Hausa Novels

Asp Zarah Hausa Novel By Jasmine

Asp Zarah Hausa Novel By Jasmine

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

ASP ZARAH*👩‍✈️

 

*BOOK 2*

 

*Page 1*

 

_Federal Lowcost Gombe State._

_Monday 6:15am._

 

……Kwance yake a kan tamfatsetsen gadon shi hannunshi biyu dafe da cikin shi, kallo ɗaya zaka yi masa ka gane yana fama da matsananciyar rashin lafiya, banda gumk babu abinda yake haɗawa. Tsaki yaja a karo na ba adadi ganin ya kasa mirginawa ya isa ga wayarsa dake kan bedside drawer domin ya kira Abdallah yazo ya taimaka mishi.

Hamdala yayi bayan ya isa ga wayar lokacin da ciwon ya lafa, cikin sauri ya danna kiran wayar Abdallah ringing biyu kuwa ya ɗauka ya fara magana cikin zolaya kamar yadda ya saba.

 

“Ango na Zara’u ya da kiran sassafe haka.”

 

Shiru yayi cikin son yayiwa Abdallah masifa amma tunawa da yayi cewa taimako yake nema ya sashi sassauta murya yace.

“Guy ka taimaka kazo ka kaini asibiti bani da lafiya ne.”

Salati Abdallah yayi cikin tashin hankali yace.

“Meya same ka haka?.”

 

“Wallahi yau da ciwon mara na kwana har yanzu yaƙi sakeni dakyar nayi sallar asuba.”

 

Mamaki ne ya kamashi jin yaja tsaki tamkar wanda yaji mugun abu, shiru ya kuma jin Abdallah ya fara magana cikin fushi.

“Wai kai M J wane irin mutum ne haka da sam baka tsoron Allah, kanada iyali a gida amma kullum kana hanyar asibiti ciwon sha’awa na damunka, watan ku biyu da aure amma ka kasa sauke haƙƙin daya rataya a wuyanka, me zaka cewa Allah idan ka mutu da haƙƙin yarinyar nan, sanin kanka ne cewa zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya amma bazaka daina zargin yarinyar nan da aikata mugun abu ba.”

 

Cigaba yayi da mishi faɗa tamkar ɗa da uba, shikuwa M.J bai ce komai ba har saida yaji Abdallah yayi shiru kafin yace

“Ka gama.??”

 

“Zan gama dai.”

 

“Taimako na nema tunda bazaka taimakamin ba toh zan kashe waya.”

 

“Wallahi Jawwad kaji na rantse koh, idan naji labarin ka kira wani likita saina gayawa su Daddy abinda kake aikatawa ga yarinyar nan.”

 

”So kake na zauna da ciwo a jikina.??”

 

“Kana da magani a gida ai, wallahi na baka minti talatin naji sakamako mai kyau idan ba haka ba yanzu zaka amsa kiran Daddy.”

Daga haka ya kashe wayar ya barshi sororo riƙe da waya a hannu cike da takaici, yana da tabbacin duk abinda Abdallah ya faɗa zai aikata kuma shi bayason iyayensa su san abinda ke faruwa tsakaninshi da yarinyar da yake tunanin mahaifansa zasu iya bada ransu a kanta, wannan dalilin ne yasa ya yanke yin amfani da shawarar Abdallah amma ta ina zai fara? Jim! Yayi kafin daga bisani ya saki wani shu’umin murmushi duk da ciwon dake nuƙurƙusarshi. Tabbas dole ya ƙara aure, hakan ne kaɗai masalaha a gareshi domin shi bai kasance mazinaci kamar ita ba, duk da yasan idan ya tado maganar ƙara aure yanzu za’a iya samun matsala amma dole hakan ne kaɗai mafita a gareshi domin bazai iya dinga haɗa jiki da rijiyar gari ba.

Agogon hannunshi ya kalla yaga 6:45am, yana da tabbacin yanzu bata fita aiki ba, a hankali ya miƙe hannu dafe da ciki ya saka bedroom slipper ɗinshi ya nufi sashin nata cike da zullumi.

Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki haka yake tafiya har ya iso side ɗin nata, falon a kimtse yake ko ina ƙal tamkar ba’a rayuwa a jikinshi ga wani ƙamshi mai sanyaya rai dake tashi a falon.

“Tana da tsabta.” ya faɗa a ƙasan maƙoshi domin yadda yaga falon abin ya burgeshi, daidai nan kuma ya iso gaban ƙofar bedroom ɗinta, shiru yayi na wani lokaci yana nazari kafin ya yanke shawarar buɗe ƙofar ya shiga da sallama a can ciki domin ba lallai wanda akayiwa sallamar taji ba.

 

A tsaye ya hangota gaban madubi tana ƙoƙarin rolling veil akanta jikinta sanye da kayan aiki, cikin sakanni ya ƙarewa ɗakin kallo ganin komai neat tamkar mutum bai kwana a ciki ba, maida kallonshi yayi gareta yana daɗa ƙare mata kallon cikin shigartata, sai yau ya iya yi mata kallon da zai iya zaƙolota a ko’ina ya ganta, tayi mishi kyau sosai zubinta ya mishi kama da wata jarumar Bollywood Deepika Padukone musamman yanzu da take sanye da riga da wando na aiki zubinsu yayi mishi kamanni a wani tallen fim ɗin jarumar daya gani( Fighter ft Hritik Roshan and Deepika Padukone. World wide release on september 2023).

Tun shigowarsa ɗakin ta hangeshi saidai tayi mamaki ƙwarai data ganshi a ɗakinta, watansu biyu kenan da aure amma zata iya ƙirga sau nawa ta ganshi a cikin wata2 domin tun ranar da aka kawota gidan yayi mata sharaɗim kada ta kuskura taje inda yake baya buƙatar komai daga gareta saidai duk sanda zasu haɗu sai yayi mata rashin mutuncin da take daɗewa tana mata ciwo. Tasan hakanan bazai shigo mata ɗaki ba dole akwai abinda ya kawoshi, batason abinda zai ɓata ranta a wannan safiyar domin tana da aiki sosai a office kwananta huɗu bata fita aiki ba saboda menstrual pain dake damunta baya ga haka kuma yau tana da ganawa da sabon commissioner da aka ce mata an naɗa bayan mutuwar wanda tazo ta tarar a garin, bata bibiyi labarin ba domin a zatonta mataimakinshi aka rantsar a madadinshi.

 

“Nazo karɓar haƙƙina ne.”

 

Tunaninta ya katse lokacin dataji abinda ya faɗa, mamaki ne ya kamata wanda har yasata juyowa ta kalleshi lokacin da yake zama a gefen gadonta domin ta tabbatarwa idonta shi ɗin ne ke magana, batace dashi uffan ba ta nufi gaban wardrobe ɗinta ta zaro abayar da zata ɗaura akan kayan tana ƙoƙarin warwarewa da nufin sakawa.

“Nasan kinji abinda nace dan haka bani da bukatar maimaitawa.” ya kuma faɗa cikin tsare gira.

 

“Zaka iya dawowa wani lokacin amma yanzu ba samu zakayi ba.” ta faɗa bayan ta ɗauki handbag ɗinta zata bar ɗakin.

Cikin bazata taji yasa hannu ya fincikota ta faɗa cikin, matseta yayi sosai kafin ya fara warware veil ɗin nata, mutsu-mutsun kwacewa takeyi amma sam yaƙi bata damar hakan.

 

“Ki bar ganin kina ƴar sanda ba iya kwacewa zakiyi ba, gara ma ki nutsu ki barnj nayi abinda zanyi nagama. Kika baiwa wasu na waje ma bare nida nake mijinki.”

Daidai nan ya ƙarasa warware veil din wanda hakan ya bama dogon gashinta mai kyau da sheƙi zubewa a gadon bayanta, da fari yayi tunanin wig ne ta saka amma sai ya gane gashinta ne yayi mamaki duk da yasan cewa suna da gashi irin na fulani amma na Zarah ya zarce irin nasu a tsayi da santsi. A hankali ya fara shafawa yana tusa kanshi a ciki _Mai neman kuka an jefeshi da kashin awaki_ , nan da nan ya fice a hayyacinsa.

Taso yimai turjiya amma tunawa da tayi bata sallah yasa ta daina ƙoƙarin kwacewa ta barshi ya cigaba da abinda yakeyi.

Takaici ne ya turniƙeshi lokacin da ya gane dalilin dayasa ta nutso ta daina ƙoƙarin kwacewa, cike da takaici ya sauka a gadon ya fice daga ɗakin batare da ya tattara kayansa dayayi watsi dasu ba.

 

Cikin sanyi jiki ta miƙe ta nufi banɗaki, bata daɗe ba ta fito cikin hanzari ta ɗauko ɗayan uniform ɗin ta saka ganin har ƙarfe takwas ta kusa kuma ganawarsu da kwamishina 7:30ne. A hanzarce ta gama komai ta fice daga gidan ta wuce office ɗin.

Tun daga harabar gurin take ganin kamar tasan wasu daga cikin jami’an dake shawagi a farfajiyar wajen bata kula ba ganin tayi latti ya sa kai tsaye ta nufi office ɗin commissioner kai tsaye ko kula da sunan dake manne a jikin ƙofar batayi ba ta kutsa kai ciki bakinta ɗauke da siririyar sallama. Tashin hankali _ba’a saka masa rana_, zuciyarta ce ta cunkushe _damuwa tayi adabo a fuskarta_. Jikin tsantsar baƙin ciki ta riƙe handle ɗin ta nufi ficewa a office ɗin……✍️

 

*BY*

*JASMINE*🌸🌸

 

_Fans Mi😜😜😜 Meerah, Zee Bassa, Nab baby, Hussy, Mrs. Mukhtar, Miss Japanese and others da kuka hana kanku bacci jiya toh gashi nan kusha karatu😅😅 A daina hana kai bacci hilis dan nima bana hana kaina 🤦‍♀️._

_Su Ummu Huzaifah a sakar mini mara nayi fitsari, kada masoyiyata ta fara nata itama JJLuV😘😘_

 

Luv y’all.

 

*ASP ZARAH*👩‍✈️

 

*BOOK 2*

 

*Page 2*

 

…Dariya yayi mai cike da ma’anoni kafin yace.

“Barka da zuwa Zarah, ya zaki koma tun baki yimin maraba da samun sauyin gurin aiki ba?.”

A hankali ta juyo ta kalleshi cikin tsana tace.

“Abinda ya kawoni kenan na taya wanda aka naɗa murna saidai wanda na tarar bai cancanci hakan ba, hmm so kake na tayaka murna kabar garin Bauchi a matsayin commissioner ka dawo Gombe a matsayi iri ɗaya? Wani cigaba kenan?. Zuwa na ya ƙaramin aiki domin kuwa ganinka da nayi anan ya tabbatarmin da cewa akwai hannunka a kisan tsohon commissioner saboda kanaso ka dawo inda nake aiki. Allah ya baka sa’a.”

 

“Dakata ai baki karɓi saƙon naki ba.” ya faɗa yana miƙewa a kan kujerar ganin tana ƙoƙarin barin offishin, tsayawa tayi harya iso inda take tsaye ya miƙa mata farar takarda yace.

“Wannan takarda ce ta dakatar dake daga aiki har na tsawon lokacin da za’a gama ƙaddamar da bincike akanki, an kamaki da laifi biyu, na farko ana zargin sa hannunki a ɓatan ƴar aikin dake muku aiki a gida wacce ta ɓata watanni biyu da suka wuce an rasata, na biyu kuma akan mutuwar ɗan jaridar da kukayi ganawar sirri dashi a ranar litinin wanda shima a daren aka kashe shi.”

 

Tsaye tayi tana kallonshi har ya gama magana kafin ta sa hannu ta karɓi takardar tace

“Kamar yadda muka saba a kowani lokaci mai girma commissioner..” tana gama faɗin haka ta saka hannu ta yaga takardar ta kuma cewa.

“Ya fuskanceni, gaba da gaba mu gwabza dashi. Kai harka manta da sharaɗina, ba kallon shugaba nake maka ba kallon abokin gaba nake maka dan haka baka da hurumin da zaka dakatar da Zarah a aiki ko da na second ɗaya ne. Idan ya cika jarumi ya fuskanceni, na barka lafiya.” daga haka ta fice a office ɗin ta barshi a tsaye sororo kamar wawan da yaga mace na wanka.

 

Bata ko tsaya amsa gaisuwar da ake mata ba lokacin data isa gurin aikinsu, kai tsaye office ɗinta ta wuce saboda sarawa da kanta yake yi yana mata masifar ciwo, kanta ta kifa a teburin ta fashe da kukan da batasan dalilin yin shi ba.

Tsagaitawa tayi da kukan batare da ta share hawayen dake zubo mata ba jin alamun za’a shigo office ɗinta batare da an nemi izini ba, tasan ɗaya daga cikin mutum biyu ne ke shigowa ko su duka biyun wato Saleem ko Jidda.

