Auren Wata Tara Hausa Novel
Tag: Auren Wata Tara Hausa Novel
*1 & 2*
*FUNTUA*
_Unguwar Jabiri_
Tafiya suke cikin unifoam d’in Islamiya su biyu suna tafe suna hira kadan_kadan.
Asmy ce ta daddabo Zarah ta ce “Zarah gafa mutumin yau ma ya na kofar gidan Ku kuma wlh nasan ke ya ke jira ”
Tsaki wacce aka kira da Zarah taja cikin sanyi murya da daman Chan tun asali haka muryarta take komai takeyi zatayishi cikin nutsuwa da sanyi ta ce .
“Aiko bazan shiga gidan yanzu ba Allah har sai ya tafi ” sai sannan na K’are mata kallo doguwa Ce mai matsakaicin jiki
Choculate colour Ce bazaka kirata fara Chan ba haka kuma tafi karfin ka kirata da b’aka
tana da round face da dogon hancinta sai d’an k’aramun bakinta da ya d’an tsuke ya bada shape d’in heart Dimple d’inta guda biyu dukkaninsu sun lotsa
wanda tun asali haka suke ko batayi magana ba a lotse wanda suke k’ara fito mata da ainahin baiwar kyaun da Allah yayi mata Fuskarnan tata fresh ba komai sai kwalli da ta kurtawa idanunta Kad’an
Zarah tana da Bala’in shape Wanda ake kira da shape d’in Coca-Cola diri da Zati da Allah yayi mata shine Babban abunda ke Jan hankalin maza gareta Dan Zarah badai diri ba Dan koya tayi tafiya haka zakaga hips d’inta na Juyawa
Wanda saika d’auka da gangan ta ke yin hakan alhalin itama Ba so take ba danma koda yaushe cikin hijab take amma dukda manyan hijaban da take sanyawa baya hana bayyanar da surar da Allah yayi mata.
“Kama hannunta Asmy tayi cikin Sauri suka shiga gidansu Wanda madaidaicin gida ne Suna shiga Ajiyar zuciya Zarah ta sauke ta ce ” Allah yasa mayen bai ganmu ba dafa saiya biyo mu ko”
Aiko da ya biyoki wlh da yaga yanda ake Rashin mutunci Dan ni ba ke bace danfa ya ganki haka salo salo ba umm ba umm umm shiyasa ya rainaki wlh Zarah ki rage sanyin nan Lafiyarki tayi yawa haba ayi mutum kullum cikin sanyi dukda wannan halin naki ya sanya har Rabi take maki irin abunda take maki Dan taga bata gamu da y’ar zamani ba haba ke Ko a makaranta Saidai na shige maki fad’a to tun wuri ma wlh ki koyi kare kanki haba hakurinki yayi yawa wlh ”
Karanta Littafin Matar Yaro Hausa NovelĀ
“Asmy ta k’arasa fad’a tana huci “Mamanta ce Da ta fito daga kitchen ta na sauraransu ta ce ” Zarah karki biyeta kici gaba da yanda kike Allah yanason masu hakuri kowani d’an adam yana da nashi kalar jarabawar kinji ke kalar taki kenan kiyi kokari wajen ganin kin cinyeta Allah ya kawo maki sassauci cikin al’amuranki ga abinci nan kuzo Kuci kunji”
k’asa da kanta Zarah tayi tana Goge hawayen da suka zubo mata na tausayin kanta ta ce “Insha Allahu Mama ” Kallon Asma’u mamanta tayi ta ce “Karfafa mata gwuiwa ya kamata ki dingayi kullum ba Wai Zuga ta ba kinji” gyad’a mata kai asmy ta yi ta ce “Insha Allah Mama ” Tuwon Shinkafar da yaji Miyar taushe mai dadi da Mama ta zubo musu suka zauna Suka fara ci
Bayan sun gama Ci nan suka fiddo Littafansu na Islamiya suka dinga duddubawa Dan yanzu gaba d’aya hankalinsu ya na Ga saukar da ke tinkarosu Bayan sun gama dibawa jin ana kiran Sallar magriba ya sanyasu tashi Bayan sun gabatar da Sallar magriba Hijab d’inta Zarah ta sanya ta ce Bari na wuce gida sai da safe “Bankwana tayiwa maman asmy tare suka fito su biyu Kasancewar gida Ukku ne tsakaninsu sai nasu Ajiyar zuciya Zarah ta sauke ganin Nura baya nan A daidai bakin k’ofar gidan Asmy ta tsaya ta ce ” Sai Gobe Zarah Zan wuce “Kallonta tayi ta ce ” bazakizo mu shiga tare ba “Girgiza kai Tayi ta ce ” Saidai kawai mun hadu gobe”to Sai Allah ya kaimu kawata ta fad’a ta na kutsa kanta cikin gidan cikin siririyar muryarta tayi sallama a hankali
k’aramun gida ne d’aki hud’u d’aya na Mama Rabi d’aya na Baba sai na ukkun nata na hudun kuma na.kannanta ” a tsakar gida ta tarar da Mama Rabi tana ganinta ta watso mata wani banzan kallo cikin Masifa ta fara magana da cewa “an fake da Islamiya ana yawon karuwanci Dan matacciyar uwarki Da kikaje kika zauna uban wani zai d’aura miki girkin ne Eh ko kin Aje wani ne a gidan?girgiza kai ta fara tuni harta fara hawaye dan a rayuwarta kome Mama Rabi zatayi mata batajin ciwon shi kamar irin yanda take zagar mata Mahaifiya da ke k’asa Goge hawayenta tayi cikin muryar tsoro ta ce ” Kiyi Hakuri Mama “Tsaki Rabi taja tare da mik’ewa ta ce ” Kafin nan da minti Talatin na baki ki gama yimun tuwo da miya Dan uwarki”to “ta fad’a gabanta na fad’uwa tare da shiga kitchen din.
murhu biyu ta hura dukda iccen jik’e ya ke kasancewar yanayin damuna Haka tayi ta hura wutar cikin k’ank’anin lokaci ta na Sauri ta gama Duka ayyukan tukwana ta fito ta yi wanke wanke Su Habiba na Nan zaune suna latsa waya ba Wanda ko tsinke ya kama mata Harta gama komai tukwana ta wuce d’akinta Dan hutawa Cire kayan jikinta Tayi Tare da daura zani Dan zafi takeji kodan yanayin garin kamar akwai hadari a kasa ya sanya zafin fitowa tayi a lokacin Mama Rabi suna cin tuwo ita da yaranta Tab’e baki tayi tare Jan tsaki ta ce “Sai anje an gama yawon ta bugas din azo ana wankan iskanci a gida ” Idan da sabo ta saba hakan yasa ko a jikinta harta fito daga bandaki Bayan tayi alwalar isha i d’akinta ta wuce tare da shimfida tsohuwar dardumarta ta sanya hijab d’inta ta Islamiya ta kabbara salla
Bayan ta gama isha i tare da shafa’i da wuriri zaune tayi a wajen ta jima tana nemawa mahaifiyarta gafara a wajen ubangiji ta na hawaye ta ce “Allah ya jikanki Mahaifiyata har kullum ina kukan rashinki a kusa dani amma kuma nakanji farinciki idan na tuna da irin mutuwar da kikayi bansankiba ban tab’a ganinki ba Amma ki sani ina tsananin kaunarki kullum da tunaninki a raina nake kwana nake tashi na tabbatar da kina raye da bazan tsinci kaina cikin wannan k’uncinna rayuwa ba amma babu yanda na iya da Lamarin ubangiji haka Allah yaso ya ganni kuma nagode masa Allah yasa kin huta”
ta k’arasa fad’a tana fashewa da kuka mai cin rai Hade kai da gwuiwa tayi ta na ta kukan halin maraicin da ta tsinci kanta da tasowarta cikin marassa imani”Malam Yusuf Da ya shigo Yanajin y’artashi na yiwa mahaifiyarta addua Saida ya Goge hawayen tausayin y’ar tashi Shi kanshi idan yana tunowa da Mahaifiyarta kuma masoyiyarsa Zarah mace mai biyayya da hakuri Sai da ya Goge hawaye karasowa yayi Tare da zaunawa gefenta ya ce “Zahra’u Kiyi Hakuri kinji yaci ace kin saba da irin wannan rayuwar kisani komai yayi farko yana da karshe kinji y’ata Allah yayi maki albarka ya jikan mahaifiyarki ya k’ara miki hakuri da juriyar zama da rabi sannan ya nuna mun ranar aurenki ni kaina badan naso ba nake ganinki cikin wannan halin”
jin muryar mahaifin nata ya sanyata saurin Goge hawayenta Dan a duniya babu abunda ta tsana sama da tashin hankalin mahaifin ta tare da kirkirar murmushi ta ce “Baba ina yini ” Murmushin ya mayar mata ya ce “Lafiya qalau Zarah ta ya makarantar munyi magana da malaminku yau ya ce Akwai kudin sauka da za a kai me yasa baki fad’amun ba tun da wuri Zarah ” kasa tayi da kanta ta ce
“Baba naga baka da kudi kuma naga ba dole bane sai anyi walimar saukar da ni tunda Dai na hardace a kaina ai shikenan ” girgiza kai Baba yayi yanajin k’aunar y’ar tashi ta daban sosai hankali da hangen nesa irin na Zarah har mamaki yake bashi akwaita da hakuri irin na mahaifiyarta cewa yayi “Allah yayi miki albarka y’ata amma ko zamu rasa abunda zamuci saina biya miki kudin ba dubu goma bane Allah ya horemun kafin lokacin” ameeen Baba nagode “Kinci abinci dai ko?eh Baba ta fad’a ta na gyada masa kai ” yawwa to shikenan Sannan ya mik’o mata d’ari biyu ya ce “Gashi ki boye ki d’an dinga kashewa kinji” Murmushi tayi tare da amsa hannu biyu ta ce “Nagode Baba Allah saka da alkhairi ” Ameen y’ar kirki ya fad’a tare da yi mata saida safe ”
Bayan fitar Baba girgiza kai tayi tana jin k’auna da soyayyar mahaifin nata ta musamman tasan Shima ba ason ranshi take fuskantar kalubalen wannan ba Boye kudin da ya bata tayi a akwatin kayanta tare da dauko Alquran mai girma ta fara karantawa cikin zazzak’ar muryarta tana rerowa cikin k’iri’a mai dad’in sauraro a haka har bacci barawo ya kwasheta
kamar yanda ta saba koda yaushe tun asuba da ta tashi tayi sallah bata koma ba nan taci gaba da aikace aikacen gidan Har Safiya tayi wajen 8 da rabi taga su Habiba sun fito Suna hamma tare da d’aukar buta Zasuyi Alwala girgiza kai tayi wai ace Sai yanzu zasuyi sallah Kodan yau sunma tashi da wuri su da har 9 kaiwa suke batace komai saboda bata manta ba ranar da ta tab’a musu magana akan Sallar Safe da suke irin tijarar da suka mata hakan ya sanyata cigaba da Harkokinta Tana cikin d’ora d’umame Khairat ta lek’o Yarinya ce da bazata wuce shekaru goma sha daya ba kallonta tayi tare da cewa ” Ina kwana Aunty “Murmushi Zarah ta sakarma kanwartata dan duk cikin gidan itace Ta fita zakka ta ce ”
