Asgar Hausa Novel Complete
Tag: ASGAR
Dasunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.
Banyi dan cin zarafin wani ko wata ba.ban yarda ajuya min labari ta kowacce siga batare da izini na ba.
P1
A cikin kasashen dake makwabtaka da kasar turkiyya,a garin Aglab akwai wani kauye Wanda jelar teku ta biyo ta cikin sa Mai suna Ajawid.
Allah ya albarkaci wannan kauyen Albarkacin wannan ruwan da ya ratso ta cikin kauyen, shiyasa sukafi ko ina samun amfanun gona, kauyen nada Arziki matuka inzaka danganta da irin arzikin da akan samo a kasan ruwa.
A kan dawakai suna cikin sahu su kimanin goma a gabar tekun kauyen Ajawid,sanye suke da bakaken kaya,hade da masks a fuskokin su,magana suke kamar ta kurame ayayin da Daya a cikin su ke dauke da wani Abu kamar kaya a kafadar shi.
Kai naga ya jinjina wa Daya daga cikin su Wanda nake ganin kamar shugaban su ne,kafin ya nufi bakin tekun nan gadan,gadan.
Wani katon jirgin ruwa ne agabar tekun anata loda masa kaya,yawancin mutanen bakar fata ne dai,daiku ne farar fata,bakamar wadannan na kan dokin ba duk da sun rufe rabin fuskokin su kana ganin gefen idanuwansu kasan farar fata ne.
Matattakalar jigin wannan mutum yake bi da kaya a kafadar shi har yasamu ya shige ciki kamar matafiyi.
Da shigar sa ya nufi wajen da aka tare wasu akwatuna masu raga,raga da isar sa wajen yasauke kayan dake kafadar shi,yabude wani akwati dake can gefe tuffa ce a ciki,wani kwando ya dauka ya zuba rabin tuffar dake akwatin aciki yanayi Yana kallon bayanshi.
Bayan ya kwashe ne ,ya dauko wannan kayan daya ajiye yasa a cikin akwatin,har ya rufe sai Kuma ya bude,gani nayi Yana kwance kayan, Abinda na gani yasani fiddo idanuwa waje,domin kuwa kyakkyawar fuskar yaro ce na gani idon sa arufe kamar Mai bacci.
Bayan ya bude fuskar ne ya mayar da akwatin ya rufe ya Dora wannan kwandon akan akwatin, da sauri ya Mike Yana Mai gaggawa domin ya Isa ga yan uwan shi,har Yana bangaje wani da ya dauko kaya akanshi zai shiga ciki.
Bayan isar wannan mutum ga yan uwanshi ne,yaiwa babban su rada, jinjina Kai yayi kamar Bebe,dokinshi ya hau,haka sukayi ta tsaiwa suna ganin ana loda kaya har aka gama,akayi sanarwa jirgi zai daga,suna kallo jirgin nan ya nausa yayi cikin teku da yaron nan kafin suka juya akalar dawakan su suka nausa cikin gari.tofa!wane ne wannan yaron?
Littafan Hausa Novels
Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan
Bayan shekaru Ashirin da hudu.
Da misalin karfe takwas na dare a unguwar badawa layout dake cikin karamar hukumar nassarawa dake kano.w.d.s restaurant & event center ne cike da manyan yara matasa masu aji da ji da kansu,yan mata ne da samari da ba za su gaza shekaru Ashirin zuwa da biyar ba,rukuni ,rukuni wasu a zazzaune a kujeru,yayin da wasu ke tsaitsaye.
Kowanne table cike yake da kayan snacks da drinks kala daban,daban,matan na sanye da ankon gawn fara da Jan belt akugunsu,mazan Kuma bakin crazy jeans ne sai farar Riga Mai ratsin ja ajikin su.
Can na hango wani babban table da cake akai yanda aka kawata table din abin kallo ne,komai awajen white and red ne ga hasken fitulu.
Wata matashiya ce zaune a gaban cake din nan tana da kyau dai,dai misali Amma tsagwaron hutun daya nuna kanshi ajikin ta shi zai sa ka jera ta da kyawawa ajin farko.
Red gawn ce ajikinta tasa farin belt da farin takalmi cover,ta yane kanta da siririn mayafi fari,agogon dake daure a hannun ta, take dubawa lokaci, lokaci.
Wata dalleliyar farar mota kirar zamani ce ta shigo wajen tayi parking,baka ganin na ciki saboda glass din tinted ne.an bude kofar bangaren driver Amma ba a fito ba.
Matasa ne su biyu a ciki da akalla zasuyi 29yrs,Wanda ke zaune agurin driver ne ya kalli dayan dake zaune a gefenshi,yace haba Asgar Kai kadai ne fa aminina,aboki,Kuma Dan uwa,in baka take min baya na fita kunyar fanan ba waye zan gayyata.wanda aka Kira da Asgar ne yace kasan banason zuwa irin nan wajen,kallon Wanda aka Kira da Asgar nayi,a kyau fari ne ba sosai ba zaifi kyau a kirashi da ruwa biyu,akwai abubuwa da yawa a tare dashi da ba duk maza Allah ya mallakawa ba,sassanyan kyau ne dashi da a kallo Daya ba lalle a gane ba,Abinda kawai ake iya gani akallon farkon shine cikar halittarsa.
Nan zan dakata bani da caji sai warning nake gani,ina jinjina wa dukkan marubuta.
Inna samu caji zan Dora insha Allah.
Ayimin sharing fisabilillah.
Aunty.
Leave a Comment