Auren Bare Hausa Novel Complete
Tag: AUREN BARE !!
{ _HOT LOVE_ }
NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS…_
_Bisimillahir Rahamanir Rahim dukkan yabo da godiya su tabbata ga ALLAH madaukakin sarki tsira da amincin ALLAH su ƙara tabbata ga shugaban halitta cikamakin annabawan ALLAH, annabin farko annabin ƙarshe shugaba jagaba annabi muhammad s.a.w Amin…._
_My fans yauma gani tafe da sabon littafi mai suna a sama da fatan zaku biyoni domin jin yadda labarin nawa ke tafe! labarin nawa ƙirƙirarre ne banyi domin cin zarafin wani ko wata ba duk wanda yaga yayi dai dai da tasa rayuwa tofa akasi aka samu._
_Labarin nawa ne nina tsara abina kuma na rubuta shi banyarda wani ko wata su juyamin shi ta kowace sigaba ba NAGODE_
*001*
_GARIN KANO UNGUWAR SHARAƊA_
Yammaci ne mai ɗauke da wani irin lullumi mai daɗin gaske, hadarine yaketa faman haɗowa kota ina garin yay wani irin luf har wani duhune ke kawo kai, sabida yadda garin yagama gamewa da wannan hadarin, ƴan matane, guda uku suna tafe kowacce hannunta riƙe da bokiti mai ruwan garai wanda hausawa ke masa laƙabi da ɗan ballasa.
Seda na ƙarasa gabansu sannan idanuna ya ganemin ashe ba kansu ɗaya ba, domin farar cikinsu itace mai ƙiba amman ba canba tana da cikar halitta irin ta ɗiya mace, kallo guda zaka mata kagane ƙarancin shekarunta domin daga gani bazata haura shekaru goma sha shidda a duniya ba, se ragowar biyun suma sunada haske amman dai basu kai wannan ɗin ba, sukam kallo ɗaya zaka musu kagane ƴan biyune sabida yadda suke tsananin kama da juna, waɗanda bazasu haura shekaru goma sha takwas aduniya ba, kuma kana kallonsu kasan sun girmewa wannan farar sedai kuma daga ganinsu kaga jini ɗaya sabida tsananin kamar dasuke da ita, abin da zata fisu shine girman jiki da cikar halitta gami da hasken fata.
Ɗaya daga cikin ƴan biyun ce ta dubi wannan farar yarinyar tare da cewa “Haba Bebi! bakya ganin yamma tayi sosai yakamata mu koma gida hakan nan dan ALLAH kinsan halin mama da ruɗewa wallahi nasan yanzu haka tana ƙofar gida tana faman zagaye”. Takai maganar tana kallon ɗayar wadda batai magana ba tare da cewa “Koba haka ba hassana?” tafaɗa tana kallonta,cafkewa hassanar tai tare da jan tsaki! kaɗan”Bebi kiwa ALLAH ki rabu da bin ƴan bashin nan mutafi gida ai gobe ma ranace, wallahi mu dukke kike jamana ana ƙin sayan awararmu sabida jarabar faɗanki” takai maganar cikin ƙufula. wannan farar yarinyar wadda ita nake tunanin itace bebin ita ta dubesu cikin fitsara kana tace”Nifa karku uzzuramin wallahi saina koma na amsowa mama kuɗinta aini ba baiwar ubansu bace” takai maganar tana huci kamar taci gudu, wadda aka kira da hassana ita tai rau-rau da idanunta”Dan ALLAH bebi kiyi haƙuri mutafi nai miki alƙawari gobe zan karɓi kuɗin da kaina”. wani kallo bebi ta watsa musu tare da dire bokitin hannunta batama tsaya jiraba ta arta aguje, ko nauyin jikinta bata ji.
Baki ɗaya baki da hanci su hassana suka saki suna kallon yadda ƙanwar tasu ke gudu amman babu yadda zasuyi sabida halin bebi se ita bata tsoron kowa ko kaɗan bebi bata da kunya ga faɗan tsiya da taurin kai da mita, ganin an soma ruwa kaɗan kaɗan yasa suka ƙara sauri, domin nufar gida sedai cikin zuciyarsu tsorone fall na yadda basu san halin da bebi zata shiga a hanya ba.
