Auren Ustaz Complete Hausa Novel

Auren Ustaz Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Da k’arfi Aliyu ya rike kanshi yasaki wani irin mahaukacin kuka da yasa Umma tashi agigice tace Mujaheed waye wannan bashi da lafiyane.?

 

Shima Mujaheed din hawaye ya share ya duk’a kasa tare da rike k’afar Umma yasanya gigitaccen kuka dayasake rukita Umma, kamar zatayi kuka tace wai Dan Allah miye yafarune kuka sani gaba kuketa kuka? Wallahi nima zanyi kukan ta fad’a tana tab’e baki kamar zatayi kuka.

 

Aliyu yace Umma ni kanan Ustaz ne, zuciyar USTAZ ta kumbura, an’tabbatar muna da cewa cikin k’ank’anan lokaci in’baisamu abunda yakesoba Wallahi zuciyarshi zata buga kowa yarasashi, Umma ke uwace kinson ciwon D’a, Dan girman Allah kuyi hakuri kubashi dama ta karshe, iya horuwa USTAZ ya horu Umma, wallahi ina mai tabbatar miki da cewa bazai sake abunda yayi ba yanzu, tinda har gashi agab’ar mutuwa ,kuma Aisha ce kadai maganin ciwon shi Wallahi, Umma yayi hankali yanzu sosai ki taimakamuna tinda ya Dad’e da mayar da auransu , Dan Allah kibashi matarshi Umma ke kanki kin sauke nawi mai girma dake kanki …

 

Mujaheed ma yadasa tare da cewa Umma tsawon lokacin nan dakikaga bakiganni ba muna wurinshi, dan yanzu da USTAZ ya mike sai kiga yana k’ok’arin guduwa,dole muke tsayawa wurinshi nida yan uwanshi Umma, ni kaina da danike ganin nabarshi Wallahi dole tasa na hakura da duk abunda yamun ganin halin da yake ciki, Narokeki DA Allah Umma kiyi hakuri kimaidamishi matarshi, kibisu da ADDU’A kawai kikuma zubama sarauta Allah ido.

 

 

Still Umma batace komiba,saima zama datayi tabuga tagumi Dan ita abun yamafara bata tsoro , Ace katti su sata tsakiya suna kuka haka babu ko kunya, Ai dole bakinta ya rufe ruf.

 

Wayar Aliyu tayi ring ya zarota ya kanga ga kunnashi, tare da cewa Faruk ina jinka..

 

Salati yasaki da k’arfi tare da mikewa jikinshi na rawa yace ganinan hanya yanzu insha Allah.

 

Aguje yaso fita, umma ta tashi ta rikoshi tace mikefaruwa haka.?

 

Mujaheed yasaki kuka tare da cewa kafad’amuna dan Allah halin da USTAZ yake ciki hala ciwon ne ya motsa.

 

Aliyu ya share Hawayen shi yace jini ake bukata yanata bleeding shine akeso cikin gaggawa zanje aduba nawa agani, dan an D’ibi na Faruk.

 

 

Usman ya fashe da kuka jin ance ubanshi babu lafiya” yace ina zuwa nima”.

 

Umma ta dakko gyalanta da sadeeq a’kafadar ta dake bacci ”tace muje muduka, Dan tana ganin kamar shirine suke mata.

 

Bakaramin Dad’i Aliyu yajiba,ko ba komi yaga alamun samun nasara .

 

Kulle palon Umma tayi tafito ta iske mai gadinsu da wani driver da Saif ya ajemasu ,tace musu zataje ta dawo yanzu ita da Mujaheed.

 

Fatan dawowa lafiya suka mata .

 

 

Su Hajiya da sukaga Umma karcet basu tsaya bi ta kantaba suka af’ka D’akin.

 

Faruk ne kad’ai yayi k’arfin halin rugawa office ďin likita yafaďa musu ciwon USTAZ ya tashi, sai gasu sun yanko da gudu kusan likitoci biyar sukayi D’akin.

 

Umma ma binsu tayi tana ta hawaye, har takai bakin k’ofar sai kuma ta tsaya tare da latsa wayar ta takira number Aisha, ta kirata harta katse bata d’aukaba, Sai datamata kira biyar kana ta d’auka .

 

Afusace Umma” tace uban mikike inata kiranki baki d’aukaba?

 

Aisha batace komi ba sai kuka da tasanya ma Umma”.

 

AD’imauce umma tace” ke miye hakane wai minai miki Aisha ?

 

Cikin kuka Aisha” tace Umma gida nikeso in dawo, in nemi yafiyar USTAZ na marun da namishi cikin kasuwa,Inata mafalki akanshi marasa Dad’i Umma.

 

Umma ta ce Aisha yanzu haka muna Asibiti wajen Shi Wallahi yana cikin yanayi, Ina tsoron ya mutu Adalilin sonki duniya ta zagemu ace bamu da adalci.

 

Kamin Aisha tai magana sai jin ihu Hajiya sukayi tana cewa dan A’llah Maman Aysha ki rugo yana neman ki wai zai baki wasiyya ta karshe, Dan Allah kibiyoni Hajiya ..

 

Aguje Umma ta bita tama manta da wayar ta dake kunne suka faďa D’akin tare, babu abunda ka keji sai sautin kukan mutane, ciki kuwa harda Alhaji da jarumtarshi tayi lakwas.

 

Umma tak’arasa wajenshi batason sadda tasanya hannunta ba ta d’ago kanshi ta d’ora a’cinyarta ta shafa kanshi.

 

“Tace Abdallah gani! amma banason naji kace komi dan Allah kayi hakuri Allah zai yayemaka kaji ko?..

 

Murmushi sosai USTAZ keyi yana binta da kallo dan yanajinshi kamar a’cinyar Aisha, ko bakomi yason yanzu Danginta sun fara safkowa daga irin abunda yama jininsu,tinda gashi Rab’e-Rab’e a’cinyar mahaifiyar matarshi ,kai mai SHARI’A ka cutar Dani bakad’anba.

 

Magana yafara k’ok’arin yi amma numfashin shi baya fita sosai.

 

Wani likitane yak’ara so kusa dashi ya sauke kan USTAZ daga cinyar Umma yafara tausa kirjinshi sosai kamar yasamu pilo.

 

Wani tarike ustaz yasaki sai ga wai uban jini kamar Dunkulan hannu yafito daga bakinshi, furzar dashi yayi likitan yasanya tissue ya gogemishi kana suka koma gefe.

 

Ustaz” yace umma dama alfarmar danike so ta karshe Umma

Nayi gida kuma bana kowabane sai na Aisha, kizama sheda ko bayan raina gidan mallakin Aisha ne da yaranta ban.

 

Kan ya karasa saijin wayar Umma na Ring .

 

Shuru yayi Umma kuma ta datse kiran ganin Aisha ce.

 

Sake kiranta akai Umma ta dauka cikin kuka “tace zankiraki.

 

A’isha ma cikin kuka tace umma naji komi Wallahi najinm komi inaso kiba abdullahi wayar zamuyi magana……

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.