Asmaa Hausa Novel Complete
Asmaa Hausa Novel Complete
Aasmaa
Written by
Mrs A.M
Free book neh 🥰
Page 1
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Cikin nutsuwa nake kara sa wanke plates din da aka gama cin abincin, aiki nake yi amma fuskata ba alamar fara’a a daure take kamar ko yaushe.
Sai da na gama gyara kitchen din tsaf na bar wankin tukwanen sauran ma’aikatan dake kasa dani su wanke, hannuna na goge da towel din da nake zuwa da shi sbd goge hannu in na gama taba ruwa, a nutse na mayar da towel din cikin jakata na rataya jakar a kafada ta.
Cikin nutsuwa nabi ta kofar kitchen din na fito harabar restaurant din don bana son na bi ta ciki ko dan yadda Ogana ya takura min.
Har na fita daga restaurant din kai na yana kasa Ina tafiya Ina dan yamutsa fuska sbd yadda garin yake yau ana rana sosai.
Adaidaita na tsayar na shiga bayan na fada masa Inda zai kai ni, waya ta dake ringing na dauko a cikin jakata, ganin sunan wanda yake Kira yasa ni tsaki Ina mayar da wayar cikin jakar.
A kofar layin mu ya sauke ni don adaidaita bata shiga ciki sai dai babur, kudin sa na basa na huta ma shiga layin kai na a kasa ina kara hade rai sosai sbd samarin unguwar da basu da aiki sai gulma, dai-dai kofar Gidan mu samarin da suke zaune suka hada baki gurin cewa “Ina wuni Ya Aasma”
Fuska ba yabo ba fallasa nace “lafia qalau” Ina tura kofar gidan mu wacce ake lallabawa don saura kadan ta fadi.
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza uku Hausa Novel
-
Doctor Eshaat Hausa Novel
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi Hausa Novel
-
Aure da haihuwa Hausa Novel
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya Hausa Novel
-
Gangar Shedan Hausa Novel
-
Angon mata biyu Hausa Novel
-
A gidan mu take Hausa Novel
-
Bafulatanar Rugga Hausa Novel
-
Matar yaro Hausa Novel
-
Mr Bello Hausa Novel
-
Mijin Buzuwa Hausa Novels
-
Gidan Uncle Complete Hausa Novel
-
Yar aiki return Hausa Novel
-
Raggon namiji Hausa Novel
-
Uncle Datti Jikina yake so Hausa Novel
-
Fataucin Mata Hausa Novel
-
Juhud Hausa Novels Complete
-
Moon Hausa Novels Pdf
-
Yarima Ashman Hausa Novel
-
Bandirawo Hausa Novel
-
Matar makaho Hausa Novel
Powered by: www.mynovels.com.ng
Sai da suka tabbatar na wuce sannan daya daga cikin su yace “Wallahi Ya Aasma tana mugun kashe ni, kai nifa sonta nake shiyasa nake yawan zama anan in na dai dai ci lokacin dawowar ta daga aiki ya kusa”
Kallon sa Auwalu yai yace “eh lallai Khalifa baka da hankali ynxu Ya Aasma din kake so”
Lumshe ido wanda aka Kira da khalifa yai yana dafe dai dai zuciyar sa yace “hmm baza ku gane ba kawai amma nayi nisa a kogon kaunar ta, ta hadu ne fah ta ko ina Wallahi”
Auwal ne ya taba sani da bai ce komai ba sai kallon kasa da yake yi kawai.
Dagowa yai yana sauke ajiyar zuciya yace “ina jin sa Auwal, Ai baxan ce masa komai ba don nasan duk irin son da zai ce yana mata ba kamar yadda ni nake kaunar taba”
Cacar baki suka fara tsakanin sa da Khalifa da kyar Auwalu ya raba su kuwa ya mike ya tafi hanyar sa daban ba tare da sunyi wa juna magana ba.
Lokacin dana shiga dan matsakaicin tsakar gidan namu Umma tana zaune akan tabarma tana jin radio iska sai kada bishiyar fruit din dake tsakar gidan namu wanda yasa gidan sanyi mai dadi.
Zama nai akan tabarmar ina fadin “Barka da yamma Umma”
Murmushi Umma tai tana rage volume din radion ta tace “lafia qalau Aasmaa ya aikin”
Dan yamutsa fuska nai nace “Alhamdulillah Umma, duk na gaji yau wallahi gashi gobe da wuri zan fita an bada order din abincin biki”
Murmushi Umma tai tana dafa kafada ta tace “Allah ya bada sa’a toh”
“Ameen” na fada Ina mikewa na shiga dakin mu.
