Asalin Jinin Haila da Yadda ake Gane shi

Asalin Jinin Haila da Yadda ake Gane shi

 

 

 

 

 

 

 

 

★ ASALIN JININ HAILA DA YADDA AKE GANE SHI.

 

★ MATSALOLIN DA SUKE FARUWA BAYAN ZUBAR DA CIKI KO 6ARIN CIKI.

 

★ ABUBUWAN DA SUKE KAWOWA MATA CIWON SANYI KO INFECTION.

 

★ ILLOLIN DA CIWON SANYI KO INFECTION SUKE YIWA MATA.

 

 

Daga Al huda Islamic Medicine, masu harhahada Magunguna na Musulunci.

07050855528

 

 

ASALIN JININ HAILA.

 

1- Datti ne da ke cikin mahaifar mace, shi ne a duk wata ake wanko mata shi yana fitowa.

 

2- Kwan haihuwa ne na mace yake saukowa, idan bai samu kwan namiji sun samar da abin halitta ba sai ya lalace ya ru6e, daga nan sai a wanko shi ya fito waje.

 

Mace tana fara haila ne lokacinda ta balaga. Mata kan iya fara haila daga shekara tara ko sama ko kasa da haka, ya danganta ne da irin abincin da take ci da kuma yanayin wajen da ta ke rayuwa.

 

Wasu suna daina haila da wuri idan sun fara tsufa, wasu kuma suna dadewa ba su daina ba. Saidai daukewar haila alamar tsayawar haihuwa ce ga wadda ta tsufa ko kuma alamar shigar ciki ga mai haihuwa. Akan samu lalura kuma tasa haila ta dauke ba tare da wani dalili ba.

 

YAYA JININ HAILA YAKE?

 

Wani lokacin jini ya kan yankewa mace kuma ta kasa gane cewa ko jinin Haila ne ko kuma jinin cuta wato istihadha. Wannan ya kan rikita musu lissafi wajen gudanar da ibada da kuma sanin matsayin lafiyarsu.

 

YADDA AKE BAMBANCE JININ HAILA DA NA CUTA.

 

1- Jinin Haila ruwan kasa ne, ba ja ne sosai ba shi kuma jinin cuta za ki gan shi ja ne sosai kamar jinin ciwo.

 

2- Jinin Haila yana dan yin wari, za ki ji yana dan wani wari mara dadi amma jinin cuta ba ya wari.

 

3- Jinin Haila yana fitowa ne da karfi, ma’ana za ki ji kamar ana turo shi ne amma shi jinin cuta a slow yake fita, ba da karfi ba.

 

4- Jinin Haila ya kan zo da lalura kamar ciwon mara, ciwon kafa da dai sauransu, shi kuma jinin cuta bai fiye zuwa da lalura ba, saidai wani lokaci ya kan zo da ciwon mara.

 

5- Jinin Haila yana da kauri sosai, shi kuma jinin cuta ba shi da kauri.

 

6- Jinin Haila ba ya bushewa, idan ya diga a kasa za ki ga ya ki bushewa amma shi jinin cuta nan da nan yake bushewa.

See also  Farar Haihuwa Complete Hausa Novels

.

7- Za ki ga jinin Haila yana kyalli, yana sheki, shi kuma jinin cuta ba shi da kyalli.

.

8- Idan mace ta kasa bambance jinin da ya zo mata ta wadannan alamomi, to sai ta samu babbar roba ko bahon wanka, ta zuba ruwa a ciki, ta shiga ciki ta zauna. Idan ta ga yalo ya taso sama to jinin cuta ne amma idan ba ta ga yalo ba to jinin Haila ne.

 

YADDA MACE ZA TA GANE TA SAMU TSARKI DAGA JININ HAILA KO NIFASI

 

 

Wasu matan sukan kasa gane cewa sun samu tsarki ko kuma ba su samu tsarki daga jinin haila ba musamman ma idan jinin yana zuwa ne yana dauke musu.

 

To abu mai sauki dai hanyoyin da ake gane jini ya dauke guda biyu ne.

 

1- Tsanewa. Wato idan mace ta ciro auduga ko kuma abinda tay matsi da shi, sai ta ganshi a bushe ba jini a jiki. To jininta ya dauke kenan.