Lafiya qalau khairat Kintashi lfy “Alhmdllh ta fad’a ta na Amsar tukunyar da Take shirin dorawa ta ce ” bari na tayaki Aunty”A a a ki barshi khairat zanyi “Amsa tayi ta ce ” Nidai saina tayaki Suna cikinyi Mama Rabi ta lek’o Dan Safiya ta gulmanta mata Khairat na kitchen tana taya Zarah Aiki wata uwar ashar ta kawo ta lafta wadda saida cikin Zarah ya d’uri ruwa tuni ta dabarbarce “Kafin da d’ago Mama Rabi ta kife ta da Mari tare da cewa ” Dan Ubanki y’artawa zaki sanya Aiki tayi maki kama da kalar Aiki Sau nawa zan fad’a maki Ke kadai zaki dinga aikin gidan nan Eyye tsabar iskanci ma y’arda na Haifa itace zatayi maki aiki”Khairat ce ta mik’e cike da tausayin y’ar uwar tata ta ce “Kiyi hakuri Mama Ba ita ta sanyaniba ni naga ya kamata na tayata”
Tsawa ta daka mata Tare da nuna mata hanyar waje ta ce “Fice ki ban waje kafin na waiwayo kanki” Cikin Sauri ta fita ta bar kitchen d’in ta na gunguni”Zarah ko hawaye ne suka zubo mata Inda Mama Rabi ta shiga balbaleta da masifa Inda ta shiga ba ta nan take fita ba amma bata Ce mata uffan ba harta gama fadanta ta fita girgiza kai tayi tare da mik’ewa taci gaba da abunda ta ke ta na yi ta na hawaye “Bayan ta gama aikin D’akinta ta shiga ta share tare da daura towel ta dauki sosonta da sabulu ta fito Ta shiga wanka Bayan ta fito Nan ta iske Mama Rabi da d’iyan ta suna cin d’umamen Tuwon da ta dafa” bata bi ta kansu ba ta shige d’akinta Tare da Shiryawa cikin Wata Atamfarta da ta d’ansha jiki jin kukan yunwar da cikinta keyi ne ya sanyata mik’ewa tare da fitowa nesa da su ta tsaya tare da K’asa da kanta “Tayi shiru ”
Cikin masifa Rabi ta ce “kikazo kikayi mana tsaitsaye Mayya me za a baki” Dagowa tayi idanunta na zubar da k’walla tayi maza ta Goge ta ce “Daman abinci nazo d’auka ” Dogon tsaki taja tare da Banka mata harara ta ce “Mun cinye mu Kanmu bai ishemu ba ” Khairat ce dukda yarintarta ta ce “Mama ni bari na bata nawa na k’oshi” Harara ta banka mata tare da dankwashinta aka ta ce “inke kin koshi ni ban koshi ba ” girgiza kai kawai Zarah tayi ga abinci nan tana gani Bayan ita ta sha wahalar girkawa amma a hanata ga tsabar yunwa da takeji Juyawa tayi ta koma d’akinta tare da dauko d’ari biyun da Baba ya bata ta boye a jikinta hijab ta sanyo tare da Fitowa Tsawa Mama Rabi ta daka mata ta ce “Gidan ubanwa kuma zaki”
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza 3
-
Zuciya ta
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi
-
Aure da haihuwa
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya
-
Gangar Shedan
-
Angon mata biyu
-
A gidan mu take
-
Bafulatanar Rugga
-
Matar yaro
-
Mr Bello
-
Mijin Buzuwa
-
Gidan Uncle Complete
Powered by: www.mynovels.com.ng
āFita zanjena nemi abinda zanci “ta fad’a cikin rawar murya” koma ciki babu Inda zaki Dan Ubanki so ne kike ki k’ara jamun Zagi a wajen mutane duk abunda nake ba gani ake ba To ba Inda zaki”Amma Mama Ke fa kika hanani Abinci kuma zanje na saya ki hanani fita”ta fad’a cikin dauriya”eh bazaki ba ko fad’a zanyi ki mayar mun?
Girgiza kai kawai tayi tana Jinjina Rashin imani irin na Mama Rabi daki ta Koma tare da zaunawa ta rafka ubann Tagumi Hawayen tausayin kanta na zubo mata yaci a ce Inda sabo ta saba da halin da take ciki……✍🏿
*muje zuwa fans salon na daban ne Kudai kawai Kuci gaba da bibiyar gawurtaccen labarin da yazo cikin gawurtattu*
*ta hanyar comment da sharhi ne kad’ai zai tabbatarmun da labarin ya amshi wajenku ko akasin haka idan kun karanta ku daure Kuyi comment tare da sharing sauran grps masoyan Asali wannan itace babbar kwarin gwuiwar da makaranci ke bawa marubuci*
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ĘASA…*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ĘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huÉu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda Éaya N300
*DOMIN TURA KUĘIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ę³an Ęasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huÉu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda Éaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
Taku har kullum d’ince dai
👇🏿
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[8/21, 08:18] ❤️❤️❤️: 💑 *AUREN WATA TARA* 👨❤️👨
MALLAKAR
*Hajara L Sadeq*
*FREE PAGE*
🅿️……….*3 & 4*
Tana nan zaune tana jin yunwa har Ukku da rabi tayi cikin Sauri ta mik’e tare da sanya Hijab d’inta Dan daman Allah Allah take lokacin Islamiya yayi turaranta Wanda baiwuce Naira d’ari Ukku ba ta fiddo ta fesa Dan Ita daman Chan ma abuciyar son kamshi ce .
Fitowa tayi ganin ba kowa tsakar gidan Tare da barin gidan Gidansu Asmy ta shiga gaishe da mamansu tayi har k’asa ta amsa mata cikin girmamawa Babansu ne ya fito Shima gaishesa tayi ya amsa mata cikin sakin fuska Asmy ce ta fito daga palour tare da kallonta ta ce.
“Ki shigo yau kece da Shiryawa da wuri Ko y’ar jarabar bata nan ” Dariya Kad’an Zarah tayi tare da girgiza kai ta ce “Kiyi Sauri dai yanzu ” Kama hannunta tayi suka shiga cikin palourn su mai d’auke da kujeru matsakaita masu kyau sai madaidaiciyar plasma d’insu dake manne a d’akin Suna Kallon tashar arewa24 .
ganin ana maimaicin dad’in kowa ya sanya Zarah maida hankalinta ga kallon da ake Asmy tunda ta shigo ta lura da Idanun Zarah yanda suka fad’a tasan bataci abinci ba gashi tasan ko mutuwa zatayi bazata tab’a cewar bataci ba
Shinkafa da miya taje ta zubo dukda taci abinci Tazo ta Aje gabanta tare da kallonta ta ce “Sauko muci abinci my Besty” na k’oshi Kedai kawai kici mutafi?Harararta tayi ta ce “Aiko kice yau ba zuwa Islamiya Dan Allah sai kinci abincin nan idan ba haka ba Muyi ta zama a haka” Saukowa Tayi Dan tasan kawar tata ta aika Ta ce.
“Uwar y’an jaraba to muyi Sauri” Sai sannan Asmy ta saki fuska ta ce “kokefa my Besty wai kinsan Waec d’inmu ta fito Kuma alhmdllh Duka na cinye yanzu jiran neco kawai muke tunda ita kikayi ”
Cikin farinciki Zarah ta ce “Wow alhmdllh sis a Gaskiya na tayaki murna wlh Allah sanya alkhairi kice itama neco tana gab da fitowa muyi ta addu’a”
” Wlhko Besty Kinga murnar da nake “Har suka gama cin abincin suna Hira Inda Bayan sun gama sukayi sallah tare da wucewa Islamiya Dan duk shirye shiryen saukar da zasuyi ne nan da sati biyu ake.
Sai wajen magriba suka bar makarantar Inda daga nan kowa yayi gidansu Tun a Soron gidansu Zarah ta farajin muryar Salisu gabanta na fad’uwa Ji take kamar ta juya Dan tana tsoron mashayin Chan.
dak’yal tayi shahada ta shiga tun daga shigarta Salisu dake kan turmi yana busar sigari ya kafeta da idanu har wani lashe harshe yake Itako hade fuska tayi Tam Cikin muryar y’an maye ya ce “Daman tun d’azu nake jiran dawowarki Amaryata ”
dogon tsuka Zarah taja tare da Yin hanyar d’akinta janyo mata hijab yayi Wanda hakan ya k’ular da Zarah batasan lokacin da ta juyoba tare da wankeshi da Mari Salisu da saijin saukar Mari yayi a fuskarsa dafe kumcinshi yayi tare da nunata da yatsa ya ce.
“Ni kika Mara Aiko yau zakisan kin tab’a cikakken d’an tasha Dan uwarki Dan kin samu ma ana sonki Aiko daga yau bazaki k’ara gigin Marin wani ba ya fad’a yana zare belt d’in jikin wandonshi tuni cikin Zarah ya Dori ruwa Dan ba abunda ta tsana irin a tab’a lafiyarta Cikin Sauri Ta maza ta Ruga d’akinta Tare da sanya sakata ta rufe sai huci take.
” Salisu ko tsaye yayi ya na ta banka k’ofar ya ke kamar zai b’allata “Rabi ko shiru tayi Dan abunda yasa bata tanka ba Baba na bandaki tun daga Shigowar Salisu Kasancewar Tattare suka shigo da Zara da ido take masa nuni akan ya bari amma sai dura ashar yake ya na cewa yau sai ya raba Zarah gida biyu .
Baba ne ya fito daga bandaki cikin b’acin rai irin nasu na masu hakuri ya dakawa Salisu tsawa ” Juyowa yayi Dan duk iskancinshi yana shakkar Malam saboda mutum ne mai kwarjini Sosai Malam ya shiga F’ada ta Inda ya shiga ba ta nan yake fita ba sulalewa Salisu yayi ya bar gidan Inda ya koma kan Rabi ya ce.
“Wlh na.k’araga d’an iskan yaron nan ya shigo gidan nan zaki kuka da kanki Marainiyar Allah ku sakata gaba Kuyi ta musguna mata wlh kedai Rabi kiji tsoron haduwarki da ubangiji Dan sanya bak’inciki a cikin zuciyar maraya ba k’aramun Abu bane kina daukarsa wasa hakkin wannan yarinyar kadai ya isa ya hanaki kwanta kabari ko Dan a tunaninki duk abunda kike bansaniba .
“ina sane kuma ki kiyayi irin hukuncin da zan yanke nan gaba Dan Zarah ta fiyemun ke da kowa ma ” Tsaki Rabi ta ja tare da Barin wajen ta na gunguni “Girgiza kai Baba yayi tare da Yin alwala Dan ya wuce masallaci ya Tada musu sallah.