Hannunsu sarƙe dana juna suka shigo bakinsu ɗauke da sallama, cike da mamaki suke kallon fuskarta da ta jiƙe da hawaye, tuni hankalin Jidda ya tashi ta nufeta gadan gadan tana tambayarta abinda ke damunta.

“Babu komai fa Habibaty, kawai kaina ke min ciwo.”

 

Murmushin daya tsaya iya baki Jiddan tayi kafin da zauna shima Saleem ya zauna akan kujerun dake fuskantarta, shiru Jidda tayi ta ƙura mata ido tanason gano abinda ke damunta kafin tace.

“Kinje Office ɗin commissioner da nufin taya shi murna sai akayi rashin sa’a kika tarar da Muttaka wato tsohon commissioner na jihar Bauchi a matsayin Commissioner a garin Gombe, hakan ne ya haddasa miki damuwa kike tunanin taya zaki shawo kan matsalolin dake damunki. Shin zance na haka yake ko akwai gyara.?”

Bata koyi mamakin jin batun Jiddah ba saboda sabo da tayi da hakan, shikuwa Saleem ganin Zarah ta gyaɗa kai alamun hakane yasa shi mamakin a ina Jiddah ta samu wannan labarin suna tare amma shi bai sani ba.

 

“Jeki ɗauraye fuskarki kizo muyi magana.” Ta kuma faɗa.

Wannan karon Zarah abin na Jiddah ya bata dariya domin dai ta fahimci Jiddah ta gane fitsari ya cika mata mara ne shiyasa tace taje ta ɗauraye fuska gudun kada Saleem ya fahimci zance. Babu musu ta miƙe ta shige banɗakin dake manne a office ɗin.

 

Saleem kuwa maida kallonshi yayi ga Jiddah cikin zaƙuwa yace.

“Sa-Jid a ina kika samu labarin abinda ya faru bayan muna tare banga wani ya kiraki ya faɗa miki ba.”

Shiru tayi na wani lokaci kafin tace

 

“Nima bansan ya akeyi nake gane abinda ke ran Zarah ba, wani lokacin sai naji kamar anayi min raɗa a kunne na tuhumeta kuma na bata shawara. Abinda yake ƙara ɗauremin kai kuma shine idan mukayi amfani da shawarar sai muga ribar abin. Nima na rasa gane me hakan ke nufi.”

Jinjina kai Saleem yayi cike da gamsuwa, yana ƙara tabbatar da cewa ƙaunar dake tsakanin Jiddah da Zarah daga Allah ne, babu yadda za’ayi ɗayansu ta ɓoye damuwarta batare da ƴar uwar ta fahimci haka ba.

 

A wannan yanayin Zarah ta fito ta samesu, zama tayi suka cigaba da tattauna abinda da ya shafi binciken da Saleem yake gabatarwa akan mutuwar ɗan Jaridar.

 

“Ni fa inaga lokaci yayi daya kamata mu tunkari inda azzalumin nan yake tunda yaranshi biyu na hannu, mu tursasa sai sun faɗa mana inda yake.” Inji Saleem

 

“A’a dear lokaci baiyi ba amma saura ƙiris domin muna gab da sanin inda yake.” Cewar Jiddah.

 

“Hakane Barrister akwai sauran lokaci, baya ga haka har yanzu Raliya taƙi mana bayani akan komai daya shafe shi duk kuwa da irin azabar da ake gana mata.”- Zarah

 

“Shikenan amma ya kamata muje ki ƙara yiwa mutumin nan barazana domin shima bashi da alamar yin bayani.”

 

“Inada niyyar hakan dama tunda kunzo sai muje gaba ɗaya daganan na sake yiwa Raliya tambayoyi”.

 

“Ok muje ɗin”

Daga haka suka miƙe tare da barin offishin.

 

 

Babu wani da zaiyi tunanin mutane na rayuwa a inda su Zarah suka je, domin wani tsohon kwango ne da ya ji jiki ginin gaba ɗaya ya fara rugujewa. A haka suka shiga tare da kutsa kai a wani babban ɗaki, Saleem ne ya isa daidai inda wasu shukoki suke ya kauda ƙasar dake gurin gefe sai ga wani murfi kamar na rijiya ya bayyana a gurin. Key Zarah ta miƙo mishi ya saka ya buɗe babban kwaɗon dake wajen tare ɗage murfin sai ga matattakala ta bayyana. Juyowa yayi ya kallesu yace

“Muje ko.”

Kamar ko yaushe sune ke fara shiga sai ya biyo bayansu, yauma hakan ce ta faru saida suka shige kafin shima ya bisu bayan ya dudduba baiga kowa ba.

Tana ɗaure a jikin kujera sai wata mata dake gefe a zaune tana daddana waya, ganin shigowarsu Zarah ne yasata miƙewa tana musu barka da zuwa tare da gaishesu, amsawa sukayi cike da fara’a kafin Zarah tace

“Babu wata matsala ko Jummai.?”

 

“Babu ranki ya daɗe, sai dai jiya tayi ƙoƙarin guduwa bayan na kwance ta zatayi amfani da toilet, amma ta rasa hanya ina kitchen naji ta shine nazo na ɗaure ta.”

 

“A tunaninta zata iya guduwa daga nan.?” -Jiddah

 

“Haka take gani.” wacce aka kira da Jummai ta bada amsa.

 

Gabanta Zarah ta isa ta ɗago fuskarta da ta nuna alamun galabaita tace.

“Kinga wannan Raliya acid ne a yau idan baki mana bayanin inda Alpha yake ba zamu kona fuskarki ta yadda ko kin kuɓuta babu yadda za’ayi ya aure ki kamar yadda kike da buri.”

 

A razane Raliya ta ɗago ta kalli Zarah tana mamakin yanda akayi tasan wannan zancen domin bayan ƙawayenta dake gidan da Alpha yake ajiyesu babu wanda yasan wannan zance, yanzu ta sadaƙar cewa ko bata gaya musu ba zasuyi amfani da asiri su karanci abinda ke ranta. Hawaye ne ya wanke mata fuska cike da takaicin yau zata faɗi wani sirri na masoyinta tace.

“Zan faɗa miki.”

 

“Muna jinki.” Saleem ya faɗa.

 

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

 

Malam Surajo Mai Idon Naira shine sunan da mutane kw kiranshi saboda tsantsar son kuɗi da yake da shi daga shi har Matar sa mai suna Lauratu. Malam Surajo da Lauratu ma’auratane da aka sansu da masifar son kuɗi da roƙo tare da bibiyar masu kuɗi suna musu fadanci, ƴaƴansu biyu kacal a duniya. Hajara itace ta farko wacce a yanzu take da shekaru 22 sai ƙanwarta Na’ima dake shekaru na 17. Duk wani buri sun ɗaurashi akan ƴaƴansu domin suna mishi kallon kadara wacce zasu dinga zamun kuɗi dasu.

Saidai a cikinsu Hajara ce kaɗai tayi gadon iyayen nata domin tana da buri sosai, a cewarta ma bazata yi aure ba idan ba mai hannu da shuni ta samu ba, saidai a ɓangaren Na’ima abin ba domin yarinya ce mai nutsuwa da sanin ya kamata sam bata yi halin iyayen nata ba shiyasa basa shiri sam dasu.

 

A daren ranar lahadi ne wanj abin farin ciki ya samesu a cewarsu, domin wani baƙo ne ya zo musu da wata kwangila mai tsoka. So yake su yi sanadin da ƴarsu Hajara zata auri ɗan shahararren mai kuɗin nan wato Eng. Muhammad Jawwad Sulaiman, batare da tunanin komai ba suka amince saboda zunzurutun kuɗin da za’a basu bayan haka kuma zasu samu kuɗi sosai idan ƴarsu tayi nasarar auren shi. Ya tsara musu komai da yadda Hajara zata haɗu da M.J tare da kalan aikin da yake so tayi mishi idan taje gidanshi, a haka suka rabu bayan ya ajiye musu makuɗan kuɗi domin yin hidima tare da faɗa musu cewa ta kasance cikin shiri domin a kowani lokaci zai iya kiranta domin su haɗu da M.J ɗin.

Wannan abu ya matuƙar faranta musu rai, domin a ganinsu fa kakarsu ta yanke saƙa.

 

Washegari kuwa kamar yadda yace, ya kirasu tare da yin magana da Hajara bayan ya gama gaya mata abinda zatayi idan ta fita.

 

A ɓangaren M.J kuwa bayan ya sha magani ya ɗan samu sauƙin abinda ke damunshi, shiryawa yayi ya fita zuwa gurin aiki domin bazai iya zama a gidan ba. Yana tafe zuciyarsa cike da tunani kala-kala, bai ankara ba hannu motar ta kwace mishi cikin rashin sa’a kuwa ya bige budurwar dake ƙoƙarin tsalleke titin tana sanye ta dogon hijabi har ƙasa milk colour, da hanzari ya taka birki ya kashe motar cikin tashi hankali ya fito ya sameta a zaune tana ƙoƙarin miƙewa alamun motar bata taɓata sosai ba.

 

“Sannu kinji baiwar Allah, kiyi haƙuri, daure ki mike na kaiki asibiti a duba ki.”

 

Cikin sanyin murya tace

 

“A’a banji ciwo ba ka barshi kawai.” tana mikewa da kyar tamkar saniyar dake naƙuda.

 

“Kar muyi haka dake dan Allah muje na kaiki ko da Pharmacy ne a duba ki.”

 

Babu musu ta bishi tana takawa dakyar har ta ƙarasa inda yake tsaye ya buɗe mata ƙofar motar yana jera mata sannu babu adadi. Bayan shigarta ne shima ya shiga motar ya tada ta suka bar gurin zuwa asibiti…..✍️

 

_Kai na na mini ciwo_.🥺

 

 

*BY*

*JASMINE*🌸🌸

 

*ASP ZARAH*👩‍✈️

 

*BOOK 2*

 

*Page 3*

 

Da kwatance take nuna masa hanya ya Isa har ƙofar gidansu bayan ya kaita Pharmacy an duba lafiyarta duk da ba wani rauni sosai ta ji ba, ita ta fara shiga cikin gidan jim kaɗan kuma Na’ima ta fito ta gaidashi tare da faɗin ance ya shiga daga ciki, babu musu kuwa ya bita har cikin gidan inda aka shimfiɗa masa tabarma a tsakar gurin Inda su Malam ke zaune tare tare da Hajara.

Bayan gaishe gaishe ne M.J ya kuma basu hakuri akan abinda ya faru, nan suka nuna babu wata matsala, miƙewa sukayi duka inda aka barshi da Hajara bayan ta kawo mishi sihirtaccen zoɓon da Ummansu ta haɗa mishi, duk da yake mutum ne mai ƙyanƙyami amma haka bai hanashi shan zoɓon ba ganin kamar yanayin mutanen baiyi kama da ƙazamai ba.

Sun daɗe suna hira kamar da ma can sun saba duk da shi ba mutum bane mai yawan magana amma ya sake sosai yana hira da ita, ya jima kafin ya musu sallama ya tafi bayan yayi musu ɓarin naira tare da alƙawarin zai dawo ya duba jikin Hajara, haka sukayi sallama zuciyar wannan ahali cike taf da farin cikin samun wannan arziki da sukayi.

 

Yana tafe amma zuciyarshi fal tunanin mutanen da yau ne ya fara haɗuwa dasu musamma ƴar su da ta riƙe mishi zuciya lokaci ɗaya yaji kamar sonta na barazanar kamashi, lokaci guda kuma zuciyarshi ta aminta cewa ya samu kalar matar da yake nema a fannin tarbiyya duk da yanason mace wacce tayi karatun boko, fata yake a cikin ranshi Allah yasa babu wanda ya riga shi domin kam bazai yarda yayi rashin wannan kamilar mace ba. Da wannan tunanin ya isa office amma ya kasa taɓuka komai tunanin yadda zai ɓullowa su Daddy da zancen ƙara aure ne ya dameshi musamman da bayaso auran ya wuce nan da wata ɗaya ko biyu.

 

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

 

Cike da ƙosawa Jiddah ta kalli Raliya dake faman zubda hawaye tace

“Kina daɗa ɓata mana lokaci fa idan ba zakiyi magana bane ki faɗa tun wuri mu samawa kanmu masalaha.”

 

“Bansan ta yaya bane zaku isa ga inda Alpha yake domin nima bansan hanyar inda yake ba bare nayi muku jagora.” ta faɗa gami da sunkuyar da kanta ƙasa.

 

Cikin ɓacin rai Jummai ta kawo mata duka saidai bata kai ga isarta ba Zarah ta tare ta tana faɗin.

“Sassauta Jummai abinda ta faɗa gaskiya ne amma tsaya muji ƙarashan zancen” komawa baya Jummai tayi tana huci kamar wani firgitaccen zaki.

