Anya Baiwa Ce Hausa Novel

Hausa novel
Hausa novel

Anya Baiwa Ce Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: ANYA BAIWA CE?

 

Na

 

*AMEERA ADAM*

 

 

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM ZA’A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624,DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

 

 

FREE PAGE 1

 

 

 

Tafe take tana ɗan waige dan gudun kar wani ya ganta ko taci karo da wani a hanya, saboda abin da ta gano take san zuwa ta isar da shi ko ta samu ɗan alheri, aikuwa batayi aune ba tana shiga soron tsakiya suka yi gware da mutum a zabure ta ja da baya tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce tayi tseren gudu, kallan tsaf yayi mata yana karantar yanayinta yasan tabbas akwai abinda ke ƙunshe cikin bakin ta, aɗan diriri ce ta kalle shi ta ce.

 

“Yautai mugun tsuntsu masha miyarka sai yayi dare”

 

Kallanta yayi sai da yayi murmushin gefen baki yana ƙara karantar yanayin ta sannan ya ce, ” Tauraruwa mai wutsiya…, Kura kike ga tsoro ga ban tsoro. Ina zaki kike sauri kina ta juye-juye haka? ” Sai da ta juya hagu da dama ta kuma leƙa soron ƙarshe tana mai miƙa wuya cikin ƙasa da murya ta ce, ” Gobara daga teku maganin ta sai Allah, wata ƙura ce take ƙoƙarin kunno kai a cikin gidan nan amma karka ce kaji daga baki na ” ta ƙarasa magana tana kuma duba gabanta da bayanta.

 

“Jakadiya Kubura kenan, ay harbi ga ɗan jaki gado ne, kuma iya ruwa fidda kai gayamun ina sauraron ki kowa ya biya allon sa ya wanke ” ya faɗa cikin son jin labarin.

 

Sunkuyowa tayi dabda shi sannan ta ce, ” Kasan koda girgiza kurna tafi magarya, mai tsoron a mutu shi yake maho ” Ƙara gyara tsayuwarta tayi sannan ta ce, ” Ƙaramar kyauta tafi babbar rowa ” ta ƙarasa faɗa tana miƙa masa hannu alamar ya bata wani abu.

 

Ya gano abinda Jakadiya ta ke nufi, dan haka ya sa hannu cikin aljihu ya ɗebo mata silallah ya zuba mata akan hannun ta yana faɗin, ” Ke dai ciki kike mai manta kyautar jiya, kuma Kura kike mai manta alherin baya”

 

Juya su tayi cikin jindaɗi ta kunto bakin zaninta ta ɗauresu tana faɗin, ” Domin rana ɗaya ba’a ƙin zuguri, kuturu da kuɗinsa alkaki sai na ƙasan langa, buɗe kunnen ka yanzu zaka sha labari, ashe Fulani Zaliha ciki gareta har ya girma, kasanta da shegen nunkufurci ba ta cika bada fuska a shiga sashenta ba ” zaro idanu yayi waje shima yana waigen bayansa sannan ya ce, ” Lallai tsugunne bata ƙare ba ansai da kare an sayi Mage, naji daɗin wannan albishir naki jeki anjima zan neme ki ” ya faɗa yana yin gaba abinsa.

 

Jakadiya Kubura ta fahimci sarai inda maganar Galadima ta dosa har yaje bakin ƙofa ta ce masa, ” Injunan ka sammako wani tafe ya kwana, kuma hargagin ɗan damisa bashi tsorata Namijin zaki, ka taka a sannu kasan Fulani Maryama ba kanwar lasa ba ce ” kamar bazai bata amsa ba sai kuma ya juyo ya ce mata, ” Tabbas inkaji mutum na tsoron dare ba’a ɗaure shi ya ƙwance bane, Ki bar ganin allura ƙarama itama ƙarfe ce, dan haka bazan ce miki komai ba mu zuba mu gani kowa tasa ta fishsheshi ” yana gama faɗa ya sanya kai ya fice daga cikin soron.

 

Bin bayansa tayi da mugun kallo sannan ta ce, ” Mai ƙafa huɗu ma ya faɗi bare mai biyu, ajuri zuwa rafi wata ran tulin zai fashe ” tana faɗa ta juya ta cigaba da tafiya, kai tsaye sashen Fulani Maryama ta nufa.