Zarah ko ta nan tana hawaye har taji fitar Salisu da yanda Baba yayi musu saitadanji sassauci Amma dukda haka tsoron bud’e d’akin take Dan tasan Rabi duk abunda Baba yayi mata akanta zata huce Ga tana son taje tayi salla ta na tsoro Gashi yau batayi musu girki ba tasan ta bani ta na nan rufe ta kasa fitowa tanajin irin ruwan zagi da masifar da Mama Rabi ke Surfa mata tayi mata banza
sai da kanta taje tayi girki wajen 11 PM tukwana Zarah ta fito tayi alwala tana sanda ta koma daki tare da hade Sallar magriba da isha i tukwana ta nemu waje ta kwanta
Dan Daman batasa ran cin abinci ba tama girka sai Anga dama dama ake bata Ko idan Baba na gidan bare ba ita ta girka ba Cikinta na kukan yunwa a haka har bacci barawo ya kwasheta.
Washegari Tana kwance da Yamma tana bitar karatun Islamiya kasancewar Alhamis ce suna gida taji yaro yayi sallama tare da cewa ana kiran Zarah a waje ”
Mama Rabi Ce dake waje ta ja tsaki tare da cewa “kaje kace bata nan ” Baba ne da shigowarshi gidan kenan ya kalli yaron ya ce “je kace gata nan”
Fita yaron yayi yayinda Mama Rabi ke cika tana batsewa Kwalawa Zarah kira Baba yayi Bayan ta fito Ya ce “Jeki shirya Ana Kiranki kofar gida”
” to “tace tana kasa da kanta dan bazata iya musu da mahaifinta ba Tare da komawa ciki ta sanyo k’atuwar hijab d’inta Ta fito Mama Rabi na binta da harara Dan tana bakincikin taji ankira Zarah waje zance.
kamar yanda tayi tsammani shidinne sanye cikin wani bakin yadi gashi bak’i ga bakin yadi sai suka saje tsaki taja a ranta tana turo baki harta isa Inda yake tare da ja ta tsaya tana kauda kai .
“Nura ko cikin farinciki ya ce ” Yakike masoyiyata Yaudai Ranar ta musamman ce a gareni tunda kika amsa kirana “Wani banzan kallo Zarah ta watsa masa tare da Jan tsaki ta ce ”
“Malam idan ka gama zan wuce ina da Aikin da nake “a ah yi hakuri gimbiyar mata kinsan ke din ta musamman ce sai ana lallabaki Dan Allah Zarah ki amshi tayin Soyayyata tsaki Zarah taja ta ce ” Inma kana wannan mafarkin Ka daina Dan bana sonka na fad’a maka ba sau d’aya ba basau biyu ba Amma ka nace ayi mutum ba zuciya ta fad’a tana Kara Jan tsaki tare da Juyawa ta shige cikin gidan ta na gunguni.
Baba na ganin shigowarta rai bace ya ce “Lafiya y’ar Amanar Baba waya tab’amunke naga ranki bace ” Cikin shagwabarta da tunda aka haife take da ita ta ce .
“Baba Nura ne kuma nace masa yadaina zuwa wajena yak’i dainawa” Girgiza kai Baba yayi tare dayi mata murmushi ya ce “in banda abunki Zahra’u meye aibun Nura yaro mai hankali da sana’arsa da komai ”
Zarah ji take kamar tayi kuka ta ce “Ni Baba bana sonshi kuma ni da ba Aure zakamun ba Duka nawa nake” Dariya Baba yayi ya ce “to shikenan y’ar Baba kwantar da hankalinki ai ba a dole a soyayya Yawwa daman zuwan da nayi kauye jiya na sayar da akuyata Dubu sha Biyu Yanzu haka daga wajen malamin naku nake harma nakai kud’in sun bani receipt ya fad’a yana nuna mata receipt din” .
Cikin farinciki Zarah ta d’ago ta ce “Kaii amma nayi farinciki nagode Baba Allah saka da alkhairi ya k’ara budi nagode Nagode”
” Ameen y’ar kirki “ya fad’a yana Mikewa Mama Rabi Ce ta mik’e cikin Masifa ta ce
” Amma dai Malam kasan Irin faman da muke a cikin gidannan kullum cikin cin tuwo Miyar kuka muke Maimakon da kud’in ko y’ar shinkafa ma auno mana Shine zakaje Ka biya asara Har dubu koma akan Saukar da bama ta kirki ba aka bibiya izif biyar bazata kawoshi a ka ba wlh abunda kake Malam ba adalci bane na tabbatar cikin yarana Khairat ko Safiya acire Habiba da Salamatu tunda ba yaranka bane Babu wacce zaka biyawa Har dubu goma idan zasuyi sauka amma ita y’ar gwal din ka lale Naira na dukan Naira har dubu goma ka biya mata”.
girgiza kai kawai Baba yayi Dan ba a komai ya fiye mata ba ya ce “Suma cikinsu Wata ta dage tayi saukar taga ko sama da dubu goma idan ban bayarba yaran da kin lalata su islamiyar ma na sanyasu amma ba zuwa suke ba Shine har zakizo kina kushe karatun yarinyar da ta shekara da shekaru tana gangariyar karatu ta gama sauka gashi yanzu har tayi harda Wanda iya tsawon rayuwa baxan iya tuna ince ga ranar da Zarah bataje makaranta ba ince Salamatu da Habiba ba sun girmeta ba cikinsu ba mai izif Biyu cikakke gwarama khairat shine zaki hadata da su wannan Abun da kike za a iya daukarsa a hassada ce ”
” Sosai maganganun baba suka b’atawa Rabi Tai masifa ta shiga surfawa Inda ta shiga ba ta nan take fita ba hada kuka wai yayiwa diyanta gori Baba bai kulata ba ya ficewarshi tana ganin fitar Baba ta sauke ruwan masifarta akan Zarah saida tayi mai isarta itadai Zarah bata kula tab’a sai aikinta da ta kama .
suko su Habiba ko akansu ita da da Salamatu suna Chan suna wayar batsarsu da samarinsu Bayan Mama ta gama masifarta daki ta shiga Inda ta samesu kowanne da earpiece suna Waya sai huci take Salamatu ce ta katse wayar tare da cewa.
“kema Mama ki daina tada hankalinki akan komai meye akayi akayi wata banzar Zarah kina da mu ” Tsaki Rabi taja ta ce “ba dole na damu kaina ba yarinya duk tazo tana neman muku zarra Kuna nan zaune bakinku primary amma yarinyar nan shegiyar da bala i na da komai Amma saida har ta gama secondry school sannan gashinan har tana hardar alk’ur ani amma ku shaggun ko izif d’aya cikakke bana ce zaku kawoshi ba ga shegen farinjini tsiya yarinyar nan Duk ta na neman ta rikitamun lissafi ”
“Habiba ce ta turo baki tare da cewa “kema Mama meye abun damuwa anan har waccen figaggiyar yarinyar y’ar shekara 16 zata dameki sannan da kike maganar Karatu har wani amfani ke gareshi a zamaninnan Mama Me muka nema muka rasa Muma dai daidai gwargwado muna da namu farinjinin tunda manyan yaran da suke zuwa wajenmu da kud’in da ake kashe mana ma kadai ya isa ki gane munyiwa yarinyar Chan zarrah Mama”
“Kullum maganar kenan kuna tare da manyan yara yau a sauke ku a wannan mota gobe a saukeku a waccen amma har yanzu an rasa na aure guda d’aya gaisuwa ma suzo abun ya gagara”.
Kwana a tashi ba wuya a wurin Allah a yaune ranar saukar su Zarah Duka daliban makarantar sanye suke da ankon atamfa tare da hijab Blue Sabbi sai tag din shaidar su a wuya manyan malamai sosai aka gayyato a walimar .
Wanda wurin ya cika sosai kowa da d’an uwanshi iyaye da abokan arziki sunzo Zarah na zaune ita da Asmy Dan Mamansu Asmy ma tayi musu ankon kayan A gidansu Babu Wanda yazo Sai Baba Dan tanajinsu khairat da tace ma.zatazo Mama Rabi ta hanata .
Hakan bai dameta ba Dan daman ba buk’atar zuwan nasu take ba Fuskarta rufe take da nikab nan aka shiga kiraye kirayen dalibai Bayan sunyi karatu a basu kyaututtuka har akazo kan sunanta.
*Zarah yusuf*Gaban Zarah saida ya bada daram saboda sosai takejin kunyar ratsa mutanen nan Saida aka k’ara kiran sunanta sau biyu tukwana ta mik’e Shima saida Asmy ta zungureta tana mata Dariya kamar wacce batason ta taka kasa Haka take ratsa wajen Wanda duk Inda ta gitta sai an bita da Kallo dukda kwayar idanunta kadai ake gani fuskarta rufe take bai hana Kyaunta bayyanuwa ba .
a haka harta isa kan step din mik’a mata abun karatu akayi amsa tayi tare da Fara rero qir’a cikin zazzak’ar muryarta Mai dadin sauraro tsakiyar suratun bak’ara take karantawa babu mahalukin dake wajen da zaice karatun Zarah bai ratsa sa ba Mutane har wani lumshe ido suke iyaye da dama sunajin inama y’arsu ce jin irin yanda take fitar da tajwidi.
Baba ko wani farinciki da annashuwa ce yakeji na shigarsa yana Godiya ga Allah da ya mallakamai Zarah a matsayin y’a tayi minti ashirin tana karatu batare da gargadaba tukwana Aka amshi abun maganar tare da yi mata kabbara .
Duka wajen kabbara ya d’auka Inda manya daga cikin bak’i suka mik’e tare da Fara yiwa Zarah kyauta Bayan ta amsa tayi musu Godiya Malam ta mik’awa jinjina mata Malam yayi da hannu Dan daman sunsan Zarah zata fiddasu kunya a taron nan
Bayan nan Aka shiga bada kyautar karramawa ga d’alibai Inda yawaici Duka Zarah ta amshe kyaututtukan saboda duk fagen da akazo ita d’ince saida taci kyauta ukku d’aya ta wacce tafi kowa kokari a ajin ta biyu kuma Wacce bata fashi ,ta Ukku nutsuwa da girmama malamai.
,itama Asmy ta amshi kyauta biyu d’aya ta maida hankali a karatu d’aya kuma ta Rashin makara Bayan nan suma sauran dalibai aka shiga basu nasu kyaututtukan sai around 2:pm aka k’are taro Bayan baki sun tafi Ya rage daga dalibai sai malamai .
nan Malaman suka bawa Zarah kyaututtukan da ta samu duk a emblem ne wasu Ba yanda batayi ba akan malaman su rik’e sukace a a a nata ne Sosai Malaman sukeson Zarah saboda kwazo da kokarinta Tabbas Zarah tabar makarantar zasuyi Babban rashi Dan duk musabaqar da ta tashi da ita ake turawa kuma ita ke ciyo musu na daya.
