
Aneesha ko Aneesa Hausa Novel Part 1
[08/10, 7:44 am] +234 706 345 2697: *ANEESHA KO ANEESA*
*🌺🌺🌺⭐⭐⭐☀☀☀🌺🌺🌺*
*Zan dinga amfani da waɗannan flowers da sters ɗin da kunga novels da haka to Indian Girl ce nagode*
*Aƙalamin*
*Zainab Muhammad (Indian Girl)*
*Women Writers Association*
*W.W.A*
*Ga wani sabon salo mai rikitarwa soyayya ce tsagwaranta cin amana da sauran su ku dai kawai ku biyo ni muje zuwa*
*Littafin kuɗi ne gama son biyan nata kuɗin kafin na gama bunus tai min magana ta wannan number 07063452697*
*Sai kun zo*
*Bunus page 1*
*_____________________________________* Sanye take cikin wata doguwar riga pink colour mai matuƙar kyau,ta yane kanta da mayafin rigar.
Kyakykyawa ce fara doguwa tana da jiki amma bata da ƙiba,komai da ubangiji yake halittar kowacce mace da shi ya yi mata domin komai masha Allah kamar itace tai kanta.
A gurguje take saukowa daga step ɗin bene hannunta ɗauke da iphone ɗinta da littafai,tana sakkowa ƙasan falon ba tare da ta lura da kowane a falon ba ta nufi hanyar fita daga falon.
“Ke Aneesha!”
Kyakykyawar matar dake zaune akan ɗaya daga cikin kujerun dake falon wadda a shekaruta a ƙalla ba zata wuce 45 ba,taci kwalliya cikin wata haɗaɗɗiyar atamfa marron mai tsananin kyau da tsada.
A slow Aneesha ta juyo ta kalli sai tin inda maganar ta fito,kafin cikin wata irin sanyayyar murya mai daɗi.
Tace”Na’am Mammy”
Matar da aka kira da Mammy Tace”Aneesha ina zuwa haka ba kya ko kallon gabanki?”
Aneesha ta dafe goshi sannan Tace”Oh Mammy sorry na sha’afa ne saboda ina sauri zan tafi makaranta”
Mammy Tace”Amma dan za ki tafi makanata ai ya kamata ki natsu ki tafiyar ko”
“Mammy sorry ki bari na dawo domin lecture ɗin malamin ya na da wahala”
Mammy Tace”To amma dai ai kya tsaya ki yi break fast ko?”
“Ni dai Mammy idan na dawo na yi gaskiya”
Tana gama faɗar haka bata jira abinda Mammy za tace ba ta fice daga falon tare da jan ƙofar ta rufe.
Mammy ta ɗauke idonta daga kallon Aneesha tun da ta fice,sannan ta mai da hankalinta ga tv plasman dake ɗakin.
Fitar Aneesha daga falon ta nufi motar da ke ajiye a harabar gidan ta shiga tare da nufar get,mai gadi ya buɗe mata get ɗin ta fice.
Sauri sosai take zu bawa tana duba agogon dake cikin wayar ƙarfe 6:30am za su shiga gashi yanzu har 6:20am,na ta daɗa gudun motar dan ta isa da wuri.
Ƙarfe 6:28am cif ta isa makarantar da sauri ta paking motar ta ba tare da ta tsaya ɗaukan komai ba ta ɗaukin littafanta ta fice tare da nufar ajin dan ko wayarta bata tsaya ta ɗauka ba.
Bata lura da akwai malami ko babu ba a class ɗin ta danna kai kawai tare da ƴar siririyar sallamarta,waje ta samu ta zauna tare da runtse idonta a ranta tana godiya ga Allah da ya sa ta shiga lecture ran bai shigo ba.
“Keee!”
Aneesha da idanunta ke kulle ta tsinkayo muryar sa cikin kunnuwanta,a hankali ta buɗe idon tare da ɗora su akan malamin dake tsaye a gaban allo,ta firgita da ganinsa haɗi da ganin har ma ya yi writing akan allo sai ta ɗan basar.
Ya sake cewa fuskar sa a haɗe,”Wai ke ba dake nake ba?”
Aneesha ta ɗaga kai ta kalleshi ta san da ita yake domin itace ta shigo class ɗin yanzu.
“Malam mai name is Aneesha Bashir”
Ta faɗa kanta na ƙasa domin bata iya tsawa haɗa ido da mutum.
A harzuƙe malamin Yace”Dan ubanki naƙi na gaɗi sunan naki,ke ƴar gidan uban wace da zaki shigo min aji ba tare da neman izini ba?”
Aneesha bata iya rashin kunya ba kuma sannan bata iya magana mai tsawo hakan ya sa taja bakinta tai shiru.
Malamin ya sa ke ƙufula da ganin ba tace komai ba,Yace”Dan ubanki tashi ki fice min daga aji tun da ina miki magana kin min ban za”
“To Malam me kake so nace,idan na yi magana ka ce na maka rashin kunya?”
Aneesha ta faɗa cikin ɗan zafi domin ta gaji da zagin ubanta da yake tayi bayan ba ubanta ne yai ma sa ba ita tai masa.
Malamin Yace”Ki tashi ki fice kuma daga yau idan har na shigo class ko kin makara ko baki makara ba ki fice domin bana son ganinki na tsaneki”
Ba Aneesha ka ɗai ba har student ɗin dake class ɗin da sauri su ka kalli malamin jin irin kalaman da yake jifan Aneeshan da su,ba damar magana dan gashi su na ganin abinda yai mata sai su ka shiga gyaɗa kai kawai.
Aneesh da baƙin ciki ya kamata sai kawai hawaye su ka shiga zubo mata wanda ta yi ƙoƴarin riƙe su amma ɓacin rai ya hana ita ta tsani taga ana wulaƙanta mutum balle a ce itace akaiwa,ya tsane ta fa yace to shine wanda ya halicceta.
Hakan take faɗa a zuciyarta,a hankali ta kwashe littafanta ta fice tana goge hawayen da ke zu bo mata,can ta nausa ta nufi wani garden dake cikin makaranta ta sa mu waje ta zauna nan take wani irin kukan takaici ya kamata.
Wai yau ita ake cewa ba a so ba a son gani kuma? ko da yake ita wace tun da wa su al’umma marasa amfani su ka ce ba sa son annabin rahma to ita a wa ƙaramar halitta.
Wannan tunanin takw a zuciyarta hawayen ba su dena zu bo mata ba.
“Amincin Allah ya tabbata a gare ki ya ke wannan kyakykyawar halitta mai cike da kwarjini da kyawawan halaye,ki dena zubar da hawayen ki a ban za akan abinda ba shi da amfani ki sani cewa da ma haka duniyar take ka sa mu mai sonka sannan ka sa mu maƙiyinka”
Wannan amon magan ganun ta ji su na tashi ta ko ina ya yin da su ke shiga kunnuwanta,a ɗan tsotace ta shiga waige waige ko za ta ga mai wannan maganar amma ina ba ta ga akamun kofa sahun biri ba balle na mutum.
Take taji wani tsoro ya ɗan kamata hakan ya sa ta mike jiki a sanyaye ta bar wajan ta koma cikin mutane ta sa mu waje ta zauna ta ɗora kanta a cinyarta ya yin da zuciyarta ke bugawa tana tuna wannan maganar ko wane ya ke faɗa oho.
“Au Aneesha dama kina nan nake ta nemanki ban ganki ba?”
A hankali Aneesha ta ɗaga kai ta zu ba wa ƙawarta Farisa idanu amma ba ta ce komai ba.
Farisa ta sa mu waje ta zauna ku sa da Aneesha sannan ta sake,Cewa”Wallahi Aneesha tun da kika malamin nan ya koro ki daga class ɗin na hankali na ke kan ki”
Aneesha ta ɗan yi murmushi amma ba tace komai ba.
Farisa tacigaba da magana,”Wallahi san da naji malamin nan yana zaginki haɗi da furta miki kalmar tsana take naji duk nima na tsane shi”
Aneesha ta ɗan zaro ido da,Cewa”Subhanallahi Farisa ba bu kyau fa kace baka ƙaunar mutum alhalin ba kai ka halicci wannan mutumin ba”
Farisa Tace”To mene dan na faɗa shima fa naga haka ya furta ba tare da ya yi tunanin ya ci miki mutunci ne a gaban mutane ba”
Aneesha Tace”Ke dai ki dena faɗa tun da na san kina da hankali ba kamar shi ba”
Farisa za ta sa ke magana Aneesha ta katse ta da,Cewa”Kinga tashi muje mu nemi wani abun domin wallahi na fara jin yunwa dan banci komai ba na fito”
Farisa ta gane nufin Aneesha ba ta so a cigaba da maganar malamin ne ya sa ta sa ko wani zan cen,murmushi Farisan tayi sannan.
Tace”Ok tam tashi muje”
Nan su ka miƴe gaba ɗaya su ka nufi inda ake sayar da abinci a makarantar,su na isa Aneeesha ta ba da umarnin abinda za a kawo mata sannan ta kalli Farisa.
Tace”Kefa me za a kawo miki?”
Farisa ta ɗan yi jim sannan,Tace”Uhm anya ni zan ci wani abu wa”
Aneesha Tace”A’a ki daure dai domin na san bakya ra sa abinda kike so ba”
Farisa Tace”Allah bana buƴatar cin komai ni domin nai break kan na fito”
Aneesha Tace”Ok”
A taƙaice.
Nam aka kawo wa Aneesha abinda ta buƙata nan ta fara ci,bayan ta gama ta ba su kuɗin su sannan su ka ta shi su ka bar wajan.
Kai tsaye class ɗin su ka nufa da sauran student da yawa a ciki su na shiga Aneesha ta tuna abinda malamin nan yai mata take taji ƙwalla ta ɗigo daga idanunta.
Nan su ka sa mu waje su ka zauna,ƴan ajin ne su ka dinga bata haƙuri akan abinda malamin yai mata dake Aneesha kowa yana ya bawa da ita domin ba ruwanta gata shiru shiru.
Mirmushi Aneesha ta yi kafin,Tace”Ba komai ai domin dama zana tare ya gaji haka zo mu zauna zo mu saɓa,dan haka ba komai”
Nan wa su da dama su ka ƙara jin sonta a ran su daga mata har mazan class ɗin,ya yin da maƙiya kuma haushinta su ka dinga ji.
Ranar haka dai su ka gama ɗaukan lectures ɗin su ka tashi.
Aneesha ce ta ɗauki Farisa a motarta ta sauketa a gida sannan ita kuma ta wuce gida.
Tana isa gida bayan ta gama paking motarta ta nufi cikin gidan,tana shiga kai tsaye wajan firij ta nufa ta buɗr tare da ɗaukan robar ruwa ta buɗe ta sha sannan ta aje tare da hayewa bene zuwa ɗakinta.
Tana shiga kai tsaye wanka ta fara shiga ta yi sannan ta fito ta sauya kayan dake jikinta zuwa atamfa riga da zani,sun matuƙar yi mata kyau.
Wayarta ta duba dan ta ɗauka amma sai bata ganta ba tunani tai ashe fa ta barta a mota dan haka ta nufi ƙasa,da sauri da sauri ta nufi harabar gidan tare da buɗe motar ta ɗauki wayar sannan ta koma cikin gidan.
Ɗakin Mammy ta shiga dan tai mata sannu da gida,tana shiga ta sami Mammy kwance a kan gadonta da wayarta a hannunnta.
Sallama Aneesha ta yi sannan ta nemi waje ta zauna bakin gado,bayan Mammy ta amsa sallamar.
Aneesha Tace”Mammy sannu da gida”
Mammy ta gyara kwanciyarta tare da ɗauke kanta daga kan wayar ta kalli Aneesha.
Tace”Lafiya Ƙalau Aneesha kin dawo”
“Eh Mammy”
Aneesha ta faɗa.
Mammy Tace”Ok ki tashi kije falo ki ɗauki break fast ɗinki ki yi domin na san kin ɗebo yunwa”
Aneesha tai murmushi da,Cewa”Ai Mammy nayi a makaranta sai dai in anjima idan an gama lunch”
Mammy Tace”Ok to shikenan”
Aneesha ta miƴe tana Cewa”Mammy bari naje ɗaki”
Mammy Tace”Ok li kwanta ki wuta kinji?”
Aneesha ta amsa da “To” sannan ta fice ta nufi ɗakinta,tana zuwa kan makeken gadonta ta faɗa tare da kulle idanunta wata irin ƴar nutsuwa ta zo mata take kuma kwakwalwarta ta shiga tuna mata da maganganun malamin nan a gareta,ganin kamar tunanin yana neman ya aa ranta ya ɓaci ya sa ta kau da shi.
Bata jima da kwanciya ba bacci ya kwasheta sakamakon tashin wuri da tai yau ya sa bata sami ishashshan bacci ba.
Tana cikin baccin ne taji ana bubbuga mata ƙafa alamar ta tashi,a hankali ta buɗe idanunta ta sauke shi a kanta.
Ita kuwa cikin masifa ta fara magana,”Yanzu saboda Allah Ya Aneesha wani banza yai miki cin mutunci har yace baya ƙaunarki amma kiƙi koda ramawa haba dan Allah ni wallahi kin ban kunya,a ce ma tun da ke ba za ki rama ba ba sai ki kirani ba tun da makaranta ɗaya ne amma wai sai labari nake ji”
Sakin baki Aneesha ta yi tana kallon Aneesa har ta gama faɗar abinda ke bakinta,sannan ita kuma.
Tace”Ban da abinki Aneesa kin taɓa gani an ja da malami?”
“Ai va malamin islamiyya bane balle ki ce”
Aneesa ta faɗa tana turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.
