Hausa Novels

Anjane Hausa Novel Complete

Anjane Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Anjane Hausa Novel Complete

★★★ *ANJANE* ★★★

(Rashin sani)

★★★★★★★★★

 

 

_*PAID BOOK*_

 

 

Story/written by Ouummey.

 

Wattpad @ouummey.

 

 

 

From The author of:

 

*HAƘORIN DARIYA*

*ƘASAR MU A YAU*

*BA NI DA LAIFI*

*SARAKI (the accused prince)*

*ABOTA CE KO SOYAYYA*

*And now…….ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

 

 

 

 

 

*FREE PAGE 001*

 

 

 

Ina the name of Allah the most beneficient, the most glorious and the most merciful.

 

Dubun salati ga fiyayyen halitta Manzon tsira Annabin mu Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

Anjane

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa me komai da ya Wada ta ni da rai da lafiyar da na sake dawowa gare ku cikin wani salon rubutu na daban, Allah yadda ka bani ikon fara rubutun nan lafiya kasa in gama lafiya, Allah ka bani ikon rubuta abinda ze amfane ni ya amfani al’umma gaba ɗaya, ya Rabb ka hane ni rubuta abinda ze cutar dani ya cutar da ƴan uwa musulmai.

 

At long last nake cewa hellooooooo to You my fans💃💃💃💃💃.

 

Gani dai na sake dawowa, Ouummey ce dai taku tafe cikin wani sabuwar tafiyar da nake fatan ku so kuma ku ƙauna ce shi fiyeda littattafai na na baya, soyayyar da kuka nuna min a littafin *SARAKI da ABOTA CE KO SOYAYYA* is really amazing and unpredictable, am using this opportunity to say thank you once again, Ouummey loves you so dearly 💖.

 

Sedai fa ba kamar baya ba this novel isn’t FREE kamar na baya, it’s a *PAID BOOK at ₦300 ONLY!!!.*

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng

Na sani you guys won’t make me feel unloved or ashamed, nasan zaku nuna min ƙaunar da kuke min ta hanyar siyan littafina dan rubutu na ba abin yar wa bane, isn’t so??!.

 

Kar dai na cika ku da surutu, ga duk me buƙata zai/zata biya kuɗin ta ta wannan account ɗin, RABIATU ABDULLAHI

2391368231 ZENITH BANK tare da turo shaidar biya ta 09013101854

Ko a turo katin MTN ta wannan number

09013101854.

 

Son so fisabilillah 💋💋.

 

 

WANNAN LITTAFIN SADAUKAR WA NE GARE KU MY FAMILY, HEART U ALL AND ALLAH YA QARA MANA ZUMUNCI DA QAUNAR JUNA, AMEEN💞💝💖💗.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

________________________📖 Gudu take cikin fitar hayyaci cikin dokar dajin dake da shegen duhu duk kuwa da cewa ba wai dare ne ba dan lokacin bai wuce ƙarfe huɗu da rabi zuwa biyar ba, takun mutanen da take jiyo wa a bayan ta yasa ta tabbatar basu daina bin ta ba haka suna daf da ita, wani irin kuka ne ya kubce mata ta shiga yin shi tana sakin numfarfashi, bata san me yasa azzalumai suka yi yawa ba a duniya, bata san me ita ko ƴaƴan ta suka tare wa maƙiyan ta ba da suke san se sun shafe labarin su ta kowace hanya, a rayuwar ta bata da abokin gaba tun daga yarinta har zuwa girman ta, kai har zuwa yanzu da take wannan gudun na ceton ranta da na ƴaƴan ta bata san dalilin neman kashe su ba.

 

Kukan da yarinyar bayan ta fara ne yasa na gane jaririya ce sedai ba wai ɗanyar haihuwa ba dan zata kai watanni, bata rufe bakin ta ba wani kukan ya shiga tashi, se a lokacin na lura goyon gaba da baya ne matar tayi kuma da alama ƴan biyu ne dan itama ta gaban macece, wannan kukan shi ya kuma ruɗar da uwar ta saki nata kukan me sauti tana cigaba da gudun da take yi.

 

“Yauwa gata can, ku ƙara gudu mu cin mata tun kafin ta kai ga ficewa dajin nan dan na gaban sa ya fishi duhu ba lallai mu iya ganin ta ba”.

 

Cikin azama ta ƙara gudun ta dan jin abinda wani da take zaton shine babban su yace, burin ta a lokacin be wuce ta fita daga nan ta faɗa dajin gaban ba dan tsira da numfashin su sedai bata kai ga hakan ba taji saukar katako ta bayan ƙeyar ta, su ne suka jefo mata ko kuwa daga ina yake ba ta sani ba.

 

Faɗuwa tayi sedai da sauri tasa hannu ta dafe ƙasa dan gudun kar ƴar ta taji ciwo, jin takun su daf da ita yasa ta hanzar ta miƙewa duk kuwa da yadda taji jini na bin wuyan ta ban da kuma jirin da take gani, neman wajen fakewa take yi sedai kamar babu wani loko a dajin, a lokacin ba ta rayuwar ta take yi ba ta rayuwar ƴaƴan ta ne, ta sani ba lallai su tsira daga hannun wadan nan azzaluman ba sedai tana fata ƴaƴan ta su tsira ko da kuwa ita zata hallaka, yara ne da basu san komai ba basu kuma fara komai a rayuwar su ba dan yanzu ne suke watanni na uku da haihuwa, ba zata so rayuwar su ta tsaya iya nan ba haka kuma ba zata so maƙiya suyi galaba akan ta ba, ta sani saboda yaran ake neman kashe ta saboda kada uban su ya sami wani haske ko ƙanƙani a rayuwar sa.

 

Bata san me yasa marasa imani suka cika faɗin duniya ba sedai tana tausayin mijin ta kuma uban ƴaƴan ta, yaran ne dukkan wani farin ciki, jin daɗi da walwalar sa shiyasa mahassada ke neman ganin sun raba shi dasu har itama ta samu nata rabon ƙaddarar, rayuwar su cike take da baƙin duhun da bata taɓa tunani ba se a yau da take wani siraɗi na mutuwa ko rayuwa, se a yanzu ne abubuwa da dama suka dinga dawowa kanta da yaci ace ta ankare da su tuntuni sedai tsabar pious heart ɗin ta yasa bata taɓa zargi ko kawo wani mummunan lissafi ba, se a yanzu ta tabbatar da tabbas tayi kuskure, kuskure kuma mafi girma na ɗaukar cewa kowane ɗan Adam kyakkyawar zuciya gare shi.

 

Wani ɗan haske da take hangowa yasa ta nufi wajen cikin matsanancin gudu cikin fatan Allah ya kawo mata matserata ko da ta rayuwar ƴaƴan ta ne kaɗai, ta yarda ita ta mutu in har zasu rayu, tana fatan suyi kyakkyawar rayuwa ba dan saboda komai ba se dan kwaɗayin samun addu’ar su, Manzon Allah yace addu’ar ƴaƴa salihai ga iyayen su karɓaɓɓiya ce haka kuma sune kawai arziƙin da mutum ze mutu ya bari a duniya ya tadda shi a ƙiyama bayan sadaƙatul jariya wanda tasan bata da rabo a wannan ɓangaren dan ko tunanin hakan bata taɓa yi ba.

 

**********

 

Kamar ko wane hutun makaranta in an yi, yau ma tafe take da ƙafa kamar yadda ya zame mata jiki ba kamar ragowar ƴaƴa masu gata ba da za’a je ɗaukar su a mota, mashin ko keken amalanke ko kuwa motar ƙurƙura, ita da ƙafa take takawa har zuwa ƙauyen su wanda tsakanin shi da makarantar tafiyar awa huɗu da mintuna ne a ƙafa, bata taɓa jin ba zata iya ba dan tana matuƙar son karatun kuma ta san in ma ba tayi ba kanta kaɗai ta cuta dan shine kaɗai gatan da take tunanin zata iya samu da ze zama sanadin canjuwar rayuwar ta da ma duniyar ta gaba ki ɗaya.

 

A hankali ta shiga takawa lokacin dan ta gaji, tsakanin ta da ƙauyen su be wuce tafiyar mintuna Talatin ba dan ta kawo kusa sosai sedai a yadda ta gaji se take ganin in tayi yanke ta cikin daji zata fi saurin zuwa gida maimakon ta bi ta hanya sosai, ba ɓata lokaci ta danna kai cikin dajin cikin dajin ba tare da tsoro ba dan shiga daji a jinin su yake dan sun saba, in basu shiga yin itace ba sa shiga tsinkar magunguna ko kuma kayan marmari ko kuma yawon su.

 

Ƙarar gudun da taji yasa ta ɗan dakata tana tunanin anya lafiya, jin kamar gudun ba na mutum ɗaya ba yasa ta ɗare wata doguwar bishiya da sauri ta yadda zata samu damar ganin abinda ke faruwa, mace take hangowa da goyo har biyu wato gaba da baya tana gudu yayinda wasu mutane masu riƙe da makamai suke binta, hankalin ta taji ya tashi duk da bata san me tayi musu suke bin ta ba sedai a ƙananan shekarun ta tasan ba abu me kyau yasa suke bin ta ba tun da har ga makamai banda haka kuma mutane da yawa na shiga wannan dajin dan aiwatar da munanan ayyukan su saboda duhuwar dajin na basu kariya daga idanun jama’a, bata san me yasa ba sedai kawai taji a ranta ya zama dole ta taimaki wannan matar, ba zata bar wannan azzaluman su yi galaba a kanta ba.