“Ke muke saurare Raliya bamu da lokacin da zamu cigaba da zama anan.”

Shiru tayi na wani lokaci kafin tace

“An haifeni ne a garin Jos, ni kaɗai ce ƴar da iyayena suka haifa kuma mahaifina hamshakin mai kuɗi ne na ban mamaki yana da dukiyar da shi kanshi bai san adadinta ba, watarana sai harƙalla ta haɗasu da Alpha batare da yasan ko shi waye ba. A zahiri Alpha dukiyar mahaifina kaɗai yaso karɓa amma ganin mahaifin nawa yasan wasu daga cikin sirrikanshi yasa watarana da daddare yazo har gida ya same mu ni da iyaye ya basu zaɓin ko ya barsu a raye ya kasheni ko kuma ya barni a raye ya kashe su. Haka ina ji ina gani ya bani bindiga na kashe iyaye na da kaina, daga nan ban kuma sanin inda kaina yake ba sai lokacin da na farfaɗo na tsinci kaina a Alpha Villa.” wani gauron numfashi taja mai bayyana abinda take faɗa yana mata zafi a rai kafin ta cigaba da cewa

“Bahagowar Rayuwa muke yi acikin wannan gida ni da wasu daga cikin matan da yanayin rayuwa yakai su wannan wajen, na daɗe kafin nasan wasu daga cikin abubuwan dangane da Alpha a lokacin ne nagane cewa ba shi ne yaje ya samu mahaifina ba wani yaronsa ne domin a yadda ake bani labari babu wanda ya taɓa ganin wani ɓangare na jikinsa wanda za’a iya shaida shi dashi, tun daga lokacin na ɗau alwashin sanin wani abu dangane dashi. A haka na cigaba da neman kusanci da shi har zuwa lokacin da nayi nasarar ganin faratanshi waɗanda zan iya ganewa a ko’ina idan naga mai kalansu ko shi ɗin, bayan ya gano ni ne kuma ya saka aka shigar dani ɗakin duhu inda anan yake horar da yaran dake mishi akai. Ta haka ne nasan Alpha sosai har na kamu da sonshi matuƙa duk da har yanzu bai taɓa bayyana kanshi gareni. Na rantse da sarkin dake busamin numfashi wannan ne iya abinda nasani game da shi ko da kuwa zaku bani qur’ani na dafa iyaka gaskiya ta kenan.” daga haka ta cigaba da rera kuka a hankali ta barsu kowanne da abinda yake saƙawa a ranshi.

 

Zarah ce ta fara katse shirun ta hanyar tambayarta tace

“A wani mataki kika tsaya da karatu kafin afkuwar wannan lamarin.”

 

“Ina shekarar farko a jami’ar Jos na fara karantar Mass com.”

Shiru suka kuma yi duka na wani lokaci babu mai tankawa kafin Jiddah tace

“Akwai wani ɓoyayyen al’amari da kika sani dangane da rayuwarsa ko wani nasa?”

 

Kusan mintuna uku kafin ta ɗago tace

“Ehh na taɓa karanta wani kundin sirri a ɗakinsa, akwai wata da naga hotonta da sunanta Phalmata.”

 

A tare suka kusan haɗa baki wajen faɗin

“Phalmata.??” fuskar Zarah da Jiddah cike da mamaki.

 

“Meye alaqarsu da ita.”

 

“A yadda na karanta na fahimci cewa ita kishiyar mahaifiyarsa ce kuma tare suka fara duk wannan harkallar, a yadda na gani ma ita kaɗaice yanzu a duniya tasan sirrikanshi na da dana yanzu. Inajin idan kuka nemeta zata iya sanar daku komai akansa musamman a yanzu da suke halin gaba zaku fi samun ingantattun bayanai.”

 

“Kinsan wani abu dangane da inda zamu sameta ne.”

 

“Eh toh ita ɗin fasihiyar na’ura ce bayan haka kuma tana ƴan tsibbace tsibbace, ina ganin ta hanyar tsibbu ne kaɗai zaku iya isa gareta.”

 

“A ina take.?” Saleem ya tambaya cike da ƙosawa domin shi burinshi kawai yaji inda zasu samu wannan matar

 

“Tana garin Dutse a Jigawa.”

 

“Zaki iya tuna adireshinta da kika gani a kundin.”

 

“Eh zan tuna harda fuskarta ma domin yanzu ba ita kaɗai take aiki ba kamar dai Alpha, idan ba sanin wani abu nata akayi ba zata iya haɗa mutum da wata daga cikin masu yi mata aiki a matsayin itace.”

 

Miƙewa Zarah tayi tana gyara tattarewar da kayanta yayi saboda tsugunno da tayi, kana ta kalli abokan tafiyar tata tace

“Muje koh? Jummai ke kuma zuwa gobe ki wuce da ita gidanki ta cigaba da zama acan amma ki tabbatar da tsaro.”

 

“Toh ranki ya daɗe Allah ya tsare.”

Da haka suka fice zuwa inda motarsu take, kai tsaye office ɗin Zarah suka wuce domin tattaunawa.

 

“Zamu ɗaukarwa Raliya malamin dazai dinga koya mata zane-zane domin lallai da taimakonta ne zamu samu zanen hoton Phalmata da yatsun Alpha.” cewar Zarah bayan sun zauna zaman tattaunawa akan matsalar.

 

“Nima nayi tunanin haka, amma bakya ganin koyamata zai ja lokaci? Ina ganin a neme mai zanen kawai ta dinga fasalta mishi ya zana koh.”

 

“A’a Saleem yarinyar tana da kwakwalwa sosai zata koya cikin ƙanƙanin lokaci musamman idan muka mata barazana, da kanta zata fi iya zana komai da ta sani ba kamar idan faɗa take yi ba.”

 

“Wannan haka yake, amma tsawon wani lokaci kenan.?”

 

“Sa-Jid yau muna ɗaya ga wata, a cikin sati ɗaya Raliya zat gama koyan zane tare da yi mana zanen da muke buƙata, a sati biyun da zasu biyu baya na binciko inda Phalmata take ne, a satin ƙarshe na wannan watan kuma zanje Abuja na neme takardar shaidar kama Alpha kunga kenan a wata ɗaya zamu gama wannan task ɗin muje na gaba wato binciko inda Alpha yake tare da kamashi.”

Tafi suka mata cikin jinjina da barkwanci, Saleem ne yace

“Wani lissafin ƴan sanda ne kaɗai zasu iya shi.”

Murmushi kawai tayi sannan tace

“Zanyi magana da Daddy idan yaso shi sai yayiwa M.J maganar tafiyarmu Zamfara”

 

“Shikenan wato har yanzu kunƙi sasanta kanku” cewar. Saleem

Bata ce komai ba ta fara haɗa abubuwanta domin tafiya gida, tare suka fito ta shige motarta bayan sunyi sallama sannan suma suka tada motarsu suka wuce.

 

A kwanakin da suka biyo baya sam Zarah bata zauna a gida ba saboda ta tsaya kai da fata wajen ganin Raliya ta koyi abinda suke buƙata, a ɗaya ɓangaren kuma suna shirye-shiryen tafiya Zamfara ita da ɗan’uwanta Sadiq da kuma Jiddah da Saleem domin tafiyar da zasuyi ba ƙarama bace saboda adireshin da Raliya ta basu yana da nisa da garin dutse sosai dan haka suna buƙatar su shirya sosai.

Wannan dalilin ne yasa kwata-kwata basu haɗu da M.J ba.

 

💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕

 

A ɓangaren M.J da Hajara kuwa soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi ne ya shiga tsakaninsu, basa iya ɗaukar dogon lokaci batare da sunji muryoyin juna ba. Da fari Hajara tanason auran M.J ne saboda kuɗinshi saidai daga baya ta gane shine irin mijin da take so kuma gashi ta samu dan haka ne ma tayi alwashin cewa idan akayi aurensu ta gama aikin da zata yiwa Alpha zata cigaba da zama da mijinta domin ta samu kalarta. Shima a nashi ɓangaren yana mamakin yadda cikin ƙanƙanin lokaci ya kamu da matsananciyar soyayyarta.

 

Takurawar da Malam Surajo ke mishi akan idan yanason ƴarsa ya turo magabata ne yasa yau yasha alwashin bayan ya tashi a aiki zai biya ta gidan ya sanar musu komai zai faru ya faru.

Ƙarfe shida ya tashi a office kai tsaye kuma gidansu ya nufa, saida ya tsaya yayi sallar magriba a masallacin dake unguwar kafin ya ƙarasa zuwa cikin gidan nasu.

A harabar gidan ya ga motar Zarah hakan ya tabbatar masa cewa tana cikin gidan, ba ƙaramin daɗi yaji ba kuwa domin yana son duk abun da za’ayi ayi a gabanta. A babban falo ya tarar da su duka suna ƙoƙarin yin dinner Daddy, Momi, Sadiq da kuma Zarah, dan haka shima kai tsaye teburin ya nufa da suci abincin tare. Gaishe da iyayensa yayi kana ya baiwa Sadiq hannu suka gaisa fuska babu yabo ba fallasa ko da Zarah ta gaidashi sharewa yayi batare da ya amsa ba wanda duk su Daddy sun lura da hakan amma babu wanda ya tanka haka suka fara cin abincin cikin nutsuwa kowa da abinda ke ransa.

 

Bayan gama cin abincin kuwa cikin falon suka koma suna hira har kaɗan kaɗan, cikin dakiya da dauriya tare da fargaba M.J ya buɗi baki yace

“Ehhmm Daddy dama nazo muyi magana ne.”

Tun farkon shigowar shi Momi ta fahimci akwai abinda ke tafe dashi amma sai ta basar batayi magana har yanzu da ya furta da kanshu, murmushin manya Daddy yayi kana yace

“Ina jin ka.”

Shiru ya kuma yi har sai da Daddy yace

“Ko maganar na buƙatar sirri ne.”

Cikin hanzari yace.

“A’a ba wata magana ba ce, dama ehmm dama iyayen yarinyar da nake nema ne suka ce na turo magabata na ayi magana, a taƙaice dai aure nakeson ƙarawa.”…✍🏻

 

 

_BY_

_JASMINE_.🌸🌸

 

*ASP ZARAH*👩‍✈️

 

*BOOK 2*

 

*Page 4*

 

Wata irin zabura Momi da ke kan kujera tayi har saida ta sauko ƙasa ta dira a gaban M.J tana ƙura mishi ido, shikuwa Sadiq wayarsa ƙirar IphoneRx dake hannunshi ne ta saɓule ta faɗi ƙasa ji kake tasss ta fashe akan tiles, murmushin da akewa laƙabi da na ciwo shi Daddy yayi sannan ya kalle Momi da Sadiq yace

“Mene ne haka kamar kun riski saƙon mutuwar wani na jikinku.?”

Jan jiki Momi tayi ta jingina da kujerar da Zarah ke zaune,wacce tun faɗar maganar M.J zuciyarta taki nutsuwa a ƙirjinta sai barazanar fitowa take yi. Daddy ne ya kuma magana yace

“Muhammad Jawwad kace aure zaka ƙara koh.?”

Cikin fargaba da tsoro jin Daddy ya kira asalin sunanshi abinda bai taɓa ji daga bakin uban nasa ba tun yarinta,ya gyaɗa kai yace

“Ehh Daddy.”

 

“Ƙarya kake yi wallahi ba isa ka jamin zagi a gari ba Jawwad, bazai taɓa yiwuwa ba wani kallo kakeso a dinga min idan na shiga cikin mutane.” Momi ce ta faɗi haka cikin hargowa tana mai fashewa da kuka.

Kaɗa kai kawai Daddy yayi cikin takaici ya kuma maida hankalin shi ga M.J yace

“Shin zan iya sanin dalilin ƙarin auren ko akwai wani abu da Zarah take maka ne wanda bakajin daɗinsa.”

 

“Babu komai Daddy dama muna soyayya da yarinyar ne yanzu kuma mahaifinta ya ce yana bukatar aurar da ita.” ya fada kai a sunkuye.

 

“Kaji ka amince cewa kanason yarinyar kuma zaka aureta .” Daddy ya kuma tambaya.

 

“Ehh Daddy.” ya amsa a taƙaice.

 

“Shikenan tunda dai kai kazo da zancen bazan hanaka raya sunnah ba , na yarje maka kaje kayi aurenka amma bawai dan hakan zai min daɗi a raina ba, kaje ka fara shiri sannan ka turomin adireshin gidansu yarinyar nan da sati biyu masu zuwa in sha Allah za’a ɗaura maka aure da ita kamar yadda kake so. Sai dai inaso ka shaida wallahi duk wani abu da ya biyo baya karka tunkareni da shi. Tashi kayi tafiyarka.”