Gidan mu dan karami ne sosai mai dauke da daki falle biyu sai toilet a tsakar gidan da wani guri daga can karshen gidan inda aka kewaye mana shi da langa langa anan muke ajiye kayan kitchen dinmu.
Daki daya muka dauka nida Umma wanda yake da dan girma, raba sa mukai da labule daga ciki katifar muce da yar karamar wardrobe din kayan mu sai wasu tarkacen dai a gefe, daga inda muka mayar palo kuwa ledar daki ce kawai sai wani karamin table a gefe wanda Umma take ajiye kayan kukar da take siyar wa akai.
Cikin dakin na shiga na cire kayana Ina dan tsaki sbd zafi, zani na daura na zira hijab, kwandon wanka na na dauka na fito.
Sai da na jawo ruwa daga rijiya sannan na shiga toilet, na dau lokaci Ina wanka sannan na yi alwala na fito Ina sauke ajiyar zuciya don sai Ynxu iska take shiga jikina.
Daki na shiga na zira rigar bacci ta mai tsantsi na sa hula, wayata na dauka daga jaka ta na fito zuwa tsakar gidan.
Ban nemi abinci ba sai hira da muke da Umma a hankali Ina bata labarin irin girkin dana yi yau da kuma yadda nake yin abincin.
Sallar magriba da aka Kira ne yasa mu tashi muka shiga daki, ni da yake Ina da alwala sallah nai, bayan na idar ban tashi ba zama nai ina jan carbi a nutse, sai da nayi sallar isha’i nayi shafa’i da wutr sannan na tashi Ina ninke sallayar.
Daki na shiga na dauko bargo da pillow na shinfida a palon na kwanta Ina gane a wayata don ynxu Umma lokacin jin radion tane nasan baxa ma ta tsaya saurara taba shiyasa nayi kwanciya ta a palon.
Da Sallama Umar ya shigo hannun sa rike da bakar leda.
Ina daga kwancen na amsa masa sallamar.
Zama yai daga gefena yace “Ya Aasma barka da dare”
Murmushi na masa har dimple dina suna lotsawa, a nutse nace “lafia qalau Umar ya kasuwa?”
Murmushi yai shima yana gyara zama yace “Alhamdulillah yau kasuwa tai kyau ai har kayan abinci na siyo mana don naga namu sun kusa karewa”
Mike wa nai Ina janyo ledar na bude fuskata dauke da fara’a kamar yasan tunanin dana wuni Ina yi kenan, don jiya na duba naga shinkafar mu saura baifi kofi uku ba sai masara da gero.
Dagowa nai na kalle sa nace “Masha Allah, Allah yayi ma albarka kamar kasan abin da nake ta tunani wallahi tun da safe abin da yasa ma ban maka magana ba sbd gobe in Allah ya kaimu zamuyi abincin biki kuma nasan za’a sallame mu akai”.
Gyada kai yai yana murmushi yace “ai bata baci ba Ya Aasma sai mu karo wasu kayan da kudin yadda zamu dan dade bamu siya ba koh”
Daga kai nai nace “hakan zamu yi Insha Allah kuwa”.
Mikewa yai yana dafe cikin sa yace “yunwa nake ji sosai bara naje na dibi abinci nasan nawa ne ya rage kawai”.
Umma dake daki tana sauraren su hawayen daya zubo mata ta goge tana kara godewa Allah daya bata yara masu tausayi da Jin kai, da badan yaran ta ba ai da bata san yadda rayuwar ta zata kasance ba lokacin da mijin ta ya rasu.
Lumshe ido tai tana binsu da addu’a.
Ni kuwa Ina game bansan lokacin da bacci ya dauke ni ba sai da Umma ta tashe ni na mike na shiga daki da kyar don baccin nawa ya fara nauyi.
********
Mami ce ta mike ta nufi dining area don ganin me Abdallah yake yi tun dazu wajen 2 hours kenan ko tashi bai yi ba.
A zaune yake idonsa akan handout dinsa yana karatu, sosai ya bada dukkan attention dinsa gurin karatun don gobe suna da test.
Dafa sa Mami tai tace “Abdallah karatun ya Isa haka don Allah ka tashi kaje ka huta mana”.
Dago sexy eyes dinsa yai da suka dan yi ja alamun gajiya a tattare dasu, daga kai kawai yai ya mike yana hada kan takardun sa.
Kallon Mamin yai da kyar ya bude bakin sa murya kasa kasa yace “good nyt”.