 

Da sauri ta ɗirko daga bishiyar tareda nufar wajen matar da saurin ta dan gasu da suka saba da dajin bawa wani ganin duhuwar sa, da sauri ta fizgi hannun matar daidai lokacin da wani yayi nasarar sakar mata harbi a ƙafa ganin yadda take wahalar dasu, wani kogo ne na bishiya ta shigar da matar haka kuma da sauri tasa hannu ta since goyon bayan ta ganin wuyar yarinyar na reto alamun ta suma ko ta mutu, a galabaice matar ta kwanto ta gaban ma ita kuma tayi saurin tare ta.

 

Numfarfashi kawai matar ke yi dan ta galabaita to the extent da bata iya ko da buɗe idanun ta sosai balle tayi magana, hannun yarinyar da bata san wacece ba ta ruƙo da sauri tana fizgar numfashi kamar me asthma, da ƙyar ta buɗe baki da idanun ta tayi magana mara tsayi

 

“A…am..maa..naa, su..su..tsira..dan.. Allah”.

 

Wani irin duka ƙirjin yarinyar ya shiga yi jin abinda matar ke faɗa, da sauri ta shiga jijjiga ta,

 

“Ki tashi Aunty mu gudu, kar ki rufe idanun ki ni ban san inda zan kai yaran nan ba wallahi”.

 

Bata iya tace mata komai ba se yatsun ta duka goma ta ɗaga mata kafin ta shiga nata nuni da zobunan dake jiki wanda guda biyar ne, uku a hannun dama biyu a hannun hagu, da sauri ta sa hannu ta cire mata dan a tunanin ta sun dame ta ne, wuyan ta ta sake nuna mata nan ma ta cire mata sarƙar jikin ta da ɗan kunne, ajiyar numfashi matar ta saki tana buɗe ido sosai cikin ƙure ƴaƴan ta da kallo kafin wannan karan cikin cikakkiyar magana tayi magana

 

“Ki kula min dasu dan Allah, ban bar komai ba a wannan duniyar se su, sune fitilar zuciyar mahaifin su, kije dasu na baki halak malak amma dan Allah su tashi cikin kyakkyawar tarbiyya kamar kowane cikakken bahaushe musulmi, kije dasu ki kula dasu da wannan kayan sarƙar na hannun ki dan Allah kar su cimma na su kashe mu gaba ɗaya, kar ki tsaya wata magana dan ni tawa ta ƙare ko basu kashe ni ba mutuwa zan yi dan bana jin akwai ragowar jini a jikina, fatana ƴaƴana su tsira kuma alhamdulillah Allah ya turo min ke dan cetar su, ki tafi, ki tafi gasu nan, dan Allah ki tafi”.

 

Jin takun nasu da gaske kusa daf da bishiyar yasa yarinyar damƙe set ɗin sarƙar hannun ta ta zuba cikin jakar makarantar ta ta buhu dake hannun ta tare da saɓa yarinya ɗaya a ƙafaɗar ta ta goye ɗaukar tare da ɗaukar jakar buhun ta shige cikin dogayen ciyayin wajen cikin rarrafe dan kar su gan ta, seda ta ɗan yi nisa sannan ta tsaya jikin wata bishiya tana kallon yadda suka cimma matar a inda ta bar ta, haske haske sauka dinga yi da wayoyin hannun su cikin neman inda ta ɓoye yaran sedai basu ga komai ba, tsawon lokaci kafin suka koma wajen da suka bar uwar da mutum ɗaya na gadin ta,

 

“Yanzu ya zamu yi, me zamu cewa matar nan game da ɓatan yaran?”.

 

Ɗaya daga cikin su ya faɗa kafin ɗaya ya kai ƙafar sa yana shurin matar da ke jingine har lokacin yana tambayar ta inda ta kai yaran sedai tuni ta faɗi rigija alamar rai yayi halin sa, tsabar jinin dake kwance a inda ta jingina zaka yi zaton wata ƙaramar dabba aka yanka, wani mugun tsaki mutumin ya saki kafin ya umarci ragowar su ɗau gawar tata sukai mota shi kuma ya cigaba da bincika wajen sedai dake ba sanin kan dajin yayi ba ko kaɗan be ko kai wajen da yarinyar take ba rungume da baby ɗaya a ƙirjin ta idanun ta na zubar da hawayen tausayin matar da kuma ƴaƴan dake hannun ta da yanzu suka zama marayu, bata san wane irin marasa imanin mutane ne yanzu ke rayuwa a wannan duniyar ba, ko ina cike da azzalumai, kowa ba ya tausayin kowa, kowa ba ya san kowa, kowa kan sa kawai ya sani, ya ilahi duniya ina zaki damu.

 

Ganin kuka me sauti na neman kufce mata yasa ta miƙe wa ta shiga tafiya a hankali cikin takatsantsan dan ba zata so abinda ze jawo hankalin mutanen cen ba balle har su kashe Innocent babies ɗin hannun ta, tafiya me ɗan nisa tayi kafin ta fita daga dajin ta yanka ta cikin gonaki ta shiga ƙauyen su, garin yayi luf luf babu rana se iska me daɗi kasancewar magrib ta doso kai dan yanayin na nuna alamun be fi karfe biyar da rabi zuwa shida na yamma ba.

 

Ba tare da  tunanin komai ba ta nufi gidan su da yake babban gida kuma ginin ƙasa ba, sallama ta shiga kwaɗa wa a ƙofar babban zauren su sedai ba wanda ya amsa mata kamar ko da yaushe, sa kai tayi ta nufi sashen da take rayuwa yayinda tsirarun mata da yaran dake babban tsakar gidan bin ta da kallo suna maganganu ƙasa ƙasa ganin ta goyon jaririya ga kuma wata a hannun ta.

 

Wata sallamar ta kuma yi a ƙofar sashen su sedai nan ɗin ma ba’a amsa mata ba se dogon tsakin da aka ja, kai a ƙasa ta shiga ƙofar tana tafiya a hankali kamar wata ɓarauniya ko wadda ƙwai ya fashewa a ciki, inna mariya dake tsugunne bakin malalallabta tana rege shinkafa ta tsugunna har ƙasa tana gaisar wa sedai maimakon amsa se zagi da yarfe ne ya biyo baya kamar yadda ta saba

 

“An dawo daga yawon ta zubar ɗin da sunan Makarantar boko, atoh mun dai sani ba wata wata boko se tambaɗewa da karuwa ci da ake yi ake fake wa da boko, wa ya sani ma ko an yi guzurin ɗan boko a ciki”.

 

Bata wani damu da abinda Inna mariyar ta faɗa ba dan ba yau ta saba ba, ba ita ba kusan duk ƴan gidan ma haka suke cewa, bata damuwa ne dan tasan ita karatu take yi ba yawon kafuwan ci ba kamar yadda suke faɗa, gaban ta ne yayi kwanci kwanci ya faɗi lokacin da yarinyar da ta Saɓa a kafaɗa ta calla wani irin kuka me sauti cikin Muryar ta ta jarirai, ashe ta daɗe da farkawa tun lokacin da sanyin la’asar ya buge ta amma bata dawo hayyacin ta ba se yanzu.

 

Zabura Inna mariya tayi tana dafe ƙirji cikin zare ido

 

“Me nake ji haka kamar kukan jarirai?”.

 

Ta faɗa tana juyowa ga yarinyar da tayi saƙare cikin tashin hankali, bata yi tunanin me ze je kazo ba lokacin da ta karɓi yaran, bata yi tunanin abinda ze iya faruwa ba dan a lokacin ba abinda ke ranta face ganin ta tseratar da rayuwar su, sam a lokacin ta manta da wane kalan mutane take rayuwa se yanzu da yarinyar ta shiga kuka kamar yadda aka san jarirai ƴan watannin ta da haihuwa.

 

“Innalillahi, a’uzubillahi ni mariya jikar me shanu, me nake gani a hannun ki haka SALAME kamar jaririya?”.

 

Yarinyar da aka kira da salame bata iya tace komai ba yarinyar bayan ta itama ta shiga kuka alamun itama ta farfaɗo, gaba ɗaya se hankalin ta ya rabu kashi kashi, ga kukan yaran ga kuma kururuwar da Inna mariya ke yi mata, bata san me yasa taji zuciyar ta na zafi ba jin kukan yaran dan har tsakiyar ranta da kanta take jin kukan dan haka d sauri ta zauna tana ɗora ta hannun ta kan laps ɗin ta ta shiga kiciniyar kunto ta bayan ta, jijjga babyn ta shiga yi tana tapping ta kan cinyar ta dan tayi shiru shiyasa sam bata lura da mutanen da suka taru saman kan ta ba se da Muryar kawu Habibu ta ratsa kunnen ta lokacin da ya daka mata razananniyar tsawar da ta sa har ta kusa yar da ƴar hannun ta kafin tayi saurin tare ta………………..✍🏻

 

 

Ya Rabb ka tsare mu daga sharrin zuciyoyin mu ka hana mu hassada, baƙin ciki da ƙyashi ga nasara da ɗaukakar wani, Ameen.