 

“Nagode Daddy.” ya faɗi haka da hanzari ya mike ya fice daga falon gudun kar Momi ta kuma yin magana

 

Baki sake kamar mutum-mutumi Momi ke kallon Daddy kamar wacce taga wani abin al’ajabi mai girma, shikuwa Sadiq sarkin zuciya har ya mike ya finciki hannu Zarah da nufin su fice a falon Daddy ya dakatar dashi, cak! Ya tsaya ita kuwa Zarah tuni ta fara sana’ar tata na kuka.

 

“Indai ka ɗauke ni a matsayin uba ka dawo ka zauna.”

Babu musu suka juyo suka zauna zuciya sam babu daɗi, mintuna suka shuɗe babu wanda ya tanka kafin daga bisani Daddy ya ce

“Ku yi haƙuri da kalan hukuncin da na yanke, akwai wani abu da na hanga ne da sannu zaku ga abinda zai biyo baya domin jikina baya bani akwai alkhairi a ciki. Kiyi haƙuri Zarah faruwar komai jarrabawa ce daga Allah watarana sai labari., labarin ma watarana va za’a samu masu bada shi ba. Kiyi hakuri kinji, Allah ya jiɓanci lamuranki, kai Sadiq tashi ka rakata gida.”

Babu musu ya miƙe ita kuma ta yi musu sallama suka wuce, a hanya babu mai magana a cikinsu har lokacin da suka isa har cikin harabar gidan M.J kafin Sadiq ya riƙo hannunta ya ce

“Ki dinga yawan tunawa da nasihar da Abba yake mana a ko yaushe, hakuri shine ribar zaman duniya, nima inaso na dinga kwatanta hakan sai dai zuciyata bata iya jure ganin ɗayan ku cikin ƙunci. Da sannu ni da kai na zanzo har cikin gidan nan na ɗauke ki na kaiki inda zaki samu farin ciki na har abada.”

Murmushi kawai tayi mishi kana ta fita a motar ta shige gida, shi kuma ya juya kan motar ya fice a harabar gidan.

 

Kamar yadda suka tsara cikin sati Raliya ta zana musu fiskar matar kamar yadda ta dage wajen koyan abinda ake koyar da ita. Sai dai batun tafiyar ta su a katse sakamakon tasuwar bikin mijin Zarah.

A wannan lokacin kuwa tuni batun auran M.J ya kankama domin an bada sadaki sannan ankai kayan aure ranar kawai ake jira tazo a ɗaura auran, sai dai mutane da dama basuyi farin ciki da wannan auran ba amma babu yadda aka iya da hukuncin Allah.

 

Rana dai aka ce bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, kamar yadda ya kasance ranar juma’a bayan zagayowar sati aka ɗaura auran Muhammad Jawwad Sulaiman da Hajara Suraj, bikin daya kasance tamkar na bazawara saboda rashin jama’a.

Haka amarya dai ta tare a gidan mijinta cike da buri a ranta na abubuwan da ta shigo cikin gidan da niyyar aikatawa.

 

Hausawa kan ce _Rawar da aka fara ta da tsalle ƙarshenta baya kyau_, kamar haka ce ta faru a gidan M.J wanda tun farkon kawo amaryarsa ya nuna mata cewa Zarah bata da wani matsayi a gurinshi face na ƴar uwa domin baya mata kallon matarsa, wannan dalilin ne ya saka sam Hajara bata ganin girmanta bare ayi tunanin zasuyi zaman amana, a wasu lokutan a gaban Hajara M.J ke yiwa Zarah cin kashi tare da cigaba da yi mata ƙazafin zina batare da lura da illar hakan da zai haifar masa anan gaba ba.

Yau ma kamar kullum Zarah ta dawo daga aiki a gajiye liƙis, ta shigo babban falon ɗauke da sallama a bakinta, kamar ko da yaushe suna kwance a dogowar kujera manne da juna suna soyayya tamkar zasu haɗiye juna, yau kwanansu goma kenan da aure amma kullum a haka suke wuni tare batare da M.J yayi tunanin bada haƙƙin addini akan wanda yayi sabon aure ba ko da yake bata zaton hakan daga gareshi domin ko da take ita kaɗai ma baya bata haƙƙinta daya rataya a wuyansa. Tunaninda takeyi ne ya katse sakamakon muryar Hajara da ta daki cikin dodon kunnenta tana faɗin

“Hubby haka kenan gidanka zai cigaba da kasancewa mafakar fasiƙai alhalin da ranka da lafiyarka.?” mikewa yayi daga kwancen ya zauna sannan ya dubi Zarah dake ƙoƙarin shigewa part ɗinta ya ce

“Ina fatan kin wanke janabar da kika ɗebo tun a waje baki shigomin dashi cikin tsabtaceccen gidana ba.?”

Kaɗa kai kawai tayi sannan ta shige ɗakinta cike da takaici domin ya ci ace ta saba da irin cin kashin da mijinta da kishiyarta ke mata a duk kwanan duniya.

 

*1:45am*

 

A daidai wannan lokacin ko wani halitta na ɗan adam yana tsaka da bacci in ka ɗauke ɗaiɗaiku da wani uzurin ya hana su bacci, cikin waɗanda basu yi bacci ba a wannan lokacin harda Zarah dake zaune gaban na’urarta tana gabatar da wani aiki gefenta kuwa wani ƙaramin kofi ne da shayi a ciki sai tururi yake yi, tana sanye da riga da wando na bacci mai santsi kalar sararin samaniya ta ɗaura wata hula mai gashi a kanta, gabaɗaya hankalinta ta maida akan aikin da take gabatarwa.

A hankali ta miƙe ta nufi window ɗin ɗakin saboda jin alamun kamar hayaniya na tasowa daga farfajiyar gidan, labulen ta ja kaɗan tare da leƙa tsakar gidan ga mamakinta sai taga kamar gilmawar mutum, ganin dare ne yasa bata wanj damu ba ta koma inda take zaune da ta cigaba da aikinta.

Zamanta ke da wuya ta ji an hayaniya da kururuwar Hajara a babban falon tare da sallallami da M.J ke yi, take ta gane cewa wasu sun shigo cikin gidan, da sauri ta miƙe ta ɗauki jacket ɗinta ta saka sannan ta zari ƙaramar bindigarta ta nufi falon. Ai kuwa kamar yadda ta zata mutane ne a falon su tara kowanne da shiga mai kyau fuska a rufe, uku daga cikinsu ne kawai maza amma duk sauran mata ne, ganin fitowarta ne yasa wasu mata su huɗu suka nufeta da nufin rikota, wani wawan naushi ta kaiwa waɗanda ke da nufin riƙe mata hannu da duka hannuwanta biyu sannan ta sunkuya ta kaiwa wacce take gabanta naushi a ciki take ta durƙushe saboda zafin da taji. Sai dai kafin ta kuma wani yunƙuri wasu suka tura ta ta faɗi ta gaba kafin ta ɗago suka yi nasarar ɗaure mata hannaye. Ɗaya daga cikinsu ne yayi maganar su ƙyale Zarah haka sannan ya juya ya kalli M.J ya ce

“Ran matan ka ko kuma dukiya.?”

Cikin kauda kai M.J dake riƙe a hannun ƙarti biyu da mace ɗaya yace

“Malam ni matata ɗaya ce kuma gata nan” ya nuna Hajara sannan ya cigaba da cewa” Ku kama wacce ta muku laifi ku rabu da mu.”

 

Dariya yayi sannan yace

“Ya za’ayi mu yarda da hakan bayan a mun shaida ɗaurin auren ku.”

 

Shiru yayi na wasu mintuna sannan yace

“Idan kuna so ma zaku iya shaida warwarewarsa.”

Cike da dariya mugunta ya kuma cewa

“Mai zai hana kuwa.”

 

Cike da takaici Zarah tace

“Yaya Jawwad kada kayi abinda zaka zo kana da na sani, ina da rauni sosai sannan ni marainiyace. Kada ka lalatamin rayuwa ta hanyar maida ni ƙaramar bazawara.”

Bai kula da maganganunta ba ya ce

“Na sake ki saki ɗaya Zarah.”

Tabbas mutuwar aure babu daɗi ko da babu soyayya wannan dalilin ne yasa Zarah taji zuciyarta tayi mata zafi sosai lokacin da ɗan’uwanta ya furta kalmar saki a gareta.

 

“Kinsan abinda ya kawo mu dan haka ki bamu salin alin saboda yau zamu yi ta mukare tsakanin mu da ke.” Mutumin ya kuma faɗa batare da ya kula da halin da take ciki ba, kauda kai tayi gefe tana addu’ar Allah ya bata nasarar kunce kanta duk da suna da yawa tasan zata iya musu mugun lahani ba tare da makami ba ma. Saura ƙiris ta fasa ƙara saboda wani gigitaccen zafi daya ziyarce ta a gefen cinyarta, kallonta ta maida gurin taga ashe ɗaya daga cikin matan nan ne ta yi mata muguwar yanka a cinyarta take kuwa jini ya ce dama hanya nake nema nan ya fara zuba tamkar kwararo shi ake yi, raɗaɗi take ji sosai amma hakan bai sa ta amsa tambayar da ya kuma mata ba, ya ce

“Ba zakiyi magana ba ke wace iriyar yarinyace mai taurin kai ne, mtsssw ku shiga ku bincika min ko ina a cikin gidan nan.”

Dukkansu suka nufi hanyar da suka ga Zarah ta fito mutum uku kaɗai suka bari biyu na tsare da M.J da Hajara sun saka musu bindiga akai sai babban dake gefen inda Zarah ke ɗaure yana wasa da wuƙar hannunshi yayinda ɗaya hannu ke rike da bindiga. Kusan mintuna arba’in suna dube-dube a cikin gidan amma basu ko ga wata alamar da zata nuna musu cewa Diamonds ɗin suna cikin gidan ba, cike da rashin kwarin gwiwa suka dawo suka sanar da shi, bai ce komai ba ya zaro waya ya daddanna sannan ya kara a kunnenshi jim kaɗan ya fara magana yace

“Yallaɓai jiya i yau fa, taurin kan yarinyar yayi yawa ta tushe kowace hanya bata bamu damar sanin komai ba.”

Huci ya furzar mai zafi kana yace

“Wannan karon inaso ku taɓa Zarah, ina so taji a lafiyarta cewa ba’a gardama dani, ina so taji lallai cewa bazata iya cigaba da ajiyar Diamonds ɗin nan ba, lallai ku yi mata mummunan lahani kamar yadda zuwa yanzu na tabbatar idan Raliya tana raye to tana cikin mawuyacin hali.”

 

“Angama ranka ya daɗe.” daga haka ya katse wayar ya kalli matan dake tsaye ya ce

“Ku cika aiki” tamkar suna jira haka suka ruftu su biyar akan Zarah kowa da irin dukan da yake kai mata amma duk da haka ko tari bata yi ba bare ayi tunanin zatayi kuka.

Karo na farko Hajara taji mugun tausayi da dana sani sun baibayeta, ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, sosai taji da na sanin haɗa kai da ita da akayi tun farko har zuwa yau da suka shigo cikin gidan nasu. Shikuwa M.J ba yadda za’ayi ka gane yanayin da yake ciki domin fuskarsa tana nan yadda take.

Cikin mintuna ƙalilan farin tiles ɗin dake falon ya fara rinewa yana yin ja saboda jinin dake gangarowa daka jikin Zarah sakamakon bugu da yanka da suke jikinta, ganin kamar ta daina numfashi ne yasa ya dakatar da su sannan suka fice a gidan.

Da hanzari Hajara ta rarrafa ta isa kanta hawaye na biyowa a idanunta ta juya ta kalli M.J ta ce

“Hubby ɗauki key da sauri mu kaita asibiti.”

 

“Ni? Asibiti? Babu inda zan fita da daren nan, ita ta jawo wa kanta.”

 

“Ka dubi halin da take ciki mana dan Allah ka taimaka.”

 

“Yaya Jawwad dan Allah ka kiramin Daddy ko da bazaka kai ni asibitin ba.” Zarah ta faɗa a galabaice, numfashinta na fita ɗaiɗai.

Bai kula ta ba ya zo yaja hannun Hajara suka nufi ƙofar part ɗin shi, tsayawa yayi cak! Sannan ya dawo ya tsugunna a gabanta yana ƙare mata kallo shi kansa yasan tana buƙatar taimako na gaggawa amma yana jin zafinta sosai a ƙasan zuciyarsa, gyaran murya yayi sannan yace

“Kinsan yanzu babu igiyar aure tsakanina dake, dan haka zan taimaka miki ne kaɗai a matsayin karuwar da nakeso ta tuba ga Allah kafin ta mutu, wannan ne kaɗai gatan da zan miki, kin amince na taimaka miki.?”

 

“Zan fi ƙaunar na mutu a haka matukar da wannan ƙudurin zaka taimake ni, na tsane ka, baka da tausayi ko kaɗan, kai mara imani ne.”