Bayan sun taho daga Makaranta kai tsaye gidansu Asmy suka nufa a kofar gida Zarah ta tarda Baba Dan ya rigasu tahowa Wajenshi suka nufa Kallonsu yayi ya ce “Allah yayi muku albarka Zarah ked’in y’a ce ta gari da kowani uba zaiyi sha’awar kasancewar ki y’arshi ina matuk’ar alfahari dake Allah yayi miki albarka ya baki miji na gari mai tausayi da jin k’ai”.
murmushi Zarah tayi tanajin dad’in addu’ar Baba ta ce “Ameen Baba nagode mik’a masa kyaututtukan da ta samu tayi ” nan ya shiga d’agawa emblem na farko kud’ine tsabarsu dubu Hamsin na biyu kuma turmin atamfa na Ukku alqur’an ne sai sallaya a ciki da charbi”Cikin fara a Baba ya ce……..✍🏿
Ga masu buk’atar a tallata musu hajarsu su tuntub’eni akan number wayata kamar haka 07026166526
Ko masu buk’atar shiga grp sharhi ko tambaya hanya a bude take
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ĘASA…*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ĘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huÉu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda Éaya N300
*DOMIN TURA KUĘIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ę³an Ęasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huÉu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda Éaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[8/21, 15:53] ❤️❤️❤️: 💑 *AUREN WATA TARA* 👨❤️👨
MALLAKAR
*Hajara L Sadeq*
🅿️………*5 & 6*
“Masha Allah natayaki murna y’ata Allah sanyawa karatunku albarka ”
Ameen suka fad’a ita da asmy Mik’a mata kyaututtukan Baba yayi da niyar ta amsa.
“girgiza kai tayi ta ce ” a a a Baba banason komai a ciki komai na sama na sameshine ta dalilin tarbiya da jajircewar da kayi a gareni “.
girgiza mata kai yayi ya ce ” na sani Zarah ta amma Bazan amsar miki Komai ba nasan kina da buk’atar abubuwa da dama bakya tambayata Dan haka ki biya bukatunki dasu .
“Girgiza kai tayi ta ce ” a a Baba wlh bana buk’atar komai kafini bukatarsu Dan Allah ka amsa “.
Duk yanda Zarah tayi Baba ya amsa kin amsa yayi saida Asmy tasa baki dak’yal ya Anshi Dubu ashirin Inda ya mik’awa Asma’u sauran kudin ya ce ”
“Amshi ku tafi Sannan ya kalli Asmy ya ce “kiyiwa mamanki Godiya kice nagode Allah ya saka da alkhairi Tabbas Saratu ta cika y’ar mutunci kuma ta cika Alkawarin aminiyarta mariganyiya Kinga yarinyar nan saboda kawaici bata fad’amun akwai maganar Anko ba Allah sarki ashe har tayi muku saida safe take fad’amun angode Allah bada lada”.
Murmushi Asmy tayi ta ce “To Baba ” Barwa Baba sallayar sukayi tare da Qur’an din Inda suka koma gidan su Asmy sai tayasu murna ake nan y’an uwa da abokan arziki suka shiga shigowa tayasu murna da Yamma suma sukayi y’ar k’aramar walimar su Wanda mamansu Asmy ce ta shirya hakan.
Bayan magriba isha’i Asmy ta kalli Zarah ta ce “Wai kudinnan sis me za ayi miki dasu” ki bawa Mama kawai ni ba abunda zanyi dasu”Mama ce dake jinsu ta ce “Har ance babu abunda za a yi da kudi Zarah zandai Aje miki ” .
Girgiza kai Zarah tayi ta ce “Mama Dan Allah ki rik’e wlh babu abunda zanyi dasu ke ai tamkar uwa kike a gareni Dan Allah Mama ki rike ” .
girgiza kai Mama tayi ta ce “a a fa Zarah Aje miki kawai zanyi karki k’ara cewa wani Abu ”
shiru Zarah tayi badan taso ba Dan a abunda maman asmy take mata ko jininta ce ita sai haka .
“Asmy ce ta ce ” Mama babansu zarah yace nayi maki Godiya “girgiza kai tayi ta ce ”
” Ai Tsakani na dasu ba Godiya Komai nayiwa Zarah Ban fad’i ba irin zaman mutuncin da mukayi da mariganyiya da amintar da mukayi a lokacin bamu da hali amma Matar nan bata ci banci ba akwai lokacin da saimun kwanta bacci haka zata buga mana gida na bud’e naga abinci ne ta kawomun a lokacin muna cikin wani hali da haka zamu kwana bamuci ba muna halin Rashin babu Amma Matar nan bata tab’a cin Abu Bancishi ba Munyi zama na amana da mutunci da mahaifiyar Yarinyar nan “.
Goge hawayenta tayi ta ce Har yau idan ina tuno da zahara’u bazan daina kukan rashinta ba mace mai kirki hakuri da juriya Allah dai ya jikanta yasa ta huta”.
Sosai sukayi sanyi Cikin k’asa da murya Zarah ta ce Ameen ganin ta na shirin yin kuka ne ya sanya Mama barin maganar tare da kama musu hirar duniya Har ta samu ta d’an warware
Bayan sunci abinci Cire kayanta Zarah tayi tare da sanya rigar baccin Asmy Dan daman nan gidan take Aje sabbin kayanta saboda su Habiba suke lalata mata su sanye mata kuma bata isa tayi magana ba hakan yasa take ajewa gidansu Asmy .
nan gidan kawai take samun walwala da farinciki Sai wajen 10pm ta wuce gidansu har bakin kofar gidan Asmy ta rakata tukwana ta Koma Zarah koda ta shiga Zaune ta tarar da Mama Rabi na girgiza k’afa tana ganinta ta taso tare da Wanke da Mari Dan da bakincikin kyaututtukan da akace Zarah ta samu ta yini hakan ya sanyata huce haushinta na dalili marar ma ana da tushe nan tahau dukanta tana bala i tana cewa .
“Y’ar iska tun safe rabonki da gidan nan Sanadin mutane su dinga zagina suna kin lalace a hannu na Bayan duk yanda zanyi inayi iya kokari na Amma kullum baki da aiki sai jamun Zagi cikin unguwa Itakuma saratun in gidanta zaki koma saitazo ta daukeki Dan kazar kazarta kuma daga yau bazaki kara fita ba daga gidan bare ki fake da islamiya na kara ganinki gidan saratu wlh duk tsiyar da na shuka maki ke kikaja shine kikayi zaune gidanta yau babu aikin da kikamun uban wani kike tunanin zai maki aikin gidan Dan matacciyar uwarki ” .
Zarah kuka take sosai ta durkushe tana bawa Mama hakuri anma bata Rabu da itaba da hannu take jibgarta Baba ne ya shigo tun a soro yaji kukan y’ar lelen nashi .
cikin b’acin rai Baba ya shigo Tare da wanke Mama Rabi da Mari cikin b’acin ran da idan kaga yayishi tofa rai ya b’aci ya ce “Duk iskancin da kike kikaga ina kyaleki ba tsoronki nake ba Rabi gudun tashin hankali ne me marainiyar Allah tayi miki da Zaki hauta da duka daman an fad’amun irin zalincin da kikewa yarinyar nan idan ba Dan kin sameta mai hakuri bata fad’amun shiyasa kika maida ita jakar ki to hakuri na ya fara kaiwa Bango daga yau Zahra’u bazata sake Wani aiki a gidan nan ba su d’iyanki aikinme suke idan bazasuyi aikin ba gidan ya rube karewar kazanta kumasannan daga yau Kika Kara d’aga hannu kika daki yarinyar nan kin daki igiyar auranki a bakin aurenki”
Nuna kanta Rabi tayi ta ce “Ni kake fad’awa haka Malam ” Amfad’a maki ko akwai abunda zaki iya”jinjina kai tayi ta na girgiza k’afa na borin kunya Dan Malam bai tab’a mata haka ba tasan yakai bango Har ya iya d’aga baki ya furta mata a igiyar Aurenta tofa ya fara gajiya da ita hakan yasanya ta yin lakwas Dan Tasan ta rabu da Malam asirinta ya gama tonuwa Dan duk cikin mazajenta biyar da ta aura babu mai hakurin Malam bazata tab’a yarda Auransu ya lalaceba
wucewa ciki tayi kamar zata tashi sama Baba ko Kallon Zarah yayi ya ce “Tashi ki shiga kici gaba da hakuri kinji wataran sai labari ” Mikewa Zarah tayi ta ce “Toh Baba nagode ” tare da shiga d’akinta tana hawaye har bacci ya d’auketa.
Washegari koda ta tashi bata sa ran Bata abinci ba Ta na nan zaune wajen 10 koda ta lek’a ta tambaya ina abincinta Da masifa Mama Rabi ta korota ta ce Daga yau bazata k’ara cida ta ba Tunda ubanta ya hanata ta girka to itama bazataci shi ba ta nan zaune ta na hawaye taga shigowar Asmy dakin maza tayi ta goge hawayenta Murmushi suka sakarwa juna “Zarah ta ce
” yanzu nake tunaninki Besty”wlhko nima tunaninki ya sanya na taho ta fad’a tana zaunawa gefen katifar da take kallonta tayi ganin yanda fuskarta ta kumbura Alamun Tasha kuka kamata tayi ta ce “Mai ya faru Besty ” kirkira murmushi tayi ta ce “Bakomai me kika gani”?hmmm karkiyimun karya Zarah ina gane halin da kike ciki ko baki fad’amun ba nakanji a jikina fad’amun meyake faruwa ”
nan Zarah ta fad’a mata abunda ke faruwa Mikewa asmy tayi tare da dura ashar ta ce “Wlh iskancin Matar nan yayi yawa bari zan gwada mata ni y’ar zamani ce ā
” ta fad’a tana niyyar fita kamota Zarah tayi cikin Sauri ta ce ‘ki Rufamun asiri sis Dan Allah karkije ki k’ara jamun ni komai tayimun na barta da Allah .
dak’yal Zarah ta samu Asmy ta hakura Kama hannunta tayi ta ce “Taho muje gida ki karya ” tare suka fito ” Mama Rabi ta bisu da harara da tsaki suna isa gidan su asmy nan Zarah ta karya Dan tare suka shiga kitchen suka dafa indomie Bayan sun karya gadon d’akin asmy suka kwanta Dan su huta daman Zarah da gajiyar jiya bata saketa ba Aiko kafin kace me bacci yayi awon gaba da ita itace bata tashi ba sai wajen Azahar
tana tashi tayi wanka ta sanya kayanta a gidan Anko sukayi da asma u da Yamma Mama ta aikesu gidan babbar yayar Asmy dake Aure wata unguwar Gyara fuskarta Zarah tayi tare da shafa hoda Wanda Asmy ce ta sanyata shafawa Bayan ta sanya doguwar Hijab d’inta mai hannu tana shirin daura nikab asma u ta rik’e tana Dariya ta ce “Haba Kinga yanda kikayi kyau kuwa please muje a haka Dan Allah ”
tana murmushi ta ce “Allahko Besty” Eh mana ai nikab bakoda yaushe ake sanya shiba itama kalar hijab din ta Zarah ta sanya Bayan sun fito Mama ta basu kudin napep tare da cewa kar kuyi dare to suka fad’a tare da fita basu jima ba Suka samu napep koda suka isa gidan Hauwa’u daman sun saba zuwa tare sai nan nan take da Zarah kamar ma itace kanwartata Zarah ko sai wasa take yiwa k’aramun d’anta ganin magriba tana gabatowa ya sanya su mata bankwana Suka fito
d’ari biyu ta basu waigawa sukayi unguwar suka ga ba Alamun Abun hawa Tafiya suka fara Kad’an kad’an parking d’in mota sukaji daga bayansu hakan baisa sun juya ba saima cigaba da Tafiyarsu da suke Zarah ta ce
“Wannan tafiyar da mukayi ai daman karasawa mukayi a k’asa munkusa fa Rabi” Wlhko ai inbanda magriba da kawai a k’asar muka tafi muka ma sai awara da kud’in napep din wlh “cewar Asmy ” Assalamu alaikum warahmatillahi ta ala wa bara katuhu ā
“Suka tsinkayi Muryar wani saurayi daga bayansu ” Zare idanu sukayi tare da Kallon juna ta wutsiyar ido Asmy ce tayi k’arfin halin amsa masa sallamar yayinda Zarah ta k’ara yiwa saurinta mai “matashin saurayin ne ya ce ” Dan Allah y’an mata idan ba damuwa minti biyu zaku bani muyi y’ar magana
“Asmy ce kamar zata tsaya Zarah ta juyo tare da banka mata harara cikin siririyar muryarta ta ce Kiyi Sauri mana mu tafi munyi masa kama da matan da za a Tara a titi ta fad’a tana turo baki” Tare da tsaida napep da sukaga zata wuce “maza tayi ta shiga Asmy ko girgiza kai tayi tare da Kallon matashin saurayin ta ce ” Kayi hakuri Malam ba mutunci bane tsare mace a titi shiyasa ā
“tana gama fad’ar haka itama ta shiga cikin napep d’in Cizon yatsa Hafiz yayi zazzak’ar muryarta na dawo mashi har tsakiyar kansa kyakyawar fuskarta ce ta shiga yi masa gizau rumtse idonsa yayi da karfi tare da bud’ewa ganin napep d’insu na shirin yi mashi nisa ya sanyashi saurin komawa mota ya tada tare da binsu Dan shifa ya ga Matar Aure.