Aneesha tai murmushi Tace”Haba Aneesa ta ki rage wannan zafin naki mana ba na so wallahi duk school sai dai naji ana ta ƙanwata bata ji ga rashin kunya ni kuma bana jin daɗin hakan”
Ai da sauri Aneesa ta ɗaga kai ta kalli Aneesha jin ta faɗi cewar wai ana faɗar rashin kunyarta,Tace”Kan bala uban wane yace ban da kunya wallahi sai na ci uban mutum”
Zaro ido Aneesha tayi,Tace”A’uzibillahi! haba Aneesa zagi kamar ke dan Allah ki dena kinji”
Aneesa Tace”Kin ga ba ma wai abinda student su ka faɗa ne yake damuna ba a’a abinda wannan shegen malamin yai miki ne kuma wallahi gobe sai na yanka masa tsiya”
Aneesha ta saki baki tana kallon ƙanwar tata Aneesa,duk da ta san halin Aneesa na rashin ji da rashin kunya amma bata son taji wani yace tai masa.
Dafe kanta tayi da ya fara yi mata ciwo sakamakon tashin da Aneesan tai mata alhalin ta san idan tana bacci aka tashe ta kanta ciwo yake amma saboda masifa na cinta ya sa ta manta da wannan.
Bata iya komawa baccin ba dan haka ta miƴe ta shiga toilet tai wanka ta ɗauro alwala jin ana kiran sallar azhar.
Ita kuwa Aneesa tana fita daga ɗakin Aneesha ɗakinta ta wuce sai wuci take ta samu ta cire kayanta ta shiga wanka,lokacin da ta sakarwa kanta shower ne taji ɓacin ran nata yana ɗan raguwa.
Bayan ta gama ta fito tana shanshane jikinta kafin ta isa gaban mirror ba wani makeup tai ba powder da lip ta shafa kawai ta ɗauki ƙananan kaya wanda sune kayanta ta saka riga da wando ma su kyau.
Ta so ta kwanta ta wuta amma tana son fita unguwa hakan ya sa ta ɗauki key da wayoyinta ta fice ko sallama ba taiwa Mammy ba.
*______________________________________________________________________________________________________________________*
Sanye yake cikin ƙananan kaya riga da wando ma su matuƙar kyau bluen riga da black ɗin wando kayan sun matuƙar yi ma sa kyau.
Farine kyakykyawa amma duk wani abu da ubangiji yake wa ɗa namiji a halitta yaiwa ma sa.
Tsaye yake a filin jirgin sama na Aminu kano wanda da alama jirgine ya sauke su yanzu domin jama’a da dama kowa neman ƙbarin wajan yake,gaban sa kuwa ƙmanyan akwatuna ne manya guda uku,mai taksi ya sa mu ya tara ya hau tare da faɗa ma sa inda zai kai shi,haka mai taksi ɗin ya ja su ka tafi.
Tun da su ka fara shigowa unguwar yake gani sauye sauye kala kala domin an daɗa ƙawata unguwar ba kaɗan ba,a wani bakin ƙaton get milk yace mai taksi ɗin ya faka.
Bayan ya fito ya miƴawa mai taksi ɗin dubu biyar mai taksi ya kalleshi da neman ƙarin bayani.
Yace”Na bar maka”
Godiya mai taksi ya yi sannan ya ja ya tafi.
Matsawa jikin get ɗin ya yi yai knock mai gadi ya buɗe yana tambayar wane,ganin wanda ke tsaye a gun ya sa shi washe baki cike da farin ciki.
Mai gadin Yace”Ah mai gida yanzu ka sauka? Sannu da zuwa”
Shima fuskarsa ciki da murmushi ya bawa mai gadin umarnin a shigo ma sa da kaya sannan ya shige ciki.
A hankali take saukowa daga kan steps ɗin da wayarta a hannunta shirin fita tayi domin shigar tata ce a jikinta wato ƙananan kaya riga da siket wannan karan,ta ɗaga kanta daga kan wayar tana kallon hanyar fita ai a miliyan ta ƙarasa saukowa ta tafi ta rungumeshi tana.
Cewa”Lahhh! Ya Tahariq saukar yau she?”
Shima murmushin yake yana mai mamakin girman ƙanwar ta sa duk da yana ganin pics ɗinta ta waya amma ba kamar yanzu da ya ganta zahiri ba.
Yace”My Little ƙanwa yanzu muka sauka”
“Amma shine koka kira a zo a tafi da kai”
Aneesa ta faɗa cikin fushi domin ita abin fushi baya mata wahala.
Ƴar dariya Tahariq ya yi sannan,Yace”Sorry! Sorry!! My Little dama so nai na baku mamaki”
Kafin Aneesa tai magana su ka jiyo muryar Mammy dake saukowa daga benan yanzu tana,Cewa”Aneesa baƙi mu kai ne”
Ai ba ta san san da ta ƙarasa saukowa ba fuskarta cikie da murmushin ganin ɗan nata.
Shima Tahriq yai saurin ƙarasawa wajan Mammy na sa ya rungumeta cike da kewar shekarun da ya yi ba tare da ita ba.
“I miss you Mammy”
Ya faɗa cikin muryar shagwaɓa.
Itama Mammy ta mayar ma sa da,”I miss you too My Son”
Sun ɗan jima a haka ita kuwa Aneesa tana tsaye sai aikin murmushi take,Mammy ta sake shi sannan.
Tace”Amma My Son mai ya sa baka kira ka faɗi cewar ka sauka ba?”
Tahariq Yace”Sorry Mammy dama na so na baku mamaki ne tun da kuna cewa ba zan gane hanya ba”
Dariya su duka su ka saka kafin su ƙarasa su zauna akan kujerun dake falon.
Tahariq ya hau kalle kalle kafin daga bi sani,Yace”Wai Mammy ina My Sweet Sis ne?”
Kafin Mammy tai magana sai ga Aneesha tana saukowa daga steps fuskarta cike da fara’a,ta ƙaraso cikin falon sai ta ja ta tsaya tana murmushi.
Tahariq ya miƴe yana,Cewa”Come My Sweet Sis”
Ya ƙarasa faɗa yana buɗe mata hannun sa alamar taje tai hug ɗin sa.
Aneesha ta kasa ko da ɗaga ƙafarta balle tai abinda yace ɗin.
Tahariq Yace”Ok! kenan baki kewar Yayanki ba ko? Shikenan ba komai”
Sai ya ɗan haɗe rai.
Ganin haka ya sa Aneesha tai saurin ƙarasawa tai hug ɗin na sa duk da ba ta so haka ba gani take kamar bai dace ba duk da su na uwa ɗaya uba ɗaya.
Wani irin shock ya ji lokacin da ya ji tai hugging ɗin sa,sun ɗan jima a haka kafin ta sake shi ta nemi waje ta zauna ku sa da shi ɗan ne sa kaɗan.
Aneesa dake dariya Tace”Wallahi Ya Tahariq Ya Aneesha ƴar kauyece ita wai duk irin waɗan nan abubuwan sai tace ba kyau ba za tai ba”
Tahariq ya kalli Aneesha su ka haɗa ido a idanun sa ta ga yana mata tambayar wai haka?.
Aneesha idanunta su kai rau rau kamar za tai kuka,Tace”Na rantse Ya Tahariq ƙarya take mun”
Tahariq yai murmushi yana kallon Aneesa,Yace”To kinji da bakinta ƙarya kike mata Little”
Aneesa da saurin fushi ta cuno baki,Tace”Wallahi Ya Tahariq ba rantsewa tai ba ai”
“To rigimammu da idan har kuka haɗu sai kun nuna halin sai ku rabu da shi ai ya samu yaci abinci ya wuta tun da ya kwaso gajiya”
Mammy ce tai wannan maganar.
Da sauri Aneesha ta miƙe tana,Cewa”Ya Tahariq ta so muje kaga na haɗa maka kala kalan abinci”
Hannunsa ya miƙa mata ta kama ya tashi su ka jera wajan dinning ɗin su na murmushi abinka da ƴan uwan da aka daɗe ba a haɗu ba.
Aneesa ta taɓe baki,Tace”Aikin banza tusa kai ba kwarjini”
Aneesha tai saurin kallonta jin abinda tace ya sa har idanunta sun fara kawo hawaye.
Tahariq ganin Aneesa so take ta ɓatawa Aneesha rai kuma a wannan ɗan zaman da su kai ya fuskanci Aneesa saurin fushi da tsokana gareta ita kuwa Aneesha ba ruwanta sannan tana da sauƙin kai.
Yace”Little so kike mu yi faɗa daga dawowa ta ko?”
“Sorry Ya Tahariq amma ai gaskiya na faɗa”
Aneesa ta faɗi haka tana miƙewa za ta fice.
Da sauri Mammy ta tsai da ita ta hanyar,Cewa”Ke! Aneesa ina zuwa kuma?”
“Mammy unguwa zan ɗan je”
Aneesa ta ba Mammy amsa.
Mammy Tace”To ba inda zaki,ke ko dan Yayanki da tun kuna yara ya bar gari sai yanzu da kuka girma ya dawo ai kya tsaya ki nuna farin ciki baki ga ƴar uwarki ba”
Aneesa ta zumɓuri baki,Tace”To Mammy ai na yi farin ciki kuma sannan ai yanzu zan dawo”
“To ba inda zaki”
Mammy ta faɗa tana miƙewa dan isa wajan dinning ɗin.
Kuka Aneesa ta saka ta haye sama tana shiga ɗakinta ta faɗa gado tana kuka wai ita mai ya sa Mammy ke son takura mata ne eyye? ta tambayi kanta.
*Acan ƙasa wajan dinnig*
Ita kuwa Aneesha daɗi taji da Mammy ta hana Aneesa wannan shegiyar futar wadda da an magana tace yanzu zata dawo.
Haka ta shiga zuzzubawa Tahariq duk kalar abinci da su ka girka a plat har sai da yace ta bar shi haka,haka ta zauna yana ci su na hira har ya gama ita kuwa Mammy cike da farin cikin yadda taga ƴaƴan nata su na yi duk da ba wani sabone a tsakanin su ba ta miƙe ta haye sama zuwa ɗakinta.
Bayan Tahariq ya gama Aneesha ta kwashe kwanukan ta kai kitchen sannan ta dawo ta taimaka ma sa su ka kai akwatinan ɗakin sa duk da sun mata nauyi,aikwa Tahariq yai farin ciki ganin yadda ƙanwar ta sa ke tarairayar sa.
*Tofa ga wani salon mai rikitarwa soyayya cin mutunci salo dai kala kala*
*Amma fa littafin kuɗi ne*
[08/10, 7:50 am] +234 706 345 2697: *ANEESHA KO ANEESA*
*🌺🌺🌺⭐⭐⭐☀☀☀🌺🌺🌺*
*Zan dinga amfani da waɗannan flowers da sters ɗin da kunga novels da haka to Indian Girl ce nagode*
*Aƙalamin*
*Maman Amaturrahman*
*Ga wani sabon salo mai rikitarwa soyayya ce tsagwaranta cin amana da sauran su ku dai kawai ku biyo ni muje zuwa*
*Littafin kuɗi ne gama son biyan nata kuɗin kafin na gama bunus tai min magana ta wannan number 07063452697*
*Sai kun zo*
*Bunus page 2*
*_________________________________________________________________________________________________________________________* Bayan ta sun gama shiga da komai Aneesha ta juya zata fita.
“Nagode sosai My Sweet Sis idan na huta zan kira ku ku karɓi tsarabar ku”
Aneesha raji muryar Yayan nata ya faɗi haka,ta juyo tare da cuno ɗan ƙaramin bakinta.
Tace”Haba Ya Tahariq godiya kuma sai kace ni ba ƙanwar ka bace”
Tahariq yai murmushi sannan,Yace”Sorry ƙanwata ai hidimar da kikai min dole nace na gode”
“Ni dai ban so”
Aneesha tai maganar cikin shagwaɓa.
Murmushi Tahariq ya yi sannan,Yace”Ok! ok!! na dena to”
Murmushi kawai Aneesha tai bata sake cewa komai ba ta fice daga ɗakin.
Sauke ajiyar zuciya Tahariq ya yi gaskiya Aneesha sauƙin kanta na burge shi.
Wanka ya shiga bayan ya fito ya kwanta domin ya ɗan wuce gajiyar sa.
ANEESA.
Kuka taci sosai har ya kusa sa mata ciwon kai saboda Mammy ta hana ta fita unguwa.
Wayarta dake ku sa da ita ta hau ruri da ta so ta share wayar amma mai kiran ba zai yiwu ta share shi ba dan haka ta sa hannu ta janyo wayar tare da amsa kiran ta kara a kunne,kafin tai magana taji ya fara magana.
“Haba Baby ya za ai ki shanyani kuma ki ƙi zuwa?”
Aneesa tai rau rau da muryarta sannan,Tace”Sorry Dear wallahi Mammy ta hanani fitowa”
“Da Mammy ta hana ki fitowa ke baki da dabarar da zaki ki fito,haba sai kace ba wayayyiya ba”
Ya sake faɗar haka da ɓacin rai.
Aneesa Tace”Babu damar hakan shi yasa”
Cikin ɗan ɗaga murya,Yace”Ok shikenan tun da ba zaki zo ba no problem”
Bai jira abinda za ta ce ba ya kashe wayar.
Da sauri Aneesa ta miƴe daga kwancen da take tana kallon screen ɗin wayar lokacin da taji ya kashe wayar,dafe kanta ta yi ita kwa ya za tai ta fita daga gidan nan taje wajansa?.
Tunaninta kenan amma ba mifita,can sai wata dabara ta zo mata dan haka tai murmushi tare da miƙewa ta fice zuwa ɗakin Mammy.
Zaune ta sami Mammyn akan sallaya da alama sallar la’asar ta idar amma bata tashi ba.
Sallama tai ta isa bakin gado ta zauna sannan ta dubi Mammyn kafin.
Tace”Mammy yanzu aka kira ni aka faɗamin muna da wani test”
Mammy ta ɗaga kai ta kalli Aneesa,Tace”Test kuma amma ai yau ba ku ce za ku school ba ko”
Aneesa ta raunatar da murya Tace”Mammy yanzu fa wata friend ɗina ta kira take faɗamin”
“To ita kuma Aneesha fa ba ita?”
Mammy ta tambaya.