 

 

©️ Ouummey 📚✍️.

 

 

☑️Ote, Comment, share and patronize fisabilillah.

[03/12, 11:30 am] +234 901 310 1854: Ouummey 02 [ 10/11/2022 12:16 PM ]

 

★★★ *ANJANE* ★★★

(Rashin sani)

★★★★★★★★★

 

 

_*PAID BOOK*_

 

 

Story/written by Ouummey.

 

Wattpad @ouummey.

 

 

 

From The author of:

 

*HAƘORIN DARIYA*

*ƘASAR MU A YAU*

*BA NI DA LAIFI*

*SARAKI (the accused prince)*

*ABOTA CE KO SOYAYYA*

*And now…….ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

 

 

 

 

 

 

 

FREE PAGE 002

 

 

 

 

 

 

 

 

 

________________________📖 “Dama na daɗe da sanin lalacewar ki kawai kika saka gaba shiyasa kika dage ke se kin yi wani karatun boko saboda ki samu mafaka dan kin san a nan bazan lamunci wannan iskancin ba shi kuma megari har da wani ɗaure miki katara, zaki faɗa min wanda yayi miki cikin da kika haifi waɗannan shegun ƴaƴan ko se naci uban ki, shegiya ƴar iska kawai”.

 

Kakkarwa jikin ta ya shiga yi haka ma bakin ta rawa yake tsabar tashin hankali, da ƙyar ta iya buɗe bakin ta tana sharar hawaye

 

“Kwarankwatsa ni ba ƴar iska bace kawu, wallahi bani na haifi ƴaƴan nan ba ni ban taɓa iskanci ba ku yarda dani”.

 

Wani tokari kawu Adamu ya sake mata a bakin da take magana take kuwa bakin ya fashe ya shiga fitar da jini, dafe bakin tayi da sauri hawayen ta na ƙaruwa saboda azaba

 

“In ba ke kika haife su ba to tsinto su kika yi?, Kaji min sheɗaniyar yarinya, wato har kin san ki buɗe wa wani gardi cinyoyi ko, Abu bani icen can me wuta, yau in baki faɗi gaskiya ba ba abinda ze hana ni kwaye fatar bayan ki da wuta”.

 

Kukan ta ne ya ƙaru ta shiga rantsuwa da magiyar su yadda ita ba ƴar iska bace sedai ina no one is willing to listen to her, ɗebe yaran Inna mariya tayi ta dangwarar da su a dandaryar jar ƙasar wajen shi kuwa kawu habibu ya shiga dukan ta da wannan icen,ihu ta shiga yin tun ƙarfin ta har Muryar ta ta dishe amma ba wanda yaji ko ɗigon imani ko tausayin ta balle ya bawa kawun haƙuri.

 

Seda ya dake ta iya yadda yaso kafin ya jefar da icen dake fitar da hayaƙi alamun akwai wuta a jikin sa har lokacin ya dubi kawu Adamu

 

“Kaje yanzun nan ka sanar da maigari kafin su iro su dawo mu tafi mu kai shegun yaran can, mukam Kamisu ya mutu ya bar mana annoba wallahi, haka kawai muna zaman zaman mu ya haifo shegiyar ɗiyar sa ya mutu ya bar ta gashi nan ta jawo mana abin kunya da Allah wadai zata lalata wa ƴaƴan mu suna”.

 

Da kallo kawu Adamu yabi bayan kawu habibu da ya fice yana ƙananun magana saboda masifar da ke cin sa a rai kafin ya maida hankali inda Salame ke tsugunne a takure kayan jikin ta duk sun yayyage saboda dukan da tasha, tsaki yaja ya sa ƙafa ya fice yana shura siɗaɗɗun takalman sa da suka ci duniya dan ƙullin leda a jikin su ya fi biyar.

 

Feƙeƙƙen zanin ta Inna Abu ta tattare tana kaiwa zaune kan jar ƙasar da ta kwanta saboda ruwan da aka yayyafa mata

 

“Ni yanzu damuwa ta saurayin A’ilo kar yace ya fasa auren ta saboda kayan kunyar da wannan annobar ta jawo mana”. Ta ƙarashe tana jefa wa Salame dutsen da yayi nasarar sauka a kan ta take kuma kanta ya fashe sedai ba’a iya banbance yadda yake zubar da jini dan ciwukan jikin ta ma duk jinin suke fitar wa so se ya haɗe.

 

“Sauƙin abin ma shima ƙanwar sa wasila ta taɓa yin cikin nan kin ga ba zasu ɗaga mana kai ba”.

 

Cikin rashin jin daɗin maganar ta Inna Abu ta haɗe rai dan duk abinda ze sa a Faɗi aibu ko a soki saurayin A’ilo bata so dan ba ƙaramin morar shi suke yi ba, wannan maganar da Inna mariya ta fara yasa ta miƙe tana ficewa da ƙafar ta da duk take cike da faso manya manyan saboda rashin sa takalmi.

 

Hararar ƙofar da ta fita Inna mariya tayi dan ba ƙaramin haushin Inna Abun take ji ba saboda yadda take musu ɗaukar kai kan saurayin A’ilo dan gaskiya duk gidan ba wanda ya taɓa saurayi me maiƙo kamar ta dan ɗan gidan maigari ne, kukan da yaran suka kuma sanya wa a tare yasa taji takaicin ta ya ƙaru.

 

Ji take kamar taje ta shaƙe su har se sun mutu sedai rashin imanin ta be kai haka ba so se ta dubi Salame da bata ko numfashin arziƙi saboda wahala ga kuma azabar da ciwukan jikin ta ke mata

 

“Kin tashi kin kwashe wannan tsiyar dake neman hanani nutsuwa ko se na kwashe su na watsa a rijiya?”.

 

Duk yadda jikin ta ya kai ga nauyi saboda dukan da tasha ban da azabar da take ji amma haka ta miƙe ta shiga takawa cikin ƙarfin hali har ta kai inda suke kwance se ciccilla hannaye da ƙafafu suke yi, a kafaɗa ta ɗora ɗaya tana runtse ido saboda zafin da taji dan akwai ƙuna a wajen ɗayar kuma ta rungume ta wuce akurkin ɗakin ta da ke daf da zubewa saboda yadda ya takwarkwashe, duk da gidan dukan sa na ƙasa ne amma babu ɗaki mafi muni kamar nata dan madafar su ma tafi shi nesa ba kusa ba.

 

Kan yagalgalallen buhun da take kwanciya ta shimfiɗar da yaran kafin ta kuma fice wa ɗauko jakar buhun ta, cikin ɗan hanzari ta ƙara sa ta ɗauke jakar ganin Inna mariya bata wajen da alamu ta shiga bayan gida ne.

 

Cikin cije baki ta kai zaune gefen yaran ta shiga bin su da kallo tana yaba kyan su a ranta kafin kuma ta ji wani sabon so da tausayin su na ratsa ta tuno yadda aka kashe mahaifiyar su,

 

‘duk abinda ze faru bazan yarda in rabu da ku ba, mutuwa kawai zata  raba tsakanin mu insha Allah”.

 

Ta faɗa a ranta tana jingina da bangon ɗakin sedai da sauri ta janye jin raɗaɗin da ya ratsa kwanyar ta hakan na shaida mata akwai ciwo a nan ɗin ma.

 

Ƙofar ɗakin taje ta saya kafin ta tuɓe kayan makarantar jikin ta da suka yagalgale saboda ƙunan wuta da kuma dukan ice, wani koɗaɗɗen zani ta ɗauko wanda dama uku ne kawai da ita kuma da su take rayuwar yau da gobe ta ɗaura, wanka take son yi sedai ta san yau ko mutuwa zata yi ba zata samu ruwan zafi ba se kawai ta ƙudure yi da na sanyin ta fita zuwa ƙatuwar rijiyar su dake tsakiyar gidan.

 

Babbar rijiya ce dan dukkan su na iya ɗiban ruwa a lokaci ɗaya dan tana ɗaukar guga sama da biyar, ƴan mata biyu ne suke ɗiban ruwa suna hirar su, tun da ta nufo wajen suke dariya suna nuna ta, duk da bata jin me suke cewa dan da ɗan tazara tsakanin su amma tasan ba abu me kyau suke faɗa ba, hakan ba sabon abu bane a wajen ta dan duk faɗin gidan ba zata iya ɗaga mutum ɗaya tace gashi me son ta da ƙaunar ta bane, daga masu ƙi da tsanar ta se kuma ƴan ba ruwa na sune wanda ba zasu dake ta ba ba zasu zage ta ba sedai ba zasu taimaka mata ba irin su kawu Adamu kenan.