 

Tana shiga ta zube ƙasa cikin salon kirari ta fara magana, ” Barka da hutawa Uwargida na bango madafar bayi, uwar marayu uwar mara gata mai iyayenma kin gamai musu komai, Ƴar sarki jikar sarki Matar Sarki kuma gaki Uwar Sarki, Allah ya ƙara girma ya raya mana Yarima mai jiran gado, Mulki da Sarautar Masarautar Kano gaba ɗaya ta ku ce, Mai Uwa agindin murhu bazai ci miyarsa lami ba… ” murmushi Fulani Maryama tayi saboda jin daɗin kirarin da Jakadiya tayi shiyasa ma ta katse ta da faɗin, ” Jakadiya anjima zan turo da saƙon maɗi mai ke tafe da ke?? ” russunar da kai Jakadiya tayi tana mai sauya yanayin fuskarta cikin damuwa ta ce, ” Tuba nake Uwar gijiyata banzo dan isar da mugun labarin nan dan wata manufa ba sai dan ki tashi tsaye ki ɗau mataki kuma asan abin yi, Kaicona da tuntuni ban ankare ba har lamarin ya girmama, amma dukda haka ba za’a rasa abinyi ba dan ba’a rasa nono a riga, ina mai neman gafarar ki saboda labarin bamai daɗi bane ranki shi daɗe ”

 

Tunda Jakadiya ta fara magana Fulani Maryama gabanta ya yanke ya faɗi saboda tasan labarin bazai mata daɗi ba, shiyasa a hargitse ta wurgo mata tambaya, ” Jakadiya banasan Kewaye-kewaye tafi kanki tsaye, Me yake faruwa ne?”

 

Jakadiya kara sauya muryarta tayi ta ce, ” Ina neman gafararki da jin kalamai na dama Fulani Zaliha ce ke da juna biyu, kuma ayanayin dana lura har yayi ƙwari…” cikin tsananin tashin hankali Fulani Maryama ta ƙunduma wani ashar sannan ta ce, ” Aikin me kike tun tuni baki sanar dani ba tunda wuri? ”

 

Jakadiya ta bata amsa da, ” A gafarce ni Uwargijiya ta kinsan Yarinyar da nunk…”

 

Katseta Fulani tayi cikin tsawa ta na faɗin, ” Ya isa haka, Lallai Fulani Zaliha ta ɗebo ruwan dafa kanta, Samun sararin kuturu gaɗa a cikin rama, wato haka ta miƙe ƙafa da yawa? Lallai abinda ya faru a shekarun baya dole ya ƙara faruwa yanzu, tabbatas dole labari ya ƙara maimaita kansa, Aikuwa kowa yaci tuwo dani miya yasha, tashi kije Jakadiya anjima zan neme ki bayan Sallar Isha’i ”

 

Jakadiya najin haka ta kuma rissinawa ta ce, ” ALLAH ya huci zuciyar Fulani, Ramin kura da wuyar shiga a gayawa kare yayi hankali, tabbas bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane wace ce Fulani Zaliha da zata iya haɗa sahu da Uwar ɗakina, ni mai bin Umarnin ki ce akowanne lokaci ” Jakadiya na gama faɗa ta tashi ta fice zuciyarta fess saboda tasan ba ƙaramin alheri zata samu ba.

 

Tunda Jakadiya ta fito daga ɗakin, Fulani Maryama ta kasa zaune ta kasa tsaye sai kaiwa da komawa take, abun duniya gabaɗaya ya isheta, ita kaɗai sai saƙa da warwara ta ke tana san nemarwa kanta mafita, Jaririnta ɗan kimanin wata biyar da ke kwance ta je tasa hannu ta ɗauke shi tana juya shi cikin zuciyarta da shawarar da ta yankewa kanta.

 

A fili ta fara surutai kamar wata zautacciya, ” Yarima yanzu kai ake shirin yiwa kishiya a gidan nan, tabbas bazata yuwu ba tunda ban bari wata ta haifi namiji ba dole na dakatar da cikin Zaliha ”

 

Jakadiya tunda ta fito daga sashen Fulani Maryama kai tsaye sashen su ta wuce tana zumuɗin sauraron kiran da Fulani Maryama ta ce zata yi mata, kamar wacce a ka mintsina tashi tayi ta fito daga sashen bayi wani gida ta faɗa bakin ta ɗauke da sallama, ” Balaraba matar Ciroma dake tankaɗe ta amsa mata sallamar tana faɗin.

 

” Yau kuma Jakadiya ce da doshin magariba haka?? ” Kujera Jakadiya ta janyo ta zauna sannan ta ce, ” Eh ko bakya maraba da zuwan nawa ne?? ” cigaba da tankaɗenta tayi ta bawa Jakadiya amsa, ” Ni na isa nace banten Sarki yayi ɓurtu, ai hanyar lafiya abita da shekara, meye labari?? Dan nasan bakin ki baya rasa motsi?? ”

 

Murmushi Jakadiya tayi ta ce, ” Ai dama ni kujera ce dole a zauna dani, kuma abokin cin mushe ba’a ɓoye masa wuƙa, wai kuwa kinsan Fulani Zaliha na ɗauke da juna biyu?? Wa ya sani ma itama ko Namijin zata haifo ni zanso ma ta haifo Namijin naga yanda Fulani Maryama zatayi ” ta faɗa tana ƙasa-ƙasa da murya.

 

Da sauri Balaraba ta saki rariyar Hannunta waigawa bakin ƙofa tayi sannan ta cewa Jakadiya, ” Da gaske kike wannan maganar?? aikuwa muddin zancen nan yaje gun Fulani Maryama kinsan bazai mata daɗi ba, kuma kinsan dole wani abu ya biyo baya”

 

Jakadiya ƙara matse bakin zanin ta tayi ta ce, ” Ai a bakin wawa akanji magana, wai da kunne yaji muguwar magana wuya ya tsere, kinsan dai ai ciki badan tuwo akayi shi ba, bayan ke babu wanda yasan da wannan maganar ”

 

Tsuke fuska Balaraba tayi da alama bataji daɗin maganar Jakadiya ba dan haka ta maida mata da martani, ” Tafasar tukunya bata gefe ɗaya bace, haka nan abinda baki ya ƙulla hannu bashi iya kunce shi, idan kinji makaho ya ce ayi wasan dutse to tabbaci haƙiƙa ya taka dutse, Jakadiya koma dai mene ne daga bakinki wannan maganar ta fito kuma ni nan da kika gani na iya taku na”

 

Miƙewa tsaye Jakadiya tayi tana gyara ɗaurin zaninta ta fara takawa har sai da taje wajen bakin ƙofa sannan ta juyo ta ce, ” Mutum fari ne shi ke rina kansa ya zama baƙi, bakinki dai ƙanin ƙafarki kuma harshenki linzaminki ” bata saurari mai Balaraba zata ce ba ta fice daga gidan.

 

 

_UMMOU ASLAM BINT ADAM

[18/07, 8:16 am] : *FIRST CLASS WRITERS ASSO

 

 

*ANYA BAIWA CE?*

 

Na

 

*AMEERA ADAM*

 

 

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA’A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

 

 

FREE PAGE 2

 

 

 

Da daddare Bayan sallar Isha’i Jakadiya ce tafe tana lalube har ta ƙarasa sashen Fulani Maryama, da sallama ta shiga ta russuna tana cewa, ” Barka da hutawa Uwar ɗakina ance kina san ganina yanzun nan ”

 

Fulani Maryama dake tsaye hannunta ɗauke da Salman miƙawa Jakadiya shi tayi ta ce, ” Jakadiya inasan muyi tafiyar sirri kamar yanda muka saba da ke a shekarun baya, ayau basai gobe ba zamu kai ziyara ga Boka Marduska, saboda bazan iya kwana da maganar da kika sanar da ni ba, batare na nemi mafita ba ”

Riƙe Salman Jakadiya tayi tsam kamar wani zai ƙwace shi sannan ta ce, ” Duk abinda kika ce haka za’ayi, bani da ikon bijirewa umarninki, da kai da kaya duk mallakar wuya ne ”

 

Fulani Maryama na gama jin haka ta juya ta shiga cikin ɗakinta, cen ƙasan adakarta ta buɗe ta ɗauko wani kurtu tasa hannu ta ɗebo waɗansu irin wuri guda biyu da wani ɗan ƙaramin zobe, maida kurtun tayi sannan ta dawo gurin da tabar Jakadiya ke tsaye.

 

Miƙawa Jakadiya Wuri ɗaya tayi sannan ta fara karanta waɗansu irin ɗalasiman tsafi, ba’a ɗauki lokaci ba sai wani haske ya mamaye gurun atake suka ɓace daga cikin ɗakin.

 

Tsaye suke abakin wani kogon dutsen dake cikin wani surƙuƙin daji mai matuƙar duhun gaske, Fulani Maryama runtse idanunta tayi ta fara ƙwalawa bokan kira har sau uku, ” Marduska! Marduska!! Marduska!!! ” tana gama faɗa ta buɗe idanunta.

 

Ji sukayi ankece da wata mahaukaciyar dariya sai da aka ɗan ɗauki lokaci anayi sannan aka tsagaita, sannu a hankali haske ya mamaye gurin, cikin wata irin murya aka fara basu umarni, ” Ku sanya ƙafafunku cikin waccen ƴar ƙoramar sannan ku tako ku shigo ciki.

 

Kamar yanda aka gaya musu haka suka bi umarnin mai magana sannan suka shiga cikin kogon dutsen, daga cen nesa suka hango shi zaune akan buzun damisa, gaba ɗaya jikinsa lulluɓe yake da gashi tamkar ba bil Adam ba, Fulani Maryama na gaba Jakadiya na biye da ita a baya.

 

Zama sukayi sannan Fulani ta kalli bokan zata fara magana ya ɗaga mata hannu sannan ya kuma kecewa da dariya, sai da yayi mai isarsa sannan ya fara magana,

 

” Ai duk wanda ya bamu iska dole kwaɓarsa tai ruwa, Maryama kin ɗauke mana ƙafa na wasu shekaru sai da buƙatarki ta tashi zaki waiwayo mu ”

 

Fulani Maryama ta russunar da kai ta ce, ” A gafarceni sarkin bokayen duniya, nayi kuskure awancen lokacin amma yanxu baza’a sake ba ”

 

” Na amshi tubanki kuma nasan abinda yake tafe dake, kalli nan ” ya janyo wata ƙwarya mai cike da jini yana nunawa fulani.

 

Tana leƙawa Fulani Zaliha ta gani kwance akan gadon ta tana baccinta hankali kwance, jinjina kanta tayi ta cewa Murduska, ” Ya babban boka sarkin bokayen duniya so nake a salwantar da cikin da ke jikinta inda hali ma akashe su gaba ɗaya, domin bayan Salman bana san kowacce matar sarki ta sake haihuwa acikin su saboda bansan gaba mai zasu haifo ba kuma bansan mai hakan zata haifar ba ”

 

Ƙwala-ƙwalan idanunsa ya kafe ta dasu yana ce, ” Daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaƙi, badan kinzo ayanxu ba da tuni sauran damar data rage miki ta ƙare gaba ɗaya ” A zabure Fulani Maryama ta ce, ” Ban fahimce ka ba Marduska ”

 

 

Wani mudubin tsafinsa ya ɗauko yasa wata jelar ɓauna dake hannun sa na hagu cikin ƙwaryar ya yarfawa mudubin, inuwar wani ɗan ƙanƙanin Yaro ce ta bayyana na ɗan wani lokaci sannan ta ɓace, maida mudubin yayi gefe sannan ya maida kallonsa ga Fulani Maryama ya ce, ” Alƙalami ya riga da ya bushe, duk duniya babu wani ko wata da zai iya dakatar da cikin jikinta har sai ta haifeshi, Zata haifo Ɗa namiji Mai kama sak da Mahaifinsa kuma koda baki ci wannan Alwashin ba haihuwa ta dakatawa Sarki Aminullah, duk wacce kika ga ta kuma haihuwa sai dai in wani ne mahaifinsa ba Aminullah ba ”

 

Cikin damuwa Fulani Maryama ta ce, ” Yanxu babu wata mafita da zaka bani ya Shugaba na?? ”

 

Wani Allon jar ƙasa ya ɗauko ya jingine ya na faɗan waɗansu irin kalmomi, yana watsa wani tafasashen jini dake cikin wani ƙoƙon kan Ƙwarangwal, yana cikin haka baiyi aune ba sai gani sukayi Allon jar ƙasa ya ruguje wani irin hayaƙi mai wari na fita daga jikinsa.