 

Kafaɗa ya kaɗa ya mike sannan yace

“Duk yadda kika gani sai ki kira wanda kike jin shi zai iya taimakonki ko a cikin abokan watsewarki ne.” daga haka yaja matarsa suka shige suka barta a nan kwance.

Cikin dakiya da juriya ta miƙe zaune tana jan jiki harta isa ƙofar da zata sada ta da farfajiyar gidan cikin tsananin azaba da ciwo.

 

 

 

A firgice ta miƙe daga baccin da take yi, juyawa tayi ta kalli agogo 2:05am kallonta ta maida kan Saleem dake sharar baccinsa hankali kwance, a hankali ta fara bubbuga bayansa har ya farka ya buɗe idanunsa ganinta a zaune ne yasa shima ya zauna yana miƙa ya kalleta yace

“Lafiya kuwa me ya same ki.?”

 

“Sa-Jid nayi mafarki Zarah na ta kirana tana faɗin na taimaka mata, zuciyata da jikina sun amsa bana jin daɗi sam ina da tabbacin cewa akwai abinda ke faruwa da ita.”

 

“Me zai faru da ita da wannan daren haba dan Allah mafarki fa ba gaskiya bane.”

 

“Na sani amma dai wannan yayi kama da gaskiya, miƙomin wayar can na kirata.”

 

Hannu yasa ya ɗauko wayar dake kan bedside drawer ya bata, cikin hanzari ta fara danna lambar Zarah tana kira amma kusan kira 30 babu amsa. Zuwa lokacin ta gama ruɗewa, kuka ta sakawa Saleem akan lallai sai ya kaita gidan Zarah a daren duk yadda yaso ta haƙura amma taƙi, sanin da yayi cewa idan damuwa zata iya jawowa ƙaramin cikin dake jikinta matsala ne yasa dole ya miƙe ya zura jallabiya ya ɗauki key ɗin motar suka fice a gidan, har zuwa lokacin kuma bata daina kuka da sambatu ba…✍🏻

 

 

*BY*

*JASMINE*🌸🌸

 

*ASP ZARAH*

 

*BOOK 2*

 

*Page 5*

 

… Su uku ne zaune a cikin wani ƙayataccen falo da yaji kayan alatu tamkar na shugaban ƙasa Sadiq, Rahma da kuma Zarah, kallo ɗaya zaka musu ka gane suna cikin tsantsar farin ciki da suka daɗe basu samu ba duba da yanayin yadda fuskokinsu suka kasa ɓoye farin cikin da suke ciki. Rahma ce ta ajiye cup ɗin dake hannunta a center table ɗin dake gabanta sannan ta juyo ta dubi Sadiq dake nunawa Zarah abu a waya suna ƙyalƙyala dariya ta ce

“Bazan iya tuna ranar ƙarshe da naga dariyarku haka ba musamman Zarah.”

 

“Ba mu da wata sauran damuwa ne shiyasa ki ka ganmu haka, ke ba abin farin ciki bane a gareki ace yau wanda yayi sanadin da iyayenmu suka bar duniya shima ya mutu ta dalilinmu, baya ga haka ƴar’uwar mu wacce muke tunanin ta zauce yau ta samu lafiya ingantacciya, kinga kuwa dole mu yi farin ciki.” Sadiq ne yayi wannan sharhin bayan ya maida hankalinsa kanta.

 

Gyaɗa kai tayi ciki da gamsuwa tace

“Haka ne amma naku ne kawai ke fitowa fili, nawa na barshi a zuci.”

Zarah waccw tun da aka fara maganar bata tanka ba ta ɗago tace

“Meye zai hana ki fito dashi fili mu haɗu mu yi murnar tare.”

Cike da zolaya Rahma tace

“Yau kam naci girma na bar muku.”

Ɗaya daga cikin ƙananun pillows ɗin dake kan kujerar Sadiq ya ɗauka ya jefeta da shi cikin harara yace

 

“Ke banson raini fa”

 

Itama cikin zolaya tace

“Kwanaki ƙalilan a ne tsakaninmu fa.”

 

“Duk da haka dai ya riga ki shaƙar iskar duniya.” Cewar Zarah.

 

“Haka ne toh na baka girman ka, yanzu daga nan ina zaku wuce.”

Shiru sukayi na wani lokaci kafin Sadiq yace

“Daga nan Malasia zamu wuce, Little zata fara karatun masters ɗinta acan, ni kuma na cigaba da aikina.”

Fuska ta sauya kamar zatayi hawaye tace

“Za mu ƙara yin nisa da juna.?”

 

“Ki shirya mu tafi tare.” fadin Zarah.

 

Hararar wasa ta mata sannan ta kuma cewa

“Na gaji da kawaici fa, tun ɗazu inaso ku ɗauko min hirar abubuwan da suka faru amma kun share.”

Dariya suka yi duka sannan Sadiq yace

“Tun ɗazu na lura dake kawai na yi miki shiru ki furta da bakinki.”

 

“Na tambaya yanzu a gayamin meya faru.”

 

“Labari ne mai tsawo fa ki nemo biro da takarda” Inji Zarah.

 

“A’a bani wannan baiwar sai dai na kira Sis Jasmine ta mana aikin rubutun.”

 

“Tom shikenan haka za’ayi.”

 

“Ke nake sauraro.”

 

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

 

Ina cikin tsananin azaba a wannan rana da yaran Alpha suka shigo har gida sukamin rauni amma Yaya Jawwad yaƙi ko kula da lamarina bare yayi tunanin kaini asibiti duk da a lokacin babu dangantakar aure a tsakaninmu amma nayi tunanin zai taimakeni a matsayi na na ƴar’uwarsa sai dai hakan bai kai ga ci ba. Ganin sun bare yashe a falo cikin jini ne yasa nayi ƙoƙarin nafara jan jiki domin zuwa na saka Baba Mai gadi ya kiramin Daddy ko Sa-Jid saboda a halin da nake ciki a wannan lokacin nasan komai zai iya faruwa dani sakamakon jinin da ke zuba daga jikina, da jan jiki na fita har farfajiyar gidanmu zuwa ɗakin Mai gadi sai dai nayi rashin sa’a domin shima sun yi mishi duka bai san inda kansa yake ba. A lokacin nafara ficewa daga hayyacina saboda tsananin azaba da zafin raunukan dake jikina, ina cikin wannan halin ne naji ana horn a ƙofar get ta waje amma bani da kuzarin da zan iya xuwa na buɗe, an daɗe anayin horn ɗin daga baya kuma akazo jikin ƙofar ana bugawa, ganin gate ɗin a buɗe ne yasa su shigowa ba kowa bane illa Sa-Jid.

Ko da suka shigo da ni suka fara yin arba a kwance cikin jini ai kuwa hankalinsu ya tashi sosai domin saida Jiddah ta suma dakyar ya samu ta nutsu kaɗan sannan ta taimaka mai suka shigar da ni cikin motar ba su ko kula da mai gadi ba bare su ɗauke shi mu tafi asibitin a tare saboda tsananin firgici da suke ciki. A guje Saleem ya ja motar muka bar cikin anguwar muka nufi hanyar asibiti, gudu yake yi tamkar zai tashi sama saboda azalzala da Jiddah ke yi masa, ni dai a lokacin sama-sama nake iya jiyo maganganunsu saboda zafin raunukan dake jikina da kuma jinin da har a lokacin bai daina zuba ba. Cak! Motar ta tsaya taƙi yin gaba ko baya duk yadda Saleem yayi ƙoƙarin ta motsa amma taƙi hakan ne yasa ya fito daga cikin motar cikin tsananin mamaki domin yasan motarsa lafiya lau take sannan akwai mai sosai a ciki, buɗe-buɗe ya fara yi yana dubawa ko zai ga ta inda matsalar take amma bai fahimci komai ba, ganin haka yasa itama Jiddah ta fito a motar tana taya shi dubawa ko zasu gano matsalar motar. Kamar wanda aka umarta haka ya sunkuya ƙasa tare da leƙa ƙasan motar, abinda ya gani a gurin ne ya matuƙar bashi mamaki, bakomai ne ya hana motar tafiya ba illa wani littafi ƙaramin dake ƙasan tayar gaba na hagu, cikin al’ajabi ya sa hannu ya zaro littafin da ƙarfi, cikin zarewar idanu ya nunawa Jiddah littafin wanda a bango cikakken sunana ne a rubuce cikin rubutu mai matuƙar kyau. A wannan lokacin bana tsayawa wasu maganganu bane saboda halin da nake ciki hakan yasa Saleem ya ajiye littafin a gaban motarsa zuwa lokacin da zan samu kaina. Bansan abinda ya faru ba domin a lokacin juriyata ta ƙare tuni na sume, a haka muka isa asibitin cikin gaggawa, ba mu sha wahalar samun likita ba domin a wannan asibitin Jiddah ke aiki sannan ita ke dubani lokuta da dama idan kalar hakan ta faru, a wasu lokutan ma bama zuwa asibiti idan zamana a asibiti na da hatsari.

Emergency room aka shigar dani, nan da nan Jiddah da wasu likitoci biyu tare da nurses suka duƙufa domin ceto rayuwata, sai bayan da aka idar da sallar asuba’i kafin numfashina ya daidaita bayan sun gyaramin raunukan dake jikina sannan nasha ɗinkuna a waɗanda ke buƙatar ɗinki. Daga haka aka yimin alurar bacci sannan Jiddah da kanta ta turani ɗakin hutu. Sai a lokacin ta samu sukunin kiran Daddy ta shaida mishi abinda ke faruwa, ba’ayi mintuna ashirin ba kuwa sai gasu a cikin asibitin gabaɗayan su harda Baaba, ganin yanayina kuwa ta matuƙar ta da musu da hankali nan suka tambayi abinda ya faru, Saleem ne kaɗai ya iya buɗe baki ya musu bayani tun daga kan farkawar Jiddah daga bacci har zuwa lokacin da nake kwance bansan me ke gudana ba.

 

Sun shiga damuwa sosai musamman Baaba da a lokacin take tunanin na mutu ne ake ɓoyewa, shi kuwa sarkin zuciya Sadiq ya kasa furta ko kalma ɗaya amma kallo zaka yi masa ka gane yana cikin tsananin damuwa da ɓacin rai duba da yadda idanunsa suka sauya kala zuwa jajaye sannan kyakkyawar farar fuskarsa ta rine tana nuna alamun ɓacin rai. Haka suka zauna shiru har ƙarfe goma na safiya amma ban farka ba wannan dalilin ne yasa Momi da Daddy suka nemj komawa gida domin taho da abinda ba’a rasa ba na buƙatar majinyaci domin ita kam Jiddah ta ce babu inda zata motsa sai taga farkawa ta, tana gefen Baaba a zaune acan wata kwanar ɗakin suna sharar kwalla lokaci lokaci.

Duk cikinsu babu wanda yayi tuna M.J bare ayi tunanin abinda ya hanasa zuwa a matsayinshi na mijinta, Sadiq ne kawai ya farga ga haka tun lokacin da yazo baiga M.J a wajen ba yasan akwai wata manaƙisar a ƙasa saidai ya share saboda jiran farfaɗowata amma cikin ranshi ya ɗau alwashin cin zarafin M.J matuƙar ya bincika ya samo da sa hannunshi a cikin abinda ya faru dani.

Wani abu da nafara manta wanzowarsa a cikin shafin rayuwata shi ya sameni a lokacin da nake tsaka da baccin dole da likitoci suka sani yi sakamakon allurar baccin da akamin, duk da daɗewar shekaru amma ko a ina naga wannan fuskar zan ganeta, kinsan wacece?”

 

Rahama dake sharar kwallar tausayin ƴar’uwar tata ce ta girgiza kai alamun a’a domin ba zata iya bude baki tayi magana ba, tabbas ta daɗe bataji ko a labari ba wacce ke da irin ƙaddarar Zarah, domin da ta fita daga wannan take kuma shiga wata batare da ta warke ƙuncin da ke ranta ba.

 

Numfasawa Zarah tayi sannan ta cigaba da cewa.

 

Ba kowa bace face Almajirata wacce na daɗe da fara manta abinda ya gudana a tsakaninmu, ina tsaka da wannan baccin nayi mafarkinta ta zo min tana hawaye tace

“Kamar yadda na ɗaukar miki alƙawarin cewa zan barki a baya amma zan kuma dawowa domin taimakonki, Batula ban taɓa nesa daga inda kike ba saidai kawai ina ɓoye kaina ne saboda alƙawarin da na miki na rashin bayyana a gareki. Sai dai a yau na bayyana gareki ne domin taimaka miki akan abinda kw jefa rayuwarki cikin ƙunci. Ki riƙe wanna littafin duk wasu bayanai da zaki buƙata na Alpha yana ciki baki da buƙatar zuwa wani waje domin samo su.” Ta ƙarashe maganar tana mikomin wanj ƙaramin littafi dake hannunta, cike da rauni na miƙa hannu na karɓa ina kallon jikin littafin, ɗagowa nayi da nufin tambayarta saidai kuma banganta ba. A daidai nan na farka daga baccin a firgice ina faɗin “Kin bani littafin.?” a gaggauce Jiddah ta matso kusa da ni ta riƙeni tana ƙoƙarin maida ni na kwanta.