Koda suka isa gida Ana gama Sallar magriba Suna isa salla sukayi Bayan sunbawa mama sak’on da itama ta bayar a kawo mata ana isha’i nan sukayi sallah Wutar da aka maido ne ya sanya Asmy saurin Mikewa tana murna ta ce ” alhmdllh daman yanzu ake tsaka da series din da nake kallo a zeywood ā
Ta fad’a ta na kunna kallo Zarah ko na kwance a doguwar kujera nan Asmy ta zauna tana cigaba da Kallon Indian series din da ake hankalinta duk ya na wajen Zarah da ba kallo take ba Ganin yanda Asmy ta maida hankalinta a wajen ya sanyata Fara kallo Sosai taga ana zuba romance love a film d’in Tuni taji wani irin feeling ya bijiromata tun daga tsakiyar kanta Rumtse idonta tayi sosai tare da matse cinyoyinta lokaci guda mararta ta fara mata wani irin murdawa
Cikin karfin hali ta na murya dak’yal ta ce “Sis ki kashe Dan Allah ki kashe” ta fad’a ta na rumtse ido”Cikin Sauri Asmy ta kashe shataf ta mance da yanayin kawar tata da bata kunna ba cikin Sauri ta je Wajenta tare da kama hannunta ta ceā
“Sorry sis Na manta larurarki ne kuma banzata zaki kallaba shysa ” murda kawai Zarah take cikinta na mata wani irin murdawa “tuni ta fara shafta uwar zufa cikin kid’imewa Asmy ta mik’e Dan bata mance irin bak’ar wahalar da tasha ba kwanaki Wanda har saida akaje Asibiti shawarar da doctor ya basu ta fad’o mata a rai cikin Sauri ta mik’e tare da………..✍🏿
*Domin magana da marubuciyar sharhi tambaya ko kuma Karin bayani 07026166536*
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ĘASA…*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ĘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huÉu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda Éaya N300
*DOMIN TURA KUĘIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ę³an Ęasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huÉu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda Éaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
*_Miss Hajo ce_* 🤙🏿
[8/22, 13:59] ❤️❤️❤️: 💑 *AUREN WATA TARA* 👨❤️👨
MALLAKAR
*Hajara L Sadeq*
*TEAM GAWURTATTU BIYAR*💃
🅿️………*7 & 8*
Tare da rugawa Dakinsu maganin baccin da Dr ya basu akan idan ta fara haka a bata zai iya taimaka mata ta maza ta fito tare da bude kwalbar maganin Tado kanta Kad’an tayi tare da sanya mata kwalbar maganin a baki
Saida Tasha kusan rabi tukwana Asmy ta janye Ba ayi minti goma ba wahalallen bacci ya kwashe Zarah Ajiyar zuciya Asmy ta sauke tare da zaunawa gefen kawartata .
Mama ce ta shigo kallonta ta yi ta ce “Lafiya asmy naga Zarah kwance kamar bata lafiya ” kasa da kanta Asmy tayi ta ce “Eh Mama bacci ta ke ” Okay ta fad’a tare da komawa kitchen Dan ta dagosu tunda taga kwalbar maganin bacci hannun Asmy .
zarah ita ce “bata tashi ba sai wajen la asr ta na tashi taji sauk’i.
Haka rayuwar Zarah taci gaba da wakana da dadi ba dadi danma yanzu ta samu sassauci tunda Baba yayima Mama Rabi wannan Abun bata Kara yunkurin dukan ta ba.
sannan daman su habiba ba wani harkansu take shiga ba Dan magana ma saita kama take had’asu gwarama khairat itace Dan Safiya ma dukda yarinyartarta ta fara kwatsawa dasu Habiba shekararta 13 amma rannan ta hangota suna tafiya da wani wai Saurayi har yana rik’e hannunta.
irin dabi’ar yaran gidan nasu Sosai take mata ciwo dan ma Baba yana bakin kokarinshi Amfi karfinshine saboda yanayin aikin da yake ba na zama bane.
Neco d’in su Zarah ta fito masha Allah ta samu 9 credit ranar zokuga irin farincikin da ta shiga ita da kawarta sai tsallen murna suke Suna cikin murna gidan su Asmy aka Aiko wani yaro aka ce Ana kiran ” Zarah
“jekace bana nan ” Zarah ta fad’a tana yamutsa fuska mamansu Asmy ce ta ce “je kace gata nan” Kallon Zarah tayi ta ce “y’ata jekiga waye ne Ai ba a haka ”
“,to Mama ta fad’a tare da mik’ewa ta sanya hijab d’inta har k’asa ta fito Rungume da hannayenshi ta sameshi A jikin motarshi kirar corolla L E sanye yake cikin shadda ash Bak’ine amma coculate colour bashi da muni haka bazaka kirashi da kyakyawaba.
” k’arasawa wajen Zarah tayi tana jin d’ari_d ‘ari Hafiz ko tunda ta fito ya kafeta da idanu ya na k’ara yabawa da zubi da kyan sura uwa uba kyau irin na Zarah dan tunda ya ganta a wajen safka ya kwallafa rai a kanta.
Dan lokacin da suka haduma arashi akayi yaje unguwar wajen wani abokinshi Hakan yasa ya bi mai napep din Har ya gano gidansu Zarah Inda ya nemu information a kanta kuma ya samu bayanin komai a kanta.
tundaga tarihinta da irin wahalar da take sha sosai ya tausaya mata hakan ya k’ara sawa yaji soyayyarta a ranshi.
“Da fara’arshi yayi mata sallama tare da cewa “fatan na sameki lafiya sarauniyar mata ”
Batasan lokacin da murmushi yazo mata ba ta ce “wa’alaikumussalam yaushe na samu wannan mukami haka Ba nad’i ba komai a nadani har sarauniyar mata anma bansaniba wannan mukamin ai sai manya “.
āai kin fi ma a kiraki da sarauniyar mata saboda ked’in ta musamman ce a cikin mata”K’asa da kanta zarah tayi ta na wasa da zoben hannunta.
“Da farko dai su na na Hafiz ma’aruf Mahaifina tsohon Dan kasuwane kuma.manomi a wannan garin namu nine Third thild d’insa A yanzu na kammala Degree d’ina a Umyuk Inda yanzu ina shirin jonawa masters wannan shine takaitaccen tarihina”
“Tsaki Zarah taja a ranta ta ce ” ji shegen surutu kowa ya tambayesa a fili kuwa cewa tayi”masha Allah Nice to meet uh”.
gyaran murya Hafiz yayi ya ce “da farko dai tun ranar da na fara ganinki Naji kin tafi da imani na kuma ina sonki so na aure inason ki zama uwar y’ay’ana duba da tarbiyarki,hankalinki da nutsuwarki a Gaskiya Zarah ki godewa Allah a zamaninnan samun kamarki sai antona Allah yayi miki komai a rayuwa kina da kyau tarbiya ga kuma ilimin addini both side boko da arabi kafin nazo wajenki saida nasan wacece ke ina fatan za amshi tayin soyayya ta”
” uhm Zarah kawai tace tare da cewa”Gaskiya zan fad’a maka ka fara zuwa wajen mahaifi na ka nemu izini a wajensa Dan bai bani ikon kula kowaba har sai an nemu izininshi sannan nagode da soyayya”
“ta na gama fad’ar haka ta juya ta shiga gida Dan ta tsani namiji mai yawan surutu .
” Hafiz ko yaji dadi a ranshi tunda da kanta ta ce yabi ta iyayenta hakan ba k’aramar dama ce ta sameshi ba”.
“Zarah na komawa gida Nan Tabawa Asmy labarin yanda sukayi ta na Jan tsaki ” Dariya asmy tayi mata ta ce “Uhm nikan banga makusha a wajensa ba wlh daga gani yana da nutsuwa”
Harararta Zarah tayi ta ce “Ke wani ganin baki da hankali ma wlh Haba mutum sai shegen surutu ke nifa sanin kankine bansan surutu ” .
Chab nikam zanso naga mijinki zarah kowa yazo saikince ga aibunshi Asa Nura ma wannan ba Mate d’inki bane amma hakafa kwanaki wani daga katsina yazo wajenki saida kika koreshi Kinga Zarah kiyiwa kanki fad’a “.
Kamar yanda ta fad’a masa da daddare yaje ya samu mahaifinta a waje Inda Yayi mashi bayanin abunda ke tafe dashi Malam yaji dadi sosai Dan dukda a dare ne baiga fuskarsa ba kasancewar duhu amma a kalaman yaron yasan yana da nutsuwa”.
ce masa yayi ba damuwa zai iya fara zuwa Wajenta hakan sosai yayi wa Hafiz dad’i.
Washegari Baba saida ya sanya aka masa bincike akan Hafiz kuma aka tabbatar masa da yaro ne mai hankali da nutsuwa hakan yayiwa Baba dadi sosai .
Ranar da daddare ya samu Zarah a d’aki Inda ya shiga mata nasiha tare da cewa ” Kinga Zarah yaron nan da alamu ya na da hankali kuma na bincika an bani kyakyawan zato a kansa zai dinga zuwa wajenki har Allah yasa ku daidaita kanku kinji”
Dagowa tayi kamar zatayi kuka ta ce “Bab.” shit karkice komai Zarah kice “Allah ya zab’a miki alkhairi Dan ba abunda nake da burin gani a rayuwa da raina sama da aurenki na k’agu naga ranar da zan Aurar dake zarah kema ki huta da wahalar gidannan shi yasa kullum Addua ta da buri na naga ranar Auranki Allah ya baki miji na gari Wanda zai rikemunke da amana”
kasa da kanta Zarah tayi Bayan Baba ya fita daga d’akin saida tayi hawaye ita harga Allah Hafiz d’innan bai mata ba Amma yanda taga Baba yana yabonshi kuma ya nuna yanason alakanta dashi dole ta kula shi ko Dan son farincikin mahaifin nata.