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza 3
-
Zuciya ta
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi
-
Aure da haihuwa
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya
-
Gangar Shedan
-
Angon mata biyu
-
A gidan mu take
-
Bafulatanar Rugga
-
Matar yaro
-
Mr Bello
-
Mijin Buzuwa
-
Gidan Uncle Complete
Cikin wani irin zafin nama take gudun baki ɗaya tagama jigata kanta harseda takai dai-dai jection ɗin sharaɗa kai da ƙafa, sannan taja ta tsaya ta huta, lokacin ruwan harya soma saukowa, hijabin jikinta ta cire tare da ɗaurawa a ƙugunta, baki ɗaya manyan breast ɗinta waɗanda suka zame mata kaya, masu bata tsananin haushi duk sun fito waje, ta saman rigarta amman haka ta kurmutsa cikin kan dakalin da matasan samarin ke zaune cikin zafin nama da masifa ta dubi ɗan baƙin cikinsu “Kai siba dallah kabani dari biyun awarata idan ba haka ba wallahi zamu kwashi ƴan kallo anan wajan dakai” takai maganar tana riƙo ƙugunta tare da jijjiga jikinta wanda ya baiwa albarkatun kirjinta damar kaɗawa kamar da gayya wanda ita ko kaɗan batai wannan tunanin ba, wanda aka kira da siba ne ya taso daga cikin samarin yana ɗan shafa gemunsa tare da lasar ƙasan lip’s ɗinsa kaɗan yana binta da wani mayen kallo, wanda kafin ya furta wani abu ruwan dake zuba kaɗan ya kece da ƙarfi, cikin tsananin zalama yake dubanta”idan har kika bari na taɓa nan” ya nuna saman kirjinta,”Nikuma zan baki ninkin kuɗinki, amman idan kika saka taurin kai na cinye kuɗin inga uban daya isa ya karɓa miki” yakai maganar yana dariya wadda baki ɗaya mazan wajan suka haɗe baki wajan sakin ta suna mara masa baya kamar da gayya, cikin tsananin ƙufula bebi ta dubeshi “Kai! dakata gaja da kai dawani ƙazamin hannunka mai datti kakeson taɓa min jikina lallai da uwarka ta haifi mai yankakken hannu kuwa” takai maganar tana mayar da hijabinta jikinta, dariya ya saki kana ya kai hannunsa dai dai wajan wuyan hijabinta wanda tunma kafin ya ɗago hannun yaji saukar mari! tas!tas!!tas!!, har sau uku, baki ɗaya idanunta ya juye ya koma kamar banata ba”Dan uwarka dan ubanka shege bunsuru jikina yafi ƙarfin gaja irin……..,” bata ƙarasaba taji saukar yatsunsa a fuskarta, kafin ta ɗago taji muryar okasha yana magana”Haba baba kafayi kwafsi tayaya zaka bari mace taga weak ɗinka haba dallah wuce kabarta da yawarta” yafaɗa yana watsa mata kallon banza, sam bebi tama kasa furta komai illa maganar siba wadda ke cike da borin kunya ta karaɗe mata kunnenta”hakane fa oka bara nabar wannan wawiyar wadda bata da arabi bare boko ƴar matsiyata masu gidan buhu, ƴan makarantar tallah………” yafaɗa yana bin bayan okashat abokinsa, tsaye suka bar beby wadda tai saƙare kamar doluwa still kuma ruwan yana kuma zuba ajikinta su basu bata kuɗin bashin taba gashi kuma sun barta da dukan ruwa.
Wata ƙwallar takaici ta saki wadda takejin zuciyarta na mata suya kamar zata faso ta fito abinda tun tasowar ta bata yarda dashi ba kenan kuka! sam bebi bata yarda tai kuka akan abu sabida tsabar kafar kanta tare da yawan faɗanta, jan ƙafafunta tai tare da barin wajan tanajin yadda ruwan sama ke sauka ajikinta.