Bansan abubuwan da nake furtawa ba a lokacin sai dai naji Jiddah na faɗin

“Littafin yana cikin motar Saleem bari na kira shi ya shigo miki dashi.” daga haka na maida kaina ina sauke numfashi a hankali. Shuɗewar mintuna goma ne ya dawo dani hayyacina, a lokacin ne kuma na fara jin raɗaɗin raunukan dake jikina, haka nayi ta daurewa har zuwa lokacin da wata Nurse ta shigo, ganin idona biyu ne yasa ta kuma suka dawo da likita ya ƙara duddubani tare da tambayata inda kemin ciwo, nan na faɗa mishi ina jin zafin raunukan jikina cikin sanyayyar muryata ta marasa lafiya, take ya haɗa allurai yayi min sannan suka fice a ɗakin suna mai ƙara yimin addu’ar samun sauƙi.

Fitarsu ke da wuya Baaba da Jiddah suka ƙaraso kusa da gadon nawa suna jeramin sannu kamar zasu aro baki, da taimakon Jiddah na samo na miƙe zaune bayan ta saka filo a bayana na jingina da gadon, zafin da nakeji ya ragu sosai sakamakon allurar rage zugi da akamin, wannan ne ya bani damar yi musu ƴan tambayoyi game da mutanen da nake da tabbacin zasu zo dubani, nan Jiddah ke gayamin Daddy da Momi suna hanya sunje gida su dawo ne, Saleem kuma ya fita samo musu wani abu su ci kafin Momi ta kawo abinci sai Sadiq da ta nunamin wanda kw zaune a can gefe. Sai a lokacin na juya a hankali na kalli inda take nunamin ai kuwa na ganshj zaune yana aikomin da murmushin da iyakarsa fuska nima na maida masa martani, a hankali ya miƙe ya tako zuwa inda nake ya dafa kafaɗa ta cike da kulawa yake tambayata ya jiki na amsa mishi. Shiru ya biyo baya kafin ya nisa yace

“Little meya faru ne? ina mijinki yaje ne da bai samu damar kawo ki asibiti ba sai su Jiddah ne suka kawo ki? Meyasa tun zuwanmu ba muga yazo domin duba lafiyarki ba ko baya ƙasar ne?”

 

“Habu ka kiyayeni fa, yarinyar na gadon jinya zaka tasa ta a gaba kana yi mata irin waɗan nan tambayoyin da basu shafi lafiyarta ba.” Baaba ta faɗa cikin hargowa.

Murmushi nayi mai ciwo sannan na kalleta nace

“Baaba ina jin ƙarfi sosai a jikina yanzu,karki ga laifinshi dan yamin waɗannan tambayoyin. Yaya kasan meye a tambayarka akwai gyara, a yanzu zaifi dacewa ka dinga danganta Yaya Jawwad a matsayin Yayana ba miji ba, domin a yanzu yadda nake nan babu igiyar aurensa a kaina.” Na faɗa ina zamewa da nufin na koma na kwanta.

 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un, Allah yasa kunnuwana ba daidai suka jimin ba.” Abinda Momi ta faɗa kenan wacce suka shigo a tare da Daddy suka tarar ina wannan zancen, gabaɗaya muka juya gareta muna kallonta har ta ƙaraso inda nake ta zauna tana fuskantata tace

“Zarah dan Allah me naji kina faɗa yanzu? Kice min ba abinda naji kika faɗa ba dan Allah.?” ta ƙarashe maganar tana riƙo hannuna ɗaya da babu ciwo, tausayinta naji ya kamani zuciyata tayi nauyi, tabbas nasan banason auren nan nayi biyayya amma mutuwar aure sam babu daɗi musamman ga mace mai irin aikina lokaci guda mutane zasu juya maganar zuwa wata daban, ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, nasan tabbas Momi tana jin wani irin yanayi a cikin ranta kwatankwacin yadda nakeji, ban taɓa son M.J ba har gobe amma ban taɓa fatan ace aurenmu dashi ya rabu ba. Cikin murya mai rauni na ce

“Ehh Momi hakane aurenmu da Yaya Jawwad ya rabu a daren jiya.” wasu hawaye masu ɗumi naji suna zubomin saboda hoton abinda ya faru a wannan daren daya bayyana cikin kwakwalwata. Salati suka saka gabaɗaya illa Jiddah gwanar kuka da tuni ta fara zubda hawaye, shikuwa Sadiq yana tsaye a gefena har wannan lokacin sai dai babu wanda zai iya tantance yanayin da yake ciki.

Daddy ne yayi ƙarfin halin tambayata yace

“Daughter me ya faru ne kin saka mu a cikin ruɗani.”

Cikin nauyinsu da nakeji na labarta musu abinda zan iya tunawa, ai kuwa tamkar waɗanda ke jiran ƙiris nan suka soma fashewa da kuka hatta Daddy sai da yayi hawaye illa Sadiq da kallo ɗaya zaka mishi ka firgice da yanayinsa na tsantsar ɓacin rai da yake ciki.

Nan suka fara jajanta abin kowa da abinda yake faɗi akai musamman Momi da saida Baaba ta tsawatar mata saboda ɗiban albarka da take yiwa M.J ba ƙaƙƙautawa.

Tare muka wuni a asibitin har Daddy kowa da kalar kulawan da yake bani, cikin wuni ɗaya kuwa tamkar wacce ta daɗe tana jinya naji na samu ƙarfin jiki sosai, duk waɗannan abubuwa dake faruwa zuciyata a ƙage take dare ya ratsa na samu na karanta littafin da Saleem ya kawomin wanda dashi nakeson amsa musu tambayoyin da suke ta yimin akan littafin musamman Jiddah.

Sai wajen ƙarfe goma na dare su Momi da Saleem suka yi mana sallama aka barni da Baaba da Jiddah domin kwana da ni, duk yadda akaso Jiddah ta je gida ta turje hakan yasa aka barta mu kwana tare.

Kaɗan-kaɗan muke hira har bacci ya rinjayi Baaba ta kwanta ta barmu ni da Jiddah muna hirar, ganin baccinta yayi nisa ne yasa na fito da littafin daga ƙarƙashin filon da nake kwance na yafito Jiddah tazo gefena ta zauna muka buɗe littafin a hankali mu ka fara karantashi cikin zumuɗi.

 

*ASALIN LABARIN WANZOWAR ALPHA*…✍🏻

 

 

_🙏🙏🙏 Nima na shaida nasan kuna haƙuri da ni sosai musamman ƴan VIP da yanzu bana iya muku update kullum. Dan Allah kuyi haƙuri abubuwa suna yimin yawa ne amma zan dinga ƙoƙari in sha Allah.🥰🥰 Kamar yadda nasan kuna yi inaso ku cigaba da sani a addu’o’inku akan abinda na sa a gaba.🙏🙏🙏 Ina son ku irin totally💃💃💃

 

 

*BY*

*JASMINE*🌸🌸

 

*ASP ZARAH*👩‍✈️

 

*BOOK 2*

 

*Page 6*

 

_Mafarin Lamarin_.

 

Asalin sunansa Al’amin, ya kasance ɗa na biyar ga Malam Mudi da matarsa Inna Habi, sauran ƴan’uwansa uku mata da namiji ɗa inda ya kasance auta, bayan haihuwar Al’amin ne Malam Mudi ya ƙaro aure inda ya auri wata bazawara da ake kira da Phalmata, tun daga lokacin kuma rainon Al’amin ya dawo hannunta.

 

Saboda kulawar da take bashi yasa Inna Habi ta bayan ta yayeshi ta tattara kayansa ta maidawa Phalmata riƙonshi gaba ɗaya.

 

Shekararsa takwas kacal a duniya Allah yayiwa Inna Habi rasuwa, a wannan lokacin duk sauran yayyinsa sunyi aure illa ɗan’uwansa guda da shima yake shirin yi. Tun ƙuruciya Phalmata ke koyawa Al’amin dabarun sace kuɗin mutane da zarar sunyi sake sai dai duk da haka bata gaza wajen ganin cewa ya samo ingantaccen ilimi saboda wani buri da ke ranta, baya ga haka itama tayi karatu kuma ta ɗanɗani daɗinsa.

 

Tun girmansa sai ya kasance ya kara haɗuwa da abokai masu irin tarbiyarsa, tun daga wannan lokacin lamarin satarsu da fashi ya shahara, sai dai suna yin komai ne cikin basira basa taɓa bari su bar shaidar da za’a gane su.

 

Bayan kammala karatunsa na Jami’a ne Allah yayiwa mahaifinsa rasuwa, a wannan lokacin ne Phalmata ta baiyana masa shirinta na zamewarsu shahararrun ƴan ta’adda da zasu addabi ƙasa da duniya baki ɗaya. Suna kashe duk wanda suka nemi dukiyarsa ya hana, sannan muddin suka kwallafa rai akan abu sai sun samu. Haɗewar sunan Phalmata da Al’amin ne ya samar da sunan ALPHA wanda mutane da dama suke tunanin sunan na mutum ɗaya ne.

 

Shararsu ne tasa gwamnati ta shiga neman hanyar da zata kamasu gadan-gadan, sai dai sun siye baki mutane da dama daga sama wannan dalilin ne yasa duk sanda zasu tura yaransu yin fashi suke hada baki da manyan jami’ai domin a dakatar da tsaro a inda zasuje ɗin.

 

Sun yi nesa da inda mutane suke sannan sun alkinta kansu ta yadda babu wanda zaiyi tunanin saninsu ko yasan wani abu dangane da su.

 

A yanzu haka suna rayuwa ne a garin Enugu a cikin wani ƙauye da ake kira Keruba, wani abun mamaki shine duk da a cikin mutane suke amma hakan baisa mutane sun shaida su, dalili kuwa shine, wani madaidaicin gida kamar ko wanne gida da kuka saba ganin mutane na rayuwa a ciki, amma a ƙasan wannan gida rantsatstsiyar fada ce tamkar ta sarakai wacce aka yiwa laƙabi da _ALPHA VILLA_.

Babu wanda yasan a inda ƙofar dake sada mutane da Alpha Villa take a cikin wannan ƙaramin gida, a duk lokacin da mutum zai shiga ko fita sai an shaƙa masa hodar dake saka bacci na wasu mintuna.

 

Ta hanya ɗaya ne kacal zaku iya nasarar kama Alpha a sauƙaƙe.

A kowacce ranar Lahadi yana ɓadda kama ya fito daga wannan gidan don ya zaga gari, yakan kwashe awa guda da rabi yana zagawa kafin daga baya ya koma mazauninsa. Babban lagon Alpha guɗa ɗaya ne, wato mace mai ciki. Yana matuƙar tausayin mace mai ciki ko da wucewa tayi ta gabansa sai yaji hawaye na neman fitowa daga idonsa. Saboda haka idan kunason kama Alpha dole ku nemi wata mace da ke da ciki don samun lagonsa.

 

Mun daɗe mu na karatun wannan littafin har dare ya ratsa sannan mu ka gama, ajiyar zuciya mu ka sauke a tare ni da Jidda bayan na rufe littafin na maida shi inda yake, kallon juna mu ka yi cike da rauni kafin Jiddah ta ce

“Na samo mana mafita.”

 

“Mafita? Wace iri?” na tambaya.

 

“Mai ciki ake nema kuma gani sai ki zame min ƴar jagora.”

 

“Ke baki da hankali ne Jidda kinsan me kike faɗa kuwa.”

 

“Wallahi idan kika kuma mu sa min akan abinda na faɗa ban yafe hakkin ƙaunar da nake miki.” Jiddah ta fada tana mikewa ta koma kusa da inda Baaba ke kwance itama ta kwanta, ta barni sororo ina jimami.

Na jima a zaune kafin daga baya na tura littafin ƙasan filo,sannan na sulale na kwanta zuciyata cike da tunanin mafita.

 

Washe gari tunda farar safiya

Sadiq ya iso asibitin, kallo ɗaya za’a masa mutun ya gane cewa bai runtsa ba, Baaba ya fara gaidawa sannan nida Jidda muka gaishe shi ya amsa yana tambaya ta ya jiki. Zama yayi a gefena yace lafiyarki”

Cikin mamaki muke kallonsa ni da Jiddah kowa da abinda yake saƙawa a ranshi.

 

“Amma Yaya me yasa ba zaka barni anan ba.”

 

“Ina so ki yi nesa da M.J banaso ya kuma ganinki bare wani abu ya shiga tsakaninku ko da kuwa kalmace ta fatar baki.”