Soyayyace da shakuwa ta fara shiga tsakanin Zarah da Hafiz Sosai yake nunawa Zarah soyayya da kulawa a nata bangarenma ta fara sabawa dashi saboda mutum ne mai barkwanci kullum yazo sai ya sanyata Dariya hakan yasa ta fara sabawa dashi Saidai duk wata sayayya ko kudi da zai bata bata tab’a amsa ba ba yanda baiyi da itaba amma bata amsar abun hannunshi.
ta bangaren Mama Rabi ko bakinciki take da Hafiz d’innan dake zuwa wajen Zarah ba irin Karfar da batayiwa Zarah a wajenshi ba Anma yace Eh yaji ya Gani yana sonta Dan kafin yazo wajen Zarah an bashi labarin Mama Rabi ko ita wacece da samarin da take korarwa Zarah.
Washegari Zarah ta tashi da ciwon Mara Wanda hakan ya tabbatar mata da perioud d’inta na kusa sosai hankalinta ya tashi Dan duk wata a darura takeyi saboda tsananin wahalar da take sha cikin Sauri ta sanya hijab d’inta tare da fitowa ta nufi gidan su Asmy
Dan bata mance irin sharrin da Mama Rabi take mata ba akan ciwon marar da take akwai lokacin da tace k’ilama cikine aka zubar mata ake mata rufe rufe hakan yasa ta maza ta zame tana zuwa gidansu Asmy Bayan ta gaishe da Mama a daddafe ta shiga d’akin Asmy Inda ta sameta ta na guga kwancewa tayi kan gadon ta na maida numfashi .
“Asmy ce ta ce ” Lafiya Besty”Gyada mata kai Zarah tayi tana ida kwanciya kan gadon ta ce “Da sauki dai perioud d’ina ne zaizo wlh na farajin ciwon Mara” Cike da tausaya Asmy ta ce “wayyo my Zarah Allah dai ya yaye maki wannan larurar Dan larurace wlh ace duk wata sai ka sha bak’ar azaba hada su suma ” .
bata Kara cewa komai ba Zarah saboda murdawar da cikinta ke mata ruwan zafi Asmy ta d’auko tare jika tsumma take Dan shafa mata a ciki sannan ta had’a mata tea mai zafi ta bata ta sha ciwon sai gaba yake Inda Zarah duk ta firirice ta fara fita hayyacinta kafin ka Ce me sai amai nan ta fara kwararashi Asmy dai Sannu kawai take mata Bayan ta gyara wajen mamansu Ce ta shigo ta ce.
“Lafiya Asma’u” cike da damuwa ta ce “Mama perioud din Zarah ne yazo” cike da kulawa Mama ta ce “wayyo Allah sauwake amshi ki maza ku tafi Asibiti ayi mata allurar ta fad’a tana mik’a mata d’ari biyar amsa tayi tare da kama Zarah dake murkashi .
mai napep ta fara tarowa tukwana ta zo ta kamata suka tafi asibitin da suka saba zuwa suna zuwa nurse din tayi mata allura daman ita ke mata duk wata ita kanta tana tausayawa irin wahalar da yarinyar takesha.
Sai wajen magriba Zarah ta samu kanta Taji ciwon ya lafa Asmy itake jinyarta kamar kowani lokaci harta gama perioud d’inta.
Yau ta na zaune tsakar gidansu ta na sintar gashinta aka Aiko akace ana kiranta ” to ta amsa ”
Mama Rabi na banka mata harara saida ta ida sintar tukwana ta mike tare da sanya Hijab ta fita .
” kamar yanda tayi tunani shi d’inne dai murmushi ya sakar mata Itama ta mayar masa da murmushin yak’e sun tab’a Hira sosai kasancewar yamma ce Sai wajen magriba da zai tafi kwalin waya kirar hot10 ya mik’o mata ya ce.
“tata ce saboda su dinga waya ko baya nan” nanfa Zarah ta ce bata San wannan zancen ba ba irin yanda baiyi da ita ba akan ta amsa amma takiya saboda bata da sha’awar abun hannun namiji kuma Baba ma yayi mata wannan kashedin Hafiz badan ranshi ya soba ya juya.
Zarah na d’akinta ta na karatu taji Asmy ta Banko k’ofar batayi aune ba saiji tayi ta Rungumeta cikin farinciki ta ce “Sis ki tayamu murna ina applying da Mukayi a wayar Mama kwanaki na A B U zaria to yanzunnan sukayo message sun amshemu sannan daman kinga ita ce first choice dinmu s jamb Ranar Monday ma zamuje muyi PUMB kai sis Kinga farincikin da nake ciki”
“Wow Zarah ta fad’a ta ce ” Gaskiya ni kaina nayi farinciki Sai kuma tayi sanyi ta ce “Sis nadai tayaki murna ammani kinsan bamu da halin da zantafi wata makarantar gaba primary da secondry dinma a yaya na yita ina da burin karatu mai zurfi amma dole na hakura saboda karatun yanxu na masu da shi ne ”
Lokaci guda asmy ta hade rai Tare da cewa “Insha Allah tare zamu tafi yanda muka fara tun daga pri tare haka zamu cigaba har university ai idan babuke nima wlh Saidai na hakura da makarantar kuma bari naje nayiwa Baba Bayani ”
sakin firar Zarah tayi ta Kama wata sun jima suna Hira kafin Asmy ta tafi.
Babansu Asmy ya samu Baba da maganar makarantar da su Zarah suka samu Inda Baba ya nuna masa baida ra’ayin tura Zarah karatun gaba Aure yake da burin yi mata tayi a gidan mijin ta ”
shi kanshi babansu asmy baiji dadiba ace yanda yarinyar nan take da tsabar kokari da baiwa Ta tsaya iya sec Dan shi kanshi yasan Asma’u ma Zarah ta taka rawar gani sosai a rayuwarta Dan yasan ba wani kokarin kirki gareta ba Amma tare da Zarah ya sanya itama take dagewa take kokari saboda kunsan ance shi abokin mai sayar da turare Shima kullum cikin k’amshi yake gashi yarinyar ya yaba da tarbiyarta 100%yasan ko makarantar suka tafi baida shakka a kansu saboda bazata bari Asmy tayi wani abun da bai kamata ba.
Koda yaje ya fad’awa Mama yanda sukayi da baban Zarah itama bataji dad’i ba Asmy ko hada kukanta nan ta tubure ta ce itama ta fasa zuwa makarantar.
gidansu Zarah taje tayi ta mata kuka akan dan Allah ta lallaba Baba ya barta sutafi tare idan kuma ba haka ba Itama ta hakura da karatun itama Zarah saida tayi hawayen d’an ba k’aramun so takeyiwa karatu ba.
Da dare duk tayi sanyi baba ya shigo gaisheshi tayi ya amsa tare da cewa .
” Dazu baban su Asma’u yake samuna da wata magana Wai ta karatu to Gaskiya na nuna masa Rashin amincewata saboda Har kullum burina Zarah bai wuce naga ranar Auranki ba naga na sauke nauyin da Allah ya doramun a kanki sannan na cikama mahaifiyarki burinta na Aurar dake sannan na had’aki da danginta kiyi hakuri Zarah bazan barki kije karatu har wani gari ba Kuma ma a halin yanzu bani da k’arfin wannan kiyi hakuri idan Allah ya sanya kinyi Aure sai kici gaba da karatunki gidan mijinki hankali kwance kinji”
Duk yanda hankalin Zarah ya tashi bata yarda ta nunawa Baba ba kasa tayi da kanta ta na mayar da hawayen da suka zubo mata ta ce.
“To shikenan Baba daman bansa haka a raina ba Allah sa haka shi yafi zama Alkhairi”
Ameeeeern y’ar Amanata Allah ya yi maki albarka ya jikan mahaifiyarki”
“Ameen ta fad’a kasa kasa saboda kar ya gane rawar da muryarta keyi ta na shirin fashewa da kuka Baba na fita daga d’akin ta fashe da matsanancin kukan da take rikewa .
batasan ya akayi ba da bata sa burin karatu a ranta ba Amma daga lokacin da Asmy tazo da maganar taji yanzu duk duniya bata da burin da ya wuce Karatu Sosai take kuka har saida kanta ya fara ciwo sai wajen 2 wahalallen bacci ya kwasheta.
washegari da ciwon kai ta tashi saboda kukan da tasha ranar sukuku ta yini ba walwala .
da Yamma koda Hafiz yazo yana kallonta yasan akwai abunda ke damunta da damuwa a fuskarsa ya ce .
“Me yake damunki ne my Zarah naga kamar kinyi kuka ” Kamar jira take take nan ta fashe da wani kukan da batasan yazo mata ba.
“subhanalla Zarah me yake damunki wani abun aka maki ” Saida ta tsagaita kukan tukwana cikin muryarta ta shagwabar da batasanma tayi ba ta ce…..✍🏿
*Hmm Kudai muje zuwa fans ba a fara komai ba wannan shi ake kira somin tab’i bama mu shiga cikin wasan ba wannan duk Bayan fagene*
_07026166536 domin magana da marubuciyar_
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ĘASA…*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ĘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huÉu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda Éaya N300
*DOMIN TURA KUĘIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ę³an Ęasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huÉu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda Éaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
~Share please~
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[8/22, 14:35] ❤️❤️❤️: 💑 *AUREN WATA TARA* 👨❤️👨
MALLAKAR
*Hajara L Sadeq*
*TEAM GAWURTATTU BIYAR*💃
🅿️………*9 & 10*
“Baba ne ya ce Wai bazanci gaba da karatu ba Aure yakeson yayi mun”
Yanayin yanda tayi maganar ne ya bashi Dariya saida ya Dan dara tukwana ya ce “My Zarah kenan rigima to meye a ciki ba saimuyi Auren mu ba Kinga ni bazan hanaki karatu ba daga degree har masters.
Turo baki tayi gaba ta ce ” nidai banason Auren karatu nake so”To kwantar da hankalinki gimbiyar mata anjima zanje na samu Baba da maganar insha Allahu zai amince.
Cikin Sauri ta d’ago ta ce “da gaske ya Hafiz” saboda haka take ce masa”murmushi ya sakar mata ya ce .
“Insha Allahu” zokuga murnar da Zarah tayi kamar ance Baba ya amince.Aiko ranar Duk miskilancinta ajeshi tayi itace hada Hira da Hafiz Wanda hakan ba karamun mamaki ya bashi ba.
Da daddare Hafiz yaje ya samu Baba da maganar karatun Zarah Inda ya nuna Rashin amincewarshi sosai Hafiz ya dinga yiwa Baba magiya akan dan Allah ya amince Zarah ta tafi karatun tunda ta na da hankali nutsuwa uwa uba Ilimi Sannan ya ce “Insha Allahu kuma Baba ni zan d’auki nauyin karatunta har ta gama”.