Aneesa ta cuno ɗan ƙaramin bakinta wanda na lura da cewar al’adar su ce ita da Aneesha,Tace”Mammy kowa fa da akwai abinda ya ke karanta ni ina karantar catering ne ita kuma Aneesha nursing ne kinga ai ba department ɗin mu ɗaya ba dan haka bai zama dole abinda za mu yi shi za su yi ba”
Aneesa ta iya zuba zan cen wanda ba zaka taɓa cewa ƙarya take ba.
Har Aneesa ta kai ƙarshen maganarta idanun Mammy na kanta tana kallonta.
Kafin Tace”Ki tashi kije Allah ya tsare sannan kuma ki riƙe mutuncin kanki da a kullum dai nake sake faɗa mu ku”
Aneesa cike da farin ciki amma bata nuna Mammy ta gani ba,Tace”Insha Allah Mammy sai na dawo”
Mammy Tace”Allah ya tsare”
Aneesa ta amsa da ameen sannan ta fice,kai tsaye ɗakinta ta koma bayan fitowarta daga ɗakin Mammyn.
Wanka ta sake yi ta canza kaya zuwa riga da sket matsatstsu waɗan ita kanta badan ta saba ba da ba zata iya sawa ba saboda matsewar da su kai mata,komai na halittar jikinta ya bayyana barin ma saman ƙirjinta duk ya fi ko ina fitowa.
Gyara gashin kanta tayi tare da ɗaukan afta dress ta ɗora akan kayan wanda ba mai ganin halin da jikinta ke ciki,takalmi mai tsina ta saka sannan ta ɗauki wayoyinta bako mayafi ta fice zuwa harabar gidan inda ake aje motoci.
Wata black ɗin mota ta hau mai kyau wadda Aneesha ke tafiya school da ita,tuƙawa tai ta fice daga gidan.
Tana cikin tuƙin ne ta ɗauki wayarta ta danna number sa tai ta ringings amma ba a ɗaga ba har sai da ta kira sau 4 sannan ya ɗaga ba tare da yace komai ba.
Tace”Haba Dear fushi kai da ni?”
Cikin faɗa Yace”Kinga malama me zaki faɗa? Ki faɗa na kashe wayata”
Rau rau idanun Aneesa yai kamar za tai kuka ya yin da a zuciyarta take cewa’duk dan ya ga ina son sa ne yake min wulaƙanci amma ya zan yi’.
Cikin muryar kuka,Tace”Dan Allah Dear ka yi haƙuri gani nan fa na tawo kana ina yanzu?”
Sassanyan murmushi haɗi da ajiyar zuciya ya sauke sannan cikin basar da ita,Yace”Ai kawai ma ba sai kin zo ba ki koma na ma samu wata ai”
Wani tuƙuƙin baƙin ciki haushi ya kama Aneesa kukan da ya zo mata take ƙoƙarin riƙe shi ya kubce mata,cikin kukan ta fara.
Cewa”Dear ka samu wata fa kace? Dama ni ba sona kake ba? kuma ai naga na baka haƙuri”
Har ga Allah ya ji zafin kukan nata a zuciyar sa domin idan yace baya ƙaunar Aneesa yai wa kan sa da zuciyar sa ƙarya.
Cikin lallashi Yace”Haba Baby da wasa fa nake miki ke a tunaninki akwai wadda ta isa ta zauna gurbinki?”
Dariya ta subcewa Aneesa tai mai isarta sannan,Tace”To kana insa?”
Ya kwaikwayi maganarta dake cikin shagwaɓa tai maganar,Yace”Ina guest house ɗina”
Aneesa tai dariya sannan ta kashe wayar.
Haka taci gaba da tuƙin har ta isa wata unguwa ta masu kuɗi,unguwar bata da hayaniya haka ma gidajan dake cikinta ba su da yawa sai ɗai ɗai ku.
Wani gida mai green ɗin get ta nufa kafin ta shiga bugawa mai gadi horn,da sauri mai gadin ya ta so ya buɗe mata ta cinna hancin motar ta zuwa cikin harabar gidan.
Bayan ta gama paking ta cire after ɗin a cikin mota ta ajiye sannan ta fito ta nufi cikin gidan kai tsaye,tana isa jikin ƙofar ta danna abin dannawa (ƙararrawa)
Yana zaune daga shi sai farar singlet da dogon wando na yadi fari,jin an dana ƙararrawar shigowa ya sa ya miƙe ya isa ga ƙofar domin ya san itace.
Buɗewa ya yi lokacin da yai arba da ita da kuma shigar dake jikinta take fuskar sa ta cika da fara’a,janyota yai ya manna da jikin sa sannan ya kulle ƙofar.
Ba su bar bakin ƙofar ba ya shiga kissing ɗin bakinta mai kama da lawar minti.
Cikin kasalalliyar murya Aneesa Tace”Sorry Dear mu ƙarasa ciki”
Ba musu ya jata suka isa ga kan ɗaya daga kujerun dake falon ya zaunar da ita akan cinyar sa fuskokin su na fuskantar juna.
“Baby naga kin ƙara kyau yau ɗaya?”
Ya faɗa yana ƙoƙarin ɗage mata ƴar mitsitsiyar rigar jikinta sama take manyan breast ɗinta masu matuƙar kyau da ɗaukan hankali su ka bayyana.
Aneesa Tace”To ba dole na ƙara kyai ba ina tare da kyakykyawa”
Su kai murmushi gaba ɗaya.
Nan ya fara sarrafa breast ɗinta cike da kwarewa domin ya san sunnar sarrafa su domin yana mutuƙar ƙaunar su sosai.
Haka ya cigaba da sarrafawar kafin su canza salon zuwa wani salon.
*Wannan kenan*
*Idan an comments da sharhi na cigaba*
[08/10, 7:51 am] +234 706 345 2697: *ANEESHA KO ANEESA*
*🌺🌺🌺⭐⭐⭐☀☀☀🌺🌺🌺*
*Zan dinga amfani da waɗannan flowers da sters ɗin da kunga novels da haka to Indian Girl ce nagode*
*Aƙalamin*
*Zainab Muhammad (Indian Girl)*
*Ga wani sabon salo mai rikitarwa soyayya ce tsagwaranta cin amana da sauran su ku dai kawai ku biyo ni muje zuwa*
*Littafin kuɗi ne gama son biyan nata kuɗin kafin na gama bunus tai min magana ta wannan number 07063452697*
*Sai kun zo*
*Bunus page 3*
*___________________________________________________* Zaune su ke a falo dukan su amma banda Daddyn su wanda ya tafi office,nan Tahariq ya fitowa da kowa tsarabar sa ya ba Mammy nata sannan ya turawa Aneesha akwati mai ɗan girma.
Yace”My Sweet Sis gashinan ku raba ke da Little”
Aneesha da murmushi a fuskarta cike da jin daɗi,Tace”Lah! Ya Tahariq duk mu kaɗai? Kai amma mun gode”
Murmushi shima Tahariq ya yi sannan,Yace”To Sweet Sis ai ba yawa dan ma tafiyar ce da kowa akwatin sa zan ma sa”
“Mtssssssa!”
Aneesa taja tsaki.
Da sauri duk su ka bita da kallo,kafin Mammy Tace”Aneesa lafiya me yake samunki?”
Tahariq Yace”Nima tambayar da zan mata kenan”
Ita kuwa Aneesha baiwar Allah kawai kallon Aneesan ta yi.
Cikin nuna damuwa Aneesa Tace”Yanzu sabida Allah ya za ai ace komai wai Ya Aneesha za a ɗora akai ni kenan ban da amfani?”
“Baki da tun da Aneeshan sa’ar kice duk da kun kasance twins amma kin san ta riga ki shaƙar iskar duniya”
Mammy ta faɗa cikin ɓacin rai dan halayan Aneesan ta fara bata haushi.
Tahariq Yace”Haba Little kin san fa itace babba dan haka komai ita za a fara ɗorawa kafin ke”
Miƙewa Aneesa tai fuuu kamar iska ta haye sama tana surutai.
Aneesha kuwa sauke ajiyar zuciya ta yi tare da dafe kanta,wai da ita Aneesa ke kishi? Allah ya kyauta.
Mammy ta lura da yana yin Aneesha ya sauya domin ta san ta da damuwa,cikin kwantar da hankali.
Tace”Kar ki damu da abinda tai kinji domin inda sabo ya ci a ce kin sa ba”
Aneesha ba tai magana ba sai wasu siraran hawaye da su ka biyo kumatunta.
Tahariq ya ji zafin hawayen nata har ran sa,cikin lallashi ya fara.
Cewa”Haba My Sweet Sis mene kuma na kukan,kin manta da idan mu kai waya kike cewa Aneesa rayuwar ki ce kina matuƙar son ta duk abinda take so kina so wanda bata so bakya so”
Datiya Aneesha tai domin bata manta da hakan ba dan yana zuciyarta.
Tahariq shima yai dariyar,Yace”Ko ke fa ai kin fi daɗa kyau idan ki kai murmushi ko dariya”
Mammy itama dariyar tai domin tana son taga ƴaƴan nata cikin farin ciki.
Miƴewa Aneesha ta yi tana jan akwatin da kyar,Tace”Bari naje mu raba domin wallahi na ƙagara naga mene a ciki”
Su Mammy su kai mata dariya sannan taja akwatin ta hayr sama zuwa ɗakin Aneesa.
*••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••*
Haɗaɗɗan gida ne mai tsananin kyau da girma da ganin sa ka san naira tai kuka domin sai kai tafiyar awa nawa baka zo ƙarshen gidan ba,komai na gidan a tsare yake abin sha’awa.
Haɗaɗɗan babban falon gidan wanda ke ɗauke manyan kaya na alatu masu tsada a ciki.
Zaune su ke a misalin 10:00am na safiyar a sabar zaune a ƙawataccan wajan cin abincin wanda ya gaji da tsaruwa.
Meema and Dad and Mom sai ƴaƴan su Salima and twins Abeed da Abeeda.
Kowa gabansa abinda yake buƙatar ci ne suna break fast.
Dad ya dubi Salima Yace”Ɗiyar Dad a ina kike son a samo maki aiki?”
Salima ta yi farr da ido tana tunanin wane gari zata zaɓa.
Sai Tace”Ni dai gaskiya Dad a kano nake son a samon lecturing a wata universityn”
Dad yai murmushi sannan,Yace”Amma kina ganin da abuja da kano bai nisa ba”
“No Dad bai ba can nake da sha’awar yi”
Salima ta faɗa.
Dad Yace”Ok tam shikenan an gama ɗiyar Dad”
Meema Tace”Au yanzu Salima kin fi so ki tafi ki bar mu?”
Dariya Salima tayi,sannan Tace”Wallahi Meema garin ne ina son sa shi ya sa amma ai ma dinga ganin juna a waya kafin ranar wutu”
Mom Tace”Rabu da ita Meema kin ji muma bama ra’ayin zaman nata tun da itama bata son zama damu”
“A’a fa Mom ba wai haka take nufi ba aiki ne ai zai kai ta,ko ɗiyar Meema”
Meema tai maganar tana kallon Salima.
Salima Tace”Yes! Meema na faɗawa Mom dai”
Haka dai su ka dinga fira cike da jin daɗi da farin ciki.
Bayan sun gama yin break ɗin ne Dad ya miƙe yana saka wayar sa a aljihu,Yace”Wai Meema har yanzu Jalal ba fito ba ko lafiya”
Kafin Meema tai magana sai ga wani kyakykyawan matashin saurayi ɗan kimanin shekaru 34 fari mai kyau kimai na sa ma mai kyau,tafiyarsa yana yin sa komai.
Yana ƙarasowa inda iyayen nasa suke ya gaida su sannan Salima da sauran ƴan uwanta su ka gai da shi,baya da son magana dan haka cikin ƙasa ƙasa da murya ya amsa.
Dad Yace”Jalal mene ya hana ka fitowa a yi breakfast da kai?”
Jalal ya ɗan sosa kai,sannan.
Yace”Wallahi Dad tun da na dawo daga masallaci sallar asuba na kwanta shine ban tashi da wuri ba”
Dad Yace”Ok shi yasa to ni bari na wuce office sai na dawo”
Ya faɗa yana kallon matan na sa.
Su kai ma sa fatan alkairi sannan ya fice.
Shi kuwa Jalal wajan cin abincin ya nufa ya shiga bubbuɗawa tea kawai ya haɗa ya sha sannan yaci ɗan farfesu na kayan ciki kaɗan,bayan ya gama ya miƴe zai fice.
“Abdul”
Yaji muryar mahaifiyar sa ta faɗi sunan domin ita ka ɗai ke kiran sa da Abdul.
A hankali ya isa gabanta tare da durƙusawa,Yace”Meema gani”
Meema Tace”Yanzu ina za ka idan ka fita?”
Cikin muryar sa na rashin son magana,Yace”Meema kamfani zan je tukun”
Merma Tace”Ok tam sai ka dawo”
“Am Merma aike ne ki faɗi abinda zan miki?”
Jalal ya faɗa kan sa a ƙasa.
Meema tai murmushi,sannan Tace”A’a Abdul ka tashi kaje ma yi waya kawai”
Jalal bai sake magana ba domin ya san Meema bata son idan tace abu a yi jayayya.
Ya miƴe su kai masa a dawo lafiya sannan ya fice.
Nan su kuma su ka zauna a falon su na hira,ita kuma Salima ta miƙe ta haye sama zuwa ɗakinta.
Fitar Abdul Jalal ke da wuya daga falon yaje ya hau motarsa ya fice zuwa ma’aikatar su,bayan ya isa ma’aikatar ya fito cikin tafiyar sa mai jan hankali ya nufi cikin ma’aikatar.
Take hankulan mata da mazan dake campanyn hankalin su da kallon su ya dawo gare shi duk inda ya wuce su na miƙo masa gaisuwa,amma shi Jalal bai san ma suna yi ba.
Office ɗin Dad ya nufa ya gaishe shi sannan ya nufi na sa office ɗin ya zauna akan kujerar sa ta zama kan tebur ɗin kuwa tulin takar du ne birjin su na jiran sa.
Ko hutawa bai yi ba ya fara duddubawa yana cike wa.
Yana cikin aikin ne sakatariyar sa tai knock ya bata damar shigowa,bayan ta shigo.
