Hausa Novels

Aure da Haihuwa Hausa Novel

Aure da Haihuwa Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: aure da haihuwa
I’d card d’in dake gaban rigarta ta gyara sannan ta gyara farin glass d’in dake fuskarta,cikin murmushi takai dubanta gareshi,tace cikin harshen turanci.

“Ranka ya Dad’e,bawai baze yiwu bane,ina de so ka gane ne wannan shine kwayoyin haihuwarka,da gwajin mu ke nuna mana na k’arshe ne, dole se anbi komai cikin kulawa da takatsantsan,inba haka ba,za’a iya rasa komai”cewar doctor Amina Galadima kamar yadda aka rubuta agaban rigarta.

 

 

 

aure da haihuwa

Gyara zama yayi sannan yakai dubansa gefen matarsa dake ta cika tana batsewa, yayi murmushin k’arfin hali sannan yace.

 

 

“Doctor badamuwa na mik’a lamuran ga Allah, ko adace ko akasin hakan,Dan haka kiyi me yiwuwa kawai,kinsan yarda da nai dake ne kesawa in baro k’asata in zo gareki “be gama fad’in abinda yakeson fad’i ba,matar tashi ta katseshi da cewa cikin fad’a da harshen larabci.

 

 

 

“Farhan wannan shine karo na biyar da za’ai dashen kwayoyin halittarnan,wallahi matuk’ar ba’a daceba,to ni kuma zamanmu yazo k’arshe,taya in banda toshewar basira,kana zaune a k’asar Dubai, zaka wani taho Nigeria Neman haihuwa,shekara biyar kenan muna zuwa kullum ba sauyi,to Nide na fad’a maka”ta k’arasa maganar tana huci.

 

 

 

aure da haihuwa

Jingina yayi da kujerar da yake zaune ya lumshe kyawawan idanuwanshi,yana sauraronta,harta gama,sannan ya budesu a hankali,ya zubesu akan matar tashi wacce yake ji inba ita baze iya rayuwaba.

Dubansa ya kai gun doctor Amina sannan yace cikin sark’akk’iyar murya,”doctor please do something meaningful to save my marriage”

Cike da tausayawa doctor Amina tace “insha Allah”

Sallama sukai mata suka wuce masaukinsu,bayan an amshi seamen sample d’inshi,ko a hanya matar tashi me suna shehnaz in banda masifa ba abinda take masa shide kallonta kawai yakeyi,Dan besan yaze mata ta fahimceshi ba.

 

 

 

Bayan wasu kwanaki doctor Amina ta buk’aci daya kawo matarsa Dan adasa mata D’an tayin acikinta.

Koda suka iso asibitin doctor ta shiga tiyatar gaggawa Dan haka d’aki na musamman aka basu su zauna domin jiran fitowarta.

A d’akin suka tarad da wasu mata da miji zaune suma daga dukkan alamu ita suke jira.

 

aure da haihuwa

Sosai ma’auratan suka tafi da hankalin Farhan,kasancewar manne suke da junansu cikin so da k’auna,ya tsinkayo hirar da sukeyi cikin harshen turanci,inda mijin ke cewa.

“Baby ina fata da addu’ar Allah yasa in anyi dashennan mu dace da samun haihuwa”

 

Matar Makaho Hausa Novel
murmushi matar tayi sannan ta shafi gefen fuskarshi tace”insha Allahu dear za’a dace jikina yabani hakan”ta fad’i cike da murna a fuskarta.

 

 

Sosai suka burgeshi duba da ganin yadda suka damu da junansu kowa k’ok’arin kwantar da hankalin d’an uwansa yake,sab’anin shi da tashi matar wacce keji kamar ta shak’eshi ya mutu ta huta.

 

 

 

Suna nan zaune doctor Amina ta shigo d’akin ita da wasu ma’aikata guda hud’u,daga kallon shigowar tata kai ba se an fad’a maka ba tana cikin tashin hankali.

 

 

 

 

Duk a firgice take,hakan yasa dukan su maida hankali kanta,cikin sauri sauri tace cikin harshen turanci.”don Allah Ku gafarceni,Mahaifina ne Allah yayiwa rasuwa yanzu sakamakon hatsarin mota, zani gida yanzu,amma nayi musu bayanin komai,kuma zasu gudanar dashi cikin nasara”ta k’arasa maganar tana nuna ma’aikatan data shigo tare dasu.

 

 

Name: [AURE DA HAIHUWA]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: November, 2021

 


7 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!