Shiru Baba yayi kamar mai nazari kafin ya d’ago ya ce ”
“bank’i taka ba yaro kozan iya Amincewa Zarah ta tafi karatu tofa Indai da gaske kake sonta ka turo magabatanka a tsaida maganar Aure duk lokacin da ta gama amma haka kawai sakaka bazanbar y’ata ta tafi karatu ba sannan Ko kana fara d’aukar nauyin ta tofa sainaji magana jinjina daga magabatanka”
“Alhmdllh Hafiz ya fad’a a ranshi daman wajen da yake jira akai kenan ” Nan take ya ce “Baba na Amince insha Allahu gobe magabatana zasuzo wajenka yanzu zanje na samesu da maganar”.
Ajiyar zuciya Baba ya sauke ya ce ” ba laifi”Ranar Hafiz cikin farinciki ya koma gida Koda ya samu iyayenshi da maganar basu wani kin Amincewa ba saboda sunsan Malam Yusuf Babban limamine da garin d’aid’aine basu sanshiba kuma sunsan mutumin kirki ne duk y’ar data fito daga wannan gidan tofa za a sameta da tarbiya.
a washegari magabatan Hafiz sukaje wajen Baba Bayan an mutunta juna Inda suka tsaida magana akan Lokacin gama karatunta za ayi Auren shi ma lokacin sannan ya gama masters dinsa hakan yayiwa kowa dadi musamman baba.
Zarah da bata San wainar da ake toyawa ba “saida dare Baba ya fad’a mata yanda sukayi ” Baka iya Tantance yanayin da ta shiga farinciki ko akasin haka Amma kuma idan ta tuno da makarantar da Baba ya amince saitaji dadi a ranta batasan ya akayi ba dai maganar Auren bata kwanta mata a rai ba.
Asmy ko koda ta samu labari hada tsallen murnar ta dan babanta dashi aka tsaida lokacin cikin farinciki ta je gidansu Zarah tare da Rungume juna suna murna ta ce.
“Gaskiya nayi farinciki wlh sis bantaba tunanin Baba zai sauko haka ba inye kaga amarya a gidan Hafiz d’inta” turo baki Zarah tayi tare da “Kai mata Bugu a baya ta ce “.
” kinsan bansan zolaya “Ranar kusa raba dare sukayi suna Hirar yanda Tafiyarsu makaranta zai kasance.
Hafiz ko koda yazo Zarah kin fita tayi Dan kunyarshi take ji shiko sai fara a da farinciki ya ke ji yake kamar anmasa Albishir da gidan Aljanna bai tab’a tunanin zai samu Zarah ba cikin Sauk’i haka ba.
Ranar Monday su Zarah suka shirya tafiya Zaria domin zana jarabawarsu ta FUMB Hafiz shi ya kaisu Har Zaria Inda ya jira saida suka gama tukwana Ya juyo dasu A hanya sai kallon Zarah yake yanda take sisinna kai a gaba ”
murmushi yayi tare da Kallon Asmy ya ce “Bestynmu yau fa mutuniyar Naga sarautar takeji ”
murmushi Asmy tayi ta ce “Naga alama kam inaga kunyarka takejifa ”
Harara Zarah ta watso mata daga gaban da take Wanda hakan ya sanya Asmy da Hafiz yi mata Dariya “Turo baki gaba tayi tare da Kallon hanya ”
har suka isa funtua suna Hira jefi jefi kasancewar ba wani nisa ke akwai ba tsakanin funtua da Zaria gidan su Asmy suka sauka Dan huce gajiya kafin ta wuce gidansu Ta na isa ta samu Mama Rabi na Surfa bala i ta na cewa.
“Aikin banza aikin hofi ko anzata bamusan iskanci da karuwancin.da ake a jami’ar ba To ayi mugani idan tusa zata hura wuta Aikin banza aikin hofi ” Sosai take jifar Zarah da mugayen kalamai Inda ita ko a kanta Dan itadai burinta bai wuce tabar gidan nan ta huta ba.
Cikin ikon Allah jarabawar su ta fito Kuma duka sunci sun samu admission Inda Zarah mass com suka bata saboda daman shi ta cike ita kuma Asmy suka bata Biology education .
zokuga farincikin da suka shiga Daga ranar suka fara sayayyar Tafiyarsu makaranta sun amshi kudin da Zarah ta samu a wajen sauka Inda suka sassayi kayan sawa dasu Komai iri daya suka saya da Asmy kala biyar biyar sukayi atamfofi suka saya Zane bibbiyu suka Kai d’inki ita kuma Mama ta d’inka musu manyan hijabai hurhudu saboda su Kara da nasu.
baban su Asmy shi yayi musu registration ba yanda Baba baiyi dashi ba akan ya bari zai sayar da tumakishi a kauye ya rage masa ya ce
“a.a daman shi yayi niyyar ni musu ai anzama daya ” Sosai Baba yaji dadi kuma yayiwa babansu asmy Godiya sosai Zarah ma tayi mashi Godiya kwarai da gaske yanzu zaman gidansu ma gagararta yake saboda koda yaushe suna gidan su Asmy suna shirye_shiryen tafiya saboda Abun na tunkarowa Dan yanzu wata Guda ya rage musu su fara lectures Wanda ji suke kamar su jawo ranakun”
*Wacece zarah*
*Zarah Yusuf* shine cikakken sunanta mahaifinta Malam Yusuf haifaffen garin Batsari ne Noma da kasuwanci shi ya kawoshi garin funtua kasancewarshi malamin addini .
ya samu karbuwa sosai a garin kasancewar lokacin Su ilimin addini bai wadatu ba Sosai sai ya kasance yana koyar da wasu manya magidanta karatu a masallaci Bayan kammala Sallar isha i kasancewar shine limamin masallacin Unguwar da masallacin juma’ar yankin”
wannan dalilin ya k’ara sanyawa mutane da dama suka sanshi a lokacin sosai Malam Yusuf yake da rufin asiri saboda gona guda ya ke amsar haya yayi shukar masara da wake Wanda alkhairi da yake samu ba Kad’an bane .
Bayan nan kuma daman yana kiwo a kauye ganin irin cigabar da yake samu a garin ya sanyashi sayan fili a unguwar jabiri Inda a hankali a hankali ya fara gininsa cikin ikon ubangiji har ya gama .
ana haka ne wata rana yaje Noma Ya hadu da wata matashiyar budurwa sai gudu take ta na hak’i sosai hankalinshi ya tashi kuma yayi mamakin daga dajin da ta b’ullo ga Saran maciji jikinta cikin Sauri ya taimaka mata Inda anan take ta sume kai tsaye Asibiti ya nufa da ita bayan an duba Saran da macijin yayi mata nan akayi mata allura aka bata magani.
Gidanshi ya koma da ita nan ya cigaba da kula da ita ganin har lokacin Bata farka ba gudun zargin mutane ya sanyashi daukarta ya tafi da ita garinsu Batsari Inda ya ajeta gidan baffanshi dan mahaifanshi sunjima da rasuwa a hannun kanin mahaifinshi ya taso nan aka cigaba da kula da ita harta farka Saidai me koda ta farka.
bata iya magana Saidai ta kalli mutane Cikin ikon Allah da addua da komai aka samu harta fara magana Saidai me duk tambayar da akayi mata game da Iyayenta ko y’an uwanta bata iya tuna komai duk yanda taso tunawa sai ta kasa.
hakan yana damun Malam sosai kuma yana tausaya mata gata dai ba wata babba ba Dan a lokacin bazata wuce 18 years ba Saidai abunda ya basu mamaki ta rik’e sunanta Zarah.
Saida Zarah ta shekara guda gidansu Malam batare da ta tuna kowa nata ba ga kuma karfaffar soyayyar da ta shiga tsakanin ta da Malam sosai suke San junansu Wanda lura da hakan ya sanya Baffa jin dad’i kanin mahaifinshi kenan Wanda shi ya tsaye musu har aka daura musu Aure.
ranar wannan masoyan sun shiga farincikin marar musaltuwa A funtua suka tare sabon gidan Malam da ke jabiri zamansu yaci gaba da wakana cikin soyayya da k’aunar juna saboda Zarah macece mai biyayya hakuri uwa uba Kirki Dan a zamanta da mutanen unguwar sai dai Sam barka Dan kowa Santa yake da kaunarta
aminiyarta d’aya a unguwar Saratu watau maman su Asmy a lokacin yarinyarsu d’aya Hauwa’u a lokacin suna cikin halin talauci Wanda hakan sosai ke damun Zarah hakan yasa bata iyacin Abu bata bata ba sunyi zama cikin mutunci da amintaka dukda Saratu ta girmi Zarah amma haka take girmamata kuma suke girmama juna.
“ana haka ne Zarah ta samu ciki Wanda tunda ta samu cikin takeshan wahala ta ke jin a jikinta cikin kamar shine ajalinta A tattare suka samu ciki da Saratu Inda lokacin mijinta ya samu warwara saboda daman yayi karatu Inda ya samu aiki a Bangaren agric saboda daman karatun malamin gona yayi .
kwana a tashi ba wuya wajen Allah a yanzu cikin Zarah ya shiga wata Tara Inda ranar wata Juma a ta tashi da nakuda kai tsaye Asibiti aka wuce da ita sosai take shan wahala tasan rayuwarta tazo karshe a lokacin ne kuma ta tuno da rayuwarta Ta baya Tana cikin halin nakuda ta ce ” .
a kira mata Malam “haka ko akayi shigowarshi d’akin tayi daidai da haifo santaleliyar y’arta sak mai kama da Ita kamar an tsaga Kara an karya.
Ajiyar zuciya Ta sauke Kallon nurse tayi dake shirin Tafiya don a shirya d’iyar tayi cikin k’arfin ta ce ” mik’omun naga kyautar da Allah yayi mun”
mik’a mata y’ar akayi Inda ta tsaya tana kallonta hawayen tausayin y’ar na zubo mata shafa kanta Tayi Tare da kissing din goshinta ta ce “Allah yayi maki Albarka Zarah ya sa mai taimakon Addini ce Ina sonki Sosai y’ata saidai Allah bai nufa Ba zamu rayu tare Allah ya shirya munke yayi miki albarka Albarkata taci gaba da bibiyarki har k’arshen rayuwarki ”
tari ne yaci karfinta Mik’awa Malam y’ar tayi tuni harta fara fita daga hayyacinta Tare da cewa ” ga Amanar y’ata na a hannunka Malam ka kula mun da ita ka bata tarbiya ka zame mata uwa da uba ka bata duk kulawar da zan bata ka bata tarbiya harka Aurar da ita Malam ga Amanar yata nan ”
a lokacin ne maman asmy ta shigo ita ma cikin kid’imewa ta nufi gadon tana hawaye ta ce “me kike cewa haka Zarah ai cuta ba mutuwa bace haka haihuwar take kowa haka yakeji”
Murmushin yake tayi tare da girgiza kai ta ce “bakisan irin abunda nakejiba shiyasa wannan ba zafin nakuda bane sannan ta kamo hannunta tana hawaye ta ce “Ga Amanar y’ata nan A hannunku ku rik’emun ita amana sannan ku bata tarbiya nasan zaku iya “.
” Malam ne da har zuciyarshi ta karye Ya fara hawaye ya ce “Bazaki mutu ba Zarah ta Insha Allah muna nan tare Harsaikinga auran Zarah da kanki zaki Riki y’arki” .