Tace”Sir kayi baƙo”
Jalal bai ɗago kai ya kalleta ba,Yace”Wane?”
Sakatariya Tace”Yace a ce maka Ashman ne”
Duk da kan sa na ga takardun sai da murmushi ya subce ma sa jin abokin sa kuma ɗan uwan sa ya kawo masa ziyara daga kano,Ashman ɗan yayar Meema ne uwa ɗaya uba ɗaya wato mahaifiyar Jalal.
Yace”Ok kice ya shigo”
“Ok sir”
Sakatariyar ta faɗa sannan ta fice daga office ɗin.
Fitar ta ke da wuya sai ga shi wani haɗaɗɗan guy ya shigo wanda na tabbata shine Ashman ɗan,wow na furta domin ganin tsananin kyansa tamkar ɗab ruwa komai masha Allah.
Tun kan ya ƙarasa shigowa Jalal ya miƙe ya isa gare shi su ka rungume juna na ɗan mintuna sanna su ka saki kowa ya sami kujera ya zauna.
“My Bro your welcome to my visit”
Jalal ya faɗa yana murmushi.
Ahsman shima murmushin yai,kafin Yace”Ai na kusa yin fushi domin kai baka ziyara”
Jalal Yace”Sorry My Bro wallahi aiyuka ne sun yi yawa sai a slow”
Ashman ya ɗan harari Jalal cikin sigar wasa,sannan Yace”Ba wani nan amma tun da haka ka ce shikenan”
Jalal Yace”Ba wannan ba ma wai yaushe ka shigo garin ne amma dai tafiyar asuba kai yo?”
Ashman yai dariya Yace”Ah haba da safe na tawo wajan ƙarfen 7 shi yasa yanzu kuwa ai ƙarfe 10:30am ne kaga awa uku da rabi kenan nai”
Jalal Yace”Cabb gaskiya kai sauri ko da yake tuƙin ka kamar za atashi sama ai ba mamaki”
Ashman ya kalli Jalal,Yace”Ban ganr ba me kake nufi kana nufin aljanu gare ni ko me?”
Jalal yana dariya Yace”Ah ni ba haka nake nufi ba bro”
Haka dai su kaita hira dake sun shaƙu sosai daga ƙarshen ma tashi Jalal yai daga aikin su ka tafi gida.
Lokacin da su ka isa gidan Mom bata nan sai Meema dake ɗakinta yara kuma sun tafi makaranta Salima kuwa na ɗakinta,ɗakin Meema su ka shiga dan Jalal ya gaisheta.
Lokacin da su ka shiga ɗakin Meema tana zaune gaban wardrob tana gyaran kayanta da aka wanko,da sallama a bakin su su ka ƙarasa.
Amsa sallamar ta yi tare da miƴewa cike da farin cikin ganin Ashman,Tace”A’a’a Ashman kai ne yau a gidan namu barka da zuwa”
Murmushi ɗauke akan fuskar Ashman,Yace”Eh wallahi Meema ina kwana”
Meema ta amsa da,”Lafiya ƙalau Ashman ya su Mommyn naka”
Ashman Yace”Suna lafiya ƙalau su na gaishe ki”
Meema Tace”To masha Allah muna amsawa”
Bayan sun gama gaisawar su ka koma falo.
Waya Jalal yai wa Salima na yana son ganinta a falon ƙasa,ba a wani jima ba da wayar sai gata ta sauko sanye take cikin doguwar riga ta atamfa ta saka hijab akai milk iya gwiwa.
Tana ƙarasowa in da su ke ta gaishe su domin ta san Ashman dan yana yawan kawo ma su ziyara,bayan sun gaisa ɗin ne ta dubi yayan nata.
Tace”Ya Jalal gani”
Ba tare da ya kalleta ba,Yace”Ki kawo wa Ashman abin break domin yanzu ya zo”
Salima ta amsa da to sannan ta miƴe ta nufi kitchen.
Bayan tafiyarta ne wayar Ashman ɗin ta shiga ruri ya ɗauka ganin Mommyn sa ce ya ɗaga da murmushi a fuskar sa.
Daga can ɓangaran Mommyn Tace”Ash ina ka tafi ne na aika ɗakin ka an ce baka nan,amma jiki na ya na bani kana abuja”
Ashman yai dariya sannan,Yace”Wallahi kwa Mommy ina can”
Mommy cikin nuna kulawa Tace”To amma mene ya sa ka tafi baka faɗawa kowa ba?”
“Sorry Mommyna wallahi kawai yau tashi nai da son zuwa ganin ɗan uwa na duk da shi bai ma damu da ni ba”
Ashman ya faɗa yana kallon Jalal,shi kwa Jalal ya harare shi.
Salima da ta iso wajan ɗauke da tre a hannunta ta ɗora kan table ɗin da ke gaban su na falo sannan ta koma ɗaki.
Mimmy Tace”A’a Ash kar kaiwa ɗana sharri fa”
Kafin Ashman yai magana tuni Jalal ya amshi wayar,gaida Mommy ya yi sannan Mommyn.
Tace”Ɗana wai hakane abinda Ash ya faɗa”
Jalal Yace”No Mommy kyale shi ɗan rai nin hankali ne”
Mommy tai murmushi Tace”Nikwa ai dama na sani”
Haka dai su ka ɗan taɓa hira da Mommy da Jalal ɗin,duk da Jalal baya son yawan yin magana amma idan da familyn sa ne kamar ba shi ba.
Bayan ya kashe wayar Ashman yai break ɗin sannan su ka fice zaga gari.
[08/10, 7:53 am] +234 706 345 2697: *ANEESHA KO ANEESA*
*🌺🌺🌺⭐⭐⭐☀☀☀🌺🌺🌺*
*Zan dinga amfani da waɗannan flowers da sters ɗin da kunga novels da haka to Indian Girl ce nagode*
*Aƙalamin*
*Zainab Muhammad (Indin Girl)*
*Ga wani sabon salo mai rikitarwa soyayya ce tsagwaranta cin amana da sauran su ku dai kawai ku biyo ni muje zuwa*
*Littafin kuɗi ne game son biyan nata kuɗin kafin na gama bunus tai min magana ta wannan number 07063452697*
*Sai kun zo*
*Bunus page 4*
*_____________________________________________________________* “Assalamu alaikum!”
Aneesha ta faɗa lokacin da ta shiga ɗakin Aneesa.
Aneesa dake kwance akan gadonta tayi ruf da ciki ta rungume filo ko kallon in da Aneesha take ba tai ba.
Aneesha bata damu da rashin amsa sallamarta da Aneesa tai ba ta nemi bakin gadon ta zauna,sannan.
Tace”Sisi na ki tashi ga kayan nan mu raba kin ji”
Aneesa tai mata shiru bata ce komai ba.
Aneesha ta sake cewa idonta na kawo kwallah domin bata ƙaunar taga ƴar uwar tata a damuwa.
“Kiwa girman Allah Sisi ki tashi a raba ki duba ki ga fa biyo ki nai”
Aneesa da itama hawayen su ka fara ƙoƙarin zubowa daga idanunta,Tace”Shikenan”
Ta ƙarasa faɗar hakan tana tashi zaune.
Murmushi Aneesha ta sakar mata itama ta mayar mata.
Haka su ka shiga duba kaya cikin farin ciki kamar ba Aneesa dake fushi ba,nan Aneesa ta zaɓe duka kayan tabar Aneesha da tarkace.
Amma ita Aneesha bata damu ba ko a jikinta ta ɗebi nata ta fice zuwa ɗakinta dan ta shirya zata tafi majaranta.
Fitar Aneesha ke da wuya Aneesa tai murmushi tare da furta ‘ina matuƙar ƙaunarki ƴar uwata amma ban san kalar zuciyata ba’.
Aneesha tana shiga ɗaki wanka ta shiga bayan ta fito bata wani yi make-up ba ta shafa mai da farar hoda sai man leɓe amma tayi matuƙar kyau abinka da kyakykyawa,sannan ta ɗauko atamfa mai kyau riga da zani ta saka kayan sun matuƙar yi mata kyau sosai da sosai.
Hijab ta saka zumbulele har asa sannan ta saka takalmi kalar hijab ɗin ta ɗauki wayarta da jakarta wadda kayan karatunta ke ciki ta fito zuwa falo.
Ganin Mammy ta bar falon ya sa ta bita tai mata sai ta dawo,Mammy ta bata kuɗi sannan ta fice.
Tana ƙoƙarin shiga mota taji muryar yayanta,taja ta tsaya tana jiran ƙarasowar sa inda take.
Yana ƙarasowa Yace”My Sweet Sis ina zuwa haka kike sauri?”
Ɗan ya tsina fuska Aneesha tayi wanda hakan ba ƙaramin kyau ya ƙara mata ba.
Tace”Wallahi makaranta zani muna da lecture na ƙarfe 1:00pm”
Tahariq ya yarfa hannu baya sannan,Yace”Ok bari na kaiki domin tun da na dawo ban wani yawo ba”
Dariya Aneesha tayi da,Cewa”Ok tam muje”
Suka shiga motar ya ja mai gadi ya buɗe masa get ya fice.
Suna tafe su na hira har su ka isa makarantar yai paking motar.
Aneesha ta ɗauki wayarta da jakarta kafin ta kalli yayan nata,Tace”To Ya Tahariq nagode sosai”
Ya ɗora hannun sa akan laɓɓan sa,kafin.
Yace”Kar na sake ji kin min godiya nifa yayanki ne”
“Sorry Ya bari na shiga”
Aneesha ta faɗa cikin muryar ban haƙuri.
Tahariq Yace”Ok tom shikenan idan an tashe ku ki kira ni na zo na ɗauke ki”
Aneesha ta amsa da to sannan ta fice,sai da taga ficewar motar yayan nata daga makarantar sannan ta nufi department ɗin su.
Tana dosar class ɗin da su ke ɗaukan lectures taja ta tsaya tana addu’oin eman tsari da nasarori,tana tsaye tana addu’oin ne malamin daya hanata shiga class ya zo zai shiga ajin.
Ɗan jim ya yi yana kallon ta kafin ya shiga ajin.
Taɓe baki Aneesha tayi bayan ta kammala addu’oin,sannan ta koma can gefe ta zauna tana nazarin wani littafi.
Ko da malamin ya shiga ajin sai yaji ya kasa samun nutsuwar da zai wa ƴan class ɗin karatu gashi yau babu masifa,har ya fara rubutu akan allon dake ajin sai kuma ya juyo kafin.
Yace”Am wai ya sunan wannan yarinyar ta ran nan dana kora?”
Farisa cike da jin haushin sa dan tun ran da yaiwa ƙawar tata wannan cin mutuncin ta ƙara tsanar shi.
“Aneesha Bashir”
Abinda kawai Farisa tace kenan taja bakin ta ta tsuke.
‘Aneesha! Aneesha!! Aneesha!!!’
Ya shiga mai maita sunan a zuciyarsa sunan mai daɗi haka ma mai sunan,sai ya tuna ranar data faɗi sunan da bakinta da muryarta mai daɗi.
“Tashi kije kice ta shigo”
Ya faɗa yana kallon Farisa.
A hankali Farisa ta miƴe ta fice,can ta hango Aneesha tana karatu ta ƴarasa tare da mata sallama.
Amsawa Aneesha tai jin muryar ƙawarta.
“Yane Fari naga kin fito ko kema ya kore kin?”
Aneesha ta faɗa tana kallon fuskar Farisa.
Farisa Tace”A’a ba koroni yai ba cewa yai wai nace ki shigo”
Aneesha cike da mamaki,Tace”Me? cabɗi da bakin sa”
Farisa Tace”Wallahi haka yace”
Aneesha ta jinjina kai cike da mamaki.
Fatisa ganin Aneesha bata da halin tashin yasa,Tace”Tashi muje mana”
Girgiza kai Aneesha tai hawaye na zubo mata sakamakon tunawa da waccan ranar daya zageta yanzu bata san me zai faru ba.
Tace”Gaskiya Fari bazan shiga ba na haƙura in dai lecture ɗin sa ce”
Tana gama faɗar haka ta tattara wayarta da littafanta ta zuba a jaka zata bar wajan.
Farisa bata iya cewa komai ba dan itama gaskiya ko itace ba zata iya haƙura ba balle ma Aneesha dake da haƙuri har gashi ta kawo wuya,har Aneesha ta ƙule sannan Farisa ta iya jan ƙafa ta koma class ɗin.
Kafin ta ƙarasa shiga tuni malamin ya jeho mata tambaya,”Ina take naga baku shigo tare ba?”
Kan Farisa a ƙasa Tace”Ban ganta ba kuma na dudduba”
Bai ce komai ba Farisa ta sami waje ta zauna.
Ba tare da malamin ya gama karatun ba ,Yace”Idan ta shigo kuce mata ta zo office ina nemanta”
Bai jira amsar su ba ya fice.
Fitar sa ke da wuya class ya ruɗe da wai gaskiya malamin ya ƙure Aneesha tun da raƙi dawo wa duk haƙurin ta.
Itakwa ɓangaran Aneesha inda ta saba zuwa ta tafi wato lambu,kamar yadda ta saba jin sautin wannan muryar yau ma haka taji ba tare da taga kowa ba.
Wannan shine yake bata tsoro take barin wajan ba tare da ta shirya ba.
Class ɗin ta koma sallama kawai tai musu ta nemi sit ɗin su da su ke zama ta zauna.
Zamanta ke da wuya ƴan aji suka shiga faɗa mata saƙon malamin,kallon su kawai Aneesha ta shiga yi ba tare da tace komai ba.
**** ****
Wayace maƙale a kunnan sa.
“Hello Baby yau ba zaki shigo school bane?”
Aneesa dake kwance yadda take tun fitar Aneesha ta ɗan muskuta kwanciyar,sannan.
“Gaskiya ban jin zan iya zuwa domin kai na ke ɗan min ciwo”
Yace”Ok dan kan ki yana ɗan maki ciwo shine ba zaki shigo ba?”