“Allah ya tashe mu lafia” ta fada tana binsa da kallo don ynxu miskilan cinsa ya daina bata mamaki sai dai tsoro mutum kamar aljani sam baya magana.
Dakin sa dake gefen part din Mami ya bude da key din hannun sa ya shiga yana lumshe idonsa, dakin ya gaji da haduwa da tsadaddun furnitures komai ash ne da ratsin white.
Akan resting chair din dake dakin ya zauna yana lumshe idonsa, mika kawai yake yana tsaki akai akai sai da ya gaji da tsakin sannan ya mike ya shiga toilet yayi wanka.
Gajeran wando yasa kawai ya kwanta akan lallausan bed dinsa yana jan bargo ya lulluba idonsa a rufe.
Tunanin test din da zai yi yake ga kuma lawyer dinsa yace ya samu lokaci a goben yazo yayi signing paper din estate din da zai siya Abuja.
Karamin tsaki yaja yana matse kafafun sa, shi duk wannan ba damuwar sa bace sha’awar dake damunsa kadai ta ishe sa, juyi kawai yake akan bed din yana matse kafa da kyar ya samu bacci ya dauke sa……..
Ya kuka ji salon labarin labari neh mai dauke da tsantsar soyyaya mai tsaya wa a rai🥰🥀
Domin magana da marubuciyar kai tsaye 09066728387
Mrs A.M🥰
[17/12, 11:52 am] +218 92-2035171: You should read “Aasmaa” on #wattpad #romance
Aasmaa
🥀🥀🥀🥀🥀
Written by
Mrs A.M
Free book neh 🥰
Page 2
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Washe gari Ina idar da sallar Asuba ban koma bacci ba sai fito wa da nai tsakar gidan mu na share simintin dake kasan duk da wasu guraren sun farfashe haka na share da kyau na dibi ruwa a rijiya na wanke simintin, toilet na wanke da toka da omo sannan na shiga daki shima na gyaro shi.
Ba alamar gajiya a tattare da ni ko bacci don na saba da wannan aikacen tun da akai wa Maryam aure ni nake yin komai sai dai wani lokacin in na makara ko Ina sauri na bar wa Umar yayi.
Ruwa na jawo a rijiya na ciki katon durom din mu dake ajiye daga gefen kitchen, sai da na tabbatar na gama cika ko Ina har randar dake daki d wacce take tsakar gidan sannan na jawo dan karamin gas dinmu na kunna.
Tea na dafa wanda na sa masa Kayan kamshi na juye a cikin flask din mu, flour da Umar ya siyo jiya na kwaba nayi fanke, kafin 7 na gama komai na ajiye a daki.
Wanka na shiga nai a nutse bayan na fito shirya wa nai cikin Riga da zani sun min das a jikina kamar a jikina aka dinkasu, duk kuwa da yadda nake tabbatar da kar ayimin dinki matsattse a banxa don ko ya yake in nasa sai yabi structure dina.
Umma dake zaune a kan sallaya kallo na tai tana murmushi ita kan ta tasan duk namijin daya auri yar tata ya moree.
Murmushi nai cikin kunya na zaune a gefenta ina janyo flask din tea, tea na hada mana na bata cup din ta ina zuba mana fanken a plate.
Muna cikin ci Umar ya shigo shima da alama yayi wanka, zama yai yana gaishe mu shima ya hada tea dinsa.
Da muka gama tattare kayan yai ya wanke su ya kife, dama haka muke in har muka gama cin abincin safe ko dare shi yake wanke wa sai dai in baya gidan.
Mikewa nai na zira Hijab dina light brown wanda ya min kyau sosai, jakata na rataya a kafa da Ina Murmushi na kalli Umma nace “na tafi Umma kar na makara”.
Murmushi tai tace “Allah yayi muku albarka ya bada sa’a”.
Fuskata dauke da Murmushi nace “Ameen”
Kallon Umar nai nace “na tafi Allah ya bada sa’a”.
Murmushi yai yace “Ameen Ya Aasma, ko zan baki kudin mota?”.
Irin kallon dana masa yasa shi dariya yana daga hannun sa yace “wasa nake miki wallahi”.
Tabe baki na nai Ina nufar kofar zan fita don ni maganar da zan fada masa ma ta min wahala gwanda nayi shiru.
Muryar Umma ce da take ce min “kinga Aasmaa na manta ban fada miki ba kuwa, jiya Maryam ta kira ni tace don Allah wai me yasa baki son zuwa gidan ta”.