 

2- Idan mace ta ga wani ruwa yana fito mata mai garai-garai ko kuma mai kamar an wanke danyen nama, to alamace ta jininta ya dauke, wannan ruwan dauraya ne yake zuwar mata.

 

KARIN BAYANI

★Koda jini ya zarce kwana goma sha biyar yana zuba, indai ya cika alamomin jinin haila, to hukuncin mai haila ne akanta.

 

★Jinin cuta ba ya hana mace ibada, saidai ana so ta dinga tsaftace jikinta kuma kowace sallah za tay mata alwalarta.

 

★Jinin Nifasi ko Jinin biqi da matan da suka haihu suke yi, hukuncinsu daya da jinin haila a wajen ibada.

 

ABIN LURA

★Matan da samsam ba sa yin Jinin Haila to ba za su iya haihuwa ba.

 

★ Matan da suke ciwon mara mai tsanani lokacin al’ada yana da kyau su nemi magani.

 

★ Idan jinin mace yana zuwar mata bakikkirin, ma’ana kalarsa ta zama baki maimakon ruwan makuba, to itama tana da matsala.

Illar Yin Family Planning Ga Mace

★ Haka wadda take yin Haila mai doyi ko kuma wari sosai, to itama ta nemi magani.

 

★ Idan jini yana zuwa ya daukewa mace, kamar yau ya dauke gobe ya dawo. To lallai ita ma ta nemi magani.

 

★ Idan wani ruwa mai wari yana zubarwa mace mai kamar koko, to itama ta nemi maganin sanyi.

 

Wasu daga cikin wadannan cututtuka matsalar Sanyi ce take kawosu wato Infection, wasu kuma matsalace ta jinnu.

 

MATSALOLIN DA SUKE FARUWA BAYAN ZUBAR DA CIKI KO 6ARIN CIKI.

 

Miscarriage ko Abortion

 

Zubewar ciki ko wanda akayi da gangan ko wanda yazo saboda wani dalili, akwai abubuwa na ruda kai da suke zuwa bayan yinsa wadanda wasu suke tafiya dakansu ba tare da an sha magani ba wasu kuma sai an sha magani ko an dauki wani mataki.

See also  Illolin Istima'i (Masturbation) Ga Lafiyar Dan Adam

 

1-Infection na daya daga cikin matsalolin da zubewar ciki yake haifarwa, kamar idan akwai sauran tsoka da ta rage a cikin mahaifa bayan zubar cikin.

 

Sannan wani lokacin idan anyi amfani da wasu abubuwa wajen zubarda cikin kuma suna iya haifarda kwayoyin cuta ga mahaifa.

 

Idan mace tasamu irin wannan musamman Idan tasamu wasu alamomi kamar haka

 

i) Zafin jikin ta watau temperature ta yakai 38oc.

 

ii) Yawan bugun ziciya kamar ya buga sau dari cikin minti daya.

 

iii) Kumburin ciki, ciwon ciki, taurin ciki.

 

iv) Idan ruwa mai wari yana fita ta vagina.

 

v) Jin rashin lafiya ko gajiya sosai.

 

To idan infection ya samu wadda tayi 6arin ciki ko zubar da ciki a irin yanayin, wannan bazai tafi ba har sai an tabbatarda ancire abinda yayi saura a cikin.

 

2-Zubarda jini fiyeda kima, shima wannan wani damuwa ce ko matsala da take faruwa bayan mace tasamu barin ciki.

 

Shima wannan yana faruwa idan daya daga cikin wadannan yafaru

 

i) Kodai shi ma akwai sauran wata tsoka data rage a cikin mahaifar bata gama fita ba.

 

ii) Ko kuma idan anyi amfani da wasu abubuwa yayin zubar da cikin kila anji ciwo a wani wurin.

 

iii) Kokuma kila bakin mahaifa ko mahaifar takamu da infection.

 

Saidai a sani idan akwai sauran wani abu daya rage a mahaifa to wannan infection din kokuma bleeding din bazai tafiba harsai an fitar da abinda yarage a cikin mahaifar.

 

3- Akwai matsalar kumburin ciki, ciki zai kumbura sosai kamar Akwai ciki wata hudu.

 

Wani lokacin cikin yana tafiya da kansa, musamman idan ba wasu matsaloli dayawa, amma wani lokacin cikin na daukar wasu watanni kafin yatafi amma ana samun wasu matan sukai har wasu shekaru ma yana kumbura akai akai wanda dukkannin wadannan matsaloli ciki bazai shiga ba harsai an magance su.