“Haba Haisam mai ya sa baka da haƙuri ne dan Allah”
Ta faɗa a ɗan raunane domin ta san bai son fushi ko faɗa.
“That good,im no problem”
Yana faɗar haka ya kashe wayar.
Itama Aneesa cilli tai da wayar can nesa da ita akan gadon.
“Baka uzuri kai sai dai ai maka,kuma wallahi ba zan zo ba”
Haka ta faɗa kafin ta miƙe ta fita falo dan samin abinda za taci.
Mammy dake falon ko kollon Aneesa ba tai ba lokacin data fito har ta isa wajan cin abincin.
Zama tai ta zu ba abinda zata iya ci sannan ta fara ci cikie da nutsuwa.
********** ************
Sai ƙarfe 4:30pm su Aneesha su ka tashi daga lectures ɗin su,sai da kowa ya ɗaɗe sannan su ka fito ita da Farisa bayan taiwa yayanta waya.
Suna tafe suna hira har su ka iso bakin get tsayawa su kai su na jiran ƙarasowar Ya Tahariq.
“Baby a she kina school ɗin na kira ki kikai min wulaƙanci?”
Su Aneesha su ka ji sau kan maganan a kunnuwan su ya yin da su ka ga mutum a gaban su.
Ganin ba wacce tai magana yasa ya kuma magana cikin zafi.
“Ok dan kin gan ki da ƙawarki shine zaki dizgani? Ok ba damuwa”
Farisa ta kalli Aneesha kafin itama Aneeshan ta kalleta suna tambayar juna lafiya.
Farisa Tace”Wai kam wannan dawa ya ke?”
Aneesha tai alamar oho sai dai in dake yake.
Ganin duk daga haka ta nuna ita ba ma ta san shi ba yasa yaji zafi a ransa ya juya zai bar wajan,a dai dai nan motar Ya Tahariq ta iso wajan babu wata wata su ka shi.
A zafafe shima ya ƙarasa ga tasa motar ya shiga ya bar wajan.
Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta zauna.
“Yane My Sweet Sis kin gaji da jira na ko?”
Tahariq ya faɗa yana kallonta ta mudubin gaban motar.
Aneesha ta ɗan ya tsina fuska sannan.
Tace”Wallahi a a Ya Tahariq kawai dai jina nake na gaji”
Taariq cike da kulawa Yace”Wayyo sorry yanzu zamu i sa gida kin ji?”
Aneesha ta ɗaga kai alamar to.
“Ya sunan ɗaya ƙanwar tawa?”
Tahariq ya faɗa yana sai ta motar akan kwalta,sannan ya lura da kallon da take masa tun shigowar su motar.
Cikin jin kunya da sauri Farisa tai ƙasa da kanta,kafin.
Tace”Ya Tahariq barka da wannan lokaci”
Ta faɗa kamar yadda taji Aneesha ta faɗa.
“Lafiya ƙalau,your name fa?”
Ya faɗa tare da tambaya a ƙarshe.
“Sunana Farisa”
Ta faɗa kanta na a ƙasa.
Ya jinjina kai ba tare da yai magana ba.
Haka ta cigaba da tuƙin sa har su ka sauke Fsrisa tai godiya sannan su ka ƙarasa gida.
****
“Ni ni banje school yau ba”
Yace”Kar fa ki rainan hankali malama na ganki da wata ki share ni sannan wani ya zo da mota ya ɗauke ki”
Dafe kai Aneesa tai domin gayan ya fara ƙoƴarin sa mata ciwon kai.
Tace”Na rantse maka da…”
Sai kuma ta fasa ƙarasawa sakamakon tunawa da tai ai Aneesha taje yanzu haka ita ya gani,yes itace ma hakan kuma yai min dan bana son a san cewa mu biyu ne.
Ta faɗa a ranta tana murmushi.
“Sorry dear wasa ne fa nake maka”
Ta faɗa cike da kwarin gwiwa.
“Wasa ta wannan hanyar?”
Ya tambayeta.
Aneesa Tace”To mene dan anyi irin wannan wasan tsakanin masoya?”
Yace”Babu,amma…”
“Amma kayi shiru kawai mu yi wani hiran”
Aneesa ta faɗa dan kawar da zan cen tambayoyin da yake mata.
Haka ya bar zan cen su ka shiga hirar su mai daɗi.
*******************************************
Wanka ya shiga a gurguje ya yi ya fito ya shirya cikin ɗaya daga cikin kayan Jalal domin suna yin hakan.
Shi kuwa Jalal yana zaune bakin gado ya ɗan kashin giɗs ƙafarsa ɗaya akan gadon ɗaya a ƙasan,hankalin sa da idanun na kan waya.
“Wai kai ina zuwa kake ta wani ƙaƙale ƙaƙale?”
Jalal yai tambayar ba tare da nuna alamun shine yai maganar ba.
Shima Ashman dake ɗaure igiyar takalmi.
Yace”Aiken da kai min zan tafi”
Jalal bai kalle shi ba ya kyaɓe baki,Yace”Oh!”
Ba wanda ya sake magana har Ashman ya gama shiri.
“To malam a tashi a rakani”
Yai maganar hannuwan sa duka a cikin aljihun wando.
Miƙewa Jalal yai yana saka wayar sa a aljihu sannan.
Yace”Muje kaiwa Meema sallama daga nan kuma shuuuuu!”
Ya ƴarasa maganar yana alamar shuu da hannun sa.
Ashman bai magana ba suka fice daga ɗakin,ɗakin Meema suka nufa yai mata sallama sannan su ka fice.
Jalal na tsaye Ashman ya shige mota,sannan ya leƴo da kai.
Yace”Sai yau she kuma guy?”
Harara Jalal ya watsa masa da,Cewa”Zan zo gaida su Mommy da Abba banda kai”
Ashman ya taɓe baki wanda hakan kamar duk a jinin su ne.
Yace”To so what dan ba ka zo dan ni ba?”
“Kai ka jiyo,dallah malam ja mota ka tafi kar dare yai ma”
Jalal ya faɗa yana daɗa gyara tsaiwar sa.
Haka Ashman yaja motar ya bar gidan suna ɗagawajuna hannu har ya ƙule sannan Jalal ya koma cikin gida.
*Comments and Sharhi*
[08/10, 7:54 am] +234 706 345 2697: *ANEESHA KO ANEESA*
*🌺🌺🌺⭐⭐⭐☀☀☀🌺🌺🌺*
*Zan dinga amfani da waɗannan flowers da sters ɗin da kunga novels da haka to Indian Girl ce nagode*
*Aƙalamin*
*Zainab Muhammad (Indian Girl)*
*Ga wani sabon salo mai rikitarwa soyayya ce tsagwaranta cin amana da sauran su ku dai kawai ku biyo ni muje zuwa*
*Littafin kuɗi ne game son biyan nata kuɗin kafin na gama bunus tai min magana ta wannan number 07063452697*
*Sai kun zo*
*5*
*_____________________________________________________* Sai yamma lis ya isa kano,ana kiran sallar magriba yai paking a harabar ajiye motoci dake gidan su.
Bayan ya gama paking ya nufi gidan kai tsaye alamun sa babu wani gajiya daje ya saba da tafiya irin wannan.
Mommy na zaune a falo tasha kwalliya cikin lass mai matuƙrar kyau da tsada,kallo take gabanta kuma akan ɗan ƙaramin table ɗin dake tsakiyar falon juice ne ɗan haɗi na kwakwa sai ƙamshin daɗi yake ta zu ba wani a ɗan aramin cup na glass da alama sha tai ta ajiye.
Dake akwai spears na mukullan gidan ya sa Mommy bata ji shigowar Ashman ba sai huge ɗinta data ji ya yi ta baya yana faɗar.
“Missing you my dear Mom”
Mommy ta juya ta kalleshi kafin cikin so da ƙauna ta harare shi.
Tace”Nima nayi missing naka Son,to amma wai yaushe za ka girma ne?”
“Sai ranar da kika aurar da shi”
Su ka jiyo muryar wata dattijuwa daga baya tana faɗar haka,dan haka duk su ka juya suna kallonta.
Dattijuwar tsohuwace fara mai kyau da haƙorin maka taci ado da atamfa da alama kakar su Ashman ɗin ce,ta ƙaraso ta sami kujera ta zauna kafin taci gaba da sababi.
“A ce dan masifa da bala’i kullum zangamemen ƙato an mai da shi tamkar ɗan goye ya yi aure yaƙi sai kullum ya zauna a gida yana kallo na to ni nafi ƙarfinka miji na dan shi ka ɗai a kaiwa ni”
Gaba ɗaya dariya matar ta ba su jin maganar ta ta ƙarshe data faɗa.
Ashman ya galla mata harara sannan.
Yace”Ke dilla rufe mana wannan dagajejen bakin naki duk goro ya kashe,tsohuwa dake duk kin ya kushe me zan kalla a hakama haƙuri nake dan in na ganki kamar zan amai”
Ai zabura Kaka tayi tare da zazzaro ido waje.
Tace”Ashamanu nice kake kallo kamar kayi amai,wayyo Allah ni Hadhiza na shiga uku Aliyu ka zo kaji bayanka abinda yake faɗi”
Ashman ya galla mata harara,kafin
Yace”Kar ki kuma ɓatan sunan ki shiru idan baki iya ba idan ba haka ba wallahi zan daki bakin ki haƙoran robar su cire”
“Wayyo Allah yaron nan mai sunan ƴan iska ya kashe ni wayyo baki na shikenan ya na kasa ni ya zaunar dani ya cire min baki jini jini!”
Kaka ta faɗa cikin kururuwa.
Ashman ganin tana ƙoƙarin yin sharri yasa ya nufe ta haiƙan wai bari ma yai mata da gaske sai tace an matan.
Da sauri Mommy ta miƙe tare da hana shi.
Tace”Kai shige ka tafi ɓangaranka kaje kai wanka ka huta kar na sake jin bakin ka”
Ashman bai sake magana ba ya nufi hanyar ɓangaran sa yana hararar Kaka wadda har ga Allah ta tsorata ta dai dake ne dan ta san halin sa zai iya nufarta dan ya firgitata.
Ajiyar zuciya ta sauke ganin ya shige ɓangaran nasa,ta nemi waje ƙasan carfet ta zauna tare da mimmiƙe ƙafa.
“Kai amma wannan yaro uhum da halinka”
Kaka ta faɗa tare da ɓanlar goro a baki bayan data kwanto a zani.
Mommy bata kulata ba taci gaba da sabgar gabanta.
*Ashman prov*
Yana shiga ɓangaransa ya cire kayan jikinsa ya ɗaura towel ya shiga toilet dan ya ɗan watsa ruwa,yana shiga ya sakarwa kansa shower na ƴan mintuna kafin yau wankan ya fito yana tsane jikin sa da ɗan ƙaramin towel yellow mai taushi.
Bakin gado ya zauna yana cigaba da tsatstsane jikin nasa kafin daga bi sani ya miƙe ya nufi gabon mirror wanda aka ƙawata kan tebur ɗin gabansa da kayan amfanin maza masu kyau da tsada.
Shafe shafen mai ya ɗan yi sannan ya nufi wajan wardrobe wanda ke shaƙe da kaya kala kala masu kyau ɓangarare ɓangare,ɓangaran ƙananan kaya ya nufa ya ɗauki blue black t-shirt da jeans baƙi mai kyau.
Kayan sun matuƙar yi masa kyau abinka da kyakykyawa kuma wanda ya iya ado da ɗaukan wanka,komai daya saka ya sa ka ‘to much’ ne abin gwanin sha’awa.
*(Ni kwa Zainab a raina nace shi kuma wannan baya gajiya daga dawowa ya kuma sabon shiri ko ina za shi oho😒😒?gulma fa na kawo muku😚😚)*
Wayarsa da mukullin motar sa ya ɗauka ya fice daga ɗakin tare da kullewa ya fice ta baya ba tare da ya sami sa’idon ƴar tsohuwa Kaka ba.
Motarsa ya shiga ya bata wuta ba jira mai gadi ya buɗe masa get ya fice.
Bayan ya harba motar kan kwalta yana tuƙi a nutse cikin kwanciyar hankali ya kunnawa sautin motarsa tsohuwar waƙar india ta ‘hy shona hy shona’ yana bin waƙar da rawar kanar shi ya yi cike da shauƙi.
****** ☀ *****
“Aneesha badan kina karatu ba dana ɗan aike ki nan baya gidan Hajiya Lami kin karɓon kaya zan siya”
Mammy ce ta faɗi haka lokacin data tsaya akan Aneesha dake zaune a kan gado hannunta ɗauke da littafi tana karartu dan gobe za su fara test.
Murmushi Aneesha ta yi,Tace”A’a Mammy bari na aje naje na dawo sai na cigaba”
Ta yunƙura tana ƙoƙarin saukowa daga saman gadon.
Mammy tai saurin dakatar da ita.
Tace”A’a kinga yi zamanki bari naje na tura Aneesa ita da na abinda take”
Aneesha bata son musu da nagana mai tsayi dan haka ta koma ta zauna taciga da karatunta ita kuma Mammy ta fice zuwa ɗakin Aneesa.
Ko da Mammy ta shiga ɗakin Aneesa a zaune ta sameta gaban mirror wanda hakan ya nuna daga wanka ta fito riga kawai ta zira ƴar kanti mai silbi.
Jin shigowa ɗakin bai sa ta juyo ba har Mammy ta isa gareta,bayanta ta dafa da murmushi a fuskarta.
Tace”Gaskiya ina sake yiwa ubangiji godiya a kullum kuma a ko da yaushe daya bani ƴaƴa kyawawa kamar ku masu albarka”
Aneesa tai farrr da ido jin kalmar kyau data fito daga bakin Mammynt.
Aneesa Tace”Ai Mammy ko da yaushe mutane suna yabawa da wannan kyan”
“A duk san da su ka ya ba ku ce tubarkalla masha Allah”
Mammy ta faɗa.
Aneesa Tace”Haka muke faɗa ai Mammy”
Mammy Tace”Yawwa,am Ameesa idn kin ƙasara shiryawa ki zo kije gidan Hajiya Lami ki karɓon kaya zan gani domin d safe za a fita da su”
“To Mammy ganinan”
Aneesa ta faɗa sannan Mammy ta fice zuwa falo.
Hijabi Aneesa ta ɗauka iya gwiwa ta saka sannan ta ɗauki wayarta tana duba lokaci 7:10pm ta fita zuwa wajan kiran Mammy.
Ko da taje cewa Mammy tai taje tace kawai ta bata saƴon.
Aneesa ta amsa sannan ta miƙe ta fice.
Tana tafe hankalinta na kan waya tana laluban number Haisam,da sauri ta ɗauke kai daga kallon wayar ta mayar ga motar dake gabanta wanda haskenta yasa bata ganin komai kuma da alama bigeta mai motar ya zo yi sanadin danna wayar data tafi tana yi.
Har wanda ke cikin motar ya fito ya tsaya a gabanta bata kula ba saboda hasken motar ga dare dan ma abinka da unguwar masu kuɗi kowanne gida da hasken inji.
“Wow! so beautyful girl!”
Kalmar data sa tai saurin kara hannunta dan ganin wanda wannan maganar ta fito daga bakin sa.
‘Masha Allah kyakyakyawane sosai gaskiya amma na fishi’
Aneesa ta faɗa a ranta dan zata yabi abu amma ba zata yar da abin ya fita ba.
Da kyar ta iya haɗa kalma ta faɗa dan ba ƙarya gayen ya tafi da tunaninta.
“Sorry ban kula da motar bane ina danna waya”.
Daga haka ta sauya hanya zata tafi.
Da sauri Ashman wanda ya daskare yana kallonta ya daɗa shan gabanta,kafin
Yace”Dan Allah ɗan tsaya kinji”
Aneesa duk rashin kunyarta kasa kallonsa tai.
Tace”To ina jinka mene?”
Sassanyan murmushi Ashman yai,sannan
Yace”Wallahi ina haɗa ido dake sai naji wata kibiya ta soki zuciyata”
“To me kenan?”
Aneesa ta faɗa duk da ta san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƴi.
Ashman cikin murya mai sace zuciyar duk wanda akaiwa.
Yace”Soyayyace mana,ina sonki!”
Take kirjin Aneesa ya buga ta shiga furta a zuciyarta ‘idan na amince da soyayyarsa zan caɓa amma kuma ai zuciyata tana ga Haisam ne’.
“Ba kice komai ba”
Ashman ya faɗa yana kallon fuskarta.
Cikin sanyin murya Aneesa.
Tace”Kayi haƙuri karatu nake bana soyayta”
Daga haka bata jira mai zai sa ke cewa ba tai tafiyarta.
Tsintar kansa yai da binta da kallo har ta ƙule,sannan da kyar ya iya shiga motarsa ya ƙarasa gidan su abokinsa wanda dama wajansa ya zo ya haɗu da ita,yana isa gidan kai tsaye ɗakin abokin nasa ya nufa.
Ɗakin da mutane 4 maza 2 mata 2 kowacce mace tana sanye da shiga wadda sai sai dai muce Allah ya gyara,kowa ƙoƙari take ta nunawa ƴfarantawa ga namijin da take tare da shi.
Shigowar Ashman yasa su ka ɗan tsaya daga abinda suke,hankalin ƴan matan ya koma kan su.
Kujera Ashman ya nema ya zauna tare da dafe kansa tunanin Aneesa wadda ko sunanta bai tambaya ba yana cizon zuciyarsa.
“Ah wai mutumina yane naga ka shigo wani iri kuma kaƙi magana ka zauna kawai?”
Ashman yaji muryar abokinsa yana faɗa lokacin daya dafa kafaɗarsa.
Ashman ya ɗaga kai ya kalle shi sannan ya sauke ajiyar zuciya.
Yace”Wallahi wata yarinya nagani a layin nan kyakykyawa sosai kamar aljana har munyi magana”
“To tana ina?”
Abokin Ashman ya faɗi haka.
“Ta tafi kuma ma ban tambayi sunanta ba ta tafi”
Ashman ya faɗa ba tare daya kalli abokin nasa ba.
Abokin Yace”Ok ba muhimmanci kaga kawai ka manta da ita kaji”
A hankali Ashman ya ɗaga kai ya kalli abokin na sa,sannan
Yace”Kai wannan fa ta dabance ba wadda za a manta bace”
Jin haka yasa abokin ya zauna kusa da shi sannan cikin rarrashi.
Yace”Na fahimta kaga yanzu kai rayuwarka kaji daɗinka idan ya so zuwa gobe sai mu nemeta muga ko za mu ganta”
Duk yadda abokin na sa mai suna Haisam zai ya kwantar masa da hankali ya yi kuma ya samu nutsuwa.
*(Naji ance Haisam😳uhm amma bari dai nai shiru kar ace na fiye surutu😗)*
“Bari na tashi na wuce gida”
Ashman ya faɗa yana miƙewa.
Haisam Yace”A’a tun yan zu kuma?”
Ɗaga masa gira Ash ya yi kawai ya fice daga ɗakin,yau jin haushin ƴan matan yake ban da wadda ya gani kawai.
*Aneesa prov*
A gurguje taje gidan Hajiya Lami ta karɓo kayan ta koma gida.
*Ashman prov*
Kaka ta kasa ta tsare sai taga shigowar Ash ko da zai kai 1 dare ne duk da a sannan ƙarfe 8:00pm.
Duk kowa ya tafi ɗakin sa amma ita taja tunga a falo,har Abba yai fama taƙi yai rafiyarsa.
Ƙarfe 8:12pm Ash ya shiga cikin falon ya ga Kaka amma kota kanta bai bi ba ya shige ɓangaransa.
Ganin dare bai wani yi ba ya shigo ya sa ta taɓe baki ta miƙe ta shige ɗakinta ta kwanta.
*_________________________________________________________*
Yau tun bayan da Aneesha tai sallar asuba tajita cikin farin ciki kai tsaye ta nufi kitchen domin ɗora break fast,haka ta dinga aiki cike da nishaɗi har ta gama.
Ɗaki ta koma tai wanka tai shirinta cikin riga da siket na atamfa ɗinkin yai matuƙar yin kyau ajikinta,haka ta gama shirinta tsaf na tafiya makaranta ta fice zuwa ɗakin Mammy.
Mammy dake shigowarta ɗakin kenan,tana gyaran ɗakin Aneesha ta shigo.
Sallama tai Mammy ta amsa sannan ta gaida Mammy.
Mammy tana gyara saituwar zaman zanin gado.
Tace”Au wai Aneesha yau da wuri zaki tafi ne?”
Aneesha Tace”Eh wallahi Mammy test za mu fara ne”
Mammy Tace”Ah to Allah ya taimaka,amma ki tsaya ki break fast idan ma zaki tafi da shi to”
Aneesha ta amsa da to,sannan ta juya zata fita.
Mammy ta dakatar da ita ta bata kuɗi,Aneesha taƙi karɓa tace tana da kuɗi sannan ta fice.
Halayen Aneesha yana burge Mammy da duk ma wanda ya zauna waje ɗaya da ita ko da na ƴan mintuna ne.
Pan ƙananun food flask Aneesha ta ɗauka ta haɗa break fast ɗinta a ciki sannan ta saka a basket ta fice.
Motar ta ta shiga ta fara driven mai gadi ya buɗe ta fice.
*Aneesa prov*
Kwance take akan gadonta tai ɗai ɗai tana sanye da riga doguwa ta bacci,fuskarta ɗauke da annuri hankaki kwance sai munshari take.
A hankali ta motsa tare da buɗe idonta,ta ɗan jima a haka sannan ta miƴe ta shige toilet.
Wanka tai tai brush sannan ta ɗauro alwala,sai da tai sallar sannan ta nufi gaban mirror.
Kwalliya bata daga tsarin su dan haka mai ta shafa sai powder da man leɓe sai turaruwa data fesa kamar ana ɓarin sa a jikinta.
Wardrobe ta nufa ta ɗauko kaya riga da wando ɗamammu kamar me,ta gyara gashinta ta sa ribom sannan tasa takalmin ta ɗauki wayarta da jaka ta fice.
Ɗakin Mammy ta leƙa taga bata ciki hakan ya bata tabbacin tana falo dan haka ta nufi falon.
Mammy tana zaune a falo tana duba kayan jiya da Aneesa ta karɓo Daddy da Ya Tahariq sun tafi office,ƙarar sautin takalmin Aneesa ya sa ta kalli steps ɗin har ta ƙaraso.
“Mammy good morning?”
Aneesa ta faɗa lokacin data ƙaraso falon.
Mammy ta amsa a hankali sannan.
Tace”Amma yanzu tsakani da Allah Aneesa ba zaki dena saka irin waɗannan kayan ba? Ke bakya ganin yadda ƴar uwarki take?”
Taɓe baki Aneesa tayi kafin
Tace”Kai ke dai Mammy kullum sai kin faɗi kushen shigata ni ban ga abinda tai ba”
“Ai dama ba zaki gani ba”
Mammy ta faɗa cikin macin rai.
Ganin haka yasa Aneesa tsuggunawa ta dafa gwiwar Mammy.
Tace”Haba dan Allah Mammyna kiyi haƙuri zan dena”
Mammy taji daɗi da Aneesa tai haka,dan haka sai
Tace”To Allah ya nufa”
Aneesa ta amsa da ameen,sannan ta sake.
Cewa”Mammy bari naje school”
Mammy Tace”Ki tsaya ki break”
Aneesa ta miƙe tana,Cewa”A’a Mammy nayi a school”
Bata sake bari Mammy tai magana ba ta bar falon.
Mammy ta girgiza kai tare da yiwa Aneesa addu’a ta cigaba da duba kayan.
*Aneesha prov*
Tana isa makarantar a gurguje ta nufi department ɗin su,yau ta hanyar department ɗin su Aneesa ta bi saboda bata son ta haɗu da wannan malamin hanyar da take bi kuma hanyar sa ce shi ya sa ta canja.
Duk in da ta wuce sai a dinga nuna ta ana cewa a’a yau kuma diamond wannan shigar akai sha’awar yi,har da masu kawo mata hare hare kala kala.
Wasu su zo za su taɓota sai tai nagana tace ba wadda su ke nufi bace abubuwa dai ba daɗin ji bare gani.
Duk farin cikin da Aneesha ta fito da shi sai ta neme shi ta rasa domin ranta ta ɓacin ganin wai duk ƴar uwarta ake wa wannan,kenan haka Aneesa ta zubar da mutuncinta? Aneesha ta tambayi kanta.
Haka tai ta tafiya tana tunani kawai taji tai karo da mutum,a hankali ta dafe goshinta wanda tai karon a wajan tare da ɗaga kai dan ganin wanda su kai karon da shi.
[08/10, 7:55 am] +234 706 345 2697: *ANEESHA KO ANEESA*
*🌺🌺🌺⭐⭐⭐☀☀☀🌺🌺🌺*
*Zan dinga amfani da waɗannan flowers da sters ɗin da kunga novels da haka to Indian Girl ce nagode*
*Aƙalamin*
*Zainab Muhammad (Indian Girl)*
*Ga wani sabon salo mai rikitarwa soyayya ce tsagwaranta cin amana da sauran su ku dai kawai ku biyo ni muje zuwa*
*Littafin kuɗi ne game son biyan nata kuɗin kafin na gama bunus tai min magana ta wannan number 07063452697*
*Akwai group wanda za a dinga post kullum 500 wataran ma har biyu za a iya samun post,300 kuma post ba kullum ba*
*Sai kun zo*
*6*
*________________________________________________________________________________* Ƙasa tai da kanta ganin wannan malamin wanda ko sunan sa bata sani ba,ta juya zata koma da baya taji ya fara magana.
“Ke shine jiya na bada saƙon ki zo office amma baki zo ba?”
Shiru Aneesha tai ta kasa magana dan bata so a maimaita irin ta ran nan da har ya zage ubanta,sannan a hankali ta jiyo da fuskarta daga juyawan da tayi.
“Uhum ina sauraran ki”
Ya faɗa yana zuba hannunsa a aljihu.
Cikin mamakin yadda ta ga ya canza sannan yana magana cikin sanyi ba zafin rai,ta basar da mamakinta tare da ɗaga kanta ta kalleshi
Tace”Am malam san da su ka faɗan kai na na ciwo da aka tashi sai na tafi gida kawai,shi ya sa ban zo ba”
Cikin jimamin jin cewar da tai kanta yai ciwo a jiyan.
Yace”Ayya sorry Allah ya sawwaƙe”
“Ameen nagode malam”
Aneesha ta furta a hankali.
Malamin yai murmushin jin daɗin saukar zazzaƙar muryarta a cikin kunne da jikinsa gaba ɗaya,ya ɗan lumshe ido.
Aneesha tana lure da shi ya yin da a ranta take cewa’wannan kuma ko lafiya yake wani limshe ido?’.
Ahankali ya buɗe idanun sannan ya kalleta.
Yace”Aneesha ko?”
Aneesha ba tai magana ba ta ɗaga kai alamar ‘eh’ kawai.
Ya gyaɗa kai kafin,Yace”Ok daga yanzu ki dinga shiga class kinji”
Nan ma Aneesha ba tai magana ba ta ɗaga kai.
Yace”Idan kin fito daga test ɗin ki zo ina son magana dake”
Bai jira abinda za tace ba ya juya ya bar wajan.
Da kyar Aneesha ta iya ƙarasawa cikin class ɗin ta nemi waje ta zauna.
Dake duk ƴan class ɗin sun ji hirar su da malamin ya sa duk suka bita da kallo data shigo.
“Aneesha”
Farisa ta kira sunanta tana kallon fuskarta.
Aneesha ta ɗaga kyawawan idanunta ta kalli Farisa alamar na amsa ina sauraranki.
Farisa Tace”Gaskiya da magana a tare da mutumin nan fa,tu amma…”
Sai tai shiru
Aneesha a taƙaice Tace”Amma mefa? To ki faɗa”
“A’a Anee mu dai bari muji tukun daga can”
Farisa ta faɗa.