 

A tsorace gaba ɗaya suka ja baya Marduska ba ƙaramin tsorata yayi da ganin faruwar haka, cikin yanayin firgici ya fara magana, ” Tabbas Ruhin wasu ababen hallita na katange da shi, idan na matsanta halaka shi ba mu ba hatta Aljanun da suke taya ni aiki sai sun halaka, maganin kar ayi kar afara inba haka ba wanda baiji bari ba yaji woho ”

 

Fulani Maryama jikinta ne ya gama sanyi amma duk da haka zuciyarta bata karaya ba ta ce, ” Marduska abar batun Halaka shi tunda ni kaina ganau ce ba jiyau ba, amma bayan haihuwar sa ba damar a aiwatar da wani aiki akansa ko a nakasa shi? ”

 

Matsawa yayi bakin wutar dake ci ya ɗebo wani garin magani mai haɗe da garin naman mage da haƙoran jemage ya zuba aciki, take wutar ta kuma tashi sama sannan wata ƴar ƙaramar ƙorama ta bayyana aciki, daga cikin ƙoramar wasu litafan tsafinsa ya ɗebo guda biyu ja da baƙi, baƙin ya fara jefawa cikin wannan jinin dake cikin ƙwarya sannan ya zura kansa yana karewa Ƙwaryar kallo dake ta zaɓalɓala.

 

Sai da ya gama kallo tsaf sannan ya ɗago da kansa da yayi gumi sharkaf ya fara mata bayani, ” Tabbas cikin biyun za’a iya gudanar da ɗaya amma biyun bazasu iya wanzuwa akanshi ba, zamu iya nakashi ta kowacce siga haka nan zaki iya sawa a fitar dashi daga cikin masaurautar, amma shi ne kuskuren da zaki fara tafkawa a rayuwar ki, domin kuwa ta wannan silar dukkan asiran da kika binne za’a binciko domin kuwa allura ce zata tono garma”

 

Fulani Maryama harta fara jin daɗi ƙarshen maganarsa ya sa ta shiga damuwa, kallansa tayi cikin rashin fahimta ta ce, ” Bangane mai kake nufi ba? ” mayar da ƙwaryar yayi cen gefe ya ce, ” Abinda na gani kenan zaɓi ya ragewa mai shiga rijiya…, kowanne zaɓi kika ɗauka yana da nashi ƙalubalen da zaki fuskanta ki nutsu da kyau ki saurare ni inba haka ba zakiyi gudun gara ki faɗa gidan zago ”

 

Jakadiya dake gefe tayi tsuru sai raba idanu ta ke cikin zuciyar ta ta ke faɗin, ” Lallai Fulani Maryama kema ba ƙaramar makira ba ce, amma ajuri zuwa rafi…, Ay bahaushe ya ce inzaka gina ramin mugunta gina shi gajere, amma lallai wannan Ɗa na Zaliha ya zama kainuwa dashen Allah, wata ƙila shi ne zai zama magajin mulki muga ta tsiya, dama ance kayun Ɗan ƙwarai ya gaji Ubansa ”

 

” Ina sauraren kowacce kalma da zata fito daga bakinka kuma kowacce zan saka ta amazaunin da ta da ce ” Fulani Maryama ta faɗa.

 

Miƙe ƙafafunsa yayi da gaba ɗaya gashi ya rufe su sannan ya fara mata bayani, ” Zabi na farko zamu iya baki garin maganin da za’a zuba masa a ruwan wanka ina nufin wankansa na farko a duniya kuma ko yaya ne asamu a bashi wannaa maganin ya sha, sai kuma na turare wanda ita Zaliha tana fara Naƙuda zaki turara mata, karki bari yaro ya faɗo ba tare da kin turara shi ba, to idan kika yi haka bazai iya gani da idanunsa ba, har tafiya da magana ke komai da kika sani sai dai ayi masa, saboda zai kasance a kwance sai dai duk abinda za’a furta zai ji shi babu abinda zai iya wanzarwa ”

 

Murmushin jin daɗi Fulani Maryama tayi ganin haka yasa boka ya ce mata, ” Sai dai akwai sharaɗin da zaki kiyaye, akwai ruhin wata da na gani tana jingine da shi, zata shigo cikin gidan masarautar ku tana ƙasƙantacciya muddin kika bari ta shigo cikin gidan sarautar, abubuwa marasa daɗi zasu fara faruwa gareki kuma duk ranar da tayi tozali da shi suka haɗa ido, a ranar aljanun dake riƙe da ƙafafunsa zasu tarwatse alƙadarinsu zai karye, idan kika yi sake ta ɗau wani abun ci ko abin sha ta bashi da hannunta to a ranar suma aljanun da ke riƙe da bakinsa zasu gushe zai fara magana, sai dai aranar zai fara wani irin ciwo kamar zai mutu zai yi ta amai ba ƙyaƙyƙyautawa kamar zai amayar da ƴan hanjinsa, hakan zai ɗaga hankalin Mai martaba har yasa anemo wanda ya bashi wani abu tunda shi zaiyi tunanin guba ce aka bashi, amma ba haka bane amayar da gubar da take jikinsa yake ta tsawon shekaru ”

 

 

 

_UMMOU ASLAM BINT ADAM

] : *FIRST CLASS WRITERS ASSO*

 

 

*ANYA BAIWA CE?*

 

Na

 

*AMEERA ADAM*

 

 

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA’A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624,DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

 

 

FREE PAGE 3

 

 

Ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke sannan ta ce masa, ” Wace ce yarinyar? Kuma daga wane gurin zata xo? Babu damar dakatar da zuwan nata? Ya za’ay na gane ita ce dan na ɗauki matakin daya dace akanta?? ”

 

Boka ya ce, ” Daga ni har sauran matsafan duniya babu wanda ya isa ya ja da yarinyar domin ita ɗin FILSIFI ce, abinda muke kira da FILSIFI kuwa aharkar bokan ci, tarraya ko haɗakar shuɗaɗɗun ruhika mabanbanta daga jinsi Mabanbanta, zo ki duba nan ” ya ƙarasa faɗa yana buɗe mata wannan jan littafin da ke gefensa.

 

Zanen wasu matasan mata ta gani guda uku sai dai duk cikinsu babu wacce zanen fuskarta ya fito sosai daga ƙasan kowacce anrubuta wani irin gwamammen rubutu, ta farko ya fara nuna mata yace, ” Wannan da kike gani ita ce Muhaibish ita ta rayu ne tsawon dubbannin shekarun da suka gabata, Ƴar Sarkin jinsin Fararen Aljanun ƙarƙashin ƙasa ce, tunda take bata taɓa taka doron ƙasa ba ”

 

Zaro idanu Fulani Maryama tayi tana mamakin abinda ya faɗa, ta biyu ya nuna mata ya cigaba da cewa, ” Wannan kuma sunan ta Kalimsiyat Ƴar sarkin fararen Aljanu ce amma ta nan doron ƙasa itama ta rayu atsawon dubbanin shekaru, acikin wani littafin bincike na karanta cewar ta yi rayuwa ne tun bayan zuwan Annabi Yusuf (A.S) ita kuma tunda ta ke bata taɓa nutsawa ƙarƙashin ƙasa ba a matsayinta na jinsin aljanu, kuma ita Kalimsiyat mace ce mara haƙuri mai faɗan gaske, kuma abinciken da nayi dukkan su biyun kashe su akayi bisa doron zalinci, kuma abinda zai baki mamaki kusan duka ruhinsu guda ne, sai dai banbancin nahiya da zamani.

Sai ta Ukun su ita ce aka ce zata xo aƙarshen zamanin nan, sunanta Rayzuta ita ta haɗa dukkan abubuwan da waɗancen suke dashi harma da wanda suka rasa, ƴar baiwa ce me ɗauke da ɓoyayyun al’amura, ita kanta batasan da wannan baiwa tata ba.”

 

Yana rufe baki cikin azarɓaɓi Fulani Maryama ta ce, ” To itama ta ukun nasu Aljanar ce? kuma meye alaƙar su da junan su? Kuma meye alaƙarta da gidan masarautarmu? ”

 

” Maryama kenan azarɓaɓin me kike yi? Ai duk gaggauwar asara ta jira samu, kuma duk gaggawar unguwar zoma ta jira a haihu, mai kike ci ne na baka na zuba inkinyi haƙuri sannu-sannu bata hana zuwa sai dai adaɗe ba’a je ba ”

 

Murmushin tayi sannan ta bashi amsa da, ” Hmmm Marduska ai Ranar biyan buƙata rai ba’a bakin komai yake ba, na ƙagu na ji matsayin Yarinyar da ka ce da kuma ya alaƙarsu ta ke? ”