 

Akwai wasu matan kuma da jinin al’adarsu yakan dauke zuwa wasu kwanaki masu yawa, wasu kuma har zuwa wasu watanni ma ko shekara ko shekaru wasu kuma sai aga yana wasa sosai.

 

Duk wannan wani lokaci jiki ba shi da bukatar wani treatment, zai koma a hankali kamar yadda yake a baya.

 

4- Wasu matan kuma za aga insukayi barin ciki yan kwanaki kasa da sati daya zasuyi bleeding kawai amma bayan sati biyu saiya dawo da karfi kokuma wasu matan suyi bleeding sati daya zuwa sati biyu bayan yadauke da kwanaki kadan sai su ga wani, to in suka lura ba jinin zubar cikin bane, a’a, spotting ne wanda nasha yin magana kansa.

See also  Wani Haske Complete Hausa Novel Page 105

 

Wasu kuma sukan wuce sati biyu suna bleeding, idan wannan bleeding din yazo da ciwon mara sosai, fitar jini sosai misali duk bayan hour daya zuwa biyu ana canza pads, ko jiri, ko gani bishi bishi ko jikin mutum yayi weak sosai kokuma jinin yana fita da clots duk wadannan yana bukatar aje asibiti amma kafin haka mace da ta ke bleeding musamman da zubewar ciki sai asamu abinci masu sinadarin iron ko iron supplements tarika amfani dasu sannan kuma asamu hutu.

 

ABUBUWAN DA SUKE KAWOWA MATA CIWON SANYI KO INFECTION

 

 

1)Rashin sanya pant.

 

2)Barin pant yay dauda sosai ba a canja ba. Ana so in da hali kullum a canja pant sau biyu a wanke.

 

3)Saka pant a jiqe da ruwa.

4)Yawan tsarki da ruwan sanyi.

 

5)Yawan tsarki da ruwan da zafinsa yay yawa.

 

6)Rashin aski.

 

7)Wasa da gaba.

 

8)Yawan cin `Danyar Albasa.

 

9)Yin amfani da Magungunan mata marasa inganci ko kuma ba bisa ka’ida ba.

 

10)Dadewa akan Masai ko toilet.

 

11)Rashin shan iska.

 

12)Musanyar tufafi musamman under wears.

 

13)Saduwa da mai cutar.

 

12)Cutar Aljanu, wato Jinnul Ashiq. Su ma suna sanyawa mace infection mai wuyar magani.

 

ILLOLIN DA SANYI KO INFECTION YAKE YI WA MATA

.

1)Yana sa Rashin Sha’awa.

 

2)Yana sa ciwon mara mai tsanani.

 

3)Yana haifar da kurajen bakin mahaifa ko ya toshe mahaifar baki daya.

 

4)Yana sa mace ta dinga jinin al’ada bakikkirin maiwari.

 

5) Yana sanya farin ruwa mai wari ya dinga fito mata.

 

6)Yana sanyawa a dinga jin mace tana wari mara dadi kuma a rasa ta ina yake fitowa duk wankanta.

 

7)Yana sa jin zafi yayin saduwar aure ko kuma ganin jini a maimakon ruwa.

 

8)Yana rikitawa mace kwanakin al’adarta, su dinga karuwa ko raguwa ko jinin ya dinga wasa.

 

9)Yana sanyawa mace tusar gaba, wato iska ta dinga fita ta gabanta.

 

10)Yana sanyawa mace yawan `Barin ciki ko kuma rashin shigar cikin kwata-kwata.

 

11)In yay karfi yana hana mace haihuwa.

 

12) Wani infection din alama ce ta zaman Aljanu a jikin mace, musamman idan tana mafarkin namiji dare ko jarirai.

 

MAGANIN SANYI WATO INFECTION A TURANCE

 

Idan mace tana fama da kaikayi ko kuraje ko fitar farin ruwa mai wari ko bushewa ko daukewar ni’ima ko budewa da kwailewa da rashin sha’awa ko gamsuwa da sauran cututtukan sanyi, sai a tututbaimu dumin samun maganin

 

Al huda Islamic medicine kutubaimu dumin samun maganin cutukanku dakuma gyaran jikinko dayar Allah. 07050855528/09015546668. Like and share

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top