 

Baaba da ke zaune can gefe ne ta ce

“Haka ba shine mafita ba Sadiq a barta anan ɗin kawai, ai an riga da anyi kuskure ba za’a kuma bari kalan haka ta faru ba.”

 

Ganin Baaba na son jan maganar ne yasa ya ja bakinsa ya yi shiru bai kuma magana ba. Mu na zaune a haka su Daddy suka shigo shi da Momj da Saleem, hannun Sa-Jid ɗin ɗauke da kwandon abinci, gaishe-gaishe aka yi suna ƙara tambayata ƙarfin jikin. Momi ce ke faɗamin cewa Ammi ta kira waya tana gaishe ni, sannan ta ce zasu taho a satinnan, cikin jindaɗi na amsa ina ƙara jaddada ƙaunata a zuƙatan waɗannan mutanen. Jidda ce ta zuba mana abincin, dafa dukan cous-cous da farfesun kayan ciki, sosai naji daɗi abincin kuma na ci sosai irin wanda na jima ban ci ba saboda a lokuta da dama ba na samun damar yin girki saboda aiki, dama kuma M.J ba abincina ya ke ci ba bare nayi tunanin dafa mishi.

 

Ƙamshin turarensa ne ya fara sanar da ni zuwansa, mu na zaune su ka turo ƙofar ɗakin shi da Hajara cikin kyakkyawar shiga irin na masu morar amarci, da alama hankalinsu kwance yake kamar tsumma a randa.

 

Da sallama a bakin Hajara, Baaba ce kaɗai ta iya amsa sallamar hatta Daddy kai ya kauda gefe. Ganin haka ne yasa suka gaida Baaba kaɗai sannan suka nemi guri su ka zauna. Jim ɗakin ya yi babu wanda ya tanka, Daddy ne ya ciro wata farar takarda daga aljihunsa sannan ya baiwa Sadiq ya miƙawa M.J da kansa ke a sunkuye, cikin son ƙarin bayani ya kalli Daddy sai dai ya kauda kansa gefe, hakan yasa shi buɗe takardar don ganin abinda ta ƙunsa. Cikin razana ya ɗago ya ce

 

“Kotu! Daddy me na yi?”

 

“An haɗa baki da kai wajen cutar min da ƴata.”

 

Da matuƙar mamaki mu ka ɗago a tare muna kallon Daddy, Baaba ce tayi ƙarfin halin cewa

“Sulaimanu wanj zance nake ji haka, wa za’a kai kotu.”

 

“Ba wani abin tashin hankali bane fa Baaba, komai zai zo da sauƙi.” Daddy ya faɗa.

 

“A wani garin marasa hankalin aka taɓa aikata haka Sulaimanu? Kana nufin kenan Muhammadun ya fi ƙarfin ka eyeee. Kai ba za ka iya masa hukunci ba kenan har sai ka dangana da wasu a waje, kai ne uban ko shine? Ban yarda ba, ban amince ba, matuƙar na isa da kai toh ban yarje maka ka kai ƙarar Muhammadu kotu ba.” Baaba ce ta yi wannan zance.

“Baaba laifin da Jawwad yayi mai girma ne, ko da Gwamnati ne ta ji labarin abinda ya aikata ba zata barsa ba, ki bari kawai a hukunta shi.” Cewar Momi

 

“A’a ban yarda ba a nemi wata hanyar hukunta shi amma ba ta hanyar kotu ba.”

 

“Ko da yaushe wannan tsohuwar sai kin kaucar da mutane akan hanya.” Sadiq ya faɗa.

 

“Ka kiyayeni fa Habu, ba na wasa da kai.”

 

“Shikenan Baaba za’ayi yadda kike so, amma wannan karon Jawwad ya ɓata mana rai matuƙa dan haka zan yanke masa hukunci mai tsauri.” Inji Daddy.

 

“Yauwa ɗan albarka ai idan rai ya ɓaci hankalj baya gushewa.”

 

Daddy ne ya maida kallonsa inda M.J da Hajara ya ce

“Ka tashi ka tafi banaso na ƙara ganin fuskarka.”

 

“Dad-dy!” M.J ya faɗa cike da rauni.

 

“Ehh ka tafi Jawwad ba ma so ƙara ganin fuskarka a cikin mu.” Momi ta faɗa cikin hawaye.

 

Gwiwarsa ya zube a ƙasa da nufin ba ta haƙuri sai dai ta riga shi da faɗin

 

“Ka bani kunya Jawwad, wallahi da nasan akwai ranar da zata zo da zaka yi sanadin shigata baƙin ciki kamar yadda nake ji a yanzu, da tun kafin Allah ya bani cikin ka zan roƙe shi ya hanani cikin ka, Allah ya jiƙan Rahama ko da ɗaure fuska nayi cikin wasa sai hankalinta ya tashi, kai da nake tunanin zaka maye min gurbinta sai gashi kaine mai son kashe ni da baƙin cikin ka, Allah ya w….”

 

“Kul! Kada ki yarda ki ƙarasa, kin san munin da tsananin da fushin iyaye ke jawo wa ƴaƴan su kuwa? Banason ƙara jin kunyi mugun furuci akan yaron nan.” Baaba ta katse Momi da ke magana cikin tsananin fusata.

 

Gabaɗaya ya firgice da kalaman iyayensa, ya san fushin su akan sa babban musiba ne a gareshi, hawaye ne suka fara sintiri a kuncinsa.

 

“Matuƙar na buɗe ido na same ka a ɗakin nan ban…✍🏻✍🏻

 

 

*BY*

*JASMINE*🌸🌸

 

*ASP ZARAH*👩‍✈️

 

*BOOK 2*

 

*Page 7*

 

…”Matuƙar na buɗe ido na same ka a ɗakin nan ban yafe maka ba.” Momi ta yi wannan furucin cikin zafin rai.

Da hanzari ya miƙe ya fice Hajara ma ta miƙe ta bi bayan shi ba ta re da ta ce komai ba. Nan Baaba ta rufe Momi da Daddy da faɗa, ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, su dai sai haƙuri kawai suke bata, daƙyar suka samu ta daina faɗan.

A wannan ranar ma tare muka wuni da su cikin kulawa, wajen ƙarfe tara na dare ne muna zaune sai sallamar Ammi muka ji, cikin mamaki nake kallonta Momi kuwa sai dariya ta ke min tana faɗin dama taki sanar da ni ne saboda zumuɗi irin nawa. Cikin murna muka gaisa tana tambayata yanayin jikina, ko da lokacin tafiya yayi sai Ammi ta ce nan zata kwana, daƙyar aka samu Jiddah ta bi Saleem suka tafi gida. Tare muka kwana da Ammi tana bani kulawa kamar zata maida ni ciki.

 

Kwana na goma a asibiti kuma naji sauƙi sosai sakamakon kulawar da likitoci suke bani a gefe guda kuma ga kulawar da su Momi ke ba ni. Tun waccan ranar kuwa ban ƙara saka M.J a idanuna ba, saboda su Momi sun ɗau zafi sosai, Ammi ce ma wani lokacin nake jin su suna magana a waya wanda yawanci roƙonta ya ke akan ta baiwa su Daddy hakuri akan fushin da suke yi dashi. A yadda na fahimta, ko kaɗan abinda ya same ni bai damu M.J ba fushin da iyayensa ke yi da shi ne kaɗai abinda yake damunsa. Kayana da ke gidansa kuwa tun waahegarin da Ammi ta zo suka je da Jiddah aka kwashemin aka maida min gidan Daddy, part guda aka waremin tamkar wata matar gida.

 

Gabaɗaya mun gama shirin tafiya Enugu sallamar likita kawai muke jira, dama na riga da na jima da karɓar takardar shaidar kama Alpha dan damƙa shi a hannun hukuma a ko wani hali, dan haka abinda kaɗai nake jira shine na ƙarasa warwarewa don mu tafi Keruba. Tafiyar ta mutane bakwai ce Ni, Sa-Jid, Yaya Sadiq, sai wasu jami’aina na sirri guda uku da zamu yi tafiyar tare.

 

A daren da na cika sati biyu ne a asibiti likita ya sallameni inda a washegarin ranar kuma zamu wuce Enugu, tafiyar da bamu da tabbacin ko zamu yi nasara, haka dai muke ta shiri zuciyoyi sam babu dadi.

Kasancewar tafiyar mota zamu yi yasa washegari da asuba bayan munyi sallar asuba muka yi sallama da su Daddy muka ɗauki hanyar tafiya cikin motoci biyu.

 

Sallah kawai ke tsayar damu a hanya amma duk da haka ba mu isa cikin garin Enugu ba sai wajen sha biyu na dare, hotel ɗin da muka kama ta internet muka nufa kai tsaye ba mu sha wahalar ganewa ba saboda munyi amfani da google map, cikin lokaci ƙanƙani muka isa wajen.

Bayan karɓi makullan ɗakin ne muka wuce don kowa ya huce gajiyar da ke tattare da shi.

 

Kwananmu biyu muna huce gajiyar hanya kafin ranar asabar da yammaci muka shirya tafiya garin Keruba kamar yadda aka kwatanta mana zuciyoyin mu cike da zullumi duk kuwa da kasancewar a daren wannan ranar kwana muka yi sallah muna neman zaɓin Allah a cikin lamarin. Sai Yamma lis kafin muka isa cikin garin wanda yake da kyawun tsari, duk da mun baro arewacin Najeriya a bushe amma wannan yankin ko ina da damshi alamun dai basa dadewa ba ta re da ruwan sama ba. Wani ƙaramin masauki muka kama don mu kwana a ciki kafin washegari mu ƙaddamar da abinda ya kawo mu. Wannan dare kwana nayi a gaban maliccina ina kai mai kukana ya taimaki ne akan abinda na sa gaba. Wallahi ban taɓa sanin cewa addu’a na da wannan ƙarfin ba sai a washegarin wannan dare, ban taba tunanin abubuwa zasu zo mana da sauƙi ba sai a lokacin na tabbatar cewa babu kamar hawayen wanda aka zalunta a wajen Allah.

 

Washe gari kamar yadda aka faɗa mana cewa Alpha na fita zagayawa a gari cikin ɓadda kama haka muma muka shirya ɓadda kama tamkar wani shirin film. Duk da cewa cikin Jiddah bai wani girma ba amma a haka muka yi amfani da ita. Kasancewarsa mutum mai kaifin basira yasa ba mu yi tunanin yin ƙaryar yin dressing da bandage ba gudun karya gane ƙarya muke yi. Dole ta sa aka yi wa Jiddah rauni a jikinta, duk yadda ta so daurewa sai da ta kasa na gane cewa tana matuƙar jin zafi a jikinta.

 

Kayan masu aikin Momi da muka karɓo muka saka sannan wata daga cikin jami’an nan ta shafa mana wani abu a fuska da jiki wanda idan ba mutum ya sammu sosai ba bazai gane mu ba. Tunda wuri muka yi wa hanyar da Alpha zai bi tsinkaye, cikin tsananin shiri da taka tsantsan.

A tsakiyar hanya muka zauna Jidda ta kishingiɗa ta yi matashi da cinyata, kasancewar a yanki kudu kowa harkar gabanshi yake yi ya sa babu wanda ya kula da lamarin mu kowa ya zo wuce wa yake yi batare da ya tambayi dalilin da yasa muke zaune a gurin cikin wani yanayin da babu kyan gani ba. Mu na zaune a wajen har kusan mintuna talatin ni da Jiddah, yayin da su Saleem ke can nesa a ƙasan wata bishiya suna zaune.

 

Tun daga nesa na hango tahowarsa, kallo ɗaya zaka masa ka fahimci cewa yana taƙama da izza saboda yanayin yadda yake tafiya tamkar mai tausayin ƙasa, duk da shiri ne amma ni da Jiddah mun gaji sosai kallo ɗaya zaka mana kasan mun galabaita. Magana nayi a hankali na sanar da Jidda tahowarsa, ai kuwa tuni ta fara juyi kamar wacce ke naƙuda alhali cikin nata wata 3 ne kacal, ƙamshin turarensa kaɗai ya isa sanar da cewa mai kuɗi ne na gaske, domin indai hancina ya jiyo min ƙamshin nan daidai Abbana yana amfani da kalan turaren nan sanda yake da rai, saboda akwai watarana da na dage sai ya bani kyautarsa shine Mami ke gayamin kuɗin turare yakai dubu ɗari uku.

Cikin takun ƙasaita yazo ya wuce ta gefen mu ba ta re da ya kalli ko gefen da muke ba, take naji hawayen rashin nasara sun sauko daga idanuna, har ya ɗan yi nisa naga ya tsaya sannan ya juyo ya nufo inda muke, farin ciki ne ya kamani dakyar na saisaita kaina gudun matsala.