 

Marduska ya cigaba da cewa, ” Har zuwa wannan zancen da nake miki ruhin su na nan ya wanzu a dora ƙasa, sai dai babu inda zasu ya da zango sai akan cikon ta ukunsu, kuma ba kowa bace cikon ta ukunsu sai Yarinyar da nace miki karki sakankance har ta shigo Masarautar ku, har yanxu mudubin tsafi na ya gagara gano mun mutum ce ko kuma itama tana cikin jinsin Aljan, sai dai bincike ya nuna akwai wani ɓoyayyen al’amar dake bibiyar jinin zuri’ar sarki Aminullahi ”

 

Damuwa ce ƙarara a fuskar Fulani Maryama ta kuma jefo masa tambaya, ” Ita yarinyar ba dama ka nuna mun hoton fuskarta yanda zan gane kamaninta? ”

 

Mudubinsa ya janyo ya fara wasu surutai yana watsa masa wani ruwa mai yauƙi, wata irin ƙara suka ji ta tsagewar mudubin har sai da suka tsorata, cikin damuwa Bokan ya ce, ” Gaskiya gaba ɗaya aikin da kika zo dashi akwai damuwa da tashin hankali, haka kawai banci nanin ba nanin zata ci ni, na dakata akan binciken Yarinyar nan saboda ceton rayuwa ta ”

 

Abin duniya gaba ɗaya ya dami Fulani Maryama amma duk da haka ba ta gushe ba tana faɗin, ” Ka taimaka mun kayimun wani abu, ni da kai kaɗai na dogara ”

 

Wani mugun kallo ya bi ta dashi sannan ya ce, ” Baki da hankali ne a gabanki munanan abubuwa suka faru amma zaki ce na taimaka miki kinga idan kinganni a lahira kaini akai, babu uwar da zan iya taimaka miki, bincike na biyu da zan gaya miki shi ne, idan kika sa aka fitar da shi tun yana jariri to ba makawa acikin ƙasa da makwanni goma zai faɗa gurin da zai gamu da ita wannan yarinya kuma dawowarsu shi da ita bazai miki daɗi ba, dabara ta ragewa mai shiga rijiya…”

 

Zufar dake goshinta ta goge sannan ta ce masa, ” Marduska wai dole sai akaina wannan masifun yarinyar zasu sauka? Kaina ya kulle fa, dan Allah ka bani mafita…” katse ta yayi da ƙarfin gaske yana cewa, ” Da alama kin manta dokar kogon dutsen, azaba ta gaggawa zata iya wanzuwa agareki ” sunkuyar da kai ƙasa tayi ta ce, ” Tsafi ya dafa tuba nake bokana Sarkin bokayen duniya, ina gwanin wani ga nawa Aljani Garbunsa ya ƙara ja da zamanin ka ”

 

Motsa bakinsa yayi alamar jindaɗi sannan ya ɗauko wani ruwa dake cikin tukunyar ƙasa ya ɗaga shi sama da hannunsa ya fara surutunsa na tsafi, ya jima ahaka sannan ya sauko da shi ya leƙa wani tiriri ne yake fitowa, sai da ya gama kallon ƙwaryar ya ce, ” Akwai wasu ɓoyayun al’amura mai tafe da sarƙaƙiya, da alama shuɗaɗɗun abubuwan baya ne zasu iya dawowa wata ƙila Tarihi ne zai kuma maimaita kansa, amma bani da tabbas harsashe ne nayi, ƙarɓi wannan ” Ya miƙa mata wata manyan layu sannan ya cigaba da bayani.

 

” Ita wannan layar ki saƙaleta aɗakinki zata taimaka miki na bunnuwar wasu sirrika na ki, wannan kuma ki binneta akan ƙofar shiga gidan masarautarku, bance zata Hana faruwar komai ba sai dai wannan layar zata hana tonuwar muhimmin sirinki musamman akan wance yaran, kinfi kowa sanin dai ba jinin Aminullahi ba ne hasalima ba jinin masarautar Kano bane, to ki saƙale ta gun da kikasan bazata faɗo ba, ita wannan ta ƙofar gidan wasu aljanune zasu miki gadin bakin ƙofar don hana ta shigowa, amma banda tabbaci yaƙini nake watakila shigowar Rayzuta gidan ya sa ta faɗowa wata ƙila kuma bazata faɗo ba, kuma na lura da faɗuwar gaba a duk lokacin da zaku haɗu da ita wannan yarinyar, sai ki riƙe wannan duk lokacin da kikaji faɗuwar gaba ki dinga lura da waɗanda suke tare da ke, ni nayi iya yi na ku tashi ku bani guri ”