Kanta tsaye sharaɗa police station ta nufa dukkan kayan jikinta suna ɗigar da ruwa domin sun riga da sun jiƙe jagaf da wani ɗan sanda taci karo ɗan gajere baki, yana ganinta ya washe baki yaga ƴar fara kyakykyawa”A,a madam lafiya na ganki cikin ruwan nan?” yafaɗa yana ɗan matsowa gabanta, da baya taja kaɗan tana ayyana yadda wasu mazan suke hali kamar na kwartaye, kana ta dubeshi”Officer na kawo ƙara ne akan ina son abimin haƙƙina” yadda ta kame kanta tana kora masa bayani seka rantse babbar macece mai hankali, seda ta gama yi masa bayanin duk yadda sukai dasu siba hatta marin daya mata bata ɓoye masa ba sabida tun asalinta ita bamai yawan ƙarya bace, sannan ta ɗora da cewar”idan da hali officer ina son ku ɗauko mota aje na nuna muku har inda yake domin a karɓar min naira ɗari biyuta”. takai maganar da iyakar gaskiyarta, wata iriyar dariya officern ya kece da ita, da kallo ya bita yana nazarin ko ta samu taɓin hankali sedai kuma tsaf take babu alamun ƙazanta ko rashin hankali agareta, dai dai ta nutsuwar sa, yay tare da ɗan haɗe ransa kaɗan”Ke yanzu ƙanwata idan banda abinki haka ake kawo ƙara wama yace miki muna aiki da kane?” ya jefa mata tambayar yana kallonta tsaki! taja kaɗan tare da ɗan sharce ruwan daya zubo mata saman fuskarta”Kaga ni daman wajan shugaban wajan nan nazo idan bazaka tai makamin na karbo mana kuɗinmu ba kaban wuri kawai malam ruwa yana faman jiƙani” tafaɗa tana murguɗa masa baki, haɓa officer ya kama sannan yace”To muje naga wasu tsagerun samarin ne base kin shiga cikiba sabida ba kowa ne ze fahimce kiba”, babu musu bebi taja ƙafarta suka jera da officer seda takai har kan dakalin ƴar rumfar dasu siba ke ciki sannan taja ta tsaya tana nunawa officer siba, wanda yaketa faman zaro idanu tamkar yay ma sarki ƙarya.
“Officer wannan ne kadai san bayanin dana maka tun acan ko?” tafaɗa tana makawa siba harara, da kallo officer yabi siba tare da ce masa “Kai kuwa abokina tayaya zakaci kuɗinta na sana,arta kaƙi bata abin kuma yakai ga cin zarafi harda mari?” yafaɗa cikin sigar tambaya, duk ruwan da ake bai hana siba sharce gumi ba wato duk jarabar yarinyar nan da ake faɗa masa bai taɓa tabbatarwa ba se yau, inda yasan akan ɗari biyunta zata kaishi ƙara ai da tuni anwuce wajan ya bata abinta, basar da tunanin yay kana ya ɗago “Officer ai min aikin gafara Bebi kiyi haƙuri insha ALLAHU hakan baze kuma faruwa ba, gama 500 nan wallahi ki riƙe duka” yafaɗa cikin sauri kana ya zaro sabuwar ɗari biyar daga pocket ɗinsa wanda daman can iya shege ne yasa ya hanatan, wani watsatstsen kallo ta watsa masa tare da murguɗa bakinta gaba”Ni ai bana buƙatar kuɗin ƴan tasha haƙƙina kaɗai zaka bani na kama gabana nasan inda dare yay min” tafaɗa tare da kauda kanta gefe, mamakine ya kama ƴan wajan harshi kansa officer sannan ya dube ta,”Haba ke kuwa an miki alkhairi ai kya amsa ko?”……..wawan kallo ta masa tare da cewa”officer na gode da taimako kaga siba bani ɗari biyu ta nai gaba bana son ɓata lokaci”. a wajan okashatu siba ya amshi ɗari biyun ya bata hannunsa na rawa, bata tsaya kallon kowa na wajan ba bare taiwa officer godiya taja jikinta tabar wajan, har taje titi ruwan bai bar dukantaba…………………
*AUTAR MANYA*
_08142105218_
[*AUREN BARE !!*
{ _HOT LOVE_ }
NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS…_
*002*
Tsaye tayi abakin titin ruwan yana kuma jiƙa mata jikinta, ganin yamma tana kumayi magariba tana kawo kai, yasa ta yanke shawarar bita lunguna, hakance ta faru ta lunguna tabi har zuwa cikin layinsu wanda yake da tazara sosai a tsakaninsu da wajan dasuke kai awarar.
Nufar bakin wani ɗan ƙaramin gida tayi wanda katangar gidan take ƴar ƙarama domin batafi taku uku ba, yaye labulan buhun da aka rufe ƙofar gidan dashi tayi, tare da ɗanyi ƙasa da kanta gudun bugewa domin tsayinta yaywa. ƙofar kaɗan, karo sukaci da wani ɗan matashin namiji wanda baifi shekaru goma sha bakwai ba, kallo ɗaya zaka masa ka gane shiɗin yayanta ne, da kallo ya bita”Kedai kinji kunya wallahi kullum cikin saka mama a damuwa kike, to yanzu ma wai daga gidan ubanwa kike, kin ɗagawa kowa hankali?” yafaɗa yana kawo mata hannu kamar ze bugeta, da gudu tai baya tana watsa masa harara” wai kai shahid ɗin nan meya ruwanka dani ne kuɗin awarar uwata akacinye shine naje nabi bashin tunda ƴan biyu su baxasu iya ba”…….,”Seke tsagera?” yafaɗa yana zabga mata harara, bata bi takansa ba tai cikin gidan, shima sabida yasan bazata raga masa ba yasa yay wajan gawayin sa dayake saidawa acan bayan layinsu.
Wani ɗan mitsitsin tsakar gida ta shiga tare da fara kiran “Mama! mama!! mama!!!, kina ina ga ƴar albarkarki ta iso” tafaɗa da ƙarfi tare da tsayawa ƙyam a tsakar gidan batare data shiga ɗakinsu ba.
Cikin sauri wata farar mace tas ta fito daga cikin ɗakin dayake ƙwaya ɗaya tall acikin gidan, kallo ɗaya zaka mata kagane ita ɗin mai kyauce kuma mahaifiya ga bebi domin ga kama nan kamar an tsaga kara,da sauri ta ƙaraso gabanta tare da riƙo hannunta tajata zuwa cikin ɗakin data fito daga cikinsa , wanda yake shinfiɗe da ledar, tsakar ɗaki tare da ƙatuwar kafita se sip ta kaya, ƴan biyu suna zaune akan katifar suna kallo a ƴar wayar mama, se arfa da ihsan a gefe suna cin taliya, suna shiga ta saki hannunta tare da haɗe ranta kaɗan “Yanzu bebi kullum sekin ɓata min raina kike jin daɗi?” tafaɗa muryarta tana karkarwa, da kallo bebi.
tabi mama tare da cewa”Mama kuɗin awararmu fa na tsaya na amsar mana idan kuma ƙarya nake gobe muje dake wajansu”girgiza kai mama tayi tare da cewa”Bana son jin ba,asi kullum ina gaya miki cewar duk wanda yaci awarar nan bai baku kuɗi ba to ku barshi da ALLAH, ke mace ce bebi bana son wannan faɗace-faɗacen naki sabida baki san bakin wani ba”.dira ƙafafunta tafara a ƙasa tana ƙoƙarin sakin kukan shagwaɓa, “Haba mama idan nabar musu kuɗin dame zamu dinga cin abinci wallahi mama indai akan haƙƙina ne se inda ƙarfina ya ƙare”, da kallo mama ta bita tana mamakin halin ƴar tata, sam batayo halin kowa na gidanba, mama bata ƙara shan mamakin bebi,
ba seda ta zayyane mata yadda sukai har zuwa wajan ƴan sandan datayi sannan ta fito da ɗari biyun data amso ta miƙa mata sannan tai rau rau da idanunta”Mama dan ALLAH kibani ɗari aciki anjima na siyo nama wallahi miyauna har tsinkewa yake sabida ƙwaɗayi”. cikin mamaki mama tace”Kice zuwa kikai wajan maza kika nuna rashin tarbiya harda tube hijabi wato haka na baku tarbiya?,haka kikaga ƴan uwanki sunayi BILKISU soki ke kijamin maganar dangin ubanku ko?, dasuka zuba mana ido suga gudun ruwanmu?” tafaɗa tana kokarin kai mata hannu, da baya tai waje tana furta”Mama bazan kuma ba” tana yarfe hannayenta.
Zama mama tayi a bakin katifa tare da kallon ƴan biyu dasukai tsuru batare dasun cigaba da kallon da sukeba suna sauraran dramar bebi da mama, suna kuma tsoron suyi magana tai musu rashin kunya.
“Ya salam ni Aishatu ALLAH ka kawomin sauƙi cikin lamuran wannan yarinya, na haifeki ban haifi halinki ba” ta faɗa a fili, hassana ce ta dubi mama, tare da ɗan matsowa gabanta kaɗan bayan ta taso daga kwanciyar datayi, dafa hannun mama tayi tare da cewa.
“Mama kiyi haƙuri haƙiƙa Bebi tana buƙatar addu’arki, ta uwa mama ki ɗora akan wadda kike insha Allahu babu abinda ze faru se alkairi”.
Tafaɗa cikin nutsuwa, ɗan murmushi mama ta saki, kaɗan tare da kallon hassana tana yaba irin baiwa tare da hankali irin ta ƴan biyun, nata, kana tace.
“Hakane Allah ya rufa asiri”. daga haka ta miƙe ta fita zuwa tsakar gidan tsugunne taga Bebi, ga ruwan yanata faman dukan jikinta, sabida da yaɗan tsagaita amman yanzu ya dawo da ƙarfinsa, ruwan taɗan sharce daga fuskarta, wanda yake faman zubowa tamkar da bakin ƙwarya, itama mama duk yabi ya jiƙa mata jikinta.
“Watakam so kike ki sakani cacar siyan maganin zazzaɓi ko Bebi?” tafaɗa tana kallonta.
Cikin tsoron dukan mama Bebi ta ɗago idanuwanta da suka firfito tare da cewa”Dan Allah mama kada ki dakeni, wallahi yunwa nakeji rabona da abinci tun safe”. tausayin Bebi ne ya kama mama.
Da kallo tabi ƴar ta’ta tare da cewa…….
“Bazan miki komai ba bebi maza ki tashi ki shiga cikin ƴan uwanki, amman ki tuɓe kayan jikin naki tukunna”.
Mama ta faɗa tare da shiga cikin wani ɗan ƙaramin kicin wanda baze ɗauki mutum biyu ba, ko mutum ɗayan nema seyay da gaske, irinsu bebi masu ƙiba kuwa ma yay musu kaɗan.
Cikin rawar ɗari Bebi ta ƙarasa cikin ɗakin nasu harara! ta watsawa hussaina wadda take baje a katifa tana kallo, sannan ta bugawa su ihsan tsawa! “Dalla ku rufe idanuwan ku zan tube kayana”.
Cikin sauri yaran suka rintse idanuwansu, janyo marufin sip ɗinsu tayi tare da kare rabin jikinta, sannan ta tube kayan jikin nata waɗanda sukai sharkaf har ɗiga suke.
Ko ɗaɗɗiyar atamfa riga da zani ta ɗauko wadda da ƙyar ta saka rigar sannan ta ɗaura zani ajikinta wanda kayan ya sami damar kama mata jiki ɗam ɗam.
Hijabi ta ɗauka ta saka sannan ta ɗebe kayan data cire ta fita waje, igiya taje ta shanya duk da ruwan har yanxu yana sauka.
Bayan ta kammala ta nufi cikin ɗan madai daicin banɗakinsu wanda yake wanke ƙar ƙar, kama ruwa tayi tare da fitowa ta dauro alwala, shiga ɗakin ta kumayi ta shinfiɗa sallaya tare da tayar da sallar la’asar wadda ta makare mata.
Bayan ta idar ko hijabin bata cire ba tayi waje lokacin an ɗauke ruwan dan duk su hassana suna tsakar gidan har sun gyara shi sun goge ruwan daya jiƙa tsakar gidan.
Duk suna zaune hussaina tana tankaɗen garin tuwan dare wanda shahid ke fita dashi can cikin kasuwar sharaɗa kai da ƙafa.
Hassana kuma tana daka kayan miya danginsu daddawa da sauransu, ihsan wadda bazata wuce shekaru goma sha biyu ba, tana faman wanke ƴan kwanika a bakin rariya.
Kanta tsaye ƙofar kicin ta nufa tare da tsayawa”Mama abani abinci yunwa nakeji”.
Juyowa mama tayi duk fuskarta tagama haɗewa da gumin haƙayin itacen dayabi ya addabi kicin ɗin, ni kaina seda nabi fuskar mamansu bebi da kallo sabida yadda take da tsananin kyau ɗan gaske farace jajur kamar ka taɓa jini ya fito sedai kuma wahala ta saka duk jan maman ya du sashe sedai kuma tsantsar kyanta ɗan gaske! har yanzu yana nan bai gushe ba.
“To Bebi baki ga yanzu nake kici-kicin na haɗa ruɗen tuwan ba?, ai kya jira na gama ko?”.
Zaro idanu Bebi tayi waje wanda hakan yake acikin al’adar rayuwarta muddin zatai magana seta zaro su duka waje, sannan ta haɗe ranta tamau kamar kace mata kat! ta fashe, sannan ta soma magana muryarta tana rawa kamar zatayi kuka!.
“Mama yunwa nakeji wallahi tun safe dana sha koko har yanzu ban kuma kai mai ɗumi cikina ba”.
Ta ƙarasa maganar tana zubo da hawaye! shaaaaaaaa, kamar famfom.
Mama bata kula Bebin ba illa cigaban datayi da tuƙa ruɗenta harta kammala sannan ta fito waje ta wuce Bebi wadda take ta faman kukan yunwa.
Abakin ƴar tabarmar da su hassana ke kai mama ta xauna sannan ta ɗan ɗaga murya kaɗan.
“Wai ke! Yaushe zaki hankaline?, Nace yaushe zaki hankaline?, idan da abincin nan me zanyi dashi dazan aje naƙi baki?”.
Ta kalli Bebi cikin jin haushinta.
“Wallahi tunda kuka tafi tallah ban ɗora ko ƙwayar hatsi acikin gidan nan ba, ina zaune ina jiran ikon Allah, shahid ne yazo da taliya leda ɗaya, ita na dafa na zubawa, su ihsan shima na zuba masa, ina jiran ku dawo naga abinda Allah ze mana, sam hankalina ya tafi ga inga na haɗe kuɗaɗan nan na shahid ya zana jarabar wannan kema na baki kuɗin jarrabar shiga aji huɗun nan amman har yanzu abin yaƙi tafiya, seki zauna kijira in gama tuwo kici tunda ke har yanzu baki san abinda yake dai dai ba”.
Mama ta ƙarashe maganar tana jin ranta na mata suya na halin kunci da rashin da suke ciki.
“Mama dan Allah ki rabu da ita, ga ruwa can a randa tasha ta jira tuwo”.cewar hussaina wadda taɗanfi hassana zafi.
Wata uwar harara! Bebi ta makawa hussaina tare dajan tsaki! batare datayi magana ba taja ƙafafunta zuwa cikin ɗakinsu.
Rufda ciki tayi tare da sakin kuka! “Ya Allah ka kawo mana ɗaukin ka na alkairi a wannan zamanin talaka yana cikin matsala……………
Tnx
Tnxs dan Allah yaxan samu complete nashi