Juyuwo nai gaba daya Ina kallon Umma bakina yana motsi magana nake son yi amma sbd miskilancin daya zamar min jiki yasa in har zanyi magana sai na dan yi shiru na some seconds.
Ajiyar zuciya na sauke ina gyara hijab dina nace “Umma ita dai Maryam ta cika rigima Wallahi, Ynxu kawai god’ai god’ai dani sai naje gidan kanwa ta”.
Tsaki Umma tai tana kawar da kanta fuskar ta a hade tace “toh meye a ciki dan kinje gidan nata? Ina ba kwana zaki je kiyi ba ziyara ceh fah Aasmaa”
Dan turo baki gaba nai nace “Umma kawai ki bata hakuri Gaskia ai ni tasan baxan ma saurare ta ba shiyasa ta biyo ta gurin ki”
Kafe ni da ido tai tana nazari nah, gyada kai tayi tace “ynxu dai baxa ki je ba kenan?”
Gefe na juyar da kai na badan naso ba sai dan ganin kamar ran Umma ya baci nace “zan je”
Murmushi Umma ta saki tace “ko ke fah, Ynxu yaushe zaki je na buga mata waya na fada mata”.
Shiru nai kafin nace in “na tashi daga aiki sai na leka kawai Umma”.
Da sauri tace “ban yadda ba gaskia, nasan irin zuwan da kike nufi ko 30 minutes baxa kiyi ba zaki fito ki bari sai ranar da baxa ki aiki ba koh kinga ai sai ku dade ma kuna hira”.
Daga mata Kai kawai nayi nace “Allah ya kaimu”
Sallama na sake musu na fito duk rai na a jagule, ni Sam bana son zuwa gidan Maryam don wani iri nake ji in naje, tana kanwata kawai sai na dinga zuwa mata Gida ai abin ma kamar ba tsari, Ko Yaya itama ban cika zuwa gidan taba don ni Ynxu ma na manta yaushe rabon naje gidan nata.
Ajiyar zuciya na sauke kawai Ina Jin wani abu daga kasan zuciya ta yana tasomin mai daci.
Ina wannan tunanin na tari adaidaita na tafi gurin restaurant dinmu.
Tun da na shigo ciki na hade rai na ganin motor wanda bana son tarayyar mu da shi, ban san meye matsalar sa dani ba da yake son lallai sai ya jefa rayuwa ta a cikin hatsari.
Kai na a kasa naji yace “Assalamu alaikum Queen”
Sbd nasan muhimmancin Sallama shiyasa na amsa shi Ina kara hade rai na.
Murmushi ya saki yana nade hannun sa ya zuba min ido fuskar sa dauke da Murmushi daya ke bayyana farin cikin sa na ganin na da yayi.
Ganin yadda ya babbake hanyar yasa ni kara daure fuskata nace “Malam matsa min koh”
Langwabe kai yayi cikin kasa kasa da murya yace “Haba Queen ynxu kin daina fadin sunana me yasa uhm?”.
Dago ido nai nayi masa wani kallo da manyan idona, lumshe idonsa yai yana dafe dai dai zuciyar sa a nutse yace “ina kaunar ki”
Tsaki nai Ina girgiza kai na kawai cikin kausasa murya wai ni nan irin zan sa ta zama katuwa sai dai a bisa rashin sani kara mata dadi nai.
“Me yasa ka tsane ni neh Kabir, a hakan kake ikirarin kana so na bayan ni dai kiyayya nake gani kawai kana nuna min”.
Rude wa yai jin cewa wai tsanar ta yake, shi daya ke haukar son ta, tun ranar daya soma dora idanu akan ta zuciyar sa ta mace a cikin kaunar ta amma wai yau shi take cewa baya son ta.
Tausasa murya yai yace “Queen taya zaki ceh bana son ki don Allah magana ko dadin ji babu haka”
Hade rai na sake yi sosai nace “tabbas baka sona don naga alama nema kake ka janyo min zagi a gurin mutane, sannan amintar da aka kulla tun yarinta kake so ka rushe ta”
Gyara tsayuwar sa yai yana kallon ta dama yasan wannan ne damuwar tata.
A nutse shima yace “maganar mutane duk ba damuwa bace Queen, ni dai Ina son ki kuma fata na shine ki amince dani wallahi bada shiririta nazo ba auren ki nake son yi”.
Ajiyar zuciya ya sauke yana dan dafa motar dake gefen sa yace “ita kuma Hajjo bata da damuwa nasani, sbd kullum maganar ta shine tana so taga kinyi aure kema”.