 

Ƙaramin guga ta ɗauka ta zura cikin rijiyar ignoring all the curses da suke rending mata ta shiga ɗiban ruwan ta dan tun da da basu samu dalili ba ma ƴar iska suke ce mata balle yanzu da ta zo da ƴaƴa har biyu gida,

 

“Iyayen karuwa dai sun yi asarar haihuwa, ke in kika bibiya ma sule me shago ne yayi mata cikin da ta haifi yaran nan dan kin ga shine kaɗai yake kulata a garin nan”.

 

“Kai anya kuwa sule ne, kin ga fa Inna tace yaran sun yi kusan watanni biyu da haihuwa shi kuwa ai rabon shi da ita tun da tayi ƙaryar jarabawa ta zauna wata goma a makaranta”.

 

“Eh ba mamaki ma a can wani malamin ya ɗirka mata cikin, kin san dama buba ya faɗa mana kafirai ne”.

 

Haka suka cigaba da maganganun su na aibata ta amma bata kula ba ta ɗibi ruwan da take buƙata ta koma sashen su, da saɗab saɗab ta zagaya wani ɗan fili dake bayan ɗakunan su ta yaye zanin ta kwara wa jikin ta ruwan, sauƙin ta ruwan rijiya akwai ɗumi ban da haka kuma yau ɗin an yi rana sosai shiyasa ya sake yin ɗumi kamar an gauraya dana zafi.

 

Zanin ta mayar tana barin cinyayyen bokitin a nan wajen ta koma ɗaki bayan ta leƙa ta tabbatar Inna mariya bata wajen, yarinyar da ta fi yin kuka ta ɗauka ta shiga jijjigawa har ta yi baccin wahala dan yunwa suke ji sedai bata san me zata basu ba, haka tayi wa ɗayar ma ta samu itama tayi bacci.

 

Tuno da wata hamsin a jakar ta yasa ta maza ta jawo jakar ta shiga zazzage ta, kayan sarƙar babar ƴan biyu da suke zube a ƙasa ta ɗaga ta shiga kalla tana yaba kyan su kafin ta shiga hawaye sanin me su ta daɗe da zama gawa, hawayen ta share ta shiga tattara su tana mayar wa haka dan ta san a yadda suke da kyau muddun Inna mariya tayi ido biyu dasu shikenan sun zama nata.

 

Hamsin ɗin ta shiga juya wa a hannun ta tana tunanin ta yadda zata fita daga gidan ba abin ta haura ta katanga ba jikin ta na mata ciwo.

 

Dan son samun sauƙin fita ta siyo musu kunu ta basu ta ƙara sa inda take ajiye gishiri dan tasan hakan kawai zata yi taji sauƙin raɗaɗin ciwon har ta iya haura katanga zuwa anjima.

 

Gishirin ta ɗauka tare da kwance ƙullin da tayi wa ledar ta ɗebo a hannun ta tana runtse ido saboda azabar da ta dan zata ji ta kai kan guraren da ƙunar take, duk yadda zugi da raɗaɗi ke ratsa ƙwaƙwalwar ta bata dena ba har se da ta gama kafin ta kwanta tana fidda numfashi ɗaiɗai kamar me cutar asthma.

 

Wannan horon kawu habibu ne lokacin da tana hannun matar sa Inna Abu kafin ta dawo hannun kawu iro, tun tana yarinyar indai tayi laifin da aka dake ta haka kawu habibun ze ɗebo gishiri ya dinga danna mata a wajen ciwon, karon farko da ya fara yi mata da hankalin ta suma tayi amma ko da ta farfaɗo haka ya sake yi mata.

 

A lokacin seda ta suma so uku amma ba hakan yasa ya fasa abinda yayi niyya ba, tun daga lokacin kuma yake mata wannan azabar, tun tana damuwa tana shiga tashin hankali har tazo ta daina ba kuma wai dan bata jin zafi ba se dan ta riga ta saba danne zafi da raɗaɗin a ranta.

 

Tsawon lokaci kafin taji kamar an yi ruwa an ɗauke duk ta daina jin azaba shigar gishirin jikin ta haka kuma tuni waccan azabar ta disashe ta zafin ciwon shiyasa se ta ke jin yanzu kamar babu ciwo a jikin ta, koɗaɗɗen zanin ta ta maida tare da zura rigar sa ta salallaɓa ta fita jin an shiga sallar magrib, ta katanga ta haura kamar yadda ta ƙudira.

 

Gudu ta sha sosai kafin ta kai ga isa wajen Sare me kunu, hamsin ɗin ta miƙa mata tana numfarfashi tare da faɗa mata ta bata na Naira goma ƙullin biyar biyar, a farar leda aka ƙulla mata ko wanne kafin a saka a baƙar leda ta miƙa mata,da hanzari ta karɓa sannan ta wuce wajen sule me shago, bata tsaya amsa tambayoyin da yake mata ba na ance ta dawo da ɗanyen goyon shegun yaran da ta haifa har biyu ba tace ya bata siga na goma se madara ta Ashirin.

 

Madarar kusan Naira ɗari ya zuba mata haka sugan ma ya fi na hamsin ya bata yana faɗin tabar kuɗin kawai dan ba ƙaramin so yake wa Salame ba, godiya ta masa ta juya zuwa hanyar gidan su cikin gudu sosai har ta kai, ta katanga ta koma kamar yadda ta fita dan ba wata katangar arziƙi bace kun dai san fences ɗin ƙauye.

 

Hango Inna mariya a Zaune kan tabarmar da take zama daga bakin ƙofar ɗakin ta yasa ta rasa yadda zata yi ta wuce, ta daɗe tsaye kafin taga shigowar kawu iro sashen nasu, kayan hannun sa Inna mariya ta karɓa ta shige ɗaki tana masa sannu da zuwa shima ya mara mata baya, da wannan damar ta samu ta saci kofi ɗaya cikin kofunan sashen ta shige ɗaki da sauri.

 

Seda ta saya ƙofar duk da ba mai shigo nata dan ko neman ta Inna ke yi sedai tai ta ƙwala mata kira, kunun ɗaya ta juye cikin kofi ta sa sigar kaɗan ta juya da wani kara kana ta ɗau yarinya ɗaya ta fara tashin ta har se da ta buɗe ido, buɗe baki tayi da nufin komai Salame ta maza ta sa mata kofin a baki, cikin yunwar da ta galabaitar da ita ta shiga sha ba wani musu, sosai tasha kunun kafin ta saki tana sa harshen ta tana lashe saman cute small lips ɗin ta, murmushi Salame tayi ganin yarinya ma ta san zaƙi dan ta tabbatar da bata sa sugar ba baza ta sha da yawa haka ba.

 

Ajiye ta tayi inda yarinyar ta shiga cilla ƙafafu tana wasa da hannayen ta, ƴar uwar ta ta ɗauka itama ta tashe ta tare da bata kunun, itama ta sha da ɗan yawa duk da be kai yawan na ɗayar ba, ajiye ta ta ƙara ɗaya na biyar ɗin kan wanda suka rage ta ƙara sugar ta shiga sha itama dan ta san yau kam ko itace tafi kowa maita ba zata samu abinci ba a gidan nan, da ɗan dama ta rage saboda kar yaran su ji yunwa su nema kuma babu, jakar ta ta ɗora ta rufe cup ɗin dashi sannan ta juya ga yaran ta ƙure su da kallo.

 

Kyawawan yara ne Masha Allah kamar ƴaƴan turawa, ba ramammu bane dan da ƙibar su daidai sanye da kayan masu kyau suma kansu an kakkama da soso da ya daɗa ƙara musu kyau, addu’a ta shiga yi musu tana tofa masu na Mayu da baki dan akwai Mayu sosai a ƙauyen.

 

Seda ta gama yi musu addu’a sannan tayi wa kanta ta nemi waje kan buhun ta ta kwanta dan zannuwan ta biyu ta haɗa ta shimfiɗa wa yaran da har yau bata san sunan su ba dan maman su bata faɗa mata ba ita kuma bata san da sunan da zata kira su ba.

 

Washegari kuwa tun kiran sallar biyu da ta tashi bata koma ba, tana idar da sallah ta fita tsakar gidan su ta hau aikace aikace kamar yadda ya zame mata wajibi muddin tana garin, tana gama wa ta ɗau bokitan su ta fita rijiya ta shiga jido ruwa, se da ta cika ko ina kafin ta hau kunna ruwan komo, tana juye kokon ta kai duban ta kan ƙofar su Inna mariya dake kulle har lokacin, da sauri da sauri ta dafa ruwan zafi ta kai ɗakin ta ta ɓoye cikin wata madaidaiciyar roba sannan ta dawo wajen ta kashe wutar.

 

Ɗakin ta ta koma ta surka ruwan a bokitin ta ta shiga yiwa yaran wanka, wankan jariri ba sabon abu bane dan tun tana shekara bakwai aka fara bata rainon yara haka kuma tana shekara sha biyu suka fara sa ta wankan jariran su, tana gamawa Hassana kamar yadda ta raɗa wa wadda taga tafi girma a idon ta ta ɗau Ussaina ta mata ita ma sannan ta ɗau ruwan nasu ta shiga banɗakin su ta kwarawa jikin ta ta maza ta fita tare da maida bokitin ta bayan ɗaki.

 

Ko da ta koma tuni yaran sun koma bacci da alama sun ji daɗin wankan, murmushi tayi tana jan kumatun Ussaina daidai lokacin da taji Muryar kawu habibu cikin ihun kiran sunan ta…………………..✍🏻.

 

 

 

 

©️ Ouummey 📚✍🏻.

 

 

 

 

 

 

☑️Ote, Comment, share and patronize fisabilillah.

[03/12, 11:30 am] +234 901 310 1854: Ouummey 03 [ 10/12/2022 12:08 PM ]

 

★★★ *ANJANE* ★★★

(Rashin sani)

★★★★★★★★★

 

 

_*PAID BOOK*_

 

 

Story/written by Ouummey.

 

Wattpad @ouummey.

 

 

 

From The author of:

 

*HAƘORIN DARIYA*

*ƘASAR MU A YAU*

*BA NI DA LAIFI*

*SARAKI (the accused prince)*

*ABOTA CE KO SOYAYYA*

*And now…….ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

 

 

₦300 to the below account details

Rabiatu Abdullahi

2391368231

ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.

 

 

 

 

 

FREE PAGE 003

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

_________________________📖 A gigice ta Fito daga ɗakin har tana yin karo da durƙusasshen bangon ɗakin wanda banda tsari da kariyar Ubangiji wata iska me ƙarfi nan in aka yi ze zube ne.

 

A firgice ta ja baya tare da maƙewa jikin garun ganin dukkan su mazan gidan ne a wajen wanda tasan ba dan kowa suka haɗun ba se dan ita.

 

Wani irin rawa jikin ta ya ɗauka haka ma zuciyar ta ta shiga addu’ar Allah ya taimake ta kar su ƙara mata wani ciwo da nauyin jikin da sabon dukan da ta san in ba Allahn ne ya tare ba se ta sha shi.

 

“Shegiya munafuka me suffar muminai, tana sussunkwi da kai tana baɗala a haka kuma take cutar wasu suke mata kallon saliha ta gari se gashi ƴaƴan namu dai da ake zagin sune nagarin, kin matso kusa ko se na harbo ki da ƙafa ta, tambaɗaɗɗiya kawai”.

 

Da sauri ta matsa dan ta san kaɗan kenan daga aikin baba iro ya harba tan kamar yadda yace, ƙasa ta sa gwiwoyin ta tare da kai kanta ƙasa abinda su kuma suka fi tsana kenan dan sunce hakan wani salo ne na munafurci.

 

“Me zata zauna tayi mana a nan iro, kawai taje ta kwaso ƴaƴan shegun nata mu wuce wajen megari dan wallahi ji nake kamar in watsa a turmi in dake shegu ita kuma uwar in shaƙe ta har se ta mutu”.

 

Baba habibu ya faɗa da iya gaskiyar sa yana demonstrating da hannayen sa, ita dai tana duƙe har lokacin dan ba’a ce ta tafin ba shawara ce suke yi a tsakanin su.

 

Uban dundu Inna mariya ta ɗuma mata ta kuma bita da zagi

 

“Ka ga min fitsararriyar da ba zata rama ragon sunan ta ba, wato ga sa’annin matacciyar uwar ki na magana shiyasa kika zauna kina kallon mu, to bari in kwaso shegun yaran in watsa a masai muga ta tsiya”.

 

Ai kafin inna ta gama rufe bakin ta tuni ta ɗiba tayi ɗakin a guje jin za’a watsa mata su a masai, Hassana ta riƙe a hannu yayinda ta goya Ussaina dan ta fahimci Hassanar tafi haƙuri dan bata fiya kuka ba se in Ussaina nayi ta kama.

 

A saɗaɗe ta fito dasu wannan karon kanta a daidai tana bin su da kallo har ta kai gaban su ta sake tsugunnnawa, a yanzu kam Inna A’i da kallon da take bin su dashi ya ɓata wa rai itace ta kai mata duka a fuska, ba wai mari ba dan ba kuncin ta ta nufa ba kuma ta na sane ta kuma same ta a idon ta na dama, duk yadda idon ya ɗau raɗaɗi bata ko motsa hannun ta da niyyar taɓa wa ba.

 

Ta daɗe da sanin idanun ta na ɗaya daga cikin abubuwan dake jawo mata tsana, kyara da tsangwama a cikin gidan, wato wani irin ido Allah ya halitta mata me kamar na maciji ko mage za’a ce, dan ƙwayar idon ta ba baƙa bace haka ma ba brown ba, wata color so similar to golden, sedai golden ɗin irin me ɗan duhu kaɗan.

 

So da yawa su kawu, matan su ko ƴaƴan su sun sha goranta mata yanayin idanun nata duk tayi laifi, kai koma bata yi ba indai zasu haɗa ido se sun tanka mata, shiyasa tun lokacin da malamin Islamic studies ɗin su yayi musu addu’o’i ciki har da na baki shikenan ta ke yi, la haula kuwa kowane dare se tayi adadin da bata sani ba dan ba carbi ne da ita ba ta shafa a fuskar ta kafin ta kwanta haka kuma da asuba in ta tashi.

 

Bata san a wajen wa ta gado irin wannan idon ba cikin iyayen ta dan bata yi wayo da ko ɗaya ba sedai da alama ba wajen babanta da yake ƙanin baba Habibu da baba Adamu wa ga baba iro ba ne, tafi kyautata zaton wajen mahaifiyar ta ta gado ko kuwa dai Allah ne yayi mata nata halittan daban, ko a makaranta seda hakan yaso ya zame mata barazana dan har se da shugaban makarantar ta tsawatar tukunna shiyasa har tayi ta gama bata da wasu cikakkun ƙawaye sedai na gaisuwar mutunci, kowa gudu da tsoran ta yake saboda kalar idon ta da ba’a saba gani ba cikin jama’a, tun bata saba da hakan ba har ya zo ya zame mata jiki ba ta ma damuwa.

 

Zama suka yiyyi kan tabarmin da ke shimfiɗe a fadar me gari kafin suka shiga kai gaisuwa shikuma dattijon dake amsa sunan maigari na zaune kan kujerar ƙarfe kan sa ɗaure da rawani yana amsa musu.

 

Kafin kace me jama’a sun fara ciki dan haka ake wa duk ƴaƴan da suka yi ciki a garin amma fa marasa galihu dan da Allah yasa ƴar maigarin tayi shiru kake ji wai maye yaci shirwa, karuɗuf ƴar magulmaciya tayi ciki, ba wanda yasan da zancen seda faɗan kishiyoyi ya haɗa shima kuma har rana wata yau ba’a yi irin wannan zaman a kanta ba gashi har ta haife tuni.

 

Seda fadar ta gama cika sannan maigari ya fara sanar da abinda ya tara su wato dai batun cikin da Salame tayi ta haife batare da sanin su ba har gashi ƴaƴa sun kusa rufa watanni uku, hayaniya ce ta shiga tashi inda mutane da yawa ke Allah wadai da ita yayinda ƙalilan da abun ya faru kan ƴaƴan su suma suka shiga yi mata fatan Allah ya shirya a ganin su ai hakan ƙaddara ce (saboda ya faru ga nasu).

 

Se da gurin ya lafa kafin maigari ya shiga jawabin sa kamar yadda ya saba

 

“Bisa ga tsari na wannan gari bamu yadda da abun kunya ba ko yaya yake kuwa dan haka zamu aiwatar da abinda muka saba yi duk sanda aka samu irin wannan san zuciyar, a yanzu haka zamu karɓi ƴaƴan a kai su can nesa inda ba wanda ze san nata ne balle ayi mana gori kamar yadda muka saba tun da wannan shine karon ta na farko, da na biyu ne kuwa ko sama da haka to fa kun san hukuncin kora ne a kanta”.

 

Yana gama faɗar haka wasu fadawan sa suka nufo ta da zummar amsar yaran inda ita kuma cikin matsanancin firgici da tashin hankalin jin abinda ake kiran ze faru ta sake ƙanƙame ƴaƴan ta ta shiga kurma ihun ba ta yadda ba ba zata bayar dasu ba, kowa a gurin ya shiga mamakin abinda tayi, a ganin su ƴaƴan shegen take ihu dan za’a raba ta dasu, to meye abin so cikin ɗan shege?!.

 

Muryar Salame da fiye da rabin ƙauyen zasu ce basu taɓa ji ba se gata ana jiyo ta tun daga farkon hayin maigari saboda yadda take ihun da iya ƙarfin Muryar da Allah ya bata, duk irin tsawa da zagin da babannin ta ke mata bata ma san suna yi ba balle ta saurare su ta daina ihun har se da maigari yasa fadawan su janye daga kusa da ita kafin tayi shiru ta sake matse ƴaƴan tana sauke numfashi sedai sam hankalin ta be kwanta ba dan tasan ba wai an ƙyale ta bane.

 

Seda megari ya gama ƙare wa jama’ar wajen kallo kafin ya muskuta yana zarar ido

 

“Tun da har wannan yarinya taƙi yadda da hukuncin mu to mun bata zaɓi biyu kuma a yanzu a nan gurin zata bayyana mana wanne ta ɗauka, na ɗaya ko dai ta bada yaran nan ayi kamar yadda aka saba dasu ko kuwa na biyu ta tattara ta bar mana garin ma’ana mun kore ta daga ita har ƴaƴan haka kuma duk sanda muka sami labarin shigowar ta to tabbas hukunci mai tsananin tsauri ya hau kanta, wannan sune zaɓin”.

 

Shiru kowa yayi kallo ya koma kan Salame da take jin komai da aka faɗa haka kuma ba tare da second thought na halin da ita ko yaran zasu shiga ba sanadin zaɓin ta ta buɗe baki ta zaɓi abinda take ganin ya fiye mata

 

“Ba gari ba ko ƙasa ce zan iya haƙura in bar ta akan ƴaƴana dan haka na zaɓe su akan komai da nake dashi ciki kuwa har da asalina”.

 

Kusan a tare duk su baba Habibu, baba Adamu da baba iro suka miƙe jin abinda ta faɗa, wato ta zaɓi ta bar garin saboda ƴaƴan ta haka ta zaɓe su akan Asalin ta wato su dangin ta kenan.

 

Shi kan sa maigari ba haka yaso ba dan a tunanin sa zata zaɓi bayar da yaran ne tun da in ta bar nan wa ta kama?, Bata da kowa banda dangin baban ta, mahaifiyar ta kuwa bama ƴar nahiyar bace, a yawon tuƙin babban mota baban ta ya auro ta dan haka ba wanda yasan komai a kanta kamar yadda basu faɗa wa kowa komai game da ita ba har kuwa ranar da ta bar duniya sanadin hauka da aka sa mata da ya kai sedai a ɗaure ta a ɗaki.

 

Umarni me gari ya bayar kan dogarawa su bita gida ta ɗebi abinda zata ɗauka a rakata bakin gari ta tafi sedai fir baba iro yace ba abinda ta aje a sassan sa bare ta koma ɗauka dan haka su rakata bakin garin kawai, bata Musa ba ta shiga gaba dogaran na binta a baya dan tun da ta shafa taji jakar makarantar ta na jikin ta hankalin ta ya kwanta.

 

Seda suka tabbatar tayi nisa da gari kafin suka juya zuwa gidan maigari suka sanar dashi an cika umarnin sa inda ya amsa da cuskunenniyar fuska dan ba haka yaso ba.

 

Abinda mutanen garin basu sani ba shine maigari siyar da jarirai yake wa ƴan birni da suka rasa haihuwa da kuma masu aikin asiri though be san me suke dasu ba, shidai kawai a bashi kuɗi shikenan, da an samu yarinyar da tayi ciki se ya hana a zubar yace ta haife shi kuma ya sami ƙarin jari.

 

Lokutan da kuma ba’a samun na banza hatta na sunna kaiwa yake dan akwai ungozomar da suka haɗa kai in ba na shege se a kai na sunna, yadda suke yi kuwa se an gama haihuwa lafiya lafiya se ta shafawa yaron wani magani da ta samo a wata asibiti dan ta taɓa zaman birni shikenan yaro se ya birkice da koke koke, ƙin kama nono da sauran su daga nan se a nufi wajen babban me maganin da suka yadda dashi da dukkan imanin su, dake shima nasu ne se yace ai ɗa ko ƴa na aljanu ne sun ɗauke naki sun musanya miki dan haka maza maza akai daji kaza daidai wuri kaza a ajiye musu kayan su, se an kai an ajiye ita kuma tabi dare ta ɗauka ta kaiwa maigari cikin gidan sa na sirri dake can bayan gari gefen dajika inda yake harƙallar sa.

 

Guri ta samu ta zauna tana haɗiyar busasshen yawu dan gaba ɗaya bakin ta ya bushe da ƙishirwa, tafiyar ƙafa sabon tace dan haka ba zata ce ta gaji ba sedai rashin ruwan ke neman kassara ta ga kuma ƴaƴa har biyu gaba da baya ga jaka me nayi se abin yayi mata yawa.

 

Mutsu mutsun Ussaina da taji yasa ta san ta farka dan haka ta sauke ta dan ta ɗan huta da goyon sedai ita ba hutun take nema ba abinci take nema da bata samu ba kuwa ta buɗe baki ta shiga canyara kuka da ƴar Muryar ta na jarirai, kukan Salame ta shiga yi itama dan abin ya haɗe mata goma da ashirin.

 

Haka Ussaina tayi kukan ta har ta gaji baccin yunwa ya ɗauke ta kafin itama ta haƙura ta goge fuskar ta ta maida ta baya dan ba zata iya riƙon hannu ba ta cigaba da tafiya.

 

Se da rana ta faɗi gaba ɗaya kafin ta shiga wani ƙaramin ƙauye dan gaba ɗaya gidajen dake ciki basu fi a ƙirga ba haka kuma daga ganin gidajen su kasan har yau su kam suna cikin duhun rayuwa wato ba wayewa ko ta misƙala zarratin dan duk bukkoki ne ba gidan ko ƴar jar ƙasa ɗaya.

 

Kan wani kututturen dabino ta kai zaune tana ajiyar zuciya tare da numfashin ta dake fita ɗaiɗai saboda wahala da jigatuwa, nan take zaune har se da wani tsoho ya zo wucewa ya ankara da ita kafin ya ɗan matsa nesa da ita ya shiga ƙare mata kallo Sannan ya gyaɗa kai ya wuce.

 

Be daɗe ba ya dawo dashi da wasu dattijan da kuma matasa suka dinga magana da Yaren su da bata san wanne bane kafin ɗaya daga cikin matasan ya nufi ta.

 

Tambaye ce daga ina take, me ta shigo nema a shiyyar su, me take buƙata haka dai, amsa ta bashi da sunan garin su wato BA MUNI wanda sunan ya samo asali ne daga yadda duk wani ɗan garin yake kyakkyawa sedai wani yafi wani amma mummuna kam babu sedai ko baƙo shiyasa suke saurin gane baƙo a cikin su.

 

Iyayen sa ya koma ya sanar da amsar da ta bashi, sunan garin su da kuma taimakon da tace ta zo nema, seda suka kuma sake zantawa cikin dai Yaren nasu kafin wani saurayi ya tafi be daɗe ba ya dawo da wata tsohuwa sedai ba tukuf ba, nuna mata ita suka yi inda ita kuma ta ƙarasa ta kamata ta miƙe kuma cikin fara’a tace mata

 

“Kunto min jikokin nawa mana, da alamu sun daɗe a goye”.

 

Bata ƙi ba ta kunto Hassana ta bata ta bar Ussaina

 

“Ita ma sauko ta ta huta hakana”.

 

“Tana da kuka ne Inna”.

 

Murmushi innar tayi alamun ta gane kafin suka shiga tafiya hannun ta dafe da zanin ta dan cikin sa ta ɓoye jakar ta da zasu je wajen Maigari ashe Allah ne yayi suna da rabo da yadda kawu iro yace ba zata koma masa gida ba shikenan sun salwanta.

 

Bukka ce me ɗan girma suka shiga sedai abin mamaki har dasu gadon ƙarfe a cikin ta, fita Inna kamar yadda ta kira tsohuwar tayi bayan ta kwantar da Hussaina tsawon lokaci tukunna ta dawo da bahon katako a hannu, ruwa ne masu zafi a cikin sa haka kuma ba fari bane da alamun an zuba wasu abubuwan banda kuma ganyayyaki dake ciki, tuɓe Hassana tayi ta mata wanka da yasa yarinyar ta ringa sauke ajiyar zuciya a jejjere, Ussaina kam ta sha ihu da ana yi mata dan alamu sun nuna ba su taɓa shiga ruwa masu zafi haka ba.

 

Se da ta tabbatar sun gasu kafin ta ɗau abin ta fice inda Salame ta yi saurin isa ta ɗau yarinyar ta shiga jijjiga da lallashi har tayi shiru,

 

“Ga can ruwa ki je kiyi wanka kema ko kya watsar da gajiya”.

 

“Toh Inna”.

 

Tace tana kwantar da Ussainar a hankali gudun kada ta tashi daga ɗan baccin da ya fara sanɗar ta……………………….✍🏻.

 

 

 

 

©️ Ouummey 📚✍🏻.

 

☑️Ote, Comment, share and patronize fisabilillah.

[03/12, 11:30 am] +234 901 310 1854: Ouummey 04 [ 12/1/2022 1:12 PM ]

 

★★★ *ANJANE* ★★★

(Rashin sani)

★★★★★★★★★

 

 

_*PAID BOOK*_

 

 

Story/written by Ouummey.

 

Wattpad @ouummey.

 

 

 

From The author of:

 

*HAƘORIN DARIYA*

*ƘASAR MU A YAU*

*BA NI DA LAIFI*

*SARAKI (the accused prince)*

*ABOTA CE KO SOYAYYA*

*And now…….ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

[03/12, 11:31 am] +234 901 310 1854: Ouummey 05 [ 11/27/2022 9:24 PM ]

 

★★★ *ANJANE* ★★★

(Rashin sani)

★★★★★★★★★

 

 

_*PAID BOOK*_

 

 

Story/written by Ouummey.