Kafin Aneesha tai magana sallamar wata malamin yasa duk suka kalli gaban allon suna amsa sallamar.
Nan malamar ta raba musu test ɗin kafin su mai da hankali su fara abinda ke gaban su.
*Aneesa prov*
Aneesa kafin ta ƙarasa paking jama’a sun kewata mata da maza suna shewa ana.
Cewa”Sai diamond girl sai babbar yarinya”
Aneesa tana murmushi ta fito daga motar tai masu fari kafin a ɗunguma zuwa department,suna zuwa ba su shiga class ba suka nemi waje suka zauna.
Nan wata ta dubi Aneesa.
Tace”Diamond girl ɗazu fa mun ga wata mai kama dake sak ama dai shigar ta ban banta”
Damm! ƙirjin Aneesa ya buga ‘kar dai sun ga Aneesha kenan?’.
Cikin basarwa.
Tace”A gaskiya aljanata kuka gani domin ni bani da wata mai kama dani”
Za su sake magana ra katse su da zan cen aka ɗau wani shagalin.
“Gaskiya diamond wannan wankan zan siye shi”
Wani ɗan guy ya faɗa yana murmushi da kallon inda ya bayyana na jikin Aneesa.
Wani mugun kallo Aneesa ta jefe shi da shi sannan.
Tace”Kai kar kaiwa kanka illa ka duba tsaf kaga ni ba sa’ar yara bace”
Ƴan,matan su ka ɗauki shewa suna.
Cewa”Hakane diamond faɗa masa”
Nan da nan Aneesa ranta ya ɓaci kawai saboda abinda wannan guy ya faɗa,ana haka wayarta ta shiga ƙara a hankali tasa hannu ta ɗauka bayan taga mai kiran ta falaɗa fuskarta da murmushi.
Tana ɗaga wayar ta kara a kunne.
“Baby banda lafiya ki zo gida yanzu”
Haisam ya faɗa kuma bai jira abinda za tace ba ya kashe wayar.
Hankalin Aneesa ya tashi dan haka ta miƙe ta nufi motarta ta shiga ta bar makarantar,kai tsaye ta nufi godan Haisam.
*(Ni kwa nace ba zaki karatun ba kenan?)*
Su kwa ƴan matan cike da jin haushi suka miƙe suka nufi class domin yau ba mai siya musu abinci idan sun fito daga lecture.
********* 🌺 *********
Dad ne tsaye a falon cikin shirin fita ya yin da Meema da Mom ke tsaye a kusa da shi.
Salima ce take saukowa daga steps ɗin benan dake falon hannunta ɗauke da akwati da jaka ƙarama,tana ƙarasa saukowa ta ɗaga kanta da idanunta dake zageye cikin baƙin glass ƙarami.
Tace”Yawwa Dad na gama”
Dad ua dubeta sannan.
Yace”Ok”
Sannan ya sake juyawa ya dubi Mom da Meema.
Yace”To mu za mu wuce”
Fatan alkairi su kai musu.
Salima ta dube su da murmushi a fuskarta.
Tace”Mom and Meema to sai mun yi waya”
Mom da fuskarta ba annuri ba tace komai ba.
Meema ta ɗan haɗe fuska sannan.
Tace”Au ke murna kike ko? To ba komai”
“Meema sorry wallahi ina son aiki a can ɗin ne”
Salima ta faɗa tana haɗe hannuwanta waje ɗaya.
Meema tai murmushi kafin.
Tace”To shikenan Allah ya taimaka Allah ya kai ku lafiya ya dawo da ku”
“Ameen ameeen my Meema”
Salima ta faɗa.
Nan dai su ka ɗinguma zuwa harabar gidan,sai da Dad da Salima su ka hau mota driver yaja sannan su Meema suka koma cikin gida.
Tun da suka ɗau hanya suke hira tsakanin Dad da ɗiyar ta sa akan aikin nata daga baya kuma ya shiga waya da mutanansa ita kuma ta shiga chat da ƙawayenta.
Cikin ikon Allah su ka iso garin kano a makarantar,bayan driver yai paking Dad da Salima suka nufi office ɗin babban director makarantar.
An tarbesu da fara’a da mutunci sun ɗanyi maganganu kafin su fito suyi sallama da Dad da Salima ya tafi shi da driver dake a hotel za su zauna kafin lokacin jirgi su bi dan motar Saliman za a barwa.
Tafiyar su ke da wuya ta nufi office ɗinta ta aje kayanta ta zauna kan babbar kujera tana mai da gajiya,sai da ta ɗan huta sannan ta shiga dudduba bayanan koyarwa.
**********************⭐********************
“Wallahi yau na gaji da yawa duk da ba wani abu akai sosai ba”
Aneesha ce ke wannan maganar lokacin da suka fito daga aji ita da Farisa.
Farisa Tace”Ke dama haka kike ai,amma ko da yake ai anyi aiki tun da test yafi ɗaukan kectures wuya”
Aneesha Tace”Wallahi hakane”
Haka suka fara tafiya cikin nutsuwa.
“Au Aneesha dan Allah ki daure yanzu ki amsa kiran malamin nan kinji”
Farisa ta faɗa cikin alamun tunawa da maganar.
Aneesha Tace”Ok muje ki raka ni”
Farisa Tace”To”
Suka rankaya suka nufi hanyar office ɗin nasa,suna zuwa sallama su kai ya ba su izinin Aneesha ta shiga dan haka Farisa ta tsaya ita a waje tana jiranta.
Sallama Aneesha ta sake yi sannan ta durƙusa.
“Malam gani kiran daka ce na zo”
Aneesha ta faɗa kanta na ƙara tana wasa da gefen hijab ɗinta.
Kallo ya bita da shi yana jin wani irin abu na fusgarsa a zuciya,sauke ajiyar zuciya ya yi sannan ya fara magana.
“Da farko dai ina mai baki haƙuri akan abinda ya faru dani dake a class kiyi ƙhaƙuri”
Ya ƙarasa maganar yana haɗe hannu waje guɗa.
Cikin sanyin murya Aneesha Tace”Malam ai ba komai ni dama ban riƙe ka ba”
Yaji daɗin maganar tata ya sake.
Cewa”To ina matuƙar godiya sosai”
Aneesha ta ɗaga kai kawai.
Yace”Daga yanzu ba zaku sake gani na a class ɗinku ba saboda an canzan department yanzu sabuwar malama aka kawo muku”
Duk maganar da yake kai kawai Aneesha ta ke ɗagawa har ya kai ƙarshe.
“Aneesha”
Ya kira sunanta da wani salo wanda ita kanta sai da taji yarrr.
Ta ɗaga kai ta kalle shi sannan tai ƙasa da kanta.
“Ina sonki! ina sonki!! ina sonki!!! ina ƙaunarki”
Ya furta cikin salo na soyayyya.
A razane Aneesha take kallonsa tana girgiza masa kai,kafin
Tace”A’a malam kar ka faɗi haka a gareni dan Allah domin tawaya ne hakan ga rayuwata da zuciyata”
Yace”Aneesha ba sunana malam ba sunanan Anwar kuma soyayyar da nace ina miki har ga Allah da gaske nake ina sonki kuma ba zan iya cirewa zuciyata ba”
“Amma malam rayuwata fa? Ni ba zan iya ba”
Aneesha ta faɗa hawaye na zubo mata sakamakon jin baƙuwar kalma a tare da ita.
Miƴewa tsaye malam Anwar ya yi kafin
Yace”Aneesha zaki iya dan haka kije ki tunani,tashi kije Alkah ya tsare hanya”
Miƴewa kawai Aneesha tayi ta fice hawayen nabin kumatunta,fa fitarta Farisa ta nufota tana tambayarta lafiya amma ta kasa mata magana hakan yasa Farisa kama hannunta su ka bar wajan.
Yana kallon su har suka ƙule ya koma ya zauna yana jin zuciyarta gwara daya faɗa mata ya huta da wahalar da ya ke sha.
Aneesha kasa tuƙin tai sai Farisa ce ta tuƙa har su ka je gida,koda Mammy ta gan su ta shiga tambayar lafiya? Farisa tace bata da lafiya kanta ke ciwo.
Ɗakinta kai tsaye su kai da ita sannan Farisa tai musu sallama ta tafi,ita kuma Mammy ta bata abinci da magani sannan ta lulluɓeta ta fice.
Lumshe ido tai bayan fitar Mammy ta shiga tuna maganganun Anwar ganin kanta yana ƙoƙarin sarawa ya sa ta kau da tunanin kafin bacci kuma ya ɗauketa.
***********************🌸*******************
Haisam ya daɗa jawota jikinsa yana manna mata kiss kota ina.
“Haisam”
Aneesa ta kira sunan sa.
A hankali ya amsa.
Tace”Gaskiya Haisam ya kama ka aika a nema maka aure na saboda abinda muke ba kyau fa”
Haisam da bai fasa abinda yake ba.
Yace”Hakane ai na faɗawa Daddyna kuma yace za suje wajan Daddyn ki”
Murmushi Aneesa ta yi ba tare da tace komai ba su ka cigaba da abinda su ke.
Sai da ta kintaci lokacin tashin su school ya yi sannan ta sake wanka ta saka kayanta ta tafi gida.
[08/10, 7:55 am] +234 706 345 2697: *ANEESHA KO ANEESA*
*🌺🌺🌺⭐⭐⭐☀☀☀🌺🌺🌺*
*Zan dinga amfani da waɗannan flowers da sters ɗin da kunga novels da haka to Indian Girl ce nagode*
*Aƙalamin*
*Zainab Muhammad (Indian Girl)*
*Ga wani sabon salo mai rikitarwa soyayya ce tsagwaranta cin amana da sauran su ku dai kawai ku biyo ni muje zuwa*
*Littafin kuɗi ne game son biyan nata kuɗin kafin na gama bunus tai min magana ta wannan number 07063452697*
*Akwai group wanda za a dinga post kullum 500 wataran ma har biyu za a iya samun post,300 kuma post ba kullum ba*
*Sai kun zo*
*7*
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya ya yin da ɓangaran Aneesha ta amshi soyayyar Anwar kuma suna soyayya mai tsafta,ita kuwa Aneesa sai abin da yai gaba ita da Haisam domin yadda ka san matarsa haka ya mai da ita.
Wannan kenan.
*____________________________________________* “Gaskiya Anee abinda kike aikatawa ya fara damuna haba haba dan Allah ke bakya tausayawa halin da zan shiga?”
Aneesha take maganar hawaye na zubowa daga idanunta.
Aneesa ta kyaɓe baki tare da gyara kwaciyarta akan gado.
Tace”So to mene damuwarki da rayuwata ke Aneesha kike ni Aneesa ai ba haɗi dan haka dan Allah kiyi abinda ke gabanki nai nawa please”
Aneesha ta bi Aneesa da kallo sannan.
Tace”Au haka kika ce Anee nice fa wadda aka haife mu tare rana ɗaya amma kike cewa ba ruwan rayuwarki dani?”
“So what to da da akwai?”
Aneesa ta faɗa tana kallon Aneesha.
Girgizai Aneesha tai alamar a’a bata sake magana ba ta miƴe tabar ɗakin tana hawaye,koda ta shiga ɗakinta kuka tasha kafin ta barwa Allah.
Ita kuwa Aneesa ba wai zafin abinda takewa ƴar uwar tata ne bata ji ba a’a ba yadda za tai ne dole tai na kwatar kai.
Ranar haka Aneesha ta hini sukuku har sai da Mammy da Ya Tahariq suka fahimceta suka tambayeta amma sai tace bata da lafiya.
*_____________________________________________________* Kaka tana zaune a falo tana shafa roob a ƙafa Ashman ya shigo dake miƴe ƙafar tata tai da zai wuce sai ya ɗan takata,aikwa kaka ta kwalla kururuwa wadda yasa Mommy da Abba fitowa.
Abba cikin tambaya ya kalleta.
Yace”Inna lafiya meya same ki?”
Kaka ta kalli Ashman dake tsaye yana danna waya kamar ba abinda ya aikta,sannan.
Tace”Wallahi Aliyu nagaji da wannan mugun ɗan naka mai zuciyar arna”
Mommy ta zaro ido domin ta san tunda taji Kaka ta faɗi haka wani abun ya aikata.
Abba Yace”To Inna yau kuma me yai miki?”
Kaka Tace”Ba gaka gashinan ba ka tambaye shi ya faɗa maka da bakin sa”
Abba ya juya ya kalli Ashman sannan.
Yace”Son me kaiwa Innata?”
Taɓe baki Ash yai sannan ya ɗaga kai ya kalli Abba.
Yace”Bafa wani abu bane Abba kawai na ɗan takata ban gani ba shine ta saka ihu”
“Au ɗan takani ma kai to kaje Allah ha isa ya isar min”
Kaka ta faɗa tana mutsitstsika ido.
Abba Yace”Subhanallahi dan Allah Inna kiyi haƙuri kai Son bata haƙuri”
Kyaɓe baki Ash yai sannan yai hanyar ɓangaransa ba tare da ya bata haƙurin ba.
Itama Mommy ta koma ɗaki shi kuma Abba yai zaman lallashi.
*_______________________________________________________*
“Aneesha”
Malama Salima ta kira sunanta cikin sanyin murya.
Aneesha bata ji ba har sai da Farisa ta taɓota saboda zurfin tunanin data shiga tun jiya da su kai magana da Aneesa shikenan ta rasa sukuni.
Ta miƙe tsaye ba tare da ta amsa sunanta da malamar ta kira ba.
Malama Salima Tace”Aneesha zi muje office ina da magana dake”
“Ok malama”
Aneesha ta faɗa.
Malamar ta fice Aneesha ta bi bayanta.
Ko da su kaje office malama Salima ta kalli Aneesha tsaff sannan.
Tace”Aneesha meke damunki da har kike so ki sawa kanki tunani eyye?”
Ajiyar zuciya Aneesha ta sauke.
Tace”Malama yau banda lafiya shi yasa kika ga haka”
Cike da tausayi malama Salima Tace”Wayyo Allah sarki kinsha magani amma ko”
Aneesha ta amsa da eh.
