tayi tana murmshi tace “Aneesah kina lafiya”!?.
Wani mugun kallo ta watsa mata tace”daga ina kike kuma wa ya aikeki”!?.
Cikinta yace kuullluuu dafe cikin tayi tace”Amm dama dama.
[…] Aneesah Romantic Love Novel […]