 

“Sannunku bayin Allah” Sautin muryarsa naji ta daki kunnena, zan iya rantsewa tun da nake a duniya ban taɓa jin wata murya mai zaƙi irin tasa ba, mintsilin da Jiddah ta yi min a gefen cinya ne ya dawo da ni da ga duniyar tunanin da na tafi. Cikin sanyi na amsa mai da

“Yauwa sannu” na kauda kaina gefe ina matsar kwalla.

 

“Me ya sa kuke zaune anan gurin da babu tsabta haka.”

 

“Ƴar uwa ta ce ba lafiya cikinta yana ciwo, kuma akwai ƙaramin ciki a jikinta shiyasa na zauna anan mu ɗan huta ta ce ba zata iya tafiya ba.” Na faɗa cikin rauni.

 

“Subhanallah! Taimako ya kamata ke nema a kaita asibiti ai, ciwon cikin masu juna biyu ai ba daɗi.” Ya fada da alamun ruɗewa a tare dashi. Bance komai ba illa kwallar da na cigaba da matsa kamar wacce ke cikin wani babban tashin hankali, wata tsadaddiyar waya ya ciro a aljihunshi ya fara dannawa ya ce

“Bari na kira ƴar uwata ta taimaka sai mu kaita asibiti.”

 

Da “Toh” na amsa mishi. Magana yayi da wani yare da ban fahimta ba sannan ya cire wayar a kunnensa ya tsugunna a gabanmu yana jera ma Jiddah sannu kamar wata matarsa. Ban san cewa na da wani shiri a ƙasa ba domin bata faɗamin ba, ni a yadda muka tsara jami’ai ne zasu zo su kamashi lokacin da ya tsugunna a wajen, sai dai ba zato ba tsammani batare da dukkanmu biyun mun ankara ba Jiddah ta zaro wuƙa mai kaicin gaske da alama ma sabuwa ce, cikin zafin nama ta kwace a jikina sannan ta caka mishi wuƙar nan a gefen ciki, wata ƙara ya kwalla ya dafe gurin, kafin yayi yunƙurin guduwa tuni jami’an sirri da Gwamnatin Enugu ta bamu suka zagayeshi wasu daga ciki kuma suka damƙi hannunsa suka maka mai ankwa, cikin mintuna ƙalilan sai ga motar asibiti, nan aka sashi a motar tare da wasu jami’ai aka wuce da su.

 

Bansan a wani yanayi na tsinci kaina ba lokacin da na ga jami’ai sun kama Alpha har sun saka mishi ankwa, wannan ranar na ɗaya daga cikin ranakun da bazan manta da su ba a tarihin rayuwata, bansan me ya faru ba sai dai bude idona nayi na ganni a gadon asibiti, sai a lokacin Yaya Sadiq ke fadamin wai sumewa na yi, a lokacin ne na fara tariyo abubuwan da suka faru ina daɗa mamakin yadda kama Alpha ya zo min da sauƙi haka tamkar a mafarki, dole na gode ma Allah da ya banj nasara akan makiyina sannan dole zan godewa Almajirata.Lol.

Murnar da na shiga a wannan ranar ko runtsawa na kasa yi, kwana nayi ina sallar godiya ga Allah, wannan ranar kadai nake jira dama na ajiye aikin ƴan sanda, ranar da zan kama wanda yayi sanadin mutuwar mutane masu gurbi na musamman a rayuwata, Abbana, Mami, Kakannina, lukutar ƙanwata da kuma rigimammun ƴan biyun ƙannaina, a wannan ranar na ji ni na kammala ba ni da wata sauran damuwa da ta ragemin. Har ƙaramar walimah muka hada a resturant ɗin hotel ɗin da muka sauka, Sadiq ne ya ɗauki wannan nauyin.

 

Washegari kamar yadda ya zo a hukumance tunda Alpha ya amsa laifin da ake tuhumarsa sannan yayi bayanin inda za’a samu Phalmata da yadda za’a kuɓutar da matan da ya ajiye a Alpha Villa, bayan an damƙo Phalmata da sauran masu yi musu aiki ne aka wuce da su Abuja inda anan za’a yanke musu hukunci, yaran nan kuwa kowa an haɗasu da jami’ai domin a sada su da iyaye da ƴan uwansu, gabaɗaya mu ma Abuja muka nufa inda zamu haɗu da su Daddy acan don zasu zo ganin yadda shari’ar zata kasance.

Sunayen manyan ƙasar nan da suke da sa hannu a miyagun laifukan da su Alpha ke yi ba zasu kirgu ba, sunan Commissioner na daga farko-farko a cikin jerin mutanen, cikin kwanaki biyu aka cafko kowannensu, masu muƙami kowa tuni Gwamnati ta karɓe abin ta, sai dai mu yi fatan gyaruwar ƙasar mu.

 

Ranar da aka yi zaman kotu kuwa garin Abuja ta karɓi baƙuncin mutane da dama, sai da aka cika kotun nan maƙil babu masaka tsinke domin wasu a waje ma suka tsaya don babu gurin zama kowa nason ganin mutum ɗaya jal! da ya daɗe yana gallazawa mutane, bayan alkali ya zo ne aka gabatar da tuhumar da ake musu inda lauyan Gwamnati ya gabatar da kansa, babu batun lauyan da ke kare waɗanda ake tuhuma domin ba su da shi, cikin sauƙi ba ta re da wahalar da shari’a ba aka zartar musu da hukunci, Al’amin da Phalmata hukuncin kisa ta hanyar rataya inda sauran kuma hukuncinsu zaman gidan kaso na har abada. Daga haka Alƙali ya sallami kowa sannan aka bada umarnin wucewa da masu laifi gidan yari, kotu fa ta hargitse kowa da abinda ke fadi inda mutane da dama su ka so ɗaukar doka a hannunsu sai dai babu hali.

 

Sosai na so ganawa da Alpha amma Sadiq ya hana ni gudun kada wani abun ya faru, haka ina ji ina ganin muka bar garin Abuja zuciyata sam babu daɗi saboda yadda na so mu yi sallamar ƙarshe da Alpha, sam a wannan lokacin sai nake jin tausayinshi na kamani matuƙa ta yadda mace ɗaya ta lalata mishi rayuwarsa ta duniya, ko da yake shima yana da laifin biyewa son zuciya don bai tsaya a inda Allah ya ajiye shi, yana da kyau na ɗaukar hankali wanda iya shi kadai zai iya zama jarinsa don ga dukkan alamu mutum ne mai farin jini, dole daga baya na cire tunaninshi a raina. Rayuwa kenan ban taɓa kawowa cewa al’amurana zasu warware cikin sauƙi haka ba. Tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin talikai wanda baya zalunci sannan baya barin masu aikata zalunci.

 

Kwananmu biyu da dawowa Gwamnati ta shirya mana ƙayataccen Dinner wanda ya haɗa da ƙarin girma, gabadaya jami’aina an musu ƙarin girma inda ni kuma Gwamnati ta tura ni ƙasar Malasia domin yin course na musamman a harkar tsaro, na so naki karban wannan tayin amma Daddy ya tursasa dole banj da wani zabi daya wuce hakan. Haka dai aka kammala taron Dinner ɗin zuciyoyin mutane cike da murna.

 

Washe gari gaba ɗaya muna zaune a dinning mu na breakfast, M.J ne kawai bayanan a wannan zaman, cikin nutsuwa kowa ke cin abincin da Momi da kanta ta sarrafa shi, wayar Ammi da ke falo ce ke ta ƙara don haka ta kalleni ta ce

“Little miƙo min wayar nan kinji, na ga wanda ke kirana haka da safe ko karyawa ba za’a barni nayi ba.” Dariya muka yi duka kana na miƙe domin zuwa ɗauko mata wayar.

Da sauri na taho na bata wayar sakamakon wani kiran da ya shigo, mijinta da ga ƙasar Egypt Dr. Adam ke wannan kira, cike da mamakin kiransa a wannan lokacin ta ɗaga, bai jira ta yi magana ba ya riga ta, ai kuwa sai gani muka yi ta mike tana faɗin

“Alhamdulillahi Allah mun gode maka Ya Allah kai kadai ke yi a duk sanda ka so ya Allah muna ƙara gode maka da ni’imomin ka gare mu.” ba su dade ba ta sauke wayar a kunnenta fuskar ta kaɗai ta isa fallasa farin cikin da ta ke ciki, zuba mata na mujiya mu ka yi cikin son ƙarin bayani, ai kowa fahimtar hakan da ta yi ne ya sa ta ce

“Wani abin farin cikin ya kuma samun mu, wallahi ashe labari mai dadi ne Dr. Ke san gayamin tun dazu shi ke kiran wayar.” cike da zumuɗi na ce

 

“Ammi meya faru ne”

 

Cikin fara’a ta ce

“Rahama ce ta warke daga Trauma ɗin da ke damunta, yanzu haka ta dawo hayyacinta harta labarta ma Dr. Abinda ya faru waccan ranar shine ta ke daɗa tambayar duk ina muke.”

 

Wani wawan tsalle na daka na rungume Ammi da ke tsaye cikin murna, hamdala duk mutanen da ke wajen suka fara, an ɗau lokaci ana maida magana kafin Daddy ya ce

 

“Ai kamata yayi a kira Rahama ɗin ta video mu ganta ta ganmu ko hankalinta ya kwanta.”

 

“Wallahi abinda na ce ma Dr. Kenan amma wai an yi mata allurar bacci saboda kukan da ta ke yi.”

 

“Toh masha Allah sai kuma ayi shirin tafiya koh” cewar Baaba. Dariya muka yi ganin yanayin yadda ta yi maganar. Daddy ya kuma ce wa

 

“Insha Allahu kuwa sai tafiya a yau ɗin nan zuwa dare sai mu wuce. Tunda akwai private jet ɗin kamfani na sai mu wuce gabaɗaya kawai.”

 

“Haka za’ayi kawai Daddy amma dare kamar yayi nisa fa.” Jiddah ta faɗa a shagwaɓe.

 

“A’a Mamana(sunan da Momi ke kiran Jiddah da shi kenan kasancewar sunan Mahaifiyarta ne) babu kyau gaggawa aikin shaiɗan ne a bari zuwa daren mu shirya a nutse, zan kira Hajiyarku (Mahaifiyar Jiddah) na shaida mata nasan itama za ta so ayi tafiyar nan da ita.”

 

“Hakane ya kamata a shaida musu kam.”

 

Bayan mun kammala breakfast ɗin ne duk muka miƙe don fara shirye-shiryen tafiya, inda Saleem ya ɗauki Jiddah suka wuce gida don yin nasu shirin. Bayan na dawo daga rakiyar su Jiddah ne na tarar Sadiq na ƙoƙarin fitowa daga falon don zuwa sashensa, wani tight and friendly hug ya bani, dama nasan ɗazu kunyar su Daddy ya sa bai wani nuna ɗokin shi ba, cike da farin ciki ya ce

 

“Little ina taya mu murna ragowar farin cikinmu ta dawo hayyacinta, bansan wani irin murna zanyi ba wallahi.” sassauta riƙon da yayi min yayi sannan ya riƙe hannuwana biyu ya ce

 

“Ku kaɗai ne farin cikina yanzu a wannan rayuwar, tabbas a yau na ƙara jaddadawa kaina alƙawarin amanarku da Abbanmu ya bani, zan ɗau alƙawari har a gaban ubangijina bazan taɓa bari ku ji kewa ko maraici ba, zan kasance Uwa, Uba sannan Yaya a gare ku ke da Rahama bazan bari ko ku ƙara yin kukan baƙin ciki ba matuƙar ina numfashi a duniya.” hawaye ne ya silalo a kan fuskarsa, hannu na saka na share mai sannan na ce cikin zolaya

 

“Ka tafi ka shirya ka ji young Abbah.”

 

Doka ya kaimin cikin sauri na sunkuya na wuce ciki da gudu, kai tsaye ɗaki na nufa don haɗa kayana. Wayata na ɗauka na kira Jummai sannan na gayamata ta baiwa Raliya 1million sannan ta sallameta idan da hali ma ta kaita har gaban danginta.

 

Ƙarfe bakwai na dare muka private jet ɗin Daddy ya ɗaga damu zuwa ƙasar Egypt and here we’re tare da Trauma Patient Rahama.

 

Dukan wasa Rahama ta kaiwa Zarah lokacin da ta kawo ƙarshen labarin. Kana daga baya ta rungumeta tsam a jikinta tare da fashewa da kukan tausayin ƴar uwarta ta, sun jima a haka har sai da Sadiq ya yi magana kafin suka tsagaita yin kukan.

 

Satinsu Daddy ɗaya a Egypt suka koma Nigeria inda aka bar Sadiq da Zarah saboda daga nan zasu wuce Malasia.

Su ma kwanaki goma kacal suka ƙara jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar Malasia.

 

_Bari mu leƙa amarya da ango._..✍🏻

 

 

Name: [My Novels (www.mynovels.com.ng)]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na TelegramPowered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!