Malama Salima tai mata sannu sannan tace to tafi Allah ya ƙara sauƙi.
Haka kawai Salima ke ya bawa da hankali da nutsuwar Aneesha ko a class ba ruwanta.
*________________________________________* Cike da tashin hankali Aneesa take kallon Haisam kafin ta fara magana.
“Haisam na shiga uku wasu suna min barazana da pics tsirara ya zan yi”
Cikun nuna alamun ko a jikinsa.
Yace”So to mene kawai ki basar”
“Basarwa? Basarwa fa kace ina mutuncin mahaifina dana gidanmu idan pics ɗin suka isa gare su?”
Haisam dan ya kawantar mata da hankali.
Yace”Sorry kwantar da hankalinki kinji za a san abin yi”
“To mene shi?”
Aneesa ta tambaya fuska jaɓe jaɓe da hawaye da magaji.
Haisam Yace”Ki cigaba da tafiya da masu maki barazanar da yadda suke so idan ba haka ba nima ban san abin yi ba”
Aneesa ta goge fuska sannan.
Tace”Kana ganin hakan ne mafita?”
Ya ɗaga mata gira “Yes hakane”
Kafin ta sake cewa wani abu wayarta ta shiga ruri,da sauri ta ɗauka ganin number da ake kiranta ta ɗaga.
Kafin tai magana daga can an fara cikin murya mara daɗin sauraro.
“Malama ko ince Hajiya Aneesa kin fi buƙatar ganin tsiraicinki a idon iyayenki da duniya ko?”
Girgiza kai Aneesha ta shiga yi,sannan.
Tace”A’a bana so son wani ya gani please dan Allah”
Aka ce “Ok hakan ya yi amma muna buƙatar kuɗaɗe idan kin bayar mu kuma zamu goge duka”
“Nawa kuke ɓuƙata?”
Aneesa ta tambaya cikin sauri.
Akace”Million 10 muke so ka ɗai sai mu goge duka pics ɗin mu kuma”
Gaban Aneesa ya buga ita kwa ina zata ga waɗannan maƙudan kuɗaɗe?ta faɗa a ranta.
Kafin tai magana an kashe wayar.
Ta juya ta kalli Haisam.
Tace”Haisam wane wannan yai min haka?”
Haisam Yace”Waɗanda kika sallamawa jikinki mana”
“Kai kaɗai nake sallamawa jikina Haisam na san kuma kai ba za kai min haka ba”
Aneesa ta faɗa tana tunani.
Haisam Yace”Wai da suka kira kin me suka buƙata?”
“10millions”
Aneesa ta bashi amsa cikin sanyin murya.
Haisam ya ɗan nuna alamun mamakin yawan kuɗin da aka buƙata.
Yace”To a ina zaki samu?”
Aneesa Tace”Babu Haisam”
Sai kuma ta fashe da kuka mai cin rai tana dana sanin mai da kanta ƴar iska da tayi duk da ba karuwanci take ba.
Miƙewa Haisam yai yace mata bari yaje ya dawo,itama ganin ba abinda za tai idan ta zauna ya sa ta miƙe ta tafi.
Ko da ta koma gida ba wanda ta kula tai ɗakinta,Aneesha mai gigin mata maganar itama yau ba tai ba.
Tunda Aneesa ta shiga ɗaki ta kwanta ta kasa komai saboda fargaba tunaninta duk ina zata sami waɗannan kuɗaɗen.
*Washe gari*
Da sassafe wasu mutane suka bawa mai gadi saƙo suka ce ya ba alhaji dan haka Daddy ya fito za su tafi office mai gadi ya bashi.
Daddy bai tsaya buɗawa ba abu ya faɗo daga emp ɗin da aka bashi dan haka ya sunkuya domin ɗauka,inannalillahi wa innalaihirraju’un.
*To jama’a free page fa ya ƙare dan jin cigaban wannan zazzafar cakwakiyar ku saurin antayowa domin biyan na ku akan sassauƙan farashi*
*Na sake mai maita muku garaɓasar 500 post kullum 300 kuma ba kullum ba dan haka a zo a kwashi gara da wuri ar arha tasa ta ƙare wasu basu samu ba*
*Ƙarin bayani ta wannnan number 0⃣7⃣0⃣6⃣3⃣4⃣5⃣2⃣6⃣9⃣7⃣ sai kun zo*
[08/10, 7:56 am] +234 706 345 2697: *ANEESHA KO ANEESA*
*🌺🌺🌺⭐⭐⭐☀☀☀🌺🌺🌺*
*Zan dinga amfani da waɗannan flowers da sters ɗin da kunga novels da haka to Indian Girl ce nagode*
*Aƙalamin*
*Zainab Muhammad (Indian Girl)*
*Alsm alaikum jama’a masu karatu Aneesha ko Aneesa dai na mai da shi free book sakamakon wani dalili,abinda nake so da ku kawai shine wanda ya karanta yai min addu’a ta fatan nasara da kariya daga duk ka abin ƙi.Sannan yaiwa iyaye na da iyayenku addu’a Allah ya ƙara musu lafiya waɗanda suka mutu kuma Allah yai musu rahma ameen,waɗanda ke raye kuma Allah ya ƙara musu lafiya da nisan kwana,ku min addu’a ta alkairi nagode*
*Sannan dan Allah idan har nai post kuma kin san kin karanta kinji daɗi to nima ki comments da sharhi naji daɗi wanda hakan zai ƙara kwarin gwiwa wajan cigaba da yi muku*
*8*
*_______________________________________________________* Koda ta isa tashar sai ta tarar da mota ta cika dan haka ba tare da ta san motar wane gari bace ta afka ciki dama mutum ɗaya ake jira dan haka mota ta tashi aka fara tafiya,hawaye ne masu ɗumi suka zubo a idanun Aneesha ba komai ya sata kuka ba sai wai yau zata bar mahaifarta ba tare da jin daɗi ba.
Haka mota tai ta tsala gudu a sannan Aneesha ta zubawa hanya idanu tana kallon yana yin garin da inda suke wucewa da bishiyoyi.
*__________________________🏤__________________________*
Ta sake kallon agogon hannunta sannan ta kalli hanya ya yin da a ranta take tunanin ko lafiya yau bata zo da wuri ba har gashi an gama test na farko za a shiga na biyu.
Wayarta tai ta kira amma shiru a kashe hakan yasa ta haƙura da kiran tana tunanin ko lafiya,amma ta bari idan ta tashi daga makarantar zata gidan su taji.
Shigowar malama yasa su ka mai da hankali gareta.
Ko da ta fito daga class ɗin tana tsaye tana wani tunanin daban ta hango malam Anwar ya nufo inda take,yana ƙarasowa ya tsaya a gabanta.
Yace”Malama Farisa yau ina ƙawar take take? Ko ta tafi?”
Sauke ajiyar zuciya Farisa tayi kafin.
Tace”A’a yau bata zo ba gaba ɗaya kuma na kira wayarta a kashe yanzu ma gidan su zani”
Malam Anwar Yace”To Allah yasa dai lafiya domin kwa nima na kikkirata nama zata ko sharrin network ne ko kuma ta kashe ne saboda tana class”
Girgiza kai Farisa tai Tace”A’a ba haka bane nima ban san mene ba”
“To Allah yasa lafiya,amma dan Allah yadda akai kice ta kira ni”
Farisa Tace”Tam shikenan”
Godiya yai mata sannan ya juya ya tafi itama ta fice,tana fita ta sami abin hawa ta faɗa masa inda zai kaita ta shiga.
A ƙofar bakin get ɗin gidan ya sauketa ta bashi kuɗin sa ta nufi cikin gidan,sai da su ka gaisa da mai gadi sannan ta nufi cikin gidan.
Knock tai aka buɗe mata ta shiga,zama tai akan kujera sannan yarinyar ta shiga faɗawa Mammy cewar tai baƙuwa,bayan ta faɗa mata Mammy tace gata nan.
Fitowar Mammy ke da wuya taga Farisa ce dan haka sai hankalinta taji ya tashi ta shiga tunanin me zata faɗa mata game da Aneesha,amma saboda kar Farisa ta fuskanci wani abu yasa ta saita kanta.
Gaisheta Farisa tayi sannan.
Tace”Mammy Aneesha ko lafiya na kira wayarta a kashe sannan bata zo makaranta ba yau?,shine nace bari na zo na gani”
Mammy ta faɗaɗa fuskarta da murmushin yaƙe kafin.
Tace”Allah sarki Farisa ai Aneesha kakar su aka tafi kaiwa iya saboda bata da lafiya kuma ba kowa a wajanta shine yau su kai sammako suka tafi dake da nisa garin zaria ne”
Farisa tai murmushi jin cewar Aneeshan lafiya take.
Tace”Tam masha Allah naji daɗi da lafiyarta ƙalai,kaka kuma Allah ya bata lafiya”
Mammy ta amsa da ameen tana mamakin kanta da irin wannan ƙarya data zuba.
Nan Farisa taiwa Mammy sallama ta tafi.
*________________________________________________________________________* Zaune yake a office ɗin sa da biro a hannunsa yana ta cike wasu takardu,wayarsa dake ajiye a gefe kan table ɗin ta shiga rings ya ɗauka tare da duba mai kiran kafin ya saki murmushi wanda iya laɓɓansa ne kawai.
“Ya mutumina na san yanzu kana wajan aiki hasalima aikin kake tamkar agogo”
Ashman ya faɗa cikin tsokanar ɗan uwan nasa.
Jalal ya ɗan ya mutsa fuska kafin.
Yace”Oh kenan nine agogon? To naji dai.Ya akai ne ka kirani da wannan safen ko kaka ce?”
Ashman ya kyaɓe baki sannan Yace”Kai rabu da wannan tsohuwar ba ita bace,nafa kamu kuma ban wace yarinyar ba ko aljana ce ma oho dan ban ƙara ganin ko da pics ɗinta ba”
Jalal yai ɗan ƙaramin tsaki sannan.
Yace”Ni wallahi na zata wata magana ce mai muhimmanci ashe ma wannan zan cen ne mara amfani”
Ashman Yace”Ban gane mara amfani ba ce maka nai fa na kamu da soyayya kuma ban san yarinyar ba dan ban ƙara ganinta ba”
“To so what? Kasan fa ni idan har zan cen soyayya ne bana ciki saboda ni bata gabana”
Jalal ya faɗa yana jujjuya biron hannunsa.
Ashman ya sauke gwauran numfashi.
Yace”Dan Allah bro ka tsaya mana ka saurare ni idan dan kai baka yi ai ni sai ka tsaya ka dubi matsalata sannan laban shawara mai ma’ana”
Jalal ya ɗan runtse idanunsa sannan ya buɗe.
Yace”Ok tam yanzu dai ka bari sai zuwa neigh sannan kaga na samu nutsuwa”
Ashman Yace”Tam shikenan ina jiranka”
Jalal bai magana ba ya kashe wayar dan maganar ma shi wuya take masa.
“Hakurin ka jefa kan ka a wahala Ash domin soyayya wahala ce”
Jalal ya faɗa kafin ya cigaba da aikin dake gabansa.
*_______________________________________________________* Sai da gari yai duhu magriba ta rufa sannan suka shigo cikin tashar garin.
Nan jama’ar dake cikin motar suka shiga firfitowa amma ita Aneesha ko motsawa ba tai ba,sai da kaf ƴan motar suka fito ya rage saura ita kaɗai sannan ta fito ta shiga kalle kallan tashar ya yin da itama jama’a ke kallonta saboda kyanta.
Bata san ina bane nan hasalima sunan garin bata sani ba ta faɗa a ranta,wata mata dake ƙoƙarin ɗaukan kayanta ta tambaya.
“Baiwar Allah dan Allah ina ne nan wane gari ne?”
Matar data kalli Aneesha sai da ta dake domin kyanta da bata taɓa ganin ko da mai makamancinsa ba.
Matar Tace”Sunan garin katsina”
Tana faɗar haka ta kwashi kayanta ta ƙara gaba dan tana tunanin ko ba mutim bace.
Aneesha ta mai maita sunan garin gashi dare ne to ina zata dosa Allah masani.
Nan ta koma can gefe domin ta bar cikin jama’ar dan taga kamar ma gudunta suke,can ta samu wani benci ta zauna tana kallon jama’a da ɗan sauran hasken farin watan dake sama.
Wayarya dake jaka ta ɗauko ta kunna nan taga ashe dare dai ya yi domin har ƙarfe 7:45pm,ta mayar da wayar ta miƙe dan ta san inda ta dosa.
Hanyar da take bi babu jama’a ɗass hanyar,haka ta dinga jefa ƙafarta a ko ina ba tare da ta san ina bane.
Can wasu samari dake zaune saman wani benci da alama sun shahu sun ƙat domin har da sauran wata a hannunsa suna sha,hangota su kai tana tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ɗayan ya dubi ɗaya cikin muryar maye.
Yace”Kai baba kaga wata yarinya mai zafi”
Ɗayan shima yace cikin muryar mayen.
“Kai ai wannan aljana ce”
Na farkon da yai magana ya sake.
Cewa”Ba aljana bace duba da kyah ka gani”
Na biyun ya sake Cewa”Eh nagani mutum ce aikwa mu tashi muje mu kwashi gara”
Duk suka miƴe suka nufi inda Aneesha ke tafiya,dake a gabanta suke sai suka tsaya a gabanta.
Aneesha ta ɗaga kyawawan idanunta ta zuba musu ganin sun tare hanyar da za ta bi.
“Bayin Allah lafiya mene?”
Aneesha ta faɗa tana kallon su.
“Kai Baba riƙota muje bayan can”
Ɗayan ya ba ɗayan umarni,nan su ka shiga kiciniyar da ita sai sun riƙeta aikwa ta kwasa a guje ta nausa cikin rashin sani ta gwabza tuntuɓe da dutse aikwa ta faɗi.
Nan waɗannan samari suka ƙaraso tare da tsauawa akanta su kai mata rumfa,kafin su sunkuya dan cire mata hijabin dake jikinta.
*Comments da sharhi*
*Indian Girl ce*
Leave a Reply