 

Wattpad @ouummey.

 

 

 

From The author of:

 

*HAƘORIN DARIYA*

*ƘASAR MU A YAU*

*BA NI DA LAIFI*

*SARAKI (the accused prince)*

*ABOTA CE KO SOYAYYA*

*And now…….ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

 

 

 

 

 

 

 

₦300 to the below account details

Rabiatu Abdullahi

2391368231

ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

FREE PAGE 005

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

_________________________📖 A sittin ta runtse ido tana taune leɓen ta sabida zafin da ya ziyarce ta ita kuwa Hassana da zaƙuwa take zuƙa tana sauke ajiyar zuciya har ta ƙoshi kafin ta saki.

 

Se lokacin ta buɗe idon ta da ya ɗan canja kala ta kalli yadda yarinyar ke numfashi a hankali a hankali tana ciccilla ƴan ƙafafuwan ta tare da wasa da hannayen ta se ta ji wani sabon farin ciki ya kamata har ma taji zafin ya tafi.

 

Zanin ta ta gyara a ƙirji ta miƙe ta saɓa ta a kafaɗa ta shiga jijjiga ta dan tayi gyatsa, a haka baba Husaila ta tadda ta se ta kwantar da Ussaina ta karɓi Hassana ta fita da ita a kafaɗa ita kuma ta koma ta zauna tare da ɗaukar Ussaina.

 

Haka ta shayar da ita itama sedai ba kamar Hassana ba Ussaina akwai ci dan se da ta daɗe kafin ta ƙoshi hakan ma se da ta canja mata ɗayan shiyasa gaba ɗaya ƙirjin nata ya ɗume da zafi.

 

Tun daga lokacin take shayar dasu amma duk da haka baba Husaila na haɗa musu da ƴan dabaru musamman Ussaina da ta fahimci yarinyar akwai tsotso in aka barta bata ƙi ta wuni da nono a baki ba.

 

Iya ƙauna da mutuntaka baba Husaila da ƴan uwan ta sun gwada mata, Abinci da abin sha bata taɓa rashin su ba, ga kula da ita da ƴaƴan ta da suke yi tun bare baba dan ko rigimar Ussaina ce ta tashi da dare bata bari ta tashi cewa take ta koma tayi kwanciyar ta ita kuma tayi ta fama har se tayi bacci tukunna hankalin ta ze kwanta.

 

Ruwan wankan su kuwa kullum se ta sa musu magani shiyasa alhamdulillah jikin su yayi ƙwari se fatar su da ta ɗan dafe saboda zafin ruwa da kuma kalar magani duk da yanzu sun fara sabawa da zafin ruwan.

 

Sannu a hankali har ta cinye wata ɗaya tare dasu basu ankara ba saboda zama da yayi daɗi, jakar ta kuwa baba ta adana mata dan ce mata tayi da su ne za’a bar ta ta shiga makarantar in taje, yadda ƴan uwan baba ke son ta ita abin har mamaki yake bata, wai yau ita Salame da kowa ke gudu itace yau ake so ko da yake ai ba ita ake so ba ƙaunar ƴaƴan ta ce ta shafe ta dan haka be kamata tayi wani kauɗi ba.

 

Mace ɗaya ce ta taɓa son ta a Karan kanta yadda take wato Hajiya Hadiza principal ɗin su, Allah ya sani tana son matar a ranta irin son da bata san yadda zata kwatanta shi ba.

 

Ta so ta a lokacin da kowa ya ƙi ta, ta bata gatan da bata taɓa zaton samu ba, a bayyane yake badan ita ba da ba zata taɓa samun damar karatun da take so ba, ita ta ɗau ɗawainiyar komai na makarantar ta, kuɗin PTA, uniform, littattafai, takalmi, Safa, abinci da komai da zata buƙata a makaranta tun da ta fara kuwa bata gaza ba har wata ɗaya da kwanaki baya da ta gama, ita kuwa ai sedai tace da ita Allah ya saka da kuma ya zame mata wajibi ta so ta.

 

Kallon baba Husaila dake zaune gaban ta tana mata lissafi kawai take yi yayin da idanun ta suka tara ƙwalla, kuɗi ne daga kan ƙwandala zuwa na takarda wai wanda aka haɗa mata dan tafiya makarantar su da zata yi duba mijin ta in yazo (kamar yadda tace musu).

 

Hannu ta sa ta share hawayen

 

“Dan Allah baba ki maida musu kuɗin nan kin ji, zan fa iya zuwa da ƙafa”.ta faɗa murya na rawa

 

“Amma dai salamatu baki da kirki, ya za’a yi mutum yayi alkhairi a maida masa, to kul kar in Kuma ji ko ke kin yi hakan kin ji ko?”.

 

Da kai ta amsa wa baba kafin ta shiga yi musu godiya da addu’a kamar Allah ne ya aiko ta har se da baban ta gaji ta fice ta bar mata ɗakin.

 

Tuhumar kanta take kan me yasa tayi masu ƙarya gashi su kuma sun yarda da ita sun zauna da ita da zuciya ɗaya, jaddada wa kanta take Allah ma ya sani ba’a san ran ta tayi ƙaryar ba, bata so a raba ta da yaranta ne kawai.

 

Da wannan ta tattara kuɗin da suka tasamma dubu ɗaya ta zuba cikin jakar makarantar ta, ta kuma haɗe kayan ƴan biyu ta ninke ta zuba cikin jakar su ta rakuɓa nata kala huɗu da take dashi.

 

Kashegari tayi sallama dasu cikin rashin daɗin rai dan har da kukan ta haka ma baba Husaila da ta zauna wajen ta, ji take kamar yarinyar ta dawwama tare da ita dan bata da matsala sam, yarinya ce me kirki ga ladabi da biyayya, gata ba har dama, ga nutsuwa da rashin ƙyuya, duk sanda taga ta tashi aiki bata bari tayi komai se karɓe ta shiga yi shiyasa so da yawa ma bata tashi yi saboda tasan ba zata bari tayi ba.

 

Su kuwa ragowar ƴan gari da matasan su ƴaƴan ne suke jin kamar su ƙwace ta tafi ita kaɗai dan sun shiga zuciyoyin su barin ma Hassana da bata da rigima, in aka fita da ita har se an tausaya an dawo da ita dan bata kuka se dai in ko Bata da lafiya ko kuwa ta kai maƙura wajen jin yunwa, toh haka dai aka rabu kowa na mararin kowa, rayuwar kenan!

 

Ganin tana da isassun kuɗi a hannu se kawai ta tare mota bayan ta fita sarari, sunan Makarantar su ta faɗa masa suka yi ciniki ta hau ya kai ta har bakin gare kuwa.

 

Wajen baba megadi ta bada ajiyar jakar kayan su ta wuce office ɗin Hajiya Hadiza wato principal, ba abinda ya dawo da ita makarantar illa son karɓar sakamakon ta tare da certificate ɗin kammala karatun ta dan tana so a duk inda taje ta ɗora karatun ta dan shine burin ta tun bata san ze iya cika ba ko kuwa ze rushe ne har zuwa lokacin da ta fara hasashen cikar sa wato da maigari ya sanya baki a kan karatun.

 

Ba kaɗan ba Hajiya Hadiza taji daɗin ganin Salame wadda ke amsa sunan Salama kamisu a makarantar, cikin nutsuwa ta bata takardun ta da WAEC result ɗin ta dan dama alƙawari ne tayi mata ana sakin result zata bada a ciro mata nata.

 

Cikin ikon Allah tana da credit bakwai da excellent biyu, Salame kam har dasu kukan godiya ga Allah dan ta san shi yayi mata komai ba wai ita ba haka kuma ta sanadin wannan matar me kyakkyawar zuciya ne wato Hajiya Hadiza, godiya kam haka ta dinga zuba ta tana yi tana hawaye lokacin da take faɗa mata ga Form nan na College of Education ƴan gora, wata local government a babban garin da ƙauyen su yake ta cike ta mata submission in tana so ita Kuma zata biya mata komai, da ƙyar ta iya tsayar da kukan ta sukai sallama ta tafi.

 

Se da ta tsaya ta karɓi kayan ta wajen Maigadi ta ma sallama tukunna ta wuce, mota ta tara zuwa tasha inda batare da tunanin komai ba ta biya motar garin GAMJI dan a can ne makarantar da take son yi take.

 

Motar na cika aka fara tafiya inda ita kuma ta fara nata tunanin kan irin rayuwar da zata yi a can ita da yaran ta dama yadda rayuwar karatun ta zata kasance, shafa Form ɗin da Maah Hadiza ta bata ta sake yi tare da lumshe ido tana ayyana batutuwa da yawa a ranta.

 

Zata cike Form ɗin tayi submitting a can makarantar a karan kanta batare da jiran Maah Hadiza ba dan bata jin nan kusa zata kuma komawa koda hanyar ƙauyen BA MUNI ne, da kanta zata tsaya wa kanta tayi komai sedai ta yaya tunda ba kuɗin hakan ne da ita ba, gashi yanzun nan in bata manta lissafin da Maah take mata na kuɗin da za’a kashe kusan dubu sha biyar ne, registration goma da ɗari biyar ragowar kunji kunji kuma su cinye sauran.