Kallon y’ar kawai take tana tari cikin k’arfin hali ta Ciro wata zoben gold dake hannunta Tare da awarwaron zinaren da dukansu tare aka tsinceta da su ta mik’awa Malam ta ce .
“idan y’ata ta girma har lokacin Aurenta ku bata wannan shine Babban abunda zai taimaka mata wajen gano Dangina lokacin da zan maku Bayani ya K’ure sannan ku sanya mata suna na Fatima Zarah sosai tarinta ya k’ara tsananta kafin kuma daga karshe suji ta fara Salati ta na Salati har ta cika.
Allahsrk mutuwa kenan mutuwar zarah ba Malam kadaiba hatta mutanen dake unguwar ta Girgiza su Malam ko Kullum kamar ba namiji ba haka zai zauna yayi ta kukan mutuwar zarah danma idan ya kalli y’arta sai yaji wani sanyi a ranshi tunda bata mutu ba har saida ta bar masa Jininta kuma photocopy d’inta Dan sak Zarah mahaifiyarta ce har dimple dinta sai kyau ma da tafi mahaifiyarta.
Kasancewar maman asmy itama ranar ta haihu saboda tashin hankalin mutuwar aminiyarta itama nakudar tazo mata Tasha kukan wannan Babban Rashin da sukayi ita ta Shayar da Zarah tare da y’arta da taci suna Asma’u ita kuma Zarah daman tun ranar da aka haifeta kamar yanda mahaifiyarta ta fad’a haka Baba ya sanya mata sunan mahaifiyarta Zarah “.
kulawa ta musamman maman asmy ta dinga bawa Zarah tare da Asma’u ta had’u ta dinga renonsu Malam ko yanzu baida wata jinjinar sana a saboda tundaga mutuwar zarah komai ya tsaya masa baya iya Zuwa ko ina koda akayi shekara biyu da mutuwan da zai koma harkar nomansa Ya samu Mai gonar har ya bawa wani haya nan ya dawo gida yaci gaba da tawakkali da Allah harya samu Aikin bakanikanci a wani garrage gyaran mashina da motoci Inda ya fara aikin A lokacin ne kuma danginshi suka fara korafin akan baiyi Aure ba yaci yayi Aure yanzu.
Inda ya hadu da Wata zawara rabi’atu da yaranta biyu a lokacin kamar mutuniyar kirki haka ya aureta tare da yaranta duk yanda zaiyi saiya ciyar dasu Inda Ya maido da Zarah gidan Wanda a lokacin ta nuna Duk d’aya ne a gaban idonshi zata nuna tafi kowa son Zarah Inda Bayan idonshi irin azabar da take gana mata kare baici Malam bai tab’a ganewa ba saboda Zarah ta tashi da wani irin hakuri kome za a mata bata tab’a fada masa ba.
ta haifi yaranta Biyu da Malam Safiya sai kuma khairat Azaba sosai take ganawa Zarah kasancewar ta sameta yarinya mai hakuri Wanda Malam baisan da hakan ba saidaga baya ya fahimta A unguwar ba Wanda baisan irin wahalar da rabi keba Zarah ba.
Malam ya tsayewa Zarah Karatun boko da na arabi Zarah yarinya ce mai baiwar kokari Dan kokarinta saidai a kirashi na baiwa saboda yanzu za a ayi yanzu za a kwashe duk karatun da tayi tare sukayi da Asmy Dan sun zama kamar y’an biyu kuma maman asmy ta rik’e Amanar da aminiyarta ta bata danma Mama Rabi dake azabtar da ita Yaran Mama Rabi duk sun lalace saboda Rashin tarbiya da bata basu ba khairat ce cikinsu kawai ta fita zakka zarah tunda ta taso ta fara perioud take shan wahala dan duk wata saidai akaita ayi mata allura irin fita daga hayyacinta da take har suma take sannan tana da larurar tsananin sha’awa mai karfi wanda wani lokacin abun ya taso mata saidai a bata maganin bacci wanda shawarar dr din da aka taba kaita wajenshi ne dan ya bata magani ya basu hakan .
wannan kenan.
*FCT ABUJA*
Manyan motoci ne na gani na fad’a Sunkai Sha biyar jere suke suna tafiya cikin gudu saboda bikin da za a gudanar na bud’e shahararren sabon shopping mall d’in da ya amsa sunansa.
Wajen shake yake da manyan mutane tun daga kan y’an kasuwa “shahararrun masu kudi da sauransu *MD SHOPPING MALL*naga an rubuta a saman ginin yanayin yanda akayi rubutunma kad’ai ya isa ya sanyaka Yin k’auyanci.
Waje ne da ya tsaru da kyau saika rantse ba k’asa Nigeria kake ba saboda yanda zakayi mamakin irin dukiyar da aka zuba a ginin ma b’ata lokaci ne.
Nan aka fara gudanar da bikin bud’e Wajen Bayan jawabai daga bakin manya da shahararrun y’an kasuwa Inda akazo ga jawabi wajen mai gayya mai aiki wato mamallakin wannan shahararren wajen watau Mustapha Dikko *MD* .
“hamshak’e ya ke a wajen banyi Tunanin yana jin hausa ba saboda kwata_kwata baiyi kama da hausawa ba Fari ne sosai kamar bature ko kuma ba indiye Sanye yake cikin bak’ar coated wacce ta amshesa ta kara fito masa da kyau da kuma hasken fatar sa kallo d’aya zakayi masa kaga asalin ba india
sanye ya ke cikin siririn farin glass sumar kan nan nasa lufluf gwanin sha’awa da burgewa ga kuma sajenshi Dake zagaye da kyakyawar fuskarsa daya kara kayatar da tsananin kyaun da Allah yayi mishi.
a gaskiya ni kaina saida na rude da ganin zubi da kyau irin na wannnan bawan Allah zan iya cewa tsawon rayuwa ta ko a film bantaba ga namiji da kyau irin haka ba duk inda karshe da baiwar kyau take tofa Yakai a kirasa da komai Dan guy din ya had’u karshen had’uwa (lol).
Daga zaunen da yake batare da ya mik’e ba ya amshi abun maganar tare da Fara jawabi cikin zazzak’ar muryarsa Yanayin yanda yake.maganar saika d’auka wani sautin wak’a ne mai ratsa zuciya ke tashi.
baiyi wata magana mai tsayi ba saboda shi daman Chan ba mutum bane mai fiya son magana da yawa ba Hasalima yanzu a k’agare yake A gama taron nan ya tafi dukda dalilinshi kowa yazo wajen amma ya k’agu saboda hayaniyar da ake a wajen dan shi ba mutum bane mai son hayaniya .
camera ce A kansa ta gidajen television da dama kowa so yake ya d’auka jawabin harya gama ana haskasa da camerori.
“Tsaki yaja yana kauda kai Dan ba abunda ya tsana irin taron jama a ”
jabir ne dake kusa dashi ya rad’a masa a kunne”Sorry bloody Dan Allah yau karkayi mana halin naga ka fara tsaki ka.daure har a gama bikin nan kasandai duk Wanda yazo wajen nan kai yazo tayawa farinciki”.
Lumshe ido MD yayi tare da bud’esu a hankali batare da yace uffan ba kamarma ba dashi jabir yake magana ba hakan bai damesaba saboda idan da sabo ya saba da halin aminin nasa Shidai burinshi Indai bazai kwafsa musu ba ya jira har agama falilllahil hamdu”.
Ba aja wani lokaci ba aka gama komai Inda MD ya Mike Security na take masa baya Sunkai su 30 yanda kasan wani president .
security gabansa haka bayansa ma sai kakkaresa ake nan fa y’an jaridu suka shiga d’aukar rahoto har ya isa motarsa Inda suma suka shiga motocinsu A motar ma tunda ya shiga Danna waya ya ke
“Jabir ne dake gaban motar da juyo tare da tambayarsa ya ce ” Ranka ya dad’e ina muka nufa”Kamar baya da shirin magana Ya ce “Airport” Ya fad’a yana cigaba da latsa waya kamar bashi yayi maganar ba “Jin haka ya sanya jabir ganowa Kaduna Zasuje kenan “.
Ko a Airport d’inma saida nayi mamakin irin yanda mutane ke kallonsa y’an mata har Tuntube suke suna cewa.
” wlh shine MD ne “wata har tsuma take tare da Rungume y’ar uwarta ta ce ” Alhmdllh Gaskiya yau rakiyar nan munzo a sa’a ganin mutumin Dan ban tab’a tunanin tab’a gani ba a rayuwa yau nagansa karkiga yanda nake da muradin ganin guy d’innan cikin Sauri ta d’auko wayarta tare da shiga snap daga nesa ta dinga daukoshi Dan tasan ko giyar wake ta sha bata isa ta tunkari wajenba yanda security d’inshi ke zagaye dashi.
Ba b’ata lokaci jirginsu ya d’aga Kaduna koda ya isa Kaduna Chan dinma haka ne Tsaki ya dinga ja shi d’aya saboda a Rayuwarshi ba abunda ya tsana sama da Kallo da kuma yanda y’an mata ke rudewa idan suka gansa Har suka isa Unguwarsu da ke G R A ya na Jan tsaki .
Horn biyu sukayi mai gadi ya Wangale musu Get d’in Aljannar duniya kenan gidane katoton gida mai girman gaske fad’ar kuma kyau da tsaruwar gidan ma b’ata baki ne Dan saimu cinye page Ukku zaku iya kwatanta gidan da gidan indimi.(lol)
Motoci biyar Duka suka danno gidan kai tsaye Ta tsakiyar ita ce tashi A hankali yake fitowa daga motar bayan ya fara ziro kafufuwanshi dake shanye da hadadden cover shoes koda ganin takalmin kasan ba na kananan mutane bane a haka harya karasa fitowa daga motar.
kamar Wanda baison taka k’asa ya fara tafiya securities d’insa ne suka biyo shi da hannu ya musu nuni da su dakata Kai tsaye hanyar Part d’in mahaifiyarsa Ya nufa Kafin ya k’arasa shiga Yaga fitowar Chuchu da gudu Tare da rugowa ta fad’a Jikinshi Sosai nayi mamakin yanda Ya sakar mata murmushi Wanda Ya Kara fito masa da baiwar kyawun da Allah yayi mishi ashe daman idan yayi fara’a yafi kyau yake tamke fuska.
“Shima Rungumeta yayi Tare da shafa bayanta ya ce ” I’m very glad to see you my Beloved sister “Cikin farinciki da muryarta Mai kama da ta masu iyayi ta ce ” me too yaya nafi kowa farincikin ganinka tunda akace ka taho nake ta zumudi” Ta fad’a ta na kama hannunsa Tare da janshi Dan su shiga ciki ta ce “Yaya muje kaga irin abubuwan da na shirya maka Dafota yayi kamar dafayya tun a hanya ta shiga fara zuba masa surutu Wanda har ya fara isarsa har suka isa tafkeken palourn ta na zuba masa surutu…….
ā
Name: | [ ] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |
Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV
Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi
Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi
Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram
Plz part two littafin ki nakeso na auren wata tara in ya fito kiyi tag dina
Dan Allah complete book na auren wata tara inyafito pls
Dan Allah complete auren wata t
ara
Don Allah complete auren wata tara
Dan Allah complete auren wata tara
Masha Allah Allah yakara basira
Pls auren
wata tara
GODIY