 

Jakadiya dake gefe tsumu tayi najin kalaman boka cikin zuciyarta ta ke faɗin, ” Au dama Salman ba jinin Takawa bane? Lallai duk inda makirci ya je Fulani Maryama ta kai cen, babu ko tantama ɗan wajen Fulani Zulaiha shi zai zama magajin Izza, muje zuwa mahaukaci ya hau kura na tabbata akwai ranar da Ya zata ɗakin Ƙanwa, Fulani Maryama kinyi shuka a idon makwarya, lokaci na nan zuwa da kwaɓarki zatai ruwa, tafiya sannu-sannu kwana nesa. ”

 

Kamar Fulani Maryama tasan abinda yake ran Jakadiya aikuwa ta juyo cikin tsuke fuska ta fara mata magana, ” Jakadiya duk abinda kika ji agurin nan ki tabbata da ya zama sirri banasan kowacce magana ta fito daga bakinki, bakinki ƙanin ƙafarki, kinsanni sarai kinsan wacce Fulani Maryama bani da kyau banida daɗi, idan na sake naji wata magana ta ɓilla waje to daga gareki ne, kuma insa a hallakaki ba abu ne mai wuya agurina ba ”

 

Jakadiya sarai ta san Fulani Maryama zatayi abinda yafi haka ma ta rissinar da kai ƙasa ta ce, ” Wane ni da wannan ɗanyen aikin ya Shugabata indai wanda ya mutu zai dawo to maganar nan zata tashi, ai duk wanda ya ƙona rumbunsa yasan inda toka take tsada, ina ni ina bayyana sirrin Uwar gijiya ta idan nai haka ai kamar na daɓawa kaina wuƙa ne ”

 

Fulani Maryama ɗauke kanta gefe tayi tana faɗin, ” Ki tabbatar da kin kiyaye abinda kika faɗa domin ni ginshiƙin dutse ce kowa yayi karo dani shi ka faɗi, idan kunne yaji gangar jiki ta tsira ” Jakadiya haɗiye yawu tayi mai ɗaci saboda jin haushin maganar Fulani, cikin zuciyarta ƙwafa tayi ta ce, ” Tunkafin ahaifi uwar mai sabulu balbela ta ke da farinta, Fulani Maryama dani kike zance wallahi duk wannan wulaƙancin da kike mun akwai lokacin da zan farke miki laya. ”

 

” Muna godiya Ubangidana maganin kuka na dukda yau ce rana ta farko da zan fita daga kogon dutsen bada biyan dukkan buƙata ba, amma ni mai bin umarnin ka ce akan duk abubuwan daka gindaya mun, tsafi ya dafa hatsabibancin ka ya cigaba da wanzuwar har ƙarshen zamani ” Fulani Maryama ta faɗa tana karɓar layun da ya bata.

 

Cikin jindaɗin kirarinta ya ce, ” Taɓewa ta tabbata ga mai yin shirka kije tukwicin aikinmu na ga cikin bayin Masarautar ku kamar yanda muka saba duk lokacin da kuka ziyarce mu, zan ƙara miki tuni idan kun wayi gari da mutuwar wani bawan babu ku babu cin kayan sadakar inba haka ba zaku bishi, ku fice daga kogon dutse kuna masu ambatan sunan mu ” yana gama faɗa ya ɓace daga gurin, Jakadiya da Fulani tashi suka yi suka fita, suna zuwa bakin kogon dutsen Fulani ta kuma runtse idonta tana karanta ɗalasiman tsafin, atake haske ya kuma mamaye su suka ɓace daga gurin.

 

Lokacin da suka koma cikin Masarautar tuni dare ya tsala babu motsin komai sai kukan tsuntsaye da ƙananan dabobbi, Fulani karɓar Salman tayi dake hannun Jakadiya sannan ta ce mata, ” Ƙuda wajen kwaɗayi akan mutum ina fatan baki manta maganar boka ba ” rissunawa Jakadiya tayi ta ce, ” Ina ankare ya shugaba ta ”

 

 

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published.