 

A ina zata samo wannan kuɗin ita da ba ta da kowa bata da kuma komai?

 

Wannan shine tunanin Salame yayinda mota ke ta tsuga gudu a titi, ragowar passengers kowa da abinda yake yi, wasu hira, wasu kallo, wasu karatu wasu kuwa bacci.

 

Itama dai cikin tunanin ta da yake kakare mata sanadin rashin abokan rayuwa wato kuɗi nata baccin ya saɗaɗa saɗaf saɗaf yayi wuf! Yayi gaba da ita.

 

Hayaniyar da ta cika wa kowa kunne ce ta sanar da masu barci an iso in da zasu wanda Salame na cikin su, miƙa tayi a hankali ta kalli Hassana dake ɗaure a gabanta tana baccin ta hankali kwance, tun da aka fara tafiyar bata yi wani rigima ba se Ussaina da ta ɗan yi kuka ta kunto ta ta bata tasha ta kuma maida ta bayan ta ɗan bata ruwan leda da ta saya guda biyu tun a can tasha kafin su tashi.

 

A hankali ta sauka daga motar hannun ta riƙe da jakar kayan su ɗayan kuma jakar makarantar ta da ta saka Form da ragowar takardun ta a ciki.

 

Tun da ta sakko taji ana shelar kowa ya kula da jakar kuɗi ko kayan sa saboda ɓarayi ta kuma damƙe jakar makarantar a ƙirjin ta ɗayar kuwa ta mata riƙon da tasan ba me iya fincike ta a hannun ta ta sauƙi.

 

Tunanin inda zata nufa ta shiga yi se kuma ta tuno yadda suka yi da Maah Hadiza da ta tambaye ta ko ina zata zauna in ta zo karatun tace mata ai duk me napep ɗin da tace ya kai ta gidan haya ze kaita dan ba ya wahala a garin GAMJI.

 

Bakin tashar ta fita taƙi kula duk me napep ɗin dake cikin tashar dan bata yarda dasu ba, suma zasu iya zama ɓarayi ne, a nan titi ta sami wani tace ya kai ta gidan haya.

 

Seda suka fara tafiya ya tambaye ta gidan mutane da yawa ko kaɗan

 

“Kamar dai biyar ko bakwai”.

 

Amsar da ta bashi kenan shima be kuma magana ba ya shiga tuƙa abar sa cike da ƙwarewa, wata unguwa ya shiga mara wadatacciyar tsafta ga nan gidaje a wajen ba fasali se uban yara da suka cika layin jikin su ba kyan gani.

 

Gaban wani gidan bulo yayi fakin tare da nuna mata gidan

 

“Ko a layin in kika lura gidan na cikin gidaje masu kyau haka ma ɗakunan su suka da yawa megidan ma a nan take rayuwa a ɗaki ɗaya, yanzu dai bani kuɗi na in tafi”.

 

“Tsaya dan Allah, nawa ake biya na hayar?”.

 

“Wata shida dubu uku shekara kuma dubu shida”.

 

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta sauka tare da fidda kayan ta ta bashi Naira hamsin ɗin shi ya tafi.

 

Cikin ɗari ɗari gaban ta na faɗuwa ta shigar da kayan zauren gidan ta shiga doka sallama kamar sabuwar warkewar makanta

 

“Kai haba wannan wane irin bala’i ne tun ɗazu ake ta waalaikumussalam amma dan baƙin rashin mutunci an ƙi shigowa, to dan Allah mutum ya ɗige a wajen ƙarƙari in na gaji in ɗau taɓarya in jirge mutum dan na gaji da iskancin ƴan unguwar nan, me ake da gidan haya ni saratu ban da dai ƙaddara”.

 

“A ƙaddarar dai ya rufa miki asiri in ba haka ba mutum ya fita titi mana ya kwanta, se shegen baƙin faɗin rai yawa ƴar ƙaruna, naga kuɗin hayar ma har yanzu ina bin ku ciko amma har kika samu bakin kankanba “.

 

Salame dake zauren banda zarar ido ba abinda take yi jin sabuwar duniyar da ta shigo yau da rana tsaka, a gidan hayar ma wato dai ba hutawa mutum ze yi ba, ya baro masifar dangi ya shiga masifar wasu mutanen daban kuma.

 

“Bismilla, ina me sallama ta shigo in ga kowace da kuma me ya kawo ta tunda Allah ya rufa asiri yasa nidai ba’a sanni da cin bashi ba”.

 

“A’a Hajiya wannan magana taki kuma me kike nufi, ina ce faɗan ku tsakanin ke da saratu ne to me kuma ya shigo da ni ciki?”.

 

Matar ɗaya ɗakin ta yi but ta fito tana faɗin haka acewar ta Hajiya ita take neman faɗawa magana da tace ba’a san ta da cin bashi ba.

 

“Ai ba zan yi mamaki dan kin yi uwa kin yi makarɓiya a zance na ba Huwaila, in ma Baki yi magana ba ai se a canja miki suna, to ni dai na faɗa ba’a sanni da cin bashi ba sedai in ke aka biyo dan kece gandun bashi mara haƙuri da kaɗan a gidan nan”.

 

Turo ɗankwali gaba Huwaila tayi da alama zata karta rashin mutunci ne se kuma ga Salame ta shigo dan ta gaji da tsayuwa ta kuma fahimci da ɗaiɗaya da ɗaiɗaya wannan maganar se ta fiddo duk matan gidan ita kuma ba zata iya jumurin su gama ba, so take ta sami wajen sauke yaran nan ta huta.

 

Kallan kallo aka shiga yi tsakanin ta da magidanta biyu wato Hajiya da kuma saratu se kuma matashiya ɗaya wato Huwaila,

 

“Dama nace a kai ni gidan haya zan kama ɗaki shine aka kawo ni nan”.

 

“Aiho Allah sarki, ashe abin arziƙi ne ya same ni saratu da Huwaila ke neman yi min tawaiwai, shigo baiwar Allah ai nice me gidan ɗaki kuma Allah ya soki akwai ɗaya da masu shi suka tashi”.

 

Ajiyar zuciya Salame ta saki tana ɗaukar jakar ta ratse Huwaila da saratu ta shige ɗakin Hajiya da tace ta shiga.

 

Ruwa me sanyi ta bata ta sha kafin tayi mata bayanin kuɗin ɗakin da ya ragu be kai sauran ba dan duk shine ƙarami dan haka zata bada dubu biyu wata shida dubu huɗu kuma shekara se ta zaɓa in sunje ta ga yayi mata.

 

Buɗe ɗakin tayi suka shiga a tare sedai gani kaya a ɗakin yasa Salame juyowa ta kalle ta

 

“Wanda suka saki ɗakin basu sami kwashe kayan su bane?”.

 

“To ni dai abin ne da mamaki, ganin gida suka tafi basu dawo ba dama sun ce min ba lallai su dawo ba dan haka suka kwashe kayan sawar su, wannan kuma suka ce in suka rufa wata uku basu dawo ba to sun bar min, yanzu kuma ana batun watan su na shida kenan basu dawo ba, ina ta son ɗaukar kayan ina kuma tsoro amma tun da gaki ga yara kuma naga baki taho da komai ba se ki yi amfani da kayan sedai zan ɗau ƴan abubuwan amfani da nake so acikin kwanikan”.

 

Saroro tayi tana bin Hajiya da kallo kamar wadda bata gane abinda tace ba, se da Hajiyar ta taɓa ta sannan ta sunkuyar da kai

 

“Amma Hajiya daga gani na yau har se ki bar min duk wannan kayan arziƙin bayan ke aka bawa?”.

 

“Kin shiga ɗakina fa kin gani mene bani dashi da zan ce zan ɗauka?, wanda nace ɗin ma sha’awa ce kawai irin ta ɗan Adam amma gwargwado ai Allah yayi min suttura, kinga ki kwantar da hankalin ki ni ba haka nake ba dan haka ki shiga ɗaki in har yayi miki gobe zaki bani kuɗi na”.

 

Tana faɗa tayi gaba abinta Salame ta bi bayan ta da kallo tana murmushi, da alama matar zata yi daɗin zama ɗan alamu sun nuna bata da ƙyashi da hassada haka kuma bata da san kai.

 

Jakar su ta shigar sannan ta shiga ta tsaya tana sake bin ɗakin da kallo, labulaye masu kyau kuma sababbi, fenti me kyau ga katifa ma me taushi da tudu, flower vase ƙarama a gefe, dustbin, tiles, carpet ƙarami tabarma nannaɗe a tsaye ga kuma wardrobe madaidaiciya itama a gefe.

 

Hamadala ta shiga yi tana hawaye kafin ta kwance yaranta ta shimfiɗe kowacce kan zanin ta ta shiga gyara ɗakin……………………..✍🏻.

 

 

 

©️ Ouummey 📚✍🏻.

 

 

 

 

☑️Ote, Comment and share please.Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Anjane Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!