Murmushin takaici nai Ina girgiza kai na namiji kenan, wai ni yau mijin Hajjo yake bi yana fada min cewa so na yake da aure mijin aminiya ta wacce muka tashi tare har ynxu bani da aminiyar data fi ta duk da Ina dan jan baya da Ita tunda Kabir yazo min da wannan maganar.
Kallon rainin wayo na masa cikin takaici nace “daya ke yawan ce maka tana son taga nayi aure ta taba ce ma ka aure ni”
Da sauri ya tari numfashi na da cewa “don Allah kar ki haramta min abin da yake halal neh, Wallahi ko lokacin dana fara ganin ku ke ceh wacce zuciya ta take matukar kauna, kwarjinin da kika min ne yasa na koma gurin Hajjo ba wai don ita din nake so ba sai dai Ina ganin kamar ke din matar Manya ceh?”.
Tabe baki nai Ina gyara tsayuwata na kalle sa cikin ido nace “tabbas bakai karya ba ni matar manya ceh ka yi min yaro da yawa don nasan baxa ka bani shekaru 10 ba ni kuma na fison na auri Wanda ya girme min sosai ta haka neh kawai zan samu nutsuwar yi masa biyayya yadda ya ka mata”.
Juyawa nai na shiga cikin restaurant din kai na yana sara min don wannan maganar da nayi dashi har ta haddasa min ciwon kai, ban taba tsaya wa nayi magana dashi sosai ba don bana son tsautsayi ma yasa wani idon sanin ya ganmu tare yaje ya fada wa Hajjo don baxan ki dadin hakan ba, shiyasa yau na tsaya na fada masa abin da yake rai na in yaga dama ya kyale ni yaje can ya kulla da matar sa.
Tsaki naja a fili rai na duk a bace wai ni yake so mutumin dana san in ya girme ni Toh da shekaru uku neh.
Haka na shiga kitchen muka fara aiki gadan gadan don karfe 3 za’a kai abincin.
Kabir kuwa yana tsaye har sai da yaga shigar ta cikin restaurant din sannan ya lumshe idonsa, Allah ya sani yana matukar kaunar Aasmaa kuma baya jin zai iya rabuwa da ita.
Nannauyan numfashi ya sauke yana dafe kan sa shi Ynxu yadda zai shawo kan Hajjo yake ne ma, wata kila in ya shawo kanta ya samu Queen dinsa ta saurare sa.
******
Cikin takun sa na cikakken namiji ya shigo palon, sanye yake da gajeran wando black wanda ya kama sa daga kasa sai riga white mai gajeran hannu wacce ta kama sa ta fito da damtsen hannun sa, kafarsa sanye da black boot.
Yayi kyau har ya gaji shigar ta matukar haska farar fatar sa sai kamshi yake.
Yusrah ce zaune a palon tana kallo sai twins da suke game a iPad dinsu, bin ko Ina da kallo yai so yake ya bude baki ya tambaye su ina Mami amma bakin ya masa nauyi kawai sai ya nufi hanyar dakin nata.
Ajiyar zuciya Yusrah ta sauke da karfi bayan wucewar sa, tun da ya shigo gabanta yake faduwa don har sai data matse remote din dake hannun ta da karfi sbd yadda zuciyar ta take bugawa.
Allah ya dasa mata son Yayan nasu har bata san yadda zata yi ba gashi ita dai ba zata iya fadawa Mummy ba don tasan kashe ta ne kawai baxa ta yi ba.
Yadda Mummy din suke zaman kishi da Mami tasan abu ne mai wuya su amince wa auren su da yayan nasu, bama wannan ba in har sun amince shi zai yadda kuwa?
Wannan tunanin ne yasa taji wani hawaye mai zafi ya zubo mata da sauri ta mike ya fita daga palon, garden dinsu taje ta zauna ta hada kai da gwiwa tana kuka mai tsuma zuciya..
**
Kallon sa Mami take tana Murmushi, yaron nata kullum girma yake sake yi yana zama cikakken saurayi, a yadda yake dinnan ba wanda zai yi tunanin shekarun sa 24 sbd girman jikin sa tsaf sai kace ya kai 30.
Yar dariya ta saki tace “toh Abdallah na zama sirikar kane, kana zaune amma kayi shiru tun dazu kan ka a kasa”
Idonsa dake lumshe ya bude yana bude baki da kyar yace …….
Comments nd share please
Mrs A.M
Name: | [Asmaa Hausa Novel Complete] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |